Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   93 / 100

276K to 279K   out of 299.8K words

yayanki mijinki gubar mutuwa kika dasawa kanki baqin cikin da zaki dawwama cikinsa,
Meyasa zakiyi hakan mami?
Meyasa kika bari shedan ya rufe zuciyar dake kirjinki da idanuwanki?
Meyasa zaki saka mu a cikin wannan halin da babu abinda zamu iya miki dan cetanki?
Meyasa zaki sakamu a halinda zamu kalla hukunci ya hau kanki batareda munada ikon komaiba.


Kuka me karfin gaske ya zowa meryam itama jin kalamansa na karshe dan kuwa da gasken basuda abinda zasu iya yimata a matsayinsu na yayanta sbd Allah ya kwace dukkanin dama daga hannunsu,
Aslam kasa cewa komai tayi suka zuba dukansu qasa a gabanta suna fasa kuka suna rerowa mai tsananin shiga zuciya,
Daga mata da yayan dasuka fi kowace me rai dake boyem daraja yau sun zama mafi qasqancin rayuka a boyem sbd abinda Mamin tayi ayau zai shiga tarihin da har jikokin jikokinta zaa fada,
Zuriarta bazasu taba sake daraja ko ta qimar kallo ce daga yanzu har abada a tarihin boyem,

Jininta daga yanzu sun rasa daraja da martabarsu da jininsu sbd abinda tayi hatta matsayinsu duka zasu rasa a cikin masarautar da duniya gabaki daya.

Kukan da sukeyi mai tsananin karfi da tsima jikin kowannensu yana jijjiga ya sakata zamewa itama ta zube qasa tana fasa kukan tareda cusa kanta cikin kafafunta zuciyarta na mata wani irin tsananin zafi da ciwo da radadin da nauyin datake jin har numfashinta yana toshewa.

Shi kansa Asim din kuka yakeyi sosai mara sauti jikinsa na rawa yana jin inama baizo duniya a cikin jinin sarauta ba,
Inama ya fara zuwa bangaren Maminsa kafin ta fita tayi wannan aikin mummunan kaddarar,
Inama tin suna yara suka gane komai suka sauya rayuwar da zata amfanesu ba wannan ba.

Keelah ne da wasu securities suka shigo aka fitar da 'yayan nata suna kuka suna jin wani irin tashin hankali da mummunan tsoro da firgici sbd jin kaman bazasu sake haduwa ba da ita.

Ganin halinda suka shiga suna ficewa zasu barta ya sakata fasa kuka tana riqesu da hannuwanta dake rawa tana cewa kada su barta su tsaya da ita su kadai gareta a yanxu.

Yanda ta rikice tana kuka jikinta na rawa ya sakasu sake shiga mummunan hali amma a haka akai karfin halin rabasu aka fice dasu aka barta tana wani irin jijjiga.

Rufe bangaren akai ba kowa a cikinsa bayan ita aka zagayesa da tsaro me karfin gaske.

Suma su Aslam bangare daya dole suka koma suka zauna cikin tsaka me wuyar tinanin kaddarar data samesu a dare daya.

Asim ma dole bangaren sultan ya koma ya zauna tareda NUAB daya kasa zama da samun kowace irin nutsuwa.

Tsit masarautar ta dauka dare ya sake tsalawa sosai komai ya tsaya musu cak,

Duk wani me matsayi a masarautar da manyan fada tsoffi da sabbi da duk wanda yakeda alaqa da jinin boyem din labarin mummunan lamarin ya isar musu kafin safe dan haka koda aka wayi gari da mummunan labarin aka tashi komai ya tsaya cak ana jiran farfadowansa wadda likitocin sun tabbatarda ba tabbas sunyi iya abinda zasuyi sai ajira hukuncin ubangiji kawai.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

171
Duk hanyar dasu Ammi zasu samu labarin abinda yake faruwa NUAB ya saka aleey ya toshe ta sbd sam anqi barin kowace kafar media ta fidda labarin hakama masarautar tin daga babbar gate din farko aka dakatar da kowace irin shiga da kowace irin fita komai ya tsaya a yanda yake sai an samu sanin halinda sultan zai kasance,

Babu wanda ya rintsa babu wanda ya matsa,
Sallar asuba ce kadai ta fiddasu amma suna bangaren sultan din sun kasa sun tsare suna jiran tsammani cikin zallar fargaba.

