sakawa da batada su da kuma ma koda tanada su Maa tasan tayaya zatai shigar da batasan me zata fada ba Akan hakan dan haka saita barta itama tana saka uniform kamar su Salmah wainda da kanta taje ta karbo mata su Kala biyar sabbi daidai jikinta,
Ita kanta Bahar din tafi jin nutsuwar tsayawa ga matsayin dasu Salmah suke dashi sbd tafi tafi son ta kasance a matsayin da shine ya kamace ya kuma zai barta tayi rayuwa qasa qasa batareda shiga wata daula ko shiga mutanen da bazata iya kallan kanta a cikinsu ba dan haka kaman yanda Wanda ya kawosu ya buqaci rashinta da rashin bayyanar da ita ga wadda itace takeda alaqa sa mahaifinta itama sai taji tafi kowa ma buqatar rayuwarta a cikin bayi kuma a matsayinsu hakama bata jin tana buqatar kowa a rayuwarta tinda ta Riga ta rasa mahaifinta sha shine kowa a rayuwarta hakama kwata kwata sai batajin kowannensu a cikin ranta da zata ma iya jin feelings na alaqa komai a tsakaninsu.
Maa ce kadai take ji a zuciya da rayuwarta harma tana jin ahankali tana samun kauna ta uwa mace da Allah bai taba bata ba musamman da haryanxu data zabi zamowa mai aiki a cikin bayi Maa bata taba Dena tattali da bata kulawan da daace ba a cikin duhu da kunci ta taso ba da babu abinda zai Haba gatan lalatata sbd hatta gashinta Maa ce take wanke mata shi da wasu irin tsaftattun kayan wanke kai da oils na gashi na al’adar qasar masu kyau da qara duhu da tsayin gashi tareda santsinsa Wanda zaku iya samun irinsa sak a gurin (SHUWA INCENSE AND MORE 07042293384/09118783317) wainda suke fiddo mata kyau da tsayin gashinta fiyeda baya sbd rashin gyara,
Hakama bangaren lafiyar fatarta ma kayan wanka na musamman na matan Masarautar Maa dinta ta tanadar mata wainda dasu take wanka duk da bawai na musamman bane amma suna kawo sauyi sosai a fatarta da kwata kwata a baya bata Wani samun duka wainnan gyaran tinda ba sune a gaban rayuwarta data mahaifinta ba.
Hakama Maa bata barinta ficewa Ayyuka sai ta tsaya sunyi breakfast tare kafin tayi wanka ta saka uniform dinta ta fice gurinsu Salmah.
Yauma kamar kullum dakin ta gama gyara wa a natse ta kunna ac salma ta koya mata ta kunna qamshin da ake kunnawa me sanyi da nutsuwa kafin ta zare kayan jikinta na bacci wata doguwar rigar Maa dince datai mata yawa sosai da ita yake bacci koyaushe dan haka zarewa tayi ta daura babban towel din da Maa ta tabbatar mata da sune nata kusan Kala biyar.
Bathroom din dakin ta shige ahankali tareda rufo kofar tana isa inda brush dinta yake tafara yin brush din da brush me tsadar da suke jere a toilet din kusan guda biyar tana gamawa ta sake wanke bakinta da harshenta da mint mouthwash me qamshin tukuna ta isa ahankali ta shige ruwan Zafin dake cike da bathtub suna fidda qamshi mara tashi sosai.
Wankan kusan mintina kalilan tayi ta fito ta goge jikinta iya mai kadai ta shafa sai qamshi a jikinta ta miqe ta saka uniform dinta a natse kaman koyaushe,
Salmah ce ta kawo breakfast din data saba ta ajiye a kan table ta dauko shimfidar cin abinci ta shimfida Akan lafiyayyar carpet din tsakiyar dakin tukuna ta saukar da abincin ta jera ta fice.
Abincin sukaci Maa na sake fadawa Bahar ta kula da kanta sosai kada taji rauni a gurin aiki hakama ta ringa cin abinci sosai.
