hope bayan tafiyar Ayanah ghaz amma ayau Ayanaah ta dawo babu sauran kowane hope ga haile ma datake da yaya dashi bare ita da batada kowa da komai.
Bude idanuwanta tayi ahakali da sukai jajir tana sake sauke numfashi me sanyi ahankali tukuna ta dauke kafafunta daga qasa tana dorasu akan gadon tareda kwantawa ahakali tana rufe idanuwanta sbd daga karshe dai nacewa a auren sarauta bai bata komaiba bayan karshe me kadaici da quncin da baida ranar tafiya,
Auren sarauta ga duk macen da baa so bai taba zama farin ciki ga kowace mace ba dan haka take jin inama zata iya dawo da baya ta zabi auren soyayya da kauna akan auren sarautar da zaa badaka kyauta ko tukuici.
Shi kansa sultan a wannan lokacin dayaji isowan macen da itace rayuwarsa ayanzu ajiyan zuciya ya sauke yana cigaba da adhkar din dayake yi tin asuba yana jin sanyi da nutsuwa suna sake ratsa ruhinsa sbd yawo da kwana kwana ya qare masa lokaci yayi da ba 'danta kadai ba duniya ma gabaki daya zata san da ita matarsa ce cikakkiya a yanzu ba wishmah dinsa ba duk da duka matsayin biyu nata ne har abada.
***Su Ammi kuwa koda suka isa bangarensu bayin bangaren sun gama yiwa komai na bangaren wani irin gyara na musamman duk da ba wani aiki me girma bane sbd komai da aka sauya na bangaren harma da tsarinsa dan haka kowannensu cikin samun nutsuwa da farin cikin kasancewa a gida suka nufi dakunansu kowace bayi bayi biyu na bayanta da akwatinanta.
Kai tsaye daki bahar ta wuce a gajiye duk da tayi bacci sosai cikin jirgi ta rage ciwon kai da damuwa sbd baccin ya taimaka mata sosai,
Tana shiga dakinta su salmah suka isa da suitcase dinta har gaban closet suka bude suka fara jera mata kayan a ciki ba tareda doguwan motsiba,
Wayarta dake hannunta ta ajiye gefen gadon dakin da already an kunna mata ac da qamshi me dadi yana tashi a hankali ta nufi bathroom.
Zare komai na jikinta tayi ta fasa sabuwar toothbrush me tsada dasuke jere a toilet din ta fara brush.
Tana gamawa wanka tayi da ruwan zafi masu zafi sosai ta gama ta fito daure da towel zuwa lokacin su naimah sun fice daga dakin harma da haske sosai an rage mata.
Shiryawa tayi sama sama ta saka riga da wando na bacci marasa nauyi tai shirin sallah tai sallan asubar da basu samu yi ba tana gamawa da adduointa miqewa tayi ta haye gado ta shige ta kwanta sbd bacci takeji sosai da mutuwan jiki.
Bacci ne ya dauketa kaman yanda kusan dukansu da kowa ya gama komai baccin ya kwanta yi hankali a kwance bayan sun daga hankalin mutane da dama a cikin masaurautar da dawowansu.
Ita kanta Ammi data dawo da damuwa da bacin rai jin tayi tana samun nutsuwa da kwanciyan hankalin bacin ranta na raguwa.
Tsit masarauta tayi dan kuwa ko fada tinda sultan na hutu ayau din na rashin fitowa sai kowa ya zama a low ba wata hayaniyar aiki.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
144
Asim dayake bangarensa shima yaji isowan Ammin shiru yayi kawai yana sauke kansa qasa sbd yanada tabbacin Ammin da Bahar dinta ta taho wadda yake tsananin fatar Allah ya nesantasa da duk inda zai sake ganinta ya saketa a idanuwansa sbd hakanne kadai zai cire masa ita daga zuciyarsa ya rungumi danganar daya riga ya daukarwa ransa.
