Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   62 / 100

183K to 186K   out of 299.8K words

a dakinta dake ta cikin hanyar kitchen dan madaidaici mara girma sosai.

Maa sakinah ce ta fito itama tana wayar da Zuhrah tana sanar da ita sai yanzu suka samu kunna wayoyinsu suka fada wani zancen tana tambayar leylah wadda tin jiyan take jin duniyarta ta dawo sabuwa sbd Bahar ta tafi NUAB kuma yana nan tareda su a boyem.

Shuraim ma nutsuwan hakan yaji ya samu sosai fiyeda yanda ma ya tsammata dan kuwa tafiyar bahar ma ta saukaka musu komai dan haka shima shirin komawa Oxford kawai yaji yana son farawa sbd rayuwa a can.

Aysha ce ta hada dafaffiyar madara da zuma da tea spices masu kyau da qamshi ta jera a tray ta nufi dakin Ammi dasu,

Ko data kai Ammin na zaune a kan lafiyayyan sofar dakinta tana waya a natse cikin kwanciyan hankali,

Da NUAB take waya dan haka Aysha ajiye kayan tayi akan table din dayake gaban Ammin ta saka hannu a natse ta zuba mata ta ajiye a gabanta ta juya ta fice batareda bada kowace irin sound da zata damu wayar ta Ammin ba.

Kitchen ta koma ta sake hadowa ta kawowa su Maa dake palon kafin ta koma ta sake hada ta Bahar daban ta nufi dakinta tana fatar ta tashi.

Bahar din bata tashi ba dan haka ta juya dashi sbd dole idan ta tashi sai ansake dumama sa.

Tana fita bahar ta farka ta miqe itama toilet tafara fadawa tayo wanka ta fito tana fidda qamshin wani tsadadden shower gel dasu bodyscrub da set set na skin routine dake jere a toilet din kaman ansan nan din zata zauna an jere komai da aka tanada dan ita a gurin.

A natse ta shirya cikin doguwan riga mara nauyi har qasa ta fito tana jin gajiyanta ta sake gabaki daya,

Gaida su Maa tayi cikeda girmamawa da kulawa kafin ta nufi dakin Amminta wadda har lokacin take waya.

Tana shigowa Kallanta Ammin tayi fuskarta na cikewa da farin ciki ta miqa mata hannunta daya ta taho ta kama tana zaunawa gefenta kusan cikin jikinta sosai.

Muryansa taji ahankali ta ratsa kunnuwansa a daidai lokacin dayake sanar da Ammin baida ranar da zasu gansa sbd bazai bar boyem ba saiya seta abubuwan daya fara setawa da dama dan haka su kula da kansu kuma akwai mota da driver da aka tanadar musu yana nan zuwa ayau din shima.

Cikin kulawa da kauna me tsafta da ba sirki Ammin tace

'Ka kula sosai da kanka,
Ka rage fushinka illa ce ga lafiyarka da imaninka,
Ka sassautawa kanka akan mahaifinka,
Ka ringa cin abinci akan lokaci da samun hutu sosai
Allah ya baka kariya daga kowane sharri Hayateem'

Ajiyan zuciya nai hade da numfashi ya sake cikin nutsuwa wanda har cikin kunnuwanta taji saurin saukan numfashin nasa da yayiwa Ammin ya bude baki a taqaice yace

'Love you Ya Ammi'

Murmushi Ammin tayi tana ajiye wayar sbd ya kashe tana kallan Bahar wadda tayi shiru a jikinta tana hana zuciyarta tina abinda ya faru a tsakaninsu sbd zata iya kasa hada ido da Ammin wanda zai iya saka a gano wani abin ma.

Cikin kokarin basarwa ta gaida Ammin tana daukan cup din dayake gabanta tana bata cikeda kulawa.

Amsawa tayi tana karban cup din bata sha ba takai bakin bahar din tana cewa ta fara karyawa tukuna.

A tare suka shanye duka madaran a different cup da aka ajiye kafin Zuhrah ta kira Ammin suka dan jima suna waya tukuna aka bawa bahar itama sukai magana sosai kafin suka fito.

