Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   49 / 72

144K to 147K   out of 214K words

LamiWo Bappa ya mi?awa LamiWo hannunta cikin sanyi da nitsuwa da taushin lafazi yace.
"Allah rene, ga Aishatu matar Muhammad Jabeer.
Gata amana bisa jagoranci ka, nasabarka da yardarka.
Da kamala da nitsuwa da na gani a fuskar yaron yasa naji ?arfin guiwar baku aurenta.
Ba tare da fargaba ba, yanzu kaine kaka kuma jagora a gareta".
Sai ya kuma nuna Barrister Kamal da shima yana cikin wakilai, shi a zatonsa ma shine mahaifin Jabeer cikin sanyi yace.
"Kai kuma kaine matsayin mahaifi a gareta ku zame mata dangin ta data rasa, naso ace da mata a masu Waukanta, dan in dan?a amanarta a hannun macce yar uwarta.
Amman ba komai, na baku amanarta dan Allah kada a cutar da ita, domin nima ta kasance amanace a uwurina, domin ?a?an mu da muka haifama amanace Allah ya bamu kuma abun kiyayewa, bare kuma Wiya irin Shatu Wiyace da take da nasabobi masu yawa a gareni".
Cikin gamsuwa LamiWo yasa hannunshi ya amshi hannunta daketa karkarwa, tuni ni?ab Win fuskarta ya ji?e jilak da ruwan hawaye.

Cikin Dattaku LamiWo yace.
"In sha Allah zan kula da dukkan lamuranta tamkar yadda nake kula dashi Jabeer, kuma kada ka damu akwai masu meye mata gurbin uwa ?anwa yaya dama duk danginta a cikin masarauta JoWo, ba?oma baya kukan maraici bare kuma, matar sashin jinina".
Cikin sanyi da wasu hawaye Bappa yace.
"To Ngd matu?a".
ArWo Bani ne ya dafashi tare da cewa.
"Ka sanya mata al'barka a cikin aurenta ba zubda hawaye ba."
Sosai Haroon ya zuba mata ido.
Shi kuwa Sheykh Jabeer da mamaki yake kallon Bappa dake zubda hawaye.

A hankali su Bappa suka Wan ja da baya.

Shi kuwa LamiWo ya juya ya nufi motar ri?e da hannunta.
Haroon ne yayi saurin buWe musu marfin motar, suka nufoshi gadan-gadan.
Jalal kuwa ido ya zubawa yatsun hannunta da LamiWo ke ri?e dashi.

Shi kuwa Jabeer idonshi ya rufe da ?arfi. Sai kuma ya buWesu, dai-dai lokacin LamiWo ya kawota bakin ?ofar motar tare da cewa.
"Mamana kiyi bismillah ki shiga da ?afar dama".
Cikin shesshe?an kuka ta gyaWa kai tare da yin bisimilla kana ta Wan sunkuyo, sai kuma kukan ya kubce mata.
Shi kuwa Jabeer da sauri ya buWe marfin motar ta gefen hagunshi. Kamar gilmawar wal?iya ya fita cikin motar.
Dai-dai lokacin da Shatu tasa ?afarta ciki.
da sauri yasa hannunshi ya buWe motar Jadda tare da shigewa ciki yaja marfin ya rufe sabida ji yayi zuciyarshi zatayi bindiga, wani irin dogon ajiyan zuciya ya sau?e mai ?arfi.

Ita kuwa Shatu, a hankali ta shiga ta zauna, don batama lura da shi bane tabbas dai taga mutun ya fita cikin motar.
Tana shiga Haroon ya maida marfin ya rufe
Shida LamiWo suka koma sit Win bayan wannan sabida su a zatonsu Jabeer na ciki.


Ganin LamiWo ya shigane yasa duk kowa ya shiga motarshi.
Hakama Jadda ya shiga ya zauna hankalinshi na woje.

Sai da akaja motocin suka fara tafiya ne, ya juyo da sauri jin Jabeer na jan wani ja'irin tsaki mai tare da ajiyan zuciya.
Cikin mamaki Jadda yace.
"Haaahh kai kuma Meya kawoka nan? Yaushe ka shigo min mota!?".
Bai kula Jadda ba, asalima yi yayi tamkar bai jishiba.

