da Maa sakinah ta juya ta kalleta dakyau kafin ta dawo da kallanta akan Asim din ta Bude baki cikin kamewan mutunci da tattaro tata nutsuwar da itama take Neman kubuce mata tace
'barkan li'ul Asim da zuwa Amma nasan zuwan nan akwai Sakon dayake tafe dashi'
Bai iya batawa kansa lokaci ba sbd a matiqar matse yake da fitar hankali sbd ganin Bahar a yau din dolen dolene ko zai juya masarautar tas da bincike Dan haka Bude Baki yayi yafara jeho mata tambayar da baa cikin hayyacinsa yayi ta ba kawai amsa daya yake son fara ji duk da Babu abinda amsar Zata haifar ko hanawa akan mallakar da zaiwa Bahar da tsananin son dayake mata wanda shima a karan farko bai karbi hukuncin sultan ba,
'Menene gaskiyar auren da NUAB yace yanada shi da Bahar?
Dumm ayanah taji kunnuwanta sunyi da maganar ta sauka cikinsu wadda ta sakata juyowa a hankali ta kalli Maa sakinah taga ko taji zancen da Asim din yake fada,
Sake maimaita tambayarsa yayi wannan karan kaman kirjinsa zai Bude da tsabar tsananin baqin ciki da mummunan tashin hankalin sbd yawun bakinsa ma harsun qafe tsaf Babu komai a baki da maqoshin nasa sai kumfa,
Sauke Kai sakinah tayi zuciyarta da jikinta suna mutuwa da Sanyin data kasa furta komai bare iya kallan ayanah,
Dawo da kallo kansa ayanah tayi tana taqaita mamakin tambayarsa datazo mata a bazata tace
'NUAB baida auren kowa a yanzu ne zaiyi auren kaman yanda duniya ta sani.....
Katseta Asim yayi da cewa
'a Ina take yanzu?
A Ina tenya take shirinsu?
A Ina ne zan ganta kafin wayewan garin gobe da Zata fuskanci hukuncin kisar da mahaukacin masarautar nan ya ja mata....
Dan Allah idan kunsan a inda suke ku sanar Dani...
Kasa Dena karyata mamakinta da shakkarta ayanah tayi tana juyowa gabaki daya ta kalli sakinah wadda har lokacin kanta a qasa yake taqi fadar komai akan komai Dan bazata taba iya karya alkawarinta ba Dan haka ta zabi shiru a daidai wannan lokacin da komai ma ya kwabe Dan idan har maganar Asim gaskia ce kenan maganar auren ta fitarwa sultan,
Wasu zafafan hawaye masu tsananin ciwon gaske take riqewa tana hanasu sauko mata har Asim din ya kasa gane komai da samun komai daga garesu ya juya a fusace kaman zararre ya fice,
Yana ficewa barin gurin sakinah tayi ta nufi dakinta tana isa tura Kofa kawai ta iya yi ta Zame qasa tareda fasa wani irin kuka me tsima zuciya sbd batajin Zata iya rayuwa a yanzu Kam idan akaiwa Bahar irin wannan hukun dayake zallan zalinci,
Ayanah turo kofar dakin tayi tareda tsananin tashin hankalin abinda kunnuwanta suke kasa fahimtar koma menene,
Kukan data tarar sakinah na yi me karfin gaske jikinta na wata irin rawan ya sakata tsayawa cak a bakin kofar dakin tana kasa dauke idonta akanta zarginta akan sakinar yana tabbatuwa gabaki daya akwai abinda take boye mata,
Cikin karfin Hali ayanah datake jin tsananin tsoron amsar da Zata Samu akan tambayarta ta Bude Baki muryanta na rawan gaske tace
'Waye Bahar???
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
87
Kasa dagowa sakinah tayi tana sake cusa kanta a qasa kukanta mara sauti yana fara fidda sautin daya saka gabaki daya gashin jikin ayanah miqewa tana jin bugun zuciyarta na qaruwa me tsananin gaske,
Kasa iya Bude Baki ta furta wata tambayar tayi sbd yanda kirjinta ya toshe da fara tinanin Bahar din wadda bata taba sanin ko Kamannin dake kan fuskarta ba Amma a yanzu a yanda take ji bata buqatar kowa yayi mata bayanin komai akan Bahar din wadda abubuwa da dama suke da rudani akan,
NUAB wanda bai taba ko kallan kowace mace ba bare sanin Lamarinta Amma sosai abubuwa suke Linkin yarinyar dashi wanda take son sani ayau hakama tanada abubuwan datake son zuciyarta ta Samu tabbacinsu akan yarinyar ko Zata Samu sukunin data rasa na zuciya da ruhi tin daga ranar da idanuwanta suka sauka akan lambar bautar datake jikinta wadda tinawa kadai hana numfashinta futa daidai yakeyi,
'AYANAH BAHAR shine suna cikakken da sakinah ta ambaci yarinyar dashi idan bata manta ba,
Hakama a dakin sakinah yarinyar tamkar take rayuwa shima idan ta Tina daidai kenan,
Hakama NUAB idan ta Tina daidai Kai tsaye ya hada fatar hannunsa data yarinyar a gaban idanuwansu yana ficewa da ita batareda ya raba fatar tafin hannunsa da tata ba gurin Janta??