Breakfast sukai suna gamawa driver yaxo ya dauki bahar din suka fita tana dan jin tsoro da shakkar fita daga ita sai wanda bata saniba a qasar da bata taba saniba bare xuwa hakama batada doguwar ilimi da wayewan muama sosai da mutane dan haka a sanyaye sukai fitar.

Makarantar da zatai karatun ya kaita kai tsaye gurin wanda akace a kaita,

Suna zuwa sauran formalities aka qarasa cikewa da kammalawa akai komai da komai harma ta shiga class din karshe da dagashi an tashi.

A gajiye ta fito suka bar makarantar zuwa gida sbd ko ruwa bata iya sha ba sbd rashin sukunu da fargaban datake ciki,

Suna dawowa bata wani iya tsayawa palo ba gurin su maa dakinta ta wuce ta fara ajiye su laptop da ipad da sauran tarkacen karatun da zata duqufa dayi kafin ta fada bathroom tayo alwala tazo tayi sallah ta fita taci abinci ta zauna tana fadawa su Ammi duk abinda ya faru a makarantar tana jin kaman bazata iya karatun ba,

Karfin gwiwa Ammi da maa sakinah suka bata sosai sbd tenya tana kitchen tareda Aysha dan ita sam bata wani son zaman hutawan nan sosai hakama idan ba ita tabawa Ayanah abinci ba ganin takeyi sam batada nutsuwa.

Sosai suka bata kwarin gwiwa tareda tabbatar mata da zata iya idan ta dage sbd tana buqatan karatun da ilimin a yanxu datake da sauran kuruciyanta.

Da wannan ta sakawa ranta zata daure ta dage tayi karatun insha Allah.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

112
Washe gari da wuri ta shirya sbd karfe 8 zata ringa shiga aji dan haka bata tsaya bacci ba bare jiran Maa sakinah taxo tada ita ta fito a shirye maa sakinah na kitchen da kanta ta hada mata breakfast mara nauyi ta kawo mata tareda zaunawa gefenta tana taimaka mata gurin ci akan lokaci.

Tana cikin breakfast din Ammi ta fito ta iso gurinta tana miqa mata jakarta me kyau data hado mata yan abubuwan buqata da wayar data bude mata sabuwa dal ta saka mata numbers nasu duka a ciki tana mata addua.

Ammi da maa sakinah kaman zasu bita makarantar haka suka rakata har kofa ta fice da sauri tana musu sai anjima.

Mota ta fada suka wuce makarantar tana saka ipad dinta a jakarta.

Koda suka isa da farko taso ta sake karaya amma wadda aka hadata da ita Neesah yar qasar ghana ce a makarantar dan ta taimaka mata sosai sai ta sake mata sosai tareda nuna mata itama zata iya dan haka saita sake sakewa dan daukan kowane darasin dazai taho mata ta karatun.

Bayan fitowansu class din farko da kusan bata gane komaiba library suka nufa ta zaunar da ita can ta fara fahimtar da ita komai da abubuwa,

Bata dawo gida ba sai yamma sosai sbd lesson din da aka wuce da ita wani gurin daban wanda shima kullum daga school can zaa ringa kaita tana koyan turanci da ilimin muamala da mutane da duk inda zaka shiga.

Acan baa hadata da kowa ba dan haka shiru kawai tayi tana saurare tareda recording komai sbd neman cikakken qarin bayani idan ta isa gida.

A gida babu sauran lokacin kowane irin hutu a gurinta sbd a gidanma tanada online class da shima aka tanadar mata komai na turanci da larabci wanda zaisa tafi ganewa.

Har dare bata fito ba dan haka Ammi da kanta ta saka aka hada abincinta takai mata har dakin tana zaunawa kusa da ita suna duba karatun tare tana ganar da ita abinda ta sani itama kafin suka qarasa kammalawa ta sakata taci abinci ta koshi cikin kulawa ta goge mata bakinta da tissue.

Anan gurin daga fira bacci ya dauketa jikin Ammin cikin gajiya da dan ciwon kan rashin sabon abinda dole ya zama rayuwarta kuma.

Sai data dan yi me nisa ta rage ciwon kanta tukuna ammin ta tada ita tayi shirin bacci tayi sallar ishai da akai tini tukuna ta kwanta take baccin ya sake dauketa.

