me tsanani a gurinsa kafin kuma daga karshe ya barsa a macensa cewa shine hukuncin sa haka zaici gaba da zama tamkar dan daudu.
Baiji ciwo da Zafin hukuncin ba sosai sedai Ka quncin sa daya dawo sabo na rashin yan uwansa a rayuwarsa dayake ganin batada Sauran amfani a gurinsa,
Yanayin alaqar sa da ayshaah sauyawa tayi sbd jinsinsu daya bayyana ba daya ba dan haka ta rage shige masa sosai hakama ta Dena bayyanar da inda be kamata ba a jikinta indai suna tare sbd kiyaye dokar addini.
A hakan sukaci gaba batareda sun sauya masa tako wace hanya ba ko kadan,
Kaf garin sun San Nurat a matsayin bawan ahalin da shine bawan da zai zama na ahalin me zuwa dan kuwa idan har boukar ya mutu Nurat yana cikin gadon da zaa raba maana shi Kansa abinda Wani ze iya gada ne a gurin rabon gadon Wanda yan uwansa keta lissafi sbd arzikinsa yayi wata irin sake habbaka ya tara dukiya ke yawan gaske data saka yarsa taje rayuwa tamkar sarauniya a fada,
Da farko Bayan angane Nurat namiji ne ba mace ba mutan gari sun so korarsa sbd jifansa da ihu aka ringa yi masa daga kasuwa da aka aikesa Wanda Koda ya iso gida sun masa mummunan illar data sauya masa kamanni sosai sbd jifar ta fasa Kansa da fuskarsa amma a hakan ya iso gidan baya ko gani sosai sbd jinin daya rufe idanuwansa.
Da karfin dukiya boukar yayi amfani ya hana a kori Nurat din amma kuma tin daga wannan lokacin Nurat ya zama abin qyama da hantara tareda jifa a cikin mutane a duk lokacinda zai fita gashi har lokacin shigar mata yakeyi,
Tsananin tsana da qyama tareda hantarar dayake fuskanta a rayuwarsa tsawan shekara kusan uku ya saka rayuwarsa gabaki dayanta komawa asalin baqin ciki da qunci dan haka sai abin ya fara taba zuciyarsa da daman bata taba fita tsananin qunci ba.
Wasu bayin boukar ya siyo guda biyar masu karfi dan gadin gidansa da ako Yaushe ake kokarin kawo harin Kai karshen rayuwar Nurat din Wanda kaf garin suke ganin mugun abu ne a cikinsu zama da zabgegen namiji a cikin Kayan mata dan haka koda be bar garin ba to zasu kashesa dan zamansa a garin tamkar zunubi ne.
Cikin wannan fitinar dake tashi koyaushe yan uwan boukar dake harin rayuwarsa suka shige sbd samun biya da cimma burinsu na shekaru masu yawa akansa sbd a yanda Nurat ta zama rayuwarsa da ‘yarsa bazasu iya rabuwa dashi ba dan haka suna samun ya fara shirye shiryen barin garin da Nurat dan komawa Wani garin suyi rayuwa hankali kwance tinda yanada dukiyarsa me yawan gaske.
Ana cikin wannan halin rana tsaka kwatsam cikin dare kawai aka cinnawa bangaren abincin boukar dake gidan wuta inda tarin dukiyar abincin sa take me yawan gaske buhuhuwan hatsin da dukiya ce me tsananin gaske,
Fitowa boukar din yayi cikin duhu da hayaqin daya gauraye gidan har Baka ganin komai yana kokarin isa bangaren idanuwansa da kunnuwansa sukai masa mummunan ji da ganin daya tabbatar masa da halin yan uwansa dayake zargi na shekaru masu yawa dan haka da sauri ya juya cikin hayaqin jikinsa na rawa zuciyarsa na Wani irin radadi da firgici sbd lamarin Yazo masa a bazata.
Fada ne ya fara kaurewa da hayaniya tareda ihu a gurin kashe wutar wadda duk da tsakiyar dare ne amma take mutane da suka cika gurin da sunan kashe wutar da kuma son qaddamar da nufinsu a cikin hayaniyar kashe gobarar na kashe Nurat su kuma yan uwan boukar kashe sa dan hakanne ma suka fada sun tada wutar yanda zaa hargitse ana ihu da hayaniyar kashe wuta su kuma sukuma su aikata aikinsu tareda sace dukiyarsa dan haka basu taho da shirin barin ko ‘yarsa ta rayu ba bare bawansa.