Haroon kuwa cikin dariya ya Wan bugi sit Win da yake zaton yana wurin cikin juya harcen Larabci yace.
"Masha ALLAH, gasar ShaWi tayi mana rana mun rabaka da gwauranci".
Murmushi LamiWo yayi tare da kallon Haroon yace.
"Saura kai". Murmushi yayi tare da cewa.
"Ni ai nan kusa za'ayi".
Jin shirune, yasa Haroon yayi shiru,
Azotonshi ya ?in mgna da shariyar ne suka zowa Jabeer bare, yasan yanzu a cike yake.

Su Jalal kuwa kab da al'hini suke tafeyi.

Jadda kuwa yayi iya mgnarshi yayi shiru ganin bai kulashi ba.

A haka suka isa cikin Masarauta JoWo.

Suna isa kuwa Jabeer ya fito ya nufi Side Winsa, fitowarsa cikin motar Jadda ne yayi matu?ar bawa Haroon da LamiWo mamaki.

Haroon kuwa bayanshi yabi da sauri.

Suna shiga Side Winsa kuwa suka samu babu kowa.

Suna gama tsayuwa Sallama ya nufi Side Win Gimbiya Aminatu bisa umarni LamiWo.

Yana shiga a babban Falon ya samu. Umaymah, Ummi, Aunty Juwairiyya, Hibba, Adda Rumana wacce take yayarsu Jabeer yar farin Abba kenan, sai mai bin mata Rumaisa.
Kana sai Gimbiya Aminatu dake tsakiyarsu, sai hadimanta.

Koda ya sanar musu, sun iso.
Kusan duk a tare suka mi?e sai Gimbiya Aminatu ce bata tashiba da hadimanta.

Su kuwa da sauri suka nufi woje, Umaymah ce gaba sai Aunty Juwairiyya dake biye da ita a baya ri?e da wani tire wanda samanshi ke Wauke da al'kyabbar irin tasu ta matan masarauta da kuma wasu sauran tarkace.
Suna fitowa motar na isowa har bakin wurin. Da sauri suka nufi jikin motar.
Ita kuwa Zuwa yanzu ta tsagaita da kukanta, sabida ababen da take gani a cikin masarautar ya shallake tunanin mai tunani,
gaba Waya jikinta tsuma yakeyi, sabida idonta na gane mata ababe na ban tsoro.
Cikin ranta take mgnar zuci.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, wannan wanne irin gidane? Me yake faruwa da mutanen masarautar? Sunko san gskyar junansu?".
Da sauri ta rumtse idanunta sabida wasu irin haya?i da take gani yana tashi tako ina na gidan yayiwa gidan rumfa gaba Wayansa.

A da sauri ta buWe idonta jin an kamo tafin hannunta,
Umaymah kuwa cikin tsantsar jin daWin da farin ciki maras misaltuwa tace.
"Marhababiki ya binti". Wani irin azabebben tsinkewar zuciya da firgici da razanine ya daki zuciyar Shatu a lokaci Waya.
Da sauri ta ?ara ware idanunta, dan son kallon matar da take jawota tare da cewa.
"Kiyi bismillah ki fito da ?afar dama, ki ri?e hannuna da kyau Wiyata, ki kalleni nan nice jagorarki ki taka ?afarki a inda zakiga na taka tawa".
Ido ta zuba mata, tare da fitowa a hankali.
Tana fitowa bakin ?ofar Umaymah tasa hannu ta amshi al'kyabbar da Aunty Juwairiyya take mi?a mata.
Kangeta tayi kana tasa mata al'kyabbar, sannan ta gyara mata rufuwarshi da kyau ta rufa mata hularshi. Yadda sam mutun bazai samu damar ganinta ba.

Ga ni?ab ga kuma hular al'kyabbar da lu'ulu'u danke reto a fuskarta.
Da sauri Aunty Juwairiyya ta matso tare da cewa.
"Marhabin yar uwarta, Alhamdulillah yau kam na samu yar uwa".
Adda Rumana ce ta matso kusa da ita tare da yin mgna da fillanci tace.
"Sannu da zuwa Masarautar JoWa ?anwata".
Adda Rumaisa kuwa murmushi yaketayi tare da matsowa, haka suka sata a tsakiya.
Jakadiyarsu kuwa sai bin takun ?afar Shatu takeyin da ido.

