Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   77 / 100

228K to 231K   out of 299.8K words

zata tafi da ita ya sakata tattaro karfin hali ta miqe ta koma daidai dan tsoron takeyi kada a tafi a gane jiki taji a hannun namiji sosai a fadawa Ammin tasan abinda ya faru.

Ganin ta warke din sai ammin ta dan dakata daga maganar asibitin.

Ana sake kwana biyu ma Bahar din tini tafara zuwa makaranta sbd ta sake nuna lafiyarta kalau duk da ta kasa dena jin abinda take ji kwata kwata na zazzabi daga yamma tayi da kuma wani irin ciwon gabbai dan haka jikint yayi sanyi akan wanda take dashi ta koma kaman wata innocent baby sbd sanyi.

Su kuwa su maa ganin ta sake ta warke ras ya sakasu sake kwantar da hankalinsu suna fuskantar rayuwa Tenya naci gaba da mata irin gyara da bata abubuwan da suke bata acan baya tin farko a gaban Ammi sbd daman haka akewa mata yayan sarautar boyem anafin shekaru ana musu irin wainnan abubuwan kafin aurensu wanda yake bin jikinsu tini tin kafin su saka ran aure ma dan haka Ammi ma bata damuba wayarta take yi itama da na sultan idan kuma tayi da NUAB sai taji tana shiga tsoro da shakka da fargaba dan haka a yanxu babu abinda yake bata tsoro da fargaba irin zuwa boyem sbd fuskantar NUAB.


Bayan kwanaki da dawowan Ammin Bahar ta warke ras ta koma harkokin gabanta na karatu da classes dinta duk da wannan karan sam ta dena yawo kai tsaye koina daga school sai gida sai kuma classes dinta masu mahimmanci data zaba ta zubar da sauran tana jin bata buqatan hayaniyar da yawa a rayuwanta yanxu sbd ko jikinta a yanzu kaman ba nata take jinsa ba.

Satinta hudu rabonta dashi rabonta da kamshinsa rabonta da jin koda muryansa sbd ko waya yakeyi da ammi bata zuwa ta zauna kusa sbd jinsa yana saka zuciyarta cikin rashin nutsuwa da damuwan da batasan ta ina take shigartaba dan haka a duk lokacinda taji Ammin ta ambaci kalmar HAYATEEM take nesa da Ammin sbd kada ta rasa nutsuwanta ta kwanaki.

Kayanta data dawo dasu daga Birmingham kaf qamshinsa sukeyi hakama babu wanda zata daga ko kalla batareda tina abinda ya faru da itaba a lokacinda data sakan dan haka ta tattara su ta maida a suitcase din dataxo dasu daga can ta rife ta kaisu gefen closet dinta ta jere tabarsu acan.

Exams suke kokarin farawa dan haka Neesah datai tafiya ta dawo itama sun dade basu hadu ba dan haka a ranar data dawo kai tsaye gidan su bahar din zata taho ta kwana biyu tukuna ta koma hostel dan haka drivern Bahar dinne yaje har airport ya daukota.

Suna isowa gidan da gudu suka rugume juna tin a palo suna jin kaman sunyi shekara basunga juna ba sunata ihu.

Ihun su ne ya fiddo Ammi data gama waya da zuhrah akan maganar leylah da ba lafiya sosai kuma gashi ta rasa gane musu itada mijinta wanda shima ya kebe kansa ba wata lafiyar.

Da murmushin karfin halin ganin yanda Bahar dinta ke murna ta fito tana jin sanyi a zuciyarta tana kaunar duk abinda zai saka Bahar farin ciki da dariya koma yake sakata shiyasa take kaunar neesah a ranta sbd itace kadai kawar Bahar dinta a duniya kuma kusan itace ta tsaya ta bawa bahar confidence din datake dashi ayau.

Tenya na daki itama ta jiyosu dayake sun saba da hayaniyarsu indai Neesah na gidan dan haka bata fito ba waya takeyi.

Maa sakinah ce datake kitchen ta fito tana ajiye chicken biryani data gamo a dining tana fitowa dining din ta nufo palon.

Dagowa Neesah tayi daga qanqame Bahar din tana kallanta ta dan bugeta da kafadanta tana cewa

'Hey girl naga Birmingham ta sauyaki ko nace Our Sultan 2weeks together na tabbata kinada abubuwan danakeson ji da yawa oya oya.....

