Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   17 / 72

48K to 51K   out of 214K words

na kira Hukumar yan sanda ta nan cikin Numan na shaida musu, amman kafuran nan ma?iya Allah da Manzonsa sai cewa sukayi,
A kashe mu mana, ai an rage musu aikine.
Na kira su ArWo Bani, suna Wagawa katin wayata ya ?are.
Hadi sun kashe kowa na gidanmu.
Taroshi Hadi yayi suka faWa nan suna kuka mai cike da taraddadin rabuwa.
Cikin ?arfin hali Sale ya ture Hadi tare da cewa.
"Ka gudu Hadi ku gudu, Ni nasan bazan rayuba.
Ka gudu.
Sun kashe min Kowa har jariren tagwayen da aka haifa min shekaran jiya, sun kashesu.

Cikin kuka Hadi yace.
"Bazan iya guduba Sale su kasheni kawai, ina zanje bayan sunyiwa garin zobe.
Da ?arfi Hadi ya abka jikin Sale Jin ansa gatari an sari kafaWarsa ta dama,
Juyowar da zaiyi kuma aka tsira mishi mashi a ?irji.
Nan take ya cika, hakama Sale.

Cikin gidansu Shatu kuwa.
Ummiy ta sallame sallan kenan, taji.
Inna dasu Innawuro suna kurma ihu da salati.
Yun?urawa tayi da azama jiki na rawa ta nufo woje.
Fitowanta yayi dai-dai da lokacin da aka sare kan Innawuro, wanda kan yayi tsalle ya faWo kanta, kana ya gangara ya faWa gabanta.
Wani irin ihu mai cike da karaji gauraye da salati ta kurma lokacin da taga an burmawa Inna mashi a ciki.
Ihunta da salatinta ya jawo hankalin su, sukayo kanta.
Sai dai kafin su isoma ta yanki jiki ta faWi babu numfarfashi tamkar matacciya.

Koda suka iso, dariya suka kece da ita cikin rashin imani Wayansu yasa ?afa, ya taka ruwan cikinta, tare da cewa.
"Shegun FULANI ku mutu, mu huta, da ganinku a garinmu, gonakinku da dabobbin ku duk sun zama namu.
Mu Wauke yaranku mata mu maidasu karuwanmu, muyi musu ciki su haihu mu bawa dodo.
Muji daWi dasu.

Ganin kamar ta mutune yasa suka tattakata suka wuce suka fita daga gidan.

Junainah kuwa da Junaidun, suna gab da shigowa garin suka fara jiyo ihun mutanen garin.
Cikin azaban firgici Junaidu ya wurgar da kondon ?a?an itatuwan dake hannunshi,
da gudu yabi bayan Junainah data ruga a guje sabida hango, anata kashe mutane a gabansu.
Cikin kuka da tarin kiWima da fita haiyacinta take cewa.
"Wayyo Ummiy Wayyo Inna Wayyo Bappa, zasu kashemu.
Wayyoooooooo Adda Shatu zasu kashemu".
Ri?o hannunta yayi da ?arfi cikin rawan jiki da murya yace.
"Junainah bazasu kashekiba, zan kareki da izinin ubangiji, zaki rayu, Shatu bazata rasa kowa duniya ba.
Junainah zan zame miki Garkuwa zan fanshi ranki da nawa ran.
Ki zama tamkar yar tsira, Shatu ta zama tamkar yar jarida, ta rubutawa mutanen duniya su karanta, kisan gillan da akeyiwa Fulani mazauna daji.
Da ?arfi yasa hannu ya zaro wukar dake ?ugunshi wanda da ita ya yayyanki nonunan ayaba dasu inabi.
Wayarshi ya kuma zarowa
Ya Salmanu ya kira,
Salmanu kuma dake, kwance a gadon asibitin nan Genaral Hospital Numan.
Wanda bai workeba tun dukan shaWi da ba'ana ya mishi.
A hankali yasa hannunshin ya amsa kiran wayarshi ganin Junaidu ke kiranshi.
Cikin kiWima da firgici Junaidu yace.
"Ya Salmanu, maya?an ?abilar Sachama sun shigo Rugar mu, sunata kashemu, mazanmu da matanmu.
Ya Salmanu Junainah ina son ta tsira, ko dan ran Junainah ka kira mana hukumar yan sandan cikin Adamawa, ina son su iso su ceci Junainah kada Shatu ta rasa kowa a duniya.
Ban saniba ko zan gazawa bawa Junainah tsaro".
Gaba Waya jikin Salmanu rawa da tsuma yakeyi, katse kiran yayi da sauri ya kira.
"A.S.P Kabiru Nasir. Wanda yake, Hetkotan Adamawa.
Koda ya mishi jawabin abinda ke faruwa, a take. A.S.P ya kira.
S.P Daniyel dake Numan ya bashi doka da oda maza-maza su bawa fulanin Rugar Kikan tsaro gaggawa, shima yana nan tafe da rundunar sa. Ya bashi umarni mai ?arfi ya ?ara da cewa, muddin yazo ya samu ba dai-dai ba ta San?aren tsaro, to akan aikinshi.

