Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   43 / 100

126K to 129K   out of 299.8K words

zatai ta kwanta.

Washe gari ma haka suka tafi suka wuni da yamma suka tafiya amma sbd zai fita a lokacin sai aka Dakatar dasu su saida ya fito a shirye cikin shigar alfarma data nuna ya samu Hutu da nutsuwa a kwana biyun da bai fito ba hakama fuskarsa da faraa sosai musamman da yana fitowan da ita idanuwansa sukai tozali suna tsaye a Jere kansu a qasa da girmamawa.

Wucewa yayi gaba suka biyo bayansa batareda Sauran bayinsa zuwa bangaren mahaifiyarsa Wanda suna fitowan ko Taku biyu basu yiba sautin qarar dawowan mai BOYEM da Kansa ta dauki qara me karfin gaske tana shiga kunnuwan duk Wanda yake masarautar.

Cak ASIM din y tsaya zuciyarsa na kirjinsa na dauke bugu na seconds farin cikinsa da walwalan sa suna raguwa zuwa dawowan bacin rai da baqin cikinsa Wanda yayi danasanin sako qafarsa waje dan fitowa.

Mintina ya dauka a tsaye kafin ya Hadiye Wani Numfashi me Zafi da dacin gaske tukuna ya daga kafarsa yana wucewa suma suna biye dashi.

Kai tsaye bangaren mahaifiyarsa yake kokarin isa sbd fara gaidata kafin su tafi gabaki dayansu ga sultan yi masa Barka da dawowa.

A daidai wannan lokacin suma su Aleey suna gaba NUAB dayake riqe da hannun Amminsa suna bayansa tafe cikin wata irin nutsuwa da kwarjinsa daya saka gabaki daya bayin hanyar zubewa qasa kansu a qasa tenya ba bayansu riqe da handbag dinta data wishmah.

A daidai wannan lokacin itama Laylah yunar dataji isowan tasu ta fito daga bangaren Maraki data sauka sanye da shigar yayan sarauta da wasu irin zinari a jikinta suna daukan ido,

Aleey ne dayake gaba idanuwansa suka sauka Akan ASIM daya kawo gap shima tareda nasa bayin dake bayansa Wanda Bahar take cikinsu.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali_*HAYATEEM*_
Mamuhgee

74
ASIM dayake gaba cikin isa da iko tareda danne qiyayyarsa me Zafin gaske da yakewa rai biyun dake gabansa wato NUAB da mahaifiyarsa wishmah ya tako a natse ikonsa a bayyane ya fiddo yar girmamawa sbd cika doka da al’ada ya tsaya cak gaban Ammin ya dan sauke kai ya bude baki yace

‘Barka da dawowa cikin koshin lafiya mai girma da daraja wishmah,ina miki fatan cigaba da samun lafiya dorarriya’

Kallansa a natse cikin kwanciyan hankali da sanyin jiki Ammin tayi kafin ta bude baki tace

‘Amin ya Allah,godia nakeyi Li’ul ASIM’

Dagowa yayi a natse cikin wata nutsuwar ya kalli NUAB ya bude baki tattare da basarwa a natse yace

‘LEUL BOYEM Barka da dawowa Masarautar boyem’

Batareda NUAB ya basa kallansa cikakke ba da nutsuwa ya bude baki yace furta

‘Thank you’ yana wucesa tareda Ammin wadda hannunta yake cikin nasa har lokacin.

Aleey daya kasa wucewa Bahar ya zubawa ido cikin son tabbatarda abinda idanuwansa suka ganar masa amma baice komaiba tukuna yana buqatar tabbacin idan ita dince sbd ganinta kai tsaye a cikin bayin masarautar abu ne da tinaninsa bai daukar masa ba.

Laylah da bayinta da itama suke biye da ita su biyu bayan Ammin tabi batareda tace komaiba sbd ganin magajin guda biyu yasa yanayin gurin ya dan dauki Zafi hakama kallo daya tayiwa fuskar Wanda zuciyarta take bugawa dominsa babu alaman a wannan lokacin ta bayyanar da wanzuwarta a gurin gwara ta bisu ta isar da gaisuwan Barka da zuwanta ga mahaifiyarsa datake da cikakken labari da sanin itace rayuwar dayafi so a duniyarsa da rayuwarsa.