A haka suka zagayeta, kana hadimai suka mara musu baya.

A haka suka isa babban falon Gimbiya Aminatu.
Suna isa Umaymah ta kaita har gabanta ta ajiyeta,
Cikin tsantsar jin daWi tace.
"Alhamdulillah Gimbiya yau dai ga sabuwar Gimbiya dan yanzu itace amarya ba keba".
Cikin dariyar jin daWi Gimbiya Aminatu tasa hannu ta kamo hannun Shatu da Umaymah ke mi?a mata tare da cewa.
"Kishiya ban haushi, ta isa ta zama Gimbiya zakisa yanzu in korata woje".
Dariya sukayi baki Wayansu.

Yayinda tuni hadimai mata suketa jere ababen ma?ulashe a gaban Shatu.
Danginsu, Zuma, Madarar shanu, Da ?a?an itatuwa masu sanyi.
Ita dai Shatu ?asa tayi da kanta,
tana jin fargaba da kuma tsoron wannan bahagon gidan data shigo.

Su kuwa nan sukayi ta mata hidima da nuna mata so.

Ganin magriba ta ?ara to ne yasa,
Umaymah ta jawo hannunta ta kaita wani Waki dake nan kusa dana Gimbiya Aminatu.

Tare da cewa.
"Yauwa Wiyata kiyi salla. Za'a kawo miki abinci, kada kici komai sai nazo".
Cikin sanyi ta gyaWa mata kai.
Ita kuwa Umaymah hannu tasa ta fara zare mata al'kyabbar, koda ta cire mata shi, cikin kula tace.
"Cire ni?ab Win, babu mai shigowa nan yanzu sai nida Gimbiya Aminatu da Juwairiyya sai Jakadiyarsu".
A hankali tace.
"To".
Haka nan taji duk wani yarda na duniya ta sau?eshi kan wannan kekyawar mata mai fara'ar nan.

A hankali tasa yatsunta ta kamo ni?ab Win ta Win ta yayeshi.

Wasu irin tagwayen numfarfashi Umaymah ta sau?e tare da cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!".
Da sauri ta juyo ta ruggume Jakadiyarsu a hankali tace.
"Alhamdulillah Ummin Jabeer itace. Wlh itace".
Cikin wani irin tarin jin daWi Jakadiyarsu ta Wan kalli Shatu, tare da yin murmushi mai cike da ma'anoni.

Jakukkunan dake hannunta ta ajiye, kana ta iso kusa da ita ido ta zubawa fuskarta kana tace.
"?iyata menene sunanki?".
Cikin yin ?asa da ido Shatu tace.
"Aysha".
Kusan a tare sukace masha ALLAH.
Nan Umaymah kam ta juya da sauri ta fita.

Ita kuwa Jakadiyarsu Jabeer shirya mata kayan data shigo dasu takeyi a drower'n.
Tare da bata umurnin taje tayi al'wala.

Umaymah kuwa tana fita kai tsaye Side Win Jabeer ta nufa.

Shiru ba kowa, da kamar duk sun tafi masallaci ne.

Aunty Juwairiyya da Hibba kuwa suna sashin Juwairiyyan.
Ummi kuwa na can wurin Shatu.

Kai tsaye Wakin da nanne masaukin ta, ta nufa.
Bathroom ta faWa ruwa ta Wan watsa tare da yin al'wala kana tafito tazo ta kabbarta sallah.

Ita kuwa Shatu zaune take bisa sallayan.
Tunda ta idar da sallan bata tashiba.
Sai kanta data jingina jikin gadon da take gefenshi.
A hankali ta rumtse idanunta tare da motsa laSSanta tana karatun al'?ur'ani cikin sanyin murya, Ummey da Junainah ne suka faWo mata a rai shine ya sata zubda hawaye wasu na korar wasu.
Kewarsu da begensu, ya tuno mata su Ya Gaini da marigayi ya Lado.
Ummi kuwa itama bisa sallayan take tana lazumi.

A haka har lokacin sallan isha'i yayi.

Jin wata zazza?ar murya mai matsifar daWi na karatun.
Hannun tasa ta share hawayenta dan jin karatun takeyi yana ratsa mata zuciya ya tsananta zubar hawayenta.

A hankali ta mi?e itama ta kabbarta sallan isha'i.
Hakama Ummi.

