Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   15 / 72

42K to 45K   out of 214K words

yasan akwai abun da suka gani, ko mutun ko iska, ko maciji ko dai wani abu na daban to sukanyi wannan alamar dan sanar da makiyayinsu.
So ganin hakane yasa Lado ya ?ara kutso kai cikinsu.

Su kuwa dabbobin gaba Waya fiton da Ba'ana yake hurawane ya cika musu kunne, ai fa a take suka nausa a guje suka fuskanci gabas, da wani irin masifeffen gudu.
Shanu da dawakai na gaba tumaki da awaki na baya hatta belbelun dake cikinsu, suna kiwo binsu sukayi.
Cikin ?arfi Ya Lado yayi wani irin ihun wanda dashi suke kiran dabbobinsu, amman ina basu juyoba.

Da gudu ya fara binsu kana yana ihun neman taimako a wurin sauran makiyayan su.

Amman da yake gudun dabba dana mutun ba Waya ba,
Sun mishi nisa mai tarin yawa, hakanan shi kuma yayiwa sauran makiyayan dake biyoshi a guje su kawomishi agaji ya musu nisa.
A haka suka rin?a gudu,
waWannan mutun huWun dake laSene suka fito suka, tareshi ba zato ba tsammani kawai yaji an burma mishi wu?a juyowan da zaiyi kuma yaji an kuma burma mishi wu?a?e a tako ina na jikinsa.
A nan take ya faWi babu rai.

Su kuwa nan sukabi shanun da gudu.


Koda sauran makiyayan suka iso inda gawar Ya Lado take.
Hankalinsu yayi masifar tashi.
Tabbas sun san babu masuyi musu wannan aikin sai Sachama.
Ko han?o kurar dabbobin basayi.
Hankalinsu yayi mummunan tashi ganin gawar Lado, ga kuma tashin hankali da firgici rashin ganin su Gaini da GiWi da Seyo Manunu da Sale.
Junaidu ne yayi sauri ya kira mahaifinsu Ahaji Horo a waya ya sanar mishi halin da ake ciki.

Wannan mummunan labari yayi matukar firgita al'ummar Rugar Bani hankalin kowa ya tashi.

Hankali Bappa kuwa in yayi dubu to ya tashi,
kuka cur-cur yakeyi da idanunshi.

Junainah kam kuka da ihu harda burbuwa takeyi tana cewa.
"Wayyo Ya Lado, Bappa ku nemo min Ya Gaini na da ya Seyo".
Sai ta kuma faWa jikin Ummey daketa kuka tamkar ranta zai fita,
cikin kukan take cewa.
"Ummey kicewa Bappa suje su nemo min Ya GiWi na, kada su bari a kasheshi kamar yadda aka kashe Ya Hashimu da Ya Isa, da kuma Yaya Lado".
Babu mai iya bata amsa a cikin wannan gida.
Duk da tarin ma?ota da suka cika gidan.
suna zagaye da Inna wacce, take sume tunda taji yaranta Rai uku babusu babu dalilinsu su ko gawarsu ba'a ganiba ga kuma mutuwar Lado wanda shine yasata, sumewa.
FaWin tashin hankali da mutanen Rugar Kikan ke ciki bazai taSa misaltuwa ba.
Saidai ?unane wanda duk mai imani zai iya ?iyastashi a ranshi.

A cikin garin kuwa tuni ArWo Yabani yasa anyi shela anyi taron gaggawa, kowa ya shirya za'a shiga daji neman su Gaini, ko Allah zaisa a samosu.

Haka matasa kusufa-kusufa suka rin?a kusa kai cikin daji suna ratsa tsaununka da kozozzabai.


Bappa kuwa da ArWo Yabani da Ahaji Haro, da Ahaji Umaru ne da sauran dattawan rugarsu dana kewaye, gawar Lado suka Wauko suka dawo gida da ita da sauran shanayensu gaba Waya matasa kuma suka bazama nemansu Gaini.


