idanuwansa ba abu ne da mutane suke iya riqewaba.
Qin dauke idanuwanta tayi dik da Wani irin abu dataji Ana ratsata na son kasa kallan nasa amma tanada nata kalan taurin zuciya da kai dan haka taqi denawa hakama batajin zata iya bude baki tai masa magana kaman yanda tasan ko zata mutu a gurin shi din bazai taba mata magana ba dan tasa kalar Izzar da sarautar kenan kaman yanda Maa ke fada batareda tasan itama akwai wannan a jininta ba zata iya rayuwa a guri idan bataso magana ba babu Wanda Zai iya sakata hakan.
Wani kallan isa da nuna ita din bata kai kowane matsayiba yayi mata yana zare hannunsa ahankali har lokacin idanuwanta yake kalla yanason ganin lanqwasawa a cikinsu yaci gaba za zare hannunsa Wanda yake zarewa tareda daurin towel din jikinta sbd hannunsa ne a dafe dashi ta danne idan ya zare hannunsa zata samu kanta a yanayinda zata iya rasa ranta sbd baqin ciki dan haka yaci gaba da zarewa yana kallanta,
Rintse idanuwanta tayi da Wani irin baqin ciki tareda saka hannu ta sake dafe hannunsa amma Sam baida niyar hakan zarewa yakeyi da gayyar datake karya duka Wani karfin halinta tayi qasa da kanta hawaye na taruwa a cikinsu na tsananin baqin ciki.
Numfashi ya sauke ahankali tareda dakatawa ta saka hannunta karkashin nasa ta dafe tana Juyawa cikeda baqin ciki da mutuwar jiki.
Shikuwa Juyawa yayi ya fice tareda rufe dakin yabarta yana Jin kukanta na fara fidda sauti ya tafiyarsa bai damuba.
A palon ya zauna ya kira aleey ta waya aka Jere masa breakfast ya zauna yayi anan aleey yake sanar dasu manyan securities dinsu da suka Baro Russia a Daren jiyan sun iso.
Izinin zuwa a shigo dasu masarautar NUAB din ya bayar aikuwa haka su aleey suka isar da pass dinsu a gate Wanda haka wasu irin mahaukatan motocin da zasu iya tada gari suka ringa shigowa masarautar a jere da wasu irin bindigogin da labarin su suka isarwa manyan fada a take,
Hankalin su fara tashi yayi sunajin shakka na kokarin shirya zukatansu da rayuwarsu na tsayuwar da suke da shirin yi Akan bazaa bawa NUAB mulki ba duk uban daya taru dan haka wasi wasi yafara shigarsu sbd yaran GHAZ din da suka iso masarautar masu yawa ne hakama babu Wanda alamar ma yasan menene imani yake bayyane a fuskarsa daukan ran kowa a masarautar ba abin wahala bane a garesu.
Sultan ya samu labarin isowansu dan haka take shikuma ya saka Hannu a takarda biyu yace a fitar a dare a tashi dasu a masarautar Washe gari wato ta imebetin ASIM wadda zaa shirya masa da gaggawa a abasa hakama data auren NUAB da Leylah yunar.
Tinda NUAB ya fito a ranar yana Zaune a palonsa hankali kwance a natse cikin iko da Izzar dayake jiran komai ma kaman yanda Yaransa suke cike a bangaren hakama a ranar aka fara aikin ware Wani makeken bangaren tsohon sultan zaa rushesa gabaki daya a fara masa sabon ginin irin gidansa sak dayake russia.
Babu Wanda ya shigo ko hanyar bangaren hakama babu Wanda ya fita shi Kansa Ayau Zaune yake bangarensa babu inda ya fita ko gurin Amminsa a Karan farko bai fita yaje ba a waya yayi magana da ita yana Zaune hankali kwance har dare.
A Daren takardun sakon biyu suka fito a lafiyayyun trays zuwa bangaren mahaifiyar NUAB da mahaifiyar ASIM.
