ta Dora Akan fuskansa ta shafa tareda sakin murmushin daya saka idanunwansa qarasa rikidewa jajir sbd Ayau itace ranar farko dayaga murmushi Akan fuskar mahaifiyarsa tinda ta haifesa,
Bude Baki yayi da Wani irin sauti daya sake sakata shafa fuskarsa tana ganin kammanin da bazata taba mancewaba shimfide a fuskarsa yace
‘Ammi,Ammi na dawo gareki bazan taba sake rabuwa dake ba koda zan rasa komai Akan hakan,
Ammi bazan iya sake rabuwa dake ba,
Ammi zan nema miki lafiya da duk abinda kikeso nayi miki Alkwarin cika miki shi,
Ammi zan tafi dake na Nemo miki Abaas a duk inda yake fadin duniyar nan na kawo miki shi gabanki,
Ammi ina son ki cire dukkanin damuwa da quncin dayake ranki sbd lafiyarki,
Ammi…….
Hannunta ta Dora a bakinsa cikin nutsuwa kafin ta rungumesa tana kwantawa gefen kafadarsa ta bude Baki tace
‘Zan bika duk inda zaka tafi dani HAYATEEM,
Bazan iya rayuwa ba idan Ka tafi Ka sake barina,
Zuciyana bazata iya sake daukan rayuwa babuka ba HAYATEEM,
Karka banni Ka tafi dani ko ina ne zan bika na rayu tareda Kai sanyin idaniyata….
Yanda take maganar ya sake Sosa zuciyarsa fiyeda yanda zai iya boye wa dan haka hannuwansa suka dan ringa rawa ya rungumeta sbd akwai alaman rashin lafiyan jiki da tinina sosai a bayyane da sautin maganarta.
Maganganu ya bude Baki yafara jero mata masu nutsuwa da samar da nutsuwa a kwakwalwanta yana bayyanar mata babu abinda zai qara rabasu sai mutuwa dan haka ta kwantar da hankalinta ta cire damuwan komai dan babu inda zashi batareda ita ba.
A daidai wannan lokacin aiki akeyi gadan gadan a bangaren me girma LEUL din Yaransa suna tsaye qyam Akan aikin Wanda take aleey yayi ordern wasu manyan Kayan da abubuwan da suke buqata na ubangidansu daga wajen masarautar kuma aka kawo cikin gaggawa suka duqufa sbd kafin ya gamo ganawa da mahaifiyarsa suke buqatan komai na bangaren ya kammala daidai da hutawarsa,
Acan bangaren wishmah dinma Maa sakinah ce a tsaye tareda masu aiki da bayi Ana aikin abinci na musamman me tsari da tsaftar gaske tareda lafiya daidai da taste dinsa tin na yarinta duk da sunsan ya sauya tako ina amma dai sunsan zai kaunaci komai da zaayi masa sbd kewansu da kewan kulawansu akansa da girkinsu.
Maa tenya kuwa take qwanjinta da kuzarinta harma da walwalanta ta dawo a lokaci daya Jin kanta takeyi tenya dinta ta baya da zata iya tsayuwa ako ina dan bawa NUAB da Ayanah kariya da duk abinda sukeso dan haka take ta bada umarnin a tara bayin da zasu ringa hidimar bangaren LEUL boyem da kanta zata zabesu ta basu training me karfi da kyau dan kuwa karfinsu ya dawo fiyeda ma Wanda suke dashi a baya dan kuwa a bay suna shakkar a cutatar musu da NUAB suna basa kariya amma a yanzu shine Wanda zai basa kariya a karkashin iko da karfinsa.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
54
Tin asubar da sautin karar dawowan LEUL BOYEM ta shiga kunnuwan duk wani babba me matsayin dayake masarautar a tsaye suke suna kaida kawo cikin mamaki me girma da shakka tareda tinani kala kala Wanda rashin tinanin kamawa ma yafi yawa a cikin kwakwalwansu sbd a tsawon shekarun nan sun manta sun shafe magana da tarihin LEUL boyem daga masarautar babu Wanda ko a maida zance ya kuma tada maganarsa kaman yanda sukaga sultan bai taba maganarsa ba saisu ma suka watsar dashi da zancensa kaman yanda aka rufe babin mahaifiyarsa kwata kwata baa ma sakota a lissafin matan sultan kokuma wanzuwarta ako wace hidimar masarautar da ake buqatan halartar matan sultan din dan duk inda akace matan sultan to su uku ne keda cikakken ikon sunan sbd zamantowanta wishmah duka ya Halarta mata wannan suna da matsayin,
Ayau Asuba tsaka kawai cikin bacci da rashin tsammani ko a mafarki sukaji sautin sanarwar dawowansa batareda aiko da sakon dawowan tasa ba kaman yanda yake tilas kawai suka samu dirarsa a masarautar,
Babban abinda ya girgiza kaf manyan fadar masarautar shine a bayan ASIM ALMAZZ suke sun shirya tsaf sun yanke kuma sun kudirta shine sultan na boyem dan kuwa daga ranar da aka wayi gari babu sultan bazaa qara awa biyu ba batareda sun nada ASIM ALMAZZ ba wannan Alkawari ne da burin da kowannensu yake dashi.