Bahar,Bahar' sunan ya maimaitu a zuciyarta wadda gabaki daya ta rikice Dan haka bata sake cewa kala ba ta juya ta fice bayi kusan biyar suna biye da ita ta fice daga bangaren nata idanuwanta suna wata irin sauyawa sbd matsananin bugu da mummunan tashin hankalin daya cike zuciyarta,
Itace mutum ta daya datasan inda su Leylah suke shima Leylah dince ta sanar mata a waya a waya sbd tenya sultan ya umarceta da kashe wayarta ma kwata kwata dan haka Kai tsaye can ta nufa batareda barin kowa yaganta ba,
Tana barin bangaren nata Salman dayake boye yana gadin bangaren Dan tabbatarda duk wanda ya fito ya bisa yaga inda zasu sbd sun tabbatarda bazaa rasa wanda yasan inda suke ba,
A sace baya fidda sautin ko numfashi me karfi yabi bayan Wishmah da bata ko ganin gabanta da bayinta.
Asim kuwa daga wannan bangaren na Wishmah daya bari bangaren mahaifiyarsa ya fada Babu abinda yake amfanin arziki bare cikakken hankali a jikinsa hatta kafafuwansa rawa sukeyi,
Haile dake zaune cikin matsanancin ciwon Rai me zafin gaske tana ganinsa wani irin qaruwa taji baqin cikinta yanayi sbd shine yake kokarin lalata komai na shekarun da suka debo suna tsarawa da gwagwarmaya,
Qarasowa yayi gaban hailen ba tsammani ya zube a qasa kan gwiwoyinsa tareda fasa mata wani irin kukan daya sakata kusan sumewa a zaune sbd tsananin mamaki da tashin hankalin abinda zai saka namiji kamarsa kuka Dan bata tinanin ko mutuwa tayi a yanda yake namiji kuma magajin da zai mulki boyem yayi kuka irin hakan.
Kafafunta ya kama da hannuwansa duka biyu cikin wani irin mummunan Hali ya Bude Baki yace
'mamee Dan Allah ki bawa Sultan hakuri kada a kashe Bahar wlh Kila bazan rayuba idan ta bar duniya,
Mamee wlh tsananin son gaskia da bantaba tsammanin zanyiba nake mata,
Dan Allah Ina rokon ku tayani Neman mata tsira a gurin sultan
Mamee bazan taba moruwaba idan ba.......
Turesa haile tayi daga gabanta da sauri hannuwanta da dukkanin jikinta suna daukan rawar da komai nata yake shiga zullumin daga Ina wannan masifar ta Samu 'danta da Babu mace a tsari da qaidar rayuwansa a yanzu Amma a lokaci daya ya sauya mata yana Neman zama mara amfani duka akan mace,macen ma baiwa yakewa irin wannan soyayyar??