Wannan abun na umarni daga samane, yasa mugun kafurin nan. Firgita gudun rasa aikinsa, da tonuwar asirinsu da gudun kada a cireshi asa musulmi a kujerarsa, yasa cikin gaggawa ya haWa kan rundunar sa ya nufi.
Cikin Rugar Kikan.

Junainah kuwa wani irin karkarwa takeyi wanda, tuni fitsari ke tsiyaya yana bin sawunta.
Wani irin ihu tayi, ganin wani kafurin ya kaiwa Junaidun sara a bayanshi.
Wani irin juyi Junaidun yayi ya farma kafurin da da wu?arsa dan kare kansa da Junainah.
Duk da su biyar suka zagayesu, basuyi nasara a kanshiba, yana kare kanshi da Junainah, har saida suka tsira daga waWannan.
Sai kuma wasu, mutun takwas suka cimmusu.
Da ?arfi suka ban?aren Junaidun, suka fara kiciniyar zare Junainah da ya ruggumeta da azaban ?arfi da yayi.
Wani irin ihu yasa jin an caka mishi.
Wuka a gadon baya.
Still bai saketaba, sai ya?in kareta da ya farayi, da iya ?arfinshi.
Ita kuwa Junainah ganin an caka mishi wu?ane yasa ta sume.
Dai-dai lokacin kuma rundunar yan sandan suka iso.

Kamar bazasu guduba, dan sun san da bakin hukumar sukeyin aikin, to sai dai ganin musulman cikin yan sandan suna sakin harbine yasa.
Suka ari ta kare.


Daga nan suka rin?a gudu sunayiwa yan uwansu fito alamun su gudu.
Cikin ?an?anin lokaci duk suka gudu.

Su kuwa yan sandan, suka shiga cikin Rugar Kikan Win.
Hankalin musulman cikinsu yayi masifar tashi ganin irin kisan gillar da akayiwa bayin Allah'n nan, kisa na rashin imani.
Nan take suka kira motocin asibiti.
Suka rin?a jidon masu sauran rai suna sawa a motar ambulance suna kai cikin Genaral Hospital Numan.
Kana suna harhaWa gawakin kuma a tsakiyar garin.
Cikin mintuna talatin rundunar A.S.P ta iso.
Tare da yan jaridu.


Su Bappa kuwa. Koda suka gama tattaunawa da Maimartaba, sai ya umarci Waziri daya hanasu tafiya a bisa adalcinsa.
Yace su tsaya suci abincin rana, kana suyi sallan azahar kafin su tafi.
To haka yasa suka zauna.
Waziri yasa akayi musu duk ihsanin da Maimartaba ya bada umarnin ayi musu.
Sukaci abinci sukasha, Sannan sukayi sallan azahar.
Daga nan aka sallesu suka tafi.

Tuni cikin gari kuwa gidajen rediyo sun Wauka, batun faWan FULANI makiyaya da ?achamawa manoma, wanda akaso a juya rahoton da cewa makiyayan ne sukayiwa manomanne Sarna.



