Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   47 / 72

138K to 141K   out of 214K words

martaba LamiWo,
inda bishiyoyin tarihi dana gargajiya da magunguna suke.
Forko bishiyar Goruba suka fara sassa?an jikinshi.
Wanda shine babban makarin dukan shaWun.
Sai kuma suka haWa da wasu tsirran,. Koda suka gama kai tsaye gefen Jakadiya da sauran ma biyanta suka nufa,
Nan suka bata dukkan abinda suka Webo, suka kuma yi mata bayani.
Kana sukace maza ta haWa su ta dafa,
Sauran kuma sai sun dawo LamiWo ya shiga Wakin sirri ya Webosu.

Cikin tsananin tashin hankali da rawan jiki Jakadiyarsu ta amshi magunguna, ta nufi sashin Jabeer Win.
Cikin gaggawa ta shige kitchin Win shi, ta fara harhaWa magunguna tana dafawa.


A can cikin motar kuwa cikin tashin hankali Ya Hashim yayiwa Dr Aliyu duk bayanin abinda ya faru da halin da Jabeer ke ciki.
Ya ?ara da cewa, a shirya komai na bashi taimakon gaggawa.
Jin hakane yasa Dr Aliyu tada motar Ambulance wanda take nan cikin asibitin dake cikin makarantar nasu, tazo bakin asalin babban gate Win masarautar nasu.
Kana ya kira babban abokinshi Dr Sanju wanda ba indiyene wani aikine ya kawoshi ?asar,
tuni suka iso bakin gate Win, cikin motar Ambulance Win suka shiga suka zauna tare da haWa duk wani abu na taimakon gaggawa da za'ayi mishi.


A cikin motar kuwa, gaba Waya ya gama yage rigarsa ya fizge wonWonma ya yageshi fata-fata.
Ganin wani irin kallo da yayi Haroon ne, yasa Haroon yin maza ya matsa tare da yin mgnar zuci.
"Ka gani ko LamiWo hegen tsoho kai ka dace ka zauna kusa dashi.
Inma yagawarne ya yage ka".
A zahiri kuwa fuska ya Wan haWe tare da cewa.
"Kafa gama yaga kayanka yanzu nawane suka rage a jikina, naga ji kake kamar ka yagamu, yaseen to bamu muka kar zomonba".
Dai-dai lokacin kuma, sarkin ?ofa ya buWe musu ?ofar babban gate Win.
Kana suka kutsa kai. Suna shiga ko parking basu gama dai-dai tawa ba
Jabeer ya sa hannu ya buWe marfin motar, ?afarshi ya zuro woje,
wanda ganin haka yasa Dr Aliyu ya fito da sauri.
Sai dai kafinma ya fito tuni Jabeer ya fito cikin motar ya nufi asalin ?aramin gate Win da zai sadaka da asalin cikin farfajiyar.
Kusan a tare suka fito daga motocin gaba Wayansu.
Cikin tsananin tashin hankali Ya Hashim ke ?walla mishi kira, amman ina bai ko juyo inda sukeba.
Baya kuma jinsu sosai sabida duhu da jirin da yake gani.
Da gudu Haroon da Jalal Jamil suka biyoshi a baya cikin rauni Jamil ke cewa.
"Hamma Jabeer dan Allah ka tsaya Baba Aliyu zai dubaka, kaga fa har yanzu jinin bai daina zuba ba."
Ina ai baya tare dasu tafiya kawai yakeyi, ba tare da yasan inda yake jefa ?afarsa ba.
Ganin hakane Dr Aliyu ya koma cikin Ambulance Win ya jata ya nufi inda yake, sai dai tuni har ya shiga cikin asalin farfajiyar.

Haroon, Jalal, Jamil, Hashim, Wan Barrister Kamal Sulaiman, da Imran, duk suna biye dashi a baya da dudu-gudu da sassarfa.
LamiWo da tawagarsa kuwa, koma sukayi cikin motocin sukaja, suka nufi cikin gidan.