Guraren karfe goma sha daya da rabi Bahar ce ta fara kirasa sbd ganin bai kiraba lokacinda ya saba kira,

Bai bari ta fahimci komai ba sukai magana sama sama sbd itama bata jin dadi,

Suna gama wayar ba dadewa Amminsa ma ta kirasa jikinta a sanyaye sukai magana itama ta kashe tana kasa kiran sultan sbd batason shiga haqqin haile ko nasa hakama shi daya saba kira bai kira din ba dan haka ta hakura tana hana kanta kira dan basu lokacin daya kamata.

Shima Asim leylah ta kirasa ganin be kira dinba sukai magana ta kashe tana jin damuwa a ranta sbd shi kam bai iya dannewa da boye damuwansa kaman NUAB ba dan haka ta fahimci akwai damuwa tattare dashi ta tambaya kuma yace ba komai.

Cikin mummunan yanayi da alhini masarautar boyem din take ayau da damuwa da tashin hankali haka akai wuni guda babu haske ko kadan dare ya kuma yi gari ya waye anan ne manyan masarautar suka fara motsawa da zazzafan yanayi akan fiddo da takardar ayi gaggawan yankewa haile hukuncin abinda tayi kafin ma sultan ya tashi sbd koya tashi babu abinda zai iya yi bayan karban kowane irin hukunci fada da sultan da manyan fadan suka yanke akanta wanda zaa hada da hukuncin da musulunci yace.

A lokacinda aka gabatarwa da sultan takardar daga manyan fada data fito daga office din ministern sharia da hukunci na fadar shiru yayi yana kallan takardar wadda baida zabin daya wuce saka hannu ya buga stamp akai tareda amincewa da hukuncin da aka gabatar mata.

Asim wanda a cikin wuni da kwanan ya sauya gabaki daya ya zauce daga zaune ya koma mara madafa da rashin ina zai saka kansa yanayinsa babu wanda bazai kallesa ya tausaya masa ba sbd abin biyu yake akansa,
Halinda mahaifinsa yake ciki na tashi ko akasinsa da kuma mahaifiyarsa da itace tayi aikin hakama manyan fada sun zauna sun hada kan laifukanta da Aleey ne ya badasu da cikakkun shedunsu na kisar data ringa yi da hannuwanta a rufe batareda an bayyana,
Haka suka hada laifukan rayukan data dauka masu yawan gaske da yunkurin kisan dataiwa sultan aka fiddawa duniya wanda take masaurautar ta dauki zafi harma da wajen masaurautar akan saita amsa hukunci daidai da laifinta maana kisan dataiwa bayin Allah marasa galihu dan kawai suna bayi ba akan laifin komaiba.

Zafi masarautar ta dauka sosai da sultan NUAB wanda zuwa yanzu komai ya cake a cikin kansa da zafin gaske sbd maganar kwanaki akeyi sultan har lokacin yana cikin mummunan hali gasu Amminsa sun fara kokarin gane halinda ake ciki sbd zuwa yanzu ba lokacinda bata kiran wayarsa bata samu hakama daga NUAB din har Asim sun sauya sosai damuwansu a bayyane take qarara ko a wayar dan haka hankalin Ammi da matansu yafara tashi,

Zuhrah ce kadai tasan meyake faruwa dai tenya kuma sun kasa nunawa ma bare fada suna cikin mummunan tsoro da tashin hankali suma musamman da cikin leylah kwatsam ya bayyanar musu ta hanyar somewa data kusan yi a lokacinda taji abinda yake faruwa itama a bakin shuraim wanda baya boyem amma ya koma tini shima.

Likita aka kira ya dubata take ya tabbatar musu da ciki ne a jikinta,

Bayan wucewan likita murnar cikin sukai duk da ita tana cikin shock hakama takasa fada itama sai kawai ta samu kanta da tsananin son kasancewa da Asim wanda a yanzu yafi kowa shiga tsaka me wuya da mummunan hali dan kuwa yana ji yana gani hukuncin kisa ya hau kan mahaifiyarsa wadda itama tana samun sakon hukuncin da aka yanke mata yanke jiki tayi ta fadi tana somewa.

'Yayan nata ma babu wanda bai yanke jiki ya suma ba jin hukuncin wanda tini Sultan LEUL NUAB ya saka stamp dinsa a jiki har an fidda duniya ta dauka dan haka iyayenta da suka tsufa sosai da nysa yarta da jikokinta tini suka kamo hanyar qasar boyem cikin mummunan tashin hankali me tsanani.