Sakon na doso bangaren HAILE saleem dayake tsaye bakin bangaren saurin zubewa qasa yayi yana sunkuyar da Kai jikinsa gabaki daya yana daukan wata irin rawa sbd bazai iya karban sakon ba dan isar dashi ciki dan haka baiwar kusa dashi data fito yayi da sauri yace ta kirawo fetto sbd yasan tana fitowa itace zata Kai sakon.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
HAYATEEM
Mamuhgee
81
HAILE da gabaki daya yayanta a lokacin Zaune suke a palonta sun cin abincin dare Wanda aka jere a gabansu fiyeda Kala biyar da tarin fruits masu sanyi da tsafta a jere suma sai lafiyayyun juices d Aka hada musu fresh me sanyi,
Cin abincin sukeyi amma hankalinsu duka yana kan ASIM daya ce sultan ya amsa masa buqatarsa ta basa macen dayake tsananin so dan haka zuciyarsa a fes take Jiyan,
Tin jiyan bai damu da NUAB da Sauran kowace matsalarsa ba karban Bahar a matsayin tasa cikakkiya shine a gaban zuciyarsa dayake tsananin fatan Ayau burinsa ya cika din,
A nan bangaren mahaifiyarsa ya wuni da tsananin jiran fitowan sakonsa daga sultan Wanda yakeson Ana aikuwa ba bata lokaci akai saqon bangaren wishmah sbd baiwar dayake so acan take hakama wadda zata shiryata a matsayin imebeti itama acan take dan haka da gaggawa yake son sakon yaje can ba bata lokaci ko qanqani,
HAILE ma zuciyarta sai Wani irin rawa da harbawa takeyi da tsananin farin cikin daya hanata gabaki daya kaiwa sultan ziyara a ranar daga ita har yayanta zaman gadin isowan sakon auren sukeyi Wanda babu Wanda bayajin Dakawar zuciya Akan hakan sbd sun matsu sultan ya fidda umarnin tin kafin labarin ya sauya.
Suna Zaune dinne jiran wannan umarni kaman zukatansu zasu fado sbd matsuwa da zullumi kwatsam sai ga sakon Kira ya tahowa fetto daga waje Wanda jikinta take ya dauki rawar farin cikin karbowa HAILE da yayanta abinda Ayau suke tsananin Buri na umarnin auren danta daga sultan.
Fetto na fitowa sakon na isowa dan haka da sauri ta qaraso tana zubewa qasa gaban manzon sakon tana masa Barka da isowa tareda kirari ga sakon na sultan.
Hannuwanta biyu ta dago tana miqawa dan amsar sakon Wanda ya saka Salman sake saukar da Kansa qasa zuciyarsa na Wani irin tsima da tsananin tashin hankali yana ma kasa kallan sakon.
Fetto kuwa tsabar Murna jikinta har wani rawa yakeyi ta amsa tareda zuba godia ta juya ta shige ciki da sakon.
Ko data iso palon da suke Zaune gabaki dayansu suna cin abinci har lokacin ASIM ne idanuwansa suke fara sauka Akan hannuwanta biyu dake dauke da takardar fadar sultan dan haka ajiye cup din hannunsa yayi a hankali yana kafe idanuwansa Akan hannuwan nata ba kyaftawa zuciyarsa na cikewa da Wani irin farin cikin da tinda yake bai taba jinsaba.
Aslam da meryam kallan yanayinsa sukeyi da mamaki kafin suka Waiwaya suna kallan inda yake kalla da wannan yanayin da suma basu taba ganinsa a ciki ba.
HAILE ma juyawan tayi ahankali ta kalli inda suke kalla gabaki dayansu taga fetto na qarasowa dauke da takardar da dole daga sultan ta fito tana daukan ido sbd kyallin kalar gold dake jikinta.
Wani irin farin cikin taji itama ya cikata Wanda ya sakata ajiye spoon din hannunta taba daukan tissue ta goge baki tareda miqewa tsaye take suma yayan nata suka fara miqewa daidai nan fetto ta iso da takardar wadda ta miqawa ASIM.
Cikeda farin cikinsa dayake sake bayyana ya karba tareda budewa a hankali yana karantawa jikinsa har tsima yakeyi ganin cikakken izinin mallakar Bahar a matsayin imebētinsa wadda samunta a rayuwarsa shine matakin farko na nasarar rayuwarsa da zai fara daga yanzu,
Sunanta daya aikawa sultan shine a bayyane Baro Baro a rubuce cewan ta zama imebetinsa daga yau dan haka rufe takardar yayi hannunsa na dan rawa ya miqawa fetto ya kalleta da dukkanin idanuwansa yace
‘Ki Kai bangaren wishmah wannan sakon na tenya ne a gobe nake buqatan wara haka imebeti dina tana bangarena’
Da tsananin mamaki fetto ta kallesa tana amsar sakon hannuwanta na dan rawa sbd shock da fiyayyan mamakin Jin sunan imebeti a bakinsa Bayan Leylah jinin sarauta ce meya hadata da sunan imebeti kuma?
