numfashinta na daskarewa hakama raunikan farko dataji ya qara goge mata sun qarasa damage wata zafin da kanta yake kasa dauka yake ratsata ba daman iya ko daga hannu hakama jini take fitarwa kadan kadan wanda yake na rauni dana rabata da budurcinta me karfi da yayi suka hadu harma dan jinin ya samu fitowa.
Shi kansa wata rawa me tsananin karfi da jijjiga jikinsa yakeyi wanda take na kakkarfan zazzabin da bai taba ji ba a rayuwansa ya rufesa take ko idanuwansa baya iya budewa ya dunqule guri daya da ita a jikinsa zazzabin juna me karfin gaske yana ratsa fatar kowannensu daga junansu.
Ita nata masifaffen halin datake ciki ko motsi batayi tamkar ma ta mace ba sauran rai a jikinta sabanin ji nasa yanayin jijjiga yakeyi na karfin zazzabi wata zafi tana hurowa daga jikinsa da numfashinsa a take kuma yana rasa kowane karfinsa gashi a lokacin Alarm na sallan asuba ya fara kara mara karfi me sanyi a hankali ahankali.
Kasa iya motsawa yayi bare iya bude ido har alarm din ya gama kuka da kansa yana sake qanqameta a jikinsa dayake rawa sosai.
Lokacin sallar fara wucewa yayi batareda sauki ko daya yazo masa ba hakama ita dayaji bata motsi a jikin nasa yafi komai girgizasa dan haka cikin wata masifaffen karfin hali ya tashi ya zareta daga jikinsa sbd ya isa toilet cikin matsanancin jiri ya sakarwa kansa ruwan zafi ko zai iya dawowa daidai ya dan samu karfi.
Sosai ruwan zafi suka dakesa amma har lokacin jikinsa rawa yakeyi dan haka wanka yayi ya fito daure da towel cikin tsananin karfin hali.
Kaya masu kauri ya saka sweatset Ash na Balenciaga yayi Sallah batareda doguwar adhkar ba ya miqe ya isa gareta ya tattarota jikinsa yana jin jikinta da zafin sosai itama hakama babu alaman da sauran rai a tattare da ita dan haka bazai iya daukanta zuwa toilet ba sbd kada ya mata abinda ba shine akeyiba sai kawai ya maitada kwance ya saka mata riga tareda rufeta cikin tsananin kulawa da duvet har lokacin shima jikinsa na rawar halinda yake ciki.
Wayarsa ya miqa hannu ya dauka daqyar ya nemo numbern maa sakinah ya saka mata kira.
Maa sakinah dake zaune akan daddumar datai sallah daman a daren cikinsu ba wanda ya rintsa tinani da fargaba kala kala ne a ransu na rashin ganin bahar duk da sun sakawa ransu tana gurinsa amma sai gari ya waye zasu tabbatar tinda dukansu su biyun bame iya tambayarsa sbd a kiyaye suke dashi sbd su masu laifine a gurinsa yanxu su duka uku iyayensa,
Tana ganin shigowan kiran wayarta faduwa gabanta yayi sbd shakka da zullumin dalilin kiran nasa a wannan lokacin kodai shima Bahar dince bai gani ba zai tambaya???
Daukan wayar tayi jikinta na mutuwa tareda yar zaquwan jin Allah yasa ba Bahar zai nema ba sbd a yanzu tafara tinanin ko Bahar ta silale tabi neesah dan hakanne ma suke jiran gari ya dan fara wayewan su kira Neesah suji.
Tana dauka bai iya cewa komaiba kai tsaye sai
'Maa kizo ki dubata idan akwai abinda take buqata na gaggawa'
Shiru maa din tafara yi sbd bata fahimci me yake nufi ba tace
'Waye ba lafiya?
Bahar ce?
Tana gurinka ne tin jiya fa mun kasa ganinta bare sanin inda take...
Katseta yayi cikin sauti me sanyi da rashin karfi tareda rashin son hayaniya yace
'Maa pls'
Kashe wayan yayi yana kashe Aircon naa dakin gabaki daya ya saka safa ya ziro gucci slippers mara nauyi ya fito yana kiran Aleey sbd yana buqatan ganin likita da gaggawa shima ita kuma zaifi nutsuwa ne idan su Maa suka dubata suka mata abinda shine zatafi buqata wanda shi baisaniba.