Leylah ma dake bangaren mahaifiyarta tinda ta dawo shiru tayi tana sauke ajiyan zuciya da jin farin cikin dawowan Ammin sbd komawa bangarenta zai rage mata damuwan datake ciki sbd irin yanda su maa sakinah da Ammin ke nuna mata kulawa da kauna duk da tanajin wani irin nauyi a kirji na ganin Bahar da zatai amma kuma zata fuskanci hakan ta hadiye kowace irin radadi da nauyin da zataji harta saba ya dallashe ta dena jinsa sbd bazata illata rayuwarta akan abinda bazata taba samuba koda tanada rabon samun a gaba to gwara yaxo mata a bazata amma a yanzu tana buqatan healing duk da batajin zata samu hakan a kusa sbd damuwa data aureta harma ta zamar mata ciwon daya kasa warkewa tinda ta dawo,
Damuwa ce tai mata yawan da batada kowace irin walwal koyaushe tana kwance a daki cikin rashin karfi da zazzabi,
Abinda yake sake shigar da zuhrah damuwa da tinani kala kala akan auren leylah din shine babu ranar da Asim din baya zuwa bangaren ganinta,
Zai shigo ya gaida mum din su gaisa a girmamawa da mutuntawa tukuna ya shiga dakin Leylah din kai tsaye acan yake zuwa su gaisa ya dubata hakama yayi yai akan kiran likita ya dubata taqi yadda sbd batason mum dinta taji tana cikin damuwa me yawa ne tafara tambayarta abinda yake faruwa tinda ta tsaya akan batada lafiya ne yasa ta dawo bangaren.
Da farko mum din ta dauka laulayi takeyi sai kuma taga kaman Asim din a cikin damuwa sosai shima saita dauke tinaninta daga kan laulayin ta shiga damuwan itama ga shuraim yana kwana biyu bai shigoba batasan sakasa wata damuwan akan wadda take ganin kaman yana ciki shima ta ayyukan sarauta shima dan haka sai bata fada masa ba tayi shiru ta nema yar uwarta Ayanah ta fada mata.
Sai yamma lis kusan kowa ya samu fitowa daga dakinsa lokacin kowa yaci ya koshi ya samu hutu iya hutu,
Su Maa ne ke palo zaune cikin hutawa maa tenya tana waya tana fadawa yarta akan ziyarar da zata kawo a boyem itama,
Ayanah ce ta fito cikin shigar doguwan rigar bahrain me kyau da tsada mara ado sosai ta qaraso ta zauna tana ajiye wayarta gefenta su salmah suka fara shigowa suna jere fresh kayan marmari da sukai sanyi a tsare.
Suna gamawa suka bar gurin daidai nan zuhrah ta shigo bayinta biyu na bayanta suka tsaya daga kofar palon farko suna komawa gurin bayin bangaren dan zaunawa acan su jirata.
Itama leylah da bayinta biyu suke biye da ita dakatawar sukai suna bin bayan bayin Mum dinta.
Suna shigowa palon Ayanah ta zubawa yar uwarta idanuwa cikeda kauna me tsanani tana jinta har cikik jininta ta miqe suka rungume juna Zuhrah ta kama hannunta tayi kissing cikeda kauna kafin itama ayanah din tai kissin tsakiyar kanta tana ambatar sunanta.
Cikeda kauna itama Sakinah dasuke jinta a zuciyarsu ta maye gurbin nurat da babu a cikinsu zuhrah ta rungumeta tana kissin tsakiyar kanta sunawa juna barka da haduwa cikin aminci.
Akan leylah Ammi ta maida idanuwanta tana kalla cikesa mamakin ramar datake gani tattare da ita da wani irin haske data qara fayau ta ware mata hannu ahankali tana cewa
'Zo Yene leylah'
Tahowa leylan tayi a natse tana jin hawaye na ciko idanuwanta sbd jin kaunar da Ammi kewa mum dinta da ita.
Rungumeta Ammi tayi a jikinta sosai da kyau cikeda kauna da kulawa tana cewa
'Insha Allah koma menene damuwan zai zama alkhairi kinji Leylah'
Gyada kai leylah tayi a natse suna zaunawa gabaki dayansu a kujera tana gaida su maa sakinah cikin girmamawa suka amsa Sakinah na mata kallan kulawa da damuwan ramar datake gani a tattare da ita
Maa tenya kuwa yanayin fatar Leylah din take kalla tana shiga nazarin sauyawanta.
Zuhrah ce ta bude baki zata tambayi Bahar sai ga bahar din ta fito a natse cikin riga da wandon Flairs Purple masu fadi sosai da sukai mata kyau sosai sbd sun qara fidda haskenta sosai da sauyawan datai itama na sauyin rayuwan data samu.
