Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   5 / 72

12K to 15K   out of 214K words

a idanun mutanen duniya shi tamkar Wan akuya suke ganinshi,
Kamar yadda Ya Jafar yake ba majanuni bane amman mutanen duniya kallon majanun suke mishi".
Kanshi ya sunkuyar cikin sakekkiyar murya yace.
"Duk an li?a musu munanan tabo, a cikin rayuwarsu, Umaymah, ni ma Win bazan tsiraba tabbas nasan nima akwai wani tabon da ake kallona dashi, nasan nima bazan tsiraba".
Da sauri Umaymah ta sunkuyar da kanta ?asa wasu zafafan hawaye masu azabar zafi da ?una a zuciya suka fara kwaranyowa a idanunta, wani zazzafan shesshe?an kuka ya kwabce mata.
Jin shesshe?an kukan natane yasa Sheykh Jabeer ya Wan Wago kanshi cikin jarumta da ?arfin hali yayi wani murmushi mai ciwo a rai.
A hankali yace.
"Kuka kuma Umaymah, inada ya?inin ?arfin zuciyarkine da yasani sanar dake matsalar ?a?an ?ar uwarki, tunda ita bazata iya yin komai a kaiba".
Cikin shesshe?an kukan tace.
"Ba komai Jazlaan in sha Allah babu komai face al'khairi a cikin rayuwarku, insha Allah babu wani tabon da mutane ke ganinka dashi.
Yanzu yaushe zaka wuce Leddi julSe?".
Cikin miskilar murya mafi karamci yace.
"Yau da dare zan wuce, gobe da asuba zamu wuce Saudiyya Sittin ta matsa tana so taje taga ahlinta".
Kai ta Wan gyaWa kana tace.
"Ibrahim ma yace ya kusa dawowa".
Kanshi ya Wan rausayar kana yace.
"Eh munyi mgna dashi Wazu".
Kanshi ya Wan juyo ya kalli sauran woyoyinsh dake bisa Stull Win dake gefenshi,
Kiran shugan Waliban J.S.U ?adamaya ne ke shiga,
bai kula kiranba yaci gaba da magana da Umaymahnshi, har saida yaga ta samu nitsuwa kafin ya barta.

Tashi yayi a hankali yake taku cikin kamala da nitsuwa irinta manyan limamai a hankali yake manna farar tattausar fatar ?afarshi da in ya taka sai kaga kamar jini zai tsallo.
Yana shiga cikin Wakin nashi, al'kyabbarsa ya cire tare da buWe wani sashi na durowarsa ya san?ala a masan?alinta.
Da tattausan farar jallabiyar dake ?asanta ya shiga bedroom da ita,
Wannan lokacin wonkansa ne, babu abin da zai katse mishi uzurin domin ya kasance mutun mai mutunta lokacin rayuwarsa ko wani lokacin da abinda yakeyi.

Wonka yayi cikin tamfatsen bathroom Win nashi.
Yana fitowa, ya wuce gaban dreesing mirror, kimtsawa yayi a gaggauce dan lokacin tafiya aikinshi ya karato.

Koda ya gama kimtsawa cikin wasu tattausan manyan kaya riga da wondone da kuma babbar gariyarsa, kayan sun kasance farare ?al-?al ne, sai zazzafan aikin kufta da akayi mishi mai blue color, kana sai hular zanna bukar daya murza bisa kanshi da yake wadace da tattausan suma ba?i??irin mai sulSi da she?i,
hular itama farace sai ratsin blue, hakama takalman sawunshi da suka kasance irin na sarakuna ne,
Agogon Daimond dake hannunshi shima yanada yanayin Wigon blue mai garai-garai,
Sai kuma ya sunkuyo ya Wau?i biyu daga cikin woyoyinshi yasasu a al'jihun babbar rigar tasa,
jakar system Winshi ya Wauka da hannunsa na dama, kana hannunshi na hagu kuma sajenshi yake shafawa a hankali har zuwa kan madai-madaicin tsabtaceccen gemunshi mai Wan karen kyau da burgewa.

A haka ya fito daga cikin Wakin nashi.
Yana fitowa cikin tamfatsen falon nashi da ya kasance yanada iyaka da bayi da hadimai duk iya karsu can bakin ?ofar babban falo bai yarda da wai bayi su shigo suyi mishi hidima har cikiba,
Jamil shike kula da tsabtan sashin sirrin Wan uwan nashi.
Ido ya lumshe jin wani irin sassanyan ?wamshi da sanyi mai ratsa zuciya daya ziyarci jiki da zuciyarshi.

A hankali yake taku, har zuwa dinnin area, a hankali ya Wan juyo, jin an jamishi kujerar.
Jamil kenan.
Zama yayi bisa kujerar, kana, ya mi?awa Jamil jakar system Win nashi.
Amsa yayi ya rataya a kafaWarshi,
sannan ya matso gab kusa da Wan uwan nashi,
ba?in Tea ya haWa mishi da zuma sai bredy wanda shima da zuma a jikinshi ,
wanda yasan iya abinda zai ci ya sha kenan duk da tarin. Abinci da hadiman Aunty Juwairiyya, suke kawowa dominshi ga kuma na Hadiman Hajia Mama, wanda duk Umminshi Jakadiyace ke kawosu, domin ita tana shiga har cikin falonshi Wakin konciyarshi ne dai bata shiga, amman falo ukun nan duk tana shigarsu da kitchin da sauran Wakunan sashin.
Suna zama babu jimawa, wayar Jamil ta fara tsuwa, da sauri ya Wauka tare da karawa a kunne,
sai kuma yayi zuru-zuru da idanu ganin yadda Hammanshi ya tsareshi da fitinannun idanunshi masu sa hanjin cikinsu kaWawa, cikin yin ?asa da murya yace.
"My love Sheykh yana kusa".
Ya ?arishe mgnar da murmushi a fuskarshi, shi kuwa Sheykh kauda idonshi yayi yaci gaba da zu?an tea Win a hankali a hankali.
Shi kuwa Jamil cin abinci yai hanin?an kana.
Shi kuwa Sheykh ido kawai yake zubawa ?anin nashi bai tashiba har saida yaga Wan uwan nashi ya gama cin abincin.

Sannan suka jero suka fito falo,
A can bakin ?ofar shigowa babban falon suka samu sarkin ?ofa da kuma hadimai na jere a wurin suna hangosu duk suka rusuna har ?asa har suna haWa baki wurin cewa.
"Takawarka lfy Wan Babban Yaya jikan mai martaba sarkin Nuruddeen jika ga mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin.
Malam Wan Malam Habibullah jinin Limamen Saudia malamai magada annabawa, jika ga ?abilar da tafi ko wacce ?abilar duniya d...".
Hannun shi biyu ya Waga musu alamar amsawa gaisuwar da sukayi mishi, da kuma dakatar dasu da kirarin da sukeyin.
Kana yaci gaba da taku Jamil na biye dashi a baya, Sarkin ?ofane yayi saurin rusunawa tare da cewa.
"Hajia Mama ta turo jakadiya a sanar maka cewa tana bu?atar ganinka".
Kanshi ya gyaWa kana yaci gaba da tafiya,

Gefen dama ya nufa, inda wani tamfatsetsen part mai tarin girma yake, a hankali hadiman dake tsaron wannan ?ofar suka fara rusunawa tare da bashi hanya da gaidashi.

Tafe suke har cikin part Win, wani babban falo suka fara ratsawa kana suka wuce zuwa cikin wani corridor sai gasu a wani fitinenne falo mai wadatar tsabta da ?amshi.

Wasu ?an yarane guda biyu duka mata,
Suna ganinsu suka ruga a guje jikin Sheykh Jabeer suka faWa tare da cewa.
"Sabahul khair Uncle MJ".
Sunkuyowa yayi ya Wan shafa kansu tare da cewa.
"Sabahul noor ya Habittey".
murmushi sukayi kana suka sakeshi suka isa gaban Jamil sunkuyowa yayi ya Wauki ?aramar bayan sun gaidashi ne babbar ta juya da gudu tana cewa.
"Ummi ga Uncle MJ".
tsayawa tayi tare da kamo hannun wata kekyawar mace matashiya yar duma-duma, tayi shiga irin ta larabawa, kamo hanunta tayi suka fito falon.

Murmushi ta Wanyi tare da cewa.
"Barka da safiya GARKUWAN FULANI, GARKUWAN ahlin Sitti".
Fuska ya Wan sake still bawai yayi murmushi bane, a hankali yace.
"Barka da safiya".

"Barka dai Sheykh Dr Garkuwa".

Babbar rigarshi ya Wan gyara tare da cewa.
"Ya jikin Ya Jafar?".
Kai ta Wan ran?wafar tare da yin rau-rau da idanunta murya na rawa tace.
"Jiya kwana yayi baiyi bacciba, Sheykh, hankalina yana tashi, sabida duk randa baiyi bacciba, to kwana yake karatu yanayi yana kuka, kukan da yakeyi Win ne yake sashi zazzaSi da ciwon kai, gashi ba cikin zuciyarsa yake karatunba ya wuni karatu a baiyane ya kwana karatu a baiyane babu bacci".
Kanshi ya Wan jujjuya tare da nufar kofar wani Waki.
Jamil da Juwairiyya na biye dashi a baya.

Suna shiga cikin Wakin, da sauri Sheykh ya karisa gaban wani kekyawan mutun fari ?al mai tarin tsabta wanda yake tsananin kama da Jamil duk da duk suna kama da juna amman Jalaluddin yafi kama da Jabeer, Jamil kuma yafi kama da Jafar.
Zaune yake bisa sallaya, ya jingina kanshi da jikin gado, karatun al'?ur'ani yakeyi cikin nitsuwa da da cikar tajwid, babu Sata ko na Wigo, yana karatun ne hawaye na kwaranya daga kwayar idanunshi,
A hankali Sheykh Jabir yasa Hannu ya kamo hannun Wan uwan nashi,
A hankali Ya Jafar ya buWe idanunshi ganin mutumin da shi kaWai ke sashi yin abu yayi ko ya hanashi ya hanune ya sashi gyara zama still yana karatu.
A tausashe Sheykh Jabir ya Wan ran?wafar da kanshi cikin salon tausayawa da muryar larabawa yace.
"Sadakallahul Azeeeeeem".
Jin hakane yasa wannan bawan Allah'n ya Wago tafin hannunshi addu'o'in ya, fara karantawa kusan tsawon 3 minute sannan suka shafa a tare,
Cikin wani zafi da ?una Sheykh Jabeer ya taune lips Win shi na ?asa hannunshin yasa ya kamo na Ya Jafar Win,
ba musu ya mi?ar dashi,
kan gadonshi ya zaunar dashi,
A hankali ya juyo ya kalli Juwairiyya cikin sanyi yace.
"Yaci abinci kuwa?".
A hankali tace,
"Tunda asuba daya dawo masallaci na bashi yaci abinci, kuma yanzuma na bashi ya Wan ci".
Kanshi ya rausayar kana yace.
"Maganin shi fa kin bashi".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Eh na bashi maganin yasha".
Jin hakane yasa Sheykh ya kamo hannun kekyawan Yayan nashi ya kontar dashi bisa gadon blanket yaja ya rufe mishi rabin jikinshi a hankali yace.
"Ya Jafar kayi bacci, kaji jikinka zafi".
Shiru bai kulashiba sai dai, ya lumshe idonshi.

A hankali ya juyo ya kalli Matar Wan uwan nashi kuma ?ar kawunsu yayan Mamansu yace.
"Juwairiyya Nagode".
Hawayen dake zubo mata ta sharce tare da kamo yaranta ta ruggumesu,
Jamil kuwa tuni yaketa zubda hawaye.
Cikin rawan murya Juwairiyya tace.
"Sheykh ka dena gode min nimafa Ya Jafar Wan uwanane kuma mijinane, uban ?a?ana, to in ban kula dashiba da waye zan kula a duniya?."
Kanshi ya kauda kana ya juya ya nufi hanyar fita a ranshi yanajin ko sai yaushe manyan burukan rayuwar da fatanshi da addu'o'in shi zasu ?arSu yana ganin daraja da girman Juwairiyya domin tayi musu tsantsar halacci ta zauna da Wan uwanshi a matsayin majanuni, a haka suke tafiya yana zancen zuciya.
Jamil na biye dashi a baya.

A haka suka fito, suna tafe hadimansu na biye dasu a baya.
A hankali ya Wan juyo ya kalli Jamil da yasan yanada rauni dan Jamil yanada tausayin Wan uwanshi duk da yanada shekiyanci amman yanada rauni a kansu abu kaWan ke sashi kuka,
Sashin dake tsakanin sashin su Jamil dana Ya Jafar suka wuce wanda nanne sashin Sheykh, sashin su Jamil Win suka shiga.
Kai tsaye suka wuce har cikin bedroom.
Tsaye suka sameshi yana taje suman kanshi mai yawa ga wondo iya ?ugu duk rabin boxes Winshi a woje ga wondon da rabin jiki duk woje waishi kirezi ko? da alamun fita zaiyi.
"Meya hanaka zuwa masallacin jumma'a da wuri jiya?
WaWannan kolaben barasar na waye ne?".
Sheykh ne ya jero mishi tambaya biyu a lokaci guda,
A hankali Jalal ya juyo cikin shakku da shayi da kwarjin Hamma nasu ke sasu ji yace.
"Mamace ta aikeni, jiya shiyasa na dawo a ?urerren lokaci.
Kolaben barasar kuma nasu Ashid ne, na kwace ne lokacin da suka saya, dan karsu sha".
Kanshi ya gyaWa dan ya gamsu ya kuma yarda dan yasan duk rintsi ?anennshi basa mishi ?arya.
Cikin faWa yace.
"Ka kula da salla, ka tsaida ita kan lokacinta, kasan irin abokan da zakayi yawo dasu, ka tabbatar kaikeyi nasara akan juya halaiyarsu daga mummuna i zuwa kekkyawa. Shiyasa ban hanaka mu'amala da suba, domin manzon Allah yace.
"Mutun Waya ya shiryu ta dalilinka, tarin ladan yafi a baka tarin jajayen ra?umi.
Kada ka bari suyi nasarar juya rayuwarka daga kekkyawan i zuwa mummunan.

Kanshi ya gyaWa cikin ladabi yace.
"In sha Allah".
Daga nan suka juya baki Wayansu,
Kai tsaye sashin Hajia Mama suka wuce.
Inda hadimanta sukayi musu iso,
Har cikin bedroom Winta suka shiga,
A bakin gado suka sameta, zaune, yayinda baiyawarta Mansura keyi mata tausa.
Murmushi tayi tare da kallonsu yadda suke a jere, koda ma?iyinsu ne sai sun burgeshi sun bashi sha'awa yayi fatan inama da ?a?ansa ne.
Kan dantsatsetsen shimfiWar kilisa mai kyau da zanen tsuntsuwar Wawisu, suka zauna,
Cikin kula tace.
"GARKUWAN FULANI, Jamil, Jalal, Allah yayi muku al'barka".
Amin Amin, Sheykh da Jamil suka amsa,
Jalal kuwa shiru yayi,
Ita kuwa Hajia Mama murmushi tayi tare da cewa.
"Babanmu mai Al'farma Sarkin Musulmai Jalaluddin meya farune naga fuskarka a haWe?".
Kanshi ya girgiza alamar.
"Babu".
Shi kuwa Sheykh ido kawai ya zuba kan wayarshi,
Jamil ne ya Wan gyara zama, tare da cewa.
"Mama Abba fa".
Kai ta Wan jinjina tare da cewa.
"Abinda yasani nemanku kenan, Abbanku ya tafi Abuja jiya da dare, yanzu kuma Gimbiya Samira zatabi bayanshi".
Shiru Sheykh yayi a ranshi yake jinjina al'amarin mahaifinsu.
Babusu a cikin dukkan sabgogin rayuwarsa komai nashi saidai suji a bakin Hajia Mama ko kuma a jaridu ko gidajen Radio ceWi meWinshi da amaryarshi Gimbiya Samira ?ar sarkin Nokan ce ita kuwa mijinta shine rayuwarta babu ruwanta da sabgar kowa.
Sam Abba bai sha?u dasuba da wuya ka ganshi zaune dasu yana hira dasu kamar uba da ?a?an shi.
SaSanin Maimartaba ko meye zaiyi Sheykh zai sani shine mutumin da yake shawara dashi akan duk abinda ya shafi addini.
Kanshi ya Wan kauda tare da cewa.
"Allah ya dawo dashi lfy".
Amin Amin sukace baki Wayansu,
Cikin kula yace.
"Hajia Mama Affan fa sai yaushe zai dawo?."