Maa data kasa fahimta kanta ma taji kaman ya toshe sai kuma taji tsoro ya kamata sbd tabbas wani abin ya samu bahar tinda suka samu wayarta a kofa yashe kenan kilama yanke jiki tayi a gurin ta fadi.
Miqewa tayi da sauri tana kallan Tenya da itama akan daddumar take tafara mata bayani tana nufar kofa tayi gaba kafin tenya da batada aiki sai kiran Ayanaah amma matiqar ba itace ta kirasu ba basa samunta dan haka ajiye wayar tayi bayan ta kira ba sa'a tabi bayan Maa sakinah din suka dunguma zuwa dubowa zuciyarsu a cikeda tinani kala kala na abinda ya samu bahar amma ko a tinanin bacci basu taba kawo tinanin ma wai wani abin auren zai shiga tsakanin NUAB da bahar dinba tinda baa zauna ma akasan matsayar aurenba hakama kuma wai a gidan da suke ciki gidan da Amminsa take a dakin da suke cikin gidan kwance suna bacci ba.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
127
Dakinta suka fara zuwa suka dubo amma bata ciki dan haka kai tsaye suka juya zuwa nasa din da tinanin baya nan dan bakin gaskiyarsu ma basu yadda da a gidan ya kwana ba tinda basu san shigowansa ba bai kuma nemi kowannesu ba daya shigo da daren,
Suna sako kai hanyar palon dakin yana fitowa sanye da hulan sanyi me kauri gashin kansa a sake sbd sanyin dayake ji,
Da mamaki me tsanani tenya ta kallesa sbd da gaske dai a gidan ya kwana kenan,
To meya hadasa da Bahar a dakinsa kuma idan batada lafiya?
Gaidasu yayi a taqaice sbd yana buqata ficewa yaga doctor din da already aleey harya kirasa yana jiransu a asibitinsa sbd NUAB din baya buqatan zuwan kowane doctor gidan.
Wucewa yayi ya fice yabarsu tsaye kafafuwansu suna sanyi sbd zuwa yanxu sunji fargaban shiga yana kamasu sbd koma yayane kila akwai matsala me girma.
Maa sakinah fasa shiga tayi ta dakata tareda kallan Tenya tace taje ta duba sbd dakin NUAB ba gurin shiga bane kai tsaye musamman a yanzu da yake riqe da mulkin masarautar qasa a hannunsa,
Juyawa tayi ta koma main palo ta zauna tana jin zuciyarta na rasa dukkanin nutsuwa,
Itadai indai ba wani abin ne me muni ya samu bahar ba to da sauki a gurinta dan duk abinda zaisa ace sai an nemowa bahar masu ceto ko taimako me girma ne sbd tanada juriya akan komai.
Tenya saka kai tayi a natse a hankali ta shiga tana tsayar da ganinta a hanyar datake bi sbd kaman yanda Sakinah ta fada babu wani isashen dayake da dama ko ikon ganin makwancin Sultan idan ba masu gyarawa ba da suma kansu a qasa yake sai kuma macensa shi kuwa NUAB yanxu baida macen dan haka sai sun kiyaye dokokin da al'adunsu koda kuwa basa boyem tinda su yan can ne.
Ko data shiga bata ga kowa palon ba dan haka wani karfin hali tayi tareda shahadar isa kofar master bedroom din ta saka hannu a natse ta kwankwansa tareda ambatar sunan Bahar din,
Shiru ba alaman ko motsi ya sakata bude dakin kai tsaye ta shiga babu abinda a dakin bai cika da qamshin NUAB dinba da kosu da suke iyayensa sunsan kamshinsa basu kadai ba duk wanda ya sansa to zaisan qamshinsa sbd abune da baya boyuwa a duk inda yaje.
Tashin farko akan gadonsa taqi sauke idanuwanta saida ta duba kan sofa da qasa taga bataga bahar ba tukuna ta juya ta sauke idanuwanta akan gadon wanda take ganin bahar tamkar a mace ya sakata isa da wuri sbd har lokacin bata kawo a kanta NUAB ma yana akan aurensa ba bare kusantar Bahar din a cikin gidan da suke...