Bayan. Tafiyan su Bappa da kamar 30 minutes ne. Labari abinda ya faru ya riski Maimartaba.
Nan take yasa Waziri da Galadima da hadimai mutun ashirin suka nufi cikin Numan dan suje su tabbar da abinda akace Win.

Su Bappa kuwa, sam basuji lbrinba saida suka isa cikin Numan.
Ganin garin a hargitse ne yasa ArWo Bani ya kalli Bappa da Alhaji Haro da suke gefenshi cikin mmki yace.
"Lafiya kuwa? Meke faruwane a garin nan?".
Cikin kaWuwa suka haWa baki wurin cewa.
"Allahu alamu".
Drivern nasune, ya kallesu a tsorace yace.
"Anya kuwa yau ba faWa akeyiba a garin nan ba".

"Kai ba lfy ba kam!".
Cewar Alhaji Umaru
Shi kuwa Drivern, bakin titi ya Wan gangara ya tsaya, ya tambayi wasu yan agaji daketa.
Shiga cikin wani babban Pharmacy da alamun magunguna suke saya,
koda suka mishi bayanin abinda ya faru.
Jiki na rawa yazo ya sanarwa su ArWo Bani.
Lokaci Waya hankalinsu. Yayi masifar tashi.
Nan sukace ya wuce dasu.
Asibitin.

Koda sukaje hanasu shiga akayi.
Hakane yasa, sukace to ya wuce dasu Rugarsu.
Suga ko canma akwai uban da zai hanasu zuwa.

Nan ya nufi cikin Rugar tasu dasu.

Su Wazirima tuni, sun iso.

A can cikin masarautar kuwa,
Sosai hankalin Maimartaba ya tashi.


A can ?asa mai tsarki kuwa.

Sitti ce tsaye gefen Sheykh lokacin da yake mgna da kakanshi.
Zama tayi gefenshi, tare da tsareshi da ido.
Baibi ta kantaba, ya ci gaba da sarrafa wayarshi.
Wata number, ya dannawa kira kana ya kara wayar a kunne, jim kaWan aka amsa kiran.
Bayan sun gaisane, ya Wan gyara zamanshi tare da Wan kallon Sitti ta gefen ido
Cikin harshen fillanci yace.
"A haWa min zama da ?ungiyar TABITAL POOLAKU".
Sai kuma ya Wan sha?i sanyi da ?amshin Wauki ido ya lumshe cikin kamala da nitsuwa yaci gaba da cewa.
"A kira min ?ungiyar MIYETTI ALLAH, da gaggawa, ina da zama dasu.
Ranar Jumma'a in sha Allah".
Hannun damanshi yasa yana shafa sajenshi, tare da sauraron mgmar da. ArWon ArWaSe keyi.
"Ranar jumma'a kuma? Ka dawone?".
A takaice yace.
"Zan dawo!".
Cikin gamsuwa da mgnarshi sanin in yace eh, eh Wince in kuma yace a a, tofa a ance.
Muddin kuma yace zaiyi abu to da izinin ubangiji sai yayi shi.
Cikin jin daWi adalci da kulawarshi ga shugabanci da aka bashi yace.
"To Allah ya dawo da kai lfy".
Yatsun ?afarshi ya sunkuyar saida suka Wan bada sautin ?aras, kana yace.
"Amin ya rabbil izzati".
Daga nan ya katse kiran.

Kamar bata wurin haka ya jawo System Winshi ya fara daddannata.
Kamar babu kowa kusa dashi haka yaci gaba da aikinshi.
A system, ita kuwa Sitti ido ta zuba mishi.
Tana kallon yatsun hannunshi da yaketa sassarfa, tamkar shiya haaliccin na'ura.