Fada aka fara tareda sare sare Ana fidda jini me yawa sbd bayin dake tsaron gidan da sukaga alamar fitina a tattare da kashe wutar dan haka suka fara hanawa sedai ko gama rufe baki na farkon beyiba suka rufu a Kansa suka sassarashi suna cewa shi bawa ne bai isa ya basa umarni ba sedai su su basa.
Jin hayaniya da Ihun kashe karshen daya dauki gari ya saka boukar daya dauko makaminsa dakatawa ya juya ahankali ya kalli kofar dakin ayshahh sai kawai yaji tinaninsa ya sauya ko yayane yanason ‘yarsa ta rayu dan haka ya nufi kofar dakin da Nurat yake kwana yana zuwa Kai tsaye shiga dakin yayi ya tadashi da karfi tareda dagosa daga kwancen batareda yace komaiba ya riqo hannunsa da karfi suka fito tsakar gida yana sake shiga tashin hankalin hayaniyar da Ihun daya qarasa gauraye gari.
Abaas na fitowa yanda wutar take ci da Ihun da akeyi ya sakasa jin Kansa na Juyawa zuciyarsa na bugawa da karfin gaske komai na yanda ya faru garinsu yana dawo masa sabo.
Wani irin Zafi da tiriri yaji yana tasowa daga zuciyarsa yana gauraya jininsa komai na sake dawo masa tin daga gawar magaifiyarsu da suka fara rasawa.
Rawa jikinsa keyi kowane irin radadin daya dandana a baya yana dawowa yana zama kuzari da fushinsa dan haka dagowa yayi idanuwansa jajir da wasu irin hawaye a cikinsu sbd bazai taba yadda ya sake shiga hannun kusrawaba koda zai rasa ransa gurin cetan Kansa da ayshahh da boukar sbd har abada bayason su dandana baqin cikin daya dandana shi da yan uwansa musamman ayshaahh datake mace,
A baya rauni da rashin karfi ya sakasa zamowa nace yana kallo baida abin yi Bayan kuka aka tarwatsa rayuwar yan uwansa aka kashe masa Nurat dan haka wannan Karan a yanzu daya zama namiji ya zabi mutuwa Akan tafiya wannnan mummunan rayuwar.
Takobi da adda boukar ya basa yana kallan Zafin dayake bayyana a cikin idanuwansa yace
‘Ka tabbatarda Ka bawa Kanka da Ayshaah kariya’
Wucewa gaba boukar yayi da dan gudunsa na fuskantar komai ai kuwa yana fita take fadan ya dawo Kansa amma dayake yanada nasa karfin sosai haka ya ringa fadan dasu.
Shima Abaas baisan lokacinda ya fado cikin fadan ba idanuwansa a rufe komai na abinda ya faru dasu kawai yake gani dan haka kusrawa kawai yake gani a idanuwansa ya ringa fadan bayaji baya gani.
Fin karfinsu fadan ya fara yi sbd kusan duk bayin biyar an kashesu hakama suma anfara musu rauni dan haka boukar da jini sosai yake fita jikinsa kallan Abaas yayi cikin tsananin galabaitar daya fara yace
‘Ka tafi Ka dauki ayshahh da jaka na nan gefen gadonta na ajiye ku bar nan kuje garin neruji ku tsallaka ruwa zuwa kiyoje ku jirani anan,Ka tafi da sauri….
Kasan Juyawa Abaas din yayi yana kallan boukar din tamkar yanda Abaa dinsu yayi musu hakan ce yake sake faruwa Ayau din dan haka zaiyi musu boukar damqi hannunsa da karfi yace
‘Idan ban taho ba zuwa gobe to bana duniya Ka dauki Ayshaah Ka tafi da ita inda zata samu rayuwa me kyau ita amana ce gareka duniya da lahira,
Hakama idan ranar goben ta fadi ban bayyana gareku ba na ‘yantaka Nurat,
Ka zama gatan ‘yata ka zama gatanta da dukiyarta’
Cikin tsananin baqin ciki da radadin zuciya a Karan farko Abaas ya bude bakinsa Bayan shekaru ya furta
‘ABAAS GHAZ’
Kallansa boukar yayi da Wani irin yanayin karyewan zuciya batareda yaddarsa akansa ta girgiza ba ya bude baki idanuwansa na yin jajir yace
‘Abaas ghaz ina fatar Ka zamo gatan ‘yata da bata kariya da rayuwarka har karshen rayuwarta ko taka’
Tura Abaas din yayi da karfi zuwa cikin gida shikuma yana sake bude kofar fita daga bangarensu zuwa bangaren da hatsin zuwa da kuma zuwa kofar ficewa da tini suka shigo.