"Next month?". Ta bashi amsa a gajarce.

A gogon hannunshi ya Wan kalla kana a hankali ya mi?e tare da cewa.
"Zan wuce Hospital shugaban Waliban makarantar ya kirani cewa sunada mara lafiyar da take bu?atar kulawar gaggawa".

Kai ta Wan rausayar tare da cewa.
"A dawo lfy".
Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.

Daga nan kai tsaye FADA suka nufa.
Inda sarkin fada yayi musu iso zuwa ga Maimartaba kakansu.

Suna shiga suka samu fada na cike da dattawa karsu Waziri, Matawalle, Galadima, Wambai, ?an isa, Wanm' buram, sairkin Dogarai sarkin Gida, da kuma Duba gari, kana, sai kuma hadiman dake tsaye bayan sarki sunayi mishi fifitar sarauta da maficin fiffigen ?awisu.

Farin dattijo bafulatani, mai cikar haiba.
Yana cikin manyan kaya na sarakai, wanda al'kyabbarsa kaWai ta kai kuWin mallakar wani gidan,
A gabanshi suka zauna gaba Wayansu uku,
A hankali Sheykh yasa tafin hannunshi kan rumfar sawun kakan nashi da suke kan wani tim-tim mai girma da masifar taushi.
taSa sawun kakan nashi yayi tare da cewa.
"Barka da hantsi Maimartaba, ya sawun naka?".
Duk maganar nan da yayita a hankali yake yinta ko Jamil da Jalal dake gefenshi basujiba.
Shi kuwa Maimartaba hannunshi ya Waura kan tsakiyar kan Sheykh wanda tun kafin ya zauna ya tura hulanshi ya koma baya, dafa tsakiyar kanshi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gaidashi,
dan su sai yanzu suka haWu dashi tunda gari ya waye,
TsaSanin Sheykh da kullum tare suke dawowa masallaci sallan asuba daga nan kuma Wakin hutunshi suke shiga kakarsu mace ta kawo musu abin taSawa.

Bayan sun gaggaisa ne da mutanen fada, suka fita suka tafi.

Sashin kakarsu Gimbiya Aminatu suka nufa.
Basu da hijabi da sashin kakar tasu shiyasa kai tsaye suka shiga a falo, suka sameta,
Da alamun yanzu ta fitito Dan ga al'kyebba a jikinta ga kuma hadimanta a zagaye da ita.

Cikin tarin so da ?aunar Jazlaan Win nata take kallon su,
Murmushi tayi tare da cewa.
"Miskili kafi mahaukaci ban haushi, kai dai kaji abinda malam zaice kada kace zaka binciki aikin malam".

Shiru Jamil da Jalal sukayi, shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata.
Ita kuwa rausayar da kai tayi tare da cewa.
"Eh mana kaji abin da malam yace kada ka duba aikinshi, dazu na gama jin wani wa'azin ka da kayi kan falala da ni'imomin dake cikin aure, kana bayani duk maluntar mutun darajarsa bata cikaba in bashi da aure.
Sai najima wa'azin kamar da kanka kakeyi.
Meyasa ne Jabeer kayi niyar yin aure mana ka cikata nasabarka da kamalarka da martaba da darajar ka data masarautar JoWa".
Jalal ne ya mi?e tare da cewa.
"Ke in anzo gaisheki sai ?a?ale-?a?alen zance tsiya kika iya ni na tafi dan inada aikin yi".
Haratanshi tayi tare da cewa.
"Tafi daga nan mai ?ugu kamar buzuzu hegiyar masifa".
Hararanta yayi kana ya juya ya fita.
Ita kuwa Gimbiya Aminatu.
Jamil ta kalla wanda shima ya mi?e yabi bayan Jalal.