Ganin Ammi ya saka Bahar saurin juyawa gabaki daya tana kallan Ammin da itama su biyun take kalla cikin dan mamakin jin Abinda neesah ta fada batareda tasan Ammin ta fito ba duk da bata fahimci me neesah ke nufi ba.

Bahar dauke idanuwanta daga kallan Ammin tayi tana jin zuciyarta na shiga fargaba da tsananin tsoron Ammin ta dan janye daga kusa da Neesah din sbd ta yanke maganarta daidai nan Maa sakinah data iso kuma taji zancen ta sauyasa cikin karfin hali da basarwa da cewa

'Neesah ke da kika biyo gajiyan tafiya kuma kika biyewa bahar kuka tsaya anan kuna ihu'

Neesah na jin hakan ta juya ta kalli Ammi tana basarwa da bayyanarda farin cikin ganin Ammin tana mata sannu da dawowa cikin sakewa.

Amsawa Ammin tayi itama a sake tana rasa zancen fara kamawa sbd sunma rikitar da ita da abinda taji da shima duk ya rikitar da tinaninta sbd sai taji kaman tafiya bahar tayi waye sultan?
Su Sakinah sunsan tafiya tayi?
Sati biyu akace kokuwa?
Shin anya ma bahar dinta ake magana.

Kallan bahar tayi wadda ta sauya a take ta kasa kallanta ya sake sakata tinani ta bisu da kallo har suka shige dakin bahar suka rufo kofar.

Suna shiga neesah ta kalli Bahar zatai magana bahar ta katseta da cewa

'Ammi batasan naje koina you better know wat to say a gabanta'

Janta Neesah datasan sunan Sultan kawai a bakin Aleey wanda koyaushe ta kira tana son magana da Bahar yake cewa tana tareda Sultan kuma baa kai waya.

Har bakin gado ta kaita ta zauna tana kokarin fara gulma bahar ta tureta tana cewa 'kije ki fara barin ki huta da wannan son jin zancen naki'

Dariya neesah tayi tana miqewa ta nufi toilet a lokacin aka shigo mata da akwatinanta guda biyu dakin aka aje.

Ko data fito wanka Bahar na miqe kife a gado tana duba abu wayarta data zubawa ido kaman me jiran shigowan kira.

Shiryawa tayi a cikin kaya marasa nauyi ta saka abayan sallah tayi sallah tana idarwa ruwan dake dakin ta dauka tasha kadan ta mayar ta zauna gefen Bahar wadda tayi shiru a lafe idanuwanta rufe
Tasan ba bacci takeyiba dan haka ta shafi fuskarta me kyau da tsari tareda fixgan hankali tace

'Baby are you missing him??

Bude idanuwa bahar tayi ahankali ta kalli Neesaha din batareda ta motsaba ta kafeta da ido tana rasa abin fada.

Cikin kauna da kulawa Neesah ta kama kan bahar din ta dora akan kafafunta tana shafawa ta fara jero mata tambayoyi dan har lokacin batasan waye shi ba abu daya kawai tasan Bahar din ta fada mata akwai aure a tsakaninsu wanda batasan matsayinsa ba.


Saida aka gama shirya dining suka fito suka samu kowa yana table din kaman munafukai haka suka qaraso suka zauna sbd Bahar ta gama fada mata komai dan haka itama yanxu a tsarge take da kada Ammi ta gano komai akan maganar datai dazu.

Abinci suka fara ci a cikesa kulawa da nutsuwa ba doguwan fira,

Sunyi nisa sosai kaman daga sama maganar Ammi ta sauka kunnuwan dukansu.

'Bahar tayi tafiya ne bayan bananan?
Ina ta tafi?
Ita da wa sukai tafiya???

Dauke wuta kowa yayi a gurin tareda tsit kowa na kasa cigaba da cin abincinsa musamman Bahar din wadda ta qware tafara tari saida Ammin ta ajiye spoon din hannunta ta dauki ruwa takai bakinta tafara bata tana mata sannu cikin sake shiga tinanin tabbacin anyi tafiyar kenan.

Ruwan Bahar tasha kadan ta janye cup din daga bakinta tana dagowa ta kalli Ammin wadda ta kafeta da ido.

Sake maida kanta tayi qasa tana kasa cewa komai gabanta na mugun faduwa.

