rikitarwa tana nufar bayan gadon dakin itama zata boye tana fadawa da karfi idanuwanta suka sauka akan Bahar wadda idanuwanta ke rintse da karfi hannuwanta na toshe da kunnuwanta komai na jikinta na wata irin rawar dake nuna bata hayyacinta cikin mummunan firgici take.
Tsallaketa leylah tayi komai na jikinta itama yana rawa sosai ta wuce qurya ta durqusa itama tareda qanqame jikinta kukanta na qaruwa sosai ta saka hannu tana rufe bakinta da sauri jin yanda aka banko kofar dakin da wani irin karfin gaske.
Wasu samudawan marasa imani biyu ne a gaba gurin shigowan bayan sun bankewa haile kofar dakin kafin ta shigo komai na jikinta itama rawa yakeyi gabaki daya ta zare takejinta gawa kawai zata maida bahar ta samu nutsuwa dan haka a haukace ta nufi toilet ta banka kofar da karfi tana fadawa ciki ta duba babu kowa.
Fara birkita dakin da nema sukai cikin rashin hankali daidai lokacin Asim ya fado dakin a haukace bayaji baya gani ko gabansa
Cikin mummunan tashin hankali ya bude baki zai ambaci sunan mameen tasa salman yayi saurin rufe masa baki sbd baa taba zuwa aikata laifi irin wannan ayi magana sbd abinda zai iya biyowa baya.
Ture hannun salman yayi kokarin yi cikin tsananin tashin hankalin abinda idanuwansa suka gano masa a hanyar koina na bangaren wanda duk aikin mahaifiyarsa ne.
Bahar yake son bude baki ya tambayeta idan batai mata komaiba amma salman ya saka dukkanin karfinsa ya hanasa magana wanda yafara kokarin kokawan kwacewa amma haile tayi alaman kada ya kuskura ya bari Asim din yayi magana dan jikinsu duka ya basu akwai mutum a dakin.
Samudawan datazo dasu din ta kalla ta bude baki da sautin da bame ji idan ba su ba tace a tabbatarda mutuwar ko waye a dakin dan tinda bata ga bahar koinaba ta tabbatarda nan ne dakinta kuma tana ciki.
Bayan gadon Daya daga cikin yaran nata yake kokarin nufa shi kuma salman cikin karfi ya fara jan Asim shi da daya daga cikin yaran suna toshe masa baki da karfinsu suna kokarin ficewa da shi.
NUAB ne ya shigo palon Aleey na saurin shigewa gabansa dan basa kariya tareda nufar dakunan suna fara dubawa,
Ganin irin mummunan al'amarin daya faru a bangaren ba kyan gani koina jini ya saka Jinin NUAB kaiwa matakin karshe na tafasa da konuwa dan haka da kansa ya ringa bankar dakunan da kafarsa yana duba dakunan idanuwansa na tsananta ja hakama jijiyoyinsa.
Aleey kuwa yaransu dake waje ya kira kai tsaye suna dauka yace
'Duk motsin daya fito daga nan ko shadow na dabba ne kona mutum koma waye idanuwanku basu ga kowa ba bayan shadows na marasa gaskia just open fire,
I repeat open fire ga duk motsin dazai fito ta kowane bangaren dayake zagaye da nan din.'
'Zan tabbatarda na fasa qashin duk wanda zai fito daga bangaren na bullet dina,wannan alkwari na ne sire'
Kashe wayar Aleey yayi yana qarasa cire imanin dayake idanuwa da zuciyarsa dan fuskantar wanda yayi wannan mummunan aikin da gabaki daya ya gigita NUAB sbd yanda jikinsa ke tsananta wata irin rawar da ko gani bayayi sosai a karan farko tsoro yana bayyana qarara a idanuwansa wanda babu wanda ya taba gani duk duniyarsa.
Su salman na dosowa suka hango NUAB din da mahaukatansa su Aleey da a shirye suke da komai cikin tsananin tashin hankali suka saki Asim suna dawowa da gudun gaske jikinsu na rawar tashin hankalin da basu taba tsammata ba.
