sauketa matsayin ya kuma yiwa sultan yasar iyaka da ita wannan haka yake dan a yanzu duk abinda sultan yake nema a gareta saida izini da umarnin 'dan SULTAN LEUL NUAB wanda zamowansa sultan duka ya basa wannan ikon akan uwarsa da batada iko da yancin kanta a masarautar har yanzu,
Duka hakan ya sake tabbatuwa ne sbd ta kasance mahaifiyar Sarki me mulki a yanzu dan haka bazaayi ikonta a matsayin imebēti ko wishmah ba darajarta ta uwar boyem ce gabaki daya,
A yanzu itace uwa mafi daraja a kaf boyem sbd itace uwar me mulkin.
Bayan isowansu bangaren NUAB da aleey dake bayansa ne kadai suka shige palon sa na farko,
Tsayawa aleey yayi daga bayansa bayan ya zauna ya dan sassauta tareda tausasa sautinsa yace
'Sultan me murabus baya qasar baifi awanni hudu da dagawaba shi da Ammi wanda a lissafin dana dora tafiyar ina kyautata zaton Anjom zai tafi da ita wanda kuma hakan na nufin yasan komai akanta da 'yan uwanta a cikin video din Abaas......
Wani daci da radadin zuciya me zafin gaske ne ya ratso tin daga kansa zuwa zuciyarsa ya dago idanuwansa da har lokacin basu dawo daidai ba bacin rai na qarasa sauyasu yace
'Tayaya yasan da video din Abaas??
Dan sake sauke numfashi aleey yayi yace
'Shine ya wuni tareda ita jiyan a lokacinda take cikin halin sanin rasuwar har dare yana bangaren'
Kafe Aleey din yayi da idanuwansa yana kallo take aleey yayi qasa da nasa idanuwan sbd yasan yayi kuskuren rashin fada masa tin jiyan wanda shi kuwa yayi hakan ne sbd NUAB din bazai taba iya ganin kuka da dacin zuciyar mahaifiyarsa ba shi kuwa Sultan zai iya tsayawa ya hadiye kowane irin baqin cikinta da kukanta dan dole itama a wannan lokacin tana buqatan daya daga cikinsu biyun ko 'danta ko sultan din su kasance da ita.
Dauke idanuwansa yayi daga Aleey din yana miqewa tsaye yabar palon zuciyarsa na tafasa da abinda sultan din ya aikata dan yasan yana sane da babu me ikon mahaifiyarsa yanzu sai shi sbd haryanzu ita mallakar boyem ce tsawon shekarun bata taba samun yantawa ba daga kowa dayake da ikon yantata a yanzu kuwa Allah ya basa damar a hannunsa.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
103
Bahar ma yana ficewa daga dakin wani irin damuwa da takaici ne lokaci daya suka danne kirjinta sbd Maa sakinah zata gansa kenan,
Juyawa tayi daga bakin kofar ta isa gurin closet din dakin da wani irin sauri jikinta har rawa yakeyi sosai ta saka doguwar riga baa natse ba ta koma gaban mirror da sauri ta kashe dryer din ko busar da gashinta bataiba ta daure gashin a hakan ta saka mayafi me girma ta rufe kanta tazo ta zauna da sauri tana zaunawa Maa sakinah na shigowa dakin dan haka ta kasa dagowa gabaki daya.
Maa sakinah ma bata iya kallanta sosai ba ta qaraso tana janyo mata wani zancen batareda tayi mata maganar ganin NUAB din ba sbd jin qamshinsa a dakin ya tabbatar mata da daga dakin nata ya fita.
Ganin firar ba yi zatai ba sai kawai maa din ta sake miqewa ta fice tafiya aikin dayake gabanta,
Tana ficewa Bahar ta dago a sanyaye tareda sakin ajiyan zuciya me dumi tana jin takaicin rayuwar datake samun kanta a ciki da takaicin bayyanarsa a inda take dan kuwa nesancinsu shine alkhairi a gareta ita kam sbd bata buqatan bayyanarsa a koina na rayuwar datake yi a yanzu.
