haka suma suke fata da tsananin adduar NUAB ya zauna a masarautar sbd sun San babu ta yanda zaayi wishmah tabar Masarautar matiqar sultan nata rai a cikinta zata rayu sai koma idan sultan dinne ya fita da ita da kansa zuwa rayuwa Wani gurin.
Shirye shiryen tafiyar da akeyi hadda Maa tenya da sakinah akeyi sbd suma full nauyinsu yana kansa kaman yanda na Amminsa yake kansa dan haka shirye shiryen suke samu dan delay sbd tafiya ce ta kwata kwata zaiyi dasu su da BOYEM se labari.
Tinda Yazo qasar bai fita koina ba koyaushe yana tareda mahaifiyarsa dan bata lokacinsa kuma baida kowane irin business a qasar kuma baya shaawan kullawa dan haka sun cikin fadar hutu kawai sukeyi suna jiran komai ya hadu.
A hakan suka share sauti hudu Ana Sauran kwana biyu wata Dayan da aka yanke masa ta cika komai na tafiyarsu ya kammala tsaf Wanda ya sakasa jin wata irin nutsuwa da sanyin zuciyar cikar burin tafiya da Ammi,
Aleey ne yaje har fada shi da securities biyu suna biye dashi ya isarwa da kadir babban hadimin sultan dashi kadaine duniya yakeda sirrin komai na zuci da bayyane na sultan sakon LEUL BOYEM yana buqatar ganawa sa sultan ganawar uba da ‘da bata sultan sa magajinsa ba.
Kadir cikin girmamawa ya Karbi sakon da kunnuwa sa zuciyarsa ya isa gurin sultan daga gefensa ya dan ranqwafa cikin girmamawa daya sanar masa batareda duk Wanda yake fadar ba yaji sundaiyi tsit sbd ganin su aleey da securities din NUAB din sunsan sakon daga bangarensa ya taho.
Sultan daya gama sauraron sakon bai furta komai Wanda yanayinsa kadai kadir ya kalla ya gane me sultan din yake nufi dan haka ya juya ya koma
Inda suke ya isar musu da sakon cewa sarki zai ga LEUL BOYEM anjima Bayan sallar ishai a palon hutawarsa.
Da wannan sakon su aleey suka koma ya sanar da NUAB din Wanda yana Jin hakan ya ajiye wayar dake hannunsa gefensa yana nade hannuwansa biyu a kirji fararen idanuwansa na kafe a makekiyar flat screen din dake gabansa.
Da kansa ya sanar da mahaifiyarsa tafiyarsu a Washe gari insha Allah hakama su tenya,
Su tenya da sakina sanyi jikinsu yayi suka shiga zullumi da tinani Kala Kala zuciyarsu na rasa nutsuwa da sukuni sbd sanin hakan ba abune me yiyiwa ba batareda tashe tashin hankali ba da tsallake karfaffun sharudda daban daban dan haka a tsaye zukata da hankalinsu yake suna jiran abinda goben zata haifar idan har zasu samu barin masarautar kaman yanda NUAB ya kudirta da su kansu yanda suke so indai Zasuje suyi rayuwa da Ayanah da NUAB din sun shirya barin Masarautar BOYEM da basuda kowa a cikinta tinda ita kanta tenya yayanta duka basa nan suna gurare daban daban suna aurensu.
Tinda ya sanar dasu suke cikin zullumi da tashin hankalin da baya faduwa kuma baya nunawa musamman tenya data San aka samu matsala akasan dasu ake shirin barin masarautar da wishmah hakan zai iya zama bakin rayuwarsu dan haka suke a rashin nutsuwa da sukuni kwata kwata tareda jiran goben da zasu bar masarautar da qasar gabaki daya shikenan komai ya qare na tashin hankali da damuwa Ayanah zata rayu da ‘danta.
Ita kanta Ayanah din Wani irin rashin sukuni da zullumin goben takeyi sbd tabar nan tabi HAYATEEM duk inda yake rayuwa itama tayi rayuwar acan tareda shi da Abaas da shima yayi mata alkawarin a kwanakin nan zai fara Neman kawo mata shi.
