Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   21 / 100

60K to 63K   out of 299.8K words

batada ikon ko dogon motsin dazai tadasa amma zuciyarta na cikin mummunan halin da bazata iya riqe kanta ba matiqar da gaske ne imebētinsa da gaske ta wuce lokacinda kowace mace take dauka a tirakarsa,

Juyawa tayi ta fice zuciyarta na Wani irin cizo kaman zata feso wuta dan kuwa kishinta batajin ko yayan daya Haifa bazata iya hallakawa Akan sultan din ba dan haka gabaki daya a yanzu tinaninta da hankalinta zai koma Akan imebētinsa ne da haryanzu bata taba ganinta ba.

Ayanah tinda suka dawo a ranar kwance ta wuni cikin rashin kuzari da dumin jiki na alaman zazzabi kadan kadan dan haka babu hayaniya kwata kwata a bangaren sbd bata damar hutawa,
Inda Allah ya taimaketa ranar ce karshen kwanakinta dan haka zata huta Sosai kafin satikan su dawo.

Da daddare sosai tenya ta iso da masu duba Ayanah din sbd batason wasa da duk abinda zai taba lafiyar Ayanaah dan kuwa Ayau datakai har safe tirakar sultan labarin zai isa kunnen matansa harma da imebētis dinsa dan haka hakan zai iya zama hadari gareta sosai sbd kishin mata masu hadarin gaske ne zai rufeta tako Ina Wanda ta hakanne imebētis da dama suka rasa ransu Shiyasa duk yanda sultan keda imebētis da yawa kalilan ne a raye wainda suma kadan kadan kake Jin Ana cewa an wayi gari kawai sun mutu,

Akwai Wani irin qalubale da hadari mai girman gaske a zama imebētin da zata samu ciki a masarautar BOYEM dan haka a yanzu indai zarginta ya tabbata ciki ne da Ayanaah tabbas zata bata kariya kota halin yaya saita Haifa abinda ya dauka bazata Bari kasheta a banza ba dan hakanne ta Nemo masu dubawar cikin dare sbd Hana maganar cikin fita.

Koda masu dubawan suka shigo da Daren tenya ce a gaba su suna bayanta har zuwa Dayan lafiyayyan palon hutawar Ayanaah din suka zauna ita kuma ta kalli sakinah tace a fito da Ayanah din.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

35
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******
Sakinah dake tsaye kanta qasa zuciyarta na cikin yanayin dayake na sallar tsoro da fargaba harma da tashin hankalin abinda yake shirin faruwa dan kuwa har abada bazaso Ayanah ta dauki cikin sultan din BOYEM ba sbd mummunan hadarin da zata shiga harma ta iya rasa rayuwarta dan kuwa babu wata rai datake da mahimmanci a BOYEM Bayan ta asalin jinin BOYEM din,

Ta ina ta yaya zata iya bawa Ayanah kariya tana matsayin baiwa Bayan tana ganin yanda imebētis ke qasqantarciyar mutuwa ta rashin mahimmanci kuma sun mutu kenan a banza a wofi babu me sake tinasu sai ‘yaya idan sun haifa,

Wani irin nauyi kirjinta yayi lokacinda tenya tace ta korawo ayanah tanajin gabobin jikinta na sanyi idanuwanta na cikowa da hawayen fatar ba abinda ake tinanin bane,

Dakin Ayanah din ta nufa ta taddata kwance ba bacci takeyiba amma idanuwanta a rufe suke tayi shiru lafe a lallausan gadon zuciyarta a narke da damuwan data zamar mata jiki,

Zuba mata ido sakinah tayi tana qure kallanta akanta zuciyarta na sake shiga matsanancin tsoro da tausayi me karfin daya saka hawayen idonta fara gangarowa ta saka hannu ahankali ta shafe hawayen tana kallan sauyi sosai dayake bayyane a jikin Ayanaah din.

Ayanaah din ce ta bude idanuwanta masu haske ahankali kan sakinar sbd taji shigowanta hakama tanajin idanuwanta akanta dan haka a sanyaye ta bude ido ta saukewa sakinar batareda tace komai ba.

Itama sakinar qasa tayi da kanta sbd bazata iya cigaba da kallan Ayanaah ba zata iya fasa kukan dayake cizon zuciyarta,
Numfashi mara sauti ta sauke ahankali tareda bude Baki a natse da sanyi ta sanar da ita kiran tenya.

Tana fada ta juya ahankali ta fice daga dakin sbd kallan da Ayanah ke mata na karaya da rayuwa koyaushe.

Sai datai mintina biyu a kwancen tana kallan kofar da sakinah ta fice kafin ta tashi Zaune a hankali tareda ziro kafafunta qasa ta miqe tsaye slippers masu taushi a kafarta ta nufo kofar ta fito sanye da doguwar rigar qasar me kyau black kanta rufe da qaramin Gyale me hade da niqap din dayake da adon sarka me rawa ta zinari sbd tasan da zaa kawo masu dubata sbd zazzabinta amma bata San abinda zasuyi Bayan hakan ba kuma doka ce me karfin gaske babu namijin dazai iya ganin fuskarta tinda ta zama imebētin sultan me BOYEM gaba daya.

Ko data sako Kai a palon Qamshinta ne ya fara cike palon kafin fitowanta data saka likitocin biyu dauke kansu gaba daya daga kallan hanyar datake tahowar,

Tenya ce take kallanta su sakinah ma gabaki dayansu ficewa sukai kansu a qasa zuwa kitchen ayyukansu,

Sakinah hankalinta gabaki daya kwata kwata yana kan abinda zai faru a palon tana tsananta adduar Allah yasa Ayanah bata dauke da jinin boyem a cikinta,

Cikin nutsuwa likitocin suka nutsu suka gudanar da bincikensu Akan Ayanah wadda dukkanin tambayoyinsu ta amsa a sanyaye.

Bayan dan lokaci suna bincike da bin harbawan jijiyanta suka bar bangaren dan tafiya da sample dinta da zaa auna dan tabbatarwa kafin bude baki ga fadar kowane irin sakamako ne.

Ayanah bata buqatan sanin menene yake damunta sbd ba damuwanta bane ta rayu ko sabanin hakan,
Tenya kuwa Miqewa tayi itama ta fice ta aika aka saka mata ido sosai a cikin sirrin dan tsaro da kiyayewa batason kowa ma yasan da duk abinda zaa fada.

Jiran wuni guda tenya tayi tana jiran sakamakon Wanda ya hanata dukannin sukuni da nutsuwan zuciya hankalinta na kan koma menene,
Daga qarshe tenya da kanta ta isa bangaren lafiyyyar clinic din dake cikin masarautar,

Sai dare ta isa batareda barin kowa yasan da inda ta nufo din ba sbd tasan sosai akwai Idon HAILE Akan duk wani motsinta da abinda ya shafi Ayanah.

Ko data iso Kai tsaye babban likitan ne da kansa ne ya zauna suna fuskantar juna ya sauke Numfashi ya koro mata bayani Kai tsaye ciki ne da Ayanaah qarami.

Ajiyan zuciya da Numfashi mai karfi tenya ta sauke tareda kallan likitan Wanda ta ciro silan danyan zinari ta ajiye gabansa matsayin tukuicin zancen sa ta miqe ta juya ta fice tana Jin yanayi na farin ciki da samun nutsuwa dan Kuwa adduarta a yanzu zata sauya zuwa Allah yasa wannan Karan haihuwan LEUL BOYEM ne tazo mai albarka dazai zamo abin alharinta da uwarsa dan kuwa shine karshen baqin ciki da haukar da zata Kama HAILE dan samun namiji a gurin wata macen da ba ita ba yana nufin zarewanta.

Koda tenya ta isa babu Wanda ta sanarwa da maganar cikin imebēti Ayanaah sbd fitar zancen cikin tamkar miqa rayuwar Ayanah ce ga halaka dan haka ta zabi tayi shiru ta Hana kowa sanin cikin saiya bayyana.

Sakinah Jin shiru kwana daya kwana biyu harma kwanaki babu sakon labarin samun ciki ga Ayanaah ya sakata Jin dan sassaucin abinda take ji na tsoro da tashin hankali ta dan kwantar da hankalinta duk da kullum sake sauyawa Ayanah ke yi alaman mace me ciki yana sake bayyana gareta batareda itama tasan cikin ne yake dauke dashi ba.

A haka satikan hutunta suka cika aka fara shirin fara zuwanta tiraka sedai wannan Karan tenya bata bada umarnin anyi mata shiri me karfi ba Wanda hakan ya tado tsoron sakinah sedai kuma indai har cikin ne da Ayanah dole Ayau zasu sani kuka kowa ma dake masarautar zai gane dan bazata qara zuwa ba,

A al’adance duk macen data samu cikin sultan matiqar an tabbatar tenya ce takeda ikon sanar masa idan takai mace kwanan karshe shi kuma daga wannan ranar zai sallamota ne ta hanyar alamar rashin bata tukuicin kwanciya Wanda hakan na nufin ya gama da ita kenan shikenan kota haihu kawai matsayinta dayane ta haifar masa jininsa,

To wannan alamar ce take sakawa kowa dake masarautar yake sanin mace ta samu ciki sai kuma Bayan lokaci nai dan tsayi kafin a fara shirin zabar masa wasu imebēti din,

Tenya duk wani shiri na nutsuwa da qamshi me sanyi na bankwana da tirakar sultan shi tayiwa Ayanah tanajin damuwan sanin cikin da zuwa yanzu kowa zaiyi,

Karfe goma sha Dayan dare suka iso tirakar tasa wadda kowannensu ya tsaya cak inda shine gurin tsayuwarsu,

Silan zinari dayake da adon hoton tafin kafar jariri a jiki tenya ta bude hannun Ayanah ta saka mata batareda cewa komaiba,

Wucewa ciki Ayanah tayi batareda ta bude hannunta ba bare tasan sakon menene amma dai sanin yawancin sakon masarautar da alama a silan zinari suke Aikasa dan haka a sanyaye ta isa dakin Wanda yayi sanyi sosai qamshin sa datai sati uku bata shaqa ba yayi shiga hancinta yana ratsa kanta cikin sanyi ta dan Lumshe idanuwanta t bude a natse kafin ta fara Takawa da sanyinta sautin karar sarkar kafarta dayake daban dana matansa yana tashi a kowane takunta yana shiga kunnensa da sautin yakewa dadi,

Isowa tayi har inda yake Zaune sanye da Riga da wando masu dan kauri farare qal d suka sakasa komawa tamkar matashin saurayi,

Kanta na qasa ta zube qasa ta miqa masa gaisuwanta da muryanta da babu hayaniya a cikinta ko kadan,

Amsa gaisuwar yayi yana kasa dauke idanuwansa daga kanta dan kuwa zuwa yanzu ya gama yadda da koma menene Ayanah na basa nutsuwa da sukuni fiyeda kowa dan kuwa ko yayansa baida Wanda zaice gashinan shine yafi so ko ji a zuciya,

Bayan kujeran mulkin BOYEM yanajin a yanzu ne ya sake samun abinda bazai taba iya bawa wani ko barin yafita hannunsa dan Hak…….

Bai qarasa abinda yake zuciyarsa ba ta dago hannuwanta biyu sama kadan ta bude masa su sakon na bayyana kan idanuwansa kanta na qasa.

Qurawa tafin hannun nata ido yayi batareda y kyafta ba dan kuwa wani abin da bai taba ji ba yaji ya soki kirjinsa yana ratsawa na asalin girgiza da mamaki,

Bai taba mamakin samun ciki ga mace dayake kwana da ita ba sai kan Ayanah GHAZ wadda ya dauke idanuwansa daga tafin hannun nata ya maida Akan fuskarta data dago ahankali itama Jin shiru idanuwansu suka shiga cikin na juna ya tsareta tsaf da idanuwansa yana kasa motsawa,

Duk hadarin dayake cikin samun cikinsa Reno da haihuwansa ya sani Shiyasa sai kakkarfan tsarin Allah suke labari,
HAILE batada imani ko tausayi ko kadan Akan kishi da tsananin cika burin duk abinda take so amman bai taba damuwa ba dan itace macen da ikonta yakai tayi duk abinda take so dan itace uwargida kuma mace mafi daraja a BOYEM kasancewanta matarsa kuma bazai taba goge hakan ba amma kuma bayajin Ayanaah GHAZ zata iya wannan rayuwar hadarin,

Hannunsa ya miqa ahankali Akan tafin hannunta ya dauki silan ya damqe a tafin hannunsa ya bude Baki cikin nutsuwa sosai yace

‘Ina tayaki Murnar daukan jinin BOYEM,
Ina maraba da duk abinda zaki Haifa Ayanah Ghaz.’

Zuru tayiwa idanuwanta akansa sbd kasa fahimtar abinda yake nufi ta kuma kasa bude Baki ta tambaya sedai ta samu kanta a tsananin son fahimtar me hakan ke nufi sbd Wani irin nauyin da kirjinta yayi

Abinda ya fada mata shine abinda ake fadawa kowace macen amma ganin irin dauke wutar datai ya sakasa Dora mata da cewa

‘Ina fatan cikin dayake jikinki ya zamo na cikar burina dana qasata gabaki daya’
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

36
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******

Wani irin jiri ne ya dibeta me karfin gaske daya sakasa tarota jikinsa yana rungumeta sosai a cikin jikinsa Wanda a yake yaji yana Jin tamkar karfin Mararta datai tudu.

Ajiyan zuciya ya sauke yana miqa hannunsa ahankali cikin rigarta zuwa mararta da taurinta ya tokaresa ya shafi cikin a Karan farko kenan rayuwarsa daya shafi cikin tsatsonsa,

Lumshe ido yayi tareda jan wani Numfashi mai dumi ya bude ido tamkar yana buge a kanta,

Jajir idanuwanta sukai zuciyarta na wata irin harbawan datake nunawa har a kirjinta ya zubawa kirjin ido,

Wasu irin hawaye masu tsananin Zafin gaske ne suka gangaro daga idonta suka sauka Akan fatar hannunsa yana kallo bai motsa ba baice komaiba sai kawai yaji sautin kukanta mai tsananin ratsa zuciya ya fasu ta qamqamesa tana kukan jikinta har wata rawa yakeyi tana cusa kanta a kirjinsa.

Bai motsa ba baice komaiba kukan ne kadai sautin dayake tashi a dakin Wanda ya sakasa tinani Kala daban daban sautin kukan na ratsa kunnuwansa zuwa cikin kansa da babu komai a cikinsa yanzu Bayan na saiya tabbatarda ta Haifa jininsa koda bazai zo da rai ba saiya kuma mata Wani cikin amma tabbas yanason jininta a cikin yayansa.

Kuka sosai tayi a jikinsa har karfinta ya qare tayi lahu dukkanin tinaninta ya toshe babu komai a cikin Kanta empty yake tas,

A wannan daren babu abinda ya shiga tsakaninsu a Karan farko haka suka kwana ya sakata a jikinsa sosai dumin jikinta kadai yana basa nutsuwa da sukuni.

Asubar fari fitowan Ayanah ta saka su tenya gyara tsayuwarsu jiki duk a mace sbd wannan shine zuwansu na karshe.