Kasa tashi ma tayi kwata kwata daga inda taken bare qarasa shirinta datai cikin tsantsar gaggawa,
Acan nasa bangaren kuwa yana shiga ciki wayarsa ya fidda a natse yana zaunawa kan sofa ya saka kiran Amminsa,
Qin shiga kiran yayi sbd wayarta dake kashe kwata kwata,
Magana yake tsananin son yayi da ita dan jin yaya tafiyar take hade da sultan wanda yakeda tabbaci tabbas sultan dinne yayi ikon tafiyar da Ammin batareda saninsa ba kuma batareda ya bari Ammin ta sanar dashi ba,
Sake kiran Ammin yakeyi idanuwansa a rufe da bacin ran tafiyar da sultan din yayi da ita amma har lokacin bata shiga,
Bayajin zai iya kiran sultan dan baima da tabbacin ko akwai numbernsa a cikin wayar dan haka ya jefar da wayar a gefensa yana 'dan rufe idanuwansa sbd sassauta bacin ransa ya kwantar da bayansa jikin sofa.
Maa sakinah aikinta ta ringa yi hankali kwance bama tareda tasan Zuhrah na cikin masarautar ba ta iso har dare suna daki ta gama shirin kwanciya tana zaune tana waya da tenya akan sun isa amma basu kai ga isa can cikin garin Anjom din ba sai washe gari zasu bar masaukinsu su isa tukuna.
Bahar ma tayi shirin kwanciyanta tana gefen maa din a zaune tana sauraron wayar datake yi tana jin inama itace taje anjom din koma inama ace da itane aka tafi,
Maa sakinah na ajiye wayar ta kalleta tace
'Maa zasu dawo yaushe ne?
Zamu tafi muma wata ran amma ko?
Murmushi Maa tayi me sanyi tana ajiye wayarta a gefe zatai magana aka kwankwasa kofar dakin ta juya tana kallan kofar sbd badada wanda zai iya zuwa gurinsu a yanzu din.
NUAB ne inaga' Maa ta fada tana miqewa tsaye ta nufi kofar sbd harsun dan rufe da key daga ciki,
Tana nufar kofar Bahar ta miqe tana kokarin barin gurin zata nufi bathroom ta shige har sai yabar dakin tukuna,
Sakinah data lura da kaman NUAB din bahar zata gudarwa murmushi tayi tana qarasa isa kofar ta bude kai tsaye murmushinta na qaruwa sedai kuma wanda ta gani bakin kofar dakin ne ya saka komai nata da yawun bakinta tareda bugun zuciyarta tsayawa cak idanuwanta na tsayuwa qyam da wani irin hawayen dake cikosu hannuwanta da kafafunta na nauyi da sanyin da suke kokarin kasa daukanta ta bude baki da qyar ta iya lalabo kalman 'ZUHRAH' ta fada cikeda tsananin mamaki da shock.
Bahar ma da sunan ya sauka kunnuwanta tsayawa tayi cak daga inda take zuciyarta na wani irin muguwan bugawa tareda sarawan kai,
Kasa juyowa tayi saida Maa sakinah ta sake maimaita kalman sunan zuhrah din wadda itama take a kafe bakin kofar ta kasa motsawa idanuwanta jajir da wasu irin hawayen da rabon data fiddosu tin ranar da aka rabata da ayanah da sakinah din,
Sakinah take kalla wadda itama ita din take kalla tana sake jin gabaki daya jikinta yana mutuwa duk da sunsan zuhrah na raye amma sun cire rai daga sake haduwa da ita,
Akan Bahar data jiyo a sanyaye da mutuwan jiki zuhrah take maida idanuwanta da hawayen ciki suka gangaro daga saukan idanuwanta akan 'yar Abaas dinta jininta rabin jikinta..
Takawa tayi ahankali jikinta na tsananta mutuwa me tsanani ta isa gaban Bahar din leylah na biyeda ita cikeda mamakin dayake sakata jin kishin Bahar na tsanantar mata,
Tana isa tsayawa tayi tana kallan Bahar din da dukkanin idanuwa da nutsuwa da imaninta kafin takai hannunta dake rawa ta kamo hannun bahar din ta dago ta zubawa numbarn Abaas dake hannunta ido wani irin kuka me tsananin zafi da tsimin gaske ya taho mata ta rungume Bahar din da karfi cikin jikinta tana qanqameta tsamtsam a jikinta tana cewa
'Wannan jinin Abaas dinmu ce'
Ke jinin ghaz ce,
Kece ayanar da Abaas yakeda burin haifowa ayanah ghaz,
Ke jininmu ce,
Ina Abaas?
