Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   43 / 72

126K to 129K   out of 214K words

tashi kaje ka taimakawa yan uwanka musulmai! in kuma baka da lfy ne ka nemi bokaye irinka su duba lfyarka".
Zuwa yanzu gaba Waya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi sabida yadda ta konkotsa glass table Win da kanshi ke kife a kai. Ga kuma sautin muryarta da yake jinshi har tsakiyar kanshi.
Da sauri ya Wago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi na zaiba.
Cikin sauri Haroon ya matsoshi ganin idanunshi sun cika tab da ?walla sai she?i sukeyi alamun suna iya zubda ?ollan a ko wanne lokacin.
Cikin harWewar murya ta larabci yacewa Haroon.
"Please ka fitar da ita a nan, ta matsa kaina zata fasa min dodon kunne".

Ita kuwa Shatu cikin tarin mamaki da al'ajabi ta zaro manyan idanunta tare da cewa.
"Laaah!". Sai kuma ta fara Wan ja da baya tare da cewa.
"Afwan baka da lfy ne!?." Wani irin fitinenne murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"Eh baya jin daWi ne, Wan fita zamu kira wasu bokayen suzo su dubashi".
Cikin sauri tace.
"Subahanallahi bokaye kuma?".
Kai ya gyaWa mata tare da cewa.
"Yesss ba haka kikace ba, ya nemi bokaye ?an uwanshi su dubashi".
Kanta ta Wan dafe tare da cewa.
"No kada ka munana min zato, ina nufin likita bokan turai ka gane ko?".
Da sauri taja da baya ganin Jabeer ya mi?a tsaye da ?arfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsayuwanta kusa dashi barazana ce ga zuciyarshi tabbas zata iya faso ?irjinshi ta fito.
Ganin yadda ya haWe fuska ya nuna mata hanyar fitane, yasa ta juya ta fita.

Shi kuwa Jabeer komawa yayi ya zauna tare da sau?e wasu tagwayen ajiyan zuciya a jere a jere.
A hankali yake jin bugun zuciyarshin na Wan dai-dai-ta kamar dai yadda yaji kafin ta shigo.

Sai kuma ya fara jin zuciyarshi na tsinkewa ras-ras kamar dai tana tsoron kada wani abu yayi nesa da itane.
"Ya ilahi ya mujibadda'awati ya hayyu ya ?ayyum".
Sune kalaman da Jabeer yaketa maimatawa a saman lips Winshi.

Haroon kuwa wani irin kallo yakeyi ma Jabeer mai cike da nazari.

Jalal ma kallonshin yake cike da tarin mamaki duk da sun san baya son akeyin mgn da ?arfi a kanshi, to amman idonshi bai taSa ciko da hawaye ba, sai yau.

Ita kuwa Shatu, ido ta zubawa Rafi'a da ta tsareta da ido, cikin yin ?asa da murya tace.
"Rafi'a dama, wannan shugaban tuzuran ?asar nan, yana aiki anan asibitin gwamnatin jihar nema?".
Kamo hannunta Rafi'a tayi tajata sukayi gaba.
Haroon kuwa dariya yayi sabida, duk da rage muryarta da tayi sunji abinda tace, sabida wurin da suke Win yanada amsa kuwar amo.