Su Bahar ma har bakin bangaren queen haile suka raka ASIM din yana shigewa suka jiyo suka dawo nasu bangaren sai kuma gobe,

Suna sako kai Bahar datake jin Wani irin nauyi na danne kirjinta na rashin sanin wace rayuwar kuma a yanzu zata samu da asalin me bangaren ta dawo kuma yayar mahaifinta da aka yanke alaqarsu da ita wadda daman ita bata sakawa ranta kusantuwa da ita ba ko jin kanta a matsayin jininta sbd tasan ita a yanzu marainiyar da zata tsaya a iya matsayin baiwa take.

Maa sakinah ta zaunar da ita tini ta fada mata zata hakura da duk alaqar dayake tsakaninta da Ayanaah a yanzu zuwa Wani lokacin daya kamata amma dai itama batasan Yaushe ne lokacin ba sbd batada umarnin yankewa ko maganar cewa Akan wannan hukuncin da aka yanke musu na Dakatar da alaqar.

Bata damu ba bata ji baqin cikin komaiba sbd daman ba saninta tayi ba bakuma tada alaqar komai din da gaske da ita hakama tinda ‘danta ya zabi kada Ayi alaqar hakan ya kawo mata sauki a rayuwarta na rungumar maraicinta da kadaicinta bata buqatar kowannesu a rayuwarta daga shi har mahaifiyarsa kawai abu daya ne yake tsaye cak a tsakiyar zuciya da kirjinta dama idanuwanta shine son ganin mace daya tak da itace macen da mahaifinsa yafi so a duniyarsa fiyeda komai harma da rayuwar tasa kanta,

Ita datake ‘yarsa itace zuciyarsa da rayuwarsa da babu kamarta a gurinsa amma kuma Ayanah itace macen datake gugar matsayi da ita a zuciyarsa datake jin ma tsakaninsu waye yafi tsananin so fiyeda da rayuwarsa,

Ita jininsa ce kaman yanda AYANAH GHAZ take jininsa,
Ita bugun zuciya da sanyin zuciyarsa ce kaman yanda Ayanaah ghaz take hakan garesa,
Itace macen dazai iya bada ransa da yana raye akanta hakama zai iya badawa Akan Ayanah ghaz dan hakan so daya zuciyarta ke son ganin macen da itace rayuwar mahaifinta.

Koda suka shigo gabaki daya bayin bangaren suna tsaye Jere a gefe kansu a qasa cikeda wata irin girmamawa bazasu taba dagowa ba har sai LEUL BOYEM yabar bangaren dan haka itama a sanyaye tazo gefensu ta tsaya a natse batareda ta iya shiga ciki ba gurin Maa dinta sbd nauyin kirjin yanda zata iya fuskantar mutanen dake ciki.

Laylah YUNAR ce ta shigo bangaren Wanda suka sake dan rissinawa suka gaidata gabaki dayansu bata kalli inda suke ba bare iya amsawa gaisuwar su ciki ta wuce kai tsaye Wanda dolenta iyaka cinta palon farko ta zauna sbd babu Wanda zai taba wucewa ciki matiqar LEUL yana ciki.

Tenya ce dake Zaunawa palon Akan kujera tana kallanta da dukkanin idanuwanta tana karanto kamannin Zuhrah ghaz dake bayyane radam a bayyane kan fuskar Laylah din taji zuciyarta na narkewa da tsananin kauna da farin cikin ganin jinin Zuhrah a cikin bangaren Ayanah da hakan zai kusan bugar da zuciyarta sbd farin ciki da kauna me tsananin da zata nunawa jinin Zuhrah dinta dake gabanta.

Cikin kulawa da kauna me tsananin yawan gaske tenya ta bude baki tana kallan Laylah tace

‘Leylah Yunar barkanki da zuwa,
Ya gajiyan tafiya daga Kuwait zuwa boyem?
Ya kadaici da baquntar sabon guri?
Ya kuma kika Baro mahaifiyarki?

Numfashi me nutsuwa na jinin sarauta Leylah ta sauke kafin ta kalli tenya cikin girmamawan datake buqatar samun kauna da duka soyayyar su sbd ji da sanin matsayin dasuke dashi na iyaye mata da NUAB yake tsananin kauna ta saki kyakkyawan murmushin daya sake bayyanarda kamanninta da mahaifiyarta sak tace

‘Lafiya alhmdlh,Ummee kuma tana lafiya itama tinda nazo ba randa bata tambayana Ammi a wuni fiyeda so goma,
Kun dawo lafiya?
Yaya jikin Ammin?
Allah ya qara mata lafiya da tsawon rai me lafiya da kwanciyan hankali’

Amin’ tenya ta amsa tana kasa wucewa bedroom dinta dan hutawan gajiyan tafiya tafara kokarin jan Leylah a jiki da fira me nutsuwa da tsafta,

Umarni ta buga waya kitchen tace a kawowa Leylah kayan marmari da hutawa.