Zufa ne ya fara keto mata tana rintse idanuwanta tayi baya ta zube a kujera tana dafe kanta ta Bude Baki tace
'wannan wace sabuwar masifar ce kuma ta bullo wa rayuwata ko yanzu data bangaren ayanah,
Ayanah kin gama zama masifa da balain rayuwata data zuriata'
Aslam da meryam ne suka shigo a tare sbd samun cikakken labarin mummunan abinda yake faruwa a fada,
Ganin halinda Asim yake ciki ya saka dukkaninsu tsayawa cikeda mamaki da qarin baqin cikin da suka taho dashi na sanin kukan dayake zubawa tin a fada,
Mameen suka kalla a tare wadda take tsananin kokarin danne abinda take ji a zuciya da jininta sbd zuwa yanzu ta gama tabbatarda sun Samu babbar matsala a rayuwa tinda Asim ya kamu da soyayyar da Zata rusa su Tin daga sama har qasa Dan haka zabi dayane gareta shine ta tabbatarda yarinyar ayau ta bar duniya kafin gobe sbd idan bata nemeta a daren yau ba ta gani a idanuwan Asim ta tabbatarda bazai kwana ayau ba batareda yayi yunqurin tseratar da ita ba ta hanyar guduwa da ita wanda hakan na faruwa Babu inda zasu Kai baa kamasu bama a cikin masarautar bare sukai ga fita kuma hakan hukuncin kisar ne shima zai hau kansa tareda tsinanniyar baiwar Dan haka kafin ma yayi hakan Zata je ta tattabarda yarinyar tabar duniya a daren kafin Asim ya isa,
Aslam da kusan bugawa zuciyarta ke gap dayi sbd baqin cikin Asim kasa magana tayi ta isa gefen mahaifiyar tasu ta zauna tareda kama hannunta daya ta Dora a cinyarta tana Dan riqewa sbd bata sassaucin wutar baqin cikin dayake cin jinin jikinta,
Meryam data kasa tinanin komai sbd mamaki gurin Asim din ta nufa tareda zubewa gabansa tana kamo hannuwansa biyu dake wata irin rawa sosai wadda ta sake daga hankalinsu Dan kamar shima mutuwan zeyi kafin goben,
Rungumesa Meryam tayi da sauri tana ji a jikinta shikenan wlh sun gama samun rashin nasara sbd har abada sbd Asim ya kamu da mummunan zafaffiyar soyayyar da zai iya komai akanta,
Shikenan daga yanzu suma nasu burin ya Kai karshe ya mutu akan idanuwansu,
Wasu hawayen radadin zuciya ne suka gangaro da idanuwanta tana sake rungume Asim din wanda jikinsa ke rawa sosai,
Shiru sukai dukkaninsu a wannan mummunan yanayin kafin Asim din ya kuma miqewa kaman zararre ya fice ya koma bangaren sultan ya zube gwiwoyinsa a qasa sbd sultan din ya bada umarnin baya son ganin kowa sai zuwa dare,
Meryam biyo Asim din tayi itama ta zube a gefensa sbd tayasa rokon sultan ya basa abinda yake so din na afuwa da sassaucin hukuncinsa sbd ita a gurin ta idan samun abinda Asim din yake so zai saka ya dawo hayyacinsa akan abinda suma suke so tabbas Zata tayasa gurfana a cikin ranar har zuwa faduwanta da sultan zai gansu.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
88
*****Aleey ne a tsaye cikin yaransu suna tsananta mugun binciken da sukeyi tin dazu din Babu Hutun ko daqiqa daya sbd tabbatarda Neman inda Bahar din take a cikin masarautar,
Maa sakinah ya daga waya ya kira wadda tana ganin Kiran bata ma amsa ba ta nufo bangaren sbd ko gani sosai batayi,
Tana isowa kofar palon NUAB ta kalla wadda tinda ya shiga aka rufe bata budeba sbd yau Kam idan ba shi dinne ya fito da kansa ba Babu wanda ya isa yaje yako bugata bare budewa.
Tattaro nutsuwa aleey yayi sbd yanason fahimtar kowace amsa na tambayar da zaiwa Maa din.
Farawa yayi da fada mata komai daya faru wanda ya sakata silalewa a qasa ta zauna da karfi tana tabbatarda shikenan ta rasa Bahar,
'Maa kiyi tinanin koina da kikasan zaa iya Kai matan masu jinin boyem gyara da sauran su wankan,
Kiyi tinanin idan basa inda aka saba to inane guri mafi cancantiwa da zaa tafi Dan cika irin wannan al'adar??
Rintse idanuwa Maa sakinah tayi tareda jin bazata iya ma magana ba ta a girgiza Kai kawai alaman batada masaniyar akwai inda kaf masarautar zai kama da gurin cike wannan al'adar sbd guri daya ne basa can kuma Dan haka duk inda suke ba gurin wankan al'adar bane kawai guri ne dayake tamkar kowane bangare so tsarin dole ze kasance daban Kila.
Shiru aleey yayi kafin ya kalleta ya sake Bude Baki yace
'ina Ammi?
Bayanin zuwan Asim da ficewansa datama Ammin tayi masa wanda ya saka aleey din tsayar da tinaninsa akan Ammin wadda bata fita koina tinda take bayan chambers din sultan bata taba fitowa zuwa koina,
Ina Zata tafi yanzu data fito din?
