Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   89 / 100

264K to 267K   out of 299.8K words

din.

Babu sauran fushi ko daure fuska a tatattare da ita sbd ganin sunyi biyayya akan maganarta dan haka a sake suka gaisa da yar maganganu sama sama anan take sanar dashi tafiya zasuyi tareda sultan zuwa Anjom hakama bahar makaranta zata koma.

Kallanta yayi a natse hankali kwance ya bude baki yace

'Allah yakaiku lafiya Ammi ya dawo daku lafiya i pray'
Amman ita 'yar ghaz din Ammi kina fadamun ne a matsayin 'da kuma wanda zaiji abinda kuka tsaya kokuwa ana sanar dani ne dan neman nawa izinin sbd aurena dayake kanta? Sorry Ammi'

Zuba masa ido Ammin tayi tana kallansa da dukkanin rudewa da zallan mamaki sbd batama san me zatace ma kuma batai tsammanin jin hakan daga garesa ba sbd ta dauka zai bar maganar bahar din kila sai nan gaba.

Shima kafeta da Manyan fararen idanuwansa masu kwarjinin gaske yayi yana jiran amsarta a natse sbd wannan karan bayajin ma akwai dalilin dazai raba kansa da matarsa ba.

Cikin rasa sanin abin fada tace

'Ai ba yanzu ne tafiyar ba sai kwana biyu,zan nemeka idan an saka lokacin wucewan...

Wani kyakkyawar murmushi ya sake me nutsuwa sbd ganin yanda ta rasa abin fada masa dan haka yayi sallama da ita ya miqe ya fice.

Maa sakinah na zaune akai hakan dan haka yana ficewa nasiha ta fara yiwa Ammin akan yanda ta hana auren yayi gaba bayan komai ya riga ya faru sedai koma batason auren yanzu tayi hakuri ta dangana tinda dai ya riga ya maida Bahar din cikakkiyar mace.

Shiru Ammin tayi tana sauraron sakinah sbd itama koyaushe ta tina ya gama maida bahar din mace sai taji tarasa mafita bayan hakura tabarsu tare amma kuma tana buqatan ayiwa Bahar din biki kaman kowace mace kafin ta basa ita kuma ba yanzu ba tafison sai bahar din na gap da kammala karatunta ko tama kammala gaba daya tukuna.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

163
Sauya kaya bahar din tayi ta sako nata ta sake fesa turarenta na chanel me tsadan gaske sbd qamshinsa dayake tashi hatta a fatar jikinta.

Dakin Ammin ta taho tana shigowa suka bita da ido sbd qamshinsa daya sake shiga hancinsu amma kuma sbd ganin yanzu din ya fita sai ba wanda yayi tinanin komai akanta.

Gaidasu tayi cikin kulawa da yar shagwaba kafin ta shige dakin Ammi ta kwanta take bacci ya dauketa sbd dakinta Ac yayi yawa leylah ke so dan ita kuma cikin jikinta zafi yake sakata ji ita kuma yau sanyi take ji warm abubuwa kowai take buqata.

Dakin Ammin kashe ac tayi tashige bargon Ammin shiyasa baccin bai jimaba ya dauketa.

Wuni tayi tana bacci sallah kawai take iya tashi tayi sai ta dan ci abinci ta koma.

Da daddare koda ta koma dakinta batai wankan dare ba kaya kawai ta sauya ta kwanta koda ya kirata ko tashi batajin zata iya bare saukowa kan gado dan haka ya lallabata da zantika masu nutsuwa har tayi bacci.

Fara shirin tafiya Anjom maa tenya ta fara yi musu sbd acan zaa daura auren Maa sakinah wadda ta kasa yadda da wai aure zatai NUAB 'danta ya bada aurenta.

Ammi da zuhrah harma da maa tenya da ita kanta Bahar cikin wani irin mafi girman farin cikin hakan suka samu kansu dan haka basu damu da ba yarinya bace yanxu shirin biki sukeyi sosai da sosai dan kuwa babban fagen da ake zubar da wata irin dukiya gurin gyaransu tenya ta bude,

Ayanah,zuhrah,sakinah,Leylah da Bahar haka ta rufe ido tace su duka zatai gyaran dan haka suka shiga hidimarsu sosai,

Hatta bayin bangaren Ammin kaf dana bangaren mai girma yunar dana sultan dana kadir da sauran mutanen masarautar farin cikin hidimar sukeyi da murna sosai tareda shirin halarta wannan bikin daurin auren da zaayi har anjom wanda Sultan da NUAB suka yanke shawaran acan zaayi daurin auren sbd bayyanawar da duniya garin.

Tsawon wannan watannin tin daga ranar da sultan yasar ya baro anjom da Ayanaah ghaz ya ware dukiyar datai kusan rabin abinda ya mallaka dan bada hanyoyin zamani ga garin Anjom ghaz daya kudurci maidawa babban gari me kwanciyan hankali da wadata irin yanda yake a baya.

Masarautar Anjom din aka fara rusawa gabaki daya aka dora ginin zamani me girman gaske me hawa biyu da tarin gurare bayan an zagaye an kebe inda kabarin iyayensu dana Abaass suke an rufe.

Manyan tituna aka nema hanyoyi aka fidda tin daga cikin garin har zuwa garuruwan dake hanyar garin har zuwa babban gari me babban hanyar tinin da zata doraka akan manyan garuruwa,

Wuta da manyan businesses na kasuwancin gargajiya da zamani aka kawo tareda makarantinni da bude babban branch na manyan kasuwancin mutanen da kuma bude bodar bakin ruwa tareda kawo jamian tsaro da kaki kala kala a garin.

Koda NUAB shima aka gama hado nasa plans din na aiki aka aikosu garin aykin sultan yasar ya gama nisa dan haka shima dukiya me yawa ya ware aka rarrabawa jamaar garin dan fara kasuwancin dazai sake saka zamar da garin babban gari.

Cikin ikon Allah gyaran da akaiwa garin da cigaban daya samu y saka daruruwan dubban mutanen da sukai hijira dawowa harma da wainda ba yan nan ba take garin ya fara zama babban garin da ake huldodin kasuwanci sosai hankali kwance ga tsaro ga ilimi da kusan shine yake jawo mutane dawowa cikinsa dan bawa yaransu ilimi.

Duka wannan ayanah ko zuhrah ba wanda ya sani sedai itama zuhrah mijinta ya sani sbd yaje garin ziyarar kabarin iyayenta dan haka shima saiya dauke nauyin daya zuba asalin luxury dukiyar furnitures a masarautar data koma tamkar aljannar duniya.

Sunata shirye shiryensu na hidimar bikin
Sultan ya bada dukiyar auren me yawan gaske aka kawowa sakinah ta asalin tarin zafafan set set na sitirar sakawa da sarkokin gwal gwal masu girma da kyau.
Wainda suka gama kawo tarin kayan suka jere suna gamawa suka sake dawowa suna jere tarin wata dukiyar data girgiza kowa ta Kayan auren Bahar itama daga sultan din wa 'dansa NUAB wanda yake a shirye ya karban masa matarsa daga Amminsa sbd duka yawon dasuke na kwana office da bangaren NUAB din da safe ta koma gun Amminta yana sane amma ita ammin bata saniba.

Shi kansa yana buqatan idan an bawa NUAB matarsa yabarsa shima ya tafi inda zasu huta su nutsu da matarsa wadda ya yanke shawarar barinta ta zauna a anjom itada Sakinah babu wadda batada babban bangare me dauke da palika da dakina da maids dinsu sam da goma goma a cikin masarautar anjom da yanzu ma sarautar zaayiba iya rayuwan nutsuwa zaayi sai babban lamari zaa kawo masarautar su duba dan haka shima a yanzu rayuwarsa kusan zata koma acan ne sedai ya ringa zuwa yana lokaci anan boyem ya koma can ma yayi lokaci,

Ita kanta Ayanah datasan yayi mata alkawarin maidata anjom dan cika mata burinta wani irin farin ciki take ciki hakama bayan bayin da aka kaimusu acan da bayinta na nan zata tafi sedai idan zata taho hutu ko wata hidimar anan tazo dasu dan haka shirinsu babbane,
Zasu tafi su bawa NUAB damar yin mulkinsa cikin nutsuwa ba kowane distraction da kwanciyan hankali.

Maa tenya ma da batai rayuwa a anjom ba farin komawa takeyi acan,

Bangaren Maraki duk hidimar da akeyi tana sane dan haka baqin cikinta da kuncinta yayi tsananin datake sake rasa kanta dan kuwa takai ko miqewa tsaye bata iya yi dai an riqeta sbd cin lafiyarta da qunci da baqin cikin keyi,

Tayi tayi ta gwada dannewa ta iya cigaba da rayuwa da sultan amma sam batajin zata iya sbd hakan na nufin bugawan zuciyarta da mutuwarta dan haka takanas ta samesa ta sanar dashi sawwake mata takeson yayi a yanzu bazata iya rayuwa dashi ba dan wlh mutuwa zatai.

Da farko sallamarta kawai yayi amma sai gashi ta nace da hakan dan kuwa ta karbi girkinta tana zuwa kwana gurinsa a yanzu amma ba kwanan takeyi ba rokone take masa da nuna masa halinda take ciki da wanda ma zata iya shiga dan a yanzu jin takeyi idan har zata samu dama zata iya daukan ran ayanah kuma bazata taba so rayuwarta ta kai ga irin wannan lalacewan ba sbd shedan dayake shiga quncinta yana sakata tinanin hakan.

Tsaf ya kalleta yana nazarinta da abinda yake hangowa tattare da ita da kuma abinda take fada masa na halinda take ciki a boyem tsawon rayuwarta bata taba farin ciki ba dan haka a yanzu ta zabi farin ciki akan rayuwar da batada alkhairi ma a garesu su dukan.

Bai sauwake mata ba amma dai bayan dogon nazari na kwana biyu ya bata daman tafiya gidansu dan samun warware daga damuwa da samun nutsuwa na tsawon duk lokacinda hakan zai bata kwanciyan hankali kafin ta dawo.

Tana samun hakan bata jira komaiba sbd ba dawowan takejin zataiba har abada dan haka ko wani lokaci da dogon shiri bataiba dan batason ma hayaniya ta tattara tabar qasar boyem batareda sanin kowaba daga ita sai sultan kawai dai an dauka normal tafiya ce tayi duk da bataje da bayinta ko dayaba dan bata buqatar komai na boyem.

Tafiyarta ta saka Hankalin haile dake mummunan tashi sbd ta tabbatarda ba dawowa Maraki zatai ba tabarwa Ayanah sultan kenan,
Ita ma hakan ta fara hangowa kanta amma kuma bazatai taba yiyuwaba sbd yayanta da bazata iya barin su mutu a yanda suke a wulaqance ba hakama Asim tafiyarsa sai sake matsowa take ba gudu ba ja da baya ga ayanah sai hidima sukeyi,

Da wane baqin cikin zataji?
Tana nan tana qunci da kwana kukan baqin ciki ayanah ghaz na can na murna da farin cikin samun sultan ga kanta ita kadai Wanda ita kam bazata taba yadda ba bazai taba yiyuwaba,
Idan har bazasu samu sultan ba wlh a yanzu kam zata tabbatarda ayanah ma bazata samesa ba gwara ya mutu suyi takaba kowa ya kama gabansa.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

164
Tinda aka fara hidimar Bahar bata sake haduwa da NUAB ba sbd kwata kwata Maa tenya bata barinsu fita koina sbd gyaran hatta kofar palon barin bangaren basu taba bari ba hakama shi kansa NUAB din ta hanasa zuwa bangaren dan haka iyakacinsa da Bahar din a waya hakama Amminsa ma a waya duk da baisan dalilin hakan ba kawai dai tace masa sai zaa tafi zai sake ganin Bahar kokuma kila saima anjom.

Jin hakan ya shiga mamaki da shakkar ko zai iya dan haka ya dawo kan bahar din da lallabata da rudar da kwakwalwanta da soyayyarsa dan kawai ta samu ta fito ya ganta tin kafin ya zare amma sam ta kasa samun dama sbd ita kanta sai ahankali kwanakin bata jin daidai tana ganin kaman gyaran da ake mata ne da abubuwan shan da ake bata.

Ita kanta leylah ma da aka hanata komai sai a lokacin Asim ya samu kansa a cikin wani irin rashin sukuni da nutsuwa sbd rashin ganinta kwata kwata na kusan sati biyu.

Bai dauka ganinta a kowane dare ba ko rana ya zama dabiar da zata iya hana zuciyarsa nutsuwarta kwata kwata ba sai yanzu dan kuwa hakanan ya zama dan zuwa gaisuwan su Ammi safe da dare amma baa taba barinsa ya ganta ba dan haka ya susuce soyayyarsa dabai saniba ta gama bayyana amma tenya ta masa karfin hali kaman kowa dan sultan ma shiru yake ji.

Yawon Asim ya fara zama abinda ya zama dan kuwa bakin fama ya riqe wuta yaqi saduda hakama sultan kusan umarnin dayake badawa na son gani da magana da Ayanah sunyi yawan daya saka Tenya yanke shawaran su wuce kawai gabaki dayansu a satin maimakon sati me zuwa sbd su qarasa shirinsu acan kafin Su sultan din suzo nan da sati uku daurin aure.

Itama Ayanaah hakan ya mata dan haka ta sanar da sultan ta waya ba gaddama ya amince musu aka fara yi musu shirin wucewa banda gobe.

NUAB a waya shima Ammi ta sanar dashi tafiyar a banda gobe shiru yayi na tsawon mintina kafin yace ba damuwa sukai sallama ya kashe wayar.

Asim ma yanaji a bakin maa tenya dayaxo da daddare suna yar fira sama sama dasu Ammin rikicewa yayi daqyar ya iya riqe kansa ya fice batareda ya zubar da kafafunsa qasa ya rokesuba subarsa yaga leyalah kafin wucewan.

Yana fitowa tinanin yanda zai ganta a daren ya fara yana rasa yanda zaiyi.

Bangaren Mamensa ya tafi ya kasa barin bangaren gabaki daya ya koma nasa,

Bangaren ya rasa dukkanin haske da walwala sbd Mamin dake cikin tsananin baqin ciki da dahun zuciya hakama su Aslam sun dawo bangaren na mamin sbd kowannensu a inda yake damuwa kashesa zatai da qunci dan haka suka dawo bangaren suka dasa wani sabon zaman baqin ciki da kallan ikon Allah da yanda wasu suke rayuwar farin ciki a masarautar tamkar babu su sbd kaman ko uban daya haifesu ya manta su duk sbd sun bijire masa a baya lokacinda yaso sosai inganta rayuwarsu ta hanyar aura musu mazan da daa yanzu suna can suna rayuwar jin dadi da kwanciyan hankali harma da zuria.

Asim da sam ya cire damuwa da baqin ciki da quncin halinda suka samu kansu a ransa sai abin ya zo masa a sauki bayajin ma radadin komai sbd ya yadda da rayuwar bata tsaya anan ba lokaci bai qure ba duka zasu iya wankewa su dasa sabuwar rayuwa,

Su kuwa da basu gane hakanba da mamin tasu daidaicewa kawai sukeyi suna sake dasa baqin ciki da zafi a ransu karshema ganin sukeyi ya juya musu baya bayan akansa sukaita abinda sukaita yi din har suka samu kansu a halinda ake ciki yanzu,

Ya zauna dasu harda mamin tasu gabaki daya yayi musu nasihar cire damuwa da rufe babin rayuwar baya a bude sabuwa wanda hakanne ma ya saka zai bar nan din amma sam sun kasa ganewa su yadda sai ikirarin bazasu taba tafiya subarwa Ayanah ghaz masarautar boyem ba itada ta samesu anan a matsayin baiwa amma ace sun tafi sun bar mata masarautar itada 'danta wanda tarihi acan qarnika na gaba zai taho a tabbacen Baiwa kuma imebēti ta karbi masarautar boyem duka itada 'danta sun karbe komai na qasar sun karbe wanda ya mulketa wato sultan yasar.

Tinanin hakan kadai idan haile dasu aslam din sukai sai suji kaman zasu mutu,
A baya akai lokacinda kaf boyem ba mace me darajarta kasancewanta matar sultan ta farko kuma wadda tafi masa mata duka,hakama mace mafi kyau da ado,hakama mace me karfin iko da isa a cikin matan dake boyem kaf,hakama yayanta sune yaya mafi daraja a qasar amma ayau kamar ma duniya ta manta dasu kwata kwata ko tina da suna raye baa yi sedai ayanah da qasarta Anjom ghaz sbd kawai danta yana mulkin boyem,
Wannan dalilin ya saka taso danta yayi mulki koda zata rasa komai da kowa sbd tasan har abada bazata dena daraja ba harta bar duniya koda kuwa danta ya tsufa ya sauka mulki ne tarihi bazai dena girmamata ba a matsayin uwar sultan da yayi mulki kuma kilama kalar sultan dazai cigaba da mulki idan 'dan Asim ya hau kenan.

Numfashi me sanyi da kokarin dedeta nutsuwa Asim ya sauke yana zaunawa a palon mamin a kujeran datake kallan ta Aslam sbd suna zaune a palon dukansu meryam ta zubawa wayarta ido da hankalinta tana magana ta chat da Nysah kanwarsu akan auren data rufe ido ta fada mata ta samo mata miji acan bangaren dangin mijinta kokuma ta saka mijinta tinda babban mutum ne kuma ya manyanta sosai ya samo mata wanda zai hadasu.

Tin kwanaki sukai maganar kuma nysah taji dadin hakan dan haka taiwa mijinta magana baiji komaiba ya tabbatarda insha Allah zai kawo wanda zai nema aurenta.

Tinda akai hakan yanzu wani kusanci ne sosai ya dawo tsakaninsu biyun dan koyaushe suna kan waya suna maganganunsu tana boyewa maminsu dan kada tai tir da ita akan taje rokon neman miji da kanta kokuma kada islam taji itama tace tanaso azo a bata mata lamari tin bata kama komaiba.

Aslam dake zaune tv take kalla sbd yanxu kallan dole da karfin hali takeyi sbd batada kowane aikin yi a rayuwarta bayan damuwa da janye janyen tinani dan haka take kallan films da series yanzu dan hana zuciya bugawa.

Maminsu na bedroom dinta tana nata ciwon ran daya zama jiki,

Gyara zamansa yayi yana daga wayarsa ya turawa leylah sakon cewa taje tayiwa maminsa bankwana kafin ta wuce goben.

Yana tura sakon wata ajiyan zuciya ya sauke yana jin kaman ya koma kofa ya tsaya kafin ta taho.

Wayar maa tenya data maa sakinah ya nemo ya turawa sakon a tare yana rokar taje taiwa maminsa bankwana sbd a bata girmanta.

Adduar suga sakon akan lokaci yayi yana ajiye wayar zuciyarsa na tsalle da wata irin qaguwa.

Su Maa dama leylah dake daki kusan a tare suka ga sakon dan haka kallan wayarta tayi tana murmushi me sanyi sbd tasan ya fada ne kila sbd ta fito.

Su maa kuwa suna karanta sakon murmushi sukai tareda yaba hankalinsa sbd tabbas yayi tinani me kyau na hakan tinda koba komai uwar miji ce dole a bata girmanta.

Maa tenya dince da kanta ta samu leylah din har daki bayan ta tabbatarda dare ya sake yi sosai dole Asim ya bar bangaren kwata kwata yana nasa tace ta shirya tashiga bangaren haile tai mata sallama.

Ba musu leylan ta amince ta shirya ta fito Maa ta hadata da bayi uku su rakata sbd ita kam bazata iya zuwa bangaren hailen ba sbd gudun fitina da wata damuwar tace su tafi.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

165
Fitowa sukai daga bangaren bayinta na biye da ita wainda tasan maa ta hadota dasu ne sbd ma kada taje koina dan haka suna fitowan batama kalli kowace hanya ba sai hanyar bangaren Hailen tana sanye da babbar doguwar hijabi har qasa sbd kayan cikin jikinta marasa nauyi ne dan tayi shirin bacci.

Wayarta ma baa bari ta fito da itaba dan haka daga ita sai ita suka iso bangaren.

Acan ciki kuwa mamaki ne su Aslam keyi na yanda Asim ya kasa nutsuwa sai wani kallan waya yakeyi yana kallan kofa hakama har dare sosai yana bangaren,

Babu wanda yace masa komai akan hatta Mamin data fito ta gansa mamaki ta shiga me girma tana Qarasowa ta zauna gefensa tana kallansa zatai magana baiwarta ta shigo a natse ta sanar da ita zuwan leylah wanda ya saka ajiyan zuciya me sanyi tahowa Asim din yana dago kansa ya sauke idanuwansa a kofar shigowa cikin nutsuwa

89 / 100