Maida kallo kansu maa Ammin tayi da mamaki tace

'Ah ah tambaya fa kadai nayi naji anyi maganar tafiyan ne kuma na sani ko akan school ne sukai tafiyan kawai dai naji tinda neesah ta tambaya ba tare suka tafi ba kenan kuma nasan Bahar bazata iya tafiya ita kadaiba shiyasa hakama banason tayi tafiya koinada wainda bata saniba kuma batareda kowa na gida a tareda ita ba.'

Shiru suka sake mata ba wanda ya iya cewa komai sema karfin halin cigaba da cin abinci da sukai musamman tenya da batada abin fada.

Maa sakinah ce tace

'Ai insha Allah bama zata sake tafiya koina ba'

Ko data fada hakan tana cigaba da cin abincinta.

Bahar kasa cigaba da cin abincin tayi gabaki daya ta ajiye ta dauki tissue ta goge bakinta tana daukan ruwa tasha tana ajiyewa ta silale tabar gurin.

Tana barin gurin itama Neesah tabi bayanta amma ita taci sosai sbd tana tareda yunwa sbd tafiya.

Tana barin gurin Ammi ta sauke ajiyan zuciya tareda kallan su maa tenya dakyau ta bude baki tace akwai abinda ya kamata na sani ne??
Wani abin ya faru ne naga kaman ba wanda yaji dadin sanin danayi anyi tafiya.'

Ajiyan zuciya dukansu suka sauke a boye amma ba wanda ya iya cewa komai har lokacin dan haka ta sake shiga zargin akwai abinda ya faru din kenan.

Bata sake cewa komaiba har suka gama ta koma dakinta bayan ta gama komai na shirin bacci ta zauna bakin gado dan qarasa maganarta da Zuhrah da sukeyi akan Leylah da batasan yaya zata fuskanci meyake shirin faruwa ba.

Itace ta saka kiran zuhrah din a lokacin itama zuhran ta gama shirin bacci tana dakinta zaune sbd yunar baya qasar yana kuwait gurin uwargidansa.
#MAMUH
09033181070

HAYATEEM
Mamuhgee

141
Magana sukeyi sosai a natse da neman mafita da shawara a tsakanin Ammin da zuhrah wadda take cikin damuwa tana sake sanar mata da dole akwai matsalar dake tsakanin Leylah din da Asim wadda ta boye ta kasa fada mata amma ita tinda ba yarinya bace tana gani ta sani,

Shuraim ma wanda take neman shawaransa akan komai taso fada masa amma ganin shima tinda ya dawo daga tafiyar da yayi bata gane masa ba a cikin damuwa yake dan haka take tinanin Allah yasa ba matsala suka samuba dukansu da Sultan LEUL sbd sunce yana qasar sun barosa.

Shiru Ammi tayi jin saukan maganar a kunnenta kamar tsawa me karfi zuwa kirjinta amma bata jin taji abinda zuhrah din ta fada dakyau sbd kaman cewa tayi NUAB yazo Oxford shima kokuwa sultan yasar take nufi dan haka tsayar da tinaninta tayi guri daya dan ta fahimta tace

'NUAB kike maganar sun bari anan kokuwa Sultan?
Anan Oxford suka gansa?

'Eh NUAB din dai suka bari anan sbd shima yabar nan kusan satinsa biyar baya nan fa ashe can ya tafi acan suka barosa yandai shuraim ya fada mun'

Sake shiru Ammi tayi tanajin wata zufa na tsinke mata tana sake kasa yadda da abinda zuhrah ke fada,
Tayaya NUAB zai taho Oxford bata saniba dan kuwa koda bata nan tana dawowa su Sakinah zasu fada mata,

Basu fada mata cewan yazo ba wanda kenan baizo dinba amma kuma shi kansa Shuraim din tinda yace ya gansa kenan ya gansa din
To kenan baizo nan gidan ba qasar yazi kadai ko me??

Kasa cigaba da magana tayi ta cewa zuhrah ta bari da safe zasuyi magana,
Tana fadar hakan ta kashe wayar tana rasa wane tinanin zata kama ko wane zata fara kira ta tambaya.