Ina Abaas???
Tambayarta ta karshe ce ta saka Bahar sauke numfshi me zafi a jikin zuhrah din tana rintse idanuwanta da sukai jajir kuka ma ya kasa fitowa a cikinsu,
Sakinah datake a tsaye jiki a mace qarasowa tayi gabansu tana kasa dauke kallanta daga zuhrah wadda ta saki bahar ta juyo gurin sakinar ta rungumeta da karfi cikin tsananin kewan shekaru da kauna me karfin gaske sbd sakinah ta jima da zama jininsu.
Leylah kasa motsawa tayi ganin abinda yake faruwa tsakanin mutane biyu da bataso da mahaifiyarta dan kuwa sam bata kaunar maa sakinah sbd yanda take bayyana kaunar bahar fiyeda kowa a bayyane.
Bahar komawa gefe tayi ta rabe tana kasa cewa komai kanta a qasa,
Bahar din ce ta fara silalewa ta fice daga dakin kafin leylah ma fito cikeda zullumi sbd alamu suna nuna mata alaqa ce me karfin gaske a tsakanin mum dinta dasu ayanah ghaz wadda sunansu yaxo daya.
Zaunawa sukai hannuwan zuhrah na qanqame dana sakinah tana kukan rabonta dasu a rayuwarta da itama har wannan lokacin bata samu cikakken yancin da zata taho da yar uwarta ba sbd doka da yancin da Ayanah bata dashi tsawon shekarun,
Basu taba neman juna ba sbd zazzafar dokar data rabasu suke akanta,
Sakinah ce take kukan farin cikin daya gama kashe mata jiki ta fara bawa zuhrah labarin halinda ake ciki na rasuwan Abaas da tafiyar ayanah zuwa gida jikinta a mace da damuwa,
Kuka sosai zuhrah takeyi jikinta na rawa sosai ta qanqame hannuwan sakinah tana jijjiga da tashin hankali da baqin ciki tareda damuwa da tausayin kansu me tsanani sbd a yanzu su biyu kadai suka rage a jikin ghaz sai Bahar.
Tsawon lokaci suka dauka sosai har tsakar dare basu fitoba sai daga baya shima zuhrah kai tsayace tace anan zata kwana tareda bahar.
Leylah datake neman sake rikicewa a rudani zaunar da ita Zuhrah tayi ta fayyace mata komai wanda ya sakata shiga tashin hankali da farin ciki harma da baqin ciki duka a lokaci daya,
Farin cikinta jin yanda matsayinta yake a gurin Ayanah ghaz da NUAB wanda dole take da a kaunaceta kauna me karfi harma fiyeda bahar sbd ita ana ganin idon mahaifiyarta,
Baqin cikinta kuwa shine kasancewan bahar ce jinin abaas ba ita ba sbd kusanci da kaunar dake tsakaninsa da ayanah kenan yafi yawa akan wanda yake tsakanin mahaifiyarta da Ayanaah ghaz wanda shima bazata yadda ba bazata iya hakura ba kome zai faru ita tana son NUAB kuma tana son kasancewa matarsa sbd itace ta dace dashi ita datai karatu me zurfi ta waye ta taso cikin daula da arziki kamarsa,
Tashin hankalin data shiga da tsoro me tsananin gaske kuwa na jin tarihin da ko amafarki bata fatan ya sameta dan kuwa batajin har abada ma zata iya rayuwa a inda baa cikin daula irin boyem ba.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
104
A bangaren wishmah din zuhrah ta kwana tareda bahar itama batareda ta rintse ba tin daga farkon daren har qarshensa sbd rasuwan Abaas tayi mata irin jijjigar dataiwa Ayanah dan haka itama gari na wayewa ta koma ta sanar da Mai girma yunar tana son zuwa asalin qasarta wadda a yanzu ta samu wanda ya san inda qasar take tinda a baya itama nata 'dan yayi kokarinsa bai samar da inda take ba,
Baiyi mata musu ba ya bata damar tafiya tareda cikakkiyar iko itada shuraim da Leylah,
Maa sakinah ce ta kira NUAB ta sanar masa zuwan Zuhrah a garesu wanda shima yayi shock da jin hakan duk da alkawarine da yayi na hadasu itada Amminsa amma tinda tazo shi kuma zai isar da ita Anjom su hadu a asalin qasarsu cikin gidansu inda iyayensu da dan uwansu suke a kwance nurat ce kadai babu a cikinsu yanxu wadda sukewa fatar rahama.