Gabaki dayansu wunin a cikin zullumi me tsanani suke yinsa kaman yanda bangaren HAILE da yayanta suma suke cikin zullumin watan daya cika hakama manyan fada da suma suke cikin zullumin abinda zai iya faruwa a fada yanzu kuma dan suna ji a jikinsu duk Wanda yayi garajen kasa tsayawa ya duba kalaman sa da kyau zai iya rasa ransa batareda yakai qarshen labari ba dan haka su kawai ma barin NUAB da Yaransa suke so a masarautar ya koma inda ya fito masarautar bata buqatarsa hakama halayensa sun gama bayyanarda babuta yanda zaayi yayi mulkin qasa gabaki daya dan zai iya ringa bayyanarda tsiraicin jikinsa ga duniya ne Bayan yana matsayin sultan dan haka Sam babu ta inda zaa basa mulkin BOYEM.
Shi kansa Wani irin yanayi ne me Zafi da radadin kuruciyarsa dayake taso masa yakeji na haduwan da zaiyi da mutumin dayake matsayin ubansa amma yayi watsi dashi tinda qananun shekaru ya jefa sa duniyar da babu kowa da zai rayu dashi a cikinsa, ya kuma rabasa da mahaifiyarsa batareda tausayin halinda take ciki ba har tsawon shekaru….
Numfashi me dumi ya sauke mara sauti a lokacinda yake tsaye gaban mirror din dayake closet dinsa tukuna Kai tsaye ya wuce bathroom dan wanka,
Mintina ya dauka gurin wankan kafin ya fito daure da towel gashina na tsiyayar da ruwa a hankali.
Wani towel din ya saka a kansa qarami yana goge gashinsa dashi kafin ya iso gaban dresser ya tsaya.
Shirin mintin kusan talatin yayi kafin ya gama ya fito a lokacin 10 na dare tana gap da yi dan haka yana fitowa Kai tsaye bangaren sultan ya nufa cikin nutsuwa da Izzarsa.
Suna isa tin daga nesa masu tsaran kofar suka wangale masa kofar kansu a qasa cikeda girmawa suna masa Barka da zuwa da zallar ladabi.
Shima kadir dayake kofar a tsaye yana gadin isowansa dan tarbansa rissinawa yayi yana masa Barka da zuwa cikin girmamawa me girman gaske kafin ya basa hanya ya wuce shikuma yana gabansa dan yi masa iso har inda sultan yake Zaune cikin palon sa dayake hutawa na alfarma koina qamshinsa da sanyin ac ne ya kame ya riqe.
Su aleey a kofar suka tsaya dukkaninsu a natse sha hayaniya,
Palo biyu suka wuce kafin suka isa asalin palon dayake din yana Zaune cikin shigarsa ta hutawa tamkar ba dattijin daya manyanta sosai ba yana sanye da ash Riga da wando masu kauri da tsadan gaske da sukaiwa jikinsa kyau kwarjinsa ya cike gurin kaman yanda qamshinsa ya cike gurin.
Sako kan NUAB a cikin shigar datake kusan iri daya data sultan nasa qamshin a hankali yana gauraye gurin yana kokarin doke na sultan din sanyin nutsuwa a zuciya,
Dagowa sultan yayi yana Dora fararen idanuwansa akansa yana kallansa cikeda nutsuwa da kaunar da ba damar nunawa sbd wutar dayake gani a idanuwan NUAB din ta fushin da ba yanzu zai sauko ba shima baya buqatan ya sauko din yanzu harsai ya tirsasa karban abinda yakeson ya karba,
Kwarjini da nutsuwan kyan NUAB cike idanuwan sultan sukai kaman yanda nasa kwarjini yake kokarin shiga lafiyayyun idanuwan LEUL me BOYEM daya daukesu daga kallan mahaifin nasa yana isowa cikeda nutsuwa da izza tareda kamewa ya zauna a kujeran dake facing sultan din ya dago fararen idanunwansa ya kallesa yana yaqar wutar datake cin zuciyarsa ya bude Baki a taqaice da kamewa yace
‘Barka da wannan lokaci me BOYEM’
Numfashi me sanyi da dan murmushi sultan ya sake yana sake kafe idanuwansa Akan NUAB din Wanda shima dagowa yayi da idonsa masu razana maza ya bude Baki cikeda nasa mulkin da izaa yace
‘Barka da isowan magajin me boyem LEUL NUAB ALMAZZ,
Batareda bata lokaci ba menene dalilin son ganina??
Qarasa fada yayi yana komawa sultan dinsa sak cikeda ikon mulki ba wata sakin Fuska,
Shima NUAB din baida lokacin batawa a maganar ya dago ya kallesa Kai tsaye yace
‘Zan bar BOYEM a karo na biyu kuma wannan Karan tafiya ta har abada Wadda zanyita ne tareda mahaifiyata wadda banajin tanada Sauran amfani a masarautar…’
Qarasa maganar yayi yana dagowa ya zubawa sultan idanunwansa da suka bayyana da kyau fes Akan fuskar sultan din.
