Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   20 / 72

57K to 60K   out of 214K words

ke zama, Waura kafarta tayi Waya kan Waya.
Hadimanta, biyu ne suka zauna gefe da gefenta.
Fuskarta babu wata alamar annuri, sai tsantsar tijara, cikin isa da ?asaita tace.
"Kai Jabeer!."
Ido Jakadiyarsu ta zazzaro cikin firgici da tsoro ta kalli Jabeer da a take fuskarshi ta sauya launi,
cikin rawan jiki da tsoro tayi ?asa da murya tare da cewa.
"Jabeer ka amsa, Gimbiya Saudatu ce, da kanta."
Jalal ne da Jamil suka kalli juna, kana suka maida idonsu, kan Hamman nasu, da ya lumshe idonshi ya koma ya jingina tamkar badashi akeyi ba, kamar daga sama suka jiyo muryar Gimbiya Saudatu tana ratsa kunnuwansu.
"Kai Jabeer, ka fito kazo nan, ina nemanka".
Still bai buWe idanunshi bama, bare ya amsa ko yun?urin tashi,
sai dai laSSan bakinshi da suke motsawa yana maimaita sunan Allah a zuciyarshi da harshenshi.

Zuwa yanzu Gimbiya Saudatu tayi masifar kufula, cikin wani irin mugun kallo ta kalli Juwairiyya da jikinta ke baiyana tashin hankali ta, cikin isa da ?asaita tace.
"Ke maza wuce, kije tun wancan karen larabawan da suka turo ahlin masarautun FulSe, dan samun damar maida masarautun a hannunsu, kice mishi yazo dan kan uwarshi".
Da ?arfi Jabeer ya rumtse idanunshi, wani irin bugawa zuciyarshi ta farayi a saba'in.
Ita kuwa Juwairiyya kasa motsawa tayi daga inda take tsayen.
Ummi kuwa cikin firgici, ta kalli Jalal daya mi?e tsaye tamkar wanda aka tsabura.
Jiki na rawa ya ture kujerarshi, zaiyi baya ya fita ya nufi inda taken.
da sauri ya juyo cikin tarin zafin rai jin an ri?e mishi, hannunshi.
ganin Hamma Jabeer Winsune ya dam?i hannunshi ne ya sashi, taune lips Winshi da masifan karfi.
Jamil kuwa ido ya zubawa Hamman nasu yana ganin yadda jikinshi ke karkarwa, kowa ya sani duk duniya babu abinda yake saurin harzu?a Sheykh sama da a zagar mishi iyaye Especially uwa! Haroon kuwa zuru yayi da idanu yana kallon ikon Allah.