Bayan an idarne. Ummi ta mi?e tsaye ta ninke abin sallan, kana a hankali take taku har kusa da ita.
Cikin sanyi ta zauna bakin gadon tare dasa hannunta tsakiyar kanta a hankali tace.
"AYSHA kuka kikeyi!?."
Da sauri ta jujjuya kai alamar a a tana mai share hawayenta.
Cikin kula Ummi tace.
"Kuka mana kikeyi, gashi kinata zubda hawaye! Kiyi ha?uri kinji ko Aysha ki bar kuka, in kinji kewan mamanki ki kalleni a matsayinta, in kinji kewar yayarki ki kalli Juwairiyya a matsayinta, in kuma yayu maza kikaji kewarsu ki kalli Jalal da Jamil a matsayinsu.
In wani abu na damunki ki gayawa Sheykh, shine mijinki kuma majiSancin lamuranki in kinji kewar ?anwa mace ki kalli Hibba a matsayinta,".
Bata hafimtar kalaman wannan matar,
bare tasan me take nufi saboda babu mutun Waya da ta sani cikin mutanen data kira mata.
Abu Waya ta fahimta Sheykh shine wanda wai tace shine mijine ko majiSancin lamurane, bata sanshiba bai kuma santaba ta ina zai jiSanci lamuranta,
Shin ta yaya zata zauna a wannan gidan da tun shigowarta take ganin ababe masu ban tsoro."
Jin tayi shirune yasa.
Ummi shafa bayanta tare da cewa.
"Jikinki na rawa zazzaSi kikeyi ne?."
Cikin sanyin murya tace.
"A a sanyi nakeji".
Da sauri ta Wan mi?e tare da cewa.
"To bari in rage gudun A/C'n".
Ragewa tayi kana tazo ta zauna kusa da ita.


Umaymah kuwa tana idar da sallan isha'i, ta mi?e ta dawo sashin Gimbiya Aminatu.
Tayi matu?ar mamaki ganin batun auren Jabeer ya karaWe masarautarsu gaba Waya,
taki wani sashi kawo abincin amarya akeyi.

Ita da kanta da Gimbiya Aminatu sukayi ta shigar da Foodflaks Win abincin cikin Wakin da take suna jerawa a gabanta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer bayan an salla.
Ya fito kamar koda yaushe su Jalal na biye dasu a baya.
Haroon kuwa suna tafiya a jere,
suna cikin tafiya duk suka tsaya fuska a haWe Jabeer ya juyo ya kalli gefen hagunshi da yaji an dafa kafaWarshi, Jadda ne ya Wan kalleshi kana ya kauda fuskarshi ba tare da yace mushi komaiba.
Murmushi Jadda yayi cikin sakin fuska yace.
"?arfe tara dai-dai jirginmu zai tashi. Zamu koma da kawunan naku duka".
Cikin muryar dake nuna cewa yana cikin tsananin Sacin rai yace.
"Allah kiyaye hanya". Ya ?arishe mgnar tare da juyawa yaci gaba da tafiyarshi.

Shi kuwa Jadda murmushi ya kumayi, fahimtar Sheykh yana tsananin fushi da ba?in cikin abinda sukayi mishi.

LamiWo ne ya kalli Aminin nashi tare dayi mishi alamun ya barshi.
Su tafi.

Daga nan suka juya duk suka nufi, sashin LamiWo, inda aka gama shirya manya-manyan Foodflaks a tsakiyar falonshi bisa wani tattausan Turkey carpet mai masifar kyau da taushi.

Nan suka zauna sukayi Dinner sunayi suna hira,
Tare da yaransu.

Bayan sun gamane, suka mi?e dan tafiya Airport sabinda lokacin tafiyarsu ya kusa.
Kusan a tare suke fito zuwa babban falon dake tsakanin side Win LamiWo dana Gimbiya Aminatu.

Bayan sun zaunane, Sallama yaje ya sanarwa Gimbiya Aminatu cewa Sarki Jalaluddin yana neman Umaymah da Amaryar Sheykh.

Jin sa?on Sarki Jalaluddin daga bakin hadimanta da Sallama ya isarwa sa?on ne yasa ta mi?e ta nufi Wakin da Umaymah take.