Numfashi mara sauti aleey ya sauke tareda juyowa kansa yana sake daukan zafi ya kalli securities dinsu dake tsatsaye a gurin yace a fito da drones gabaki daya.
Fitowa akai dasu ana kokarin connecting komai shi kuma Kai tsaye cikin system na security room din masarautar gabaki daya yafara kokarin kutsawa ta laptop din daya ajiye gabansa yana tattara hankalinsa guri daya.
Gadan gadan suka fara aikin leqawa da ganin kowane Sako dake cikin masarautar duk da tanada tsananin girman da bazasu iya a qanqanin lokaci ba aikine da zasu yisa a har tsakiyar dare ko zuwa gobenma wadda Babu lokaci,
Acan cikin fada lamarin komai ya sake daukan zafin gaske sbd sama da Ghaz Boys ashirin ne a cikin fadar a tsaye a shirye da mahaukan makaman da suka dauke duk wata niimar dake gurin da zagayenta hakama securities na bakin fadar duk sun tsaresu tareda karbe kowace irin waya dake hannun kowa da kowa tin daga manyan fada har securities da wanda yake gurin tareda tsayar da kowace security cam dake gurin da zagayenta Dan haka tsit kake ji Babu wanda yasan meyake faruwa a cikin masarautar gabaki daya securities manya manya dake masarautar basu sani ba Dan basu taba tinani ko daukan akwai kowane irin threat a cikin masarautar ba.
Kaman yanda aka tsare fada haka aka tura wasu securities din suka sake tsare hanyar ficewa zuwa gate din farko na daga ciki kuma haka aka dakatar da motsin kowane irin bawa dake cikin masarautar.
Rashin fitowan NUAB yake sake tabbatarda tsananin zafi da mummunan hadarin da yanayin yake ciki a masarautar sbd fitowansa na nufin abubuwa da dama wanda zasu iya zama alkhairi ko sabaninsa.
*****AYANAH da idanuwanta suke wata irin rufewa kafafunta na rawar datake kokarin hanata isa inda take nufar gabaki daya abubuwa ne suke dawo mata daban daban akan NUAB da sakinah dama maganganun datasan NUAB bai san dasu ba Amma ta jisu a bakinsa da kuma bayyanar Baiwar datake jin bazata iya tinanin komai a kanta ba sai ta saukar da idanuwanta akan abinda takeson tabbatarwa.
Ko data iso bangaren boyayyun marasa Imanin securities din dake gurin da sultan ya saka batareda akwai me ganinsu ba Kai tsaye waya suka daga suka kira bangaren Sultan Dan isar da bayanin.
Salman ma dayake daga nesa a labe yana ganin inda ta shige din Kai tsaye juyawa yayi yabar gurin Dan isar da sakon ga uban gidansa.
Buga kofar Kai tsaye ayanah tayi da hannunta dayake tsananin rawar da zuciyarta keyi.
Baa dauki lokaci ba aka Bude kofar cikeda mamaki me girman gaske,
Tenya ce ta Bude kofar mamakinta na tsananin qaruwa take kallan ayanah din sbd bata taba sanin ayanah na fitowa koina ba a rayuwanta bayan zuwa tirakar sultan Dan kuwa ko bangaren 'danta NUAB bata taba zuwa ba..
Wucewa Kai tsaye cikin ayanah tayi batareda ya iya cewa komaiba sbd bakinta ya gama mutuwan da bazai iya furta komaiba,
Biyo bayanta tenya tayi tana kokarin tambayar abinda yake faruwa Amma sam ayanah ta gama fita hayyacinta Bahar kadai take son gani,
Dakunan dake bangaren tafara bi taba budewa daya bayan daya tana qarasa rikicewa da tashin hankali gabaki daya,
Tashi hankalin tenya yayi da bayin da suke bangaren sukai tsuru tsuru cikin fargaba tenya kuwa binta takeyi a rude da tsoron idan ba sake dawowa ciwon ayanah din yayi ba tana tambayarta lafiya.
Bata jin abinda tenya take fada kwata kwata cigaba da bin dakunan takeyi a mummunan Hali,
Dakin da Leylah take a ciki ne tana video call da mahaifiyarta ayanah ta Bude da karfi daidai lokacinda Leylah ta juyo da sauri cikin tsoro fuskar zuhrah gabaki daya ta bayyana akan makeken screen din ipad dayake riqe da hannunta kuma a daidai lokacin ayanah ta bayyana a dakin idanuwanta a rufe tana dubawa bata ga Bahar ba ta juya batareda ta kalli screen din da zuhrah take bayyane ba ta tsayar da idanuwanta akan ayanah wani irin ja me raradin gaske yana gauraye idanuwanta.