Dan hakanne dawowan LEUL BOYEM ta girgiza su jijjiga me karfi sbd basu taba saka ran dawowansa ba
Sun shirya goge sunansa da uwarsa a cikin tarihin boyem daga ranar da sultan YASAR yabar duniya hakama sun saka rai sun kwanta da tinanin koda zai dawo qasar to sanar da daya daga cikin iyayensa sun mutu.
Meya dawo dashi kwatsam haka babu zata ba tsammani?
Menene dalilinsa na dawowa Bayan shekaru masu tsayi?
Idan ma yana tinanin ya dawo ne karban matsayinsa to tabbas ya makaro dan bazasu taba Bari ba korasa zasu sake yi inda ya fito wannan Karan ma shi da uwarsa kila dan haka a shirye suke dashi zasu nuna masa karfin matsayin da suke dashi Wanda sunada ikon zartarwa,
ASIM ALMAZZ ne sultan na gaba Wanda da karfi zasu tabbatar masa da hakan ya tattara ya koma Gagarin dayake yi bada gatan masarauta ba hakama dole zai amsa kiran shugabannin Masarauta ya fuskanci hukuncin dokar daya taka ta masarauta ta zuwansa batareda ya aiko manzon aike ba da wannan zasu hukuntasa ya koma inda ya fito.
Hakan ya saka kusan dukkanin manyan suke a cikin tinani daya da shiga tsananin son ganinsa da isar dayake ji da ita dan haka suke a cikin shirin isa fada da gaggawa sbd ko sultan dole yana can cikin bacin rai da fushin abinda LEUL din yayi.
Koda karfe goma na safe ta buga duk Wanda yake masarautar ya samu cikakken labarin isowan sa,
Hakama waje da garuruwan dake qasar sun fara samun labarin dawowan LEUL BOYEM,
Yan jaridu ma da television tini suka fara yada Labaran Wanda Aleey ne da kansa ya basu cikakken bayanan ta waya sbd qasar BOYEM ta shedar da zuwan magajinta koda kuwa ziyace kadai ya kawo ba zama Yazo yiba,
Yanda zancen ya ringa yaduwa da shiga koina ya saka mutane dama yan jaridu fara jefa maganganun to a yanzu waye asalin magajin da zai mulki BOYEM,
Waye asalin me BOYEM a cikin magajin guda biyu da ake dasu,
Waye sultan zai zaba bawa mulkin da kansa kokuwa jira zaiyi saiya bar duniya Allah ya bawa me rabo saa?
Wannan maganganun ne suka fara daga hankalin wainda sai daga baya labarin dawowan LEUL BOYEM din ta samesu maana ASIM ALMAZZ kenan da HAILE wadda ta tabbatarda NUAB ALMAZZ dinne ya dawo da gasken gaske kenan.