HAILE kallansa tayi tana dan Kama Fuska zatai magana Aslam da bazata iya jiran bayani ba karban takardar hannun fetto tayi tana budewa Kai tsaye tafara karantawa rubutun Wanda yake a rubuce da yarensu da manyan baqaqe masu kalar zinari na alkalamin sultan me mulki.
Meryam data Riga Aslam gama karanta sakon Wani irin sanyi kafafunta sukai me tsananin gaske suna kasa daukanta ta zame ahankali tana Zaunawa idanuwanta na dagowa da Wani mugun kallo tana kallan ASIM dan tabbatarda farin cikine bayyane a fuskarsa na abinda yake rubucen.
Aslam miqa masa takardar tayi tana masa Wani kallan mamaki me tsananin gaske ta bude baki tace
‘Kaga menene a ciki?
Ka fahimci abin dayake cikin sakon kuwa?
Kasan me aka aiko maka?
Miqawa fetto sakon ya kuma yi yace ta fice ta Kai ya kalli Aslam zaiyi magana HAILE datake Jin yanayin zuciyarta na sauyawa ta Dakatar dashi da cewa
‘Menene yake rubuce a ciki?
Ba auren Leylah bane a cikin sakon?
Meryam datake Jin kanta na Juyawa ce ta iya bude Baki jikinta na tsananta mutuwa da Wani irin yanayin da bazata iya fassarawa ba tace
‘Imebēti aka basa a maimakon auren Leylah’
Aslam data kasa Hadiye tsananin baqin ciki da fushin dayake taso mata ta Dora da cewa
‘Kuma da alama yasan da hakan sbd farin cikin dayake bayyana a fuskarsa,
HAILE dataji kaman bata fahimci zancen da kyau ba kallan ASIM din tayi da duka idanuwanta fes a Kansa zuciyarta na sauya bugawa ta bude Baki tace
‘Imebetin?shi sultan dinne yaga ya kamata ya baka imebeti Bayan ya bawa ‘dan mistress dinsa auren jinin yunar?
Juyowa tayi Akan Aslam da meryam tace
‘Sunan ASIM dinne kuwa kuka gani a rubuce ciki kokuwa sbd sakon bazai taba kasancewa nasa ba dan ba yanda zaayi yana matsayin me jiran gadon kujeran BOYEM ya fara da imebeti batareda yayi aure ba hakama yayansa manya su fara zuwa daga imebēti,
Tayaya hakan zai taba yiyiwa?
Ba sakonsa bane?
Aslam data gama kaiwa qarshen baqin ciki dafe goshinta tayi tana bude idanuwanta jajir tace
‘Mamee yana sane fa,kuma da alama shine a buqaci hakan’
Kafesa da ido HAILE tayi sbd tanason ji daga bakinta idan sakarai ta haifa bata saniba
Kallan Hailen yayi yana matsowa gabanta ya Kama hannunta cikin tausasa harshe yace
‘Mamee ba imebeti ce kadai ba sonta nakeyi so me tsananin da zan iya komai akanta ciki hadda rasa rayuwata,
Ba jinin sarauta bace baiwa ce dan haka Banda zabin daya wuce karbanta a matsayin imebē…….
Bai qarasa ba HAILE ta sauke masa Wani lafiyayyan Marin daya saka meryam miqewa tsaye da sauri Aslam ma cikin sabon tashin hankali take kallan Hailen da idanuwanta jajir.
Kasa dagowa ASIM din yayi idanuwansa na rikidewa zuwa jajir zuciyarsa na cikewa da Wani irin ‘daci da baqin ciki me girma.
HAILE ma kasa dauke idanuwanta daga Kansa tayi hannuwanta na wata irin rawa zuciyarta na tafarfasan da bata taba ba kowace gabar jikinta wutar baqin ciki ne take ciketa tana rasa abin fada.
Bata taba sanin sakarai mara tinani da hankali ta haifa a rayuwarta ba sai yau,
Baya tayi ahankali tareda Juyawa ta sake juyowa ta kalli ASIM din ta bude Baki kirjinta na tsananta nauyi tace
‘Me zakai da imebēti Banda zuciyarka ta mutu?
Har akwai abinda wata baiwa take dashi Wanda yakai na Leylah?
Baiwa zaka fara haifar yayan Ka da zasu gaji sarauta daga gareka?
Wane soyayyar kake magana?