Asim ya rufe kansa a bangarensa yayi kuka ya buga kansa ya kusa mutuwa sbd ciwon dayake ji a kirjinsa ya rasa ya zaiyi da rayuwarsa dayake fatan ya mutu akan abinda yake ji.

Shi kansa NUAB babu wanda ganinsa ya taba zuciyarsa idan ba Asim ba wanda yake kwatanta radadin dayake ji sbd sanin matsayin uwa da girman soyayyarta a zuciyar kowane 'da.

Leylah shiryawa tayi akan uk zata tafi ta samu Asim acan daga can zasu dawo bikin.

Babu wanda yayi mamaki ko yunqurin hana tafiyar a cikin iyayen sbd kusan bame walwala a cikin wani hali sike,

Dukansu suna son tafiya boyem din amma kuma sbd babu dalilin tafiyar ya saka suka danne sukai shiru tinda basusan meyake faruwaba,

Tenya da sukasan meyake faruwa basuda ikon fada haka dai gidan ya koma tamkar gidan zaman takaba ba walwala ba farin ciki.

Bahar ma ahankali ahankali ciwo yake kokarin ya zama nata dan kuwa koyaushe a kwance take batason hayaniya ko son shiga mutane sosai,
Tsakanin kewansa da sonsa ne yake sake tsananta halinda take ciki har kuka take masa a waya idan ya kira sbd batason jinsa a cikin damuwan datake jinsa a ciki,

Kukanta da daga hankalinta akan kasa yadda da babu abinda yake damunsa sai suka hadu da damuwansa suke neman tsayar da duniyarsa cak.

Ana gobe ne ranar hukuncin Queen haile a ranar Leylah ta iso boyem da dare drivern bangaren mum dinta ne yaje airport ya daukota suka iso.

Ko data iso masaurautar koina yayi shiru ana cikin tsananin alhinin abinda zai faru goben dan haka kai tsaye bangaren mijinta ta nufa bayi biyu na biye da ita janye da akwatinta da jakar hannunta.

Idanuwanta jajir ta isa bangaren batareda jin duk gajiyan data debo ba sbd tashin hankalin datake ciki ya wuce gajiyan.

Koina duhu ne a bangaren dan haka kai tsaye dakinta ta isa ta aje komai ta fito ta nufi dakinsa,

Baya nan dan haka komawa tayi dakinta tayi sallolin dake kanta bata tsaya shan ko ruwa ba ta fice zuwa bangaren Aslam sbd kyautata zatan yana can.

Acan din kuwa ta samesu su uku cikin mummunan yanayin da take idanuwanta suka ciko da hawaye suna fara sauka ta qaraso cikinsu tana zaunawa gefensa tareda kallansu daya bayan daya tana kokarin gaidasu da jajanta lamarin wanda ba wanda iya doguwan magana a cikinsu sedai kawai gyada kai da sukeyi.

Shine kadai ya iya zuba mata ido yana kallanta yana rasa abin fada idanuwansa jajir yayi wata muguwar rama a cikin kwanaki kalilan dan kuwa abinci me suna abinci ya manta rabansa dashi a bakinsa ruwa kawai sai tea ne suke shiga bakinsa da cikinsa.

Hannunta ta miqa ahankali ta dora akan nasa tana kamawa ahankali tareda sakar masa wani soft tabawan dake bayyanarda dukkanin kulawanta da damuwanta tareda jajenta da tausayawanta.

Shiru sikai dukansu bame cewa komai sbd abin fada ya gama qare musu,

Suna zaune anan su nysa da kakanninsu suka iso tareda wasu daga yayan nysah din dan haka kuka da damuwa me zafi ta dawo sabuwa haka suka ringa kuka mai tsananin gaske suna rokon Allah ya kawo mata sauki da mafita akan wannan mummunan lamarin da zasu shedar gobe.

Asim kuwa zuwa yanzu tsananin damuwansa ya koma akan sultan ya farka kafin goben ko akwai sassaucin da zata samu daga hukuncin me tsaurin da suka kasa dauka.

Duk wanda yake masarautar kwanan damuwa da zullumi tareda baqin ciki ya yi hakama kaman kiftawan ido sukaga daren ya wuce gari ya waye,

Karfe hudu da rabi ne lokacin hukuncin haile dan haka aka bawa zuriarta damar shiga gurinta su gana,

Dukkaninsu suka shiga bayan kuka mai jijjiga zukata babu abinda sukeyi tinda suka hadu sbd babu ma me abin fada,

Ita kanta wani irin dana sani da kuka ne me yawan gaske takeyi musamman ganin yayanta da iyayenta da jikokinta suna wani irin kuka wanda tasan ta riga ta bata musu sunan da harsu mutu bazasu dena wannan kukan da fuskantar matsala ba.

******damuwa da qunci sun hana sultan NUAB da kadir kowace irin nutsuwa da gane komai dan haka suma babu wanda rama bata kamasa ba ta kwanakin hakama kowannensu ya kasa matsawa daga gadin sultan din,

Wanka da sallah kadai ke fidda NUAB daga bangaren hakama komai na masarautar ya tsaya cak sbd bama me ganin sultan NUAB din.

****Ayau din kaman a mafarki karfe uku da mintina ana gap da sallar laasar Sultan yasar ya farfado sedai bai iya magana ba idanuwansa ne kadai suka bude a cikin yanayi na rashin kuzari ko lafiya yana fidda numfashi a hankali.

Farfadowan nasa tamkar a mafarki dukkaninsu suka jita dan haka take akai gaggawan kiran likitoci suka iso kansa.

Dubasa sukai cikin ikon Allah ya farka din batareda wasu manyan complications din ba bayan rashin karfi da kuzarin jiki wanda zai jima a hakan sbd garkuwan jikinsa da kusan poison din ya illata sai a hankali ahankali lafiya da kuzarin gangar jikinsa zai dawo daidai dan ko tafiya ba yanxu ba se a gaba ahankali dan haka wheelchair zaa kawo.

Duka wannan bayanin radadinsa kadan ne a zikatansu tinda ya farka zai rayu kuma insha Allah dan haka ajiyan zuciya da wani irin numfashi NUAB ya ringa ajiye a bayyane yana jin wani nauyin daya danne kirjinsa yana sauka zuwa cikinsa yana fashewa.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

172
Koda labarin farfadowan sultan ya fita take msarautar da wajenta ma aka ringa sauke ajiyan zuciya ana farin ciki da murna tareda jiran kuma me zai faru akan abinda zaiji akan haile ayau din da zata fuskanci hukuncinta.

Asim da yana bangaren sultan ya farfado zubewa qasa yayi a natse yayiwa Allah sujjada sbd tin jiya yake rokon ubangiji ya farfado da sultan din kafin lokacin qaddamar da hukuncin yayi kuma gashi Allah ya amsa masa dan haka dashi da NUAB ne suka kimtsa sultan din yana kwance idanuwansa a rufe zuciyarsa a toshe ba tinanin komai face gangar jikinsa dayake ji kaman ba tasa ba.

Su aslam ma farin ciki ne ya shigesu wanda suka manta ma yaya dandanonsa yake suka dungumo duba sultan din.

Kaf yayan sultan din suna masarautar sun iso dan haka masarautar take ciki,

Haka suka ringa zuwa dubasa daya bayan daya suna ficewa banda aslam da meryam da nysah da suka zube qasa kansu a qasa batareda laakari da bai gama dawowa daidai ma dazai fahimci komaiba suka fasa masa wani kuka me tsima rai suna rokon ya nemawa mahaifiyarsu sassauci daga sultan NUAB wanda baya dakin ya fice gabaki daya daga bangaren sbd sauran yayan sultan da zasu shigo dan haka gurin zaiyi hayaniya ko yayane.

Yana barin bangaren bangarensa ya koma sai a lokacin ya samu damar kiran Amminsa da kansa ya sanar da ita abinda yake faruwa cikin kwantar mata da hankali.

A tsaye take amma kafafuwanta sukai wani irin sanyi da sanqarewan data zame ta zauna kan kujera da karfi tana dora hannunta daya akan kirjinta cikin tsananin jin wani irin radadin datasan zafi da ciwonsa a baya sbd radadi ne kadai datake kasu idan wani abin ya samu daya daga cikin jininta su abaas da nurat da zuhrah.

Ja idanuwanta ke rikidewa sunayi ta kasa bude baki tace komai ta kashe wayar kawai tana sakinta idanuwanta na neman rufewa da duhu tayi saurin jingina bayanta tana rufe ido dan numfashinta dake neman toshewa.

Maa sakinah ya kira ya sanar da ita abinda ya faru da kuma fada mata ta kula da Ammin kada ta shiga wani halin hakama duk tsanan kada Ammin taxo Anjom zaa taho da sultan din anan zai qarasa jinyarsa dan haka su jira kowane lokaci zaa iya isowa da sultan.

Tashi hankalin maa sakinah yayi ta fito a rikice jikinta na rawa ta fadawa tenya da zuhrah abinda yake faruwa sai a lokacin suka samu damar fidda tashin hankalisu da suketa dannewa dan haka suka taru suna shiga damuwar bayyane da tsoro da mamakin haile.

Ammi dai kusan kasa dauka zuciyarta tayi sbd numfashinta daya ringa sarkewa yana neman daukewa dole sukai gaggawan neman likita ya iso ya fara bata taimakon gaggawa daya kamata.

Bahar da saida jikin Ammin ya rikice tasan meyake faruwa kusan itama zubewa tayi saida Maa sakinah ta riqeta jikinta tana kallanta da kulawa tace

'Ki kula da kanki fa'

Tsoro me tsananin gaske ta shiga na kwatanta halinda LEUL ya shiga a kwanakin batareda kowa da zai kula dashi ba a kwanakin musamman daya boye musu ya shiga tashin hankali da quncinsa shi kadai
Ga kuma halinda Ammi take shiga ayanzu..

Zazzabi me karfi ma taji yana rufeta sosai dan haka kafafunta suka tsananta rawa ta kasa tsayuwa ta sake zubewa jikin maa sakinah tana jin mararta na wani irin murdawa da karfi take jini kawai ya balle mata.

Zuhrah ce ta fara lura da jinin dayake biyo kafafunta ta kalla da kyau tana bude baki cikeda sabon tashin hankali tace

'Me nake gani ni zuhrah?

Maa sakinah da tenya tare suka kalla inda take kalla take suka qarasa rikicewa da tashin hankali mai tsananin gaske sakinah na cewa

'Ciki ne fa a jikinta ita kanta batasan dashiba mun shiga uku ze fita?

Ita kanta Ammi dake kwance tana jin hakan yunqurawa tayi cikin wani irin karfin hali tana cewa ayi gaggawan kiran likitocin da aka tanadarwa masarautar suzo a taimaketa kada cikin ya zube indai shine da gaske.

Waya zuhrah ta fidda hannuwanta na rawa tenya kuwa da kanta zata bazata iya jiran kira ba sakinah kuwa riqota tayi hakama Ammin dole ta miqe cikin karfin hali suka kama Bahar din wadda jikinta ke rawa sosai tana jin wata irin azaba a mararta mara iyaka amma zuciyarta shi kadai takeson jin muryansa a lokacin.

Koda doctors biyu suka iso tafara jin jiki sosai wani zufa take fiddawa tana qanqame Ammi da azaba me tsananin gaske amma ta kasa bude baki tace komai.

Kiransa ne ya shigo wayar Ammi a lokacin wanda take itama ta kasa dagawa dan batason ya sani dan haka kasa dauka tayi suna jiran tsammanin jiran abinda likitocin keyi gurin tsaida cikin zullumi da fargaba.

A daidai wannan lokacin koina ya dauki tsit a masarautar boyem sbd lokacin fitowa da haile yayi zaa kaita bangaren azabar bayi acan zaa yanke mata hukuncinta ta hanyar rataya amma baa gaban jamaa ba sbd sirrinta yanayinta sbd yayanta wainda zuwa yanzu ma Aslam tana kwance jiri ya debeta ta sume tana bangarenta batasan inda kanta yake ba bayi biyu ne akanta.

Shiga akai fitowa da ita anan ne sultan duk da baya iya magana sosai ya bude baki ya nema mata sassauci daga NUAB wanda ya zubawa sultan din ido yana kallansa sbd yanda yake maganar cikin tausaya mata sbd yayansu da kuma zaman auren da sukai.

Dauke idanuwansa yayi daga sultan yana maidawa akan Asim wanda yake tsaya a gefensu idanuwansa jajir ya dago kansa ya sauke idanuwansa akan NUAB wanda shi yake kalla.

Shiru sukai dukkaninsu kafin Asim ya motsa ahankali ga tsananin mamakin NUAB da sultan da kadir dake

93 / 100