Su kuwa sauran matasa majiya karfi daji suka rin?a ratsawa.
Amman babu koda kurar dabbobin nan, bare alamun su Gaini illa iyaka dai takalmansu da suka tsinto.

A Rugar Bani kuwa, hankali na matukar tashe, Bappa ya tasa gawar Lado a gaba wacce sunyi mata wonka sun kimtsata cikin sutura kamar yadda shariya ta tanadar.
Kuka mai tsananin cin raine ya kwabcewa Bappa, yana ruggume da gawar.
Inna ma da yanzu ta farfaWo da kukan ta farfaWo, kuka takeyi tamkar ranta zai bar gangan jikinta.
Hakama sauran matan ma?ota.
Hiden da Binto ma kuka sukeyi sosai a gidajensu sabida Sacewar samarin su.


Dattawan ne sukayi ta bawa Bappa ha?uri da tausan zuciyarshi.
Ganin dare yayine yasa akace dole a bar gawar tayi kwanan keso.

Su Sule, Iro, Ado, Junaidu, Madu, Ari, Sani, Ibi, ja'eh, Ori, Binbi, dama sauran samari majiya karfi kuma kab sun cikin daji.


Haka suka kwana a can. Suna tafiya suna nema, kafin gari ya waye, wasu sun isa har jihar taraba, wasu Gombe, wasu har bauchi, wasu har cikin iware da mutun biyu na taraba,
Wasu sun nausa da nisa, sabida in dai tafiyace bata taSa bawa bafulatani tsoroba domin anyi ittifa?in duk ?abilun duniya babu ?abilar da takai ?abilar fulani saurin tafiya da jumurin doguwar tafiyar ?afaba, bayan laraban da.


Washe gari Litinin.
Win, sauran dattawan garin suka sallaci Ya Lado, kana suka zauna amsar gaisuwa.
Suna kuma jin labarin inda yaransuke.
Ganin sunata wahalar tafiya ba lbrine yasa.
Bappa yace su dowo. Domin wanna abu addu'ace mgninshi.
Sannan kuma wannan karon bazasu saurari masarautar Numan ba , gangami zasuyi su kai kukansu, ga masarautar JoWa, wanda a cikinta ne GARKUWAN FULANIN ?asar Nigeria gaba Waya yake.
Da fari ArWo Yabani bai gamsu da hakanba saida Bappa yayi mishi bayanin.
Dolefa suna da bu?atar hukama mai tsarki ta shiga tsakaninsu da ?abilun ?achamawa nan, kana dole mgnar ta isa ga babbar masarautarsu, wacce za'a mi?a mgnar ga ?ungiyar *TABITAL POOLAKU, DA KUMA ?UNGIYAR.*
*MIYETTI ALLAHA*
Wannan dalilin ne yasa Ardo Yabani ya umarci gaba Waya matasan da suka bazama neman su Gaini su juyo su dawo gida.
Haka kuwa akayi kafin yamma sai gasu duk sun daddawo domin.
Wasu da yawa motoci suka shigo.

Bayan sallan ishane suka zauna zaman mitin domin sun gama shirya komai gobe dai kai tsaye masarautar JoWa zasu wuce.

Bayan sun gama tattauna yadda abun yake suka tsaida zance kan cewa dattawansune zasuje.
Daga nan Duk suka tashi taron kowa ya koma gidanshi da tarin al'hini a zu?atansu.


A can cikin birnin ?adamaya kuwa cikin makarantar su Aysha.