Ko da ya iso bangaren Bahar na jin qamshinsa ta silale tin bai shigowaba ta koma dakin maa sakinah tai kwanciyanta bata fitoba ba har saida ya gama abinda yakeyi ya fita cikeda samun nutsuwan mahaifiyarsa zata kasance da yar uwarta a yanzu.
Aleey ne ya fara musu shirin tafiya anjom din su uku Mum zuhrah,shuraim da leylah sai securities biyar da zaa hadasu dasu,
Leylah jin bada NUAB din zaa tafi ba hakama bada bahar ba sai taji kwata kwata batason tafiyar hakama ita tsoro ne me tsananin gaske a ranta na ziyartar garin sbd ganin takeyi kaman zaa iya sacesu a lula wata qasar dasu a siyar kaddararsu ta sauya sbd suka su mum din ai sunada daula da sarauta aka sacesu.
Shuraim daya lura da yanayinta ne ya dan kwantar mata da hankali sbd zuwan nasu yanada mahimmanci tinda shiga takeson samu da damar da zata auri namijin dayake zuciyarta,
Basusan yariga da ya auri bahar ba dan haka sunada tabbacin zai auri leylah din koda ma ya auri bahar dinne ai ya kasance itama zata iya shiga,
Shuraim baida mugun hali ko daya halayensa daban suke dana yar uwar tasa sedai shikuma ya fita tsananin kishi da tsananin so sbd yanda yake kaunarta da mum dinsu komai yana iya yi akansu hakama kowa yana iya batawa akansu shi haka tasa kaunar da halin yake sam akansu baya duba daidai da abinda ba daidaiba amma bayan wanna baida munin dabia da hali ko daya hakama shima yayi kararu sosai me zurfi fiyema da leylah din sbd a yanzu yana akan matsayin cikakken likita ne.
Kafin su tafi irin kaunar da zuhrah kewa Bahar itama yasake gigita zaman lafiyar zuciyar leylah duk da tasan kowane irin so mum dinta zataiwa bahar bazai taba wuce wanda take mata ba ita data haifa amma sam bata jin zuciyarta daidai akan irin kaunar da dukansu suke mata musamman ta Ayanah datafi komai gigita mata zuciya sbd a bayyane yake ayanah zata iya bada rayuwarta akan bahar din.
Suna wucewa shima NUAB ya shiga wani irin busy na harkar sarautar boyem din daya buqaci dukkanin dokoki da sharudda da kaidojin mulkin msarautar boyem din masu zafi a gabatar masa dasu kaf da tarihinsu da inda suka samo asali da kuma hukunce hukuncensu sbd yana son shafesu kaf ya budewa boyem sabon tsarin mulkin da zai tabbatar musu da shine LEUL BOYEM yake mulki hakama har abada wainda zasuyi mulki bayansa zasu samu yancin da sarakunan baya da kamanninsu basu samu ba,
Manyan fada cikin tashin hankali da tsaka me wuyar wannan tsari da bayanan daya buqata wainda zasu zaqulo asalin asalin boyem suka fara shirye shiryen wannan umarnin nasa da allah kadai yasan waye da waye zasu rasa matsayi da sunansu da zuriarsu har abada.
Aleey ma kusan yafi kowa zama busy sbd shine zai tabbatarda hada kowane bayani da tabbatarda gaskiyarsa da komai tareda fidda duk wani hukunci akan hakan da sultan LEUL boyem zai fitar tareda sabbin dokokin mulkin qasar wainda gabaki daya boyem da duniyarta suke jira cikin zullumi da fargaba da jiran tsammani.