Tin daga duhun doguwar hanyar isa palon sa na farko tenya zubawa Inuwar Ayanah din ido tana kalla cikeda Wani irin sanyin rashin samun yanda taso,

A darare Ayanah take tako wa kafafunta sun mata Wani irin nauyin gagarumar damuwan data kame duka gabban jikinta da idanuwanta tareda kwakwalwanta ko gani sosai batayi take isowa.

Kyallin dayake haskowa daga hannuwan Ayanah dan dake gaba ya saka tenya bude idanuwanta da kyau cikeda tsananin tsoro da mamaki sbd babu macen data taba samun ciki ta koma shimfidarsa a tarihi idan ba matansa ba dan haka ganin silallan zinari kaya guda a hannun Ayanah dake gap da rasa ranta sbd tashin hankali da qunci ya sakata Jin kaman tsoro n kamata sbd alamar cigaba da zuwanta tiraka kenan maana indai tenya ta fahimci sakonsa daidai kariya ce ga Ayanah da cikinta dan kuwa cigaba zuwanta na nufin babu Wanda zai zan da akwai ciki a jikinta kenan.

Rawa kafafun tenya suka fara dan kuwa wannan lamari ne me girma ke shirin faruwa boyon ciki a masarautar har zuwa haihuwansa.

Zufa ta sharce tana tare Ayanaah data kusa faduwa sbd jiri take suma Sauran bayin suka matso dan gaggawar barin gurin da ita,

Sakinah kuwa tinda idanunwata suka sauka Akan tukuicin kwanciya da ake bada wa kullum taji zuciyarta tana sanyi da samun nutsuwa godia ta ringa jero wa sbd babu ciki kenan a jikin Ayanah din.

Cikeda kulawa aka isa da ita bangarenta daqyar tayi sallah ta sunkuyar da Kai ta fasa kuka mai cin zuciya tana dagawa Allah hannuwanta biyu da Neman sassaucin wainanna kaddarorin nata da basa qarewa daga wannan se wannan dan ayanzu bata San ta ina zata faraba da ciki a jikinta,

Bata taba Jin zata iya cigaba da rayuwa a BOYEM ba daga ranar da Allah ya bata ikon fiddo da jininta Zuhrah daga kurkuku,
Bata taba Jin kaunar cigaba da rayuwa anan din ba daga ta samu yancin fidda tata yar uwar amma yanzu ga jinin BOYEM a jikinta datasan babu ta yanda jinin BOYEM zai taba barin BOYEM hakama itama batajin zata iya Hana kanta tsananin son abinda zai fito daga cikinta ba,
Wace irin kaddara ce wannan zata kawo yarta duniya ta fuskanta a matsayin yar imebeti.

Kuka takeyi sosai tana Neman sassauci a gurin ubangiji tareda Neman zabi mafi alkhairi,

Haka ta wuni batareda barin kowa ya ganta ba ko sakinah sedai ta kawo mata abinci ya juya babu wata magana fata shiga tsakaninsu sbd ita sakinah samun nutsuwarta shine koma menene tinda ba cikine da Ayanaah ba to da sauki, ita kuma Ayanaah bata iya maganar cikin kwata kwata da kowa ma dan kuwa zata sakawa ranta babu komai a jikinta tabarwa Allah zabi Akan zuwansa duniya yayi rayuwa ko kuwa sabanin hakan Allah zai zabar mata.

Da daddare cikeda farin ciki da Wani irin shauqi tenya da kanta ta shirya ta na musamman takaita tiraka,

Shi kansa sultan din Ayau wasu shafikan gamsashiyar alaqa ya bude musu daga shi har Ayanah din wadda batada zabin daya wuce duk yanda yayi da ita,

Haka ta share sati tana basa sabuwar nutsuwar da bai taba samuba sbd baya kusantar macen dayake ciki koda matarsa dake haihuwa ce Hutu yake bata saita haihu yana yarta tayi wayonda baa zuwa da ita shimfida tukuna take dawowa.

A sati Dayan nan ya samu sauyi da sabbin feelings da dama Akan

21 / 100