Zaune take bisa salla hannunta ri?e da carbi tana ja.
Kana hannunta Waya kuma rike da wayarta, wacce taketa kiran yayunta kab baya shiga tun jiya da yamma.
Cikin kula Rafi'a ta kalleta a hankali tace.
"Aysha ba komaifa, kinsan garin naku kunada matsalar Network, wasu lokutan kuma kinsan basu da cajine".
Kanta ta jingina da jikin gini, murya can ?asa tace.
"Gaba Waya fa, woyoyinsu basa, shiga, na ma?otanmu kuma ko sun shiga basa Wagawa, Rafi'a hankalina ya tashi."
Da sauri Rafi'a tace.
"No kada ki damu tunda kikaga basa Wagawa alamun kenan woyoyinsu na wurin cajine ko?".
Idonta ta lumshe tare da cewa.
"Zuciyata na yawan sinkewa Rafi'a, fargaba nakeji".
Cikin sanyi Rafi'a tace.
"Yauwa to ki kira Ba'ana mana".
Kai ta gyaWa tare da cewa.
"Eh hakane fa".
Ta karishe mgnar tana dannawa wayarshi kira.
Bugu Waya ana biyu ya Waga,
Da sauri tace mishi.
"Ina wuni ya Ba'ana".
Ba'ana dake zaune tsakiyar ?abilun ?achamawa suna mitin yadda zasu farma garin Rugar Bani da ya?in sun?uru gobe, murmushi yayi cikin sonta yace.
"Lfy lau Mata, ya karatu?".
Alhamdulillah tace tare da cewa.
"Ya Ba'ana ya garinmu ya lbrin gidanmu duk suna lfy?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Duk suna lfy garinmu duk anata kewarki Wazuma na wuce ya Ladonkin a kwance yanata shan baccinsa babu ruwanshi da damuwar duniya".
sam bata kawo komai a rantaba kan mgnarshi ta ?arshe, saima sanyi da ta Wanji daya bata tabbacin, suna lfy, sabida iya tsawon zamanta da Ba'ana bai taSa yi mata ?aryaba, koda zaiyiwa duk mutanen duniya ?arya to ita baya mata ?arya, kuma duk zafin gskyar mugun abunda yakeyi zai gaya mata. Abu biyu ya Soye mata a rayuwarshi sata da kisan da yakeyi, sai dai yana gaya mata in dai a kantane zai iya kashe kowa ma.
So cikin sanyi tace.
"To yasu Ya Gaini kuma".
Murmushin mugunta yayi tare da cewa.
"Shima na wuceshi wurin Binto sunata hirarsu har tanata raira masa wa?o?in soyayya".
Murmushi ta Wanyi tare da cewa.
"To ka gaida min su bari in Wanyi wonka".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To Mata kiyi wonkanki anjima zan kiraki muyi hira".
To tace mishi kana ta katse kira, tare da cewa Rafi'a.
"Alhamdulillah duk lfyarsu lau ashe".
Itama Rafi'a murmushi tayi kana sukaci gaba da hirarsu sai dai still fa tsoro da fargaba da bugawar da zuciyar Aysha keyi bai bariba, ganin hakane yasa Rafi'a, kallonta kasancewar Rafi'a ?wararriyar mai koyar da girgirkene, a zahiri cikin makarantar tasu, da kuma social media. Cikin kula da son samawa aminiyar tata nitsuwa tace.
"Yauwa GARKUWA, zomu shiga kitchin, muyi Wan alalan kwai, naga kin kawo mana koyaye da yawa."
Murmushi Aysha tayi wace, akefi kiranta da ?arshen sunanta.
hannun ta mi?a Rafi'a, cikin sanyi tace.
"Help me my friend, jikina yayi sanyi da yawa, ji nake kamar bazan iya tashiba".
haka nan itama Rafi'a jikinta ya fara sanyi, sai dai sanin in ta baiyana kasalarta tashin hankali Aysha zaifi tsananta ne yasa ta dake, cikin sauri ta kamo hannunta ta jata-ta mi?a kana suka shiga kitchin Win.
Nan suka fara aikin sunayi tana Wan janta da hira.
a haka dai har suka gama, kana, ta shiga wonka.