A cikin Wakin kuwa, cikin kula Umaymah take gabatarwa Aysha da abin ci dana taSa ka lashe dana motsa baki.
Adda Rumana kuwa kamar tasa mata abinci har bakinta,
Itako Aysha kanta a sunkuye, ta zubawa kulolin abincin ido tana ganin ikon Allah dake wanzuwa cikin kayayyakin cimar, da sai dai gidan wane da wanen.
Fahimtar kunya ne ya hanata cin komai yasa suka fito falo suka barta, da Umaymah kawai wacce taketa janta a jiki ganin hakane yasa, ta Wan yarda taci abincin kaWan.

Suna zaune a nanne Gimbiya Aminatu ta shigo ta sanar musu sa?on sarki Jalaluddin nan, Umaymah ta sake saka mata wata al'kyabbar cikin jin daWi tace.
"Aysha ki saki jikinki dani, ki gaya min dukkan abinda kikeso, yanzu kinga wurin kakanunki zan kaiki.
Sarki Jalaluddin mahaifina ne, wanda kuma shine mahaifin maman mijinki, Waurin auren sukazo shida yayunmu da ?annenmu maza yanzu zasu koma jiharmu ne.
Kinga wannan kuma Gimbiya Aminatu itace ta haifi mahaifin mijinki.
Kana Sarki Nuruddeen Wan Sarki Bubayero jikan sarki JoWa, shine kakan mijinki.
Mu ma mahaifiyarmu na Raye mijinki ne yasa mata suna Sitti, tana jiharmu ita bata samu zuwaba sai daga baya zata zo".
Ajiyan zuciya tayi tare da kamo hannunta kana taci gaba da cewa.
"Mijinki Wan babban family ne gaba da bayanshi.
A ?alla zai Waukeki shekaru goma cikin masarautar JoWa data musulmai baki gama sanin adadin dangi da yawan yan uwan mijinki ta gefen mahaifiyarshi da mahaifinshi ba.
Yanzu muje su ganki ki gansu."
Cikin sanyi tace.
"To Aunty".
Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"Ba Aunty ku bace, Mijinki Malam Jabeer yafi yarda da ita fiye da kowa a dangin mahaifiyarshi, Umaymah yake kiranta".
Kai ta gyaWa tare da mgnar zuciya.
"Ikon Allah".
Ita kuwa Umaymah murmushi tayi kana tana hannunta suka fita.
A falo suka samu Jakadiyarsu, da sauri Umaymah tace.
"Yauwa kinga wannan itace Jakadiyarsu, itace ta rainesu tun suna yara, bayan mahaifiyarsu babu wanda yasan halin Jazlaan sama da ita a cikin wannan masarautar, ki kasance mai bin umarnin ta, domin itace idonki cikin wannan masarautar, Jazlaan a matsayin uwa mahaifiya yake kallonta ba baiwar gidansu ba".
Cikin nitsuwa Aysha ta gyaWa kai tare da cewa.
"Nagode".
Ita kuwa Ummi murmushi tayi tare da bin bayansu.

Suna isa bakin ?ofar tayi musu iso bayan ta shiga ta sanar musu da isowarsu.

