Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   31 / 72

90K to 93K   out of 214K words

yasashi sa hannunshin ya Wan ?on?osa ?ofar bathroom, still shiru.
Hakane yasa ya Wan tura ?ofar, wayam baya ciki.
Ganin hakane ya sashi juyawa,
shima Win cikin takun ?asaitar ya fito gefen Jalal ya zauna tare da kallon Juwairiyya,kana yace.
"Baya cikifa".
Wani irin kallo Mom tayi mishi, wanda yake nuna abinda ke bakinta, cikin Wan sakin fuska yace.
"Allah kuwa Mom baya ciki".
Kanta ta gyaWa tare da yun?ura ta tashi tsaye.
Kana a hankali tace.
"Uhummm". Sai kuma ta juya ta kama hanyar fita, hadimanta na biye da ita a baya.
Har yaje bakin ?ofa ta juyo tare da cewa,
Ga breakfast Win Garkuwa".
Haroon ne yayi godiya kana ta juya ta fita.

Cikin mmki Haroon ya kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil baya cikifa".
Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Kun dai haWa baki, kun?i ya fito, ya gaisa da Mamanshi".
Jalal ne ya ?ara tsuke fuskarsa tare da cewa.
"Mamarshi ko makirarshi".
Jakadiyarsu ta Wan gyara zama tare da cewa.
"Uhummm, sanin halin mutum sai Allah".
Sai kuma ta kalli Haroon tace.
"Haroona kace mishi yazo yayi karin kumallo, kace mishi daga sashin Gimbiya Aminatu ce, ga kuma na Juwairiyya".
Cikin jaddawa yace.
"Allah kuwa Ummi baya cikifa".
Da mamaki a fuskokinsu suka Wan kalleshi, Jamil ne yace.
"Bai fita bafa".
Juwairiyya ce, ta amshi zancen da cewa.
"To kuma dai bai biyo nanba, tunda ya shiga bai fitoba".
Shi dai Haroon Ido ya zuba musu, ganin kamar basu yarda Jabeer baya cikiba.
Kuwa hakanne, saida Jamil yaje ya duba babu shi a ciki babu alamarsa.

Cikin tarin mamaki ya sanar musu, baya nan Winfa.
Jalal ne ya Wan kauda tunaninsu da cewa.
"To kunata surutu, ta ina zakuga sanda ya fita, kai Jamil hankalinka duk na kan waya ina zaka ganshi."
Cikin kula Jakadiyarsu tace.
"Kaga fitarsane?".
Baki ya Wan taSe tare da cewa.
"Ni ban ganiba, na dai san shi ba kuWi bane bare ya Sata, ku jira zaku ganshi".
Da haka sukayi amanna dan a zatonsu yaga fitarshi kawai bauWewarshi ne yasa bazai sanar musuba.

A can cikin fadar Masarautar JoWa kuwa, falon sashin mai martaba LamiWo, cike yake da ?a?anshi maza, ziryan, wanda kullum iwar hakan suke haWuwa domin gaidashi kana su gaisa da juna, ya tambayi lfyar ko wanne Wanshi da ahlinshin.
To yau ta kasance jumma'atu babbar rana, wanda kuma, duk safiyar jumma'a.
Cikin wani Wakin gadon sarautarsu, yakan shiga shida kanshi, yake tsabtace wannan Wakin duk ran jumma'ar duniya, a tarihi da tsarin masarautarsun babu wanda zai shiga Wakin sai wanda yake, matsayin Sarki.
Babu wani wanda ya taSa shiga wannan Wakin, sai wanda yake sarki.

Suna cike a falon a ?alla sun kai su bakwai dukansu. Manyan mutanene masu tarin wadatar duniya, jinin sarauta na yawo a jikinsu.
Suna zaune kamar yadda kullum suke zama, suna Wan hira a tsakaninsu.