Da sauri Abaas ya juya yana jin zuciyarsa na yanka da Wani irin yanayin da yake sakasa jin kaman bazai iya tafiya yabar boukar ba amma kuma matiqar zasu bawa ayshahh kariya su tseratar da rayuwarta dole ya tafi.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
67
Kai tsaye dakinta ya isa da gudun gaske ya banka kofar bai tsaya komaiba ya dauki jakar da boukar yace ya miqa hannu ya damqi hannunta datake tsaye ta miqe cikin tsananin tsoro da fargaba.
Janta yayi da karfi suka fito tsakar gidan Wanda yake hayaqi da ci da wuta take ta riqe hannunsa da karfi cikin tsananin tsoro da tashin hankali tace
‘Meya ke faruwa,
Ina Abbu??
Baice mata komaiba ya jata da saurin suka bi ta kofar baya da babu Wanda ya sani sai iya su zasu fice ta qwace hannunta zata koma da gudu tana kwala kiran sunan mahaifinta.
Riqota Abaas din yayi da karfin gaske yana kokarin sake tafiya da ita ta fara fizgewa tana Ihun daya sakasa rufe mata baki da karfi yana kallanta cikin duhun hanyar ya sanar da ita abinda yake faruwa da kuma abinda mahaifinta ya ce akan zuwansu su jirasa.
Kasa iya barin mahaifinta tayi ta fara Wani irin kuka da rawar jiki tana kokarin kwacewa sbd tasan mahaifinta bazai tsiraba kashesa zasuyi batada kowa bazata iya rayuwa ba mahaifinta ba,bazata iya shiga duniyar da tasan bazata taba sake dawowa ba anan ko kabarin mahaifinta ta ziyarta ba dan haka gwara ta mutu a guri daya da mahaifinta.
Rufe mata baki gabaki daya Abaas yayi zuciyarsa na jin abinda take ji sbd shima ya shiga irin wannan mummunan yanayin harma nasa ya zarce nata nesa ba kusa ba dan haka daukanta yayi cak yabar gurin da ita yana sake rufe mata baki da duka karfinsa.
Gudu yakeyi da ita a cikin tsananin duhu da shukokin da sun kusa finsu tsayi dan haka cikinsu kawai yake jefa Kafafunsa da ko takarmi babu yanaji qayoyi manya da qananu suna sukarsa da abubuwa masu laifin da harma sun fasa kafafunsa jini suke fiddawa amma bai tsayaba gudun yakeyi sosai sbd yana jiyo hayaniyar biyosu da akai Wanda hakan ya tabbatar musu su duka biyun da boukar ya fadi.
Kuka Ayshaah takeyi sosai dukkinanin jikinta na sakewa a jikinsa tanajin duniyarta ta gama kifewa da lalacewa kenan har abada dan haka bazata taba dawowa daidaiba.
Shi Kansa jin yakeyi jikinsa na Neman mutuwa da wannan mummunan baqin cikin na rasa Wanda yakeda mahimmanci a rayuwarsa datake a rube Bayan rasa iyaye da yan uwansa amma ganin a yanzu shine gatan ayshahh da kuma zai samu yancin zuwa Neman yan uwansa da sune kadai rayuwarsa ya saka yake sake tattaro karfinsa yana cigaba da Wani irin gudun da kafafunsa ke fidda jini sosai amma bai tsayaba dan basu tsira ba.
Gudu sukeyi har kusan asuba hakama karfinsa ya kare daqyar yake iya daga kafa sbd galabaita da jininsa daya fara qasa da kuma wata irin azababbiyar ciwon kirji amma hakanan yake dagewa yana daga kafa.
Koda suka isa wani garin dayake daga shi sai inda boukar din tace suje anan suka samu suka tsare wa wainda suka biyosu amma duk da hakan bai tsayaba dauketa kawai yayi ya Kama hannunta tamkar wadda bata gani haka ya ringa Janta ba karfi a jikinta ko kadan.