Shi kansa Asim din da aka saki Zabura yayi yana juyowa da gudun gaske batareda ya bari kafafunsa sun saki sauti ba dan kuwa harbi guda Aleey zai sako ya fasa kansa ta bayan qeyarsa dan haka da wata irin tata me saurin gaske ya koma shima ya fada dakin rawan jikinsa na tsananta hakama habon hancinsa dayake gangaro jini ya tsananta sbd tashin hankalin da shima bai taba tsammata ba daya diro masa na ganin NUAB,
Cikin wata irin sauti mara fita suka kalli haile da sauri suna cewa NUAB ne da mahaukatansa sun shigo da manyan makamai.
Kallan yanda jikinsu gabaki daya ya dauki rawa tayi zuciyarta na wata irin harbawa ba daidai ba hannuwanta na rawa ta kalli kofar tana jin wani abu na tsaya mata cak a kirji dan kuwa idan har NUAB ne yake nan kenan ba shine ya karbi mulkin boyem ba wani ne daban,
Waye ne to?
Kokuwa kuskuren da baa taba yi bane akai yau na buga qarar?
Kokuwa harbe harben da akeyi ne aka bugawa qarar sabon sultan sbd a dakatar?
Kama hannunta Asim yayi komai na jikinsa yana rawa wanda shima ganin NUAB anan ya tabbatar masa da ba shine ya hau milki ba hakama sunada tabbacin yana ganinsu anan wallahi bazai qara minti daya ba batareda ya rabasu da duniya ba.
Jan haile Asim yayi da karfin gaske suna juyawa suka fice da tsananin gudun gaske suna hana kafafunsu fidda sauti suka fada wata kofar da zata kaisu kitchen wanda ba zaa rasa kofar baya ba a cikinsa su salman na bayansa sun baro mutim biyu wanda haile ta tabbatar musu da ko zasu mutu su kashe mata bahar wadda suka tabbatarda akwai mutum bayan gadon.
#MAMUH
#LOVE
#SULTAN NUAB BOYEM
#BAHAR GHAZ BOYEM
#SULTAN YASAR BOYEM
#AYANAH GHAZ BOYEM
#BEAUTIFULLOVE
#ROYALTY VS LOVE
HAYATEEM novel
700
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
92
Kai tsaye bayan gadon yaran biyu na haile da aka bari suka qarasa isa idanuwansu a rife dasu kammala aikin su bi bayan su Salman,
Leylah da idanuwanta suke bude tana kuka sosai da bakinta toshe ihu me karfin gaske ta sake tana ganinsu tareda fara wata irin jijjiga tana me karfi tana ja da baya tana qasa nisa a cikin bayan gadon,
Bahar da bata hayyacinta kwata kwata bata motsa ba rawa kawai jikinta yakeyi sosai har lokacin idanuwanta a rinte gam hakama kunnuwanta,
Leylah dake ihun da zai iya basu babbar matsalar da zasu iya rasa ransu suka fizgo da karfi waje tareda daga wata kakkaifar wuqa zasu ratsa cikinta da ita aka bugo kofar dakin da karfin gaske da saida gefenta ya balle,
NUAB ne ya bugo kofar amma bullet din aleey ne guda biyu suka riga NUAB din shiga dakin suka sauka kai tsaye akan wanda yake riqe da leylah daya a tsakiyar goshinsa daya a tsakiyar wuyansa wanda jininsa ya fesu har a gefen fuskar Leylah wadda tayi mutuwar tsaye kunnuwanta na dauke ji sukai dip bata jin komai sbd qarar bindigar daya ratsata da kuma mummunan shock na jinin daya sauka har a jikinta.
Dayan cikin tsananin sauri yakai hannunsa bayan gadon zai sokawa bahar wuqar hannunsa da dukkanin karfinsa sbd koda zai mutu ya cika aikin da yayi alkawarin cikawa,
Ko numfashin daya shaqa na yunkurinsa bai fitarba NUAB ya fizgi wata arniyar wuqar dake soke jikin yaronsa dake gefensa ya jefa masa da karfin gaske wadda lokaci daya ta sauka da bullet din aleey a jikinsa ta sauka tsakiyar jijiyar hannunsa data saka jijiyan ya kewa a take tana feso jini
aleey kuwa gefen wuyansa ya harba wanda ya goga wuyan sosai kafin ya harbe gefen kafarsa ta dama itama wadda ta sakasa zubewa qasa take cikin mummunan hali sbd suna buqatarsa a raye.
