Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   67 / 100

198K to 201K   out of 299.8K words

na iya kokarinsa gurin yar sakewa da dan uwansa sabanin Leylah da hankalinta yake kan bahar da har lokacin bata dawoba.

Shi kansa Asim hankalinsa na kan dawowan Bahar din wanda duk leylah na lure dashi takaicinsa duk yabi ya sake ciketa sai tsoki mara sauti take saki yana sane da ankare da ita amma yaki ko kallanta jira yake su koma yaji dalilin rainin wayon abinda take masa.

Abinci aka gama shiryawa a dining suka dunguma dukansu suka zauna suna kokarin farawa Bahar ta dawo gidan ta hanyar jin shigowan mota ya saka sukasan itace dan haka kasa fara cin abincin sukai duka su biyu suja juyawa ga kofar.

Cikin nutsuwa aka buga kofar wadda ta saka Maa sakinah da Maa tenya suma dakatawa suka juya ga kallan kofar sbd sanin ba Bahar bace sbd ita bata buga kofar sedai kawai ta bude ta shigo,

Faduwa gaban Maa tenya da sakinah sukai a lokaci daya sbd sanin ba kuma ayanah bace sbd ko yanzu basu jima da gama waya da itaba tana Liverpool haryanzu to waye kuma dan suna cikin matsanancin yanayin da basa buqatan zuwan kowa idan ayanah bata dawoba.

Asim kuwa zuciyarsa tafi ta kowa bugawa sosai sbd idanuwansa har wani sauyawa sukai tamkar hawaye zasu ciko a cikinsu sbd tsananin shauqin son ganin bahar wadda ganinta kawai zai saka zuciyarsa sanyaya.

Leylah ma da faduwan gaba take tsananin son ganin bahar din dan haka dukansu kafe kofar sukai da ido babu ko kyatawa.

Sake buga kofar akai kafin kai tsaye aka budeta gabaki daya wanda iska ta kado musu qamshin daya saka dukansu miqewa daya bayan daya idanuwansu na kasa daukewa daga kofar,

Aleey dayake gaba shine ya fara sako kai yana qarasa budewa mai boyem din kofa yana sako kai a natse cikin wata sanyin iko da izza tareda kamewan datake qafar da yawun bakin dukansu.

A daidai wannan lokacin karfe 9:30 ta buga kuma a daidai lokacin motar bahar ta shigo gidan tana kallan motoci biyu dake harabar gidan zuciyarta ta fada mata Amminta ta dawo bata fada mata ba dan haka da sauri ta fito motar tana sanye da purple Milan palazzo mai tsananin fadi da vneck chiffon shirt da ake ganin vest din kayan daga ciki sai scarf na versage da hanbag dinta ta lv tayo cikin gidan da sauri ta fado palon tana qwala kiran Ammi kowa na tsaye cirko cirko zuciya na bugawa ba dadi.
#MAMUH
09033181070


HAYATEEM
Mamuhgee

121
Kowa kasa motsawa yayi daga inda yake bayan sun mimmiqe tsaye dukansu,

Kusan dukansu tsoro ne mai tsananin ya cika gangar jikinsu da zuciyoyinsu sbd shine mutum na karshe a duniya da zasuyi tsammannin gani a wannan ranar kuma a daidai wannan lokacin,

Shi kanshi Asim tsoro ne yaji ya shigesa mai tsanani na bayyanar NUAB din gidan sbd kai tsaye sunsan meya kawosa koda kuwa su Maa sakinah su basu taba kawo hakan ba sbd ganin wa yake aure.

Naimar gurin gabaki daya daukewa tayi tai wani irin tsit dumi da tiririn gaske yana tirnike yanayin kuma har lokacin ba wanda ya motsa ba wanda ya bude baki,

Idanuwansa da suka gama kallansu daya bayan ya tabbatarda ko waye da waye a gabansa ya dan rufe su ahankali sbd sauyawan da suka fara suna wata irin yajin da zai iya saka kafafuwansu kasa daukansu daidai wannan lokacin ne itama bahar din ta fado palon tana kwala kiran Ammin wanda har cikin kirjinsa sautin muryan ya keta yana yankarsa akan radadin dayake jin kansa na dauka da zafi,

A rikice cikin wata irin shock ta tsaya cak bayan ta iso tsakiyar palon ganin Aleey da shine yake facing kofa take komai nata ya fara dena aiki daidai yana slow ta kasa juyawa bangaren datakejin qamshinsa na bugowa ta tsayar da idanuwanta akan su maa dake cirko cirko.