Dago kyawawan idanuwanta tayi ta kalli Maa din cikeda girmamawa da kauna tareda shaquwa ta Gyada kai tana karban cup din madara me Zafin datake kokarin bata a baki ta amsa takai bakinta tafara sha ahankali ta bude Baki tace
‘Maa Nagode,Abaa ma ya gode’
Murmushi Maa din tayi a duk lokacinda Bahar zatai godia sai tace Abaa dinta shima ya gode,
Tissue ta dauka tana gogewa Bahar din baki inda madarar ta bata a gefen bakinta tana cewa
‘Nima na gode wa Abaa daya haifo mun Ayanaah Bahar’
Sakewa fuskar Bahar din tayi tareda sakin Wani sanyayyan murmushi me sanyi tace
‘Hadda Maama Dina amma’
Dariya me sauti Maa sakinah tace sake tana cewa
‘To ai daman da ita nake nufi tinda itace ma ta kawo mana Bahar din duniya’
Wani sanyi Bahar taji ya ratsata a yanzu datake irin wainnan maganganun da Wani a rayuwarta dan haka Wani murmushin ta kuma sakewa tana qarasa shanye madararta zata miqe Maa ta riqe hannunta ta sake goge mata bakinta tana sake cewa
‘Bahar ki kula sosai ki kiyaye masarautar nan akwai tsanani sosai a cikinta da hadari dan haka ki kula sosai kinji’
Gyada kai tayi tareda daukan tissue itama ta gogewa Maa din gefen Fuska tukuna ta miqe ta tattara Kayan ta fice Maa na Binta da ido tana jin inama zaa bata dama ta tafiyarta da Bahar suje inda babu takura su shimfida rayuwar da zata bawa Bahar kauna fiyeda wadda zata bata anan sbd anan din karkashin dokoki da tsanani me karfi suke.
Tana fitowa kai tsaye kitchen din bangaren nasu ta nufa da Kayan tana shigowa dukkaninsu suka gaidata duk da wasu sun girmeta wasu kuma iyakacinsu shekarunta duka duka su shida ne sai ita ta bakwai kuma babu qyashi ko baqin ciki bare fitinar komai a tsakaninsu dukan dan hakan ne suke ciki kwanciyan hankali da hidimar su ba damuwan komai,
Gaidasu tayi itama batareda ta amsa tasu gaisuwan ba sbd batasan tayaya zata amsa ba tinda matsayinsu daya su dukan.
Ajiye Kayan hannunta tayi a cikin sink tana kunna ruwa tafara wankesu a hankali tareda Salmah data matso tana tayata tana bata Wani labarin a hankali fuskarta a sake da dariya ita kuwa tana saurarenta a natse fuskarta ma na dan sakewa da abinda take saurare daga bakin Salmah din.
Suna gama wanke Kayan tas Sauran suka fice zuwa ayyukan gyare gyaren Paluka da Sauran dakunan Wishmah harma dana Tenya dik da basa nan baa taba tsallake gyaran dakuna da toilets dinsu ba,
Su Bahar kuwa su uku aka Bari kitchen din suna Dora girki Wanda a yanzu daga su sai Maa ne ake wa.
Salmah da Naima ne sukeda qwarewa a aikin abincin dan haka Bahar datake koya haryanzu a gurinsu iyakacinta yanka musu abubuwa da niqawa idan ance tayi sbd sun koya mata abubuwa da dama sosai kuma tana iyawa din tunda batada iyawa Akan komai.
Girkin sukeyi Salmah da naima na kokarin bata Labaran masarautar da mutanen dake cikinta wainda Sam wasu abubuwan jinsu kadai takeyi bata Wani gane wa dan ita tafi gane wa koyan abinda yake gabanta.
Simple abinci sukai kusan Kala uku Wanda zaa ci har dare sbd Bayan girkin wanki zasu tafi cak bangaren laundry na masarautar.
Koda suka gama suka kai komai a dining suka jere tareda sake gyara koina qamshi da sanyi tareda tsit kawai ke tashi a bangaren,
Kitchen suka sake gyara wa tamkar baa yi aikin komai a cikinsa ba sukaci abinci a dakinsu dake bangaren suka gama hadda ita suka fito suka sake tabbatarda tsaftar koina tukuna suka fiddo kayan wankin dake bangaren tsaf suka fice dasu zuwa laundry su hudu suka bar mutum uku sbd baa tafi tafi duka abar bangaren ba masu hidima ko daya.