Ummi kuwa cikin rawan murya da tsoro da firgici ta kallesu murya na rawa, tace.
"Dan Allah Jabeer, kaje, tashi muje ka amsa kiranta dan Allah badon niba, dan darajar Manzon Allah".
Ta ?arishe mgnar tana ?o?arin zubewa kan guiwowinta,
Jin kalaman da tayi mishi da gane nufinta na rusuna mushine ya sashi saurin mi?ewa tsaye.
da sauri suma duk suka mi?e tsaye.
Gyara kekyawar al'kyabbar jikinshi yayi wacce take ta limamaice bawai ta sarautaba, jam hiraminshi yayi ya rufe sajenshi da kyau ya rage iya shatin fuskarshi dan yasan dole tazo da hadimanta mata.
Jalal ne ya tsaya gefen damanshi, kana Jamil a gefen hagunshi, Haroon kuwa na bayanshi, Jakadiyarsu kuwa tana gaba tanayi musu jagora.
A haka suka fara taki kan stpes Win sau?owa daga kan dinning area Win, wani irin taku sukeyi mai cike da ?asaita da kwarjini. Yana tsakiyarsu tamkar sarki da fadawanshi.
A haka suka nufo tsakiyar babban falon da ya kai wasu faluka huWu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu, wani irin hushi da numfarfashi takeyi tamkar wacce tayi gudun fanfala?i,
cikin izaya da isa, take zaune bisa mazauninshi.
Tare da cewa.
"Ina karen Larabawan yakene, Dan kan uwark?".
Bata ?arishe mgnar tataba, sabida ganinsu sun nufota gadan-gadan, wani irin kwarjini yayi mata,
wanda yasa ta haWiye ragowar mgnar tata,
shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin wani irin taku na?asaita suka karaso tsakiyar falon.
Ido ta zuba musu kana cikin tijara tace.
"Me zaka zo ka tsaya min a ka, ka zauna inada mgna da kai".
Cikin wata iriyar dakekkiyar murya mai cike da ?asaita yace.
"Ai ba sai kince na zaunaba, dama dole in zauna, tunda ni ba bawanki bane, bazan tsaya a kankiba, sabida Ni ba dogari bane".
Ido ta zazzaro woje alamun tarin mamaki, ajiyan zuciya ta sauke a ranta tace.
"Ehe mai jajayen kunnuwa, uwarka zanci".
Shi kuwa Jabeer, wani irin taku yayi mai cike da izza, bisa kujerar dake fuskantar wacce take zaune a kai ya zauna, da sauri ta tsareshi da ido tare da cewa.
"Kai ina sama kana sama, haka aka koya maka irin tasu tarbiyar ta larabawan kenan".
?afarshi Waya ya Waura ya Waurs kan Waya, kana ya gyara zamanshi da kyau,
cikin muryar ?asaita yace.
"Ki dena yimin ihu a kai, nan ba fadar masarautar waWancan surutattun bane, nan fadace mai daraja masarautar JoWa ce, kiyi hattara da lafuzanki, na baki mituna biyar daga cikin wunin yau gaya min damuwarki in baki mgninta".
Jakadiya dai gaba Waya jikinta rawa yakeyi.
Haroon kuwa, bayan kujerar da Jabeer ke zaune ya tsaya,
Jalal kuma yana gefenshi hakama Jamil.
Juwairiyya kuwa, tana inda take tun Wazu.