Shi kuwa Sheykh numfashin ya fesar tare da cewa.
"Maganinki ya kare koda saura?."
Da sauri tace.
"Yauwa magani ya ?are a kawo min wani".
To yace kana ya mike ya fita.

Daga bakin harabar sashin kakar tasu,
Fadawanshi ke biye dashi a baya har parking lot Winsu mai Wan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau.
Wasu tsala-tsalan motocine da a ?alla sun kai su takwas sai she?i sukeyi.

Da sauri Ado drevernshi ya buWe mushi ?ofar wata mota mai Wan karen kyau wacce bada ita ya fita jiyaba, dan ita sai ranakun jumma'a-jumma'a yake hawanta,
wannan ta yau mai kalar ruwan tokace sai she?i takeyi,
yana shiga sauran fadawanshi suka yi yun?urin shiga motocin dake jere a wurin a gefen wurin wanda dasu akeyi mishi rakiya.

Da sauri ya Waga musu hannu, cikin in in narsa da in yana saurin mgna yake fitowa yace.
"Kkku ba bari ba'a bukatar rakiya".
Da sauri suka Wan rusuna tare da haWa baki wurin cewa.
"Aje lafiya a dawo lfy Allah ya kiyaye gabanka da bayanka Sheykh".
Amin Amin yace a ta?aice kana ya shiga motar, sarkin ?ofa ya rufe mishi marfin sannan Ado yaja suka tafi.

Suna fita kai tsaye Babbar jami'ar dake cikin babban birnin ?adamaya suka nufa.


A can cikin makarantar kuwa,
Kasan cewar duk Waliban jami'ar sun san babban Doctor zai shigo yasa gaba Waya harabar asibitin dake cikin jama'ar cika da taron tsala-tsalan ?an mata ?a?an manya, duk mai matsalar lfy tana fatan ya dubata sabida ?warewarsa.

A hankali wasu ?an mata biyu suke taku a farfajiyar shiga asibitin, bisa alamu duka Wayar bata da lfy dan Wayar na rike da hannunta, kuma a hankali suke tafiya.

Cikin tausayawa Wayar ta kalli wacce ta ri?ewa hannun a hankali tace.
"Garkuwa ki daure kiyi sauri mu isa, wallahi zamu samu layi da yawa, kuma wannan Sheykh Win kasaitarsa nada tarin yawa, yanada doka da ?a'idoji da tsari, yanada tsauri kan tsare kima da darajar addininshi, daga shigar jikinki in kinyi kuskure kaWan na shigar kima wallahi bazai dubaki ba.
Shiyasa ahlul kitabi dake cikin makarantar nan suke masifar shakkarsa,
kinga gashi azahar ta kusa, kuma wallahi ko sarkin garin nanne yazo ya dubashi in dai lokacin salla yayi to tashi zaiyi ya fita ya barshi, gashi shiru-shiru da ido yake hukunta mutun".

A hankali wacce aka kira da GARKUWA tasa hannu ta gyara ni?ab Win dake fuskantar, wacce ta dace da wata kekyawar arabian gawn dake jikinta
wanda dama shigartace haka kullum sabida gudun kada wani ya ganta ya tsaida ita dan tasan duk namiji daya nuna yana sonta har lahira ake kasheshi wanda kuma duk Rugarsu akeda ya?inin Ba'ana ne dan mutunne mai masifar ba?in kishi, yasha sanar mata a kanta zai kashe kowa ba damuwarsa bane da fari duk wanda ya nuna yana sonta da bulalin shaWi yake korarshi, to yanzu duk wanda yace yana sonta sai dai a wayi gari ya rasu.
Cikin sanyin muryar dake nuna azabar da takeji, murya na rawa tace.
"Rafi'a, bazan iyaba marata ciwo kamar zata Salle, ki sakeni kije ki amsar mana foldana kafin in ?araso".
Jin haka yasa Rafi'a cewa.
"Zaki iya tahowa ke Waya?".
Kanta ta gyaWa mata a hankali.
Hakan yasa cikin sanyi ta saketa kana ta wuce cikin Hospital Win da sauri.

Dai-dai lokacin kuma motar Dr Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ta kutso kanta

5 / 72