Cup din hot green tea din dayake hannunsa yana hayaqi sultan yayi yana jingina bayansa a natse hankali kwance kafin ya kalli NUAB din dakyau har lokacin hankalinsa kwance ba alamar ko mamaki a tattare dashi,
Bude bakinsa yayi da cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali yace
‘Nine datake a qarqashina zan sanar idan ma batada amfanin amma ba Kai da kake baqo ba a masarautar da rayuwarta ba……
Wani irin kallo NUAB yayi masa maganarsa na sukar zuciyarsa baice komaiba idanunwansa na dan sauyawa.
Cigaba da magana sultan yayi da cewa
‘NUAB ALMAZZ mahaifiyar Ayanah ghaz ta haramta gareka da kowa ma duniya Bayan ni daga ranar data zama wishmah ko yayanta basada iko da ita saini,
Wannan shine abinda Baka gama fahimta ba inaga,
Ayanah ghaz har abada kafarta bazata bar Masarautar BOYEM ba sai ranar da bana raye nabar duniya kenan to daga wannan lokacin ne zaka iya samun ikon mahaifiyarka amma Banda ina raye..
Wani irin motsi jijiyoyin NUAB din sukeyi suna fitowa idanuwansa kuwa ja suke rikidewa sunayi me tsananin gaske ya kafe idanuwansa akan sultan din Wanda yake magana hankali kwance,
Zafi jininsa yafara yi yana tafarfasa da maganar da sultan ke kokarin fada masa na cewa baida ikon mahaifiyarsa har sai ranar da sultan din yabar duniya Bayan shi bazai iya jiran hakan ba kome zai iyayi dan a basa mahaifiyarsa….
Bude Baki sultan yayi yana sake daukan cup dinsa yakai bakinsa ya dago ya kalli kadir dayake tsaye Wanda take ya juya ya dauko wasu takardu a cikin file biyu me kyau da tsari Yazo ya ajiye gaban NUAB kan table din gabansa ya juya ya koma gefe.
Sultan ne ya kalli files din kafin ya dago ya kalli NUAB din ya sake sakin nutsatsen murmushi me kyau yace
‘LEUL NUAB ALMAZZ me boyem kanada zabi guda biyu anan Wanda nasan zaka iya sbd mahaifiyarka,
Kallan files din NUAB yayi zuciyarsa na Wani irin tafarfasa da kaunar da har jikinsa ya nuna sbd Wani irin ja fuskarsa da hannuwansa sukeyi,
‘Zabi biyu ne a gabanka,
Na hannun dama takarda nada sabon sultan dazai mulki BOYEM ne datake dauke da sunanka kanta saka hannu a cikinta gobe zaa fitarwa da Masarauta da duniya ita a matsayin sabon sultan dazai fara mulki a gobe Wanda hakan zai Baka damar samun cikakken iko Akan mahaifiyarka harma da mahaifinka da baka buqata,
Ta hannun Hagun kuwa takarda ce da zata fita a gobe itama idan Ka saka mata hannu cewan har abada kabar BOYEM da mahaifiyarka harsai ranar da Allah ya dauki raina….
Zabi na gareka me BOYEM da Moscow.
Idan akwai abinda yafi tafarfasan jini shine yake faruwa da NUAB Wanda dukkanin jikinsa ke wata irin rawa koina nasa nayin ja idanuwansa na kafe Akan sultan Wanda shima shi din yake kalla zuciyarsa a shirye da karban duk zabin da NUAB din zaiyi a cikin biyun.
Yanda jikin NUAB din ke wata irin rawa da fizgar wutar dake ci a jini da kansa da kirjinsa ya saka yayi shiru batareda yace komaiba kuma bai dauke idanuwansa daga kan sultan dayake wa Wani irin kallan tsanar datafi duk wadda ya taba yi masa a baya ba ta yau din kokarin buga zuciyarsa takeyi dan miqewa yayi ya juya yabar palon idanuwansa kaman zasu fara feshin wuta sbd fushin da bai taba shigaba rayuwarsa.
Yana fitowa su aleey suka sha jinin jikinsu taje suka bi bayansa a qame batareda cewa komaiba.
NUAB na ficewa sultan shima take ya aika wa tenya sako a cikin Daren cewan Ayi sanarwar a Daren nan ya maida mata matsayinta na komawa zuwa kwana tiraka daga yau dinnan.