Cikin yin ?asa da murya sosai Rafi'a tace.
"Garkuwa ki nitsufa ki rufa mana asiri, kin ko san waye wannan?!".
Shiru sukayi dukansu lokacin da suka juyo wata kekyawar mata tana bawa wasu ?an mata Nurses a ?alla sun kai goma lbri.
Ido Rafi'a da Shatu suka zubama wannan matar cewa.
"Shi wannan Dr Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoWa, ba kamar sauran mutane bane, shi mutunne da Allah yayi masa wasu baiwa da nasabobi masu tarin yawa".
Wata ?ar kekyawar cikinsu ne ta Wan lumshe ido tare da cewa.
"Allah ya sani Aunty ina sonshi, ina son wa'azin shi, muryarshi kawai in naji yana zuba larabci sai inji bani da sauran damuwa a duniya, sai dai shi kuma yana nan kamar dutse!".
Da sauri Matar nan tace.
"Ai bazai yiwuba, wlh bazai taSa kulakiba, duk nacinki da korkosarki, shiyasa wasu ke raWe-raWin shi waliyi ne!".
Numfashin ta sau?e tare da ci gaba da cewa.
"Duk matsayinki, kyanki, mulki, sarauta, gata, ilimi!. ko da meye kike ta?ama dashi a duniya ya fiki abin".
Kusan a tare suka haWa baki wurin cewa.
"Kawai dan shi jikan sarkine sai yafi mu komi?".
Kanta ta jinjina tare da gyara zaman ta cikin sanyi tace.
"Ba haka bane. Bari kuji kaWan daga cikin nasabarsa.
Kunga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani.
Yana Waya daga cikin manyan malam da Afirka gaba Waya take ji dashi.
Sabida a ?iyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jiki da tarin ilimin addini kamarshi.
Tun yanada shekaru takwas a duniya ya haddaci al'?ur'ani mai girma.
Sannan ya fara karatun littafai shine matashin da yakeda haddar hadisai zunzurutunsu a kanshi sama da dubu ashirin.
Kunji wannan darajeta da tasa ko manyan mutane suke girmama shi.
Sannan shi jinin Masarautar JoWa ne ta wurin mahaifinshi.
Ta wurin mahaifiyarshi kuwa shi jinin sarki Jalaluddin ne, masarautar sarkin Musulmai.
Kana ta wurin kakarshi data haifi mamanshi. Asalin balarabiyar saudiya ce, wacce zuriyarta ne limamen Harami.
Kunga nasaba kan nasaba kenan.
In kyau ne na halitta, babu irin kyan da bai ganiba,
In kuwa kuWine, ku leka ?asan gidan saman nan zakuga ayarin motocin da sukayi mishi rakiya, to ko kakan nashi LamiWo motar da yake hawa bata kai ta Jabeer ba.
Uwa uba shi mutun ne da ya ?oshi da sunna, baya son bidi'a.
Shi mutun ne wanda ya samu kekyawan zato a wurin mutanen duniya ake mishi shaidar salihi, mumini, mai tausayi."
Da sauri suka ?atseta da cewa.
"To Aunty meya hanashi yin aure har yanzu?".
Cikin maida numfashi tace.
"Allahu alamu, sai dai ance kamar shi bana miji ban????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  e!".
Cikin sauri wata tace.
"Kai mgnar. Duniya dan Allah kiji zancen ?an shashi faWi. Bita da ?ulli har an samo sharrin da aka li?a mishi bawan Allah."
Rafi'a kuwa kai ta jinjinawa Shatu alamun kinji ko, ita kuwa Shatu zuru tayi kamar makahon daya tsinka garaya".
Cikin sauri wacce tace tana sonshin tace.
"Wlh ni dai ko shi bana miji bane zan iya zama dashi a hakan in da zai yarda muyi aure".
A hankali Shatu ta gyara ri?on da tayiwa wayarta tana Waukar su video.

A hankali matar nan ta nisa tare da cewa.
"Uhum Nafeesat kenan ai kuwa da wuya ya aureki duk abinda zakiyi.
Sabida kin ga Dr sugzana yar India ce ?abilar buramin bautar wuta takeyi.
Tace tana sonshin, tace in dai zai aureta zata musulunta, amman ya?i".
Da sauri Waya dake cinsu tace.
"Sabida me ya?i duk da tayinta na shiga addinin Allah?".
Cikin sanyi matar tace.
"Yayi bayani kuma manyan malamai sun gamsu da hujjarsa, inda yace, tace dole sai in zai aureta zata musulunta, kenan badon Allah zata musulunta ba sai dan sonshi.
Ta kuma ce in sunyi aure duk yaransu rabasu zasuyi rabi suyi addininshi rabi suyi addininta bi ma'ana wasu suyi bautar wuta wa iyazubillah.
Yace wannan dalilin yasa bazai aureta ba, kuma shi baya sonta, ya kuma gargaWi mata su dena cewa suna sonshi.
Dan shi yanzu al'majiri ne sai ya girma zaiyi aure".
Dariya sukayi baki Wayansu.
Jin hakane yasa Rafi'a yana Shatu suka ci gaba da tafi.