Washe gari ma haka ta tafi tinda safe bata dawo ba sai 6 na yamma a gajiyenda saida maa sakinah ta kamota jikinta ta rungume ta rakata har daki ta tayata zare kayan jikinta ta fada toilet tayo wanka da alwala tayi sallah Amminta ce ta bata abinci kaman zata tayata ci harta koshi tukuna ta fada online class dinta wanda tayi har kusan 8 tukuna tai sallah ta sake kwantawa.

****Haka karatun nata yafara tafiya a cikin wata irin gwagwarmayan rashin hutu ko kadan wanda ya sakata tafara ramewa duk da tana samun lafiyar fata sosai sbd yanayin garin da luxurious abubuwan datake amfani dasu da kuma gyaran da fatarta ke samu a cikin sanyi da nutsuwa daga Maa tenya dinta da ita anan ne tafi kwarewa.

Dukkanin wani abinda zata buqata na rayuwa da amfani ansiya mata harma an wuce kaidarsa sbd komai nata tamkar baa san zafin dukiya ba ake siya mata shi a cikin gata da daular da suke ciki,

Ammi ta samu sauyin rayuwar da bata samu tayi ba a baya yanzu itace takeyi wato ta zamowa cikakkiyar uwa me dawainiya ga abinda ta haifa,

Ko data haifi NUAB ba itace take kowace irin dawainiyarsa ba sbd yanayin da Allah ya sakata bayan haihuwan dan haka bata samu daman wahalta masa da jiki da lafiyarta ba sai ayanzu ne take sanin menene dawainiyar 'yaya dan kuwa kusan komai na Bahar din itace takeyi duk ba itace take girki da sauran abubuwan ba amma kowace safiya itace take fitowa taje dakin ta tadata bacci ta tayata shiryawa kaman qaramar baby ta sakata tayi breakfast ta rakata har waje saita tabbatarda ta wuce tukuna take samun daman hutawa harma ta bari ayi tata dawainiyar da kulawa da ita itama har sai Bahar din ta dawo kuma ta tayata fuskantar online classes nata da sauran karatun da shine yake ramar mata da yarinya,

Maa sakinah ma kusan duk dawainiyarta akan bahar dince sbd ta saba hakama akwai abinda itace kadai take iya yiwa Bahar din kaman wanke mata kai haryanzu itace take shiga toilet tareda ita ta wanke mata sbd sam Bahar din batajin kunyarta a matsayin uwar gaske ta dauketa sabanin duk kauna me karfin datakewa Amminta bata iya shiga toilet da ita duk da wasu lokutan tanayi musamman idan maa bata wanke mata kai ba Ammin ke mata amma kuma duk ranar da Allah yasa ta tina NUAB jin takeyi bata iya shiga toilet da Ammin ta ringa zame zame kenan har sai kuma an kwana biyu ta manta.

Karatunta yafara nisa dukda nauyi da karfin da yayi mata ta tsaya dakyau tana fahimta hakama tafara ganewa sosai ga lesson din datake zuwa shima suna kokari sosai gurin ganin tafara gane turanci tana dan kokarin yi da sakewa da mutane tareda fara iya hulda dasu dayasa tafara sani da wayewa akan abubuwa ciki kuwa harda iya zuwa siyan abu da kanta gurare daban daban ita kadai sai drivernta wanda duk inda zata yana tsaye yana jiranta harta gama ya juyo da ita.

Neesah ma sosai take sake sakewa tana bada himmar karatun Bahar din sbd sun fara samun shaquwa sosai da kuma sabon karatun da Bahar din ta dage sosai akansa dan yanxu ta dena jin wahala da fargaba ta karbesa hannu bibbiyu.