Kan Asim ta saukar da idanuwanta shima tana kalla cikin tsananin mamakin ganinsa suna hada ido yayi saurin dauke nasa idanuwan duk kuwa yanda yake cikin tsananin son ganinta kaman zai rasa rayuwarsa amma yana ganin yanda idanuwan Aleey suke kafe akansa haka ya hakura ya danne maitarsa yana dauke ido sbd yana tsananin buqatar rayuwa da ganinsa maana da idanuwansa a yanzu,

Bahar daqyar ta iya daga kafafunta ta isa bayan Maa sakinah a hankali ta dan rabe wanda takunta ya sakasa bude idanuwansa da sukai jajir akanta ya qare mata kallo ita da sitirar sake jikinta kafin ya juya kansa ya kalli agogon dayake dakin da wani kallan dayake na tsantsar isa da bacin rai ya duba time karfe tara harma da rabi na dare sai a lokacin take dawowa gida,

Shine ya yanke shirun wanda ya wakana sbd iyayen nasa babu wanda ta iya samun abin fada sbd basu gama fitowa shock ba ya bude bakinsa da muryan datake bayyanarda tsantsar bacin ransa dayake iya kokarinsa gurin dannewa a lokacin a natse da kamewa yace

'Na same ku lafiya?

Maa sakinah ce tayi karfin halin amsawa tana kokarin takowa ta qaraso tsakiyar palon daga dining din zata jefa wata maganar ya sake furta

'Ammi fa??

Cak ta dakata tana fasa qarasowa gurin nasa ta kallesa tana kokarin nemo maganar da zata fada a bakinta.

Kafeta da ido yayi yana jiran amsarta wadda babu dan haka ya juyar da kallansa akan maa tenya yana jiran ko zata basa amsa itama shiru tayi tana kasa ma kallansa sbd nauyinda take ji duk da shine 'da gaskia ayau suna jin nauyi da kunya harma da shakkarsa sbd anyi masa laifi mai girma.

Jin shiru ya sake ratsa gurin ya dauke idanuwansa daga kan tenya din ya saukesu akan Bahar wadda har lokacin taqi dagowa ta kalli inda yake sbd yanda kirjinta yayi nauyi.

Bai sake iya dora idanuwansa masu daraja akan shigar datake jikinta ba sbd loosing control na tsantsar bacin rai dayaji yanayi wanda ya sakasa juyawa kai tsaye ya fice idanuwansa da jijiyiyin kansa da suka fito sunyi jajir fushi da bacin ransa me karfi daya jima baiyiba yana tasowa ya gauraye jininsa gabaki daya da idanuwansa.

Aleey daya san tsantsar bacin rai da baqin ciki me tsanani baya saka NUAB magana indai akan manyansa ne sbd komai zai iya faruwa yana ganin NUAB yanayin NUAB din ya sauke kansa qasa sbd aya fushi da bacin ran LEUL yau ya bayyana dan haka yana juyawa baice komaiba shima ya bisa din suka bar gidan a motocinsu tareda securities dinsa.

Yana ficewa Asim ne ya fara sauke ajiyan zuciya mara sauti yana kallan leylah datai mutuwar tsaye gurin kallan NUAB din zuciyarta na bugawa da karfi sbd ya dade bata gansa ba a fili yayi sauyawan data qarasa kasheta gabaki daya akansa,.

Yayi wani irin fresh da duk hasken fatarsa saida taga kaman ya qara haske ya zama cikakken kamilallan namijin dayake juya qasa guda a hannnunsa tamkar manyanci ma ya shigesa hatta fushinsa daya bayyana a tattare dashi da tsananin bacin rai qara masa wani kyau da tsari yayi dan hakanne ma harya fice bata iya dauke idanuwanta akansa ba bare motsawa.