Bahar ce ta hado kayan a babban tray me kyau da tsari Naimah ta tayata hada fruits masu sanyi da zuma da madara me tsananin kyau da kauri me sanyi sukai tray biyu suka nufo palon Wanda sanyin ac ya gama Kama koina tareda qamshi kusan Kala nawa na mutanen dake ciki masu dataja amma kusan qamshin LEUL boyem ya doke kowane qamshin duk da baya palon yana palon kurya na hutawa tareda Amminsa da Maa sakinah wadda takejin tsananin farin cikin Ayanah dinta ta asali t dawo hadda tinaninta cikakke na rayuwarsu amma ta dawo da wata irin dangana datake ji sbd Jin tamkar ta rasa fiyeda rabin rayuwarta,
Jinta takeyi babu abinda yayi saura a rayuwarta bayan fanko,
Batajin farin ciki sosai,
Quncinta yana nan shimfide a kwance qasar zuciyarta da har abada bazai taba fita ba amma a yanzu ta samu zimmar iya dannewa tabarwa zuciyarta ita kadai quncin ya cita amma bazata iya barin kuncin rayuwarta da batada komai na dadi ko farin ciki a ciki ta Hana ‘danta qwalli daya da bata hada da komaiba farin ciki da walwalansa.

Zata barwa zuciyarta komai batareda ta saka na kusa da ita damuwa da quncin da itama take cikinsa ba duk da bazata iya hakan lokaci daya ba amma zatai iya kokarin boye hakan sbd likitoci da taji a kunnuwanta sun fadawa NUAB zuciyarta ta Riga ta samu matsala dan haka tasan a cikin mummunan damuwa da qunci tasa zuciyar take.

Naimah ce a gaba dauke da tray kafin Bahar a bayanta dukkaninsu a natse suka sako kai a palon Wanda yayi daidai da fitowan Maa sakinah palon tareda NUAB Wanda fuskarsa ta qaro Wani irin fresh da daukan ido kwarjininsa na cike niimar palon tareda qamshinsa daya saka Leylah dagowa tana sauke kyawawan idanuwanta akansa a Karan farko data gansa zahirin a gaban idonta kusa sosai.

Wasu irin hawaye ne taji ma kawai suna ciko idanuwanta masu dumi sbd zuciyarta dayake Jin abinda yafi Wanda take ji farko akansa sbd a yanzu ne da idanuwanta suka gansa a zahirinsa zuciyarta ke kamuwa da asalin soyayyarsa da zata iya bada rayuwarta Akansa,
Ta shirya zama ta qarar da rayuwarta a matsayin Koda imebētinsa ce idan ma har babu aure aransa kenan dan kuwa shi din ayanzu ta tabbatarda baturen da aka fada ne dan haka ba lallai akwai tsarin aure a rayuwarsa ba,

Hakama dan taaddan da ake ambatarsa dashi Ayau ita ya shirya rayuwa dashi koda jinin mutane ma yake yanka wa yasha taji zata iya rayuwa har mutuwa dashi a hakan ta zabawa yayanta da zata Haifa a duniya shi a matsayin uba.

Kasa dauke idanuwanta da suka ciko da hawaye tayi daga Kansa batareda ta iya ko kotsawa ba harya kawo daidai inda take Zaune zai wuce a kuma lokacin Bahar ta kawo gurin itama dagowa tayi ahankali sbd qamshinsa daya shiga hancinta Wanda ya sakata tinanin shi dinne sbd qamshin ne daya tino mata da rasuwar mahaifinta dan qamshin ne a jikinsa Koda ya rasu sbd rungumar da NUAB din yayi masa.

Tana dagowa bata kallesa ba sbd zuciyarta datai mata nauyi da kirjinta na tinawa da babu Sauran kowace alaqa a tsakaninta da kowa anan Bayan Maa dan haka matsayinta a yanzu bai wuce me aiki ba tinda ita din ba baiwa bace me lasisi kaman Sauran.

Dan haka qarasowa tayi tana ajiye tray din hannunta daidai nan ya fice shima batareda ya lura ba bare kallan kowacensu dake palon,

Maa sakinah kuwa Wani irin nauyi kafafuwanta sukai ta tsaya cak zuciyarta tayi wata irin bugawa da maganar tenya data shiga kunnuwanta cewan ‘ga Leylah yar mai girma yunar da amaryarsa Zuhrah.