Ka sani wlh tallahi indai ina raye bazan Bari Ka fara karban imebēti ba batareda Ka auri jinin sarauta ba musamman wannan da kake ikirarin kana so da zata iya sakaka rufe ido Ka zabi gaibu Akan jinin Leylah datake jinin boyem.
Dagowa yayi idanuwansa jajir ya kalli mameen ya bude baki yace
‘Mamee zan auri jinin BOYEM daga baya amma a yanzu ina tsananin son wannan ita zan mallaketa….
Aslam data rasa abin cewa Juyawa tayi cikin tsananin baqin ciki taba barin palon hakama meryam da zuciyarta ke gap da bugawa ficewa tayi.
HAILE ma cikin baqin ciki ta juya tabar gurin tana yanke hukunci a ranta baiwar kowace iri ce zata bar duniya dan bazata taba zama imebetin ASIM ba a yanzu.
Fetto kuwa tana fitowa Kai tsaye bayi hudu ne suke biye da ita zuwa bangaren wishmah dan miqa sakon ga tenya zuciyarta cikeda baqin ciki itama da damuwa dan ba hakan sukeso ba.
Suna tinkaro bangaren securities din dake gurin suka miqe tsaye kowannensu ba rahama a fuskarsa dan kuwa ko wane yare ma wainnan basa ji sai turanci kawai dan haka basada lokaci ko iya tambayar komai.
Kokarin isowa sukeyi ba tsammani sukaji Wata irin azabar data zubar da su qasa tana ratsa kwakwalwansu wadda tama kasa daukan azabar.
Fetto ce ta iya juyowa taga bayin a zube qasa gabaki dayansu jini a kafafunsa sbd harbin da akaiwa gefen kafarsu batareda ta ratsa qashinsu ba.
Juyawa taji idanuwanta da kanta sunyi sakon dayake hannunta yana faduwa qasa ta dago komai na jikinta na masifar rawar mummunan firgita da tashin hankali batasan lokacinda ta zube ba zata fasa Ihun hankalinta dayake kokarin barin jikinta ganin meya samu bayin Bayan.
Wata irin damqa akai mata tamkar daurin kasar da zaa yanka akai mata tareda soka mata wata allurar data sumar da ita aka bar gurin da ita Sauran bayin ma sbd Hana hayaniya tashi a kofar bangaren na Ammin daukansu akai aka aika su clinic din cikin masarauta suna barin gurin gabaki daya tareda daukan sakon suka kaiwa aleey Wanda bai Bari ya isa ga NUAB ba ya kona sa suka cigaba da shaaninsu tsit kake ji.
Kadir ne ya iso gefen sultan a cikin Daren ya rankwafo cikin nutsuwa ya sanar masa abinda ya faru din.
Numfashi Mara sauti sultan ya sake yana dago manyan idanuwansa daga abinda yake karantawa a Wani file ya bude baki Kai tsaye yace a sake aika Wani sakon Kai tsaye a gurin tenya ta tabbatarda an fara shirin imebētin ASIM din a gobe hakama a hada tareda sabuwar takardar auren NUAB din akaiwa mahaifiyarsa.
Sabuwar takarda kadir ya fitar wadda a cikin Daren ta isa bangaren wishmah batareda sanin Bangaren NUAB ba.
Isowan sakon Wanda ya saka Ayanah zubawa takardar idanuwanta da tsananin yanayin da takasa gane wa kawai dai tasan tana farin cikin auren yar Zuhrah da NUAB dinta Wanda take Jin ma a gaggauce take son Ayi auren dan haka cikin godia da farin ciki ta amsa sakon.
Tenya ma cikeda mamaki take kallan nata sakon Wanda ya sakata shiga wasi wasin Kai tsaye menene dalilin ASIM na buqatan imebetin kuma shine ya zabeta da kansa.
Maa sakinah dake fitowa daki kallan tenya tayi tareda kallan takarda hannunta wadda idonsa suka sauka Kai tsaye Akan abinda sakon yake isarwa da sunan Bahar.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laoualiHAYATEEM
Mamuhgee
82
Kasa yadda da abinda idanuwanta Maa sakinah tayi sbd kanta dataji yana Neman juyewa ta zagayo ta gaban tenya din tana sake tabbatarda abinda yake gani a rubuce ta bude Bakinta da Wani irin sauti tace
‘Wace Bahar din ce zaa bawa ASIM a matsayin imebeti?
Da mamaki tenya ta dago ta kalli sakinah tareda cewa
‘Wace baiwar ce Bahar?