Zuba mata ido Zuhrah tayi tana kallanta da dukkanin kaunar datake wa Abaas da jinin duk wani ghaz da suka rasa tana jin inama itama zata iya dawo da baya da itace zata nemo bahar ta bata dukkanin kauna da soyayyar uwa da uba data rasa.
Hannu daya ta miqawa bahar din tana ambatarta da sunayen da suke ambatar abaas dasu da yana yaro na kaunar da batada sirki.
Qarasowa bahar din takeyi itama Ammi ita ta dago tana kalla tata kaunar da soyayyar ta daban ce kaf duniya akan bahar dan haka ko data iso itama saida ta kalli Ammin cikeda kauna da kewa na fushin datake yi da ita kwana biyun kafin ta kama hannun Mum zuhrah tana zaunawa gefenta a jikinta tana bude baki ta gaidata.
Amsawa zuhrah tayi tana tambayarta karatu da uk.
Amsawa tayi tana maida kallanta akan Leylah ta ambaci sunanta a natse tana gaidata.
Amsawa leylah tayi tana mata ya hanya a natsen itama tanajin ma bataji nauyin kirji da zafin datai tsammanin ji dinba dan haka ta dan sake jikinta a cikinsu tana tinanin halinda Asim yake ciki a yanzu data tabbatarda yaji isowan Bahar din a cikin masarautar.
Firar ahalin dake kaunar juna da babu matsaloli suka ringa yi hankali kwance suna ciye ciyensu wanda ya saka Ammin aje damuwarta a gefe tana jin dadin kasancewa a tareda ahalin da suka rage mata a duniya,
Ita kanta leylah jin tayi damuwarta ta rabe gefe tana samun nutsuwa da walwala dan haka basu tashi daga zaman ba saida akai magrib suka tashi sallah,
Dakin Bahar taje tayi sallah cikin karfin hali sbd tanason cusawa kanta salama,
Ita kanta Bahar bata damu ba daman ba itace me matsalarba dan haka dan sake mata tayi har sukai dan firar zuwan nasu uk da dawowansu kafin suka fito cin abinci wanda sukaci dukkaninsu da iyayensu.
Sai bayan ishai Zuhrah tabar bangaren ta koma tabar leylah anan wadda tace anan zata kwana.
Dakin Bahar din still tayi zamanta wanka tayi ta fito ta zauna tafara shirin bacci sbd yanzu da wuri take bacci,
Sabbin layan bacci ta dauka a cikin closet din Bahar ta saka masu kauri riga da wando da sukai mata kyau sosai sbd bata saba saka kayan bacci riga da wando ba tafison riga kawai wadda zata sauka kokuma qarama ta bacci.
Tana kokarin miqewa daga gaban mirror kiran Asim ya shigo wayarta sbd yaje can bangaren kaman yanda ya saba bai sameta ba.
Ajiyan zuciya ta sauke tana komawa zaune a hankali ta dauki wayar ga mamakinta cikin nutsuwa yace mata yana bangaren Ammin yazo ganinta.
Bata taba dauka zai iya tahowa bangaren ba kodan mahaifiyarsa da kuma bahar dan haka miqewa tayi a sanyaye sbd tasan dole zuciyarsa na cikin wani irin mawuyacin hali na zuwansa nan din.
Bata iya saka komaiba akan kayan jikinta ba sbd damuwa hakanan ta fice daga dakin hula ce kadai a kanta wadda itama gashinta dayake sake bata rufesa ba.
Palo ta fito daidai lokacinda Maa sakinah data gansa a waje tsaye tai masa iso har cikin palon cikin kulawa da kauna sbd a yanzu shi nasu ne.
Zaunawa yayi a natse yana kasa dagowa ta wuce taje ta sanarwa Ammi Asim yace yanason gaidata.
Leylah kuwa qarasowa tayi tana kallansa tareda kasa dauke idanuwanta akansa zuciyarta na wani irin harbawa ahankali da sanyi sbd tausayinsa shima dagowa yayi ya kafeta da idanuwansa masu kyau da sukai sanyi yana kallanta tareda jin confidence da karfin zuciyar iya fuskantar komai.
Fitowan Ammi ta dakatar da ita daga isa garesa sbd tasan ba qaramar quna yake ciki ba akanta ya daure ya danne ya shigo dan haka dauke idanuwanta tayi daga kansa tana saukewa qasa.