Shi kuwa Sheykh Jabeer tuni ya isa bakin side Winshi.
Cikin tsananin rawan jiki da duhu ya kusa kanshi ciki.
A babban falon ya samu Jakadiyarsu, tana ganinshi ta mi?e tsaye cikin tsananin tashin hankali ta tsaya ganin ya Waga mata hannunshi Waya, kana yasa hannunshi Waya kuma ya dafe kanshi.
Cikin wani irin kerma yake wani irin taku da jan wani irin dogon numfashi ya nufi part Win shi.
Yana shiga falonshi na musamman, su Haroon na shiga babban falon.

A nan su Jamil kan suka tsaya, shi kuwa Haroon da sassarfa yabi bayanshi.
Yana shiga falon nashi ya hangoshi ya shiga bedroom Win shi.
Ya kuma maida ?ofar ya rufe, kai tsaye bathroom ya wuce yana shiga wani irin duhu ya rufe idanunshi a hankali ya tafi...


A can Rugar Bani kuwa, kuwa Junainah har ta shiga kitchin ta sunkuyo zata Wauki akoshin naman gasassun zabbin, sai kuma ta fito a guje.
Kai tsaye inda ake gasar ShaWi ta nufa, haka ta rin?a kutsawa cikin taron, har ta isa gaba-gaba kusa da ya Salmanu, ganin irin dukan da akeyiwa wannan kekyawan mutumin data ganine yasata kuka da ihu.
Kukanta ne yasa Salmanu kuka, ya kuma ja hannunta ya fito baya da ita.
Hannunta Waya ri?ene yaji yadda jikinta ke karkarwar kamar mazari, bayan yayi sujjadar ya Wagone.
Yace mata maza ta koma gida.

A haka ta koma tana kuka.

A inda ta bar Shatu dasu Rafi'a da Ummiy anan ta dawo ta samesu.
Kai tsaye kitchin Win ta nufa, da sauri ta Wauko akoshin ta fito ta nufi inda suke, cikin rawan jiki ta sunkuyo ta sau?e musu akoshin ta ajiye a tsakiyarsu, kana itama ta zauna a kusa da Ummiy dake jingine da jikin bishiyar mangoro.
Jiki na rawa tasa hannun ta janye fefeyin da aka rufe akoshin da shi.

Wani irin lumshe ido Rafi'a tayi, sabida wani irin ?amshin daya buWe hancinta,
Ummiy kuwa ido ta zubawa akoshin tana jin yawun bakinta na tsinkewa,
Shatu kuwa gyara zamanta tayi sabida wani irin azabebben ?ugin yunwa da cikinta yayi.

Cikin sanyi suka gyara zamansu gaba Waya, a hankali Shatu ta ri?e hannun Junainah cikin zubda hawaye tace.
"Jeki wonke hannunki sai kizo, da plet da ?aramin akoshi mu Wibawa Bappa mu sawa Ummiy a plet Win".
Cikin sanyi ta tura baki kana ta mi?e tsaye, gindin randunarsu ta matso, yar ?aramar butarta ta Wauka ta wonke hannunta, sannan ta nufi cikin madafarsu.


Tana shiga ta Wauki ludeyi da ?aramin akoshi kana da pilet sannan ta fito.
Tana fitowa tazo ta zauna gabansu, ta mi?a Shatu, cikin sanyin jiki tace.
"Bawa Rafi'a ta Wiba musu, wlh jikina duka rawa yakeyi".
Amsar pilet Win Rafi'a tayi ta fara Wibawa Ummiy rabin zabuwa.
Kana ta sawa Bappa gudar da romonta,
Tana cewa.
"Garkuwa yunwace fa, ace mutun ya wuni ya kuma kwana baici komaiba ya kuwa wuni ba abinda yaci ai dole kiji jiri, gashi yawan kukan da kikeyi ne yasa miki zazzaSi."
Ta ?arishe mgnar tana rufewa Bappa nashi kana tace.
"To muci".
A tare suka saka hannunsu cikin akoshin.
Junainah ce ta fara yago tattausan farin tsokar ?undun zabuwar cikin haWiye min yau ta kai hannunta bakin t....!



Dan Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina, in kinsan Zaki fitarne gaya min in baki kuWinki, dan Allah.


