mace haka ya barta ta tafi hutunta.
Batareda sanin kowaba Ayanaah ta fara Renan cikinta da ko sakinah batasan dashi ba sbd Sam kwata kwata tenya kowa duniya Bayan ita bata Bari yasan da cikinba sbd tsaro da tsananin kiyayewa.
Ana hakan ne faree ta rasu batareda ta haifi abinda yake cikintaba hakan ne ya saka tenya tsananta kariyarta Akan Ayanah,
Abinci da ruwa da duk abinda indai Ayanah ce zata ci sa sakinah kadai ce ta yadda da ita kuma ita tabawa babban matsayin da komai na Ayanah itace kadai yake da haqqin kulawa dashi.
Ita kanta Ayanah Wani irin yanayi yafara sauyawa a rayuwarta na tsananin son abinda yake cikinta dayake shigarta ahankali Wanda a lokaci daya kuma tsoro yake shigarta dan kaman yanda bata iya rabuwa da yan uwanta yake tsananin sonsu fiyeda kanta ko Bayan baya tareda dasu haka takejin bazata taba iya rabuwa da abinda zata haifaba koda hakan na nufin bada rayuwarta.
A Dayan bangaren sakinah ta samu sanin cikin dayake jikin Ayanah sbd fitowan daya fara yi dan a yanzu yana cikin wata na shida harda kwanaki kuma har lokacin tsananin tsaro take cikinsa na rashin sanin cikin Wanda sultan din da kansa ne bai bata Sallamar da zaa San tana dauke da ciki ba,
Babban gagarumin abin mamakin dayake sake saka tenya da MARAKI ma tsoro sosai shine tsawon watannin shida kenan da HAILE ta bugaci samun hutu daga sultan sbd rashin lafiya dan haka tsawon wannan lokacin babu Wanda yake ganinta tana bangarenta a killace tana hutawa,
Sultan ya bata hutun datake buqata batareda ya buqaci wasu sabbin imebētis dinba sbd samun kwanaki masu yawa na kasancewa sa AYANAH GHAZ wadda cikinta yake girma a hannunsa da jikinsa dan kuwa sati biyu cif yakeyi da ita kafin yayi sati uku da maraki,
HAILE ciki ne da ita da manyan bokayen qasa suka tabbatar mata da haihuwar da zaayi a yanzu kafin kowace haihuwa a BOYEM ta ‘da namiji ce Wanda taurari biyu suke gani a duk lokacinda suka duba da Wanda yake a miqe da Wanda ya karkace amma basu samo maanar hakan ba tukuna amma dai sun bata tabbacin namijin ne jinin dazai sauka a masarautar wannan Karan.
Wannan tabbacin da aka bata ya sakata daukan kakkarfan alwashin kashe duk mai cikin da zata rigata haihuwa dan hakanne aka wayi gari faree tabar duniya sbd kada ma a samu akasin wata ta rigata haihuwa ta Haifa namiji tinda sun bata tabbacin namiji ne zaa Haifa bawai kuma lallai sai ita ba.
Wannan cikin datake Reno a boye tanada Wani irin Buri da quduri mai tsaurin gaske akansa hakama daga kansa batajin daga kansa sultan zai sake haihuwa da kowace mace Bayan ita duk wadda Allah yasa ma ta dauki cikin to tabbas zata bar duniya dan babu wani dan da zata yadda a haifawa sultan Wanda zaiyi gasar karban mulkin BOYEM da ‘danta sbd kujeran BOYEM ta ‘danta ce shi kadai koda kuwa rayuka da dama ne jininsu zai ringa gudana a shirye take ba sauki ko kadan,
*****a lokacinda HAILE ke boyon cikinta dake qara kusantar lokacin haihuwa itama Ayanah nata cikin yana gap da kusantar haihuwa kuma har lokacin sultan samun nutsuwa yakeyi da ita wadda a yanzu ne yake sake ciki da wajen mace dan kuwa cikinta ya bayyanar masa da abubuwa da dama dayake fatar taci gaba da haihuwan dukkanin yayan da zasu rage masa ya Haifa dan kuwa Ayanaah ghaz takai dukkanin matakin dabai kamata ba ta isa a zuciya,ruhi da gangar jikinsa da ayanzu bata appreciating kowace mace a shimfidarsa idan ba ita ba dan kuwa labarin imebeti a zamanin sa na Neman shifewa dan Bayan ita haryanzu babu imebetin daya karba an tsaya daga nan.