Gabaki dayanta da yayanta a Zaune suke babban palonta na hutawa sunyi shiru kowa da abinda yake ransa idanunwansu jajir babu Wanda jininsa baya tafasa yana hawa sbd tsagwaron zallan baqin ciki bawai dan suna tsoron sa ba sbd basa tinanin yanada abinda zai sakasu tsoron sa ko shakkarsa kawai dai sultan da suka gama samun cikakken kansa Akan tinanin yama gama Dora ASIM ALMAZZ a mulkin BOYEM yanzu kuma wannan ya dawo zai rikitar musu da tinani da raayin sultan dan haka suke cikin baqin ciki me tsanani amma Bayan hakan Sam sunsan tako ina babu inda zai kamo kafar ASIM a komai dan haka sukai shiru cikin takaici da baqin ciki,
ASIM ALMAZZ dayake Zaune a kujeran datake ta Mutum daya idanuwansa a dan rufe yayi shiru da zurfafa a tinani bude idanuwansa yayi ahankali ya sauke Akan mahaifiyarsa kafin ya bude Baki cikin tasa Izzar da Wani irin yanayin dayake ji a ransa na babu Wanda ya isa ya rabasa da matsayinsa dayake Kai da Wanda yakeso a duniyar nan batareda ta aikasa inda ya kamacesa ba yace
‘Mamee babu abinda zai faru ki kwantar da hankalinki kokarinki na shekaru bazai taba tafiya a banza ba zan tabbatarda da hakan,
Indai ba nine magajin karagar mulkin BOYEM ba to tabbas BOYEM zata rasa magaji da sultan din da zata kira nata,
Kawai dai a yanzu ku Bari wannan dan gudun hijirar daya dawo ya gama abinda ya kawosa ya tattara mistress din mahaifinsa ya qara gaba da ita zuwa yawon bin yan taaddan da akace yanayi.’
Karban zancen HAILE tayi cikin wani irin radadin zuciya da cewa
‘Banda rashin tinani irin na Ubansa da tsufan dayake cinye kwakwalwansa tayaya zaiyi tinanin ma sauya Ka daga zama mai mulkin BOYEM Akan Wanda yagamo yawon duniya da taaddanci’
Numfashi meryam kawai ta iya saukewa me zafi tana fatar koma menene kowa zeyi yayi itadai buqatarta ASIM ALMAZZ ya zamo me mulkin BOYEM ya dauke hukuncin dayake kansu ta auri koma Wanene zata samu.
Aslam kuwa can qasar zuciyarta Wani irin tsoro da fargaba takeji Wanda yake hanata cewa komai dan kuwa koma yayane dawowansa su dai ba alkhairi ce a garesu ba,
ASIM ma a qasan zuciyarsa wata shakka ce ke son shigarsa da matsuwa da son haduwa da NUAB ALMAZZ dan yaga menene yake dashi a yanzu sannan ya sheda cewa shi ASIM ALMAZZ yanzu ya fisa komai musamman ilimin daya samu cikakke me kyau Wanda ko hakan zai saka a basa mulkin shi a hana masa dan babu ta yanda dan taadda zaiyi mulkin BOYEM baa taba ba kuma bazaa taba farawa ba.
HAILE ma kusan bazasu taba gane abinda take ji a zuciyarta ba sbd har abada indai NUAB ALMAZZ yana raye batajin akwai ‘dan da sultan zai so kamarsa duk da baya tareda NUAB din shekara da shekaru amma hakanan take Jin bai taba Dena sonsa ba kawai abinda ya sakata kwantar da hankalinta shine koda yana sonsa baya tareda shi yana tareda ‘danta ne kuma gaggawar datake yi shine a Dora ASIM kafin ranar dawowan NUAB tayi gashi yanzu ya dawo batareda burinta ya cika ba dan haka yanzu sabon yaqi ne garesu su dukansu Akan tabbatarda burinsu ya cika kota halin yaya.
*****Se karfe goma da mintina ya Baro bangaren Amminsa Bayan yaci abinci tareda ita cikeda kwanciyan hankali sun samu kasancewa da juna yanda yakeso tukuna ya fito ya fice.
Lafiyayyan gyaran da akaiwa bangarensa ya saka yana zuwa Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa Wanda yake da Wani palon hutawansa a ciki kafin asalin bedroom din.
A jikin bangaren nasa akwai manyan bedrooms guda biyu da sukeda girma sosai da toilets a ciki anan Yaransa suka sauka aleey kuwa bedroom daya dayake cikin bangaren nasa ya sauka dan haka dukkaninsu shigewa sukai sbd lokacin hutun LEUL ne.
Wanka yayi da dukkanin abinda ya saba amfani dashi sbd babu abinda yake amfani dasu da aleey bai siyo ba baa.
Dogon wandon bacci na lebarto ya saka mai wani irin santsi da Laushi sbd tsadarsa sai farar rigar wandon
Kwantawa yayi ransa da ruhinsa cikeda nutsuwa take baccin hutun dayake buqata ya daukesa.
Gabaki daya bangaren da zagayensa tsit yayi sbd Yaransa da suka tabbatarda hutawa yakeyi babu kowace hayaniya da ake buqata.
Daga shi har Yaransa Hutu sukeyi Bayan an bada cikakkiyar umarnin kada Wanda ya tinkaro bangaren.