A wane bangare take?
Anan bangaren take ne aka aiko mun sakon anan kokuwa ma tana ina ne ni Bansaniba ma’
Sakinah datake kasa yadda ga bugun zuciyarta na mugun tsananta harbawa da karfi tareda Wani irin tsoro me girman gaske sbd batama San tayaya wannan Masifar ta qullo ta bullo ba,
Wani faduwan gaban ta sake ji tana tinawa da Bahar tayi aiki a bangaren ASIM din Wanda sai yanzu taje dawo da tinanin Kai tsaye shine ya buqaceta dasu naima da komawa bangarensa aiki.
Kallanta tenya keyi sosai da kyau ganin yanda zufa yafara tsiyayo mata tana shiga tinanin datake sake shigar da ita tinani da zullumi itama.
Kasa cewa komai Maa sakina tayi ta bar gurin ta nufi dakinta zufanta na sake tsananta tareda tashin hankalinta sbd bata San wane yaqin tashin duniya ne wannan zaayi ba ace matar da igiyoyin auren NUAB suke kanta itace dan uwansa yake so a matsayin imebeti,
Tayaya wannan muguwar kwamacalar zata fara?
Tayaya ma zata fara zuwa isar da wannan mugun sakon da zai Yadu zuwa safe kuma babu Wanda duk duniya ya isa ya Hana hakan tinda har sultan ya Riga ya saka hannu babu abinda zai Haba Ayi hakan.
Wani nauyi kirjinta yayi me tsananin gaske ta fara kaida kawo tsakiyar dakinta tana Jin har numfashinta yana daukewa sbd matiqar aka fara shirinta aka fara wanketa da ruwan lallen dazai wanketa tas to ta tabbata dai ta ASIM ce Wanda ko ita matiqar NUAB ya Bari akaiwa Bahar dinta hakan batajin zata iya yafe masa wannan laifin har abada dan kuwa ba amanarta ce ita kadai ba Bahar din shine ma asalin Wanda amanar tata taje hannunsa.
Tenya ajiye tata takardar sakon tayi sbd sai gobe amma dai a cikin Daren ta aika sakon a shirya bangaren wanke imebetin da tsiminta tareda wanketa a inda sai kamanninta sun sauya sbd yanda zata koma,
Farin cikin Dayan sakon tafara tareda Leylah cikin farin ciki me yawa da tsananin gaske,
Ayanah ma datake cikin tinanika da saka ido sosai Akan sauyin datake gani a tattare da Sakinah bawai dan zata cutatar da ita ba sedai tana ganin kaman akwai abinda sakinah take boye mata na damuwa ayanzu dan koyaushe bata iya hada ido sosai da ita kaman baya hakama gabaki daya hankalinta yana kan sabuwar baiwar datake tsananin son sake gani Akan abu biyu datake son sake gani da ji akanta amma ayanzu farin ciki mai tsananin gaske ta samu kanta na auren Wanda shine zai hadata da yar uwarta Rabin jikinta da sukai shekaru masu yawan gaske basu hadu ba,
Tsananin farin cikinta na ganin Zuhrah ne,
Zata ganta zata kalleta a gabanta koda kuwa basu furta su yan uwa bane zasu kasance a gaban juna a matsayin sirikan da zasu hada iri zasu hada zuria yayansu zasu auri juna zumuncinsu da suka rasa sbd rashin yanci zai dawo daga karshe zata rungume yar uwarta da zuciyanta da ruhinta suke tsananin buqata,
Wannan sune babban abinda ya saka farin cikin auren yake dake kame kowane saqo na zuciyarta da gangar jikinta dan haka Kai tsaye takejin tamkar tafi kowa matsuwa da Ayi auren.
Leylah kuwa Jin tayi farin cikinta yana danne baqin cikin datake cikinsa na Bahar da NUAB amma a yanzu sassauci da farin ciki take jin zuciyarta fes.
Maa sakinah kuwa kallan lokacin Daren takeyi tana Jin zuciyarta na sake tsinkewa da tashin hankali,
Bahar take tsananin son gani a lokacin sbd tafara ji daga gareta ko akwai maganar data taba shiga tsakaninta da ASIM hakama taga halinda take ciki sbd matiqar sakon ya kai bangaren NUAB a Daren to batajin akwai Wanda Zai iya rintsawa kaf masarautar amma koina tsit takeji dan haka take saka ran sakon bai isa can ba.
Zulluminta na qaruwa tana sake kallan Agogo tana