Shuraim ta kira a waya wanda yana ganin kiranta cikeda girmamawa da kulawa ya daga ya gaidata ta amsa a natse kafin ta dan fara da nasihar su rage saka mahaifiyarsu a damuwa koma menene damuwansu su idan wadda zasu iya sanar mata ne su sanar mata su dena sakata damuwan ganinsu a wani yanayi mara dadi.
Tana gama nasihar ta jefa masa tambayar ashe yaxo uk din batanan ta dan yi tafiya,

'Eh Ammi nima dayake ba dadewa zanyiba ina gama dan aikin daya kaini na juyo sbd kadama Sultan LEUL ya rigani baro uk din ya dawo sbd akwai ayyukan dake a qasa'

Ajiyan zuciya Ammin ta sauke tana ji dai NUAB din yaxo uk din kenan,

'Ai nama dauka tare sukayo tafiyar sbd tinanin ko tafiyar data shafi aikin masarautar ne'

'No ba tafiyan masarauta bane a rana daya dai muka isa dan nama rigasu isa nan gida gurin su Maa sbd muna can dukanmu dasu leylah ya iso gidan.'

Masha Allah' Ammi tace daqyar tana masa sallama sbd tagama jin cikakkiyar zancen daya saka jikinta mutuwa gabaki daya wayar hannunta ta zame ta ajiye tana jin tashin na rifeta na damuwa da shakka tamkar NUAB dinne ubanta haka taji fargaba ta rufeta.

Zufa tafara gogewa daga fuskanta sbd tasan ya gama samun cikakken sani ga gani ya shedar ya tabbatarda bata nan tana tarera sultan yasar,
Kwana nawa yayi yasan batanan?
Ya sani amma bai taba nuna mata yasaniba?
Yasan tana tareda sultan amma ya iya danne zuciya da fushinta bai nuna ba?
Meyake faruwa?

Kasa motsawa tayi duk da tanason motsawa taje ta tambayi su Sakinah taji me zasu fada mata akan wannan babban lamarin da bazasu ce sun manta fada mata bane dan kuwa lamari ne girman gasken daya kamata ace shi suka fara tarbonta dashi amma sukai shiru,
Akwai dalilin daya saka suka boye mata wanda ko wane irine me girma ne sbd babu abinda yakeda girman daya wuce fada mata zuwan NUAB da batanan a yanzu.

Sake shiga rudani da shakka tareda damuwa me girman gaske tayi sbd kenan akwai tashin hankali a tsakaninsa da Sultan suna haduwa dan haka taji zuciyarta na sake rasa nutsuwanta gabaki daya ta dauki waya ta nemo numbern sultan ta saka kira dan sanar masa NUAB yasan bata nan tana tareda shi tsawon wannan lokacin.

Shiru yayi shima sbd a bazata zancen ya shiga kunnuwansa dan haka ya shiga tinanin kenan lolacin da NUAB din zaisan ya shiga gabansa shima yayi dan kuwa a yanxu zai sanar dashi igiyoyi aurensa uku reras ne akan mahaifiyarsa dayake ikirarin ya rabasa da ita,zai kalli cikin idanuwansa ya fada masa har koyaushe shine gabansa sbd shine ubansa kuma a yanxu daya mallaki Ayanah ghaz ya gama dashi gamawan da har abada dole ya bisa dan a mutuwa ce kadai zata cireta daga hannunsa.

Kwantar mata da hankali yayi bata tabbacin zai nemi ganin NUAB din da kansa ya fuskance ya sanar masa da komai.

Sake tashi hankalinta yayi dan kuwa tasan idan NUAB din yaji tayi tafiya da sultan ya iya danne zuciyarsa da fushinsa idan yaji cewan aure sukai a yanzu batareda ta sanar masa ba ko neman izininsa batasan yaya zaiyi ba shi da sultan dan haka taji gabaki daya boyem din take buqatan zuwa a cikin daren sbd koma yayane ta fuskancesa a lokacin da zaiji zancen ta bawa zuciyarsa salama da sassaucin halinda zai shiga sbd tasan zata qona zuciyarsa fiyeda yanda zai tsammata.

Kasa rintsawa tayi a cikin daren ta ringa shiga wasi wasi da dana sani kala kala musamman tinawa da alkawarin da sukaiwa juna a tsakaninsu na uwa da 'da wanda babu wanda ya sani sai Allansu sbd bata taba sanin zuciyarta na maqale da sultan a cikinta ba,

A matsayinta na uwa ta karya masa alkwarin dazaiyi shattering nasa hakama duka abinda yayi yanayi ne sbd bata ingantacciyar duniya da kwanciyan hankali tareda kariya da rayuwar data rasa a baya.

