Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   40 / 72

117K to 120K   out of 214K words

Umaymah na binshi,
Jakadiyarsu na bayansu.
Suna tafe cikin jin daWi ko ina yayi lib sai sanyin korayen ciyawi da furannin da dogayen bishiyoyin gwanda da ayaba da sukayiwa ko ina ?awanya.

Suna isa ?ofar Gimbiya Aminatu da sauri.
Sallama ya basu hanya, wanda a ?a'ida sai ya shiga ya nemawa mutun izinin shiga kafin ka shigo.
So amman Jabeer baida hijabi da sashin kakanin nashi,
shiyasa kai tsaye suka wuce.
Shiru babban falon babu kowa.
Haka yasa suka wuce sashin LamiWo, a hankali yayi sallama,
Cikin murmushin LamiWo ya amsa sallamar tare da cewa.
"Bismillah, ku shigo".
Kusan a tare suka kutsa kai cikin tamfatsen falon nashi.

Wani irin kallo sukayiwa juna,
Ganin...!






By
*GARKUWAR FULANI**MEVYASA? ME YAYI ZAFI SHI BA WUTABA? ME RIBARKU A CIKIN FIDDA LITTAFINA WOJE KU WATSASHI WA DUBBAN MUTANE? ME FA'IDAR HAKAN? NIYARKU KO TUNANIN KI, KADA WASU SUZO SU SAYA NE? A ZATONKI DANKU DAN KU ?ATA MIN RAINE? KO KUNA ZATON ZAKU HANANI SAMUN BINDA ALLAH YA RIGADA YA ?ADDARA YA RUBUTA RABO NANE? Nayi matu?ar mamakin al'ummar Annabi, Ni a zatona a iya hasashena, idan mace dan Allah da Manzonsa da darajar iyayen na kai ?ololuwar makurar ro?onda duk musulmi zai yi min al'farmar abinda na ro?a! Sai dai abin tsoro ashe abin ba haka bane, to wannan abun shine kadai ya bani tsoro, lallai kam tabbas muna akiruzzaman. Ai na sani kuma kuma mutanen kirki waWanda kuka sai littafina da zuciya Waya kun sani dole za'a fitar da littafi. Sabida ba kaina farauba kuma ba kaina ?arauba. Sabida haka kuyi ha?uri, dan Allah kuyi ha?uri, kuyi ha?uri da abinda wasu daga cikinku keyi. Alhamdulillah tunda na'annabi basa ?are wa, tunda har gobe saya akeyi, wasu suna ganin gana satan a gabansu, amman sai su kauda ido suzo gareni su biya kuWinsu a sasu a group ina godiya gareku*

Bayan Allah da Manzonsa da darajar iyayen dana haWa mutane dasu bani da wani tsumi ko dabarar tsira daga sharrin masu zuciyar da basu san girman Allah da Manzonsa da darajar iyayensu ba. Domin duniya gaba Waya tana fama da gubar irin waWannan. Iya tsaro dai kamar na bankuna, to amman me ana samun masuyin kutse a ciki har suyi sata. Manyan kampanunnuka na duniya ma suna fuskantar Sarayj yan kutse, hakama ?an Film suke fama da wannan matsalar, to mu ma rubuta suwaye mu da zamu tsira dasu, Ro?ona anan dan Allah da Manzonsa abar maimaita mgnar a cikin groups Win GARKUWA. Su masu fitarwa dai na fita ha??insu tunda inai musu posting sau biyu a rana kamar yadda na faWa, su sukaji suka gani suka fitar, to wannan can musu. Ina da mutanen da nake matu?ar ganin kimarsu da darajar su a SPG shiyasa, bazan tanka musuba.


*Fatan al'khairi VIP groups ?an dari uku ina al'fahari daku, kun bawa maras Wa kunya, shiyasa tun forko nace Ni kune VIP na, duk da nasan kuma Win a cikinku tabbas akwai masu fiddawar, to amman dai naku baya zama illa kamar na SPG. Ina yinku Wari bisa Wari.*

Wlh rubutu yafi sau?i akan mu'amalat da wasu ta?adiran da yake jarabtan marubuta da mgna dasu, ya ilahi ya mujibadda'awati, kai ina jinjina muku marubuta fama da wasu mutanen, wato da a haWaka mgn da wasu gwara kawai a baka renon shanu garke guda na wuni Waya, domin shi dabba yasan abinda ake kira da makiyayinsa, amman wasu mutanen basu san darajar Allah da Manzonsa ba bare iyayensu. Allah ya kyau. Allah ka haWamu da mutanen kirki.


*Littafin GARKUWA na kuWine turo katin mtn na Wari uku kacal ta wannan layin 09097853276, ko ki turo dubu Waya ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.*

*Zan ?ara ro?o ba domin irinku kangararruba a a sai dan masoyan Allah da Manzonsa, dan Allah kada ku fitarmin da littafina. In kin san kin sayane dan ki fitar min da littafina to dan Allah da Manzonsa kizo kimin mgn ta pc kice kawai GARKUWA bani kuWina bazan iya saya ban fitarba, wlh Salim alim zan meda miki kuWinki in biki da godiya, in kuma baki sayaba zaki saya dan ki fiddane dan Allah kada ki saya. Dan Allah in kin rigada kin saya kuma Please turo ac no Winki kawai kadama kiyi mgnar kamai a take zan meda miki kuWinki in cireki in miki godiya=?O?


LamiWo da Galadima da Sarkin ShaWi. Bisa alamu wata mgna mai mahimmanci suke tattaunawa.
Murmushi LamiWo yayi tare da kallon Umaymah cikin kulawa yace.
"Khadijah lale da zuwa Masarautar JoWa."
Da sauri Umaymah ta ?arasa gabansu, cikin ladab ta zauna gabanshi tare da du?ar da kai tace.
"Allah rene Barka da dare".
Kanshi ya jinjina irin na sarakuna kana yace.
"Barka dai Khadijah kinzo lfy, ya Sarki Aliyu?".
kakan Haroon kenan wanda ya haifi baban shi.
Cikin girmamawa tace. "Yana lfy yace yana gaidaka".
Kanshi ya jinjina, kana ya Wan kalli Jabeer dake danne-danne a wayarshi.
Ya hakimce ya Waura ?afa Waya kan Waya.
Jakadiyarsu kuwa tayi shiru a gefe kusa dashi.
Galadima da Sarkin ShaWi kuwa, murmushi sukeyi suna kallon Jabeer.

Gyaran murya LamiWo yayi kana cikin dattaku yaci gaba da cewa.
"Ina amsawa, ya kika samu jikin Wan naki?".
Cikin murmushi ta juyo ta kalli Jabeer kai ta rusunar ganin samfa hankalinshi baya kansu cikin yin ?asa da murya tace.
"Alhamdulillah na samu jiki ya worke!".
Galadima ne wanda yake ?anine ga baban LamiWo ya amshi zan da cewa.
"To sai ki sanar mishi batun komawa Rugar Bani, dan ramuwa bisa cika ?aidar..".
Shiru yayi bai ?arisaba jin muryar Jabeer yana cewa.
"?a'idar Allah da Manzonsa ne da zai zama dole sai an cika, ba ?a'idar wani zalumci da tozarcinba".
Kanshi ya Wan tan?wara a wuyanshi.
Kana ya zamo kaWan ya zauna gaban Umaymah cikin nuna rauninshi yace.
"Ayyah Umaymah kada kice min inje, Please Umaymah ki fahimci wannan abunfa al'adace ba addini ba, kuma abune da kai tsaye zamu iya ce mishi makaruhi in ma bamu haramtashi ba, ya za'ayi inje in sake tuSe kayan jikina a gaban duniya wai dan in daki wani. Ni bana so.
Ba dai sune suka kainiba, suka kuma ce a dakeni, to dan me zasu buwayeni da sai munje na rama".
HaWe fuska Umaymah tayi cikin kafeshi da ido tace.
"Ni bana iya yiwa iyayena musu. Jabeer tabbas na sani al'adace ba addiniba, amman ka sani duk wani abun da zakaga ya faru a duniya to akwai dalilin faruwarshi, kada kace zaka tsananta bincike tabbas lokacin zai baiya mana dalilin.
Bana son gardama kawai kaje Dan ALLAH".
Hannunshi yasa ya dafe kanshi,
kana yayi shiru Umaymah ta gama dashi da tace dan Allah, ya sani tabbas da a madadinsa Ayyah Win da yace forkon mgnar da ya mata da ya rigata cewa Dan Allah da shike nan yasan zatayi shiru.
Shi kuwa LamiWo murmushi yayi tare da kallon Umaymah cikin jin daWi yace.
"Allah ya miki al'barka".
Da sauri tace.
"Amin ya Allah".
Galadima kuwa, murmushi yayi tare da jinjina kai.
Jakadiyarsu ma cikin jin daWin tasirin mgnar Umaymah akan Jabeer take murmushi sabida ta sani.
Shi mutunne mai kaifi Waya, in yace eh tofa eh Wince inko yace a a to a'ance.
Especially baya son duk wani abu da zaici karo da addininshi.
Kanshi ya jinjina Umaymah alamar shikenan idonshi yayi jazir alamun dole akasashi yin abinda baya so.
Kana ya kalli kakarsa dake murmushi tsuke fuskarsa yayi tare da cewa.
"Gimbiya Aminatu muje ki bani gashin da kikayiwa LamiWo".
Cikin dariya Gimbiya Aminatu tace.
"Iye gashinsama zan baka?".
Da ?arfi yace.
"Eh shi zaki bani, ai in dukane kam ya iya zille kanshi ya turani.
Shine dan gashinsa zakice iye".
Murmushi tayi tare da bin bayanshi,
ganin LamiWo na mata alamun taje ta bashin.

Nan sukaci gaba da hira, suna tattauna wasu mahimman al'amuran da sirrine garesu iya su biyar.
Wato LamiWo, Galadima, Sarkin ShaWi, Umaymah, Jakadiyarsu.
Bayan su babu wanda suke yarda da sanin sirrin Jabeer.
A hakanma kuma a suWinma akwai wani sirrin da babu wanda ya sanshi sai LamiWo da Umaymah.


Suna zuwa har falonta suka wuce.
Wani kekyawan akoshi mai masifar kyau ta Wauko mishi.
Ta ajiye a gabanshi.
Inda yake zaune a ?asa bisa carpet ya naWe sawunshi.
fork Win dake saman fefeyin ya Wauka.
Daddageggen gaseshen jan namane wanda yaji wuta ya gasu gashin tukunyar ?asa yayi tiSis.
Sai wani irin ?amshi na musamman yakeyi,

A hankali yake sa Fork Win yana yagan tattausan tsokokin yana sawa a baki.
Ita kuma tana zaune gefenshi.
Tafashesshen madaran shanu mai Wan Wumi ta mi?a mishi a wata ?ar ?warya mai kyau.
Taune naman yayi tare da haWiyewa kana cikin zuba mata ido yace.
"Dole sai na karSa da hannun nane? Ki ajiye mana.
Da wanne hannun zan amsa tunda inacin abinci dana daman".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Dole sai ka amsa, bazan baka shi a ?asa".
Kanshi ya Wan rausayar tare da cewa.
"Allah ya nuna min ranar da za'a bar.
Wannan tsare-tsaren shamfi na masarautar JoWa. Komai da ?aida da yadda ake yinshi".
Ita dai mi?a mishi ?waryar takeyi dole ya ajiye spoon Win yasa hannunshi ya amsa.

Nan suma sukaci gaba da hira.
Sai kusan sha Waya Umaymah da Jakadiyarsu suna fito.
A nan Gimbiya Aminatu ta ajiyesu suma saida sukaci gashin nata kafin suka tafi.

Kafin su isa Side Winsa dai sha biyun dare tayi.

Haka yasa suna isa suka samu ba kowa a falon.

Sai Haroon da suke jiyo muryar sa, a falon Jabeer.

Cikin nitsuwa ya matso kusa da Umaymah a hankali yace.
"Sai da safe Umaymah kiyi bacci ki huta."
To tace har ta juya zata tafi sukaji Muryar Haroon yana cewa.
"Abba yazo wurinki zaku gaisa bai samekiba, nace mishi kun tafi wurin LamiWo yace, to saida safe ya gaidaki da hanya Hajia Mama ma yanzu ta fita, tace LamiWo ya ri?e mata ?anwa".
Murmushi tayi tare da cewa.
"To Allah ya bamu al'khairi saida safen".
Amin Amin suka ce.
Kana shida Haroon suka wuce Side Winsa.

It's kuma Umaymah da Jakadiyarsu suka wuce.
Side Win da kullum in dai Umaymah tazo nan take sau?a.

Suna shiga suka samu, tuni Hibba tayi bacci, wannane ya basu damar tattauna wasu mahimman sirrukansu.

Nisawa Umaymah tayi bayan ta saurari jawaban Jakadiyarsu Jabeer cikin tsantsar tafasar zuciya da tarin ba?in ciki tace.
"Uhummm suyi dai Ni nan ina dai-dai- da ?ugun ko wanne shege da shegiya,
In sha Allahu zasusha mamaki.
Zasuga yadda Ubangiji ke ikonsa, ban cire raina ?ar uwarta zata sake rayuwar enci da salama, da izinin Ubangiji zataga sakayar waWanda suka cutar da ita da yaranta a gaban idonta.

Cikin zubda hawaye Jakidaya tace.
"In sha Allah, sai farin ciki ya dawo, a sashinta, inata addu'a a kullum a cikin dukkan sallolina, Allah ya kare ahlinta, ya kuma baiya gsky tayi halinta kowa ya gani".

Amin Amin Umaymah tace tare da share hawayenta.

Washe gari ranar Alhamis. Ta kama yau kwana shida da faruwar gasar ShaWi, kana gobene za'a koma dan ramuwa,
A goben kuma zai cika kwana goma da kisan gilla da kafurai ?abulun ?achama sukawa Fulanin Rugar Bani.

Misalin ?arfe sha biyu na safe.
Fadar Sarkin Nuruddeen Bubayero JoWa, cike take ma?il da tawagarsa kama daga.
Galadima, Waziri, Wambai, Dan buram, Dan iya, ?an isa, ?an Kade, Sarkin fada, Sarkin ya?i, Sarkin Dowaki, Sarkin Gabas, Sarkin Kudu, magaya?i, Jarma uban doma, Makawa ?urSi, Turaki, Da dai sauran members Win masarautar baki Wayansu, an cika anyi ma?il.
Sallama na tsaye can bakin ?ofar shigowa.
Dogari kuma suna tsaye gefen hagu da daman LamiWo.
Suna rike da mafici sunayi mushi fifita, Wanzagi kuma yana gefe,
Kana wasu fadawan duk suna gefen.
Gyaran murya LamiWo yayi tare da gyara zaman shi cikin shugarsa ta sarakuna masu al'farma, a hankali yace.
"To da farko dai fatan duk kowa na lfy".
Da sauri ?anzagi yace.
"Sarki ya gaisu yana yi muku fatan alkhaiy".
Sai ya kuma juyo ya kalli LamiWo tare da cewa.
"Godiya suke."
Kanshi ya Wan jingina da tattausar kujerarsa da masu son gadonta sunfi a ?irga, cikin ?asaita yace.
"Kamar dai yadda muka tattauna, kwanakin baya akan sarkin Garin Shikan,
to yanzu zan zantar da hukunci.
Sarkin aike na bada umarni kaje garin Shikan ka karSo min sandar sarautar Shikan ka kawo min shi, yau Win nan.
Kaje da jagorancin Galadima, da Matawalle da Makawa, sai sarkin ya?i".
Da sauri duk suka runsunar da kayu kansu tare da cewa.
"An gama".
Nan take kuwa suka mi?a suka tafi.

A cikin gida kuwa. Tunda asuba da Jabeer da tawagar ahlinshin suka dawo masallaci.
Kai tsaye Wakin Umaymah ya nufa, suna biye dashi a baya.
Bisa sallaya suka sameta ri?e da al'?urani mai girma tana karatu cikin tsananin nitsuwa.

Ganin hakane duk suka fito falo.
Nan Aunty Juwairiyya taja Ummi suka tafi side Win ta da Hibba da ?ar aikinta suka shiga kitchen.

Jalal kuwa shine yaje wurin Ya Jafar, don bashi mgni kamar yadda Jabeer ya umarceshi.

Jamil kuwa waya yakeyi da sabuwar budurwarsa da ya samu.
Wacce yake masifar sonta,
Ko yaushe suna li?e da juna a waya.

Haroon kuwa a falon Jabeer ya zauna yana kallon lbrin CNN.

Shi kuwa Sheykh Jabeer.
A hankali ya wuce ta gaban Haroon.

Gefen gabas ya fuskanta, inda labulaye sukayiwa wurin ?awanya.
A hankali yasa hannunshin ya yaye labulen.
Wani ?ofa ya buWe a .
Sai ga wani Wan siririn corridor.
Shiga yayi, kana ya saki ?ofar ta koma ta mannu da ?ofar sai dai bata rufuba.

A hankali yake taku cikin nitsuwa,
Lips Win shi na Wan motsawa alamun tasbihi yakeyi.
Tafiya mai Wan tsawo yayi sai gashi ya kuma riski wata ?ofar.
Hannunshi yasa ya murWa key Win ya buWe, ?ofar.
Sai ga kuma wata ?ofa irin ta ?arafuna kana dai iya hango woje.
BuWe wannan ?ofarma yayi.
A hankali ya kutsa kai.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya mai tsawo yaja ya sau?e a hankali.
Idonshi ya lumshe sabida wani irin sanyi mai masifar daWi daya ratsa mishi jiki da zuciya.

Wani irin Wan madaidaicin Garden Park ne mai masifar kyau.da sanyi da tsaruwa.

Daga nan bakin ?ofar daya fito Win.
Tayis ne fari tas a malale iya ganinka, sai gefen damanshi da bishiyoyin ayaba masu masifar duhu da sanyi dake jere reras.
Gefen hagunshi kuma bishiyoyi mangoro ne irin yan du?us-du?us Win nan ke jere,
Reras.
A hankali yake taku yana tafe yana tasbihi.
Yana jin kukan tsuntsaye mai daWin ji yana ratsashi.

Tafiya kaWan yayi sai gashi ya baiyana a wani irin wurin mai masifar kyau.
Wasu yan zagayen gini dakalin bulok bibbiyu akayi a ?alla sunfi hamsin.
A ciki ko wanne zagayen akwai bishiyar dabino. Na gabanta inabi na gaban inabi tuppa, kana sai Yazawa, sai kuma na tsada, daga tsada sai na kanya, sai goruba da na giginya.
Cikin ko wanne zageyen kuma ?asanshi koriyar ciyawa ce mai sanyi.

Can tsakiyar filin kuma wata iriyar ?oramace mai masifar sanyi,
Ruwanshi na kwance fari ?al-?al bakin wurin kuma jeren bishiyoyi goibane wanda sukayiwa kwaramar inuwa.

Gaban ?oramar kuma wasu irin kujerun silver ne masu masifar kyau da sansi a jere a ?alla sun kai goma zuwa ashirin.

Can gefenshi kaWan kuma wani shingene aka zagaye da waya.
Shuke-shuken gargajiya akeyi a wurin.

Nan kusa da ?oramar kuma shingen farar waya akayi a cikin ta wanda akayi ?an Wakuna-Wakuna a cikin.

Tsuntsaye ne a ciki iya ganinka ko wanne da muhalli shin.

Kama daga Tattabaru farare ?al-?al.
Sai kuma tsuntsu carki jajaye masu kyan launi ga kuma kanari da suke blue.

Sai kuma zabbi da suke yawo a ?asa tako ina.
Can bakin ruwan kuma agwagin ruwa ne sunfi Wari ?wa-?wa.

Sai kuma zabbin daji.
dangin tsuntsaye dai babu irin wanda babu.

Ido ya zubawa tsuntsaye tamkar mai son yin magana dasu.


A hankali ya sunkuyar da kanshi jin tattausan gashin ?awisun Masarautar JoWa da ya kai shekaru masu tarin yawa.
A hankali ya rusuna tare dasa tafin hannunshi ya shafa dai-dai ?unWun ?awisun inda wurin yake mai kalar blue mai kyau sabida Sheykh blue ne kalar da yafi so.
A hankali ta fara taku, ta juya mishi baya kana ta Waga bindinta sama samSal har yana iya taSo geminshi.
Wani irin takun ?asaita tayi kana ta buWa fikafikinta ta bazasu, ta fara tafiya a hankali.
Wannan itace suntsuwar da muddin mutun ba jinin Masarautar JoWa bace, in ka shigo mata gaba gaWi ba tare da an gabatar mata kai ba, zatayi ta yagune mutun tana caccakarshi.
Amman muddin dai kai jinin Masarautar JoWa ne, kana shiga zata zo gabanka.
Tayi maka hakan.

Sai dai kuma bayan yin hakan in mutun nada wata zazzafar nasaba a masarautar misali shine sarki maici to in tayi wannan baza fikafikinta takanyi ta zagaya sarki sau bakwai kafin ta tsaya a gabanshi sai sarkin ya umarceta data tafi kafin zata tafi.

To babban abinda ya ?ara jazawa Jabeer matsala a rayuwarsa shine,
Duk sanda yazo gaban tsuntsuwar ?awisun nan sai tayi mishi wannan abin da zagaya sau bakwai abinda a tarihin masarautar sarki kawai yakeyiwa abin.

Matsalar abin a gaban Barrister Kamal da kuma Baba Bashiru da Abba sai LamiWo ne ta fara yimishi wannan abun.
Tofa ta bakin Baba Basiru ne mgnar ta zaga kunnen mazauna masarautar JoWa.

Babban tashin hankalin masu son gadar wannan kujerar, shine yadda side Win Jabeer ke kusanci da Garden Win da take ciki.
Tashin hankalinsu ya ?ara tsananta ne tun randa Suka ga LamiWo yasa an buWawa Jabeer hanyar shiga wurin ta cikin falonshi ba sai ya zagaya yabi hanyar da kowa ke bi ba,
Ya zama shida LamiWo sune masu hanya kowa daga falonshi zai shiga wurin.

A hankali Jabeer yayi murmushi tare da kallon yadda tsuntsuwar ta gama zagayashi kana tazo ta tsaya gabanshi tare da baza fikafikinta.
Cikin harcen Larabci yace mata.
"Fatana dai ba bauta min kikeyi ba! Domin babu wani abin bautawa da gsky sai Allah, wanda shine ya halicce ni ya halicceki.
Ni kuma ba kowa bane face halittarsa, sai dai na kasance cikin halittarsa mai girma da karrama fiye da komai, dan shi da kanshi yace.
Wala?ad karramna bani Adam."
Wani irin juya kai tsuntsuwar tayi kana ta meda fiffigefa ta rufe, kafin ta juya ta nufi wani kekyawan wurin da aka ware mata, inda take tare da yayanta da mijinta.

Juyawa yayi can gefe ya hango wasu yan kyawawan tsuntsaye farare
A bakin ruwan.

Ga tattabarun sun zagaye wurin da sauran tsuntsayen.

A hankali ya zauna a wata kujera mai kamar gado.
Kishin?iWa yayi kana ya lumshe idonshi yana maijin yadda sassanyan iskar wurin ke ratsashi.
Karatun al'?ur'ani ya fara cikin sassanyan murya mai daWin sauraro.


Umaymah kuwa tunda ta fito, sai ta nufi sashin Hajia Mama, hira sukayi sosai cikin sha?uwa irin ta yan uwa.

Suna zaune a nan Abba ya shigo.
Tana ganinshi tai murmushi,
shima murmushin yayi tare da cewa.
"Maman yara".
Cikin sakin fuska tace.
"Na'am Yaya".
Murmushi mai cike da zafi da ?una wanda ya baiyana har kan fuskarshi yayi

40 / 72