Tafiya me tsayi suka kuma yi kafin suka isa garin dayake bakin ruwan da zasu tsallaka Anan dinma basu tsaya ba cikin wata gona suka boye yayi sallah a galabaice kafin suka fada jirgi suka bar nahiyar kwata kwata.
Tafiyar wuni guda sukai kafin suka isa inda zasu din suka fito jirgin tareda barin bodar bakin ruwan wadda sai anan ne Abaas ya gane garin da aka siyosa ne dan haka ya sake riqe hannunta gam suna kutsa mutane suna shiga cikin garin sosai Wanda yake a cike tamkar kasuwa koina hidima akeyi.
Wani qaramin gidan baqi da yan gudun hijira ya isa dasu suka zauna Bayan ya tsaya a hanya ya siya mata gasashiyar fulawa da zuma.
Suna Zaunawa ta cusa kanta cikin kafafunta tareda qanqame jikinta tana fasa wani irin kuka mai tsima zuciya koina na jikinta na jijjiga da tsananin quncin da batasan haka radadi da zafinsa yake ba.
Shiru Abaas yayi a gefenta idanuwansa jajir yana Kurawa ruwan dake mamaye da bakin bodar ido zuciyarsa na yanka shima sbd anan ne aka rabasa da tasa rayuwar,
Anan ne ya rabu da wainda suke rayuwarsa,
Anan ne komai na rayuwarsa ya qarasa Juyawa harzuwa matakin dayake yau akai na rayuwa da bulayi cikin duniya shi kadai babu kowa acikinta.
Radadin azaba me tsanani kafafunsa keyi Wanda ya ke sakar masa da zazzabi me Zafi amma bai damuba shiru yayi ido jajir Akan ruwan.
Kuka tayi Wanda saida ya qarasa cinye karfinta kafin tayi shiru tana Kurawa hanyar ido itama batareda ta iya cin abinda ya bata dinba.
A gurin suka kwana Zaune cikin mummunan halin daya tsananta yanayinsa dama nata datake wata rawar sanyi dan haka ya cire rigar jikinsa ya rufa mata Akan nata Kayan da babu ko kallabi a kanta gashinta a bude yake a sake sbd yanayin da suka fito.
Koda gari ya waye daqyar sukai sallah a gurin suka tashi Zaune suna sake gadin hanyar da duk masu isowa,
Duk yanda yayi da ita taci Wani abin qi tayi gashi tayi Laushi sosai ta fita hayyacinta kawai mahaifinta take son ganin ya taho din.
Haka suka wuni har rana ta Kuma faduwa babu boukar ba labarinsa,
Zuwa lokacin dagashi har ita daqyar suke Numfashi dan haka Akan dole sukaci abinci sbd suna Neman karfin cigaba da jiransa har ranar daya taho.
Wani wunin suka kuma yi ba labarinsa haka suka kuma kwana,
Ahankali ahankali kwanakin suka ringa tafiya ba boukar ba labarinsa su kuma sun kasa cire tsammani dan haka basu iya tafiya koina ba haka su kaita zaman jira a bakin bodar wadda tin baa Ankara dasu ba har aka fara ankarewa dasu Ana musu kallan mata da miji marasa hankali sbd yunwa da wahalar data Kama jikinsu take fara bayyana dan kuwa basa Wani iya cin abinci suna cikin tsananin damuwa da baqin ciki tareda rashin sanin inda zasu.
Ganin an fara saka musu ido ya saka suna cika sati shida a gurin Abaas ya tattarata suka bar qasar sbd Wani jirgin na tahowa Wanda zaiyi gaba binsa sukai sbd a yanzu tafiya Neman yan uwansa zai tafi dan haka a qasar datake gaban wannan zai fara tinda daga nan gaba akai dasu Ayanaah.
Tafiya sukai ta kwanaki a jirgin kafin suka isa qasar dake gaban wadda suka Baro,
Isarsu qasar dole anan bakin boda ya samu aikin wahala Wanda zaa ringa biyansa dan yana buqatar kudin dazai nema yan uwansa bazai taba dukiyar Ayshaah ba a gurin nemansu,
Gida suka samu Wanda ake biyan hayar daki daya ya biya hayar ya saka ayshan a ciki shi kuma yana kwana a kofar dakin.
Rayuwa a qasar qunci tafara yi musu sbd yanda ake qyamarsa ganinsa namiji da Kayan maza amma yan kunnen mata ne a kunnensa wainda ya kasa cirewa sbd Ayanah ce ta saka masa su da hannunta bazai iya cirewaba.