By
*GARKUWAR FULANI*Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa,
Kamar an watsa mishi ruwa.
Ya kamo lip Win shi na ?asa yana taunewa.
Hannunshi dake cikin blanket ta zubawa ido.
Dan son gano abinda yakeyi,
shiru tayi sawon 5 minute kana, a hankali ta Waura tafin hannunta kan goshinta,
tare goge mishi zufar, daketa tsastsafowa duk da sanyin A/C dake ratsa Wakin.
Idonshi ya saisaita lumshe su da yayi, ya sani Umaymah ce.
sabida babu mai shigar masa Waki kai tsaye sai ita.
Babu kuma mai taSa mishi goshi haka sai ita.
Cikin kula tace. "Jazlaan!".
A hankali ya gama buWe idanunshi da sukayi jazir alamun tarin ?una da yakeji a ransa.
A hankali tace.
"Jazlaan!." Ta kuma kiranshi a karo na biyu.
A hankali ya motsa lips Win shi alamun zai amsa mata.
Amman Ina zafin da zuciyarshi keyi ya danne harshensa hafimtar hakane yasata, nuna damuwarta a hankali tace.
"Kaci abinci?". ?arya ba Wabi'arsa bace ba kuma halittarsa bace, duk Wacin gsky zai faWeta, bare a kan kashi.
Kanshi ya girgiza alamun baiciba.
Cikin sanyi tace.
"To Muje kaci koda abu mara nauyi ne!."
Da ?arfin ya fizgo mgnar.
"Bazan ci ba".
Ta sani yadda yayi mgnar, ta kubce masane, dan in ransa a Sace yake baya mgna, Sacin ran mai limini kenan babu faWe-faWe bare hargowa ko buge-buge.
Sanin ko ya zatayi bazai cin bane, kamar yadda ya faWa mata yasa,
ta mi?e a hankali kanshi ta shafa tare da cewa.
"Saida safe".
Kai kawai ya iya gyaWa mata,
Haka ta fara tafiya, tana kallon yadda yake motsa hannunshi cikin blanket tabbacin. Wani abun yake yagewa.

Yadda ta bar Haroon haka ta sameshi saida safe tayi mishi kana ta wuce ta tafi.


A can Rugar Bani kuwa. Kamar yadda Ba'ana ya Waukarwa kanshi al'?awari haka ya bar ?asar ya nufi ?asar Cameroon Kai tsaye Yahunde ya nufa, cikin rugagen Fulani, yana tafiyarne da Wan sauran tsafi da sihirin dake jikinsa.

A haka ya nausa cikin ?asar Cameroon da yake jihar ?adamaya tana bakin bodar ?asar ne.


Fulanin Rugar Bani kuwa, a daren wannan ranar sukayi gangamin ramuwa, suka faWawa ?auyukan kafuran ?abilun Sacamawa dake cikin Shikan da kewayenta.
Allah ya basu nasarar ya?an kafuran nan.
Har suka samu damar ?ona ?auyem Bonon wanda shine zuciyar ?abilar Sachama, kamar yadda Abuja take zuciyar Nigeria.
Cikin daren suka ?ona ?auye dama dodon tsafinsu Bonon da suka Wauka a matsayin Ubangiji su sun ?onashi sun Sadda shi a doron duniya sai dai tarihinsa.

Wannan labarin shine labarin.
Da gidajen rediyo dana tv da jaridu sukayi.
Breakfast dashi yayinda akayita kuzuzuta cewar Fulani sun zama ?an ta'adda sun farma garuwa da ya?i.
Uhummm wannan shine halin da Fulani ke rayuwa a ciki. A zalimcesu, kaji cib duniya babu mai yin mgn su kai ?orafinsu a koresu. Gwamnatin kasar data jiha suyi kamar basujiba. In fulanin sun rama na lokaci Waya sai asa musu sunan ?an ta'adda ko yan tada zaune tsaye, har ana ikirarin korarmu.=?-?=?-?=?-?

