yakeyi zaka iya kwantar da hankalinka mai girma li'uli'
NUAB dake zaune akan sofa me fadi da laushi cikin wata irin nutsuwa da kamewa tareda zallan kwarjininsa dayake cike da gurin zuciyarsa a wani yanayi me sanyi da kowace tinani babu a cikinta empty yake jinta haka kawai dagowa yayi a natse ya kalli Asim din wanda ya zauna suna facing juna shima dagowa yayi ya kallesa jin abinda aleey yace wanda ya basa nutsuwa da dawowa daidai ya fuskanci Dan uwansa da kyau ya bude baki cikik nutsuwa da nasa ikon jinin boyem dayake yawo a jikinsa ya miqa masa gaisuwa me girmansa a matsayinsa na sultan me mulki.
Numfashi mara sauti da nutsuwa NUAB ya fidda yana kallan Asim din wanda alamun sabon mutum ne a yanzu suke bayyane a tattare dashi shima kwarjininsa na jinin sarauta yana fita daga idanuwansa kafin ya bude baki ya amsa tareda miqa masa tasa gaisuwan a matsayin dan uwansa kuma yayansa daya basa mintina qalilan a fadowa duniya.
Daganan aleey bai tsayaba ya fice daga office din yana basu guri tareda komawa kofa inda Keelah yake tsaye ya tsaya gefensa suna magana.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
169
Acan ciki magana su Asim din keyi wanda shine yake jero maganganun a natse cikin kwanciyan hankali da kamun kai akan duka abubuwan da suka faru basai ya tsaya dawo dasu ba kawai yana roko ne da fatar idan ya bar boyem mahaifiyarsa da 'yan uwansu biyu da basuyi aure ba kada NUAB ya bari su wulaqanta a qarkashin mulkinsa sbd su matan yan uwansa ne koma yayane hakama itama mahaifiyarsa matar mahaifinsa ce taci wannan darajar koma menene,
Hakama yana rokon alfarma ta karshe akan ya janye hukuncin Sultan akansu na hana zuwa kowa neman aurensu ya bada damar da kowa zai iya fitowa da zuwa neman aurensu sbd koda sun manyanta suma rayuwansu ta samu walwala ko yayane.
Yana gama rokon wannan alfarmar da bayajin a matsayinsa na dan uwa kuma wanda ya miqa roko na farko kuma na karshe NUAB zai hana masa hakan ya fidda takardarsa me tsayi da kyau da stamp dinsa yake jiki na sultan me mulki kawai yake jira ya ajiye a kan table din gabansu gaban NUAB din tareda dago idanuwansa ya kalli NUAB wanda shima shi ya dago ya kalla kafin ya maida idanuwansa akan takardar gaban nasu wanda duk wanda yake jinin boyem matiqar idan har zai bar masarautar yaje yayi rayuwa a wata duniyar daban ba karkashin masarautar jinisa boyem dole sultan zai saka masa hannu a basa wannan damar da shikenan zai iya rayuwa koina ba a cikin masarautar da ake riqesu ba kaman marasa yanci.
Wannan shine yancin da duk wani jinin boyem daya san meye dadin yanci yakeso na ficewa daga masarautar yayi rayuwansa ba dokoki ba sharudda yanda yakeso,
Mahaifinsu wannan shine yancin dayaso tin yanada kuruciyarsa akan mulkin harya manyanta bai cire rai ba saida ya samu yancinsa ya zama free daga duka matakai da daurin da mulkin yake dashi gashi a yanxu ya samu zai bar boyem din ya je ya samu free rayuwar da bai samu a kuruciya ba sai tsufa da macen dazaiso babu kowane irin shamaki sbd mulkin hatta matarka datake rayuwarka akwai sharuddan dasuke hanaka samun soyayyar da kukeso ku nunawa juna,
Bai taso da shaawa ko kaunar mulki ba,
Bai taba tinani ko kawo cewan zai taba hawa karagar mulkin boyem ba,
Baida abinda ya saba dashi ya zama cikon rayuwarsa kaman 'yanci da shimfida rayuwansa akan nasa matakan da raayin da juya rayuwansa yanda yaso wanda a yanxu shima a yanxu karagar mulkin tana kwace masa hakan daya bayan daya dan kuwa duk yanda zai tsara nasa dokokin da yin rayuwan dayake so dole tinda mulkin mutane ne akanka zaka aje wasu da yawan naka abubuwan da kake so ka kama na dokan mulkin.
Rufe idanuwansa da sukai jajir yayi yana jin a karo na babu adadi tinda ya hau shima bazai iyaba,
Bashi karagar mulkin jamaar boyem take buqata ba kaman yanda shima ba ita yake buqata ba kansa yake buqata a matsayin LEUL NUAB me Moscow,
Shi kansa Asim jajir idanuwansa sukai sosai yana kallan NUAB din zuciyarsa na danne duk wani irin radadi da ciwon dayake ji na rabuwa da qasarsa mahaifarsa dama mahaifiyarsa da abubuwa da yawa kuma tafiya da har abada ba dawowa sedai yaxo ganin gida ko wata hidimar ya koma amma ya gama zaman qasar.
Shiru sukai kafin NUAB ya dago idanuwansa ya kalli Asim ya kalli takardar ya maida idanuwansa akan seal din dayake kan table dake can gaban kujeran girmansa.
Nutsuwa ya sake yi ya tsaida idanuwansa akan Asim yana kallansa da dukkanin tinani da tausayin Asim din dashi kansa da yasan bazai iya zama sultan na boyem ba har manyanci da tsufansa ba dan haka bayajin xai taba iya saka hannu ya bari Asim yabar boyem din.
Bude baki yayi zaiyi magana bayan ya sauke numfashi yana tsayar da tinaninsa akan abu daya dan inganta rayuwansu duka aka bude office din.
Aleey ne ya qaraso gurinsu idanuwansa jajir yana hana kansa bayyanarda kowane irin tashin hankali sbd hana jinin sarautar biyu dake zaune shiga kowane irin tashin hankali ko shock.
Da sauti me kokarin bayyanarda kulawa ya sanar dasu ba lafiya ana buqatansu da gaggawa.
Asim dayaji hakan wani nauyi ne dayake kirjinsa ya fada sbd tinda ya zauna yake jin kirjinsa a toshe da nauyi me tsanani.
NUAB kuwa jin yayi duniyarsa dayake ji gabaki daya tin dazu a bushe ta qarasa bushewa tana rushewa.
Kallan Aleey yayi da jajayen idanuwansa sbd jin cikakken abinda yake nifi sbd yasan bayason bayani a taqaice.
Kasa kallan kwayar idanuwansa aleey yayi jikinsa na fidda rawa ya sanar dashi sultan ne lamarin yayi munin fada.
Bai qarasa ba NUAB din ya miqe tsaye yana nufar kofa da wani irin yanayi dake dumama wajen gabaki daya sbd har wani sauti me tada tsigar jiki takunsa ke bayarwa Asim ma na gefensa kusan a tare suke kowane taku cikin zafaffen yanayin daya saka Aleey shima tsananta shiga tashin hankali me tsananin gaske duk da babu wanda ya samu daman shiga cikin bangaren na sultan kadir ne kawai ya kirasa ya sanar masa dan haka ya shigo dan sanar dasu shikuma Keelah ya nufi can din.
Koda suka iso gabaki daya securities da bayin bangaren suna tsaye cak a kofa cikin matsanancin tashin hankali da tsoro da firgici me yawan gaske sbd wani irin magana da kadir keyi cikin matsanancin daga murya dake cike da mummunan tashin hankalin da basu taba jin ya shiga ba.
NUAB da idanuwansa suke wani zafi sbd ja basa kalluwa shine ya fara sako kai bangaren take kowa ya ja baya sosai suna qasa da kai masu zubewa qasa kuwa suna zubewa batareda dagowaba.
Kai tsaye keelah dake tsaye gurin ya bude masa kofa da sauri cikin yanayin qamewa shima
Saka kai NUAB din yayi yana shigewa tareda Asim wanda hannuwansa ke wata irin rawa hakama kirjinsa.
Suna shiga palon na kurya cikin matsanancin tashin hankali suka tsaya cak dukkaninsu sbd ganin kadir yayi kaca kaca da jinin sultan wanda babu alaman rai a tattare dashi kuma har lolacin jini fitowa yakeyi ta hancinsa.
Sarewa kafafun Asim sukai sbd tsananin rawan da suka dauka ya zube a gurin durqushe yana rarrafawa idanuwansa na cikowa da hawayen tashin hankali da tsoro da rikicewa duka a lokaci daya.
Shi kansa NUAB baya yayi kadan saida ya dafa qatuwar verse din glass dake gefensa ta fadi qasa da karfi ta fashe yana neman sake faduwa ya dafa bango da karfi idanuwansa na tsananta radadin da suke masa yaja wani numfashi me zafin gaske yana jin ihun kiran sultan da kadir yakeyi yana ratsa kunnuwansa zuwa kwakwalwansa.
Daqyar ya iya fizgo kansa daga halinda ya shiga na shock ya qaraso gurin cikin taku uku ya zube gaban sultan din yana cirosa daga jikin Kadir ya dawo dashi jikinsa gabaki daya tareda cirasa sukutum yana bude murya da karfin gaske ya qwala kiran aleey wanda amo me karfi ya amsa har zuwa wajen wanda kowa ya sake shiga faduwan gaba aleey kuwa kai tsaye ya shigo cikin rashin bata kowane irin lokaci.
Yana shigowa yaga halinda ake ciki Asim kuka yakeyi sosai yana kasa motsawa hakama kadir a cikin tashin hankali yake da baimasan me zaiyiba.
Hannuwansa na rawa ya ciro wayarsa ya saka kiran likitocinsu gabaki daya daya bayan daya.
Juyawa yayi ya fita yana kallan keelah yace a hana kowa shigowa ko fita daga bangaren da zagayensa ayi sauri a kira securities dinsu.
NUAB bedroom ya wuce da Sultan din da saurin gaske jikinsa na rawa shima kadir na biye dashi hakama Asim miqewa yayi da sauri ya bisu.
Da gaggawa NUAB yace a kawo towels
Jiki na rawa Kadir da Asim na karo da ture juna gurin sauri suka dauko daga inda towels din dakin suke a jere suka kawo masa.
Jinin hancinsa suke kokarin tsayarwa da goge fuskansa data rufe gabaki daya tai kaca kaca da jini Asim kuwa hannuwansa da suka sanqame ya riqe yana dannesu dan a tsaye suke qam.
Kaman Aleey zai tashi sama haka ya tada daren lafiyar masarautar gabaki daya gurin hana kowane motsi koda na dabbane yace a riqesa a inda dik zaa gansa sbd tsayar da komai kafin a samu sanin halinda sultan yake ciki,
Doctors kuwa take wainda ke cikin masarautar akai gaggawar tahowa dasu suna shigewa ciki da wanda yake na mata da wanda yake na yara da wanda yake na shuga da duk ma kowane iri haka aka janyosu tas aka zuba duka a cikin bangaren wanda dole suka taru akan Sultan din kafin isowan babban likitan da NUAB yafi yadda dashi wanda tini keelah ya buga mota cikin mugun speed yaje daukosa dan baa cikin masarautar yake ba shi.
Fitowa sukai suka bawa likitocin daman yin aikinsu akan sultan da babu alaman zai tashi koma ba alaman akwai sauran rai a tattare da jikinsa.
A palon da bedroom din nasa yake suke dukansu kowannensu jikinsa kaca kaca da jini da duk ya bata jikinsu da hannuwansu babu wanda yake jin daidai a kirjinsa sbd yanda suke jin fargaban abinda zai samu Sultan.
Aleey daya shigo NUAB ya kalla wanda idanuwansa suke cak akan kofar dakin yana zaune idon sunyi jajir ya qaraso gefensa ya tsaya yana ciro hankerchief me kyau da tsafta daya dauko sabbi kusan guda biyar ya miqa masa dan goge hannunsa da gefen fuskansa da har acan jinin yakai sbd yanda ya ringa rungumosa.
NUAB din bai karba ba rintse ido kawai yayi yana jin kansa kaman zai tsage biyu,
Abu biyu ne ke neman raba zuciyarsa biyu a lokacin shine tsoron rasa mahaifinsa a matsayinsa na 'da sai kuma tsantsar tsoron halinda Amminsa zata shiga idan ta rasa wani maqoyinta again a rayuwa sbd zuwa yanzu ya yadda da sultan shine wani babban bangaren dayake bawa Ammin farin ciki da nutsuwa.
Kadir ma kansa ne a qasa ya kasa dagowa yana zaune hannuwansa dake lalace ya hadasu guri daya ya riqe yana jin tsoron rasa ubangida kuma Amininsa kwalli daya a duniya tin kuruciya suna tare har tsufa.