Shi kuwa Ba'ana maida woyarshi yayi cikin al'jihunsa, kana ya kalli Sarkin maya?an ?abilar Sachama da yake ce mishi.
"Shege Ba'ana wato, yana bacci cikin kabarinsa babu ruwansa da damuwar duniya".
Dariyar mugunta sukayi dukansu,
wanda yake gefenshi ne ya kece da wata dariyar tare da cewa.
"Wai ita kuma Binto kukan natane wa?en SOYAYYA ko?".
Kanshi ya gyaWa musu cikin muguwar fuskarshi.
Wannan matashin Waya fara sokawa Ya Lado wu?ane lokacin da suka kasheshi. yace.
"Ita kuma da yake sokuwace har ta yarda k...".

Wani irin tashi sukayi gaba Wayansu sabida wani irin sha?a da naushi da Ba'ana ya kai mishi, wanda a take ya fara kakarin mutuwa.
cikin zafin rai ya hankaWa tarin mutanen dake son cotan yaron daya sha?e Win amman ina sun kasa, wata zabgegiyar wu?a ya lumtsumamishi a ciki wanda yasa sauran duk suka watse tura gawarshi yayi gaban su cikin Waga murya yace.
"Ina kashe wanda ya yabi Shatuma yace yana son Shatuma bare wanda ya zageta, duk wanda baya son ransa ya aibata min Shatu a gabana ya gani".
Cit kake jinsu sabida masifar tsoronshi sukeji.
Dan ya fisu ta?adiranci dan Ba'ana mugun babarbarene mai ba?ar zuciya.

Haka dai aka tashi wannan taron da yake dama sun gama tattauna yadda zasuyi farmakin.


Washe gari ranar wata Tuesday 21 November 2017 itace ranar da har abada al'ummar Rugar Bani bazasu mance da itaba a tarihin rayuwarsu, itace ranar da duk motsin da numfarfashi Shatu zatayi sai ta tunashi ranace data girgiza, zukatan al'ummar musulmai, ranace da tasa duk wani bafulatani makiyayi jin ?una da tafasar zuciya.
Ranace da tada hankalin al'ummar ?asarmu nan dama ma?otanmu.

Tunda safiyar ranar, dattawan garin suka gama shirinsu cikin shigarsu ta al'farma, Malam Liman (Bappa) ArWo bani Jauronsu, Ahaji Horo da Ahaji Umaru, kana Malam Yero, da kuma Alhaji Sa'idu.
su rai takwas dai suka shirya cikin kamala da mutunci. Junaidu ne yake cikin Shikan ya samo musu mota kirar siyana wacce suka Wauki shatarta, domin zai kaisu har cikin fadar masarautar JoWa kuma zai jirasu. Su dawo tare.


Nan suka shiga Mota gaba Wayansu, suka tafi.