Tana isa bata taba gadonba ta saka hannuwanta ta kamo na bahar din ta janyota gabaki daya jikinta take idanuwanta suka sauka akan abinda ya sakata kusan sakin Bahar din sbd shock da rikicewa ma,
Dauke idonta tayi da sauri a karan farko dataji hankalinta ya tashi akan irin wannan muamalan da itace aikin a boyem na shekaru masu yawa wato gyara mace ta kaita a keto ta tadawo ta wanketa ta kuma gyarata ta kuma kaita,
Bata taba jin komaiba ko kunya ko fargaba ko rikicewa sai ayau da idanuwanta suka ganar mata abinda bata taba tsammani ba kuma daya 'dan dayake nasu dan haka kunya ta qarasa rikitar da ita din ya janyo bahar da karfi tana kallan jinin dayake a shimfidar wanda ya tabbatar mata da aikin ba qarami bane hakama aikin bana wasa bane.
Karfinta ta saka ta ciccibi bahar din gabaki dayanta bayan ta saka mata abu ta rufe jikinta sosai ta fito da ita hankalinta a tashe da mamaki,
Maa sakinah na ganinsu ta miqe da sauru kafafunta na dan rawa tayo gurinsu tana bin bayan tenya din sukai daki bahar din da sauri maa sakinah na bin zanin gadon dake jikin bahar din wanda ya baci sosai da digo digon jini tana jin kanta na nauyi ta maida idanuwa akan bahar din da sauri suna qarasa shigewa dakin suka rufo.
Toilet suka nufa da ita maa sakinah ta fito tabaro tenya wadda ita aikinta ne daman koba yanzu ba koba anan ba duk ranar da NUAB dayake sultan ayanzu zai fara kasancewa da matarsa al'adace itace zata gyarata takai masa ita har chambers nasa dan haka ko yanxu maa sakinah ita kam bazata iya ba bar mata tayi duk da dawowa tayi ta zauna cikin wata irin tashin hankali da zullumi tareda tsananin tausayin 'yarta bahar da dukkanin alamu suka sauka bata samu lamarin ta sauki ba.
Asubar da leylah ta kwana tana jiran tayi lokaci nayi kuwa taje tayo alwala tai sallah tanajin motsi ta fito da sauri sbd bata rintsaba a zaune kamar mayya ta kwana tana tinanin da suka fi dubu a cikin kanta,
Tana fitowa bata ga kowa a palon ba sbd sun riga sun shige dakin Bahar din duk da haka bata komaba dakin su Maa sakinah ta nufa dan dago musu hankali su fito a nemi jin inda Bahar take dan ita sai sai taji inda take hankalinta zai kwanta,
Ga mamakinta ba kowa a cikin dakin dan haka fitowa tayi ta nufi kitchen shi ko budesa baayiba,
Juyowa tayi tana kokarin nufar dakin Bahar Maa sakinah ta fito daga dakin idanuwanta cikeda damuwa sa mutuwan jiki ganin Leylah ya sakata dan hada karfin hali tana amsa gaisuwanta tana wucewa hanyar kitchen tana amsa tambayar leylan da cewa bahar na dakinta.
Bin bayanta leylah tayi tana sake jefa tambayar to ina ta tafi ne hala a cikin daren.
Bata tafi koinaba tana nan tareda NUAB ashe' maa sakinah ta fada batareda bawa zancen mahimmancin da leylan zata fahimta ba tana cigaba da kokarin aikin data shigo yi na hadawa Bahar lafiyayyan dahuwan nama da madara me zafin gaske da zataiwa hadi me kyau dazai taimakawa abinda ya sameta mai tsananin kyau da karfi.
Saka hannu Leylah tayi a aikin batareda tasan na bahar bane sbd kawai tanason jin magana a bakin maa sakinah a cikin dubara dan tabbatarda shin acan bahar din ta kwana kokuwa a tsakar dare ta koma dakinta hakama duk tinaninta tinda NUAB a gidan ya kwana to shine zaawa breakfast din da wuri wuri haka dan haka ta sake zaqewa tana aikin tana jeho tambayoyin da babu wanda ta samu amsa me amfani daga gurin maa din.