Hankalin ?abilun ?acamawa dake cikin Shikan duk suka ari ta kare.
Hausawa da Fulani kuwa kowa ya koma, cikin gidansa.
Domin Allah ne yabi kadunsu.

Sarkin Shikan da kanshi yayi masifar girgiza da yawan da Fulani sukayi cikin garinshi da kewaye.
Gashi an ?one dodon tsafinsu nasu kuma babu abinda ya samu fulanin.
Hakane yasa shi kanshi ya arce, sai abu ya lafa ya dawo.


Su kuwa Fulani bayan sun gama.
Suka tsaya suka bawa yaransu da tsoffinsu mafaka, domin su basu kashe yara da tsoffi da mataba.
Anyi an gama, kafin hukuma tazo, ta ?ara sai saita Komai.


A cikin masarautar JoWa kuwa. Washe gari da safe.
Lbrin ya rinski Sarki Nuruddeen, shine ya bada umarnin kada a kama bafulatani ko Waya.

Aysha ce zaune gaban Umaymah Aunty Juwairiyya na gefenta ita da Hibba, cikin kula Umaymah tace.
"Yauwa Aysha kinga wannan ki Wauke ta matsayin yayarki ita Win yar babban Yayanmu ne wanda na nuna miki jiya.
Mijinta kuma ya'yan Jabeer ne, Side Winta na kusa da naku.
In kinga duk wani abun da baki fahimta ba ki tambayeta, in kin gaji da zaman kaWaici zaki iya shiga wurinta, da wurin Mamanku, da kuma nan wurin Gimbiya Aminatu".
A hankali ta Wan kalli Aunty Juwairiyya, tare da cewa.
"Ina kwana Aunty". Cikin jin daWi Aunty Juwairiyya tace.
"Lfy lau ya ba?unta". A hankali tace.
"Alhamdulillah!".Hibba ce ta Wan tsuke baki cikin sanyi tace.
"Shike nan ai, an gabatar mata da kowa sai ni aka ware".
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"To Aysha ga Hibba wutar Umaymah, duk family itace auta a jikokin Sitti na nan ?asar".
Murmushi ta Wan yi sabida ganin yadda Hibba tayi sai Junainah ta faWo mata a rai.
Ita kuwa Hibba motsata tayi tare da cewa.
"My happiness".
Cikin murmushi Aysha ta nuna kanta, alamun "Nice my happiness?".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Yes haka Umaymah tace wai kece farin cikin ahlimu da izinin ubangiji".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta.
Haka nan taji tana jin sonsu a ranta, Especially Umaymah da Hibba.
Aunty Juwairiyya kuwa da Ummi breakfast Suka gabatar mata, kana suka fita.
Umaymah da kantane ta haWa mata tea mai kauri ita da Hibba kana ta zuba musu abincin da Aunty Juwairiyya ta kawo musu tare da cewa.
"Bismillah kuci abinci".
tana faWin haka ta mi?a ta fita,
Ita kuwa Hibba da tsauri ta gyara zamanta tare da Waukan Fork ta matso gaban plate Win da aka zuba mata soyyyan dankali da kwai, hannun tasa ta soki guda biyu tare da Wagowa zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya tare da zubawa Aysha ido ganin ta ri?e mata hannunta.
Cikin sanyi da Wan sakin jiki da Hibba ta girgiza mata kai tare da cewa.
"Kada kici wannan abincin".
Cikin juya ido Hibba tace.
"Meyasa!?".
Kai ta jujjuya mata kana ta gyara zamanta, tare da Wan kallon ?ofar shigowa ta gefen idonta.
Wani kekyawan Foodflaks da aka kawo daga sashin Gimbiya Saudatu ta jawo tare da cewa.
"Ki Wiba a nan kici". Cikin mamaki.
Hibba tace.
"Aunty Aysha, ai Bama cin abincin gidan Gimbiya Saudatu, kuma naga Hadimanta ne suka kawoshi".
Cikin rashin gane manufar zancen Hibba tace.
"Meyasa bakwa ci?".
Juyawa Hibba tayi ta kalli bayanta kana ta juyo ta kalleta da kyau kana a hankali tace.
"Bata son Hamma Jabeer dama duk ?an uwanshi, cewa take zata kasheshi in ta samu dama, shiyasa Umaymah take hanamu cin abinci ta".
Wani irin nannauyan ajiyan zuciya ta sau?e tare da kallon Hibba cikin cushewar tunani ta kalli jerin kulolin da a ?alla sun kusa takwas a gabansu.
Cikin sanyi tace.
"BuWe su mu gani".
Jin hakane yasa Hibba buWe su Waya bayan Waya.
ita kuwa ido take zubawa duk kular da Hibba ta buWe.
Kular ?arshe wacce ke Wauke da Chicken Ball's mai zafi sai turiri yakeyi da ?amshi.
ta nunawa Hibba tare da cewa.
"Kici wannan".
Murmushi Hibba tayi kana tace.
"Yauwa shinema na Gimbiya Aminatu kuma ta iya girki tsohuwar hakana hadimanta, a plate ta zu musu. Kana suka faraci suna Wan korawa da ruwan tea mai zafi da kauri.
Sunaci Hibba nata janta da hira duk da ita Aysha zuciyarta a cushe yake.

Bayan sun gamane, Hadiman Gimbiya Aminatu suka shigo suka tattare komai suka gyara wurin bisa umarni Jakadiya.

Ganin Aysha ta Wan saki jiki da Hibba ne yasa, Umaymah ta wuce Side Winsa ita da Umminshi.


A falo suka samu Jafar, Jalal, Jamil, Haroon. Suna bisa kujerun Dinning area, Aunty Juwairiyya tana zuzzuba musu abincin.

Murmushi Umaymah tayi cikin jin daWin ganin su, da wal-wala hatta Jalal fuskarshi a sake take.
Jamil ne ya kalleta lokacin data ?ara so kusa dasu, cikin murmushi yace.
"Umaymah mu sai yaushe za'a nuna mana Amaryar a gabatar mata damu, ta sanmu da kyau".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ai ku tun daren jiya nagabatar da sunayenku da matsayinku gareta".
Haroon ne ya Wan kurSi tea tare da cewa.
"Yo ai Ni dai ba sai an gabatar daniba, domin nasanta tun safiyar jiya kafinma a Waura auren ko Jalal?".
TaSe baki Jalal yayi tare da cewa.
"To ni mamaki nakeyi, ko dai dama ita tazone dan taga wanda za'a aura mata".
Umaymah ce ta Wan zauna kusa da Jafar tare da kallonsu kana tace.
"Babu sam ita kanta bata saniba bata zata ba bata tsammaci aurenta a jiyaba.
Sai dai arashi kukayi, Ni tun jiya da kuka gayamin nasan arashi ne kawai ya haWaku a asibitin. Bata san komaiba akan auren nan hakama iyayenta, basu da zaSine kawai dan sun san ?a'idar gasar ShaWi ne hakan yasa sukayi ha?uri."
Kai Jalal ya jinjina tare da cewa.
"Uhummm mu dai yanzu yan kallone. Dan na sani tabbas yanzu za'a fara buga Game Win yanzu wasan zai soma".
Cikin yin ?asa da murya Jamil yace.
"Sosai ma, dan kuwa akwai kitimurmurar da za'ayi a masarautar JoWa, wannan Ustaz Sheykh Malam akarmakallahu Hamma Jabeer Win, salonshi na dabanne a dukkan lamuran yauda kullum wannan auren dai zamuga ya zai kasance!". Ya ?arishe mgnar da yin ?asa da murya sosai, yanayi kuma yana kallon hanyar falon Sheykh Jabeer.
Cikin haWe fuska na wasa Umaymah tace.
"Al'khairi shine zai wanzu".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"Inafa al'khairi a wannan abun da bashi da tushe, ni kaina naji ba?in cikin wannan al'amari, auren Muhammad Jabeer ya zama kamar a munafuce a Soye babu wani shiri bare kimtsi kun bari an auro mishi mace kamar auren ?ar tsana".
Jafar kam abincinsa yakeci, ba tare da ya kulasuba.
Jamil kuwa sai murmushi yakeyi.
Jalal kuwa shiru yayi alamun nazari.