Want haihuwan Ayanah ya tsaya hankalin tenya da sakinah yafara tashi sun duqufa tareda maida dukkanin adduarsu ga Allah Akan samun ‘dan da duniya gabaki daya zatai alfahari dashi,
Irin adduar dasu sakinah kewa cikin da ita kanta Ayanaah din ya saka take samun karfin gwiwan haihuwan da fatan haihuwar cikin sauki da aminci.
Kamar a mafarki Ayanah ta bude fararen idanuwanta da sukai nauyin bacci ta saukewa fuskar sultan dake gabanta Zaune yana mata Wani kallan dayake Jin kaman zai sauya kaddararta zuwa wadda babu me iya sake ganinta a duniya,
Hannunsa dake wuyanta tabi da Wani irin kallo tana Jin zuciyarta na bugawa da karfi ta sauke idonta a wuyanta da sarkar wishmah ta bayyana wadda ya saka mata a cikin baccinta,
Wani irin mummunan Juyawa taji kanta nayi Wanda ya saka mararta murdawa da karfin gaske a take wasu ruwa masu karfin gaske na haihuwa suka fashe mata duka sbd mummunan girgiza da shock mafi girma a rayuwanta na zama wishmah ta uku a tarihin BOYEM kaf..
Gadan gadan naquda me karfin gaske ta taso mata take aka shigo aka fita da ita mahaukaciyar sarkan daham din data saka BOYEM gabaki daya girgiza tana wuyanta.
Tenya da duk Wanda aka daukota dasu Wani irin shook suke shiga na ganin abinda anfi shekaru dari kafin wani ya sakata a wuyansa se ayau,
Kamar a mafarki aka saki qararrawar datake gauraye BOYEM har cikin gari dayake sanar da kakkarfan labarin sabuwar WISHMAH Masarautar BOYEM,
Labarin sabuwar wishmah a qasar da labarin naqudar datake yi a yau din lokaci daya ya buga kunnuwan mutane musamman manyan BOYEM da kusan kowa ya fara shirin gaggawar isa fada inda duk wani babba me babban matsayi a BOYEM zasu zauna tareda sultan jiran dakon lokacin naqudar har zuwa haihuwa sbd sanarwar haihuwar wata gagarumin lamari ne tinda magajin BOYEM ake jira dan haka take masarautar tayi tsit komai ya tsaya cak sai ta haihu zaayi bikin qaddamar da ita wishimah Wanda yake tamkar daurin aure ne.
A daidai wannan lokacin sautin qarar bayyana da tabbatuwar wishmah a BOYEM ya shiga kunnuwan HAILE wadda ta miqe daga Zaunen datake kanta na Wani irin mummunan sarawa kafin ta bude Baki baiwarta ta iso da sauri kanta a qasa ta zube gabanta ta isar mata da imebētis Ayanah ghaz na naqud…..
Bata rife Baki ba jini ya ballewa HAILE tareda ruwan naquda masu karfin gaske tana dafe cikinta da tsananin karfin gaske sbd naquda mai Zafin gaske data taso mata gadan gadan itama.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
37
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291
*******
Cikin gaggawa da tsananin sauri babbar jakadiyarta mai suna fatto ta iso tana riqeta hannuwanta na rawa da kakkarwa ta riqeta tana sanar da bayin suyi gaggawar gyara dakin da zatai naqudar.