Takaici sake cike Asim yayi yanda ita gabaki daya duk shock da halinda suka shiga bata shigaba matacciyar soyayya ce a idonta dan haka hade fuska yayi tareda dauke kallansa akanta yana juyawa gurin maa sakinah zai kalli Bahar dinsa shima sai yaga wayam bahar din ta silale ta gudu daki sbd halinda ta shiga itama wanda hadda tsoro da shakka a cikinsa hakama ba qaramar bugawa kirjinta keyiba tana jin yawun bakinta suna kafewa har lokacin qamshinsa take ji a hancinta yana shigarta duk da bata iya yadda ta kallesa ba sbd bayyanarsa a rayuwarsu yau yazo a bazatan da takasa ma tinanin komai kawai dai dukansu gidan duniyar ta tsaya musu cak.

Baqin ciki ne ya sake tirnike zuciyar Asim ganin ba bahar din dan haka a fusace yana dan boye zafin kalamansa ya kalli leylah yace

'To mu tafi ko'

Juyowa tayi ta kallesa cikeda zafi itama sedai ganin su maa da hankalinsu baya kansu ya sakata itama dan tausasa nata kalamin tace

'Kaje anan zan kwana'

Kallan baki isa ba yayi mata sbd bazai yadda ba ta fisa morewa ba wato ita ta kwana anan taita ganin Abincin zuciyarta shi kuwa yana can abanza kenan ita ya rako ma dan haka sake daure fuska yayi yace ta wuce kawai su tafi sa dawo goben ai.

Zatai gaddama cikin bayyanarda rashin mutuncinta Maa sakinah ta bude baki a sanyaye tace tayi hakuri tabi mijinta din sa dawo daga baya.

Bude baki tayi zatai magana Maa din ta katseta tana tabbatar mata data tafi din dan haka ba yanda ta iya bayan shirya ta tattaro suka fice.

Komawa dukansu sukai suka zauna a hankali a natse tareda kallan juna a sanyaye dukansu suna jin rashin dadin batawa NUAB din rai sbd yanayinsa ya tabbatar musu da yakai maqurar bacin rai da fushin da bazai iya magana shiyasa ya juya kawai ya tafiyarsa.

Tenya ce ta bude baki tana cewa

'Gashi ba samun Ayanah akeyiba idan ba itace ta kira da kanta ba bare a fada mata isowan NUAB din sbd dai a yanzu ni bansan me zan fada masa gobe ba idan ya sake tambayar'

Numfashi maa sakinah ta sauke a natse kafin ta bude baki tace

'Allah yasa dai ficewan da yayi komawansa kenan Moscow bazai dawo ba sbd shine mafi alkhairi a lamarin yanxu dan gaskia nima bazan iya qara masa bacin ran fada masa ba.'

Miqewa tenya tayi tana zuwa daki ta dauki wayarta ta sake gwada kiran ayanah din ita kuma sakinah miqewa tayi ta nufi dakin Bahar sbd dubota taji abinda ya sakata kaiwa har 9 yau bata dawo gida ba gashi an hadu da tsautsayin da basusan wace makomar zasu fuskanta ba duk da kila fushin samun Asim a gidan da rashin samun ayanah zai boye nata lefin da baima ankare ba tukuna.

Ko data je bahar ta lallaba ta shiga wanka da sanyin jiki dan haka bata tsaya ba ta fice itama taje ta dauki wayarta ta fara kiran NUAB din dan bada hakurin da zai sassauta lamarin amma tana kiran farko taji wayoyinsa duka a kashe dan haka ta gwada kiran aleey wanda shima a kashe ta jisa abinda baayi kenan jin wayarsa a kashe sbd shine kunnuwa da idanuwan NUAB baya taba yadda ajisa kashe matiqar ba yana sama ba cikin jirgi kenan.

Cikin damuwa me tsanani da rashin sanin abin yi suka zauna sunata zabga kiran Ayanah amma babu alaman zasu samu hakama tenya datake iya magana direct da sultan shima kiransa takeson yi amma tana kasawa dan batada hurumin kiransa tace a bawa ayanah sannan kuma ta fadawa ayanah ta dawo NUAB yazo duka a sultan din sam bazai yiyuba dan haka kadir ta ringa kira shi kuma wayarsa na silent yariga ya kwanta ma a lokacin.