Sanyi jikinta yayi gabaki daya taji kunyar kanta da baqin ciki tareda dana sani sun gama lalata rayuwarta babu abinda take tsananin buqata a yanxu irin tafiya boyem taga NUAB din dan haka zata tafi tareda tenya tabar Bahar da sakinah.

Ko da gari ya waye da sassafe kafin kowama ya fito su Bahar sun fice makaranta dan haka koda Ayanah ta fito cikin damuwa me tsananin gaske take bata fara komaiba bayan fuskantar su Sakinah kai tsaye ta tambayesu NUAB daya taho kwanansa nawa?
Meyasa suka boye mata ya zo??

Shiru sukai cikeda sanyi jiki sbd ba sauran boyo,

Sake maimaita tambayarta tayi cikeda damuwa da bacin rai tace

'Akwai dalilin boyemin zuwan nasa ne?
Akwai wani abin ne bayan zuwan nasa da bazaa fada mun ba??

Tenya ce tayi karfin halin cewa

'Satinsa kusan uku amma baa nan yayi su ba,
Kuma munyita kokarin sanar dake tin kina can amma baa samunki kuma kafin ki dawo ya wuce shiyasa baa fada miki ba sbd ya riga ya wuce kuma ba wanda ya fada masa ga inda kika je ya sani amma ya zabi shiru muma mukai shirun'

Shiru Ayanah din tayi tana sake shiga rudanin zuciya sbd ta tabbatar Allah ne kadai yasan abinda yakeji a zuciyarsa ya danne,
Kuma satika har uku yayi yaga bata nan?
Innalillahi' ta fada a zuciyarta tana jin kanta na nauyi.

Bata iya sake cewa komaiba suma sukai shiru ba wanda yace komai haka ta miqe daga dinin ta koma daki batareda ta iya cin abincin kirki ba,

Kasa kiransa tayi kaman yanda ta saba sbd bazata iya magana dashiba,

Kiransa ya shigo wayarta still kasa dagawa tayi tana kallo ta tsinke tana jin dole ma taje boyem.

Sai yamma su bahar suka dawo basu wani gane komaiba a gidan sbd kowa yayi tsit gidan ba kanta dan haka suma abinci sukaci suka fada karatu har dare ba wanda ya fito ko abinci kowama daban daban yaci nasa,

Bahar cikin damuwa take sosai batareda kowa ya saniba gabaki daya tarasa gane kanta karatun ma yinsa takeyi tana jin kaman baya shiga sbd hakanan take jin damuwa da fushi akansa lokaci daya hakama gashi Ammi ta gane tayi tafiya kowane minti da second tsoron kada Ammi ta gane ko ta fahimci dashi tayi tafiyar take amma duka wannan fargaban da tashin hankalin ita kadaice takeyi shi yama manta da ita da abinda zai biyo bayan idan Ammi ta sani dan haka fushi da bacin rai take ciki sosai wanda ya sana hadda wayarta ta hada haushin ta kashe kwata kwata ta ajiye.

Washe gari Neesah ta tattara ta koma hostel tabar gidan tabarsu a cikin yanayin da suke ciki,

Ammi tafiyarta boyem tafara shiryawa a lokacin ne Bahar taji maganar tafiyan a bakin Maa tenya da laifinsu na boye zuwan NUAB dan haka hankalinta yayi mummunan tashi ta shiga rawar jiki da rudanin jin Ammin tasan da zuwan NUAB,

Dakinta taje da gudu ta rufe ta zauna a qasa ta ringa kuka kaman ranta zai fita tanajin rayuwarta tagama tsayawa tinda Ammi taji abinda ya faru,

Wuni tayi tana kuka mai tsima zuciya daman kukan ne yake cikeda kirjinta tsawon wannan lokacin dan haka a wuni guda kammaninta suka sauya tayi jajir idanuwanta sukai luhu luhu ko ruwa ta kasa fitowa tasha.

Har dare bata fito ba bata bari kowa yaga yanayin datake ciki ba,

Harta kwanta aka bude kofar dakin aka shigo a natse.

Ammi ce ta iso har bakin gadonta ta zauna tareda dan qara hasken dakin kadan tana kallanta.

Cikin damuwa ta kalli fuskanta data kumbura sosai kammaninta sun sauya tace

'Subhanallh Bahar??

Kafin ta sake wata maganar Bahar din ta fashe

77 / 100