Kai tsaye har bakin masarautar suka tsaya dan an hanasu shiga,
sai da Waya daga cikin hadiman dake tsaron ?ofar, yaga duk manyan daddatawa ne yasa yaje ya samesu bayan sun gaisane sukayi mishi bayanin abinda ke tafe dasu.
Jin abin babbane yasa yaje yayiwa sarkin ?ofa bayanin.
Nan shima yaje suka gaisa suka ?ara jaddada mishi, zancen abinda ke tafe dasu, sannan
sukayi musu izini suka shigo cikin asalin farfajiyar mashigar masarautar.
Kan kujerun dake jere a wurin suka nuna musu su zauna.
Bayan sun zaunane sarkin kofa yaje, wurin sarkin fada ya sanar mishi, to nan sarkin fada ke cewa.
"To ai babu abinda zamu iya musu, tunda shi GARKUWAN FULANI, baya ?asar waye zai saurari kukansu, suje sai ya dawo su sake zuwa".
Cikin rauni sarkin ?ofa yace.
"Ranka ya daWe sarkin fada, da dai an nema musu izinin ganin mai martaba, domin bazaiji daWi ba in yaji sunzo kuma an medasu".
Cikin isa da izaya sarkin fada yace.
"A kul sarkin ?ofa ka tsaya iya matsayinka, kaje kace suyi maza su bar nan domin GARKUWANSU baya nan".
Cikin sanyi da mutuwar jiki sarkin ?ofa ya juya ya fita, koda yaje ya sanar musu, abinda sarkin fada ya faWa hankalinsu yayi masifar tashi.
Cikin tashin hankali ArWo Yabani yace.
"Shikenan danmu fulanine makiyaya mazauna daji, sai ya zama matsalarmu ba abar dubawa bace, wa al'ummar birane, duk inda muka kai kukanmu sai a koramu".
Cikin sanyi sarkin ?ofa yace.
"Kuyi ha?uri ba korarku akayiba, in sha Allah za'abi kadunku, wlh shi kanshi mai martaba in zaiji abinda sarkin fada yayi to zai barranta dashi, kuma haka nan shima GARKUWAN FULANI in da zaiji abinda sarkin fada yayi wallahi zai haWu da fushinsa mai tsauri, domin shi zuciyar Sheykh zuciyace mai cike da imani da tausayi".
Cikin rauni Alhaji Haron yace.
"Ana binmu ana kashemu, ana sace yaranmu ana kora dabbobinmu.
Munje Police station an koramu, da muka?i tafiya suka watsa mata tiyagas, muje masarautar Numan akaci mana zarafi, sannan yanzu mun gudo gareku da ya?inin zakubi kadunmu sannan kuma zaku koramu, so kuke mu Wauki makami domin ramuwa ne?".
Da sauri suka juyo gaba Wayansu jin muryar Jamil da yanzu ya iso wurin da hadimanshi, cikin sanyi yace.
"A a Baba kada ku Wauki makami domin ramuwa zuwanku nan shine babban abinda ya dace".
Cikin jin daWi suke kallonsa, murmushi sarkin ?ofa da sauran hadiman sukayi dan sun san yanzu dai sarkin fada bai isa ya hanasu ganin Maimartaba. Domin yanzu bai fito fada bama tukun so zasu ganshi a kebantaccen wuri na musamman.
Cikin kulawa da sakin fuska Jamil yace.
"Baba ku biyoni".
Cikin jin daWi sukace mishi to, kana suka bishi a baya.
Ta gaban shashin Sarkin fada suka shiga, kai tsaye har cikin fada ya shiga dasu,
shida kanshi yasa hadimai suka kawo musu ruwa.
Sannan a nitse yace.
"Baba ku zauna a nan zanje in sanarwa mai martaba, duk sanda ya fito daku zai fara, tattaunawa
In da masu bu?atan zagawa gacan wancan kusurwar in kumbi cikinta zata sadaku da bayi".
Cikin jin daWi sukace.
"Mun gode yaro Allah yayi maka al'barka".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.
su kuma sukaci gaba da zaman jiran fitowan sarki.


A can kasa mai tsarki kuma,
Sheykh ne zaune a gaban Sitti, kana Haroon da Jannart na gefenshi Sheykh Aliyu Abdulkareem, kuma da Sheykh Jabeer Aliyu da wasu manyan malamai na zuriyar tasu duk suna zaune a cikin falon.
Jazrah kuma na gabanshi da wani tray mai masifar kyau da tsada.
Madara da zuma take zuba mishi a cikin wasu ?an kananun kofuna masu masifar kyau da Waukan hankali.

Wannan ya kasance al'adarsuce ta baiyana nuna yarda da soyayya ko akasinshi, indan ana son a haWa yara aure, to za'a tattauna tsakanin manya, bayan sun gama dai-dai-ta magana tsakaninsu kamar yadda yanzu su Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen, da kuma su Sheykh Jabeer Aliyu da babban babansu Sheykh Aliyu Abdulkareem da kuma Sitti suka gama haWa zancen auren Jazrah da Sheykh Jabeer, to yanzu ta zuba mishi madara da zuma a gaban kowa, ta ajiye mishi, idan ya Wauki kofin madara to yana nufin yana sonta ya kuma amince da ita da aurenta.
In kuma ya Wauki kofin zuma, to yana nufin ya tsaneta baya kuma sonta bazai kuma auretaba bare ya zauna da ita.
Za'ayi komai a gaban manya ne, don suga zahiri kuma a tsarin ko Wan uwanka zai iya yi maka zaSin da kuma in dai am zaSa maka sai ka aura.