Neesah a hostel take zaune sbd batada kowa a garin sam iyayenta suna Sheffield city dan haka ahankali ahankali sabonsu da tsananin son karatun Bahar din ya sakata janyota gidansu tana zuwa tayi kwanaki haka tareda su kafin ta koma hostel sai kuma wani lokacin ta sake zuwa tai musu kwanaki harta saba sosai dasu Ammi da maa da suke kaunarta sbd kaunar datakewa bahar da tsayawa akan karatun bahar din wanda ya fara shigarta sosai dan kuwa bahar din ta cire duk wani kadaici da kama jiki ta fara wayewa da qasar da rayuwar qasar sbd maganar wata kusan shida sukeyi a qasar kuma sosai rayuwar ta sauya musu gabaki dayansu sun fara sajewa da yanayi qasar tinda daman sun saba da dan yawonsu na qasashe hakama a cikin daula da tasu duniyar me zaman kanta suke rayuwa dan haka babu wani sabon abu sosai a qasar da basu saba da shi ba suka waye dashi ba.


*******A tsawon wannan wata shidan babu kowace ranar da NUAB baya waya da mahaifiyarsa dasu maa ba amma bai taba tambayar Bahar ko nuna ma ya tina da akwaita cikin rayuwarsa ba,

Ita kanta Bahar din ta tattara komai nasa ta manta dashi gabaki daya harma tinawa datake dashi 'dan Amminta ne ta ajiye ta manta yanzu Ammin tata ce ita kadai ta fuskanci rayuwar gabanta datake mata dadi yanda ya kamata sbd yanzu har yawo sukeyi sosai da Neesah wadda ta zana very close da ita,

A zuciyar Ammi babo. ranar da zatai waya da NUAB din batai tsammanin ya tambayi 'yarta ba ko da badan auren dayake tsakaninsu ba kodan kasancewanta yar datake ji da ita fiyeda tata rayuwar amma bai taba tambaya ba barema nuna yasan da akwai wata rayuwar bayan su uku iyayensa dake Oxford din,

Abin yana sosa ranta kuma batason tayi masa magana sbd kada ya dauka son cusa masa ita takeyi amma hakan sosai yake mata ciwo dan haka ta tattara itama ta ajiye maganarsa da bahar auren nasu na ficewa daga ranta tana tsayar da shawara daya akan rabasu matiqar tanason ta zauna dasu kowa da matsayinsa na me mahimmanci a rayuwarta batareda ta cutatar dasu ba ga bahar ta samu rayuwar da ba takurawarsa.

*****A boyem ma gurin sultan LEUL me boyem kaman yanda Ammi ta tattara maganar auren ta ajiye akan rabuwa hakan ne a gurinsa sbd yanajin rayuwarsa a yanda take tafi masa ba damuwa da rigimar da bahar din take tattare da ita a rayuwarsa dan haka ya hakura ya taba kaiwa Ammin tasa ziyara sbd baya buqatan duk abinda zai sake saka rayuwarsa a matakin zarewa ko zama makashin dayake neman zama,

Hankalinsa yana kan mulkinsa sosai daya sauya kusan duka manyan fadar masarautar ya zuba sabbi masu zafi da ilimi me karfi da tsayuwa akan raayin gaske a cikin manyan 'yayan fadar da wasunsu ma duk sun zama dattijan zamani masu ilimi suna qasashe daban daban suna rayuwa ya gayyatosu suka dawo qasarsu ya basu matsayin daya tattaro dasu ya dawo dasu qasarsu a qanqanin lokaci dan bawa iyayensu daman hutawa daga sarautar da zaman fadar daya fara tsatsar da zuciyoyinsu.

Sultan Yasar dayake cikin masarauta yana hutun da kusan kaman baya duniyar gabaki daya bare masarautar dan kuwa ko ganinsa babu me sai wanda yaso gani
Yana sane da sabuwar boyem da NUAB yake tsarawa wadda ake ta magana a kafafen yada labarai musamman sabbin dokokin daya fitar da suka girgiza duniyar gabaki daya wanda ya fidda su jere ciki kuwa harda bayyanarda cikakkiyar Alaqar mahaifiyarsa da Matar mai girma yunar ya kuma soke kowane irin dokar da zata hana jini daya yan uwa daya aiki a cikin masarautar boyem matiqar yana mulki dama duk wanda zaiyi mulki bayansa ya dakatar ya kuma goge wannan dokar a shafin tarihin boyem gabaki daya har abada,

Dokarsa ta biyu data girgiza boyem itace soke Imebētin data wuce daya ga kowane jinin boyem ko a ina yake dan haka ga duk wanda haryanzu yakeda Imebēti zabi biyu yake dashi kodai ya sallamesu kokuma ya daura aure dasu a cikin qanqanin lokaci.

