Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   56 / 72

165K to 168K   out of 214K words

so nake in ba matsala ko zamu rin?a yin abin buWa baki ana kaiwa masallacin, da kuma bawa bayi nasu daban".
Bai kulata ba, asalima yamutsa fuskarshi yayi, ya lura wannan abar bata gama iya sanin makamar mgna ba, ji yadda take mgn a kaikace.
Kamar ba ba fullatanaba, bayan anyi ittifa?in bayan larabawa babu ?abilar dake da luggar iya sarrafa harshe sama da Fulani.
Shiru tayi tare da tura baki kana ta Wan murguWashi, tare da cewa.
"Ayyah ka amince mana?".
kanshi ya sunkuyar tare da Waga system Winshi ganin biyu dai-dai ta cika.
Mi?ewa tsaye yayi tare da motsa lips Winshi a hankali yace.
"Eh". Da sauri ta juya ta fita tana hararan bayanshi.
Shi kuwa bedroom Winshi ya wuce.

Rage kayan jikinshi yayi kana yasa hannunshi ya jawo pillow'nshi ya wurgar can gefe gaban gadon inda babu carpet,
a hankali ya kwanta a wurin,
Gudun kada daWi gado yasashi yayi baccin da zai makara sallan la'asar, Yana konciya ba jimawa yayi bacci.

Ita kuwa cikin jin daWin amincewar da yayi, tacewa Ummi.
"Ummi ya yarda yace muyi".
Mi?ewa Ummi tayi tare da nufar kitchen a tare suka shiga.
Tana cewa.
"Yauwa to taho mu gayawa Saratu abinda za'ayi.

A tsaye suka sameta a tsakiyar kitchen Win kusa da kitchen table, tana gyara ganyen.
"Yauwa Saratu kin wonke shinkarfa masan ne?".
Kai ta gyaWa tare da cewa.
"Eh na wonke,kuma mafa tun Wazu da nazo kuna kuma bacci na ji?a wani, sai dai hannuna ya zarce yayi yawa, yanzu ina gama tsinkar ganyen zan kai markaWen ne in na dawo an kwaSashin sai in fara firan Arish Win".
Ajiyan zuciya Ummi tayi tare da cewa.
"Mugamshin".
Babbar robar dake gefenta ta jawo tare da cewa.
"Gashi kinga yayi yawa wlh mancewa nai sai naga kamar na gidan Gimbiya Aminatu zan ji?a shiyasa, kinga da na haWa da wanda kika ji?an yayi yawa sosai, ko zamu rabashi biyu".
Murmushi Shatu tayi ganin shinkafar tanada yawa, kai ta gyaWa tare da cewa.
"Ba matsala hakanma yayi dama mai yawan akeso".
Kai ta gyaWa tare da cewa.
"Ga kuma ?ullun na dafa tun Wazu har yayi sanyi, shiyasa nake sauri in kai markaWen naga lokacin yayi nisa".
Motsowa tayi inda take tare da cewa.
"?auki markaWen ki kai bari in ?arisa wannan aikin".
Cikin mamaki tace.
"A a bar".
Da sauri ta katseta da cewa, jeki".
To tace cikin mamakin sau?in halinta ta Wauki robar ji?e??iyar shinkafar da ta kai mudu biyar har ta Waura a kai,
Ta kuma sauke jin Shatu na cewa.
"Yauwa naga akwai murjejjiyar gyaWa, Webo, da wata shinkafar kizo ga dabino da kwakwa a nan ki haWa ki jikasasu ki tafi dasu, na kunune kafin a markaWa wannan na masan shinma ya ji?a sai a markaWa miki shi.
Da sauri ta juya tayi yadda tace Win tanayi tana nuna mata dai-dai yadda takeso, saida ta gama kana rufe babban roban da marfinshi sannan ta Waura ?aramin a kai ta tafi.

Ita kuwa Shatu matsowa tayi taci gaba da tsinkan ganyen, ita kuma Ummi freezer'n ta buWe tare da Webo kayan ciki mai yawa, tazo.
Ta won?eshi fes, kana ta watsa al'basa mai yawa a ciki, Sannan tasa citta,kanamfari, cory tare da sauran kayan WanWanon.
Gas ta kunna ta Waura tukunyar, sannan ta dai-dai-ta wutar.

Wani babban roba ta Wauko kana ta nufi Store Arish ta Webo mai Wan yawa tazo tana fereshi cikin Wan injin Win firar lokaci Waya tayi nisa a fitar.
Ita kuwa Shatu tana gana gyaran ganyen ta Webo kayan miya tazo ta jajjagasu yadda takeso.
Kusan a tare suka gama da Ummi.
Wankeshi Ummi tayi bayan ta yishi tsillk-tsillk kana ta sashi a tukunya, tare Wan yaryaWa gishiri, ta rufeshi.
Ta ajiye gefe.
Ita kuwa Shatu cikin kula ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi me za'ayi da ganyen?".
"Miyan da za'aci masar dashi".
To bata amsa tana komawa cikin Freezer'n fruits ta Webo.
Tazo tana wonkesu tare da shiryasu cikin tray mai girma, kana ta shirya wasu kuma a wani Wan madaidaicin tray mai masifar kyau.
rufesu tayi kana taje tasasu cikin Fridge.

It's kuwa Shatu can nama ta Webo dai-dai misali won?eshi tayi tasa a tukunya tare dasa kayan ?amshi dana WanWano.
ta Waura a wuta. Ummi kuwa ruwan tea ta Waura a Waya murhun dake gas Win babbane.

Naman na sulaluwa ta kwasheshi tasa mai saida yayi zafi tasa al'basa,
ya soyu yana ?amshi kafin tasa jajjagen kayan miyar ta,
Ya soyu kana ta ?ara won?e ganyen miyar yazo tasa, ta soyashi da kyau.
kana ta zuba naman da sauran ruwan miyan.
Tasa duk sauran kayan hadin ta rufe tukunyar.
Sosai Ummi tayi mamakin yadda ta haWa miyar, to sai dai bata damuba sabida sanin ko wacce mace da yadda take sarrafa girkinta, kai yadda kakeyi daban in wani ya gani yayi mamaki, yadda wani keyi da ban in ka gani kayi mamaki.

Cikin ?an?anin lokaci dai suka haWa duk aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba.
Ita tayi miyar masan, ta kuma ?arisa ferfesun kayan cikin da Ummi ta fara.
Ummi kuwa ta tafasa musu tea ta WuWWura a flaks,
Kana ta tafasa Arish Win.
Dai-dai lokacin kuma Saratu ta dawo.
Ita Ummi ce ta Wan amshi ?ullun masar tare da cewa.
"Gskya mun Wan makara aikin Masar nan gashi ni hannuna baya tashi da wuri".
Da sauri Shatu ta matso tare da mi?awa Ummi roban markaWen kunun.
Tace.
"Ba matsala Ummi ni hannuna na tashi da wuri.
Yanzu tace mana mar?aden kunun bari in kwaSa mana Masar."
Haka kuwa akayi Ummi ta fara tacewa.
Ita kuwa kulun dafaffiyar Wanyar shinkafar ta murmusa cikin mar?aden Masar,
Kana tasa fulawa tare da yis kaWan sannan ta tarfa gishiri kaWan.
Kana ta rufeshi a robar dan babbace, motso da robar tayi kusa da Gas Win yana Wan jin Wumin wuta.
Gefen Ummi ta dawo wacce ta gama tace markaWen
A babbar tukunta ta zuba shi kana ta Waura kan wuta tare da dai-dai-ta wutar tanayi tana motsa kunun.
tare da Wan tarfa wanda ta rage, da surkin lemun tsami.
Cikin Sa'a Waya ta dama kunun shinkafar fari ?al tamkar madara.
Sugar tasa ta juye a a ?atuwar kula kana tasa a maidaciyar kula, Sannan tasa a flaks Waya, sai kuma tasa a Mug mai marfi duk ta kimtsasu gefe.
Tuni Side Win ya Win ke da ?amshi miyar masan da ferfesun nan.
BuWewa tayi ganin miyar tayine ta sau?e ta maida gefe.
Kana ta kalli Ummi tace.
"Ummi je kiyi salla la'asar tayi, in kin dawo sai inje inyi".
To Ummi tace ta fita tana mamakin saurin aikin Shatu.
Koda taje tayi sallan ta dawo ta sameta tana sau?e tukunyar ferfesun.
ganin Ummi yasa tace. "Yauwa Ummi komai yayi dai-dai yanzu kaskon tuya zamu daura kinga kullun ya tashi".
Cikin mamaki Ummi ta kalli Robar da taga har kullun na shirin zubewa.
Ita kuma Wiba tayi a wata roba kana duk tasa yankekken al'basane a ciki Sannan tasa sugar ta gauraya,
sannan ta matso da kasko biyu,
juyowa tayi ta kalli Saratu tace.
"Yauwa Sara matso. Ke ki rin?a yi kina sawa a wannan babban kulan in ya cika kisa a wannan shima.
Ummi ke kuma kisa mana namu anan suyanki mukeson ci".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"To jekiyi salla".
To tace kana ta fita.
Ita kuma Ummi ta juya ta kalli Sara tare da cewa.
"Kema kije kiyi salla".
Cikin ci gaba da aikinta tace.
"Ai nima nayi".
"To shike nan". Ummi tace kana sukaci gaba da tuyan.

A falo ta haWu da Hibba da Jamil, sai dariya yakeyi cikin dariyar yace.
"Yauwa Aunty Shatu dama idonki nazo in gani, dan ga Hibba kam ta kusa kasawa".
Murmushi tayi dan bata da sauran ?arfin yin dariya.
Cikin Wan fito da idanunta da suka Wan faWa tace.
"Gani ras dani".
Dariyar ?eta mai cike da alamun yunwa da ?ishi yayi tare da cewa.
"Inafa ras kalli yadda idonki ya fito kamar kinyi azumi goma".
Murmushi tayi kana tace.
"Um bari inje inyi salla".
Sai ta kuma kalli Hibba dake lankwabe tace.
"Sannu Hibba kwanta ki huta".
Jalal da yanzu ya shigone ya Wan taSe baki tare da cewa.
"To me tayi da zata huta tunda fa gari ya waya in anga ta tashi dai yin salla ne, tun tuni birgima take a tayis wai sanyi take nema".
Dariya sukayi mata baki Wayansu,
Ita dai Shatu ciki ta wuce.
Salla tayi kana ta fito. Koda tazo kitchen ta samu Hibba na suya musu Arish Win, tayi mamaki.
Cikin wasa tace.
"Kawo in karSeki jeki kwanta".
Cikin sanyi tace.
"Ai Hamma Jabeer ne yace min in ina aiki bazanji wuya ba, zanfi ganin lokaci ya gudu".
Dariya sukayi mata kana kowa yaci gaba da aikinshi.
Ita Shatu miyar sahur na asuba ta Waura musu.

Cikin ikon Allah shida dai-dai suka gam kan aikinsu.
Bayan Shatu'n ta taya Hibba suya kwai daban, ta jerasu a Foodflaks, in ta ajiye fefeyin soyayyan ?wai da yaji haWi da diddigin kifi, sai ta zuba soyayyan Arish a kai kana ta kuma rufeshi da fefeyin kwai haka ta rin?a jerasu saida ta cika kulan.

Ummi kuwa ta sawa Saratu komai nata.

Sannan suka kimtsa wurin fes suka fito da komai suka jera a dinning table.