Yanajin idanunta na yawo a sasan jikinshi, hakan yasa, ya Wan juya kwayar idanunshi, ya Wan kalleta ta wutsiyar idonshi, murya can ?asa yace.
"Sitti wannan kallonfa, kin san bana son kallo kam ko?".
Ajiyar zuciya ta ajiye, kana ta Wan janye Hiramin kanshi, da sauri yasa hannunshin ya kame hiramin cikin kwaSe fuska yace.
"Sitti ya haka, kinsan Haroon ba kan gadone dashiba, yanzu zai iya shigowa da yaran nan".
Ido ta Wan rufe kana tace.
"To su yaran mayune, ko yaushe kana rufe da Al'kyebba da hirami, kasha iska mana, ko nauyi basa makane?".
Kanshi ya Wan juya kana a hankali yaci gaba da aikinshi tare da cewa.
"Suturce jiki shine, zaiyiwa Wan adam nauyi, Sitti, sannan ya za'ayi in bari ko wani Tom and Jerry su kallarmin suman kai, ai shi hula da hirami kamar Wan kwaline wa mace".
Sai ya kuma Wan juyowa ya kalleta tare da cewa.
"Yauwa Sitti, bana son ana sawa Jazrah tana samin abinci, bana so, sai a turrota tazo taita kare min kallo".
Fuskarta ta haWe kana tace.
"To yayi kyau, kawai in baka sonta, ka fito fili ka faWa mana".
Kauda mgnar yayi tare da cewa.
Ki shirya in sha Allah zuwa ran jumma'a ina son in kasance cikin ?asata ta haihuwa a jiharmu a kuma masarautarmu".
Haroon da yanzu ya shigone ya Wan kalli Wan uwan nashi, cikin mmki yace.
"Sheykh kawai dan ana mgnar baka matar aure shine kake shirin guduwa zaka bar ?asar ba?".
Bai kalli Haroon ba kuma baice, komai ba, sai rufe system Winshi yayi kana ya mi?e a hankali,
gaban drower'n gadon ya nufa,
buWewa yayi, wasu E Passport guda biyu ya Wauko,
Kana ya dawo gaban Haroon.
Hannun shi ya kamo ya dan?a mishi su, kana yace.
"Gasu, ina son zamu bar ?asar nan ranar al'hamis."
Da sauri Sitti tace.
"Kaida waye zaku tafi".
Ba tare daya kalletaba yace.
"Da ke".
Kai ta kuma juyawa tace.
"A a kam ka koma kai Waya, ni ban gaji da ganin ahlinaba".
aKanshi ya kaWa tare da cewa.
"Zafa ki koma, don bazan barki a kasar nanba, kiyi ta haWa min tarko, dole tare zamu tafi, inada zama mai mahimmanci, dole inje inji da matsalar al'ummar da aka naWani GARKUWANSU, tunda ke kika sa na amince da wannan naWin, ina zamana lfya, wani mulki ko sarauta basa jadawalin rayuwata, keda waWancan tsofoffin sarakunan kuka likamin wai GARKUWAN FULANI,
To sun samu matsala kuma dole inje in bincika".
Shiru kawai Sitti tayi ganin karfin hali ziraran miraran.
Zuwa yanzu ta dena mmkin, cewa akan abu biyu Sheykh ke iya doguwar mgna, akan Alqur'ani, wanda shine zaka samu zai iya wuni a zaune yana tabsiri ba gajiya ba yunwa bare ?ishi ko bacci.
Sai kuma akan wannan sarautar GARKUWAN FULANI da aka bashi shekarun biyar baya, wanda harga Allah baison wannan Sarautar ko kaWan sai dai dole da akayi mishi, da fushin da Abbunsu ya nuna a kan haka.
Shiyasa duk sanda zaiyi ?orafi yakan iya jera mgna biyar zuwa bakwai, wanda sam shi tsarin rayuwarsu ba mai doguwar mgna bace.

Kai takaWa jin yana cewa.
"Ku Wan bani wuri".
Basuyi mgna ba suka fita, a tare, domin sun san Sheykh Jabeer mutunne mai tarin tsananin al'kuyya da killace jikinsa, shi kanshi yana kunyar kanshi a rayuwarshi ta duniya shi bai taSa yin tsirara a kan kanshi wai yaga surar jikinshi ba, Allah yasani yana masifar jin kunyan kanshi.
Haka yasa koda wonka zaiyi, baya yin tsirara,
yanada wasu tausasan gajerun towel wanda duk rintsi dasu yakeyin wonka a jikins??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hi.


