Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   98 / 100

291K to 294K   out of 299.8K words

dakyau dakyau.

Shiryawa tayi tana saka wata doguwan riga mara nauyi ta yafo mayafi mara nauyi shima ta fito ta nufi dakin Ammi wadda taketa waya da mutanenta dake mutunci sosai da hulda dasu wainda suka hadu a nadin sarautar 'danta kuma suke shige mata sosai a yanzu kowa hulda yakeson yayi da ita sbd ya samu shiga gurinta dan matsayinta.

Mutane da yawa ta gayyata kuma a ranar suketa sauka a qasar suna isowa anjom da securities dinsu cikin farin cikin kasancewa a gurin hidimar bikin auren Sultan LEUL NUAB.

Ammi na gama waya kallanta tayi tana cewa

'Kiyi breakfast ki tafi masu shirinki suna jira sbd zaa dauki time kafin gamawa gashi mutane nata isowa kuma Kinsan ba wanda zai iya ganinki'

Dan lafewa tayi gefen Ammin tana jin itama kaman bazata iya barin Ammin ba shikenan gwara a yanzu suke yanzu yafi mata tana gaban Amminta shima yana matsayin mijinta din tafison hakan.

Maa tenya ce ta shigo ta kawo mata abinci da kanta tana zaunawa gefe ta tafara bude mata komai tana cewa taci ta shanye maganin dayake cup gashinan ta ajiye mata.

Miqewa tayi ta fice sbd tanada ayyuka da yawa a gaban,

Tana fita maa sakinah wadda itama gyara ya saka ta sauya gabaki daya ta koma tamkar ba itaba ta qara wani irin haske sosai tayi fresh tana daukan ido ta iso ta zauna gefenta tana waya da mahaifiyar Haile data kira tana mata Allah ya sanya alkhairi da fatar zaman lafiya da farin ciki me dorewa har mutuwa.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

180
Abincin taci a natse da kwanciyan hankali tana dan duba chats dinta datake yi da Neesah wadda ta isa boyem din da asubar yau jirginsu ya sauka Aleey ne yaje da kansa ya daukota ya kawota gurin leylah kafin su tashi wucewa a gobe da ita zasu iso.

Gulma take mata tana fada mata Tinda tazo bataga Sultan LEUL ba ance andena ganinsa kwata kwata kaman yana mata tanadin kansa ne.

Murmushi ne ya kubuce mata ta sake tana bawa Neesah reply da cewa "you're crazy girl"

Neesah data matsu ta iso ga Bahar din sake rubuto mata abinda yasakata dariya sosai tayi tana kasa cewa komai tausayinsa da tsananin son ganinsa na sake mamayeta.

Gama cin abincin tayi tasha ruwa da maganin da aka ajiye mata ta miqe ta fice daga dakin tana komawa sakinta ta sake wanke bakinta da mouthwash me qamshi sosai ta fito Ammi na shigowa dakin hannunta ta kama takaita inda zaa fara shiryarta.

Tana kaita ta fito sbd baqin datake dasu koina.

Shirin amarya kuma sarauniyar qasar boyem aka fara cikin wata irin nutsuwa da kulawa da kiyayewa kaman baason tabata ko tsoron yaga fatarta sbd yanda ake nuna tsantsar kulawa da kiyayewa da nuna qwarewa.

Kusan masu shirinta mutum goma ne a kanta bayan masu jiran ace su miqo wannan su miqo wancan,

Kayan da zata saka kansu dake jere a tsaye sai da aka saka masu gadinsu a tsaye kansu a qasa.

Hannuwanta da sukaji wani jan lallen daya sakata ita kanta shiga mamaki da kaunarsa a hannuwanta da kafarta da baa taba mata lalle ba tinda take a duniya kaf rayuwanta sai ayanzu ta daga hannnunta daya ta dora akan saman wuyanta ta dauki hoton hannun tareda fatar wuyan iya nan banda fuskanta ko kirjinta ta tura masa mai tsaye tana sake murmushi me kyau ta ajiye wayar.

Yana zaune a palonsa yana waya a natse sanye cikin fararen gucci marasa tsayi da suka dauke kammninsa na sultan zuwa asalin Leul dinsa na Moscow sbd ko gashin kansa a sake yake.