Sake shiga tashin hankali sukeyi dare na kutsawa ba wata makama kuma sun tabbatarda NUAB matiqar ba wucewa yayi ba da bacin ran daya bar gidan to zai dawo sake buqatar ganin Amminsa ayau din su kuwa babban tashin hankalinsu kenan sbd badai zasu iya fuskantarsa su sanar dashi bata nan ba tsawon lokaci kokuma batama uk din wanda suna fadar hakan sai sun fada tareda wa take wanda abu ne da bazai yiyu jinsa a bakinsu ba sbd bazasu iya dauka da kallan fushinsa ba zaiyi muni koma yayane su gwara iyayen nasa su fuskancesa da kansu.

Da wannan tashin hankalin da fargabar tareda zullumi suka ratsa daren suka kwana har safe a zaune suna sakawa da warwarewa ga bangare daya damuwar maa sakinah biyu ce tana tsananin tsoron ace NUAB ya ankara da bahar da lokacinda ta dawo din dan haka taketa adduar masifar ta tsaya a iya guri daya.

Ita kanta Bahar a daren duk da ta dawo da yunwa sbd wani class ne na fashion design da sukai joining ya sakasu kaiwa dare sosai sbd kayan amarya da akai designing a gurin wanda dukansu aiki suka kusan wuni sunayi kasa fitowa cin abinci tayi ta lafe a dakinta har lokacin zuciyarta bata koma yanda take bugawa ba daidai.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

122
Koda washe gari tayi safiyar ta waye babu wanda ya samu kuzarin fitowa da wuri suna dakunansu a lafe suna jiran kowane irin tsammani,

Bahar ma lafewa tayi taqi fitowa sam sbd batama son tsautsayin dazai saka su hadu harma ya ankare da ita matsalolinta su dawo zata jira a gefe taji idan ya wuce kenan tukuna,

School ma bata shirya ba sai guraren after 10 ta fito a shirye tareda nufar kitchen tayi breakfast sama sama acan ta fito ta nufi dakin su maa din tana budewa suka bita da kallo kowacensu da waya a hannunta sunata fama da abu daya,

Tenya ce ta fara amsa gaisuwanta tana tambayar ko tayi breakfast tace eh tayi karta dade kaman jiya ta fada mata tana taqaita zancen anan sbd batason bahar din ta wani fahimci halinda suke ciki duk da a bayyane hakan yake suna cikin tsananin damuwa me karfi.

Maa sakinah kuwa tasowa tayi tana gyara mata rolling din dayake kanta na blue qaramin veil din doguwan shaped bahrain gown dake jikinta bata kamata ba sam suka yo palo tana jin sam batason yau bahar din ta fita koina koda school dinne kuwa sbd su fara tabbatarda ya wuce gudun dora wata fitinar akan wata dan kuwa a yanda yake yanzu wuta ne ke cinsa dazata iya kona komai.

'Bahar ko zaki hakura da school dinnan yau da gobe ne mu jira NUAB ya tafi'

Kallan maa din tayi tana dan marairaice fuska sbd tana buqatar tafiya school tabar gidan dan bazata iya barin ya taho tana gidan ba wanda a yanzu hakan haryanzu palonsu qamshinsa yakeyi dan haka gwara ta tafi idanma yazo batanan bata gansa ba bai ganta ba idan ya wuce din kuma shikenan.

Numfashi maa ta sauke ganin yanda bahar din ta narke dan haka sai kawai tace

'To ana tashi yau kada kije kowane class na komai da kuke zuwa ki tabbata kin dawo gida kai tsaye.'

Batareda taso hakan ba tace ok tareda nufar kofa ta fice.

Tana fitowa yau bata tadda Ari ba wanda bai taba fashin zuwaaba tinda sassafe kuwa sai dare yake tafiya.

Time ta kalla batason kiransa sbd kada ta janyowa kanta attention din yaransa dashi kansa dan kuwa tasan dole Ari hanasa zuwa akai ko kuma akwai wani dalilin dan haka ficewa tayi kawai ta hau mota ta tafiyarta.