Doka ta uku shine soke kawo bayi maza ko mata na siya sedai a daukesu a matsayin ma'ikata da masarauta zata ringa biyansu hakama kowane bawan dazai kai shekaru sama da talatin da shida zuwa arbain indai mace ce zaa yanta su sutafi a zuba sabbin masu karfi da sauran kuruciya idan kuma maza ne shekaru arbain zuwa da biyar kema zaa yantaka sbd kaje ka qarasa sauran lokacinka a cikin yanci.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee


113
Dokarsa ta uku itace fidda sanarwar cin kasuwan bayin qarshe na masarautar boyem da zaa ci garin da kasuwan bayin qasar take na bakin border na ruwa wanda kai tsaye a bangarensu shirin tarbon kusrawa ne a qasar sbd bazasu taba wuce wannan cin kasuwan ba na karshe a boyem hakam an saka cin kasuwar nesa sosai sbd bada isashe kuma wadataccen damar isar labarin koina na duniyar da har zai isa inda ake son ya isa harma da lokacin da zasu samu kafin hada bayi da isowa dasu qasar wadda take shirye tsaf tana jiransu dan kuwa hatta matakan tsaron kowace border ta qasar an sauyasu zuwa masu tsananin da suka ninka suka qaru suka wuce na asali dan kuwa yanzu mulki ake na tsananta kowane matakin tsaro dan bawa qasar da mutanenta kariya tako ina......

****A lokacin da aka gama kaddamar da wainnan dokokin masu karfin gaske da wainda ma bamu zayyanoba a cikin babban fadar masarautar a cikin wata irin karfin ikon data saka koina daukan tsit masu jarida da yan media na dauka da gidajen television Sultan ma dayake zaune palonsa yana ji suna sauka kunnuwansa suna ratsashi shiru yayi sbd abubuwa ne da shi baiyiba sbd takunkumin dayake daure dashi na ya riga ya kaddamar da duk abubuwan daya tarar akan mulkin batareda ya sauya ba kuma tinda ya kaddamar dasu a yanda suke tin can baya baida ikon sauyasu har abada shiyasa koda ya samu sauyin shigowan Ayanah da soyayyarta me karfi rayuwarsa bai taba samun sukuni da kwanciyan hankali ba saida ya tabbatard ya sauka ya dora wanda zai sauya masa su ko bai fada masa ba sbd raayinsu da zuciyarsu dake bugawa a matsayi daya akan kuma buri daya na inganta tareda kawon sauyin duka akan rayuwar mace daya dasuke tarayya akan kaunarta da zasu iya komai akanta wato AYANAH GHAZ.

A cikin dokokin da sabon sultan din ya fidda gabaki daya akan daya ne zuciyar sultan yasar ta tsaya a yanxu waton sallamar imebētis ko auransu kafin wani lokacin,

Wani sanyayyan numfashi sultan ya sauke yana dago fararen idanuwansa yana sake kallan makekiyar flats screen tv din dake palonsa yana kallan yanda ake jero sabbin dokokin mulkin sultan NUAB LEUL boyem wainda ake yinsu a live shima kuma dayake masarautar yana jinsu a kannuwansa a lokacin suke shigarsa a lokaci daya dana tv din,

Abu daya ne ya sani a tsawon lokacin nan da NUAB yake masarautar ya kasa ne ya tsare dan hanasa tafiya kowace qasa a tinaninsa ya rabasa da mahaifiyarsa kenan ya dauketa,

Ya aiko masa sakon a rubuce da stamp dinsa na ya dakatar dashi daga fita kowace qasa har sai bayan tsawon shekara biyu sbd ya samu hutawan sauka daga mulkin shekaru sana da talatin tareda zuba masa sabbin bayi da securities a bangarensa duka a matsayin basa hutu da kulawan daya kamata,

Ko a wancan lokacin da sakon ya samesa kai tsaye yasan bawai hutun NUAB yake nufiba ya basa a matsayin tausawa da nuna kulawa kaman yanda masarautar da duniya ta dauka yayi hakan ne dan hanasa isa ga mahaifiyarsa dayake jin ya dauke

62 / 100