Hadda ita Bahar din suka fito wadda yaune Karan farko data fara fitowa daga bangaren dan haka a gefen Salmah take tana kasa sakewa sosai sbd batada sabo haryanzu na mutane sosai Bayan su da shima sai ahankali ta dan iya sabuwa da sakewa a cikinsu dan haka yanzu data fito takejin yanayi na rashin son rabuwa da mutane sosai.
Salmah ce yake tura babban basket me kafafun da suka turo wankin a ciki suna tafiya cikeda nutsuwa da Kamun kai suna yar fira sama sama.
Tafiya me tazara ce daga bangaren zuwa inda laundry yake dan haka tafiya tafiyarsu da ba cikin gaggawa da rawar jiki sukeyinta ba sai batai tsayiba.
Suna isa babban guri ne dayake tsare da gararen wanki da hannu da kuma washing machines da gurin goge kaya dama gurin da zaka shirya su aleda Bayan gogewan da inda ma ake tirara kaya da qamshi kafin gogewa ko Bayan gogewan ma,
Gurin Bahar ta kalla tana sake dan dawo da kallanta kan Salmah dake nuna mata inda suka nufa,
Wankin hannu zasuyi duk babu mutane da yawa sosai sbd kowace bangaren dake masarautar na mata da imebeti da ‘yaya da manyan Masarauta dake cikin masarautar anan ake tahowa Ayi masu wanki da guga.
Fara wankin sukai Wanda Itama Bahar ta saka hannu duk da shima ba wani iyawa tayi sosai ba sbd koda suke a cikin qunci mahaifinta ne me mata wanki daga baya da ciwo ya hanasa kuma cikin Yaransa na fadar ne ke mata sai wasu lokutan takeyi da kanta.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
73
Sai yamma sosai Ana gap da magrib suka gama komai suka dawo komai an wanke an gode tareda tirara wa da qamshi me dadi hatta bedsheets da Sauran abubuwan an wanke an goge an shiryo a rufe cikin keda me kyau,
Fitowa sukai suka hanyar komawa Bahar dake gefen Salmah tana rungume da hannuwanta ta dan Kama jikinta a natse sbd Wani irin sanyi dayake ratsata na wankin datai me dan wahalar da bata saba da ita ba Sam sbd qunci ne kadai a rayuwarta Banda wahala batasanta ba sam.
Yanda take jin sanyin sosai ya sake sakata dan sake Kama jikinta a natse cikin sanyi batareda ta furta ba kokuma barin a gane sanyin takeji sbd baida kowane amfani tinda sabuwar rayuwar data samu kanta ne a ciki daurewa kawai ne zatai koma menene zai shiga gabanta ta Fuskancesa ta amshesa.
Suna doso hanyar isa bangarensu na wishmah da Sauran matan sultan din bayin dake hanyar suka fara sauke kansu a hankali cikin tsananin girmamawa a kuma lokacin suma taga su Salmah na matsa wa baya suka rabe tareda tsayawa cak suna yin qasa da kansu cikeda girmamawan da hatta gangar jikinsu na nuna hakan dan haka itama a natse taja Bayan tareda Kaucewa hanya amma ta kasa sunkuyar da kan nata duk da bawai ta damu da son gani ko sanin waye ake bawa girman ba kawo tayi ne sbd yan uwanta sunyi.
Qamshin ASIM ne ya doso gurin yana ratsa hancinsu daya sakasu sake yin qasa da kansu sosai,
ASIM daya fito daga bangaren mahaifiyarsa zuciyarsa na Wani irin zafi da baqin cikin labarin dawowan Ayanah ghaz daya samesu tareta sultan Wanda sukeda cikakkiyar tabbacin Ayanah ghaz ta dawo masarautar to tabbas NUAB ya gama dawowa sbd a daidai wannan lokacin bazai taba barin mahaifiyarsa ba.
Kokarin ficewa daga hanyar yakeyi idanuwansa sun sauya yanayi sbd baqin ciki me tsananin dayake ransa,
Tin kafin ya qaraso idanuwansa dake cikin fushi suka sauka Akan kyakkyawar fuskarta da bata sauke ba amman bashi ko hanyar daya fitoba take kallo hanyar inda zasu nufa take kalla har lokacin hannuwanta na riqe da kafadunta sbd sanyin dayake sake ratsata sosai ta matsu ta koma ko kitchen ne ta zauna dumin dayake cikinsa ya dan ratsata sbd koina Bayan kitchen a bangaren ac ne dashi kuma sanyi ze qara mata sosai.