Qarasowa Ammi tayi cikin kalama da kulawa tana ambatar sunansa da sakewan data sakasa dago idanuwa ya kalleta yana jin kwarjininta har cikin idonsa dan haka ya dan sauke ido yana gaidata da mata sannu da zuwa cikin girmamawan dataji dadi tai masa sannu da kokari da kuma basa hakurin sunje bata nan.
Sama sama sbd rashin sabo duka danyi magana kafin ta miqe tabar palon.
Tana barin palon leylah zubawa hannuwansa dake rawa ahankali ido tayi yana boyewa kada kowa ya lura take idanuwanta suka sake cikowa da hawaye ta tako ta iso gabansa bata iya cewa komaiba ta kama hannunsa a hankali ta miqar dashi tajasa suka bar palon suna ficewa daga bangaren.
Hanyar bangarensa take kokarin nufa dashi ya dakatawa a hankali kafin ya cire jacket din dake saman kayansa ya saka mata sbd batada rufa a jikinta duk da dare ne.
Yana saka mata ya dauketa cak daga qasa sbd hadda takarmi ta manta bata sakoba ya nufi bangaren nasa da ita yana jin gashin jikinsa na miqewa da irin lafewan datai a jikinsa tareda saka hannuwanta biyu ta zagayesa dasu sbd irin daukan da yayi mata.
Suna barin bangaren karfe tara da rabi ta buga a lokacin Ammi ita kuma ta fito dan tafiya magana da sultan wanda ta dakatar daga zuwan dayaso yi bangarenta wanda tasan tsaf zai iya haduwa da NUAB a bangaren dan shima yanada wuya ya kwana bai taho gaidataba amma ganin har 9 ta wuce baizo ba ya sakata ficewa xuwa bangaren sultan din bada niyar karban kwana ba sam.
Tana ficewa tara da talatin da hudu manyan securities dinsa biyu da duk inda ya saka kafa a cikin masarautar suna bakin gurin suka iso kofar bangaren nata suka tsaya 9:40 a natse sukuma tukuna sai gasa ya sako kai a cikin wata lafiyayya sanyayyar nutsu da izzar ikon mulki da kamewa tareda kwarjininsa me karfin gaske yana sanye da fararen Armanis da sukai masa kyau tareda fidda kyau da samartakansa.
Aleey ne a gefensa suka iso suka shigo wanda take bayin ciki suka fice daga bangaren a natse suka bar gurin gavaki daya har saiya bar hanyar gurin ma kwata kwata.
Su Maa sun shige dukansu dan haka kai tsaye palon Ammin ya nufa bai ganta ba ya fidda wayarsa ya saka kiran Maa sakinah wadda ta fito a natse suka gaisa ta sanar dashi Ammin bata nan taje gurin sultan.
Bazata iya saka kanta a tsaka me wuya ba shiyasa ta fada gaskiyar kai tsaye sbd lokaci yayi da kowa zai fuskanci abinda yake zahirin gaskia.
Shiru yayi idanuwansa na dan fara sauyawa kirjinsa na fara nauyi zuciyarsa na fara wani irin daci da jin wata irin damuwa na lullubesa sbd da gaske Amminsa takeyi Sultan zata zaba akansa.
Kofar dakin Bahar ce ta bude a natse wanda ya saka Maa sakinah juyawa ta kalli kofar daidai nan Bahar din ta sako kai a palon sanye da kayan bacci riga da wando marasa tsayi ko kadan amma ta sako hijabi dogo har qasa yana ja sbd tinanin mijin leylah din yana nan kuma tana buqatan dauko abu a dakin maa sakinah.
Batasan dashi ba saida tayi taku biyu ta tsaya cak sbd qamshin daya ratsa hancinta ahankali ya shiga kanta har zuwa kirjinta ya bawa zuciyarta ahankali cikin wani sanyi daya saka jikinta sanyi ta dago ahankali.
Numfashi me zafi na abinda yake cin zuciyarsa ya sauke yana hadiye fushinsa tareda dago fararen idanuwansa dake kashe kowace mace akansa ya sauke akanta,
Barin gurin maa sakinah tayi tana komawa dakinta tareda masa saida safe,
Kallo daya yayi mata dukkanin abinda yake jin yana cinsa yaji yafara sauka ahankali yana narkar da zuciya da sakar da duk wata zafin dake jini da zuciyarsa.