**Shi kuwa a lokacin daya fito already Aleey ya fito cikin kayan sanyi shima na jiias ya shiga mota harma ya tada ita ta kalli gate dan haka NUAB din na fitowa motar kawai ya fada aka wangale musu gate sika fice batareda doguwan hayaniyan da NUAB baya so ba,
Kai tsaye gurin wani qwararran likita suka nufa wanda yana duba NUAB din dole ya saka masa ruwa tareda allurai masu karfi sbd wasu boma boman zafi ne na karfin shaawansa daya kasa sake mata sbd kasa tantance kansa ma dayayi zuwa ga karfin lamarin suka ringa buga jininsa wannan zazzabin ya rufesa dan karansa na farko ne.
A cikin asibitin aka daura masa ruwan a floor din karshe wanda kuma aka hana kowa isa floor din a lokacin har sai yabar asibitin tukuna.
Aleey kuwa kasawa yayi ya tsare musamman ganin wani bacci me dan karfi ya dauki NUAB din wanda hankalinsa ya rabu gida biyu tinda ya baro amma kuma bayajin zai iya barin ko mace likita ta duba masa ita a wannan yanayin datake bare namiji dan haka ya zabi wainda suke iyayenta su mata musamman maa sakinah da a baya ya lura wanka ma kaman tayata wanke kai takeyi dan haka sune kadai wainda zuciyarsa ta nutsu dasu.
****Maa tenya wata irin gashi da magani masu karfin gaske data hada na abubuwa take ta ringa mata wainda suka ringa farfado da bahar din cikin matsananciyar azaha suna sake sumar da ita tana son tayi kuka me karfi amma ko karfin kukan babu sedai jikinta ya ringa wani irin bari tana qamewa tana ficewa hayyacinta,
Kusan awa biyu da rabi suka bata a toilet din tana mata abu daban daban har suka kammala ta samu dawowan hayyacinta kadan tayi wanka suka fito ta taimaka mata ta saka doguwan rigar bacci me karfi sosai ta saka kayan sallah duk da taimakon Maa din tukuna tai sallah a zaune daqyar,
Tana gamawa maa sakinah ta kawo mata instant charcoal data buqaci a kunno mata taka ta zuba masa magani shima ta saka bahar din dake kuka sosai a kai tana rawar jiki tana qanqamewa kaman zata shige ko gani sosai batayi sbd kumburan idanuwanta da fuskarta.
Kasa kalla maa sakinah tayi ta juya ta fice zuciyarta na sake shiga damuwa.
Bayan ta gasa mata gurin da kyau da wuya tukuna tenya ta kaita ta kwantar da ita sbd jikinta dake tsananta fizga da zazzabi me karfi.
Madaran da aka dafa aka kawo mata wannan karan da leylah data biyo maa din ake tana sako kai idanuwanta akan zanin gadon dake yashe a tsakiyar dakin suka fara sauka take kayan hannunta suka subuce mata tenya tayi saurin tareda tana kallanta sedai leylan ta gama ficewa hayyacinta idanuwanta kafe akan bahar kafin ta juya idanuwanta ta kalli wutar da aka gama gasa bahar din take ba wata wata ta fahimci meya faru jiri ya rufe idanuwanta sbd zuciyarta data ke dena bugawa ahankali.
Saurin ajiye kayan hannunta tenya tayi tana tareta da saurin ta zaunar da ita kujera kafin tayi magana wani amai na mummunan tashin hankali ya tasowa Leylahn ta miqe tana ficewa daga sauri tayi dakin Ammi ta fada toilet sedai aman baya iya fitowa ma sbd tsananin tashin hankali da rawar da jikinta yakeyi.
Fitowa tayi toilet din hannuwanta na wata irin rawa da kakkarwa ta dauki wayarta tana saka kiran Asim sbd tasan mutuwa ma kila zatai gwara ta fada masa tin kafin ta mutu yasan abinda ya faru a daren yau da duniyarta ita dai ta tsaya cak numfashinta sarkewa yakeyi kishi yana neman kasheta ido rufe.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
128
Rawa hannuwanta keyi wayar na kasa zama daidai a hannunta sbd tsantsar tashin hankalin datake ji ga idanuwanta basa gani sosai sbd wasu zafafan hawaye da suka cikesu,
Subucewa wayar tayi qasa ta fadi itama ta zame qasan tai zaman dabas tareda fashewa da wani irin kuka me tsananin ciwo da tarin baqin ciki har lokacin rawa hannuwanta keyi sosai.