Acan fada kuwa kowa ya cika duk wani babban masarautar yana cikin fada Zaune,
Hakama duk Wanda yake gari ko qasar datake kusa da BOYEM indai jinin BOYEM ne sun iso suna cikin masarautar wadda ta dauki dumi dan kuwa a cike take da masu fada a ji na mulkin BOYEM,
Shi kansa sultan Bayan dogon lokaci daya dauka kafin fitowansa ya fito daga karshe Bayan kowa ya gama Halarta kenan shi kadai ake jira da LEUL din Wanda baima San mesuke yiba,
Zaman fada da meeting din zafi ya fara dauka Wanda ya saka sultan yake sake jin baiyi danasanin aika dansa ba harma ya zama koma menene ya zama yanzu din dan kuwa a bayyane wata irin zazzafar qiyayya ce yake gani tako ina a idanuwa da kalaman duk Wanda yake fadar Akan sai hukunci yahau kan duk Wanda ya taka dokar Masarautar BOYEM koma wanene.
Sultan da abu dayane yake cikin zuciyarsa yana Juyawa shine rashin zuwan NUAB din garesa Bayan shigowa sa masarautar da shine yake mulki da ikonta hakama shine uban daya haifesa komai Zafin kansa da ikonsa wainda a gurinsa cikin jininsa ya gajesu,
Dagowa yayi ya kalli taron manyan qasar BOYEM din gabaki dayanta da idanuwansa da tsananin zallar mulki da ikon dayake jininsa yana bayyana,
Umarnin suke jiran ji dan haka akai tsit Ana kallansa tareda jiran abinda zai fada kowa zuciyarsa har rawa takeyi sbd jiran umarnin da sultan din zai bada.
ASIM da idanunwansa sukai jajir zuciyarsa har wani fizga takeyi ya kafe sultan din da ido yaja baza kunnuwansa jiran abinda zaa fada,
Bude bakin sultan umarnin kiran LEUL BOYEM ya bada tareda tabbatarda umarni ne me karfin gaske.
Dan aike Koda ya isa tin daga nesa ya zube qasa bakin kofar bangaren yana daga muryansa ya isar da sakon cikin tsananin girmamawa.
Dukkanin sakonsa a kunnuwan Yaransa ya isa amma babu Wanda yakeda niyar isar da sakon sbd lokacin gurinsa bai qareba dan haka manzon sakon yana zube a qasa bai tashi ba sbd Sai an amsa masa sakon zai tashi koda kuwa zai kwana ya wuni a hakan.
Shiru shiru ba dan sako Wanda ya saka fadar sake daukan zafi babu Wanda ya iya cewa komai sedai xukata sun dauki Zafi.
Awa kusan biyu manzon sakon ya shafe a durqushe cikin rana kafin me BOYEM din ya tashi baccin sa Kai tsaye ya shiga toilet yayi wanka ya bata lokaci sosai kafin ya fito daure da towel fari qal daidai nan wani manzon sakon ya sake isowa sedai wannan Karan bayi biyu ne daga bangaren mahaifiyarsa aka turo Wanda hakan ya sakasa Dakatawa cak daga abinda yakeyi sbd bayin saida suka gabatar da kansu suka isar da sakon ya kuma San me ake nufi da aiko bayin mahaifiyarsa Wanda take zuciyarsa ta fidda Wani irin Numfashi me dumi ya ajiye towel din dayake hannunsa na goge Kai ya juyo ahankali cikin isa da wata irin izza ya nufo kofa ya fito.
Aleey dayake palo a tsaye yana jiran fitowansa yana ganin fitowansa da towel take ya dauko sunglasses na Versace ya miqa masa hannu kadai ya saka ya karba yana nufar kofa Kai tsaye wadda tini aka wangale masa ita,
Yana fitowa umbrella biyu a take aka bude take a kansa batareda ya tsaya ba suka biyosa dukkaninsu tamkar zasu fashe sbd karfi ga tattoos nasu daba wasu dake bayyane sai daukan ido sukeyi,
Cikin mummunan tsoro da firgici bayin dake kofar bangaren sukai qasa da kansu jikinsa na wata irin tsima sbd firgice wa,
Wani irin daukan ido fatarsa keyi wadda azababben Hutu ne ke bayyana a kowane babu na jikinta,
Kai tsaye fadar ya isa cikin wata irin izza gashin kansa yana zube a bayansa towel din dayake qugunsa yana sake fidda lafiyar kakkarfan jikinsa dayake a murde,
Tin daga nesa securities din fadar da kaf bayin dake hanyar suka zube qasa kawunansu a qasa zuciyarsu na wata irin harbawan da kansu yake kasa dauka.