Shiru sukayi baki Wayansu falon, kowa da tunanin da yakeyi.

Sheykh Jabeer dake zaune a tsakiyarsu cikin shiga ta al'farma sai she?i al'kyabbar sa keyi, ga tattausan hirami a kanshi, ido ya lumshe daya gane manufarsu.
"Domin shi basu gaya mishi cewa, zasuyi wannan abun???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? bane daya sani wallahi da yasan duk yadda zaiyi ya gudu, ya tafi harami, har sai sun gaji sun watse.
A hankali ya kalli Sitti dake kallonshi cikin rauni da alamun.
"Dan Allah kada kace, a a yar Wan uwanane, kada ka bamu kunya nida kakanninka maza yar uwarkace kasan tarbiyarta".
Kauda idonshi yayi daga kallon Sitti, wani irin kallo yayiwa Haroon daketa yi mishi, murmushin muguntan yau dai an titseka baka da hanyar tsira.
Cikin ranshi yake mgnar zuciya.
"Ta yaya zan amince ince zan aureta? Dame zan zauna da ita?".
Sai kuma ya Wan fidda nannauyan numfashi.
"To idan ban amince da aurentaba me zamcewa, waWanannan bayin Allah'n da sukayi min dukkan gatan duniya, na zauna a gidansu tsawon shekaru masu yawa nayi karatuna har na gama, sukemin komai na rayuwa, suna nuna min soyayyar da mahaifinama baya nuna min, da wanne idon zan kallesu inna Wauki zuma alamar na tsani yarsu?".
A hankali ya buWe idonsa, jin muryar. Sheykh Aliyu Abdulkareem kakan Mamanshi kenan, baban kakarshi Sitti dottijon daya yake sonshi tamkar ranshi yana cewa.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoWa, kayi zaSin da ranka keso, bamu da nufin yi maka dole, sai dai ina da burin aurar maka jikata Jazrah Wiyar mai sunanka. Ina so da fatan ganin nasabarka ta cika, cikar nasabarka kuwa, shene aure."
Wani irin sassanyan numfashi ya sha?a a hankali, wasu irin zafafan tunanuka ne ke zirya a zuciyarshi".
Cikin harshen hausar katsinawa, Haroon yayi mgna can ?asa yadda ko Sitti bazata jisuba.
"Sheykh kafa, shanyamu, nifa zan Waukar maka Madara".
Ido ya lumshe tare da Wan jingina da jikin kujerar da yake zaune, wanda yake kusa da Sheykh Abdulkareem.
Sitti ce ta Wan kalli Haroon tare da mishi alamun ya taSo Sheykh.
cikin harshen larabci Haroon ya kalli kakar tasu, tare da cewa.
"Sitti ai nasan zaSinsa, bari ki gani in nuna miki".
Ya ?arishe mgnar yana kai hannunshi kan kofunan.
da sauri Sheykh Jabeer ya buWe kekkyawar ?wayar idanunshi da wasu ke kiransu da zaiba, wato kamar idon mage, idon ya Wan zaro ganin Haroon yasa hannunshi kan kofin M...!




=??=??=??=??=??

Masu cewa na kulle musu kai kada ku damu zan kuce kawunanne, lokaci ne=??=?O???
By
*GARKUWAR FULANI*
=???
=??=?J?????=?
?>?4?
*GARKUWA*

PAGE 12

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

=??????>?4?


Littafin GARKUWA na kuWine turo katin mtn na Wari uku ta wannan number 09097853276. KO

15 / 72