Sakon na isarwa tenya mummunan shock ta shiga Wanda y sakata mutuwar tsaye,
HAILE data fito a Daren itama cikin shirin zuwa tirakar kwana tama fitowa aka Dakatar da ita da sakon hakan Wanda ya sakata mutuwar tsaye kafafunta na kasa daukanta.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali_*HAYATEEM*_
Mamuhgee
58
Jiri me karfin gaske ne ya dibi HAILE wadda idanuwanta suke kokarin juyewa sbd dishi dishin da suke gani tsabar mummunan bugawan da kirjinta yayi tareda shock na babu tsammani,
Fetto ce tayi saurin riqeta cikeda tashin hankalin da baa saka masa rana ba itama dan kuwa kaman kunnuwansu basu ji musu da kyau
Dagowa fetto tayi ta kalli jakadiyar sakon wadda ke tsaye da bayi biyu a bayanta kansu a qasa cikeda girmamawa ta zuba musu ido bakinta na nauyin rasa ta inda zata fara jeho tambayar ta bude Baki a dan rikice tace
‘Maimaita sakon’
Cikin girmamawa bayin suka sake zubewa qasa Banda jakadiyar sakon data sauke kanta qasa cikin tsananin girmamawa ta sake maimaita sakon Wanda ya qarasa wargaza kuzarin HAILE ta Nemi zubewa jikin fetto kowace jijiyar jikinta jinin cikinta na katsewa kanta yayi nauyi sbd wata irin sarawa da yayi.
Cikin sauri da kokarin sirrinta yanayin Hailen fetto tace masu kawo sakon su wuce ita kuka Kama Hailen tayi suka juya tareda Sauran bayin dake bayansu kowa kafafunsa a nauyaye sbd jinin uwargidansu dake tafarfasa duniyar bangaren tana daukan zafi gabaki dayanta.
Suna isa Kai tsaye har bedroom dinta fetto ta kaita ta kwantar tareda fitowa take ta aika bangaren Aslam Akan a kira likita a turo sa queen haile na buqatarsa.
Aslam na samun sakon ta fito ta nufo bangaren mahaifiyar tata sbd ganin meya sameta kokuma idan Wani abin ne ya faru dan kuwa tasan tabarta da shirin tafiya gurin sultan.
Tana isowa ta tarar da ko magana Mamee din bata iya yi kirjinta ke tsananin ciwo da zafi sosai idanuwanta sunyi jajir ajiyan zuciya kawai takeyi me Zafi da karfi akai akai bakinta baya iya furta komai.
Kallan fetto Aslam din tayi ta tambayeta meya samu mameen
Bayanin komai fetto tayi mata Wanda ya saka Aslam din juyowa ta kalli mahaifiyarta itama idanuwanta na sauyawa zuciyarta tayi dum tama rasa abin fada sbd alamu na sake tabbatarda masifu da ranakun baqin cikinsu zasu bude su fara ne matiqar NUAB na nan dan kuwa dasu da bokayen su sun tabbatarda shine matsalar datake tsakaninsu da dukkanin Buri,nutsuwa,kwanciyan hankali da farin cikinsu da suke buqatar kawar wa matiqar suna son rayuwa da wainnan abubuwan.
Shekara sama da ashirin rabon sultan da Wishmarsa,
Ya rufe ya shafe babinta a rayuwarsa da shimfidarsa kaman yanda kowa da Masarautar suka rufe shafinta a cikin matan sultan,
Wace masifar ce take Neman kunno Kai da a cikin Daren nan wannan mummunan sakon zai bayyana?
Me sultan yake shirin yi na maida wishmah matsayinta a dare guda batareda tsammanin kowaba,
Tayaya macen da suke son ‘dan tawayen ‘danta ya tattarata ya tafi da ita ko su aika masa ita sama zaa ce an maida mata matsayinta dayake tabbatarwa duniya ita din cikakkiyar ikon da mallakar sultan ce.