Kukan takeyi sosai tana rufe bakinta da tafukan hannuwanta biyu sbd kada a jiyota dan batasan kukan me zata ce tana yi ba,
Sosai take kukan tana qarawa ta daga hannuwanta biyu ta dora a tsakiyar kanta ta kaman ance mata yunar da zuhrah sun mutu ta ringa rerowa.
Lokaci me dan tsayi ta dauka tana rusa kukan da ko sautinsa batada ikon fitarwa bare bayyannar da baqin cikinta ko fadarsa dan haka ya kasance kukan kurame a wahale tayisa harta gama ta miqe kafafunta na kasa daukanta dika daidai ta nufi toilet ta fada sbd so takeyi tayi waya da Asim da gaggawa,
Tana shiga fuskarta takeson wankewa amma sai data sake tsayawa gaban madubi ta kalli fuskarta ta sake fasa sabon kuka me sauti dan a toilet ba wanda zaijita kuma ta kunna ruwa dan haka sake murya tayi tai kukanta me isarta tukuna ta wanke fuskarta har zata fito ta daure ta dakata tayi wankanta gabaki daya tukuna ta fito.
Tana fitowa bata iya shiri yanda ta saba ba doguwan riga kawai ta saka ta zauna kan sofa tareda sake daukan wayarta ta saka kiran Asim wanda yake kwance yana bacci sosai.
Yankewan wayar tayi be dauka ba ta sake saka kiran harta yanke bai dagaba dan haka bata tsaya ba taci gaba da danna masa kira baqin cikinta na komawa takaici tayita kiran tana jin babu gantalalle kamansa.
Ganin bai dauka ba ya sakata sake fusata tana kasa hakura dan wlh saita fada masa sbd shima ya shiga mugun baqin ciki ya kuma ji tiririn da zuciyarta ke ji shima.
Ganin baida niyar dauka ya sakata zarar gyalenta qarami ta nada a kanta ta fice batareda ma kowa yasan fitar tata ba,
Tana fitowa harabar gidan taga securities ga mamakinta sai suka barta ta fita ba takurawa sbd su a gurinsu Bahar ce dasu Ammi basada ikon fita koina sai ance su barsu su fita dan haka ita har gaidata sukai cikin girmama batareda sakin fuska ba dan fuskarsu batada sakewa ko kadan kuma a ko yaushe hakan suke.
Tana fitowa taxi na kawowa ta tareta kai tsaye ta fada tabar gurin zuwa masaukinsu.
Tin kafin ta isa take cigaba da kiran daga karshe ganin ya tabbata sakarai ya sakata nemo numbern Shuraim ta saka kiransa dan shima a masauki daya ya sauka dasu duk da ba floor daya suke ba.
Kira daya ta yanke shima bai dauka ba ta sake tsoki tana cigaba da kiransa yaqi dauka shima dan haka kashe wayarta ma tayi gabaki daya tana jin kaman zatai bingida ta fashe tsabar baqin ciki goma da ashirin wani akan wani.
Tafiyar mintina masu dan dama sukai kafin suka isa driver na parking ta fito tai scanning ta biya ta juya zuwa ciki idanuwanta jajir a rufe da masifa.
Lift ta hau tana jin kaman dana sanin kwana a can gidan sbd shedar da abinda gashina nan zai kashe ta,
Gwara ace bata saniba bata gani ba da zuciyarta zata cigaba da bata tabbacin babu abinda ya faru tsakaninsu duk da ko a yanzu tana tabbatarda bawai samun Bahar kaiwa ga shimfidarsa na nufin yana sonta bane ko yadda da ita a matsayin queen tasa dan kila ma sauke buqatarsa kawai yayi akanta dan samun gamsuwa shikenan.
Tana isa dakinsu buga kofar tayi batareda kakkautawaba duk da baa hayaniya a gurin amma bazata iyaba gabaki dayama ta fice hayyacinta so kawai takeyi ta