Nan duk suka wuce Wauki.
Wanka sukayi, kana sukayi al'wala sannan suka fito falo. A nan suka samu Imran, Jalal, Jamil, Sulaiman.
Cikin gajiya Ummi tace.
"Yauwa Jalal ku Wauki manyan kulolin nan ku kai masallaci.
Sauran madaidaitan kuma ku ajiyewa sarkin bayi.
A bawa bayi da hadimai".
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
"Eh lallai bana bayi sun samu uwar gijiyar data tuna dasu, bayan kuma anayi musu nasu na daban".
Cikin lumshe ido Shatu tace.
"Eh suma suci abinda muke dafawa da kanmu, ba sai na gandun nasuba".

Mi?ewa sukayi suka Wauki kulolin sun zo falon kenan Sheykh na shigowa, wani hadimi na biye dashi da manyan ledodi cike da ?a?an itatuwa.
Kusan a tare suke mishi sannu da dawowa.
Murya a bushe alamun ?ishi yake amsa musu kana ya nunawa Ummi leda Waya yace.
"Ummi a wonke wannan a haWa da dabino mudu uku a basu su kai masallaci".
Ya ?arishe mgnar yana wucewa.
Da sauri Ummi tace to.
Ta mi?e kenan Shatu tace.
"Ummi zauna bari in wanke sun".
To tace kana ta koma ta zauna.
Ita kuma taje ta wonke ta zubasu a tray kana ta Wauko plates and cups masu yawa, tazo ta mi?awa Imran.
Da sauri suka amsa suka tafi.

Jim kaWan suka dawo, cikin gajiya Jamil yace.
"Ummi ansha ruwafa mun samu Ladan na cin dabino".
Da sauri Hibba ta mi?a tare da cewa.
"Su ladanannan haka suke basa kiran salla sai sun sha ruwa."
Dariya sukayi mata kana suma suka mi?e sukabi bayanta.

Zama sukayi bisa kujerun kowa da abin yake hari.
Sai dai kab Wibsu da dabino suka fara.
Ummi ce ta kalli Shatu tare da nuna mata babban tray'n da aka shirya komai na buWa cikin Foodflaks guda 3 madaidata masu kyau, sai plate Win da aka shirya fruits masu Wan karen sanyi, tupa, inabi ,kankana, abarba, gwanda, Lemu, ayaba, kana da dabino, da kwakwa,
Sai goran zam-zam madaidaci, kana sai cup da tea spoon a ciki, sai fork and knife a gefe da gefen plate Win dake cike da fruits Win komai biyu akasa.
Kulolin kuma Waya masane a ciki, Wan namiyar kuma miyar Masar ne, sai Wayan kuma, soyayyan ?wai da dankalin, Wayan kuma ferfesun kayan cikin ne.
Cikin nitsuwa Ummi ta Wago tray ta mi?a mata tare da cewa.
"Yauwa gashi kai mishi lokacin shan ruwan na tafiya, yanzu zakiga ya fito".
Cikin sanyi da gajiya ta amshi tray'n kana ta nufi falon nashi, cikin nitsuwa take takun, a hankali tayi sallama tare da kutsa kai cikin falon.
A can bisa Dinning area ta hangoshi yana zaune, kan kujera Waya, ya kuma jawo Waya kujerar ya Waura sawunshi a kai ya mi?esu, System Winshi na bisa cinyarshi.
A hankali take takowa saman steps Win tare da ratsa cikin jeren ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar she?in Daimond sai sunkuyar da kanta tayi sabida Wauke mata ido da suke.