Wasu irin samudawan da babu alamar rahama ne ASIM yaga suna shigowa fadar jikinsu na zanen tattoo din da idanunwata sun gane masa daidai guda uku daga cikinsu fuskar NU’AB ALMAZZ ce zane a jikinsu matsayin tattoo,
A kofar shigowa suka tsaya daidai nan LEUL me BOYEM ya sako Kai cikin fadar cikeda Wani irin zazzafan iko da izza,
Gabaki daya wuta daukewa duk Wanda yake fadar tayi cikeda matsanancin rikicewa da girgiza me tsananin gaske suka zubawa kofar daya sako Kai ido bakunansu a sake suna wata irin rawa.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
55
Takowa yakeyi kansa tsaye cikin isa da Zafin kansa dayake a bayyane sbd sun samu kunna inda baa kunnawa a zuciyarsa dan aika bayin mahaifiyarsa Kai tsaye kunnasa sukai shi kuwa a gurinsa bayin mahaifiyarsa sunfi duk Wanda yake cikin fadar daraja a gurinsa idan aka cire uban da yayi cikinsa.
Duk takunsa daya zuwa tsakiyar makekiyar fadar girgiza zukatan duk Wanda yake gurin yakeyi sun kasa Nemo tinaninsu da kalamansu,
Qasa suke yi da idanuwansu cikeda sake shiga mugun shock daya wuce firgici dan bama zasu iya kallan fatar jikinsa dake Wani irin daukan ido kakkarfan jikinsa dake murde yana sake shigar dasu rudewan shin a fadar BOYEM suke ko kuwa,
ASIM da idanunwansa suke rarrabuwa Akan samudawan dake tsaye a kofar wani yawu ya Hadiye da karfi a sirrince sbd tsananin mamakin dayake Neman rudar dashi
Sake bude idanunwansa yayi da kyau Akansu daya baya daya yana San tabbatarda shin fuskar NUAB ce yake gani zane a dantsen hannunsu wasu kuma a wuyansu wasu kuwa kirjinsu dayake dan bude sbd rigar da bata rufe ba botiran sama na rigar a dan bude,
Yana yana yaji idanunwansa sunayi ya maida kallansa da sauri Akan aleey dayake tsaye riqe saida waya da iPad da baya rabo dasu sbd koyaushe a shirye yake da buga waya ko aikatar da sako ba delay,
Zancen tattoo din jikin Aleey ya qarasa rikitar da tinanin ASIM sbd ‘LEUL BOYEM’ ne Baro Baro rubuce a hannunsa tin daga gwiwan hannun har zuwa gurin da tafin hannunsa ya fara,
Juya fuskarsa yayi a slow yana maida kallansa inda NUAB yake ya Dora idanunwansa da suke cikin rudani akansa ya kafesu akan bayansa dayake daukan ido sbd haske da lafiyar fatarsa idanuwansa suka sauka Akan tsakiyar bayansa da sunan ‘GHAZ’ yake rubuce cikin wani irin rubutu daya sakasa saurin dauke idanuwansa Akan rubutun yana miqewa kafafunsa na wata irin rawa ya Riga NUAB saurin isa tsakiyar fadar ya zube gaban sultan a hankali yana sunkuyar da Kai ya bude Baki zaiyi magana daidai nan NUAB ya iso gurin ya tsaya cak tareda dagowa ya zare shades din fuskarsa ya saukar da idanuwansa da suke zak na ubansa da suka sauya babu abinda yake bayyana a cikinsu Bayan zallar wutar bacin rai na shakaru ya sauke su Akan sultan Wanda idanuwansa suke kafe Akan NUAB din tin daga lokacinda ya sako kafarsa a fadar yana takowa a cikin takun dayake tabbatarda shi din jininsa ne tsatsonsa ne da a kowane hali bazai taba dana sanin haihuwansa ba da rayuwar da suke akai yanzu,
Cikin tsakiyar idanunwan NUAB din yake kalla cikeda Wani irin yanayin dayake tabbatarda alfaharinsa da samun cikar burinsa da NUAB ya rayu a duniyar datake cike da maqiyansa,
Ya rayu ya zama tsayayyen da zai iya tsayawa Ayanah ya bata kariya da rayuwarsa batareda shakkar kowa a duniya ba,
Babban