Kallo daya Maa sakinah tayiwa Leylah tanajin Wani irin farin ciki da kauna me tsafta da takewa Zuhrah tana sauka Akan Leylah amma idanuwanta na sauka kan Bahar dake gaban Leylah din tana jere mata kayan marmari a gabanta jin tayi zuciyarta na tsananta Wani sabon nauyin Wanda yake ragewa farin cikinta karfi ta dauke kallanta daga kan Leylah din ta Dora Akan Bahar zuciyarta na sake sosuwa.

Numfashi me dumi ta sauke tana daga kafafunta ta qaraso a hankali tareda dan sake murmushi tana karban aikin Bahar din tace su tafi kawai zatai aikin.

Cikeda jin dadi tenya datasan sbd kaunar datake wa Leylah ce ta saka zatai serving nata da kanta Wanda itama taji hakan hakama itama Leylah jin tayi dadi yana shiga zuciyarta na ganin Maa dince zatai serving nata sbd har sun fara kaunarta dan haka murmushi me kyau takeyi tareda dagowa daidai lokacinda aka bude kofar palon Kurya din Wanda ya saka Bahar dake kokarin barin gurin tsayawa cak zuciyarta na Wani irin harbawan datake jin tamkar mahaifinta zata juyo ta gani a bayanta sbd wadda take bayan nata rayuwarsa gabaki dayanta.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

75
Leylah wadda tata zuciyar itama take sauya bugawa ahankali miqewa tayi tsaye a hankali cikin wani irin yanayin da batasan menene take ji ba amma ganin matar data haifi namijin datake so take shirye da rasa rayuwarta akansa ya saka zuciyarta da idanuwanta Wani irin sanyi da cikewa da tsananin kwarjinta da wasu irin kammanin datake ganin suna fizgar kamannin mahaifiyarta bata saniba ko dan mahaifiyarta bata da zance saina yabo da zuzuta kyau da matsayin wishmah din Masarautar BOYEM AYANAH GHAZ Shiyasa Ayau da idanuwanta suke ganin macen datafi kowace saar miji da ‘da take ganin kaman suna fizgar wasu kamanni da mahaifiyarta.

Bahar da idanuwanta sukai Wani irin sanyi tareda cikowa da wasu hawaye suna sauya Kala Lumshe idanuwa tayi bugun zuciyarta na tsayawa cak kaman yanda gangar jikinta ke jin kowane irin yanayin Wanda mahaifinta ne yakeda haqqin ganinsa shine ya cancanta ganin wannan lokacin dan haka taji sam bazata iya juyowa ba ta daga kafarta a sanyaye zata bar gurin batareda ta juyo ba.

‘AYANAH BAHAR’

Maa sakinah ta Ambaci cikakken sunanta zuciyarta cikeda rauni itama Wanda ya saka Ammi dake kokarin sauke idanuwanta Akan Leylah dakatawa tana Juyawa a natse da Wani irin sanyi ta kalli inda Bahar din take juyowa cikin nutsuwa kanta a qasa ta sauke idanuwanta akanta tareda tsayawa cak tana kallanta batareda zuciyarta ta buga ma komai nata ya tsaya cak kallan nutsuwa take yiwa Bahar din wadda har lokacin ta kasa dagowa sbd idanuwanta sun kasa bata zarrar karban lokacin dayake na mahaifinta ne,

Ahankali Ayanah ta dauke idanuwanta daga kan Bahar jikinta na mutuwa ta saukesu Akan Leylah wadda itama Bahar din da Ammin ta kafawa ido tana kalla sbd jin sunansu dayake iri daya.

Tenya kallo daya tayiwa Bahar ta dauke kai tana dawo da kallanta kan Ayanah dake kallan Leylah cikeda farin cikin dayake kasa boyuwa a zuciyarta tace

‘Yar mai girma YUNAR da Amaryarsa Zuhrah’

Kasa motsawa Ayanah tayi sbd bugun zuciyarta daya kasa dawowa daidai hakama maganar tamkar saukar mashi a tsakiyar zuciya taji ta so keta ba tsammani,

Kafe idonta tayi Akan Leylah kafafunta na wata irin rawa suna Neman kasa daukanta tayi baya a hankali tenya tayi saurin tareta tana Kama hannunta tareda kamo hannun Leylah din ta Dora Akan na Ayanah wadda Wasu hawaye masu tsananin zafi suka ciko idanuwanta ta Kama hannun Leylah din a cikin nata ta riqe a natse tareda Zaunawa tana jin Wani irin zazzafan kauna me sanyi da nutsuwa tana ratsata bakinta da baya hayaniya ta bude a hankali tace

‘Ina mahaifiyarki?
Tana lafiya?
Tana cikin koshin Lfy?
Ta sauya?
Ta girma?
Tana cikin kwanciyan hankali da nutsuwa??