A hankali ta isa kusa dashi, cikin tura baki tare da Wan murguWashi ta ajiye tray'n, a tsakiyar table Win.
Wago kanta tayi da niyar ta Wan juya, ta fita.
Wani irin buWe idanin tayi gaba Waya tare da zubasu, bisa sharaban ?afarsa ta dama, wanda sanaWin zaman da ya Wan yi ya mi?e ?afafuwan nashi bisa Waya kujerar ne yasa suka Wan baiyana, wani irin kallo mai cike da Wimuwa takeyiwa zanen dake bisa ?afarshi ta dama, da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannun hagun ta kama kanta sabida wani irin sarawa da ya farayi da ?arfi.
Cikin sauri ta juyo tare da mi?a hannun damanta ta sau?eshi kan...!





Akwai kayan gyara na amare da uwar gidaye da masu jego, ga mai bu?atar saya ga number ta 09097853276



By
*GARKUWAR FULANI*
=???
*GARKUWA*
NA

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

=??????=?
?>?4?
ASSALAMU ALAIKUM. MASOYA NA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA, WA?ANDA SUKA BIYA DA WA?ANDA KE KARANTA NA SATA, INA MUKU FATA ALKYAIRI da fatan muna lfy, kana kuma ina mai bawa dubban mutanen da sukayi min mgn ta kafafan sadarwa kamarsu, WHATSAPP, FACEBOOK, INSTAGRAM, WATTPAD, BAKAN?AMIYA, WASUMA A TIKTOK daga jiya da yamma zuwa safiyar yau ha?urin rashin basu amsar tambaya Waya dai da aketa memeta min. GARKUWA WAI KIN SAIDAWA ?AN HAUSA FILM LBRIN GARKUWA? WAI DA GASKENE BAZAKI ?ARASA MANA LITTAFINBA? TO DUK GA AMSARKU NAN. Alhamdulillah, ngd matu?a da kulawarku. Kana ina mai baku tabbacin EHHH TABBAS NA SAIDA LITTAFIN GARKUWA GA ?AN HAUSA FILM KAMAR DAI YADDA KUKAGA YAKETA YAWO, TABBAS NA SAIDASHI WA ?AYA DAGA CIKIN MANYAN INDOSTIRI. DA IZININ UBANGIJI ZASU JUYASHI ZUWA FILM MAI ZAMAN KANSHI, IN LOKACIN YAYI KUMA ZAN SANAR MUKU. DA FARI NASO IN SIRRANTA ZANCEN NE, SABIDA SEDA MUSU DA NAYI BAWAI YANA NUFIN BAZAN ?ARASA LBRIN GARKUWA BANE, ZAN ?ARASA MUKUSHI HAR ?ARSHE DA IZININ UBANGIJI. TO SAI DAI NAYI MATU?AR MAMAKIN YADDA AKAYI MGNAR TA FITO FILI TA BAIYANA HAR TA BAZU, domin naso barinta sirrin kai da kaina sabida gudun kada hankalin makaranta na ya tashi. To amman ba komi ku kwantar da hankalinku masoya na zan ?arasa GARKUWA lfy lau. Kana suma ?an film zasuyi abunsu lfy lau. Duk wacce ta/ya sayi littafin GARKUWA sun san uzurina da yasa kwana biyu bana Update, so ku kwantar da hankali ku, in sha Allah ni AYSHA Wiyar ALIYU GARKUWA, Jikar Malam Muhammad Babayo mai Murare. Zan ?arasa mukushi lafiya in Allah ya aramin rai da lfyar.
KUYI HA?URI WA?ANDA SUKAYI MIN MGN TA PC BABU TABBACIN ZAN BIKU ?AYA BAYAN ?AYA IN BAKU AMSA.