Tana tafiya su Maa sakinah suka fito daqyar suka iya breakfast suka shishirya dan zaman jiran tsammani kaman yanda suka fada,

Karfe goma sha daya daidai su Leylah suka iso gidan tareda Asim wanda gabaki daya ya qarasa zama wani irin kamar sakarai dan kuwa sai baza idon neman bahar yakeyi ya samu ya kalleta son ransa yayi magana da ita kafin wani abin ya kuwa zuwa ya giftawa jin dadinsa,

Ita kanta leylah a zaune take suna fira sama sama dasu maa amma hankalinta a rabe yake kaman yanda nasu yake a raben kowa hankalin rabi anan rabi a wani gurin.

Suna wannan zaman ne wayar leylah tayi ringin ga mamakinta number ce kaman bazata dauka ba sai kuma ta dauka Shuraim taji take ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla taga numbern qasar ce da sauri ta maida kunne tana tambayarsa yana ina ne?baya boyem?

Fada mata yayi yana uk ya kasa samun numbern Ammi hakama yanata kiran wayar Maa sakinah baa dauka yanason zuwa gidan ne ta turo masa numbern maa tenya.

Wani yawu ta hadiye da karfi tana jin rashin dadin zuwansa sbd zuwansa zai iya hanata sakewa musamman tinda tasan shima meyake so wanda harga Allah tafison Asim ya samu bahar a maimakon shi dan uwanta sbd Asim ya samu bahar shine zata samu yancinta na abinda takeso hakama tafison Bahar tayi takaba idan Asim ya tafi a maimakon ta auren dan uwanta da zata samu rayuwar soyayya me kyau.

Badan taso ba ta masa sharing location nasu baiyi awa uku ba kuwa sai gashi a gidan ya iso cikin kwanciyan hankali shima kuma tin acan yake mamakin abinda su leylan sukeyi a gidan bayan honeymoon zasu tafi.

Su Maa da ayanzu gabaki daya basa murnar zuwan kowane baqon hakanan suka daure suka danne suka tarbesa da nuna farin ciki sosai dan haka gidan ya dauki haramar murna da yar hayaniyar farin cikin baqi da suma baqin kowa ke cikin farin cikin kasancewa a gidan.

Shuraim kai tsaye shi kam ya tambayi bahar aka sanar dashi tana school dan haka ya ringa kiyaye time dan jiran dawowanta.

Shiru shiru su maa suna jiran jin ta inda NUAB zai bullo ko a zahiri ko a kiran waya amma shiru dan haka suka dan sassautawa kansu suna kokarin sake sakewa a cikin baqin nasu da duka dai na gida ne.

Karfe uku Bahar ta dawo gidan zuciyarta na dan shiga yanayi na fatan basada kowa a gidan,

Tana sako kai a palon yar hayaniyar datake jiyowa ya sakata jin kirjinta yayi nauyi amma sanin ba NUAB bane ya sakata qarasowa tana kallan palon sbd idan shine tin a gate zata ga motoci da securities nasa hakama sam bazaa samu kowace hayaniyaba a duk inda yake a guri.

Ganin Shuraim da idanuwanta suka fara sauka akansa ya sakata sauke ajiyan zuciya me dan karfi tana maida kallanta akan maa sakinah data gode Allah bahar din ta dawo kafin zuwansa duk da sun cire rai sun tabbatarda ya wuce.

Da tsananin farin ciki da sanyin zuciya shuraim yake kallanta yana mata barka da dawowa itama kokarin sake fuskarta tayi sosai tana masa barka da zuwa kafin ta juya ta kalli Asim wanda kusan yayi mutuwar zaune a gurin kallanta tai masa barka da zuwa shima tukuna ta kalli leylah ta masa sannu da zuwan wanda duka basu samu sunyiba jiyan.

Gaggaisawan da sukai idanuwansu duka akanta ya sakata kasa zama a cikinsu ta wucewanta daki dan cire gajiyan data dawo da ita.

Leylah data kafe bahar da idanuwanta harta shige wata nauyi taji ya danne kirjinta sbd babu wani abu daya rage a bahar din data sani baya dayake tareda ita a yanzu sbd gabaki daya ta sauya sauyawa kuma ba qarama ba dan kuwa hatta skin tone nata ya tashi daga fara zuwa kaman butter dan kuwa har wani daukan ido takeyi ga wata irin calmness da class tareda basarwa kaman ita kadai ce 'yar sarauta a gurin,

Suturar jikinta da duk abinda yake jikinta babu wanda ba original designer ba,

Sake

67 / 100