Habibullah ne, zaune a can tsakiyarsu a matsayinsa na shine babban Wa ga LamiWo, hannunsa ri?e da.
CarSi, sai gefen damansa, Alhaji Sani, sai kuma Barrister Kamal, kana sai. Dr Aliyu, kana sai, Badamasi, Nasiru, basiru.
Dr Aliyu ne, ke gefen daman Habibullah, bisa alamu duk mgna yakeyi mishi a kan lfyarsa.
Bappa Nasiru, wanda shine, yake bin Habibullah a girma sai dai uwarsu ba Waya ba, gyara zama yayi tare da jan dogon tsakin da yasa duk suka meda idonsu kanshi.
Cikin kula Habibullah yace.
"Lfy dai Nasiru?."
Wani irin kallo mara daWin gani ya watsa mishi tare da cewa.
"Yes lfy lau, sai dai mu nan duk muna da aiki, ba zauna gari banza, irinka bane, kowa yanada hidimar yi gashi har yanzu,
LamiWo bai fitoba".
Murmushi yayi ba tare da yaji ciwon abinda ya gaya mishibs, a hankali yace.
"To Nasiru, ai duk saurinka kayi ha?uri dai ya fito, kaga lfyarsa yaga taka, tunda shi bai gajiya da bincikar lfyarmuba, ai muku wa bazamu gazaba.
Domin abune mai wucewa".
Wani irin kallo mai cike da tsana da tsoggoma ya mishi tare da kauda kanshi.
Basiru ne yayi dariya alamar jin daWin kallon da Wan uwanshi yayiwa Babban yayansu da suke ?an uba.
shi kuwa Habibullah Abbansu Sheykh, kauda kai yayi kar bai ganiba.

Kusan a tare suka mi?e gaba Wayansu,
tare da haWa baki wurin cewa.
"Barka da fitowa, Mai alfarma LamiWon JoWa."
Murmushi yayi tare da kallon ?a?an nashi Waya bayan Waya, a hankali ya ?arasa fitowa, hannunshi sar?afe da hannun Jabeer.
Wanda baiyanarsa yasa, gaba Waya suka zazzaro ido. Cikin tarin mamaki, al'ajabi, firgici, kaWuwa, gamida tsayawar idanunsu kan Wan babban yayan nasu, cikin wani irin daskarewa, suka juyo suka fuskaci, junansu wannan ya kalli Wannan wannan ya kalli wancan.
Murya a daburce, Nasiru ya nuna Jabeer dake tsaye, cikin wani masifeffen al'kyabbar mai masifar kyau da zadan gaske, cikin ?afewan yawun baki yace.
"Ka gafarceni LamiWo, me idonuna ke gani, daga ina ka fito da Jabeer? Me kayi dashi? Meye ma'anar hakan? Mu duk ?a?an ka bamu kai ka shiga damu ba sai shi?".
Cikin tsare fuska irin ta manyan sarakai dattawan,
ya zubawa, Nasiru idanu, wanda dole tasa ya hadiye rahowar maganar tasa.
Habibullah kuwa, wani irin rawa da karkarwa jikinsa ya fara.
Wani masifeffen tsoro da fargabane ya rufeshi akan Wan nashi, koda dai baya jinsu a ranshi kamar sauran ?a?anshi, hakan bai hanashi tsoro da fargabar abinda zai cutar dasuba. Barrister Kamal kuwa.
Wata irinyar madifeffiyar zuface ta keto mishi daga saman kanshi har tsakiyar tafin sawunshi.
Lokaci Waya yaji wani irin abu ya saki ?ahon zuciyarshi,
Ma?o?oronshi ya bushe ?amas,
duhun daya rufe mishi idone yasashi komawa zaune.
Dr Aliyu kuwa, wani irin murmushi yakeyi yana kallon Wan babban wansun.
Shi kuwa LamiWo hannun Jabeer ya kuma ja, wanda yake motsa laSSansa a hankali yana tasbihi kamar yadda ya saba.
Zama yayi kujerarsa ta musamman, kana Jabeer kuwa ya zauna gabanshi.
Cikin tattaro yawun baki Barrister Kamal yace.
"Barka da safiya. Sarkin JoWo.
Sai ya kuma danne tarin ba?in cikinsa yayi mishi rumfa da fuskarsa ta zahiri kana ya kalli Jabeer da ya Wan sunkuyar da kanshi tare da gaidashi.
Cikin dakiya yace.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen JoWa.
Yaushe a gari".
Kanshi ya Wan kauda tare da cewa.
"Daren jiya".
Nasiru ne ya katsesu da cewa.
"LamiWo, Wakin sarautar sarakunan JoWa kuma ya zama kowa zai iya shigane?".
Bai kulashi ba, har saida suka gaisa gaba Wayansu, kana, ya fuskancesu, duka cikin hikima da, kaifin basira yace.
"Rigar sarautarsu ta GARKUWAN FULANI, na bashi.
Sabida akwai tafiyar gaggawa da zamuyi zuwa, Rugar Bani, da ?aSilun wurin suka far musu da kisa."
Kai suka gyaWa alamun gamsuwa, kana duk, ya sallamesu.