Qarar harbin ya saka su Asim dake zuba wani irin sauri suna tatata sbd gudun bada sauti tsayawa cak kayan cikinsu na wata irin rawa suka waiwaya bayansu suna kalli kofar da sauri cikin sake shiga tsaka mai wuya kafin suka qarawa tatarsu sauri suna zare takarman duka kafafunsu sbd a yanzu babu abinda suke tsananin tsoro irin fitar sautin takunsu dazaisa asan da su fata kawai su isa kofar baya su fice.
Bahar da leylah a lokaci daya jinsu ya qarasa dauke wa dip sbd dukkaninsu harbin bindiga abu ne da basu taba jinsa live ba har gwara Leylah tana ji a tv da sauran guraran kallo amma bahar ko a tv bata taba jinsa ba dan haka jikinta ya fara kokarin saki komai nata na sakewa tana kasa daukan tashin hankalin daya rabata da hayyacinta.
Leylah ce tayi karfin halin bude bakinta bata cikin cikakken hayyacinta ta furta
'NUABBB' tareda kokarin isa garesa tana neman somewa.
Saukar sautin sunansa da aka ambata a cikin kunnuwan bahar da jinsu yayi qasa ya sakata bude idanuwanta da sukai mummunan jajir basa hayyacinsu tana miqewa daga bayan gadon batareda tasan ta miqe din ba,
Kokarin juyawa yakeyi a zafafe zuwa nemanta ta miqe daga bayan gadon idanuwanta na sauka akansa wasu irin zafafan hawayen da batasan dasu ha suka rufe idanuwanta gabaki daya
Wani irin abu yaji ya caki kirjinsa ya juyo tareda nufota cikin wani irin yanayin da ko gabansa baya gani ganin itace kenan akaso kashewa da bai iso dakin da wuri ba,
Yana nufota ta fasa wani irin kukan daya tada tsigar jikinsa gabaki daya itama ta fito gurin da gudun gaske tayi kansa take ta fada jikinsa yayi mata wata irin rungumar da bai taba yiba a rayuwarsa dan kuwa zagayeta yayi da hannuwansa biyu yana mata kyakkyawar runguma idanuwansa na tsananta jan baqin ciki me tsanani da bacin rai da wutar fushi dake cin jininsa.
Su aleey komawa sukai daga kofa suna juya baya tareda tsare kofar dakin bayan sun janyo wanda suke buqatar sun dauresa tsaf babu sauki a fuskokinsu.
Kuka take fitarwa sosai me sautin dayake sake tada tsigar jikinsa yana tsaye da ita a jikinsa har lokacin yanajin yanda take sake qanqamesa jikinta na tsananta rawa sosai tana qara ficewa hayyacinta,
Kasa cigaba da sauraran kukanta yayi ya dauketa gabaki dayanta yana juyawa ya nufi kofa da ita ransa na tsanantuwa da wata irin qunar da zai iya komai a lokacin ya fice daga dakin.
Babu imani aleey ya saka a jawo wanda suka kaman a qasa suka bi bayansa bayan ya juyo ya nunawa leylah hanya akan ta tafi su fice gabaki daya.
Duk da leylah na cikin matsanancin tsoro da tashin hankali jin tayi komai da duniyar sun tsaya mata cak akan abinda idanuwanta suka gane mata daga NUAB wanda baima tantance waye a dakin ba bayan bayyanuwan bahar a gabansa.
Jin tayi kirjinta yayi mummunan nauyin da gangar jikinta kaman bazata iya daukaba wasu sabbin hawayen tsantsar baqin ciki da radadi na gangaro mata take tanajin abinda tagani a idanuwan su haile suna ji a lokacinda suke dakin dan kuwa kaf dinsu babu wanda bata gani ba.
Daga kafarta tayi daqyar tana takawa jikinta na tsananta rawar baqin ciki da dana sanin kasancewa a dakin tareda baqin cikin nasarar dasu haile basu samuba akan rayuwar bahar din.
Kofa suka nufa aleey ya fara isa kofar kafin NUAB ya iso ya daga hasken daya tabbatar musu da su dinne suna fitowa kai tsaye babu inda NUAB yake tsayawa barin gurin yayi aleey na bayansa da wainda suka shiga dasu.
Suna barin gurin kawai suka fara jin qarar wata wuta da aka bude daga kofar baya babu ji ba gani kawai suna jin motsin alaman takun mutane basu tsa6a komaiba suka budewa gurin wutar da hatta bangon gurin zuba yakeyi ba kakkautawa.