Su kuma waWancan sukaci gaba da hirarsu.

Tafiya kaWan sukayi suka samu wasu yan mata da samari suna hira Waya daga cikinsu na cewa
"Ni tsarin Sheykh Jabeer yana masifar burgeni a rayuwata.
Shifa tunda yake a duniya babu wani mahalu?in da zaice yaga koda singalalin hannunshi ne a waje.
Mutum ne da Allah yayi mishi sutura, yake kuma suturce kanshi."
Cikin dariya wani yace.
"Kai nima yana burgeni sai dai tsarinshi na wai mata su dena yafa gyale, su rin?a yin shigar zurmu?a-zurmu?an hija baine bai minba, to mu matasa taya zamuyi ta kallonsu munajin daWi.
Ni wlh wani lokacin a kallonma nake biyan bu?atar damuwata sai dai inje inyi wonka".
Cikin tashin hankali Waya daga cikinsu yace.
"Ouzubilla, ka nemi gafar Allah wlh zina kakeyi".
Cikin zaro ido yace.
"Kai malam dakata ni banyi zinaba".
Cikin sanyi babban nasu yace.
"Wlh kayi sabida ita zina ai kashi-kashi ce akwai ta ido akwai ta kunne haka kuma akwai ta zahiriya, fisabilillahi ka kalli yar mutane na tafiya har kaji ka biya bu?atar ka?".
Kai ya gyaWa musu cikin sanyin jiki.
Nan sukayi ta mishi nasi daya kame idanunshi

Da sauri suka wuce su.
Ita kuwa Rafi'a cikin murmushi tace.
"To bari in baki amsar tambayar ki.
Yana zuwa nan asibitin sau Waya cikin ko wanne sati. In yazo kuma ranan duk wanda ya duba magani kyautane, in kuma aikine kyautane.
Kinga Hospital Win school Winmu shi kuma a wata yake zuwa sau Waya,
Nanam da kyar ya yarda, yanada asibitinshi mai zaman kanshi can yafi maida hankali".
Ajiyan zuciya Shatu tayi tare da cewa.
"Uhum can yake tara kuWin bayin Allah ya ?wamushewa dai".
Kai Rafi'a ta jujjuya tare da cewa.
"No ba haka bane, duk abinda zan ce miki bazaki gamsuba in sha Allah sai Next month in ciwon mararki ya tashi, zan kaiki can zakiga zahiri.
Amman dai daga sunan asibitin zaki iya fahimtar manufarsa".
Kallonta ta Wanyi tare da cewa.
"Menene sunan asibitin?".
?ara saurin tafiyarsu sukayi tare da cewa.
"Ballitai Hospital". Kanta ta gyaWa alamun gamsuwa da sunan asibitin kana taja hannun Rafi'a suka tafi can maraba da ba?i.

Abin mamaki suna isa suka samu.
Kusan rabin DOCTOR'S din asibitin duk suna wurin.
Duk DOCTOR'S Win da Shatu tayiwa mgna sunzo nan sunata basu taimakon gaggawa.
Kana ga Nurses tako Ina, sunata tura marasa lfyan ana basu gadaje.
Cikin abinda bai gaza awa Waya da rabi ba.
Komai yayi dai-dai hatta waWanda za'ayiwa aikin anyi musu.

Bisa umarnin LamiWo kana ya rin?a bin gadajensu yana ajiye musu kuWi dubu biyar-biyar.

Sosai wannan abun yayi masifar yiwa Shatu daWi, tana kallon dattijon tamkar wani nata,
Godiya sosai sukayi musu da zasu tafi, suna fita nan sukayi kiciSis da Jabeer da yanzu ya fito Wakin tiyata.

Ita kuwa Shatu Junaidun Junainah ta kalla lokacin da aka dawo dashi daga Wakin tiyata,
Inda aka Winke mishi inda aka sareshi.
Cikin murmushin yace. "Adda Shatu zamu kwana ko?".
Murmushin jin daWi tayi tare da cewa.
"A a Junaidun yanzuma zan tafi, kasan Ummey ba lfy, amman jibi ma zanzo gobe su ya Salmanu zasu zo, yanzu dai hankalinmu ya konta tunda kun samu kulawar likitocin yanzu sai matsalar abinci".
Cikin sanyi Sumaye matar marigayi Sarkin bakansu, tace.
"La abinci kam bamu da matsalarshi, tako ina zakiga musulmai na dafo abinci suna kawo mana sadaka, harda kayan za?i da kuWi wasu ke bamu".
Ajiyan zuciya ta sau?e tare da cewa.
"Alhamdulillah yau kam mutanen Rugar Bani zasuji lbri mai daWi".
Cikin kula tace.
"Toni yanzu zan tafi in Sha Allah gobe akwai masu zuwa, Allah ya baku lfy".
Ta faWi tana kallon sauran mutanen nasu.
Haka Rafi'a ma tayi musu fatan lfy kana suka fita tare.
Adaidaita suka shiga, saida ya kai Shatu tasha kafin.
Ya wuce da Rafi'a school Win su.


A can wurinsu LamiWo kuwa ganin lokacin sallan la'asar yayine yasa Jabeer cewa, suyi salla a masallacin asibitin kafin su tafi.
Haka kuwa akayi, sai gashi masallaci ya cika ma?il da bani adam,
saida suka idarne kana suka kama hanyar tafiya garin Rugar Bani.

A cikin motocin kuwa kowa da abinda yakeyi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsuratul Khaf yake karantawa a hankali.
Hakama LamiWo.

Su Jalal kuwa kowa na ruggume da waya.
Haroon ma waya yakeyi da Umaymah tana tambayarshi sun isane.
Nan yake gaya mata inda suke da abinda sukayi.


A cikin Rugar Bani kuwa, kamar ko wacce ranar jumma'a yauma hakane.
Tunda aka taso sallan jumma'a suka dawo tsakar garinsu suka zauna suna ?ara jadda mitin Win su na Waukar fansa.
Zuwa yanzu garin yana amsar ba?oncin Fulanin da suka gaiyata tako wani sashi na Afirka. Sunata shirye-shiryen su.

Suna cikin masallaci suna sallan la'asar ne suka rin?a jiyo, shigowar motoci cikin Rugarsu kamar bazasu ?are ba.


Cikin nitsuwa sukaci gaba da sallan su.

Su LamiWo kuwa suna shiga garin ganin tsit kuma alamun ana salla, sai yace su tsagaita gudun.

Jabeer kuwa zuwa yanzu tuni zuciyarshi ta fara luguden dukan ?irjinshi ya rasa wannan abu na menene?
Yanzu wannan karo na huWu kenan yana jin wannan abun a rayuwarsa, ya kuma gwada kanshi yaga bashi da BP dan sani BP nayin hakane ya sashi godawa.

A jere a jere sukayi parking motocinsu cikin nitsuwa,
Dogarai da fadawa suka fito suka zagaya motocin.

Bayan sun idar da salla sunyi addu'o'insu ne kana suka fito.
Gani fadawa da dogarai ma kaWai ya ganar dasu waye yazo.
Dan haka cikin karrama da mutun-tawa ArWo Bani ya nufi inda suke.
Sosai dogarai sukayi mamakin yadda wannan karon kuma yakeyi kamar ya haWiyesu dan farin cikin zuwansu saSanin wancan karon da yayi ta aunawa LamiWo boma-boman ba?a?en maganganu.
Jiki na rawa ya juyo ya kalli matasan tare da cewa.
"Maza ku shiga cikin gidan ku fito da dardumai da kilisai kuzo ki shimfiWa.
Ina sarkin kiWa maza a fito da gangaguna a fara sanarwa.
Mabusa ku fito."

Ai kuwa cikin abinda bai gaza 25 minutes ba aka gama shirya komai.
Tuni mutane sun cika sunyi ma?il ko ina ya cika da bani adam.
KiWe-kiWen da bushe-bushen sarewa da al'gaita kuwa tuni ya cika illahirin garin tako ina mutane ke shigowa.

Ba'ana da tun jiya yake cikin Wakin dodon tsafinsu Bonon.
Jin al'gaita ShaWi ne, ya sashi fitowa bayan ya gama shafe magunguna.
Dama yayi zaton wannan hegen mai jajayen kunnuwan zaizo shiyasa tun jiya ya shiga Wakin sirri dan a dafashi da kyau.

Jinsu ne yasa ya fito dashi da tawagarsa suka nufi Rugar Bani.


LamiWo kuwa da tawagarsa a hankali cikin ?asaita da kwarjini suke taku har i zuwa cikin rumfar karan da aka malale musu kujeru da kilisai.

Bayan sun zaunane duk dattawan wurin sukazo suka gaida LamiWo da tawagarsa.
Jabeer kuwa ji yake tamkar ya kira Sojoji su zo su zazzane mishi mutanen garin gaba Wayansu ko zaiji ya huce da abinda sukayi mishi.
Sam baya son ganin fuskokinsu, ga toshe mishi kunne da sukayi da wannan bushe-bushen sarewa.
Ga bugun zuciyarshin dake neman zautar dashi.
Allah ya sani baya son ganin ko ?asar garinne.

Cikin kula da nitsuwa da kamala Bappa ya kalli Jabeer Win tare da cewa.
"Yaro ya ?arfin jikin naka".
Ba tare daya Wago kanshiba ya amsa, sabida jin muryar tanada kamala.
A hankali yace.
"Alhamdulillah".
Gaba Wayansu suna farin cikin ganin Jabeer yazo cikin ?oshin lfy.
Sunyi masifar mamaki ganinshi garau ya worke cikin mako Waya tak.
Wannane ya ?ara sawa Ya Salmanu wani farin ciki na ban mamaki.

A hankali Bappa yace.
"Masha Allah, Allah ya ?ara sau?i".
Idonshi ya Wan Wago ya kalleshi, haka nan yaji dottijon ya cika mishi ido a hankali yace.
"Amin ya Allah".
Bukar ne ya Wan kalleshi tare da cewa.
"Yanzu yaron nan kaine? Ka sake zuwa garin nan lallai baka son ranka".
A da?ile Jabeer yace.
"Inuwa tace".
Galadima ne ya Wan kalleshi tare da mishi alamun kada yayi mgna.
Kwaffa yayi tare da murtuke fuska.

A hankali su ArWo bani suka koma wurin zamansu.
Kana Barmuji ya fara sanarwan ana son ganin Ba'ana a tsakiyar fili.

Wannan abu shine na forko a tarihin shi a nemeshi yazo tsakiyar fili dan a rama gasar da yayi.
Haka yasa cikin karsashi da buWa ?wanji yayi wani irin tsalle ya faWo tsakiyar taron.
Juyi ya farayi da ihu da Waga hannunshi sama, saida yayi kusan sau goma kafin yacewa Barmuji.
"Ka gayawa yan kallo in dai an cini gasa zan tafi in bar ?asar nan, zan koma ?asar Cameroon nida ?asar nan sai dai ziyara,
Dan ba'a yin jarumai biyu a gari Waya kamar yadda ba'a sarakuna biyu a gari Waya."
Wani irin ihu da shewa gaba Waya mutanen suka ruWe dashi lokacin da Barmuji ya sanar da ikirarin Ba'ana.

Kana dattawan garin kuma kowa da abinda ke cikin ransa ArWo Bani dasu Bappa kamar su haWiye ha?orinsu dan daWi.

ArWo Bani ne ya ron?ofo kusa da LamiWo cikin nitsuwar datattaku yace.
"Allah rene, bisimilla GARKUWA ya fito fage shi ake jira."
Kai ya gyaWa mushi kana ya juyo ya kalli gefen damanshi inda Jabeer ke zaune cikin shigarsa ta al'farma, yayi masifar kyau, yana zaune cikin kamala sai lips Winshi ke Wan motsawa a hankali alamun tasbihi yakeyi.
Cikin yanayi girma da bada umarni da tsare fuska LamiWo yace.
"Jabeer kai ake jira tashi kaje muyi abinda ya kawomu."
Fuskarshi ya tsuke tare da lumshe idonshi, muryar Galadima da yajune yasashi buWe idonshi.
Shi kuwa Galadima hannu ya mi?a ya kamo hannun Jabeer, tare da fara ja alamun zai mi?ar dashi tsaye.
Cikin mamaki Jabeer ya zubawa tsohon ido wanda yake Bappa ne ga LamiWo, in banda ?arfin hali inashi ina iya Waga Jabeer.
Muryar LamiWo yaji yana kuma cewa.
"Jabeer DAN ALLAH KA TASHI".
Tsaki ya Wan ja kana ya yun?ura ya mi?a a hankali.
Cikin jin daWi Galadima ya kama hannunshi yaja suka fara taku, zuwa cikin taron.
A hankali yake bin bayan Galadima kana fadawa na biye dasu.
Al'kyabbar shi ya Wan gyara mahaWinta.