Wani nauyi kirjinta ya ta jefar da wayarta a kujeran dake dakin tana fasa kiran likita ta bude Baki kaman zuciyarta zatai aman wuta tace
‘Yanayin Mamee baa buqatan likita baqin ciki ne da dacin zuciya zata dawo daidai zuwa anjima idan ta samu sassauci’
Tana gama fadar hakan a koma kan kujeran ta zauna tana dafe goshinta dayake mata nauyi sbd ciwon Kai da bacin ran dayake cinta,
Shiru sukai dukkaninsu kowa da yanda baqin cikinsa yake cin zuciya da kirjinsa,
Meryam da aka aikawa mameen ba lafiya Kai tsaye tana zuwa taji abinda ya faru shiru tayi batareda tace komaiba ta jiya ta koma sbd batada abin fada hakama karfinta da lafiyarta Neman qarewa sukeyi a gurin dawainiya sa dakon baqin ciki da ritirin zuciya kullum Wanda a yanzu kam ta fara gajiya gangar jikinta ta fara gazawa ga daukan wannan baqin cikin da baida ranar qarewa bata fatar ta mutu a cikinsa batareda ta dandana farin ciki da kwanciyan hankalin gidan aure da tara zuria ba.
******Tenya kuwa a tsaye take qyam kan kafafunta tinda wannan sakon ya iso mata Wanda kwakwalwan kanta itama ta kasa dauka sbd babu ta yanda zaayi ace Bayan shekaru masu yawa da yafe wishmah daga zuciya da shimfidarsa rana tsaka dare daya yace ya dawo da ita a Daren da suke kallan Daren karshe na rayuwarsu a masarautar,
A Daren da suke jiran gari ya waye masa su bar komai anan suje su shimfida sabuwar rayuwa,
Shin sultan ya San da shirin tafiyarsu ne a goben daya yanke wannan hukuncin daya girgiza zukatansu dama duk Wanda zaiji cikakkiyar sanarwar zuwa da safe,
A wane Hali NUAB zai tsinci wannan mummunan labarin ga kunnuwa da zuciyarsa sbd hakan da sultan yayi Baro Baro yana nuni da Hana cikar burin NUAB ne yayi ta hanya me sauki se karfi dan kuwa koda NUAB yake ‘danta Wanda yafi kusanci da ikonta Akan kowa zamtowanta wishmah din ubansa kuma maidata cikakken matsayinta ya kere kowace irin dama da ikon da ‘danta yake dashi akanta.
Zufa ne a tsiyayo mata ahankali yana gangarowa daga gefen goshinta ta zame ahankali ta zauna gefen sakinah datai mutuwar Zaune itama idanuwanta jajir dan kuwa matiqar wannan mummunan sakon ya isa kunnan NUAB wutar tsanar mahaifinsa datake ransa ce zata sake hauhawa sbd tafiya da mahaifiyarsa bazai taba yiyuwaba gashi a yanzu datake cikin tsananin shauqin danta matiqar ya tafi yabarta batareda ya cika mata alkawarin tafiya da itaba komai zai iya faruwa da ita dan haka akwai tashin hankali a cikin wannan lamarin daya sauka a dare daya tamkar saukar aradu.
Kasa isarwa da Ayanah sakon sukai dukkaninsu sbd basusan tayaya kwakwalwanta zata karbi sakon ba hakama basu saniba ko sakon ya isa kunnuwan NUAB shima basusan yaya zai amsa sakonba dan haka tamkar sakon mutuwa sakon ya zamewa kowane ba gangaren harda na maraki wadda itama daga sama taji sakon ya saukar mata kamar tsawa sbd ta Riga ta dauka ta sakawa zuciyarta sultan ya gama da wishmah kenan har karshen rayuwarta,
Ko HAILE da zuriarta sun dauka ya gama da ita ya rufe babinta har qarshen rayuwarsa Shiyasa komai Yazo musu a mummunan bazata da gigita.
Kowane bangare a cikin bangaren uku na matan nasa tsit ya dauka babu bangaren da ba a cikin dacin zuciya da mutuwar jiki me tsanani suke ba tareda fargaba dan kuwa abu ne dayazo babu shirinda zasu San yaya zasu tarbesa ba.
Dare sake nutsuwa yakeyi Wanda ya saka tenya da suke Zaune zasuyi kwanan Zaune miqewa tayi shirin kaiwa sultan ziyara dan isar da rokon alfarmar da zasu buqata.
Tareda bayi hudu ta isa bangaren sultan din ta isarwa da kadir roko da sassaucin da wishmah take nema daga sultan Akan zuwanta Ayau Yazo ba shiri sultan yayi mata Afuwan karbanta a gobe ba yau din ba sbd yanzu haka ta jima da bacci sbd yanayin jikinta.
Kadir bai jima sosai a ciki ba gurin isar da sakon ya fito da sakon rokonsu ya karbu Ayau sultan ya mata Afuwa zuwa goben ta dawo cikakkiyar macensa wishmah dinsa.
Da sanyin jiki tenya tayi godia da