Suna fita falo, Haroon ya tsaya yana kallon Jazrah, dake konce bisa kujera ta kife kanta a cinyar Jannart tana kuka mai sanyin sauti.
Kai Sitti ta juya ta nufi Wakinta,
Allah ya sani Jazrah na son Sheykh, shi kuwa bai nuna ya tsaneta ba, amman dai ya nuna zahirin bazaiyi aureba.

Haroon da Jannart ne suka zauna suna bata baki.
Saida ta nitsune suka fita tare.

Shi kuwa Sheykh suna fita, ya maida ?ofar Wakin ya rufe.
Kana ya dawo bakin gado.
A hankali ya zare tattausan al'kyabbar jikinshi, fararen kayan dake jikinsa suka baiyana.
A hankali ya zare rigar ya ajiyeta gefe.
Zariyan wonWon ya kunce, tare da zama, ya saSule tare da matsawa gefe.
Ya rage dagashi sai fararen boxes da vest.
Juyawa yayi yana taku mai cike da nitsuwa,
ya shiga bathroom Win.
Yana shiga ya maida ?ofar ya rufe,
kana ya rage hasken ciki.

Sannan ya cire ?ananan suturun dake jikinshi tare da Waura towel Win, a ?uginshi zuwa kan cinyoyinshi masu yelwar gargasa mai taushi da tsulSi da she?i tana,konce lib-lib a farar fatar jikinshi.
A haka ya fara, wonkan, bayan yayi Brosh a hankali yake bin jikinshi da sabulun mai Wan karen ?amshi, yanayi ya cuccuWa jikinshin.
a hankali ya iso kan ?ugunshin, cikin sabo da iya Wabi'ar tasa, ya cusa hannunshi ta cikin Waurin towel Win, ya rin?a cuccuWa jikinshin da murza mishi daddaWan sabulun ya murje ko wani lungu da sa?o na sasan jikinshi ba tare da idanunshi ma, sunga tsiraicinsaba.

A ?alla yayi sawon da?i?u ashirin a bathroom Win kafin, ya fito,
yana Waure da wani babban towel mai Wan karen kyau da taushi bayan ya matse wancan ya shanya.

Yana sa?o ?afarshi cikin bedroom Win ya...!






Solo-salo-salon GARKUWA na dabanne!


By
*GARKUWAR FULANI*
=???
=??=?J?????=?
?>?4?
*GARKUWA*

PAGE 13

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

=??????>?4?

FREE PAGE

Littafin GARKUWA na kuWine, Special Group 1k Normal 300, in kina bu?atar karanta lbrin GARKUWA turo katin mtn na Wari uku kacal ta wannan layin 09097853276. Gareku mutanen Special Group turo dubu Waya ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276.



*Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki, in kin san zaki sayi littafinane dan ki fitar dashi, na ro?eki da Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki saya bana son kuWinki, ki ri?e kudinki ki barni in ri?e littafina. Dan Allah nace badon niba.*



Yaji anata bubbuga mishi ?ofar Wakin,
bai kulaba, yazo a zauna bisa kujerar dreesing mirror, a hankali yake tsane ruwan jikinshi, bayan ya gama Wan tsane ruwanne ya busar da tattausan sumar kanshi, ta hanyar na'urar busar da gashi.
Mai ya Wan shafa, kana ya gyara gashin da kyau, sannan ya mi?e yaje gaban.
Drower'n, a nitse ya buWe, wasu datsatstsun kaya riga da wondo na yadin Lamud, yadin Sky blue ne mai masifar kyau. Sai kuma ya zaro wata farar al'kyabbar fara ?al. Da farin hirami.