Suna isa tsakiyar taron. Mabusa da makaWa duk suka kaceme wurin da bushe-bushen sarewa da al'gaita kana da kaWe-kaWen.

Barmuji ne ya matso bayanshi da alamun zai cire mishi Al'kyabbar shi.
Da sauri Barmuji ya dakata sabida ganin wani irin lallo da Jabeer ya watsa mishi cikin tabbatarwa yace.
"Kada ka sake gangancin ciremin suturar da Allah yayi min har abadan. In kuwa ka gwada tabbas zakaji yadda raWaWin marin tafin hannuna yake, in kunnenka ya kuramce ansan kuramtane yasa bazakaji gargaWi da kashedi na ba!".
Ya ?arishe mgnar da tafasar zuciya,
cikin tsuma Barmuji ya rusuna tare da cewa.
"Duk da dokar gasa ce, anyi maka wannan lamunin tunda kaine mai duka ba kai za'a dakaba".
Ba'ana kuwa wani murmushi jin daWi yayi sabida yasan yin duka da ?atuwar riga haka, zai takurashi bazai samu damar zage ?arfin shi ya zabga mishi bulaliyar ba.
(Allah sarki Ba'ana bai san zafin hannun Sheykh bane.
Sarkin ShaWi ne, ya mi?e tsaye tare da tanWun shantun da a ciki suka zuro bulalin nasu.
Ya nufi wurinsu Jabeer yana zuwa.
Yasa hannunshi ya zaro bulala Waya daga cikin bulalin ya mi?a mishi.
Hannun yasa ya amshi bulalar.
Kana ya gyara al'kyabbar jikinshi.
Shi kuwa ba'ana gabanshi ya matso ya tsaya ya buWa sawunshi, kana, yasa hannunshi duka biyu ya ri?e ?ugunshi, ya buWa ?wanjinshi da kyau.

Sheykh kuwa ?asar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ?unar sashi cire kayanshi da sukayi satin daya gabata, yana tuna raWaWin da zuciyarsa ta masa a wannan lokacin.
Busar sarewa da akayi azaban ?arfi ne, tabbacin an bada dama a farane.
Yasa Jabeer gyara ri?on da yayiwa bulalar, yana maiji cikin ransa da jikinsa zai rama dukan azaba da wannan ya mishi.
Yanajin zai ramane kuma dan tsorotar dashi kan sake dukan wani.
Yasani in sha Allah daga kanshi baza'a sake wannan gasar daba adadin bane, yayi niyar yin ramuwar ne dan tare wannan Sarakar zai ramane ko zai samu ya huce tsanar da yayi mutanen garin, sabida kasan cewarsu Musulmai ?an uwansa baya son yayi musu irin wannan tsabar lokacin Waya fushinsa na ranar ya dawo.
Shiyasa ya murza yatsunshi da kyau tare da matsawa gefe kaWan, Rumtse bubalar yayi a tafin hannunsa da kyau, kana Wagata tare kuma da cewa Bismillah, ya fara da sunan Allah kana ya Waura da fara karanto ayatul shifa sannan ya zabgawa Ba'ana ita a tsakiyar bayanshi.

Gaba Waya hankali da idon kowa bisa fuskar ba'ana yake.
Shi kuwa ba'ana wani irin murmushi yayi tare da kallon gefe da gefenshi kana, yayi fito alamun babu wani abu da yaji dai yaji tsikar jikinshi yana tashi yar-yar.

ArWo Bani da sauran dattawan kuwa har ji sukeyi tamkar

43 / 72