Ummi kuwa ware wasu kyawawan Foodflaks takeyi gefe.
Tare da abinci a cikinsu.

Bayan ta gamane ta ajiyesu gefe.
Tare da cewa Umaymah.
"Ga breakfast Win Sheykh".
Kai Umaymah ta gyaWa mata.

Nan sukaci gaba da hira.

A can Side Win Mama kuwa,
Tunda batun auren Jabeer ya basu ya riski kunnuwan ahlin masarautar JoWa,
kowa da abinda ke ransa.

Batool kuwa hankalin Mama in yayi dubu ya tashi, bisa irin kukan da Batool ketayi har cewa takeyi ta gane ai dama Mama bata son ya aureta.
Da kyar ta samu tasha kanta,

Gimbiya Saudatu kuwa, da Baba Nasiru da Baba Basiru da Laminu.
Zaman gaggawa suka tanada.

Suna tattauwana wannan ba?in lbrin da bai musu daWi ba.


Zaune yake gaban wani ?asur?umin boka matsafi.
Cikin tsantsar tashin hankali da kiWima yace.
"Boka Tsitaka haka mukayi da kai? Yaushe ka fara min ?arya kan aiyukan da nake baka? Ya za'ayi kwatsam rana tsaka ace wannan shegen yaron da nakeji tamkar in kasheshi yayi aure? Da kai mukayi mgna a nan tsawon shekaru kace min ka, kashe min wutsiyar Wan iska mai jajayen kunnuwa, babushi ba mace har yaumal ta ?unun nadi.
Ka bani tabbacin. Har gobe sihirin na bibiyarshi, kace min duk sanda zanen kan macijin ya isa kan tsaitin ?ahon zuciyarshi zai mutu kowama ya huta. Sai kuma jiya kamar sau?an aradu ace yayi aure!".
Wata iriyar razanenniyar dariya mara daWin amo boka Tsitaka ya kece da ita, wanda har saida tsaunuka da kwazazzaban dake wurin suka amsa amonta.
Dariyar mugunta yakeyi babu ?a??autawa, har saida ba?on nashi ya fara hatsala cikin tashin hankali yace.
"Wannan ai insakanci ne, in bazaka iyaba ina nemo wasu matsafan. Ya zan zo da matsalata da sanyin safiyar nan kai kuma ka kama min dariya, Ni mahaukacin gidanku ne?".
Cikin dariyar boka Tsitaka yace.
"To ai tashin hankali na banzane, kana kokonto kan aikin da shekaru goma sha biyu yana cinsa yana bin jikinshi. Kana zaton ya karye ne? To bari kaji wannan sihiri yana nan a jikinshi, har kwanan gobe wutsiyarsa bata harbawa, baya jin kanshi a namiji.
Ba kuma zaiji yadda maza kejiba har abadan.
Iya bincikena banga mai mgnin da zai gani aikin da mukayi mushiba.
Auren da akayi mishi, da ya sani tabbas da zai watsa abun. In kuwa kana zaton sihirin yana sau?a kaje ka dubu, zanen bindin maciciyar da yake tun daga kan ?ar babbar ?atsar ?afarshi ta dama, zaka samu kan macijiyar ya ?etare ?ugunshi.
Na kuma gaya maka duk sanda kan macijiyar ya isa kan ?irjinshi, saman nononshi, zai mutu, kuma yadda zai bar duniya haka ?annenshi da wanshi zasubar masarautar JoWa har abada yadda ba'a tambayi yaushe matacce zai dawo duniyaba haka suma baza'a tambaya ba."
Cikin Wan jin daWi ba?on bokan yace.
"To ai dole hankalina ya tashi, kaida kace min bazai wuce shekaru biyar ba zai rasu gashi yanzu shekaru goma sha biyu bai mutuba".
Cikin zare ido boka Tsitaka yace.
"Kai ai mun ma yi dacen yin asirin da wurine, tun kafin ya gama girma da yanzune sam bazai kamashiba, mutumin da baya rabuwa da sunan Allah

47 / 72