Wani irin mugun kallo ta watsa musu, kana cikin zafi da azalzalar zuciya da jin tarin tsanarsu ta gyara zama tare da cewa.
"Naji yau an ganka ka fito Wakin sirri na masarautar JoWa kaida mai martaba LamiWo, me hakan yake nufi?".
Ba tare da ta gama rufe bakintaba yace mata.
"Ina Wakin sirrin masarautar JoWa akace miki na fito, ba Wakin sirrin masarautar kuba na fito?".
Cikin kufula tace.
"Itama Win wannan masarautar ai tamuce, tunda ?a?anane manyan jikokin sarkin Nuruddeen, kuma babansune Galadima, shine kuka kasheshi, aka bawa wancan majanunin yayan naki mulkin Galadiman, to yanzuma kuma Wan tsurfa da tsiri uwar me kukayi a cikin Wakin sirrin? Me ya gaya maka? Me kuke shiryawa?".
Still harshenta ma bai gama komawa zaune ba ya jefa mata amsa.
"?akin sirri mgnar sirri, tunda shi jakin daya kai miki rahoton, bai sanar miki me muka tattaunaba, Ni sai in miki jagora zuwa wurin LamiWo ki samu ki ganshi yanzu sai ki tambayeshi me yace min me mukayi, tunda kinsan in bani nai miki isoba sai ki kai sati nan gaba baki samu damar ganinshi ba".
Ya ?arishe mgnar yana tsareta da fitinennun idanunshi wanda babu tsoro a cikinsu.
Cikin kufula tace.
"Ba girin-girin ba tayi mai, ta yaro kyau take bata ?arko".
Amsa ya kuma bata.
"Surkin nakine yaron? Mutumin daya haifa miki miji, kika aura har kika haifi yayan da kike son su gajeshi, shine yaron? To asheko masarautar duk yarace, ke mulkarta, tunda nasan ko tsohonki bai kai, LamiWo ba".
Ohoho ina wuta ta faWa ciki, cikin kausasa murya tace.
"Ina mai umurtarka da kada ka kuskura ka amshi wani mulkin daya wuce Garkuwa".
Cikin taSe fuska yace.
"An?i bin umarnin naki".
Wani irin Murmushi mai baiyana jin daWi da tarin Mamaki Haroon da Jamil sukayi.
Jalal da kanshi yau Hamma Jabeer Winsu ya shayar dashi tarin mamaki, ashe shi nashi ?arfin halin da ake gani wasane, ga Jarumin da jarumtarsa ta girgiza, zuciyar Jalal. Dan harga Allah shi dai ya sani bazai taSa iya yiwa Gimbiya Saudatu abinda Haammanshi keyi mata yanzuba, ashe dama haka yake, da kafiya da bada amsa tun kafin ta huta. Muryar Gimbiya Saudatu ce ta kuma katse mishi tunani.
"Yanzu bakinka ke iya furta ka haka,, yaro zakaci kan uwark".. da sauri ta zaro mishi ido jin yace mata.
"Kul kada ki ?arasa, in kuwa kikayi gangancin ?arasawa, zan". Katseshi tayi da cewa.
"Zakayi me? Gaya min isshe Wan fitsara me zakayi".
Jalal ne ya amshi zancen da cewa.
"Zan datse miki harshe, kika kuma zagar mana uwa".
Cikin tsananin tsana ta watsawa Jalal harara tare da cewa.
"Zaka aikata! Babu musu! Menene Wan giya bazai iya yiba, menene, Wan iska Wan daba bazaiyiba, banza Wan sara suka, gwada datse min harshen ka gani, in akwai wanda zai rage da harshe a zuriyar uwarku".
Jabeer ne ya Wan taune leSenshi tare da kaWa mata yatsa kana yace.
"Kulfa, ki raba kanki da zagin mace mai daraja".
Cikin isa da ?asaita tayi wani irin dariya, kana ta mi?e tsaye, gabansu ta Wan matso kana cikin izaya tace.
"Eh daraja ko? Uhummm lallai kam, aifa sai dai mace mai daraja."
Sai kuma ta Wan ja da baya kana tace.
"Mace mai daraja ko mai zunubi, ai dai kun fara ganin sakayyar Allah tun a duniya, waya san metayiwa ubangiji, y...."
Juwairiyya ce, tasaki wani irin ?ara da yasa duk sukayi shiru.
Ita kuwa ta faWi kasa a sume alamun makaranta sun dawo.
Ganin haka yasa Jakadiyarsu tayi kanta da gudu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu murmushin jin daWi tayi tare da cewa.
"Haka dai. Duk a haka zaku ?are, mulki kuwa sai dai ku ga anayi, GARKUWAN da aka bakanma, zakaga me zai sameka dashi".
Tana faWin haka ta juya ta nufi hanyar fita Hadimanta na biye da ita a baya.
Shi kuwa Sheykh Jabeer murya ya Wan Waga a hankali yadda zata iya jinshi yace.
"Babu abinda zai sameni face dama Allah ya ?addara zai sameni, domin baki isa ki cutar daniba".
Cikin harshen fillanci tace.
"A laran ai, zaka gani ai".
Bai kulataba.
Ita kuma fita tayi.