Shigowan sakon ya sakasa dago wayarsa daga kunnensa ya kalli screen din wayar yaga sakonta ne ya shigo dan haka ya maida wayar kunnensa a natse ya qarasa maganar da yakeyi yana taqaitawa da sallama yana katse kiran.

Cup din dayake hannunsa yafara ajiyewa a natse yana dawowa da bayansa ya jingina a natse yana bude sakon wanda yaga hoto ne.

Dannawa yayi ya bude hoton kai tsaye idanuwansa na sauka akan abinda shima bai taba tsammanin gani ba sbd baitaba ganin irin hakan ba shima dan baya hulda ko kallan komai daya danganci harkar mata shiyasa bai wani san lalle sosai ba duk da yanda dan ganinsa sama sama haka amma a tsaf haka bai taba kallansa ba.

Tsurawa hoton fararen idanuwansa yayi yanawa komai dake cikin hoton kallan tsafta da nutsuwan da babu abinda bai gani ba tsaf.

Wanu numfashi me sanyi mara sauti ko kadan ya hadiye ta cikin hancinsa zuwa maqoshinsa zuwa cikinsa yana jin dan dauke idanuwansa kadan daga kan wayar ya rintse idanuwansa ya bude a wani slow harma sun dan sauya kala zuwa wani shauqin soyayyar macen dayake fatar ya iya control kansa akanta idan ya hadu da ita da kuma rayuwan da zasuyi tare daga yanzu har tsufa da mutuwa.

Yatsun hannunta da suka sauka akan fatar wuyanta dake daukan idanuwa sbd haske da lafiya da glowing ya kalla yana gangaro da idanuwansa zuwa wuyan dana da dauka da gangan ta turo masa sbd sanin yana daya daga cikin gurin dake kunnasa.

Dauke idanuwansa yayi daga wayar tsawon seconds kafin ya rubuta mata kalmomin da itama suna isa wayarta dakatar da masu kwalliyan tayi tana daukan wayarta a natse ta bude tana duba abinda ya rubuto.

"Ths is murder,you know???
Duk abinda zai biyo baya karki manta kece kika turo wannan sakon da hannunki Queen Ayanah Bahar."

Murmushi me tsananin kyau da sauti ta sake tana tura masa wani hoton da dayan hannunta me lallan yake akan Wuyanta gurin kirjinta ta sama da sama saman yadan fito.

Tana tura sakon ta kashe wayarta gabaki daya tana ajiyewa fuskanta cikeda murmushi dan bazata bude wayarta ba sai kuma goben.

Baa gama shirinta bai kusan kusan yamma liss
Kafin qarasa saka mata kayan da zata saka saida tayi sallolinta tukuna aka qarasa shiryata cikin shirin da babu wanda bazai iya kasa dauke idanuwansa akanta ba sbd shigar maroon da golden akai mata ta wata fitinanniyar doguwan rigar da kudin da aka zubar gurin bada yinta ya wuce lisaafi dan kuwa dukiyar gasken gaske aka kashe gurin iya suturar kafin asalin adon zinari da diamonds din dake jikin dan kuwa hatta sarkar kafafunta adon zinarin daban yake komai nata a daban da tarihin baya yake zuwa dan kuwa al'adun masarauta biyu qasa biyu aka hade mata sai adon ya fiddota a wata kyakkyawar halittar daban da a lokacinda ta fito tsaron da aka ware sbd ita kadai ko ita sai dataji tana tsoron kanta da jin sanyin jikin itace yau a wannan rayuwan da daga ita hai mahaifinta basu taba hangowa ko kwatantawa kansu ba.

A babban hall din taron dayakeda hawa biyu na cikin babbar masarautar anjom ghaz din da akaiwa wani decoration da shima masu aikinsa daga boyem aka aikosu zaayi taron dan haka dukkanin yan media da gidajen television suna ciki da wajen gurin a jere a tsare ana jiran fitowan queen Ayanah Bahar kaman yanda mijinta yake ambatarta da cikakken sunanta.

Ko data fito su Ammi da maa dukansu sun shirya sun fito cikin nasu shirin da kowa koina ka duba gold ne me tsayi da fadi da mara tsayi ke haskawa a wuya da hannuwa da kan mutane da jikinsu musamman sauran yan Al'ardarsu da basa rufe kai gabaki daya sarkokin zinarin ne akan gashinsu anyi ado dashi a cikin gashinsu me tsayi da daukan ido.

Ammi da maa sakinah na sauke idanuwansu akanta hawaye ne suka zubo musu a lokaci daya da basusan ma hakan ya faru ba itama hawayen ne suka taho mata ta qaraso cikin wasu original jimmy choo heels da suke cikin kafafunta da riga ta rufe gabaki daya tana ja da qasa ta rungumesu su biyun a tare tana jin tamkar ta rungume mahaifinta datake jin kaman yana tareda ita matiqar tana tareda su biyun nan.

Flashers ne tako ina ke tashi kowa na jin kaman zai zube qasa gabanta sbd rawan jiki da wani irin kwarjini da yabawa tareda tsantsar jin girma da daraja gareta sbd ta tabbata dai itace mace mafi darajar a tsakanin boyem da anjom sbd anan dinma anjom itace asalin wadda take da karagar mulkin Anjom a yanxu sedai auren daya kaita wata qasar ya saka ayanah ghaz ce takeda ikon karagar a yanzu.

Walimar dare ce dan haka ko kafin a gama photoshoot da saura su daren yayi take aka fara hidimar wadda ta saka anjom dukan tsit sbd ana can ana bikin da baa taba kamarsa ba a qasar.

Tarin tsaro da jamian tsaro dake garin ranar basada iyaka sbd matan manyan qasashen duniya dake garin gurin halartar wannan gagaruman walimar.

Koda aka kammala walimar dare ta tsala sosai dan haka kai tsaye dakinta ta wuce bayinta su uku na baiye da ita sai babba shugabar makeup artist din da suka shiryata wadda zata rabata da komai na jikinta.

Zaunawa tayi a matiqar gajiye tana dan rufe ido da fidda numfashi me dumi tana jin hatta yunwa na damun babyn dake cikinta.

Fara zare mata komai akai daya bayan daya har aka kammala ta saka wipes cikin nutsuwa da kulawa tana goge mata fuskanta.

Koda aka gama komai salmah ta gama hada mata komai na ruwan wankanta ta fito daga bathroom din.

Miqewa tayi ta nufa tashige tana gajiyarta na qaruwa.

Ruwan zafi ne da qamshi suna fidda hayaqi me qamshi ta isa ta shige tana sauke ajiyan zuciya.

Kafin ta fito wankan sun sake gyara dakin da komai da aka cire harma sun fidda mata kayan baccin da zata saka da komai sun ajiye a jere inda ake aje mata sun fice.

Naimah ce ta dawo dauke da abinci marasa nauyi da tea da fruits da ruwa ta jere mata akan table na dakin ta fice.

Shiryawa tayi tana zuwa ta zauna taci ta koshi tukuna tayi sallah ta koma toilet tayo brush ta dawo ta sake tada sallar nafila sbd neman dukkanin alkhairi da kasancewa cikin farin da rayuwa me albarka ga rayuwar da zata shiga daga goben a gidan aurenta tareda fata da adduar samun zuria me albarka.

Sai gap da asuba ta gama ta dan kwanta sbd baccin dayake cin idanuwanta sosai kaman zasu kone sbd yajin bacci.

A cikin tsakiyar daren jirgin da sultan NUAB LEUL boyem yake ciki ya sauka a qasar tareda dukkanin tawagarsa da wazirinsa shim da tasa tawagar securities din dan haka manyan motocin da suka amsa sunansu motoci ne suke a jere suna jiran saukansa kodaya sauka ba bata lokaci suka bar airport din ba maganar tsayawa masauki kai tsaye hanyar zuwa garin anjom dake da nisa suka dauka a jere kaman duniyar zasu bari sbd wani irin gudu me lafiya da ake shimfidawa.

Koda gari ya waye da wuri a ranar kowa dake masarautar da wajenta ya tashi dan daurin auren da zaayi a ranar karfe goma sha biyun rana hakama baqi kashi kashi sun sauka qasar suna kan hanyar isowa anjom.

Bahar ce kadai bata farkaba hakama ba wanda ya isa ya tadata musamman sbd juna biyun dake jikinta kwata kwata ma ta guraren dakinta hayaniya ta dauke tsaf dan kada ma dameta.

Bata farka ba sai guraren goma da rabi wanda yayi daidai da isowan Motocin Sultan LEUL NUAB da kaf yan gari suka fito dan tarbansa da wata irin bada girmamawa.

Tin daga farkon garin har zuwa masaurautar anjom ghaz aka zuba masa securities masu karfin gaske.

Isowansa tare take da qasu manyan manyan bakin da suka iso daga wata qasar hakama shima tareda kusan dukkanin manyan fada tsoffi ya iso.

Dan haka kafin ya iso asalin cikin garin tini sha daya harta buga dan haka gurin daurin auren ya gama cika batsil.

Tin daga nesa securities suka miqe gabaki daya suna sake bawa koina tsaro tareda wangale gate motocinsa suka ringa zuwa da gudu suna shigewa gate din daya bayan daya suna gama shigewa aka rufe gate din ruf.

Mahaifinsa ne kansa da ango kadir da sauran manyan mutanen dake nan suka tarbesa shi da waxiri cikin farin cikin isowansu kafin suka dunguma ciki.

Bai wani bata lokaci a cikinsu ya wuce ciki bangarensa wanda tini aleey ya isa aka gyra komai.

Hutawan da batafi ta minti ashirin ba yayi yayi wanka cikin nutsuwa da kwanciyan hankali kafin ya fito ya shirya cikin shigar daurin auren da take ya fito asalin Sultan me mulkin qasashe ba guda ba a hannunsa ya fito shima aleey tini ya shirya hakama su keelah suka wuce gurin daurin auren da kowa ya gama kammala shi kadai ake jiran fitowansa a daura.

Yana isowa yan jaridu da media suka fara fesho flashers nasu ana wata irin busa da kirarin da ko masu sauraro tashi tsigar jikinsu tafara yi suna zube masa kowa yayi qasa da kansa.

Zaunawa yayi wanda take aka fara kokarin daura auren da baa dauki mintina ba take aka daurasa cikin yarda da amincin Allah.
#MAMUH
09033181070


HAYATEEM
Mamuhgee

181
Ana gama daurin auren nan ma wata hidimar aka sake shiga ta manya anata taya juna murna da taya NUAB din murna sai kuma ango Kadir da shima yake ciki tsananin farin cikin ranar dan kuwa baida wata matar ko daya tinda mahaifiyar keelah ta rasu bai sake wani auren ba sai yanzu.

Taron daurin auren bai watse ba sai kusan karfe hudu dan haka ana yin sallar laasar a babban masalaccin masarautar manyan baqi suka fara barin anjom suna wucewa da motoci da securities dinsu sbd isa babban birnin qasar su kwana acan tukuna su sake bin jirgi su koma.

Acan cikin gida babu wanda ya samu ganin sultan NUAB daya iso ranar bare sultan yasar shima dan kuwa basu gama sallama da baqi ba kwata kwata tsaf sai bayan ishai sbd hatta manyan boyem duka juyawa akai dasu a ranar zuwa babban birnin qasar washe gari zasu bi jirgi su koma sbd komawa boyem da aka baro babu manya duka an kwashe ana nan anjom.

Bangarensa ya nufa kai tsaye sbd hutawa yake buqata dakyau gashi dare yayi a ciki akwai mata da yawa har lokacin sunata shirin kai Maa sakinah bangarenta a daren wadda Su Ammi suka zaunar da ita itada Bahar akai musu hudubar aure daidai gwargwado kafin aka bawa Anty Indo Batik dama itada Anty maryam suka musu huduba sosai musamman Bahar tsawon lokaci kafin daga nan tenya tayi aikinta data rayu a cikinsa na kai matan sarauta tiraka wannan karan itada Zuhrah ne suka kai sakinah har bangarenta da mijinta dayake tamkar wata aljannar duniya da bayinta guda goma.

Suna baro bangaren ba jimawa karfe goma sha dayan dare ta buga ango kadir ya shigo bangaren yana waya cikin nutsuwa harya shigo tukuna ya kashe yana shaqar wani qamshi me sanyin gaske da ratsa zuciyar datai shekaru babu komai a cikinta.

Numfashi da ajiyan zuciya ya sauke lokaci daya yana qarasa takowa tsakiyar palon inda Sakinah din ke zaune cikin adon daya dauki idanuwansa ya sake sauke ajiyan zuciya me sanyi yana zaunawa gefenta a natse ya dago idanuwansa ya kalleta yana bude baki da kamala ya ambaci sunanta da sautin muryansa ya ratsa kunnuwanta sbd kusa da itan daya zauna ta dago idanuwanta da suka ji kyakkyawar gazal na ido ta saukesu akansa ta kallesa a hankali take ya sake sauke ajiyan zuciya a karo na kusan biyar ko shida ma daga shigowansa yana miqawa Allah dukkanin godiyansa ga wannan kyakkyawan tanadin da akai masa zuwa yanzu.

Hannunsa ya daga ahankali ya dora akan nata fatarsu ta hadu take taji yarr sbd abu ne dabai taba faruwa da itaba haduwan jikin kowane da namiji da nata dan haka dan janyewa tayi tana gyara zamanta shima sake dora hannunsa yayi akan bayan hannunta zata sake janyewa ya riqe hannun gabaki daya cikin nutsuwa da kulawa tareda bude baki yana cewa suna buqatan yin nafilar neman alkhairi da albarka a cikin wannan auren.

Miqewa yayi yana riqe da hannunta ya jata zuwa hanyar dakinsa dan yi acan.


****Bahar da Neesah kuwa suna daki suma tana sake kwantar mata da hankali sbd jikinta da yayi sanyi sosai itama dan da sassafe zasu tafi a yanda taji Ammi tana fada.

Jin tayi kaman bazata iya tafiyar ba ayau tana son ya sake qara mata kwanaki amma gashi ko ganinsa bataiba hakama takasa kiransa a waya jin takeyi ma fargaban haduwa dashi takeyi dan haka tayi sanyi sosai taxo daki ta kwanta shiru.

Ammi sanyin jikin rabuwa da yarta takeyi amma kuma tana farin cikin shedar da wannan ranar da Allah ita kadai yace zata gani banda Abaas da mahaifiyar Bahar din wadda basu taba saninta ba.

Washe gari karfe 7 na safe dukkanin shirin tafiyarsu Aleey yayi no delay sbd jirginsu na Russia karfe taran dare zai tashi daga qasar dan haka dole suna buqatan isa kafin time din da a qalla ko zasu isa sai ana magrib.

Shi kansa NUAB din bai fitoba sai daya gama baccinsa ya samu dukkanin isashen hutun dayake buqata tukuna ya fito yayi breakfast dinsa da aka jere su akan table fiyeda kala uku tukuna ya fito a natse sanye da black qananun kayan original Dior da black D&G shades ya nufi cikin gidan inda tini kowa ya watse sbd shigowan da zaiyi.

A babban palon Ammin ya sameta zaune itada tenya da zuhrah dan haka zaunawa yayi a natse suka gaisa yana musu barka gama taro lfy.

Babu wani dogon bata lokaci nasiha akan Amanar yarsu da suka taru suka basu sukai masa kafin yayi godiya da yar tasu da suka basa yai tukuna yayi sallama ya fice zuwa ganawa da sultan tukuna kafin a fito da bahar din wadda zuwa lokacin ta fara kuka sosai na rabuwa da Amminta da maa sakinarta.

Rungumeta Ammi tayi tana sake rarrashinta da fada mata magana me saka nutsuwa da kwantar da hankali a kunne kafin zuhrah ma ta rungumeta tana sumbatar gefen fuskanta tukuna da kanta ta sakata a hannun sbd yin aikinta na kaita.

Neesah ce da leylah a biye da ita hannunta n cikin na tenya aka fice da ita tana kuka mara sauti sosai.

Bangaren maa sakinah aka kaita itama rungumeta tayi daqyar aka cireta daga jikin sakinar aka fito da ita daga nan gurin sulta aka kaita ta gaidasa shima yayi mata nasihar tukuna suka fito.

Motocin tafiyarsu suna jere ras a harabar gidan ita kadai ake jira dan kuwa bar mai boyem din yana zaune yana jiranta a cikin motar hankali kwance.

Sanye take da daguwar rigar Turkish abaya Mai tsananin tsada sbd yanda har

98 / 100