Da mamaki da farin ciki Leylah take kallan Ayanaah din zata bude baki ta amsa Bahar dake jin kowace kalma da muryan Ayanaah dake sauka kunnuwanta suna narkar da zuciyarta ta nufi kofa zata fice Maa sakinah da bazata iya barinta ba ta ajiye abinda yake hannunta tabi bayanta tareda Kama hannunta batareda an Ankara dasu ba ta shige dakinta da ita.

Suna shiga rungume Bahar din a jikinta tayi zuciyarta na shiga damuwa da tausayinta mai tsananin sbd gata ga Dayar zuciyar mahaifinta amma ba damar kowace iri ta bayyanar da hakan a tsakaninsu,

Wasu hawaye ne masu dumi suka gangaro daga jikin Bahar din tana kwance jikin Maa sakinah din batareda ta furta komaiba,

Tabbas ta San yar Zuhrah din mahaifinta ce ake magana a gabanta Bayan AYANAH GHAZ wadda itace ma mahaifin nata,
Ita daban take a cikinsu sbd mahaifinta ma daban yake a cikinsu dan haka batada gata ko hurumin alaqa dasu zata tsaya iya inda aka ajiyeta ta Kama matsayinta da shine ya cancanceta.

Dagota Maa tayi daga jikinta tareda Zaunawa da ita suka zauna Akan sofa ta kalleta itama bata iya cewa komai ba bayan

‘Bahar kici gaba da hakuri da riqe kaddararki wadda lokaci zai zo da zata sauya,
Banda yanda zanyi nima Alkawari ne da iko da ban dashi suka daureni daga hanaki samun walwalan data kamaceki a gaban macen da itace zata fi kowa so da kaunarki a duniya,zata kaunaceki fiyeda kanta da duk wani Wanda yake rayuwarta,zata kauna ce ki fiyeda ‘danta data haifa sbd kece jini daya tak da hasken rayuwarta ta bata a duniya ya tafiyarsa ya barta’

Hannun Maa din dake share mata hawaye ta Kama tana Dakatar wa da nata ta bude bakinta da sauti me sanyi tace

‘Maa kaunarki kadai ma ta haskaka Wani duhun na rayuwata da baya buqatan hasken da yawa dan haka a hakan ma rayuwar da kuka bani nayi anan gode’

Rasa abin fada Maa tayi sbd zuciyar Bahar batada abinda ta sani ta sabu dashi din bayan duhu dan haka takejin kaman bata buqatar kauna da yawa daga wainda suka cancanta.

Bata Bari ta kuma fita ba tace ta tube tayi sallah tayi zamanta kawai.

Tubewa tayi tayo Wani wankan harda alwala ta fito ta zauna shiri.

Acan palo kuwa Ayanah Ayau jin takeyi zuciyarta tana samun karfin data rasa sbd ganin jinin Zuhrah dinta Ayau a gabanta a tareda ita.

Farin cikinta a bayyane yake Wanda yake sake saka tenya jin nata farin cikin yana qaruwa.

Maa sakinah ma nuna farin cikin takeyi duk da a qasan zuciyarta Bahar ce a ciki da babu Wanda ya San da wanzuwarta a duniya gabaki daya ma.

Leylah ma samun kanta tayi a sabuwar duniyar da bata taba tsammani ba sbd Karbuwan data samu da kauna me karfi daga Ammin NUAB da Maa tenya harma da Maa sakinah duk da farin cikinta da kaunarta a bayyane batai tasu ba.

A bangaren ta wuni har dare sosai kafin ta koma bangaren Maraki.

Washe gari tinda safe Bahar ya fice daga bangaren gabaki daya tareda su Naimah sbd karfafawa rayuwarta matsayin da aka ajiyeta akansa.

Tenya kuwa dakin Ammi daya dayake palonta kusa da nata bedroom din ta saka aka sauyawa komai sabo sbd Leylah da zata dawo bangaren.

Sauran bayin bangaren ne sukai aikin Wanda bai dauki lokaci ba aka gama komai,

Leylah da kanta tareda bayinta ta tattaro Kayanta suka dawo bangaren batareda sanin sultan ba sbd Ayanah sirikarta ce da ba lallai abar ta zauna bangarenta ba.

Bayan sun gama parkinga bayinta sun gama jere mata komai wanka ta sake yi ta sauya kaya zuwa doguwar Riga me ado sosai datake daukan idonta rufe kanta ta fito suka

43 / 100