Jalal da Jamil kuwa, zama sukayi gefenshi, suna mai bin kofar fita da ido.
Haroon kuwa cikin rudu da Waure war kai yake mgnar zuci.
shin wai wannan wacce iriyar fitinenneyar masarautace, mai cike da tsar?a?iya, yanzuma dama a irin wannan yanayin Jabeer ke rayuwa da ?annenshi da yayanshi da mahaifanshi.
To meyasa, bazasu bar musu masarautarba, tunda shi Jabeer bama son wannan mulke-mulken yakeba.
Sassanyan zazza?ar Muryar Sheykh Jabeer ne ta katse mushi nazari, jin yana rere karatun Alqur'ani cikin nitsuwa yake, karanta fatiha.
Bayan ya kai ?arshenta ya kuma yi bisimilla, ya fara Suratul Baqra, wanda yakeyi da Wan ?arfi, tare da fuskantar inda Juwairiyya ke kwance,
Yanayin karatun cike da ta?awa da kekyawan tajwid, shiyasa in ya fidda wani harafin kamarsu Khah sai kaji har ?asan wurin yana amsa amon sautin."
A hankali Juwairiyya ta fara buWe idanunta, tana mai bin karatun da takejin,
Cikin sau?e ajiyan zuciya Jakadiyarsu tace.
"Alhamdulillah Jabeer ta farfaWo".
Ta faWi hakane sabida tasan duk sansa Juwairiyya ta faWin in dai zai mata Rugyag rufe idonshi yakeyi.
Jin Jakadiyarsu tace ta farfaWo ne, tasashi, yin hamandala tare da cewa, Jakadiyarsu ta meda Juwairiyya Side Win ta, kana ya kalli Jalal tare da cewa.
"Jalaluddin kaje, ka kula da Ya Jafar, ka bashi abinci kana ka shirya shi, shirin zuwa sallan jumma'a kaima kaje ka shirya."
To sukace kana duk suka fita. har sunje bakin ?ofar fira yace.
"Jalaluddin kasa kayan mutunci".
Cikin sanyi yace.
"To". Sannan suka fita.
Kanshi ya Wan juya ya kalli, Jamil, tare da cewa.
"Ka gyara mana bedroom."
Yana jin haka ya mi?e ya nufi bedroom Win.
Shi kuwa Haroon ido ya zuwa Jabeer, sabida gaba Waya muryarshi ta tabbatar musu, yana cikin tsananin Sacin rai, kai Haroon ya jinjina ganin Jabeer yasa hannu ya janye hiramin dake kanshi, ya taune lips Winshi, kana ya rufe idanunshi, cikin ?arfi yasa hannunshi ya fara jan bakin hiramin , da yake sabo fil janshi yakeyi alamun zai yagashi.
Shiru Haroon yayi baiyi yun?urin hanashi ba, domin dama yasan za'a rina, sabida shi Jabeer wannan itace babbar alamar tsananin Sacin ransa, muddin fushinsa ya hauhawa to, yakan yayyaga abu da karfi.
Fass haka Haroon yaji sautin, yagewar sabon hiramin nan.
Shi kuwa Jabeer idonshi ya ?ara rumtsewa yanayi mai ci gaba da fatattaka hiramin.
Murmushi Haroon yayi cikin tare da fara Waukar shi video.
Yanayi dan tsokana.

A can sashin Hajia Mama kuwa, ganin shiru-shiru Jabeer bai shigo bane, kamar yadda ya saba in yayi tafiya ya dawo yakan,
Batul kuwa, ta gaza zaune ta gaza tsaye, ta ?en?esa ado da kwalliya tamkar mai zuwa gasar kyau.
A karo na barka tai ta kalli Hajia Mama, cikin za?uwa tace.
"Yakura, muje, side Winshin mana, mu duba lfy kuwa har yanzu bai shigoba."
Ajiyar zuciya Hajia Mama ta sauke, tare da mi?ewa tace.
"Muje Batul ni kaina, na banyi zaton zai kai iwar haka bai shigoba, dole akwai abunda ya tsareshi".
Da haka suka fito, suka nufi sashin Jabeer Win.

Kasan cewarta matsayin uwa, yasa sam bata da hijabi da sashin, haka yasa, sarkin ?ofar na ganinta suka rusuna tare dayi mata kirari kana ta wuce.

A falon suka samesu, zaune.
Haroon ya tasashi gaba da kallo da wayarshi, shi kuwa Jabeer, idonshi a rumtse, bakinshi na motsawa a hankali, yana maimaita, tasbihen daya zame mishi abokan rayuwa.
Kana hannunshi nata yage sabon hiraminshi.
Haroon ne ya amsawa Mama sallamarta, tare da cewa.
"Barka da fitowa Hajia Mama".
Da sauri ta ?arasa gabansu, kujerar dake kusa dasu ta zauna,
cikin tarin kula tace.
"Haroon da kai ake tafe kenan? Ya yar uwata, yaushe ka dawo?".
"Haroon lfy kuwa me akayiwa Jabeer? Waya taSa minshi? Waya taSo Wan lelen Umaymah'nshi Da Sitti'nshi?".
Cikin lumshe ido Haroon yace.
"To Hajia Mama wacce tamSaya Waya zan amsa miki, ta ?ar uwarki ko ta Wan rigimarku, mutun in yayi fushi sai yayi ta yage-yage, wannan in ya samu dama in yayi fushi ya samu ya dam?i ?ar mutane a hannunshi tabbas zai yageta, dan ko namiji da kyar zai iya ?watar kanshi".
Murmushi mai cike da kulawa tayiwa Haroon kana,
ta kalli Batul da zauna gefenta, ta zubawa Jabeer idonu tamkar zata cinyeshi Wanye,
wani irin sonshi da ?aunarshi takeji, jiki da zuciyarta,
Kekyawan sumar kanshi ta zuwa, idanu a hankali ta dawo da idon kam tattausan sajen da yayi fuskarshi ?awanya, har kan gashin gemunshi da ya kai kamu Waya, yayi ba?i sitib dashi ya konta lib sai she?i yakeyi, jajayen laSSan bakinsa, da suke motsawa ne ta zubawa kwayar idanunta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, sanadin tasbihin da yakeyi ne, yaji zuciyarshi tayi fes,
fushin da yakeji duk ya kau. A hankali yakejin tsikar jikinshi na amsa sautin yam-yam tana sanar mishi ana kallonshi.
Yun?urowa yayi ya tashi zaune, kana a hankali ya fara buWe idanunshi.
Da sauri ya kauda ?wayar idanunshi sabida ganin kwayar idanun Batul cikin nasa,
Hajia Mama kuwa, cikin sanyi tace.
"Innallaha ma'assabirin".
Idonshi ya kuma lumshewa, wannan abu shike ?ara sashi jin ?arfin guiwar zama cikin masarautarsun. Sabida yayi dace, da uwar da take ?ara bashi tarbiyar da yasan itace dai-dai tana danne dukkan ba?in cikinta, domin ta sama mishi nitsuwa. Duk da kasancewar shi malami.
Tana ?ara nusar dashi.
A hankali yace.
"Barka da safiya Mama".
Murmushi tayi kana tace.
"Barka dai, Muhammad Jabeer. Garkuwa mai nagarta,
Yau na tashi da tsantsar farin ciki , tunda maji muryarka da asuba, meya Sata maka rai daga dawowa?".
Cikin sanyi yace.
"Babu komai Mama, Sheykh Abdulkareem, da ahlinshin duk sun gaisheki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Tsoho mai ran ?arfe, kakanmu bawan Allah, yana lfy ko?".
"Alhamdulillah". Yace mata, yana mai sa hannu ya Wauki hular da Jamil ya ajiye a kusa dashi ya Waura a kanshi, sabida wani irin kallo da yaga Batul nayiwa suman kanshi.
Ita kuwa Batul ido ta Wan lumshe, ganin yadda ya tam?e fuskarshi ya watsawa gefen da take kallon, ?asaita.
A hankali ta buWe idonta kana ta sau?esu kan sajenshi,
Wani gajeren tsaki yaja,
tare da kauda fuskarshi.
Ita kuwa Butul mgnar zuciya takeyi.
"Masha Allah, Ya Jabeer, komai kayi kyau kakeyi, ya Allah ka tabbatarmin da mafarkina mana, wannan kekkyawan bawa naka ya zamo mijina, domin shine mijin daya dace dani, mijin kece raini da nunawa sa'a, Uhumm jin kai da ?asaita ba, kayi naka, kafin ka shigo hannuna, in sha Allah, sai na zama sarauniya ka zama bawana."
A hankali tace.
"Ya Jabeer ina kwana".
Shiru yayi kamar bai jitaba,
Allah ya sani ya tsani kallo a rayuwarsa ta duniya, baya kuma son mace, da rashin kamun kai.
Hajia Mama kuwa ganin yadda ya takurene yayi kici-kici da fuska, yasa ta Wan, kalleshi tare da cewa.
"Jabeer Batul ke gaidaka, itama jiya tazo".
Kanshi ya Wan rusunar tare da mi?ewa tsaye, cikin sanyi yace.
"Masha Allah".
Daga nan ya Wanyi taku biyu zuwa uku, kana yace.
"Mama barin inje inyi shirin jumma'a".
Murmushi tayi tare da cewa to. Dan ta fahimci zillewa yakeyi.

Daga nan shi dai yayi, ciki.
Su kuma suka, fita.

Haroon kuwa Data ya kunna,
Umaymah ya turawa video Win da yayiwa Jabeer da yana cikin fushin.


A can Rugar Bani kuwa, yau tun safe, su Shatu suka baro asibitin, sabida, matasan maya?an cikin garin Shikan Win sai kai komo sukeyi, cikin asibitin. kana sai zuwa sukeyi maja'iunsu, suna mitin.
Bisa dukkan alamu, sunada wata manufa, ganin hakane, yasa likitoci musulmai, suka bada shawarar a kwashi marasa lfyar a medasu cikin asibitin babban birnin ?adamaya, sabida su nan babban likitansu ya hanasu duba kowa.

Da wannan shawarar ne, aka kwashi duk marasa lfyan da taimakon yan agaji aka shiga dasu cikin Adamawa.
Dan an fara rade-raWin wai fulanin Rugar Bani sunce zasu Wauki fansa, to shisa ?abilar Sachama suma suketa guzurutsoma, har ta kai da matakin in dare yayi matasan hausa fulani na cikin garin ma zauna cikin garin Numan, sai su futo suyi ta yawo da makawai suna kare amguwanninsu.
Kana suma ?abilar Sachama sai su fito da makamai suna kare amguwanninsu.

Shatu kuwa basu wuce cikin ?adamaya ba, sabida Ummiy ta dawo hayyacina ta, hakama Junainah ta dawo haiyacinta da ?arfin addu'o'in da Aysha da Bappa keyi.
Dan haka su cikin Rugarsu-suka koma.

Shatu kuwa, tunda Junainah ta gaya mata batun Sacewarsu Ya GiWi da kuma kashe ya Lado da akayi, har zuwa yanzu bata daina kukaba.

Koda Ba'ana yazo wurinta daren jiya, da yaji lbrin sun dawo babu abinda takeyi sai kuka.
Shi kuwa Ba'ana, ba?in cikinsa shine da Ummiy ds Junainah da Bappa suka rayuwa,
Shiyasa yanzu, yayi musu nasu shirin mutuwa namu samman.

Inda Bugulu Maman Ma'ans ta gasa zabbbin da Ba'ana ya yanka, kana ta daka musu, yajin borkono, da busasshen kan maciji.
Ta barbaWa musu, kana ta yaryaWa man shanune da ya gauraya da dafin macijin cikin man shanun da tayi musu gashin dashi, kana ya nufi, bakin garkensu, da akoshin gasassun zabbin.
Sannan ya aika aka kira mishi Shatu,
cikin kuka Rafi'a tacewa Wan aiken yaje, ya zazzaSi ke damunta.
Koda yaron yaje ya gaya mishi,
sai yace zai a kira mishi Junainah,
Koda yazo ya gaya musu,
Sai Junainah ta mi?e tabi bayan Wan aiken.
Kasan cewar garken nasu ba nisa, tafiya kaWan tayi ta isa, ta isa ta zauna a bakin ?ar bukkarsa da yake, cikin.
cikin disashewar muryar hawaye na zuba tace.
"Ya Ba'ana, kaje ka dubo jikin Ya Junaidun ne?".
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau, cikin sanyi yace.
"Eh naje na dubashi, jikinshi da sau?i, ke ya naki jikin? Ya Ummiy da jiki".
Cikin sanyi tasa hannu ta share hawayenta dake shatata kana a hankali tace.
"Ummiy jikinta da sau?i sai dai har yanzu bata mgn, Adda Shatu kuma sai kuka takeyi".
Hararanta yayi a fakaice, ji yake kamar ya jawota ya caka mata mashi ya mata kisan zahiri sai kuma ya fasa,
Kanshi ya kauda tare da tura mata akoshin gasassun zabbin nan kana yace.
"Ayyah sannu Junnuna, kiyi ha?uri dena, kuka, kici nama, sai kije kicewa Mata, tazo zan gaya mata inda su ya GiWi suke".
Cikin rawan jikin jin yunwa tace.
"Yauwa bani inci dama yunwa nakeji, tun jiya banci komaiba, tunda muka dawo, bamuyi girkiba."
Da sauri ya turo mata akoshin tare da buWe mata fefeyin.
Cikin rawan jiki irin na masu jin yunwa tasa hannu ta...!



Uhummm Allah kaimu gobe lfy, mu ?ara sa free page, daga PAGE 15-16 an gama.






By

20 / 72