A hankali suka shiga, cikin nitsuwa take bin takun Umaymah.
Ita kuwa Umaymah har gaban Sarki Jalaluddin da Sarki Nuruddeen taje da ita,
cikin sha?uwarta dasu, ta ajiyeta a gabansu tare da cewa.
"Jadda ga amaryar Sheykh Jabeer a sanya musu al'barka".
Murmushi yayi tare da kallon Aysha. Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sau?e tare da cewa.
"Allah ya sanya al'khairi ya basu zaman lafiya. Allah yasa tazo mana da hasken da zai kore duhun daya meye hasken idanunmu".
Amin Amin suka amsa baki Wayansu.
Uncle Abdulkareem ne ya Wan kalleta cikin sanyi yace.
"Allah yayi miki al'barka dake da mijinki ya baku zaman lfy mai Worewa".
Kanta ta ?ara sunkuyawa,
Ita kuwa Umaymah matsota tayi tare da cewa.
"Kinga Wan Wago kanki ki kallesu.
Kinga ga Mahaifina. Ga Sarki LamiWo".
Sai kuma ta nuna Abba dake zaune cikin murmushi tace.
"Ga wannan shine mahaifin Jabeer mamanshi kuwa sai gobe a bisa ?aidar masarautar keda shi Jakadiyarsu da Sallama zasuyi muki jagora ku zagaya cikin masarautarsu baki Wayansu a nuna miki ahlinsu to da Wakin mamanshi za'a fara kaiki".
Kinga wannan shine babban Yayanmu sarki mai jiran gado.
Ga kuma wa ?aninmu Abdulmumin."
Murmushi LamiWo yayi tare da cewa.
"A a Khadijah a rana Waya kikeso Wiyar taki tasan komaine? Ai abun da wuya, dole sai a hankali zata gane mu".
Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa.
"Hakane kam. Amman gwara an gabatar mata da manya".
Sarki Jalaluddin ne ya gyara zamanshi tare da cewa.
"To Khadijah mu yanzu zamu wuce, ke kuma sai yaushe?".
Murmushi tayi tare da kallon gefen damanta inda Haroon ke zaune da wani kekkyawa mutun mai matsakaici shikara.
Mi kama dashi wanda bisa dukkan alamu babanshi ne.
Kauda kanshi yayi daga kallon da Umaymah keyi mishi, cikin ?asaita alamun shima jinin sarauta ne, yace.
"Ni kada ki wani kalleni, bance komaiba".
Murmushi dattawan sukayi baki Wayansu, Haroon ma murmushin yakeyi.
Ita kuwa Umaymah kauda zance tayi da cewa.
"Yauwa Aysha kinga wannan shine Haroon Wan uwa kuma aboki amini abokin faWan Jabeer.
Akwai kuma Wan yayanmu Ibrahim shine sha?i?in Jabeer shi yana Cairo, amman kwanan zai dawo ki ganshi."
Jadda ne ya kuma tsareta da cewa.
"Khadijah yaushe zaki koma?".
Cikin sanyi tace.
"Jadda in Abban Haroon ya amince zanyi wata Waya rak, sabida ganin yadda lamuran zasu tafi.
tsakanin yaran, ita kanta Aysha tana bu?atar makusanci tare da ita, sabida ba?onci a irin gidajenmu abune mai wuya ga wanda ba irin gidajen ya taso ba".
Murmushi Abban Haroon yayi tare da cewa.
"Ba laifi na Amince, Amman bazaki Wauki azumi a nan bada".
Da sauri tace.
"Na yarda".
Haroon ne ya Wan juya idonshi alum lissafi kana yace.
"Ke nan sati uku zakiyi tunda azumin saura wata Waya".
Kai ta gyaWa alamun gamsuwa,
Jadda ne ya kalli Jakadiya tare da bata umarnin su tafi ita da Aysha.
Gane abinda yake nufine yasa ta kamo hannun Aysha suka fita. Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.

Gyaran murya Jadda yayi bayan sun fita, cikin nitsuwa da girma ya kalli Umaymah tare da cewa.
"Alhamdulillah Khadijah, aure dai an Waura, duk da tarin tsana da ?in abin da Wan naki keyi.
Ha?i?a baya son wannan abun da akayi mishi. Naga fushi da tashin hankali mai tarin yawa a ?wayar idanunshi da fuskarshi.
Ina da ya?ini bisa halin Jabeer in ya tsani abu tofa ya tsaneshi kenan har gaban abadan, wannan shine babban tashin hankali na,
Sabida yanada lafiya da tsayuwa kan kaifi Waya. Ya gayawa kakarshi Sitti babu wani gari na duniya da yakejin ya tsana sama da wannan garin. Yace baya son garin da mutanen garin. Sabida anci mishi zarafi a garin a gaban kafurai an tozarta shiga ta addinin Musulunci".
Shiru sukayi baki Wayansu, tabbas sun san hakane mgnar Jadda.
shi kuwa Jadda a hankali yaci gaba da cewa.
"Yanzu kubar Yarinyar a ta kwana a nan.
Kana a Wan Waga kafa har sai an gyara mata inda zata zauna, kamar ko wacce amarya.
Sannan kada kuyi mishi mgnar auren bare ita yarinyar,
in anyi haka fushinsa bazai tsanantaba, zaici gaba da al'amuran rayuwarshi, tunda shi mutum ne mai ibada da kuma aiyuka".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"In dai baza'ayi mishi mgnarta ba, to wallahi mancewa zaiyi da ita

49 / 72