Kafeta da idanunwansa yayi yana qarasa isowa inda suke zai gifta su amma idanuwan nasa sun kasa daukewa daga gareta yana mata kallan tsaftar dabai mata ba a ranar farko daya fara sakata idanwansa,
Uniform din dasuke jikinta yabi da kallo a cikin nutsuwa da bada dukkanin lissafin kwakwalwansa datake sakawa zuciyarsa Wani irin yanayin dayaji bacin rai da fushinsa yana sauka ahankali batareda yasan meya ke shirin faruwa dashi ba sbd wannan fuskar itace take yawo a cikin Kansa da zuciyarsa tin ranar daya ganta din bai sake ganinta ba sai yau din,
Juyo da idanuwanta tayi daidai yana kawowa gap da ita idanuwanta suka sauka akansa kallo daya tayi masa ta dauke idanuwan nata sbd kasa iya cigaba da kallansa sbd Wani irin kallan dayake mata da dukkanin imaninsa da zuciyarsa.
Gifta su yayi zai wuce sai kuma kafafuwansa suka dakata sbd zuciyarsa data kasa hakura din ta tafi batareda ta samu abinda takejin tana buqata ba,
Bude baki yayi batareda ya juyoba da muryansa mai iko da mulki a cikinta yace
‘Bayin wane bangaren ne??
Sake qasa da kai sukai cikin girmamawa da ladabi Naimah tace
‘Bangaren wishmah’
Shiru yayi Wani abu ya sake sokar zuciyarsa ya juyo a natse ya sake saukar da idanuwansa Akan Bahar din wannan Karan yana tabbatarda zuciyarsa da kowace macen duniya bata taba shigaba ko a mafarkinsa baiwar take shiga ahankali kuma shiga me karfin gaske da kaifi,
Dauke idanuwansa yayi daga kan Bahar din wadda har lokacin bata dago ta kallesa ba Wanda hakan ne yaji ya sake kashesa akanta dan kuwa babu macen da rayuwarsa kaf ya hadu da ita data iya nuna darajar kanta fiyeda matsayin dashi yakeda shi na matsayin me mulkin BOYEM ta gobe ba shakka ba fargaba kamar ma batasan matsayin nasa ba da karfin da Masarautar take dashi a duniya ba.
Salman ne dayake bayansa ya qaraso gurinsu ya kalli naimah datai magana yace su fadi sunayensu daya bayan daya.
Ahankali suka ringa fadar sunayen nasu har zuwa kan Bahar din wadda itama kai tsaye ta bude baki a natse cikin tsananin sanyi da nutsuwarta ta furta sunanta ‘BAHAR’
Kafe idanuwansa yayi a fuskarta da bakinta daya fidda sautin sunan nata,
Baice komaiba Juyawa yayi yabar gurin sunan na Zaunawa daram a cikin zuciyarsa datake jin kota wane halin yana buqatarta a kusa dashi a matsayi da daman da zai iya komai dan tabbatarda da hakan,
Yana barin gurin suka Juyawa sukai dan qarasawa batareda kawo tinanin komai a ransu ba sbd babu ma Wanda ya dago a cikinsu bare su san yama kalli wata a cikinsu.
Suna isa Bahar dakin Maa ta isa ta wuceta a palo tana waya
Baya tsaya ba bathroom a nufa ta fara saka kafafunta a cikin ruwan Zafi da hannuwanta na tsawon mintina kafin tayi alwala ta fito ta sauya kaya ta tada sallah.
Tana gamawa safa ta saka a kafar tata a lokacin maa ta shigo ta zauna suna dan magana har akai ishai tana sallah apple biyu taci kawai ta kwanta sbd kaman zazzabi takeji.
******Washe gari da safe Bayan sun gama aikinsu suna kokarin girkin rana sako ya iso daga bangaren Li’ul ASIM An sauya bayi uku dake bangaren zuwa bangarensa ankawo wasu sabbi.