A take kuwa duka bayin dake babban bangaren nata suka hau shirin gaggawan tarban haihuwar,
Ruwa da wasu abubuwan al’adah suka fara gaggauta hadawa wasu kuma na gyara Wani lafiyayyan daki daya a cikin tarin dakunan dake bangaren nata,
Jini ne sosai yake zubar mata Wanda ya saka hankalin fetto da Sauran manyan bayin nata tashi take akai gaggawar isa da ita dakin da akaiwa shirin karban haihuwar tata aka kwantar da ita idanuwanta a rantse cikeda wata mummunar azabar datake sake tsananta tafasa jininta dake wata irin tafarfasa,
Budewa idanuwanta tayi da sukai wani mummunan ja zufa na jiqata ta sako wani azababben nishi tana bude baki da karfi cikin azabar datake ratsata tace
‘Sultan yasan da cikin kuma yaci gaba da kwanciya da ita a tirakarsa…….
Wishmah a Masarautar BOYEM yanzu?
Qarni qarni sun shude harma tarihin samun wishmah a BOYEM yana shirin shudewa shine yanzu rana tsaka sabuwar wishmah zata bayyana Akan sultan YASAR?
Me take dashi wannan imebetin?
Wace ce ita?
Tayaya zata samu matsayin wishmah dake kusan nuni da itace macen datake zuciyarsa fiyeda matansa na aure………
Wani Ihu mai tsananin qarar gaske ta sake jikinta na wata irin jijjiga da fizga,
Azabar naquda takeji tana ratsa dukkanin qasusuwan jikinta amma kuma baqin cikin dayake ratsa jininta shi takejin yana Neman kasheta dan kuwa Ayau da ba tata naqudar takeyiba wlh tallahi bazata Bari Ayanah ghaz ta haihuba,
Wani irin yunqurin azaba ta fara gabobinta na amsa wata kakkarfar azaba sbd bazata iya yadda Ayanah ta rigata haihuwa ba dan kuwa a tabbacin bokayenta sun tabbatar mata da duk haihuwar da zaa fara a BOYEM yanzu to tabbas namiji ne taurari sun buga sun buga sun tabbatar da hakan dan haka ko zata yage saita turo abinda yake cikinta ya fado duniya,
Cikin tsananin kulawa babbar yarta ta iso bangaren cikeda damuwa da kulawa ta iso ta gefen mahaifiyars tata batareda tana ganin wasanta dake rufe kare da wani babban kyalle green su fetto da likita mace daya da suka kirawo sai babbar baiwarta daya suna kokarin karban haihuwan duk sun hada Wani irin gumi,
Nauyi da azaba tareda rikice wa naqudar tayi wadda take sake saka jini fitowa da sauri fetto ta kalli HAILE din wadda azabar tayiwa yawan da tana kokarin ficewa hayyacinta ta bude baki zatai magana cikin girmammen baqin ciki da ukuba HAILE tace bata bawa kowa ikon ce mata komai ba matiqar ba haihuwan suka tayata yiba,
Likita data dago yin maganar dole suna buqatar kiran Sauran likitocin da zasu taimaka mata Jin abinda Hailen ta fada ya sakata yin shiru tana hada zufan tashin hankali sbd akwai Sauran time dan kuwa service dinta baima gama budewa ba dan haka sunada aiki sosai ga naqudar bame sauki bace yakeyi tinda shock ne Kai tsaye ya tado naqudar,
Fetto Kai da kawo ta fara tana fitowa tana komawa cikin tsananin tsoro da tashin hankali me girma ga Masarautar tayi Wani irin tsit babu motsin komai bare kowa alaman duka manyan BOYEM sun taru a fada jiran naqudar Ayanah ghaz wadda itace wadda kaf BOYEM yanzu ake jira dan haka a kakkarfar doka da baa takewa ta Masarautar gabaki dayanta shine duk jinin BOYEM idan zaa Haifa Ana fara naqudar sa babu me sake fitowa bare kaida kawo tsit akeyi har sai ta sauka dan Kai tsaye duk Wanda tsautsayi ya sakasa fitowa ko kaida kawo a hanya cire kansa daga gangar jikinsa ya halasta,
Dan haka ne Ayau dinma babu motsin komai bare hayaniyar komai koina tsit ne tamkar babu dan Adam ko daya a cikin masarautar BOYEM din,