Kasa dauke idanuwansa yayi daga kanta yana jin duniyarsa ta tsaya cak,
Lumshe idanuwansa yayi tareda sake wani numfashin da taji saukansa har cikin ranta itama ta sauke idanuwanta ahankali tanajin idanuwanta na cikowa da hawayen da batasan na mene ba.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
145
Saukan tafin hannunsa me sanyi taji a gefen fuskarta batareda tasan ya iso gabanta ba daya sanyata dago idanuwanta ta sauke masa yaji yana sake rasa kansa dan kuwa ayau ya gama tattarda itace farin ganinsa da babu abinda yake sauke fushinsa a lokaci daya idan ba itaba.
'Finally Yar Ammi' ya furta da wani irin sautin daya saka tsigar jikinta tashi ta sauke idanuwanta qasa daga kallansa tana jin maganar datake son fada masa idan sunzo akan Ammi da zata tambayesa suna bacewa daga bakinta amma batajin zata iya barin ta kasa fadarsu sbd zata iya somewa a gaban Ammi idan ya bude bakinsa yace magana zaiyi.
Motsi bakinta ya fara wanda yakeson furta magana amma ta kasa sbd komai na jikinta daya mace.
Kallanta yakeyi batareda motsawaba kallan da bai taba yiwa kowace irin halitta shi ba ya gangara da idanuwan a bakinta dayake motsi yagane magana takeson furtawa dan haka dauke hannunsa daga fuskanta yana sake bude baki yace
'Inason koma menene bakin yakeson furtawa a karan farko'
Kama hannunta yayi zuwa dakinta wanda tayi saurin cin burki tana kallansa da sauri ta girgiza masa kai.
Oh ok' yace yana juyawa da ita suka nufi kofa suka fice.
Suna fita taga suna kokarin nufar bangarensa dan haka da sauri ta sake cin burki tana kokarin zare hannunta.
Wani kallan yasake mata kafin ya dakata a hankali yana binta da wani irin kallo sbd ya karanci tsoronta a bayyane wanda ya saka jikinsa sake mutuwa akanta.
A sanyaye ta bude baki tace
'Magana ne kadai nakeson muyi banason Ammi tasan bana nan'
Kafeta yayi da idanuwansa yana mata kallan da zuciyarta ke tabbatar mata da mutuwa yakeyi akanta hakama itama tata zuciyar kasa riqe kanta takeyi akansa da duka kallan dayake mata wanda yake kawar da duka tsoro da shakka tareda fushin datakeyi akansa tanajin ganinsa kadai na bude nutsuwan data rasa ta dauke idanuwanta daga kallan dayake mata a hankali.
Danne zuciya da feelings dinsa yayi a cikin yanayi na karfin hali sbd Su aleey da securities din dake tareda su a bayansu nesa kadan biye dasu ya dan sauke numfashi me sanyi da nutsuwa kafin ya bude baki yace
'Na fahimta you just wanna talk right?
Ammi bazata taba sanin bakya nan ba sbd tana gurin Sultan'
Hannunta ya dan sake kamewa a cikin nasa din daman bai saketa ba ya jata a natse suka fara takawa zuwa bangaren nasa tana jin tsoro da nutsuwa a lokaci daya amma koma menene ta zabi magana dashi akan yayi mata alkawarin bazai taba maganar da Ammi zata iya tambayarsa ba ita shine kadai abinda take so.
Tsit hanyar take babu kowa ba motsin kowa sbd matiqar ya gifta wannan hanyar ta zuwa bangaren iyaye mata zuwa gurin Ammin babu me sake bi hanyar zaa tare farkonta da karshenta har sai ya gama ya fito koda kuwa awanni nawa zaiyi dan haka har suka taka a hankali a cikin wata nutsuwa suka bar bangaren babu kowa da komai,
Hanyar bangarensa suka nufa wadda take dauke da wani irin hasken dayafi koina a hanyar dan haka suna sako kai a hanyar aka fara kashe wutar hanyar daya bayan daya ana hana kowane haske haske kaskesu sbd aleey daya tura sakon a kashe wutar hanyar da gaggawa.
Duhu mara cutatarwa hanyar ta dauka har saida suka isa bakin main kofar