Da tsananin mamaki me girman gaske Maa sakinah ta amsa sakon tana jin damuwa da zullumin hakan sosai amma kuma batada ikon cewa Aa sam kokuma tambayar dalili sbd ya isa yama wuce dan haka Salmah da Naimah ne sai Bahar din wadda Maa sakina ta sake shiga tsoro da tashin hankali sosai da sunanta ya fito a cikin su ukun amma kuma batada damar cewa komai sbd yin maganar nada matiqar hadarin dazai fidda baamasan Bahar ta shigo masarautar ba ganin dasu Salmah ne sai ta dan ji sassauci kuma sbd Bahar da bazata iya rabuwa itaba koda mafarki ya sakata barin su a dakinsu ja bangaren sukuma sabbin bayin zasu ringa komawa dakinsu na bangaren bayi suna kwana su kuma su Bahar aiki kawai zasuyi acan su dawo.
Wannan shine babban abinda take tsoro da tsananin shakka a zamanta da Bahar masarautar BOYEM din dan kuwa matiqar zasu zauna zatai rayuwa ne dole a matsayin baiwa Wanda hakan shine mafi girman masifar da zasu iya shiga sbd abubuwa da dama da zasu iya biyowa ta kanta tinda baiwa ce kuma batada ikon cewa aa ko tambayar dalilin hakan dan haka a Karan farko na rayuwarta taji rayuwa a Wani gurin daban yana bata shiga ranta sbd tafiya da Bahar ko dan bata dukkanin rayuwar data kamata batareda ta shiga masifar mulkin Masarautar BOYEM ba dan haka kawai taji ta matsu NUAB ya dawo ko zai San abinda yake faruwa ya fada mata abin yi dik da taga ya manta tareda rufe maganar auren a zahirin rayuwarsa da Kansa da auren tin farko bai shiga bama.
Bahar bata damu da aikin da aka sauya musu ba sbd bawai gurine dazai rabata da Maa ba zata ringa zuwa ne suna dawowa kuma tana tareda su Salmah koina dan haka babu damuwa ko tashin hankalin a ranta.
Washe gari da sassafe suka shirya cikin uniform dinsu suka tafi babban bangaren Li’ul Asim Wanda Ayau babu inda zai iya fita hutawa zaiyi daga masifu dasuke cukuikuye da rayuwarsa wadda tinda ya taso cikin bacin rai da baqin ciki yake a kullum sbd kasa samun abinda tin kafin a haifesa akeson ya samu dan haka koyaushe baida rayuwar Kansa da farin cikin Kansa sai baqin ciki da bacin rai Bayan bai rasa komai ba n rayuwa da jin dadin rayuwa.
Suna isowa kai tsaye ayyuka suka fara tin daga gyara da girki tareda hada wanki da Sauran manyan ayyukan da sune daily rayuwarsu kullum.
Bahar a natse take aikinta Wanda yake gyaran asalin palonsa na qurya kuma yana Zaune dik aikin datake yi yana kallanta cikin kasalar da baisan inda ta fitoba dan kuwa nutsuwa da Wani wasu feelings na samarwa zuciya sukuni yakeji suna shigarsa wainda bai taba saninsu a rayuwarsa ba.
Lumshe idanuwansa yayi tareda jinginar da bayansa jikin lafiyayye kujeran palon nasa yana jin Kansa na warware da sakewa daga tarin baqin ciki da Zafin dayake cikin zuciyarsa da Kansa ma yana jin yanayin dayake shigarsa yana masa dadi da basa sukuni.
Babu kalma ko daya data fita daga bakinsa yana Zaune a natse cikin kwanciyan hankali har ta gama aikin ta fice batareda itama ta furta komai ba ta fice.
Ko data fice bai saniba sbd Nisan da yayi a cikin wata nutsuwar data saka komai nasa warware dan haka sai Bayan tsawon lokaci ma yasan ta fice.
Numfashi ya fitar me sanyin gaske tareda Wani murmushi me tsananin kyau yana sake tabbatarda yana buqatarta a rayuwarsa.
Wuni sukai a bangaren suna aiki Wanda hatta abincin da zaici sune sukai serving nasa kuma hakan ya basa appetite din dayaji abinci sosai.
A Karan farko a tarihin farko na rayuwarsa da ya waye har rana ta fadi batareda ya fita koinaba ciki hadda fita gaida mahaifiyarsa Wanda mamakin hakan ya saka queen haile shiga damuwa da zullumin ko baida lafiya ne dan haka ta ringa kiransa amma wayoyinsa duka kashe.
Su Bahar kuwa suna komawa babu wata gajiya gurin Maa ta isa tayi dik abinda