Duka tarin bayin daka bangaren Haile sun gama shirin tarban abinda zata Haifa dan haka a tsaye suke qyam babu kowane motsi dayake tashi suka anan din sai fetto daka Kai da kawo kaman zata rasa hankalinta ta zare,
Zufa sosai take hadawa gashi ba ikon magana so take taje ta isarwa sa sultan labarin naqudar Haile amma ba damar fita dan fitarta daidai take da kwananta kabari Ayau din dan saita bar duniya dan haka babu damar fita,
Su kansu bayin dake bangaren duka babu Wanda ma yakeda ikon motsi bare fita zuwa isar da sako dan haka ta rasa yaya zatai da rayuwarta fa naqudar sai abu daya ake kwata kwata babyn bai fitoba,
Ita kanta likitan kokarin tsayar mata daya jinin tayi da taimkon da zata iya bata amma dole haihuwa sai lokacin da Allah yace babyn ya fito zai fito dan haka dukansu zufa suke hadawa ba qarami ba suna rasa abin yi har HAILE din tayi Laushi sosai amma taqi yadda kowa ya tsaya hutawa sbd baqin taurin ranta Akan kada Ayanah ta rigata haihuwa,
Tana tsananin buqatar likita amma babu me ikon fita dan kuwa koda Ka isa ka isar da sako tabbas zaka karbi hukuncin barin duniyar Ka dole Shiyasa kowannensu yake hada zufa suna Kai da kawon taimaka mata gurin samun sassaucin abinda take ji,
Zufan fuskarta zuwa wuyanta ake goge mata da tsaftataccen farin towel qarami suna Jera mata Sannu da kokarin ganin ta haihu lafiya, magani kuwa haka ake kawo mata shi tana sha tana dawo da wani sbd tafara Nisan da bata iya Shan komai amma a zuciyarta ta kasa sake adduar datake yi guda daya tak wato ‘Allah ya bata ‘da namiji koma yayane kuma Allah yasa itace zata fara haihuwa’
Wannan adduar take ta maimaitawa tana kasa sakewa dan tabbacin datake dashi na Allah yana karban adduar me naquda dan haka har a tafara ficewa hayyacinta bata roqarwa kanta ko ‘yayanta komai sai wannan adduar gida biyu.
****A daidai wannan lokacin naquda sosai AYANAH GHAZ takeyi me tsanani itama Wanda ya saka itama nata bangaren da bangaren imebētis din kaf yin tsit babu ko abu daya dayake bada sauti sbd Masarautar wannan Karan tafi kowane karo yin tsit dan kuwa mamaki biyu ne yake ci da kashe kowa amma b damar magana a yanzu wato shine Wishmah data tabbata Bayan qarnika da kuma haihuwar da baa San da cikinba kuma a hakan taci gaba da zuwa shimfidar sultan,
Wannan duka wasu abu ne da suka girgiza masarautar da duk Wanda yake cikinta cikeda tsoro da mamakin dayafi Kama da firgici kowa yake,
Masu rubuta tarihin qasar BOYEM da Masarautar BOYEM kuwa a daidai wannan lokacin suna can sun fara rubuta wa a cikin kundun tarihi,
A cikin fadar sultan ma a inda ake Zaune tsit abu daya kowa ke jira wannan Karan sunfi kowace lokaci daukan tsit sbd Ana magana a tsakaninsu duk zaman jiran da akeyi amma a wannan Karan sultan YASAR babu abinda ya bude baki ya furta hankali da nutsuwar sa kaf suna ga jiran sakon haihuwan Ayanah ghaz dake saka zuciyarsa cika da Wani irin nauyi da yanayi na tsumayi dabai taba shiga b duk haihuwan da ake masa,
Sosai yakejin kowace daqiqa tana wucewa ne da bugu wan zuciyarsa mai karfin Akan haihuwar yau dayake jinta har jini da bargonsa dan haka take duk Wanda yake fadar ya dauke wuta sukai tsit suma suna shiga tsimayin jira da Jin tsananin son labarin haihuwan wishmah ta farko data sauya tarihi da dama na masarautar qasar BOYEM gabaki dayanta dan haka sai sukejin haihuwan ta jinin BOYEM wannan Karan ta daban ce a gurin sultan da wannan dalilin suka ta zama ta musamman din tinda kuwa wishmah ce zata haihu kowa yasan haihuwan soyayya ce bata saurauta ba.