Asim da idanuwansa suka gama kumbura da jajir a cikin qanqanin lokaci dagowa yayi ya kalli inda yaji motsi a gefensa Maminsa ta bayyana a gabansa idanuwanta a bushe tana wata irin rawar jikin daya sakasa ambatar sunanta sbd babu wanda ya lura da ita tinda suka shigo tana tsaye a guri daya.
Ambatar sunanta ya saka Kadir dayake cikeda tsananin tsanarta da jin zafinta dagowa ya kalleta yana miqewa tsaye shima Asim tsayen ya miqe sbd ganin kallan da Kadir ke mata me bayyanarda zallan tsana.
Aleey dake gefen NUAB zuba mata ido yayi yana gyara tsayuwa batareda NUAB ya dago ba.
#MAMUH
09033181070 HAYATEEM
Mamuhgee
170
Cikin tsananin daci da baqin ciki kadir ya kalleta yana bude baki yace
'Me yayi zafi da zaki shayar dashi poinson irin wannan?
Cak Asim ya tsaya daga qarasawa inda take yana kallan kadir da jajayen idanuwansa da sauri,
Aleey kuwa gyara tsayuwa yayi yana qarasa maida dukkanin hankalinsa akan abinda yake shirin faruwa tareda sake kallan NUAB yaga bai dago kai ba bare motsawa ko kallan inda hailen take.
Asim ma cikin sauri ya juya ya kalli NUAB din jikinsa na sake daukan sabuwan rawa ya dawo da kallansa akan kadir yana bude baki cikin mummunan yanayi yace
'Me yake faruwa?
Me ya faru?
Ya akai?
Menene ya samu sultan?
Ya kuma akai ya shiga wannan halin?
A rude duka yake jero tambayoyi a rikice yana kallan Kadir.
Wani sabon zufan tsantsan tashin hankali ne ya gangaro daga goshin kadir ya dago jajayen idanuwansa ya kalli Asim din ya bude baki yace
'Mummunan guba ta shayar da sultan gatanan a tsaye,
Ko dana iso tana tsaye a kansa tana kokarin qarasa shi da hannuwanta bayan da bakinta tana fadar idan gubar bata kashesa ba zata qarasa shi da hannuwanta....'
Baya Asim yayi cikin kasa yadda da abinda yake ji ya juyar da idanuwansa akan hailen da wani irin sauri muryansa na rawa yayi kanta ya saka hannuwansa duka biyu ya kamata yana kallan cikin idanuwanta da dukkanin imaninsa akan bazata iya aikata hakan ga sultan ba ya bude baki muryansa na rawa yace
'Mami ki fada abinda ya faru wanda ba abinda Kadir yake fada ba,
Ki fada mana meya faru?
Waye yayiwa sultan hakan?
Waye yayi wannan mummunan aikin?
Ki fada ba kece ba Mami...
Dagowa tayi ta kallesa da idanuwanta da sukai jajir itama suna taruwa da wasu hawaye masu zafin gaske ta bude baki tace
'Asim nice nayi sbd zuciyata bazata iya daukan ya zabi wata baiwa akaina ba.......
Sai a lokacin NUAB ya dago kansa cikin wani irin slow ya juyo yana sauke idanuwansa masu kaifi akanta a karan farko daya ke sanin asalin kamanninta da baima saniba,
Dagowa da juyowansa ya saka kowa tsayawa kallansa banda ita data riqe Asim dake neman sarewa qasa sbd abinda ta fada jikinta na rawa muryanta na rawa dukkanin haukacewanta na bayyana idanuwanta na rufewa kaman yanda zuciyarta ta rufe ta qanqame hannuwansa tana cewa
'Asim shine yayi sanadin halin dayake ciki,
Shine ya zabeta akaina,
Shine ya zabi 'danta akan nawa dan,
Shine ya zabi binta qasarta yabar qasarsa da ni da yayana,
Shine yace yana sonta,
Ita yake tsananin so ba ni ba,
Sbd ita ya sauka mulki sbd ita a yanzu komai na rayuwarsa yake tafiya,
Na tambayesa yace Allah ne ya saka masa hakan dan haka bazan iyaba na zabi mutuwa tareda shi sbd nasan nima mutuwar zanyi gwara na fara turasa.....
Miqewa tsaye NUAB yayi sbd yanda kalamanta ke jijjiga kwakwalwansa suna tsinka jijiyoyin jikinsa.
Yana miqewa Aleey ya saka kiran keelah a wayarsa ya bada umarnin a kai securities bangaren queen haile ba ba wanda zai sake fita daga bangaren har yayanta.
NUAB kallo daya yayi mata da idanuwansa bayan ya miqe ya dauke idanuwansa sbd abinda yakeji zai iya fasa kanta da hannunsa a gurin take dan haka juyawa yayi yana fuskantar kofar dakin da sultan yake yana kasa cewa komai tukuna.
Kadir ma baqin ciki da tashin hankalin abinda take fada sakawa yayi ya rasa abin fada ya juya baya yana dafe goshinsa da hannuwansa tareda rintse idanuwansa.
Asim kuwa da yayi mutuwan tsaye sbd tashin hankali sakinta yayi yana ja da baya ahankali tareda rintse idanuwansa hannuwansa na wata irin rawa,
Kafin ya iya dawowa daidai daga tashin hankalin daya shiga NUAB ya bude baki batareda ya juyo ba yacewa aleey akaita bangarenta a rufeta a cikinsa ya sallami duka bayin dake bangaren da duk wani me rai dayake ciki ita kadai zaa bari a rufe bangaren ba shiga ba fita tukuna.
Asim na jin hakan wasu hawaye masu tsananin zafin gaske suka gangaro masa ya rintse ido ya bude yana tabbatarda Allah ne kadai a yanxu zai fidda mamin daga wannan kaddara data jawa kanta me muni.
Aleey da daman jiran umarnin yake wayarsa ya daga zai saka kiran wainda zasu shigo su tafi da ita Asim kallansa yayi cikin wani irin mutuwan jiki yace ya bari zai kaita da kansa.
Hakan daya fada ya saka kadir kallansa hakama aleey din.
NUAB kuwa buqatan a fice da itan yake ba bata lokaci dan shaqar numfashin tsayuwanta agurin kadai toshe kirjinsa yakeyi yana neman saka masa kasa iya riqe kansa gurin mata illa.
Asim hannu ya miqa ya kama hannunta yayi gaba da ita tafara tirjewa tana kokarin kwacewa da karfi tana ihun ambatar bazata tafi koina ba sai likitocin sun fito sun sanar da mutuwar sultan.
Yanda take maimaita kalman da karfi tana kwacewa tana tirjewa Asim yana janta ya saka kadi binta a bayan yana turata cikin zafin zuciya da baqin ciki hakama aleey yana bayansu dan tabbatarda ta isa inda akace a kaita din.
Kuka takeyi sosai tana ihun fadan jiran labarin mutuwan sultan din sbd mutuwan ce ta dace dashi,
Mutuwansa ce zata saka ayanah ghaz a cikin baqin cikin datake son ganinta.
Tsit koina yayi ihun maganganunta ne kadai suke amsawa koina tana fada da karfin gaske dan NUAB yaji shima baqin cikin datake ji ya kashesa.
Asim kuwa hawaye yake fiddawa masu radadi da baqin ciki yana kasa sakin hannunta tana dukansa tana son kwacewa amma ya kasa sakinta haka ya nufi bangarenta da ita Aleey da securities da fadawa marasa imani suna biye dasu.
Tin kafin su iso su Aslam da aka fito dasu suka nufo hanyar cikin babban tashin hankalin da basu taba shigaba sbd jin abinda ya faru.
Cikin tashin hankali da tsoron gaske suka yo kanta tana ihu har lokacin tana jin idan bata ji zancen mutuwar sultan da kunnuwanta ba zata iya mutuwa sbd baqin ciki.
Kuka me karfin gaske dayake hade da mummunan tashin hankali Aslam ta fasa tana kokarin kama Mamin itama amma sam idan mutuwan sultan zaa fada mata ba batason komai.
Shigewa akai da ita bangaren har tsakiyar palonta Asim ya jijjigata da karfin gaske yana ambatar sunanta da karfin gaske yace
'Mami ki dawo hankalinki sbd Sultan bazai mutuba insha Allah,
Bazaki taba saka Ayanah baqin cikin da kikeson gani a tattare da itaba sbd ta dade da shiga kowane kalan baqin cikin rayuwa,
Babu sauran baqin cikin dazaizo mata a ayanzu da bata taba shigarsaba,
Zatai baqin ciki da radadin rasa Sultan idan ya rasu amma bazata mutu ba zata rayu kuma hankali zata dawo farin ciki sbd haka rayuwan take dan haka bazaki iya saka mata dawwamamman baqin ciki ba idan ba Allah daya halicceta ba,
Kin aikata babban kuskuren da daga lokacinda kika shayar da uban