Rufe wannan gefen yayi, kana ya buWe Waya gefen.
?ananan kayan ne a ciki kamarsu Jallabiya da boxes vest dasu zagayen ba?in abin da yake Waurawa kam hiraminshi.
Suma duk mafi akasari su fararene.
A bakin gadon ya ajiyesu.
Kana ya fara kimtsawa.

Bayan ya gama shirinsa ya fito ras cikin kalar sky blue and white sai Black half cover da kuma ba?in zagayen saman hiramin.
Ya fito ras tamkar dai yadda zuriyar mahaifiyarshi da suke tsatson limamen Harami suke fita.
Ko yaya ka ganshi dole kace shi balarabene, sabida komai nashi irin nasune. Kyau, fari, gashi, ilimin addini, nitsuwa, imani, da kuma irin shigarsu, da shima ya rainu da hakan tunda a cikinsu ya girma.

Wani turaren Oud Kareem ya feshe jikinshi dashi.
Lumshe ido yayi sabida shida kanshi ya shaida ?amshin wannan turaren nashi iyakane.

A hankali ya nufi ?ofar fita yana tafe yana tasbihi.
"Astagafirullaha wa'atubu ilaik.
Astagafirullaha zunuba jami'an. Subahanallahi Wal'hamdulillah wa la'ilahaillahu Allahu Akbar."
Da wuya ka iya jin abinda yake faWin, sai dai ina ka lura da motsawan jajayen laSSansa, masu kama da jajayen kunnen fire masu taushi zaka fahimci tasbihi yakeyi.

Ba kowa a wurin sabida haka ya nufi falo a nitse,
A falon ya samu Sitti bisa dukkan alamu, shirin tafiya harami tayi.
Tana ganinshi ta mi?e tare da cewa.
"Muje ko". Kai ya gyaWa mata, kana ya Wan kalleta bayan ya Wan tsagaita tasbihin bakinshi yace.
"Zan shiga wurin Sheykh Abdulkareem".
Cikin kula tace.
"Muje sai mun dawo mana".
Kanshi ya jujjuya mata kana yace.
"Zan sanar dashi batun komawarmu".
Gyara matafinta tayi tare da cewa.
"Na sani ai, muje sai mun dawo".
Fuskarshi ya Wan haWe tare da cewa.
"Ni a harami zan kwana".
Ganin ya kafe tasan fa duk yadda tayi, hakan zaiyi,
binshi kawai tayi,
suna shiga suka samu kamilin dottijon nan, bisa tsakiyar yaranshi, da alamun suma Win anjima zasu taho masallacin.
Yana han?oshi ya mi?a mishi, hannunshi na dama, da sauri ya isa gareshi, ya kama hannunshi tare da rusunawa, Waura hannun yayi bisa tsakiyar kanshi, sannan yayi shiru yanajin yadda dottijon ke zuba mishi addu'o'in.
Yayinda kamilan yaranshi ke amsawa da.
"Ahmeehn! Ahmeehnn!! Ahmeehnn!!!."
Bayan ya gama mishi addu'o'in ne, ya juyo ya gaida kakanun nashi, baki Wayansu.
Kana ya shaida musu tafiyarsu data taso cikin gaggawa ya kuma sanar musu dalilin tafiyan.
Sun gamsu da hakan, kasan cewar sun Wan Sata lokaci a nanne yasa. Tare suka tafi masallacin baki Wayansu.

Haroon kuwa cikin kwana biyu ya gama musu komai na tafiyarsu, gida dan shima dama yana son tafiya gida shida Jannart Winshi duka.



A cikin makarantar su Aysha kuwa.
Sam bata samu lbrin abinda ya faru a rugarsuba.

Sai da yamma, nanma Rafi'a ce, dake ri?e da wayarta tana chatting.
A nan ne ta gani a kafafen yaWa labarai cewa.
Anyi faWa a tsakanin MAKIYAYA da manoman, a garin Kikan dake gaSar kokin Namun.
Koda ta sanarwar Aysha.
Taga tashin hankali ya wuce zatonta,
hakane yasa ta bita suka tafi tare.

Su Bappa kuwa bayan sun nufi, rugar tasune, sukaci

17 / 72