Miqewa Leylah tayi cikin tashin hankali da tsoro tabi bayan ayanah batareda ta ajiye ipad din hannunta ba tana ambatar sunanta cikin wata irin kulawa da farbaba Amma gabaki daya duniya ayanah Babu abinda take ji take buqatan ganin bayan Bahar.
Dakin dayake kusa Dana Leylah din ta Bude hannuwanta na tsananta rawan data sakata fadawa dakin Kai tsaye a daidai lokacin Bahar ta fito wanka daga ita sai towel babba.
Cak Bahar din ta tsaya tareda ja baya cikin tsananin mamaki da farbaba me karfin gaske zuciyarta na harbawa.
AYANAH ma cak ta tsaya tata zuciyar na tsananin harbawan datake fatar kada abinda take son tabbatarwa ya tabbata sbd hakan zai nufi abinda bazata taba iya dauka ba a zuciyarta.
Takowa tafara yi kafafunta duka biyu suna rawa tareda kafe idanuwanta da sukai mummunan ja akan Bahar.
Qasa Bahar tayi da kanta zuciyarta na harbawa sosai bazata iya kallan ayanah ba sbd fuskar mahaifinta ayau sak da sak take gani a cikin tata.
Su tenya da Leylah kasa motsawa sukai sbd matsananin mamakin daya kame har kafafunsu.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
89
Ba zaton kowa ayanah ta tako kafafunta daqyar ta tsaya gaban Bahar batareda tace komaiba ta Kai hannunta Kai tsaye ta kamo hannun Bahar seti da inda tasan daidai lambar abaas take rubuce a jikinsa ta saukar da idanuwanta wanda suke qara tabbatarda saitin gurin,
Rawa hannunta ya fara ta riqe hannun Bahar din da karfi tareda Bude bakinta yana rawa tace
'AYANAAH BAHAR??
AYANAH ABAAS??
AYANAH GHAZ?????
AYANAH BAHAR ABAAS GHAZ????
Rintse idanuwa Bahar tayi da karfin gaske wasu hawaye masu tsananin zafi da tashin hankalin gaske suna gangaro mata wanda ya saka ayanah yin baya da sauri jiri me karfi yana dibanta.
Zuhrah ma da adaidai wannan lokacin idanuwanta da kunnuwanta suke shedar mata komai wani mummunan jirin ne ya dibeta wayar hannunta na subucewa tana faduwa.
Tenya ce tayi saurin riqe ayanah da numfashinta ke kokarin yankewa.
Wani mummunan Abu ayanah ta hadiye a kirjinta tana sake kallan Bahar batareda kyaftawa ba ta kuma maimaita sunanta cikakke tareda riqota da hannuwanta biyu ta jijjigata da karfi tana cewa
'Ayanah ABAAS???
wani kuka mara sauti me tsima zuciya Bahar ta kuma fasawa tareda zubewa qasa tana dafe kirjinta dake make tsananin nauyi.
Ganin hakan ya tabbatarwa da ayanah rayuwarta tazo karshe wani mummunan Jiri ya kuka dibanta ta zube a gurin numfashinta yana yankewa.
Cikin mummunan tashin hankali su tenya da itama take cikin mummunan tashin hankalin da Babu shiri ta dauki ayanah din tareda bayin da suka taho da ita zuwa bangarenta hankali a tashe.
A daidai wannan lokacin Salman shima ya isa ya sanar da haile inda Bahar din take sbd bai Samu Asim a bangarenta ba kafin ya nufi kofar bangaren sultan ya sanar da Asim wanda yayi mummunan laushi.
Dare ya fara Sako Kai a lokacin Amma Babu ta inda sauki yake koina tashin hankali ne kwatsam sai ga Sako daga bangaren Ammin zuwa bangaren NUAB da sultan akan halinda take ciki numfashinta ya dauke cak.
Aleey ne dole ya isar masa da sakon wanda ya sakasa fitowa duhun daren har lokacin Babu jijiyar jikinsa data koma ta kwanta idanuwansa jajir.
Yana isa halinda yaganta a ciki ya sakasa Kai tsaye juyowa ya nufi bangaren sultan wanda yake zaune a daidai lokacin shima yana zaman jiran isowansa.
Kafin isowar NUAB bangaren Asim su kuma suka bar gurin Kai tsaye shima bangarensa ya nufa ya hada cards dinsa da passport da dukiya me