Tenya data kasa ta tsare ko motsawa batai ba daga gaban Ayanah dan kuwa duk inda hannuwan likitoci suka taba a jikinta idonta na Kai sbd tsananin tsaro da rashin yadda da kowa,
Sakinah ma a wannan lokacin tana riqe da hannun Ayanah gamgam suna hada zufan tare tana Jin duk radadin da Ayanah ke ji a zuciyarta tana Jin tsananin matsuwa da son haihuwan Ayanah lafiya tana saka mata addua mai kyau a bakinta,
A bakin Ayanah din addua ce guda biyu rak take fita wato Allah ya zama gatan yan uwanta dasuke raye ya kawo sauyi a rayuwarsu sai kuma adduar Allah ya tsaya Akan kowane irin lamarin babynta da zata Haifa,Allah ya haskaka rayuwarsa ya basa kariya daga duka Sharrin duniya’
Wannan adduar itace take maimaituwa a Baki da zuciyar Ayanah da sakinah harma da tenya da ita iya babyn takewa adduar Allah ya basa kariya har qarshen rayuwa kowannensu a zuci yake adduar.
Sosai azabar tayi mata yawan data fara galabaita tsananin tausayinta na saka zuciyoyinsu sanyaya dan haka suka dage da addua da karfi da imaninsu suna Neman mata sauki a gurin ubangiji,
Sakinah jiqe take shar kaf da zufa tana tsananta adduarta a fili tana share zufan Ayanah suna sake qanqame hannun juna Ayanah na Jin kaman bazata rayuba rayuwarta zata tsaya ne daga nan sbd abinda take ji tabbas shine kowace uwa takeji yayin jeho yaya a duniya idan har ta mutu anan ta tabbatarda tayi shahada dan haka take Jin inama zata mutu anan din ta huta.
Lokuta masu tsayi suka dauka dukansu suna naquda me tsayi da rashin sauki,
Babu wadda bata Kai qarshen jigata ba a cikinsu tareda fita hayyaci,
Duk wainda suke tareda su sun sare sun shiga tsoro da fargaba tsawon wunin da babu komai cikinsa sai jiran azaba,
Karfe shida na yamma a lokacin da baby ya turo kai fitowa jikin HAILE gadan gadan take su fetto suka shirya tsaf ma tarbansa cikin tsananin matsuwa sbd suna sane da har lokacin Ayanah ghaz bata haihu ba dan akwai sautin karar da ake sakewa masarautar ta amsa gaba daya idan an haihu dan haka tinda basu ji komai ba sun San bata haihunba gashi yanzu tasu zata far haihuwa babbar matsalar shine fita a wannan lokacin batareda haihuwan Ayanah ba zuwa isar da sakon haihuwar.
Cikin azababbiyar azaba da Nishin dayake hade da ihu mai karfi Haile ta saki tana qanqame hannuwan yarta da karfin gaske ta sunbulo babyn dayake cikinta ya fado a hannun likitar dake gabanta idanuwan fetto kaman zasu fado qasa sbd jiran ganin abinda aka Haifa,
A daidai wannan lokacin itama Ayanah ta sauke wani kakkarfan nishin daya fito da nata babyn duniya itama Wanda ya fado a hannun tenya Wanda jikinta ya dauki mummunan kakkarwar abinda aka Haifa tama kasa yadda da abinda ta gani.
#MAMUH
#THE LION ARRVL
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
38
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda