Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   53 / 72

156K to 159K   out of 214K words

yace.
"Yauwa to haka zakiyi.
Sannan in sun?i yarda kada ki damu.
Umarnine gareki, kibi dukkan umarnin mijinki, kiyi mishi biyayya a cikin dukkan lamuranshi nasan bazai saki mugun abuba, kada ki saSawa umarninshi.
Kada kiyi komai saida amincewarsa.
Ki kasance mai kula da lamuran rayuwarsa kada ki bar wani abun cutarwa tare dashi.
Yanzu shine gatanki. Shine madadin GiWi, Ganin, Seyo, Lado, ?annenshi mata ki kallesu tamkar Junainah, mahaifiyarshi ki kalleta kamar Ummeynki, yan uwan mahaifiyarshi ki kallesu kamar yadda kike kallon innarku, yanzu sune ?an uwanki.
Domin naki basa kusa Ki zama GARKUWAR sa".
Shiru yayi jin kuka na son kubce mishi.
Ita kuwa tuni hawaye na kwaranya daga cikin manyan idanunta.
Cikin sanyi yace.
"Gobe zamu tafi, lardinmu, zamu koma can na wani lokaci".
Wani irin tsananin razana da tsoro ta zaro ido tare da cewa.
"Bappa zaku tafi Kardi kuma!? Ni ku barni a nan ba kowa nawa!?".
Cikin sanyi yace.
"Zamu dawo Shatu. Donke zamu dawo.
Dole muje, in sanarwa iyayen innarku abinda ya faru da ita da yaranta.
In kuma gayawa yan uwana halin da nake ciki a kan Satan yayunki, bayan salla zamu dawo. Can zamuyi azumi. Bakiga yanzu a nan ko tinkiya ba'a bar manaba".
Cikin gamsuwa da zancen Bappa ta Wan danne shesshe?an kuka tare da cewa.
"Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy. Amman Bappa ku barmin Junainah mana, a kawo min ita mana in samu i?ar uwa kusa dani".
Cikin tausasamata zuciya yace.
"Kada ki damu, su nan bazasu barki da maraiciba.
Sai mun dawo zan kawo miki Junainah da kaina".
Kit kiran ya ?atse sabida kuWin sun ?are.
Hibba da tun Wazu ta shigo tana gefenta ne,
ta Wan kalleta cikin sanyi tace.
"Aunty Shatu, meyasa kikace bakya jin daWin zama a gidan nan? Munayi miki wani abune?".
Cikin zubda hawaye ta jujjuya mata kai.
Hibba bazata fahimci halin da take ciki ba, bazata gane matsalar rayuwarta ba.
Ita kuwa Hibba cikin sanyi tace.
"Aunty Shatu nima ?anwarki ce, duk abinda zakisa Junainah tayi miki nima kisani zan miki kinji ko".
Cikin share hawayenta tace.
"To Hibba ngd".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Yauwa kuma Umaymah ta aika Ya Jamil ya sayo miki sabuwar waya iPhone".
Cikin sanyi da son tsaida hawayenta tace.
"Ngd".


Haka yammacin ranar ta yishi a bedroom Win ta.
Sai Hibba dake Webe mata kewa ne.
Da Umaymah taga basu fito bane itama taje.


Washe Gari yau Jumma'a, kuma yaune ta cika sati Waya cib a gida.
Kuma tunda yazo gidan sau uku taga Sheykh Jabeer, tun randa ya wucesu, suna batun abinci bata sake ganinshi ba, koda a gilme ne.
Yanzu ta saba da Umaymah Sosai hakama Ummi
Ita da Hibba kuwa sha?uwa ta fara ?arfi a tsakaninsu.
Tana jin Hibba kamar Junainah.
Jamil da Jalal Haroon suna Wan zama asha hira dasu.
Yau ne kuma Haroon zai tafi Leddi julSe, sabida yayi masifar kewan Jannart Win shi, wacce ta?e ?anwace ga Aunty Juwairiyya, kuma ?awance ga Ibrahim.

?arfe Waya dai-dai, Sheykh Jabeer, ne tsaye gaban dreesing mirror yana fesa turare bayan ya gama shirin jummarsa tsab.
Yau shigar ba?ar Al'kebbar da farar jallabiya yayi.
Yayi wani irin kyau mai cike da she?i.
Kusan a tare suka jero da Haroon wanda yake cikin shigar ?ananan kaya.

Su kuwa suna falon suna, zaune.

Jamil da Jalal da Ya Jafar kuwa suna tsaye alamun fitowar Sheykh suke jira.

A hankali Shatu ta Wan Wago kanta jin wani irin masifeffen ?amshi mai daWin sha?a.

Da sauri ta janye ?wayar idanunta,
Sabida idonta da suka faWa cikin ?wayar idanunshi.
Wanda shi kuwa Jalal yake kallo ganin wani shegen wondo wai shi crezi ne ko meye ne oho, duk yana SuSSule har kana iya ganin farar fatar cinyarsa.
ga saSulellen wonWo ga kafurin aski.
fuskarshi ya tsuke tare da jan gajeren tsaki wanda shiyasa Jalal juyawa, ya nufi hanyar fita yana cewa.
"To Ni banifa da manyan kayan nan, yanzu bari inje in duba ko inada jallabiya sai in saka a kai zan biyoku daga baya."
Da ido suka bishi. Haroon da Jamil kuwa murmushi sukayi.
A haka suka fita suka tafi. Har sunje bakin ?ofar fita ba tare da ya juyoba yace.
"Umaymah ku tashi lokacin salla yayi". Ya ?arishe mgnar suna fita
To tace.

Kana suma su Ummi suka nufi Wakinsu.
Aunty Juwairiyya kuma ta wuce Side Winta.

Ita kuwa Shatu da Hibba suka tafi Walinta.
Hibba ce ta fara shiga tayi al'wala.
Sannan itama Shatu ta shiga.

Tana fitowa daga bathroom Win tayi wani irin....!




Uhummmmmm tuni mun gama shimfiWan lbrin GARKUWA yanzu dai muna cikene dumu-dumu .

By
*GARKUWAR FULANI*
Ta kamo hannun Jalal da ya mi?e tsaye da nufin yarfa mata mari.

Cikin wani irin masifeffen tsana, Hajia Mama takalli Shatu.
Kana da sauri ta juya ta nufi hanyar fita.
Sheykh da tunda ya fito yake tsaye tamkar an dashi ne,
yayi saurin bin bayanta tare da cewa.
"Hajia Mama! Mama!! Mama dan Allah kiyi ha?uri, kizo karki fita Please Mama karki fita, babu wata halitta da zata miki iyaka da sashina, in kin tafi kenan kinbi umarninta."
Cikin tashin hankali yake waWannan kalaman yana mai binta a baya.

Jamil kuwa mi?ewa tsaye yayi ya zubawa Shatu idanu tamkar zasu faWo ?asa.

Aunty Juwairiyya kuwa, wani irin kallo mai sar?afe da ma'anoni takeyiwa Shatu.

Ya Jafar kuwa wani irin kallo mai surke da murmushin jin daWi yakeyiwa Aysha.

Ummi kuwa tuni jikinta rawa yakeyi da abinda ya faru.

Imran, Ya Hashim, kuwa ido suka zubawa sarautar Allah.
Hibba kuwa kuka takeyi tare da ri?o hannun Shatu tana ja tare da cewa.
"Aunty Aysha ki bari, Mamace fa! Kizo mu tafi Waki".
Tanayi tana jan hannun Shatu da ?arfin tsiya, dole yasa Shatu ta bita a baya.

Umaymah kuwa wani irin tashin hankali da tafasan zuciyane ya dirar mata lokaci Waya.
Da wani irin kallo tabi bayan Aysha dashi.

Duk wanda ya ganta yasan tana cikin tashin hankali.
Gaba Waya jikinta rawa yakeyi.
Sun daWe a haka, da kyar dai
Cikin wani irin tafasan zuciya ta saki hannun Jalal.
Tare da komawa ta zauna.
Da yatsa ta nuna musu hanyar fita daga falon. Murya a hargitse tace.
"Kul kada ka sake tunanin gigin Waga kayi nufin taSa lfyar Aysha, bana so kul.
Maza Ku tafi masallaci".
Sai lokacin suka jiyo sautin muryar Jabeer yana Hudba.
Wanda daga jin muryarsa kasan yana cikin ba?in ciki.

Wani irin numfarfashi Jalal ya sabke tare da yin koffa kana ya juya ya nufi hanyar fita shi matsalarsa meyasa Umaymah na mgn Aysha na mgn Umaymah na hanata abu tanayi.
Haka su Jamil da su Imran da ya Hashim da Ya Jafar suka fita.

Ita kuwa Aunty Juwairiyya wani irin tashi tayi ta fita ta nufi Side Win ta.

Ya zama Ummi da Umaymah ne kaWai suka rage a falon.

Shiru sukayi tamkar ruwa ya cin yesu.
"Uhuhhmmmm". Umaymah ta fesar da wani zazzafan numfashi mai Wumi.
Hakama Ummi tagwayen numfarfashi masu nauyi ta sau?e.
Kallon juna sukayi, cikin shiga al'hini wannan al'amari cikin tsoro da karaya Umaymah tace.
"Toh wai meye hakan? Meke faruwa ne? Me hakan yake nufi? Kaina ya kulle. Wani zagon kasan kuma aka shirya tsakanin Shatu da Hajia Mama ko dai dama da zagon ?asan ne?.
Wake sa?a gadar zare, muna na bi ta kai ya rubta da mu".
Wani numfashin Ummi ta fesar tare da cewa.
"Tabbas akwai babban al'amarin dake faruwa wanda bamu saniba Ni tsorona Waya kada a juya ?o?walwar yar mutane."

Shiru sukayi cikin ta'ajjudin al'amarin. A hankali suka mi?e a tare suka nufi Wakinsu jin har an idar da sallan a masallacin.
Al'wala sukayi kana sukayi salla daga bisani suka, fara tattauna wani abu na sirrin masarautar JoWa.

A cikin Wakin Shatu kuwa, tunda suka shiga ta kwanta bisa gado.
Bacci tayi bacci, hakama Hibba.
Sai ?arfe uku dai-dai Shatu ta tashi.
Cikin kasalan baccin da bai gama isarta ba, ta mi?e ta shiga bathroom.
Wonka tayi tare da al'wala.
Bayan ta fitone, ta tada Hibba, ita kuma ta kabbarta sallah.

Kafin ta idarma Hibba ta fito, gefenta tazo itama ta kabbarta sallan.

Basu tashi bisa sallayan ba, sukaji kiran aallan la'asar.
Haka yasa sukayi sallan. Suna idarwa Hibba ta mi?e ta nufi Wakin Umaymah.
Ita kuwa Shatu ninke sallayar tayi kana ta dawo gaban dreesing mirror.
Mai ta shafa tare da Wan murza fauda a fuskarta, kama ta shafa man baki.

A cikin sanyi taje gaban drower'nta,
hannu tasa ta buWe drower'r, wata tattausar doguwar riga mai masifar kyau ta zaro.
Kalar rigar Black blue mai she?i, saman rigar a Wan tsuke daga ?asan ?ugunta kuma a buWe,
yanada wasu duwasu kamar na Daimond daga sama har ?asan gaban rigar.
Hannunta kuma masu faWi.
Tayi kyau sosai cikin rigar, dogon gashinta ta haWa ta tubke wuri Waya ta kitse jelar kana ta nannaWe jelar a ?eyarta,
sannan tayi rolling kanta da mayafin wanda dai dai inda zai zauna a goshin akwai duwatsun.

Turare ta fesa, kana cikin sanyi da kasala ta nufi, falo.

A falon ta samu, Hibba a kwance tayi shiru.
Ganin bata gan fitowarta banema,
Yasa ta nufi inda take gefenta ta zauna tare da cewa.
"Hibba Wauko mana awaran".
Cikin sanyi Hibba tace.
"To". Kana ta mi?e ta nufi falon, jin shiru ba kowa a cikine, yasa ta nufi kitchen a hankali-hankali.
Foodflaks Win da suka sa awaran da suka soya ta Wauko.

Tana dawowa ta zauna kusa da Shatu tare da cewa.
"Gashi". Kai ta gyaWa mata tare da nuna mata kitchen Win ta, tace.
"?auko mana plate da roban yajin da Gimbiya Aminatu ta aiko mana.
Kizo mana da ruwa".
Ba tare da tace komaiba ta juya ta tafi.

Bayan ta dawone suka zauna suka fara cin wanda suka zuba.

A can falon Hajia Mama kuwa,
duk mgnar da Umaymah da Ummi keyi, shiru tayi ta zuba musu ido.
cikin sanyi Umaymah tace.
"Addana kiyi ha?uri, kin san yaran sai a hankali, dan Allah kada kisa wani abun a ranki wata ran ko ance tayi miki bazatayi ba".
Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kana tace.
"Uhummm ba komai Khadijah jekici gaba da shirin tafiyarki, karki damu kinji".
Ido suka zuba mata domin duk basu gamsu da mgnarta ba, to amman ya zasuyi tunda tace ba komai.

Haka suka tashi suka dawo falon.
Yau su Jalal ma basu zoba.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, tunda aka idar da sallan azahar ya dawo, ya wuce su Umaymah a falon ba tare da yace musu ?alaba.
koda ya shiga Wakin ya samu yayi bacci tsakanin azahar da la'asar kamar yadda ya saba, hakan bai samuba.
Sabida abubuwan dake ranshi.
Bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, tare da fara yage towel Win dake hannunshi.
haka yake tsaye a ?asan ruwan har saida yaji an kira sallan la'asar. Nanne ya fita ya tafi masallacin.
Bayan an idar da sallan ne ya dawo gida.
Ganin babu kowa a falon ne yasashi zama, bisa kujerarsa.
?afarshi Waya ya Waura kan Waya.

A haka su Umaymah suka sameshi.
Gefenshi Umaymah ta zauna bisa kujerar dake kusa dashi.
Ummi kuwa gabanshi ta zauna bisa carpet.

A hankali ya buWe kwayar idanunshi.
Cikin tarin Sacin rai ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi ina wannan fitsarerren abun da bai san darajar manya ba!?."
Cikin sanyi Ummi tace.
"Allah ya huci zuciyarka tuba takeyi, in sha Allah bazata sakeba, Hajia Mama da kanta ta yafe mata".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Ummi ko dai kece kika bata dama da matsayin yiwa Mama hakane?".
Cikin sauri tace.
"Wanne ni wlh bani bace".
Kanshi ya Wan juyo ya kalli Umaymah da itama shi take kallo cikin Sacin rai yace.
"Umaymah har akwai wani abun da zai hana mama shigowa sashina? Har yaushe waccar babyn robar ta samu dama da ikon bada izinin shiga da fita cikin sashina da abinda ya shafi rayuwata?
Me take nufi dani da iyayen nawa."
Kauda ido Umaymah tayi daga kallonshi kana a hankali tace.
"Ba isa bane! Akasi aka samu! Nifa inaga har yau Shatu'n bata gama sanin mutanen masarautar JoWa da kuma dangantakar makusan tankaba, ayi mata ha?uri a mata uzuri a dai wannan karon".
Juyowa yayi ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi a kira min waccar abar".
Da sauri Ummi ta mi?a tare da cewa to.

A falon ta samesu, cikin fuskar da babu yabo babu fallasa ta kalli Shatu dake gefen Hibba da alamun ta cire hannunta a cin awarar kanta ta Wan kauda tare da cewa.
"Kizo Sheykh yana kiranki".
Kai ta gyaWa tare da cewa "Toh". mi?ewa tayi taje Dinning area ta wonke hannunta, kana tazo tabi bayan Ummi.

A gabanshi Ummi ta zauna ganin haka itama ta zauna a gabanshi.
shiru tayi tana kallon yatsun fararen sawunshi. Shi kuwa kanshi na gefe ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace.
"Ke ki shiga hankalin ki, kisan abinda kikeyi da wanda zakiyi! Ke har kin kai matakin da isar da zaki ?addamar min da iko da isa a cikin gidana? Ko dai ce miki akayi gidan nakine?".
Kai ta gyaWa mishi alamun eh ance mata gidan natane!.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da ci gaba da mgna dan shi bai ga sanda ta gyaWa kanba hakama Umaymah, sai Ummi ce kaWai ta gani, su kuwa sai murmushi sukayi.
Cikin kausasa murya yace.
"In baki san darajar manya da iyayeba, to ki zama kurma bebiya makauniya a cikin giddannan kafin Ubangiji ya zantar da Hukuncin da ikon zamanki da barinshi dan ikone na Allah bana waniba.
Har kin isama Mama tazo ki koreta dan idonki basu da Wigon kunya.
Ko karen gidannan baki da ikon hanashi abu da sakashi bare Mama.
ke ta bawa abun ne da zakice bakya so.
Kece mai bakin mgn uwar fitsararru ko?".
Sam abinda bai saniba zuwa yanzu hankalinta, tunaninta nitsuwarta, jinta, da ganinta duk suna kan farar ?amarshi ta dama, da zanen maciji ke li?e kamar macijin na tafiya.
Wani irin ba hagun numfashin ta sau?e a hankali,
tare da rufe manyan idanunta da azaban ?arfi.
Sabida gani takeyi Tamkar macicijin ne ma da kanshi ke manne a jikinshi yana kuma motsa Wan bindinshi dake saman babbar yatsarshi.
A hankali ta buWe idanun kana tabi kan rumfar ?afar da ido, inda take ganin zanen maciyar yabi.
Kasan cewar a zaune yake ya kuma Wan tattare al'kyabbar jikinshi.
Shi yasa tana iya ganin har ?arshen rumfar tafin ?afar nashi.
Inda iya nan jallabiyar jikinshi ta rufe.
da sauri ta ?ara rusunar da kanta wai ko zata ga ci gaban tafiyar macijiyar.

Umaymah ce ta Wan kalleta cikin wata iriyar murya tace.
"Ki tashi muje ki bawa Hajia Mama ha?uri, ku nemi yafiyarta ki kuma kiyaye gaba, kinji".
Cikin sanyi tace.
"Toh".
Still Bata mi?eba, cikin Wan Waga murya yace.
"Tashi muje yanzu ki bata ha?uri, in ta ha?ura kinyi babban Sa'a".
cikin sanyin jiki ta mi?e tsaye.
Shima mi?ewa yayi, Ummi kuwa da sauri ta nufi Wakin Shatu.
Jim kaWan ta fito da wata kekyawar al'kyabbar matan masarauta ta zuramata.
Bayan ta gama gyrashi ne, tasaka hular.
Shi yayi gaba ita kuwa.

Tabi bayanshi Umaymah da Ummi suka biyo bayanshi.

Suna isa bakin mashigar farfajiyar Side Win Hajia Mama,
ta tsaya gis tare da yin ?asa da kanta.
Ummi ce tace.
"Muje mana".
Shiru batayi mgna ba, jin hakane yasashi juyowa, karon forko kenan da ya zubawa tsawonta ido.
cikin Sacin rai yace.
"Muje ki lashe aman da kikayi da kanki".
Cikin sanyin sauti tace.
"Ni bazan shigaba".
Da mamaki Umaymah tace.
"Innalillahi wai ke Ayshs wani irin taurin kaine dake? Menene manufarki?".
Murya can ?asa yana rawa alum zatayi kuka ta kalli Umaymah tace.
"Kiyi ha?uri Umaymah ki gafarceni, amman ni bazanje ba, in kuma zanje to ku ku koma, zanje ni Waya zan bata ha?uri".
Cike da al'ajabi Umaymah tace.
"To sabida me bazaki je da muba".
Cikin faWa Sheykh yace.
"Sabida muna furci mana, ba zuwa zatayi ba, shiyasa zatace sai dai in ita Waya zataje, maza wuce muje a gabana zaki bata ha?uri".
Cikin sanyi Umaymah tace.
"Jazlaan barta mu tsaya mu jirata anan in dai zataje ita Wayan".
Kanshi ya dafe tare da cewa.
"To wai Umaymah mu bayaninta ne da zamu tsaya muna jiranta".
Ummi ce ta mishi alamun yayi ha?uri ya yarda.
Shiru yayi tare da komawa gefen jerin bishi yoyin namiji kwanWa ya zauna bisa kujerun silver dake zagaye da wurin wanda ko wani side akwaisu.

Itama Umaymah da Ummi zuwa sukayi suka zauna.
Ita kuwa Shatu a hankali ta fara taku ta nufi cikin farfajiyar, suna hangota har ta isa bakin ?ofar.
turawa tayi ta shiga, kana ta maida ?ofar ta rufe.

Bayan kamar 37 minutes ta fito.
Cikin wani irin tafiya mai baiyana tsantsar jin daWi, fuska cike da fara'a ta nufosu.
A hankali ta isa gabanshi ciki Wan Waga murya tace.
"Na bata ha?uri ta yafe min, ta samin al'barka. Kaima kayi ha?uri ka yafe min".
Da mamaki suka kalleta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer wari irin kallon tuhuma yayi mata, kana ya mi?e tsaye tare da cewa.
"In ma ?arya kikayi, ni ba'amin ?arya".
Sai ya kuma kalli Umaymah tare da cewa.
"Umaymah kuje ki ?arisa shirinki bari inje wurin Hajia Mama".
To tace kana taja hannun Shatu suka tafi. Shi kuwa da Ummi suka nufi cikin Side Win Mama.

Bayan sallan isha'i, cike suke a falon. Gaba dayansu, Umaymah zaune a tsakiyarsu da jakarta, Sheykh Jabeer na yi mata addu'o'in isa lfy suna amsawa da Amin Amin.
Bayan sun shafa addu'o'in ne ta mi?e tsaye, tare da kallon su baki Waya, murya na rawa tace.
"Jazlaan zan tafi, zan bar hankali na, a nan ko na koma banda nitsuwa, kullum ina cikin taraddadin abubuwanda yake faruwa, Jazlaan na sani kaine GARKUWAR yayanka da ?anneka. Ga wani sabon nauyi ya ?arun maka.
Aysha ba?uwace bata san komaiba kam al'amuran Masarautar JoWa, dan Allah in tayi abinda ba dai-dai ba kuyi mata uzuri.
Ita komai a sabon abu zata ganshi abinda bata taSa ganiba.
Mun rabata da iyayenta yayunta ?annenta mun kawota tsakiyarmu, mu kasance mata adalan masu masau?i.
Na sani Jazlaan ka fini sanin haka da kuma ha??o?inta da suka rataya gareka."
Sai ta kuma kalli sauran yaran yar uwarta Win tace.
"Jalal, Jamil, Aysha matsayin yar uwarku take, yayarku ce, matar yayanku. Bana son raini especially kai Jalal, ban gamsu da irin mu'amalat Win ka da itaba.
Babu wanda yake nuna min yadda nakeso a kanta sai Jafar, a duk sanda ya ganta zaiyi mata murmushi kamar yadda yake min, in yaga bata nan zaiyi ta dube-duben da nasan da yanada baki zai tambayeni lfyarta.
Zan bar Hibba saboda itane, bana son taji kanta a matsayin bare."
Shiru sukayi gaba Wayansu sabida yadda take kuka da yin mgna tamkar mai bar musu wasiya, ko wacce wani tsohon damuwa ya taso mata.
Sharce hawayenta tayi tare da cewa.
"Ummin Jabeer zan tafi zan barki da sauran aiki, dan Allah ki kula da Shatu da mu'amalarta da Hajia Mama, ki nuna mata uwar miji ba abun rainawa bace".
Sai kuma ta mi?owa Aysha da taketa kuka hannun ta jawota tsaye ruggume ta tayi cikin zubda hawaye tace.
"I dan akaga damuna ana zaton yabanya zatayi kyau, kallon damuna nakeyi miki a cikin ahlin yar uwata.
Ina jin zaki zamo man??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a haske mai yaye

53 / 72