Wani irin harbi ne ya ratsa hannun Asim na dama ya fasa qashinsa take ya zube a gurin yana jan ciki cikin wata mummunar azabar da be taba ji ba ya ratsa da jan ciki cikin qura da duhun ya samu ya tsira yabar gurin dan bazai yadda ya mutu a banza ba hannun mahaukatan Moscow batareda ta tsira ba ya nema bahar wadda yasan a yanzu tana hannun NUAB.
Yana barin gurin haile itama bullet ya ratsa gefen cinyarta jini na zuba sosai haka ta rarrafa ta tsira ta gudu daga gurin tana jan qafar datake ji tamkar baa jikinta ba hakama idanuwanta tini suka dena gani ko tafiyar rabin barin gurin bataiba ta yanke jiki a gurin ranta na kokarin barin jikinta a some.
Cikin tashin hankalin da su aslam basu taba samun kansu a ciki ba daman suka nufo bangaren tinda suka ga mahaifiyarsu bata nan hakama Asim,
Harbe harben da suma basu taba ji ba ya sakasu lafewa cikin matsanancin tashin hankali a gurin har NUAB ya fice suna kallo sai ga Asim hannu na tsiyayar jini me yawa ya fito ta hanyar bayansu yana layin jirin dake dibarsa da sauri sukai kansa suna cire mayafinsu suka tare masa jinin da tsananin sauri hankali tashe.
Kokarin barin gurin sukeyi haile ta bullo kafin ta yanke jiki a gurin ba rai,
Ihu meryam ta sake me karfi kafin tayi saurin toshe bakinta tana qarasawa kan hailen itama ta zare sauran rufar dake jikinta ta toshe mata inda jinin ke fita.
Ba shiri suka jasu hankali tashe cikin duhun suka bar gurin dasu suna hana jini ko daya diga a qasa sbd kada a bi sahunsa.
Kai tsaye bangaren Aslam dayake kusa suka nufa dasu suna shigewa ta bada umarnin kada kowa ya shigo bangaren nata batareda izininta ba.
Waya meryam ta dauka cikin rawar jiki ta kira likitansu a boye tareda sanar dashi abinda ya faru dan haka ba shiri ya hado duk abinda zai bugata ya nufo bangaren aslam din cikin duhun daren.
******Duk abinda akeyi Sultan yana jin qarar komai a kunnuwansa amma sbd a yanzu baida hurumi ko daya na shiga ko daukan mataki a matsayin shugaba kokuma me mulkin boyem sedai a matsayin uba ko me bada shawara idan ta kama dan haka shiru yayi a zaune batateda motsawaba a zuciyarsa yana fatar a cikin yayan nasa duka da matansa babu wanda yabi sharrin zuciyarsa yayi abinda zai zama matsala ga rayuwan dukkaninsu.
Har daren yayi tsit aka dena harbin dare ya qara tsalawa koina ya sake dauke motsi batareda anyi sautin mutuwar jinin boyem ba ya sakasa sauke wani boyayyan numfashi me sanyi da nutsuwa kafin ya miqa hannunsa a natse ya dauki wayarsa ya saka kiran wayar tenye.
Babu bata lokaci tenya ta dauki wayar cikeda girmamawa ga tsohon sultan duk da dare ne sosai su kam bazasu iya bacci ba a wannan daren sbd tsimayin dake zuciyoyinsu na shedar da wannan daren na alkhairi a garesu.
Magana daya zuwa biyu yayi da ita ya kashe wayar ya sake sauke ajiyan zuciya a karo na babu adadi bayan saukarsa a matsayin sultan cikin daren tukuna ya miqe a natse cikin kamewa da samun cikakken yancin da ayau zai fara samun rayuwar da zuciyarsa ke tsananin muradi tin daga ranar daya fara dora idanuwansa akan AYANAH GHAZ.
Kai tsaye fitowa yayi batareda yan rakiyar kowaba cikin samuwan cikakkiyar nutsuwan yanci daga mulkin dayake tauye da abubuwan rayuwarsa da dama wanda a yanzu yasan NUAB zai kawo sauyi daga mulkin dayake na takura da rashin yancin kai zuwa mulkin da zai baka nutsuwa da yanci tareda hana kowace irin al'ada me tsananin datake sanadin rayuka da dama.
Kai tsaye bangaren wishma dinsa ya nufa wadda ta farka a daidai lokacin itama jikinta a tsananin sanyaye tana kokarin dawo da tinanin dukkanin abinda ya faru zuciyarta na wani irin nauyi.
Shigowansa ya saka gabaki daya bayin bangaren ficewa kofar bangaren suka tsaya gefe daya a jere har sai lokacinda ya fice.
Tenya da sakinah ma cikin tsananin girmamawa tareda farin cikin kasancewansa ayau tareda ayanah suka fito gabaki daya
Maa sakinah ma bangaren NUAB ta nufa cikin daren batareda tsoro ba dan dubo halinda Bahar take ciki.
****kai tsaye yaba baro can bangaren da ita bangarensa ya nufa wanda har lokacin tana jikinsa ta kasa dena kukan matsanancin tsoron data samu kanta a cikinsa.
Bude masa kofar shigewa palon farkonsa akai da sauri cikin nutsuwa yana qarasowa ya shige take aka rufe kofar kuma bame shiga sai gobe nadin sarautar da duniya zata sheda tinda safe.
NUAB na shigewa waya aleey ya buga fada yace KEELA babban wanda shine yake bin aleey a matsayi yace a saki manyan fada sbd nadin sarautar gobe da safe.
Ba bata lokaci kuwa aka sakesu take kowannensu ya fice jiki yayi tsami da sauri suna matsuwan gobe tayi susan waye sabon sultan din na boyem.
#MAMUH
#BEST LOVE
#SULTANS
#AYANAHS
HAYATEEM novel
700
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
93
Yana shigewa kai tsaye bai iya ajiyeta bedroom din data sama zama ba sbd bazai taba samun nutsuwa ba gabaki daya jin yake duniya kaf bai yadda da kowa da komai akanta ba dan haka hanyar nasa bedroom din ya nufa da ita har lokacin kukanta me fita a hankali na ji da shedar da balain da bata taba ji da ganiba a rayuwarta bai dena fitowa ba yana ratsa kunnuwansa.
Bude kofar bedroom dinsa da babu wanda wanda ya taba shiga bayan mutum biyu rak masu aikin gyaransa a cikin yaransa ya shige tareda rufewa yana nufar tsakiyar dakin inda lafiyayyan king-size royal bed dinsa yake komai na dakin qamshinsa yakeyi dan kuwa hatta niiman da zaa shaqa a dakin kowace iri qamshinsa ne yake tashi a cikinta hakama sanyin aircon dayake ratsa koina qamshin nasa ne shima kusan yake ratsa koina din dashi sbd komai nasa ya riga ya kama qamshinsa da babu me irinsa a masarautar masu nayan shi.
Zaunawa yayi a bakin gadonsa da ita a jikinsa yana yin shiru a natse idanuwansa na dan lumshewa kadan sbd sautin dayake ratsa kunnuwansa har lokacin yanawa komai nasa illa musamman tinaninsa dayake jin wata irin wuta na cin kirjinsa na iya daukan kowace irin mataki akan wainda suka iya haukatar da kwanciyan hankalinta zuwa ga duka tashin hankalin data shedar.
Ita kanta kasa motsawa tayi a jikin nasa har lokacin jikinta yar rawa yakeyi tana dan sake qanqamesa kukanta naci gaba.
Shiru ba motsin komai ba sautin ko fitar numfashinsu a dakin saina kukanta tsawon mintina sosai a hakan kafin tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya mara karfi sbd jikinta daya gama mutuwa da rashin karfi tayi sanyi sosai,
Shi ma shirun ya sake yi har lokacin baice komaib bai kuma motsaba tana rungume a cikin jikinsa tana qamqame dashi,
Bayan tsawon mintina bayan ta dena kukan ajiyan zuciya ta ringa jerowa a hankali cikin sunyi jikinta na qara sakewa,
Fara sakinsa tayi a hankali tana jin nutsuwanta tana dawowa jikinta,
Dago kanta tayi a hankali daga kirjinsa tana kasa kallan fuskarsa ta dan motsa tareda qasara sakinsa gabaki daya idanuwanta da sukai jajir suka kumbura suna kasa kallansa.
Qugunta daya zagaye da hannuwansa masu karfi laushin fata da wata irin dumi ya dan sassauta riqon yana saukar da idanuwansa akan fuskarta data sakasa kasa qarasa sakinta sbd yanayinta yana sake bayyanar da zarewan data kusa yi a halin data shiga.
Shiru tayi ajiyan zuciyarta na kukan datasha yana sake fita akai akai