Ita kanta ayshahh tsangwamarta mutane suka fara yi sbd tana tareda shi babu aure a tsakaninsu dan haka rayuwa tayi mata qunci da nauyi bata cikin kowace irin walwala bare farin ciki dan haka suka bar garin suka koma can quryar qasar Wani garin suka fara rayuwa shima ahankali ahankali zaman yakasa dadi sbd qabilanci na qasar sam basason baqi dan haka dole suka tattara suka sake sauya guri Wanda duk inda sukaje kaman mahaukaci haka Abaas ke Neman yan uwansa.
Shekara kusan guda da rabi sukai a qasar suka barta gabaki daya zuwa qasa ta gaba Wanda itama aikin wahalar gaske yakeyi wanda yake cin lafiyarsa sosai sbd duk wannan lokacin aikin wahalar gaske yake a rayuwarsa dan rufa musu asiri kuma har lokacin dukiyarta na nan wadda tace ta basa halak malak amma ya kasa tabawa sbd yanason ya Nemi inda zai ajiyeta dan bata rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwa amma abin ya gagara.
Ahankali suka fara Gagarin rayuwa a qasashe gurin Neman su Ayanah Wanda zuwa yanzu rayuwarsa ta qarasa macewa gabaki daya sbd ciwon wahala da azabar rayuwa da qunci da suka taru suka rufar masa dan haka ya samu qasa me dan nutsuwa yace zai siya mata gida y ajiyeta tayi rayuwarta ta huta da binsa gararin duniya kada ta qare rayuwarta kamar tasa ta mutu a banza.
Kasa yadda da hakan Ayshaah tayi sbd bazata taba iya rayuwa ita kadai babu sa ba sbd a yanzu shine t Rabin jikinta rayuwarta,
Shine kadai hasken dayake rayuwarta shi kadaine Wanda rayuwarta take dashi dan haka ta shirya mutuwa a gurin Gagarin duniya tareda shi,
Ta shirya rayuwa da mutuwa tareda shi ko an inane ko awa ce qasane zata iya zama dashi.
Da wannan suka fada qasar BOYEM Wanda Sam babu ta yanda zaa barsu su shigeta kusan watan su uku anan babu damar shiga qasar dan haka suka juya suka bar qasar.
A border ta farko da baa shiga qasar BOYEM aka daura musu aure sbd hanasu gurin zama da akai koina garin sbd basada aure dan haka suka daura aure Wanda har cikin zuciya da ransu suna tsananin son junansu hakama sun shirya rayuwa da mutuwa a tare,
Aurensu ne ya kawo wata yar nutsuwar rayuwa a rayuwarsu data cikin tsananin duhu da qunci tareda kadaici,
Kusanci da sabuwar shaquwa da kauna tareda so me tsananin gaske sukewa juna suna sake Jin karfin gwiwan fuskantar rayuwa.
Bayan wata uku suka bar BOYEM sakamakon cikin daya bayyana a jikin Ayshaah,
Cikin ya taho mata da rashin lafiya sosai dan haka tafara wata irin rama taba kofewa alaman jininta yana yin qasa dan haka Abaas ya sadaukar da rayuwarsa da kudirin sa dan bata nutsuwan rayuwan daya kamata kodan abinda zasu haifa kafa suyita yawon duniya dashi dan haka suka juya inda suka fito,
Shima kirgen garuruwan da suka Baro a baya tsawon shekaru lokacin da aka dauko su daga garinsu ya fara yi dan komawa qasar sa garinsa gidansu da iyalinsa sbd matiqar Ayanah tana raye to tabbas yasan zata je nemansa a cikin duniya kokuma anan gidan mafarinsu dan haka zai jirata daga yanzu har ranar da Allah zai dauki rayuwarsa.
*****tafiyar watanni sukai nai cikeda wahala da ukuba da tsinkewan zuciya ga yanayin ayshahh kafin Allah ya iso dasu dajin garinsu daya sha matiqar wuyar gaske kafin ya gane hakama dukiyarsu tayi qasa dan haka Koda suka iso ANJOM GHAZ cikin Ayshaah ya tsufa yakai wata takwas.
A garin ANJOM babu mutane sosai sbd garin ya Riga ya mutu dan haka babu wata daula da tatttalin arziki kaman baya amma akwai kwanciyan hankali