Duk suka fita kowa da abinda ke cikin ransa, da zuciyarsa.


Bayan fitansu ne ya kalli Jabeer cikin, tarin kula yace.
"Kaje ka shirya kazo mu tafi".
Kanshi ya kuma rusunarwa cikin ladab yace.
"Allah saine, mu bari sai bayan sallan, jumma'a ina munyi jam'i anan, mu tafi gudun kada muje bamu dawoba kafin lokacin sallan."
Gyara zamanshi yayi tare da gyaWa kai kana yace.
"Ha??un kayi, gsky to mu bari sai an sau?o mutafi, in yaso muyi sallan la'asar a can."
Da Wannan shawarar suka bari sai bayan sallan, azahar Win su tafi.
Sun daWe suna tattaunawa kafin, ya sallameshi ya tafi, shi kuma ya nufi fada.


A falonshi kuwa, yana shigowa duk suka zuba mishi ido, da mamaki cikin za?uwa Jamil yace.
"Hamma Jabeer wai ta ina kabi ka fitane? Duk bamuga fitankaba".
Kanshi ya mirgina, alamun gajiya, kana a fakaice ya kallesu baki Wayansu, tare da cewa.
"Sama".
Murmushi sukayi baki Wayansu, sabida fahimtar amsar daya basu, na nuni basuga sanda ya fita bane.

Bisa wata tattausar doguwar kujera ya zauna.
Kana ya fuskanci ?annen nashi da kyau.
Jalal ne ya Wan sunkuyar da kanshi, ganin yadda Hammanshi ya zuba mishi ido, Jamil kuwa, kanshi ya Wan rausayar tare da katse wayar da yakeyi, ya fuskanci Wan uwan nasu,
Cikin yin fiki-fiki da idanu yace.
"Barka da safiya Hamma Jabeer, ya hanya?".
Alhamdulillah, yace mushi a ta?aice, kana ya Wan gyara, hiramin dake bisa kafaWunshi.
Jalal ne ya Wanyi baya tare da lumshe idonshi cikin saisaita muryar da indai da Hammanshi zaiyi mgna to sai ya nitsu ya gyarata,
Domin yakanji yanada rauni duk sanda yake gaban Hammanshi, yana ji tamkar a gaban mahaifinshi yake.
Cikin sanyi yace.
"Ina kwana? Hamma Jabeer, ka dawo lfy t
yasu Sitti?".
Ido ya Wan kauda kana yace .
"Alhamdulillah, Jalal ya jikin Ya Jafar?".
Kanshi ya Wan jujjuya kana a hankali yace.
"Kalmace dai ta musulmi, koda cuta babu sau?i ya zame mana Wa'a muce, da sau?in, amman a zahirin gsky ciwon Ya Jafar babu sau?in, komai yaci tura, abubuwan sun yawaita".
Ya ?arishe mgnar tamkar zaiyi kuka,
ganin hakane yasa Jabeer Wan kauda kanshi, Allah yasani, baya son ganin ?unci ko ba?inci ko wata damu a fuskarsu, sabida ya Wauka cewa Allah ya barshi da rai da lfy ne a tsakiyarsu, su da akewa kallon marasa lfy ya zame musu Garkuwa. A hankali ya mi?e cikin kula ya kallesu, murya a Wan macce yace.
"Kuzu kuci abinci".
To sukace baki Wayansu, kana duk suka nufi, dinning table Win.
Wanda yake cike da abinci kala-kala.
Juwairiyya ce ta sakawa kowa abinda yake bu?atar ci,
Shi kuwa Sheykh sai jujjuya mata kai yayi alamar babu abinda zaici.
Ya dai zauna yana kallonsu,
Ummi kuwa, tana gefenshi.
Kanshi ya Wan juya ya kalli Haroon dake shan tea kuma still wayarshi na kunne yana, mgna da Jannart,
Wan gajeren tsaki Jabeer ya ja, jin Haroon na cewa.
"Ina yin breakfast ne, ke me kikeyi? Bacci? Ko kwaliya? Ko kallo?".
hannunshi yasa ya zare wayar kana ya katse kiran tare da mishi nuni yaci abinci kafin ya tsaya yin waya.
Cikin haWe fuska Haroon yace.
"Ka ganka ko? Ni shiyasa har tsoron zama kusa da kai nakeyi, sabida tsarabe-tsarabenka nada yawa, yanzu zaka fara jawowa mutum aya da hadisai, kana wani, abu kaza ba laduban kaza bane, in an jika kayi doguwar mgn to an sosa maka wuri biyu, ko ayar Allah, ko wannan mulkin da kake cewa an li?a maka jaraba".
Jamil ne yayi ?ar dariya tare da cewa.
"Mulkin nema jaraba a wurin shi ko? Gacan wasu na neman, zaunece sabida Garkuwan da aka bashi".
Jalal ne ya Wan tsuke fuskarsa tare da cewa.
"Ni kaina Wannan GARKUWAN bai wani burgeniba, sabida baya cikin, masu iya gadar mulki, sabida shi ai ba jikan sarki ta wurin ?a mace bane, jikanshi nefa ta wurin Wa namiji ta yaya zai bashi Garkuwa?".
Ummi ce taja wani dogon ajiyan zuciya tare da cewa.
"Uhummm ta yaro kyau take bata ?arko, to kai Jalaluddin, yanzu Jafar da aka bashi Galadima, wani hali yake ciki? Tun randa aka naWa masa sarautar me mutane suke kallon ya zama? Dukfa duniya kallon majanun akeyiwa Jafar".
Juwairiyya ce ta Wan rumtse idonta tare da cewa.
"Ni banyi fataba, banso a sake bawa Kowa wani mulkin da nasan baza'a barku lfy ba, shi LamiWo, meyasa ko ?a?an nashi babu wanda ya bawa mulkin komai?".
Da sauri Ummi tace.
"Sabida muddin yace zai basu sarautu, to wasu zasu hallaka wasu".
Cikin da?ilewa Jalal yace.
"Ok shine sai ya zaSi ?an Wakinmu a matakan zakarorin gwajin dafi? Ya bawa Ya Jafar Galadima, yaga yadda aka medashi dare Waya, da rashi da bazamu samu madadinshiba a duniya, an cire hankalin mahaifinmu a kanmu, sannan ya kuma bawa Hamma Jabeer wani mulkin, salon a sabautashi kenan, nest target nasu kuna, wato a kanshi ne?".
Shiru sukayi jin Jabeer na cewa.
"Azzannu zambu walau kana ha??un, na haneku da irin waWanan zantukan, babu wanda ya isa, ya cutar da wani sai Allah, domin shine mai rayawa, kuma mai kashewa, mai badawa, mai hanawa, mai cuta mai waraka. Ummi har kema, ya zakiyi ki zauna kina gaya musu hakan, to waye zai cutar damu, acikin ahlinmu, daga ?annen mahaifinmu fa, sai ?annen kakanmu, sai matasansu da jikokinsu, sai kuma ?an uwanmu, dan Allah ku bar munanawa mutane zato."
Juwairiyya ce ta Wan girgiza kai.
Shi kuwa Jabeer, cikin bada umarni yace.
"Juwairiyya jeki duba Ya Jafar, nasan zuwa yanzu ya tashi daga baccin."
To tace, kana ta mi?e ta nufi tsakiyar falon. da sauri ta tsaya tare da Wan raSawa gefe, sabida ganin Gimbiya Saudatu, na tsakiyar falon.
Da sauri ta Wan rusuna tare da cewa,
"Barka da fitowa Gimbiya Saudatu".
Zama tayi bisa kujerar da Jabeer ke zama, Waura kafarta tayi Waya kan Waya.
Hadimanta, biyu ne suka zauna gefe da gefenta.
Fuskarta babu wata alamar annuri, sai tsantsar tijara, cikin isa da ?asaita tace.
"Kai Jabeer!."
Ido Jakadiyarsu ta zazzaro cikin firgici da tsoro ta kalli Jabeer da a take fuskarshi ta sauya launi,
cikin rawan jiki da tsoro tayi ?asa da murya tare da cewa.
"Jabeer ka amsa, Gimbiya Saudatu ce, da kanta."
Jalal ne da Jamil suka kalli juna, kana suka maida idonsu, kan Hamman nasu, da ya lumshe idonshi ya koma ya jingina tamkar badashi akeyi ba, kamar daga sama suka jiyo muryar Gimbiya Saudatu tana ratsa kunnuwansu.
"Kai Jabeer, ka fito kazo nan, ina nemanka".
Still bai buWe idanunshi bama, bare ya amsa ko yun?urin tashi,
sai dai laSSan bakinshi da suke motsawa yana maimaita sunan Allah a zuciyarshi da harshenshi.

Zuwa yanzu Gimbiya Saudatu tayi masifar kufula, cikin wani irin mugun kallo ta kalli Juwairiyya da jikinta ke baiyana tashin hankali ta, cikin isa da ?asaita tace.
"Ke maza wuce, kije tun wancan karen larabawan da suka turo ahlin masarautun FulSe, dan samun damar maida masarautun a hannunsu, kice mishi yazo dan kan uwarshi".
Da ?arfi Jabeer ya rumtse idanunshi, wani irin bugawa zuciyarshi ta farayi a saba'in.
Ita kuwa Juwairiyya kasa motsawa tayi daga inda take tsayen.
Ummi kuwa cikin firgici, ta kalli Jalal daya mi?e tsaye tamkar wanda aka tsabura.
Jiki na rawa ya ture kujerarshi, zaiyi baya ya fita ya nufi inda taken.
da sauri ya juyo cikin tarin zafin rai jin an ri?e mishi, hannunshi.
ganin Hamma Jabeer Winsune ya dam?i hannunshi ne ya sashi, taune lips Winshi da masifan karfi.
Jamil kuwa ido ya zubawa Hamman nasu yana ganin yadda jikinshi ke karkarwa, kowa ya sani duk duniya babu abinda yake saurin harzu?a Sheykh sama da a zagar mishi iyaye Especially uwa! Haroon kuwa zuru yayi da idanu yana kallon ikon Allah.

Ummi kuwa cikin rawan murya da tsoro da firgici ta kallesu murya na rawa, tace.
"Dan Allah Jabeer, kaje, tashi muje ka amsa kiranta dan Allah badon niba, dan darajar Manzon Allah".
Ta ?arishe mgnar tana ?o?arin zubewa kan guiwowinta,
Jin kalaman da tayi mishi da gane nufinta na rusuna mushine ya sashi saurin mi?ewa tsaye.
da sauri suma duk suka mi?e tsaye.
Gyara kekyawar al'kyabbar jikinshi yayi wacce take ta limamaice bawai ta sarautaba, jam hiraminshi yayi ya rufe sajenshi da kyau ya rage iya shatin fuskarshi dan yasan dole tazo da hadimanta mata.
Jalal ne ya tsaya gefen damanshi, kana Jamil a gefen hagunshi, Haroon kuwa na bayanshi, Jakadiyarsu kuwa tana gaba tanayi musu jagora.
A haka suka fara taki kan stpes Win sau?owa daga kan dinning area Win, wani irin taku sukeyi mai cike da ?asaita da kwarjini. Yana tsakiyarsu tamkar sarki da fadawanshi.
A haka suka nufo tsakiyar babban falon da ya kai wasu faluka huWu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu, wani irin hushi da numfarfashi takeyi tamkar wacce tayi gudun fanfala?i,
cikin izaya da isa, take zaune bisa mazauninshi.
Tare da cewa.
"Ina karen Larabawan yakene, Dan kan uwark?".
Bata ?arishe mgnar tataba, sabida ganinsu sun nufota gadan-gadan, wani irin kwarjini yayi mata,
wanda yasa ta haWiye ragowar mgnar tata,
shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin wani irin taku na?asaita suka karaso tsakiyar falon.
Ido ta zuba musu kana cikin tijara tace.
"Me zaka zo ka tsaya min a ka, ka zauna inada mgna da kai".
Cikin wata iriyar dakekkiyar murya mai cike da ?asaita yace.
"Ai ba sai kince na zaunaba, dama dole in zauna, tunda ni ba bawanki bane, bazan tsaya a kankiba, sabida Ni ba dogari bane".
Ido ta zazzaro woje alamun tarin mamaki, ajiyan zuciya ta sauke a ranta tace.
"Ehe mai jajayen kunnuwa, uwarka zanci".
Shi kuwa Jabeer, wani irin taku yayi mai cike da izza, bisa kujerar dake fuskantar wacce take zaune a kai ya zauna, da sauri ta tsareshi da ido tare da cewa.
"Kai ina sama kana sama, haka aka koya maka irin tasu tarbiyar ta larabawan kenan".
?afarshi Waya ya Waura ya Waurs kan Waya, kana ya gyara zamanshi da kyau,
cikin muryar ?asaita yace.
"Ki dena yimin ihu a kai, nan ba fadar masarautar waWancan surutattun bane, nan fadace mai daraja masarautar JoWa ce, kiyi hattara da lafuzanki, na baki mituna biyar daga cikin wunin yau gaya min damuwarki in baki mgninta".
Jakadiya dai gaba Waya jikinta rawa yakeyi.
Haroon kuwa, bayan kujerar da Jabeer ke zaune ya tsaya,
Jalal kuma yana gefenshi hakama Jamil.
Juwairiyya kuwa, tana inda take tun Wazu.

Wani irin mugun kallo ta watsa musu, kana cikin zafi da azalzalar zuciya da jin tarin tsanarsu ta gyara zama tare da cewa.
"Naji yau an ganka ka fito Wakin sirri na masarautar JoWa kaida mai martaba LamiWo, me hakan yake nufi?".
Ba tare da ta gama rufe bakintaba yace mata.
"Ina Wakin sirrin masarautar JoWa akace miki na fito, ba Wakin sirrin masarautar kuba na fito?".
Cikin kufula tace.
"Itama Win wannan masarautar ai tamuce, tunda ?a?anane manyan jikokin sarkin Nuruddeen, kuma babansune Galadima, shine kuka kasheshi, aka bawa wancan majanunin yayan naki mulkin Galadiman, to yanzuma kuma Wan tsurfa da tsiri uwar me kukayi a cikin Wakin sirrin? Me ya gaya maka? Me kuke shiryawa?".
Still harshenta ma bai gama komawa zaune ba ya jefa mata amsa.
"?akin sirri mgnar sirri, tunda shi jakin daya kai miki rahoton, bai sanar miki me muka tattaunaba, Ni sai in miki jagora zuwa wurin LamiWo ki samu ki ganshi yanzu sai ki tambayeshi me yace min me mukayi, tunda kinsan in bani nai miki isoba sai ki kai sati nan gaba baki samu damar ganinshi ba".
Ya ?arishe mgnar yana tsareta da fitinennun idanunshi wanda babu tsoro a cikinsu.
Cikin kufula tace.
"Ba girin-girin ba tayi mai, ta yaro kyau take bata ?arko".
Amsa ya kuma bata.
"Surkin nakine yaron? Mutumin daya haifa miki miji, kika aura har kika haifi yayan da kike son su gajeshi, shine yaron? To asheko masarautar duk yarace, ke mulkarta, tunda nasan ko tsohonki bai kai, LamiWo ba".
Ohoho ina wuta ta faWa ciki, cikin kausasa murya tace.
"Ina mai umurtarka da kada ka kuskura ka amshi wani mulkin daya wuce Garkuwa".
Cikin taSe fuska yace.
"An?i bin umarnin naki".
Wani irin Murmushi mai baiyana jin daWi da tarin Mamaki Haroon da Jamil sukayi.
Jalal da kanshi yau Hamma Jabeer Winsu ya shayar dashi tarin mamaki, ashe shi nashi ?arfin halin da ake gani wasane, ga Jarumin da jarumtarsa ta girgiza, zuciyar Jalal. Dan harga Allah shi dai ya sani bazai taSa iya yiwa Gimbiya Saudatu abinda Haammanshi keyi mata yanzuba, ashe dama haka yake, da kafiya da bada amsa tun kafin ta huta. Muryar Gimbiya Saudatu ce ta kuma katse mishi tunani.
"Yanzu bakinka ke iya furta ka haka,, yaro zakaci kan uwark".. da sauri ta zaro mishi ido jin yace mata.
"Kul kada ki ?arasa, in kuwa kikayi gangancin ?arasawa, zan". Katseshi tayi da cewa.
"Zakayi me? Gaya min isshe Wan fitsara me zakayi".
Jalal ne ya amshi

31 / 72