FATAN AL'KHAIRI MASOYANA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA WA?ANDA SUKA BIYA DA WA?ANDA KE KARANTA NA SATA>???p?=??>?p?=??. Dan naga masu karanta na satan ?arfin halinsu yawa gareshi, har ?ar guntuwar nasiha sukemin wai kada in zalinci mutane na fara musu ban ?arasa ba>?#?>?#?=??. ?an Adam kayan Allah ana Wauke damu muna Wauke da halayenmu>??>??>??>??.Ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar she?in Daimond da yayiwa wurin labule.
Yayin da kuma hankalinta da idonta duk suke kan ?afar tashi tana kallon zanen da take gani har kamar motsawa yakeyi a jikinshin, da kuma suffar macijiya.
A hankali ta Wago ?afarta tare da take step Win forko, hankalinta kuwa duk yana baya, har ta juya kanta gaba Waya sam ganinta baya gaba.
Cikin rashin sa'a kafar ta tsallake step Win forko bata isa kan dandamalin ta biyu ba, ta sauketa, cikin akasi ?afar ta sule tare da yin shuuuuu tayi gaba.
Wani ?ara mai Wan karfi irin na maiyin azumi ta sake tare da rumtse idanunta da ?arfi tana jiran taji ta ina Win ta zai karye.
Wani irin ihu ta kuma sakewa, lokacin da taji ta faWi gib a kan stpes Win kanta ya bugi dandamalin sama.

A hankali ya juyo kanshi ya kalleta a fakaice,
Ba tare da yace mata ko ?alaba ya juyar da kanshi ya fuskanci tray'n data ajiye mishi, plate Win fruits ya Wan buWe kana, ya Wauki Fork Waya, janye ?afafuwan shi, yayi ya sau?o dasu ?asa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci Dinning table Win da kyau.
Fork Win yasa ya fasa cikin dabino da yake irin na kwali nanne mai laushi ne,
ture Wan yayi gefe kana ya soki dabinon a hankali ya kai bakinshi, bayan yayi addu'o'in buWa baki.
Ido ya lumshe jin lokacin da sanyi da za?i da WanWanon dabinon ya game mishi baki.

Ita kuwa Shatu kuka tasa tare da ri?e ?ugunta, da kanta cikin muryar kuka take cewa.
"Wayyo Allah na. Wayyo Ummey na, bayana ya karye ?uguna ya Salgace, kaina ya fashe ?eyana ya tarwatse".
Ta ?asa Glass Win table Win ya Wan kalleta, kana ya maida kanshi yaci gaba da cin dabino, yana maijin wani irin masifeffen dariya na taso mishi jin raki da Shatu ke zubawa.
Saida yaci ?waya bakwai, kana a hankali ya fara tsira Fork Win kan ?a?an inabi masu masifar sanyi da daWi, ci yakeyi yana jin ?ishin daya addabi mo?oshinsa na wucewa.
saida ya tsinke nonon inabin kab ya cinye, kana ya fara soka kankana da akayiwa ?a?anan yanka kana aka barbaWa garin madara a samansu, shima shanye rabinshi yayi.
Wani sassanyan gyatsa yayi tare da ture tray'n gefe.

Ita kuwa Shatu sosai taji zafin faWuwan ga azumi ga gajiyan aiki ga faWuwa ga haushin yadda duk ihun da tayi babu wanda ya kulata, bare a kawo mata agaji, abun ya haWe mata sai hawaye share-shere ta tabbatar da a gidansu ne tayi wannan ihun da gaba Waya iyayenta da yayunta da ?anwarta duk suna kanta, da tuni an Wagata a wurin ma.
Bege da kewa da kukan rashin yan uwanta da watseman ahlinsu ne ya tunzura hawayenta.
Ta kasa tashi sabida jikinta duk rawan yunwa da gajiya yakeyi ba ?arfi sam.

A hankali ya mi?e tsaye bayan ya sha ruwan zam-zam mai Wan sanyi kan ?a?an itatuwan da yaci.
System Winshi ya ajiye kan Dinning table Win, tare da wayarshi.
Gefenta ya Wan ratsa ya fara taka steps Win tare da kallonta a fakaice.
Yana gab da sau?ane ya Wan motsa lips Winshi tare da cewa.
"KaWan kenan in dai baki dena samin ido a jikina ba,
FaWuwa harda kareireyewa zakiyi in baki kiyayi yimin

56 / 72