Bahar ma da maa sakinah hankalinsu kwantawa yayi basa cikin damuwan komai allah ya sakowa bahar din dangana da samun nutsuwa sbd koba komai ta hadu da jinin Abaa dinta biyu da suka rage a duniya da kuma yake fatar ta hadu dasu tayi rayuwa a cikinsu sbd yasan ko da rayuwarsu zasu bata kariya da duka kaunar datake nema da gata a duniya.
Maa sakinah ma sakewanta tayi tana cigaba da kulawa Bahar tareda tattalinta da gyara abarta sbd yanda itama bahar din ta gashi hankalinta ya kwanta bata ganin NUAB sbd bai sake shigowa tin ranar dan busy din dayayi sosai bai nemeta ba kaman yanda itama ta tattarasa ta ajiye gefe.
Babu abinda Maa sakinah take so a yanzu bayan samar da ilimin boko me kyau da zurfi ga bahar amman batada daman fadar hakan dan haka ta tsaya a iya koya mata dan abubuwan data sani wayewa da sauransu duk da nutsuwa da wata irin kamun kai da izzar dake cikin jininta ta sarautar data gada ya saka baka iya gane batada irin wayewan da zurfin ilimin boko yake bayarwa.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
105
Acan boyem kuwa tinda su Ayanah suka isa gabaki daya rayuwarta ta dawo mata baya farko,
Tayi kuka, tayi baqin ciki, tayi inama baya ta dawo, tayi baqin cikin ganin wannan ranar data wayi gari ita daya batareda kowa nata ba a cikin jinin ghaz sedai yayansu,
A kabarin da akaiwa iyayensu daga baya a cikin masarautar ghaz din da kabarin abaas dayake jere dana iyayen nasu ta durkusa tayi musu addua me tsayi tana wani irin kukan daya saka sultan janyeta suka bar gurin,
Jamaar anjom tsoffinsu da sukasanta tin a baya wainda allah yayi suna raye dama wainda basu santa ba sunyi farin ciki me tsananin gaske na ganinta,
Sun taru sunyi jimami sun cika masarautar sun mata gaisuwan iyayenta da abaas tareda kokawa juna kaddararsu data raba kowace ahalin datake anjom babu gidan da bai samu mummunan kaddarar shekarun bayan ba na iftilain daya fadowa anjom din.
Har tsakiyar dare sosai suna garin sai da sukai asuba tareda jamaar garin suna kokarin bankwana su tafi Su zuhrah suka iso.
Isowan zuhrah ya saka sultan barin Ayanaah a garin ya koma jirgi dan kuwa suna buqatan lokaci me tsayin gaske a cikin gidan da shine asalinsu shine abu na karshe daya rage musu na ahali da asalinsu.
Ayanah a lokacinda ta hada idanuwanta da zuhrah bayan shekaru masu tsayi na rayuwarta kasa motsi tayi bare cewa komai hakama kukanta daukewa yayi tsaf sai ajiyan zuciya kadai ta iya ringa saukewa tana bin zuhrahn da kallo ita kuwa kuka takeyi me tsananin gaske tana kasa fuskantar ayanah daga qarshe zubewa tayi a kan kafafunta tana kama kafafunta tana kuka me tsanani.
Tsawon lokaci ayanah din bata motsa ba tana jin kukan yana ratsata kafin ta motsa a hankali ta kama zuhrah din ta miqar da ita tsaye ta rungumeta ahankali jikinta a matiqar sanyaye ta bude baki da sautin daya sake saka zuhrah mummunan yanayi tace
'Yene Zuhrah,
Daga karshe kin dawo gareni Zuhrah,
Allah ya bamu ikon qarasa rayuwarmu a cikin ta juna a tare tareda 'yayanmu'
Rungumeta zuhrah tayi itama da karfin gaske suna qanqame juna da tsananin karfi zuciyarsu na samuwa da cike gurbinda har abada insha Allah ya cike kenan.
Kabarin iyayensu da dan uwansu suka koma kafin suka sake komawa dakin mahaifiyarsu anan suka shige dan anan zasu sake kwana kafin su koma asalin birnin qasar inda sultan yake jiran Ayanah a lafiyayyar daular daya sauka.
A nan anjom suka kwana wanda kafin safe leylah ta kusa zarewa ta rasa hankalinta sbd mummunan halinda takejin tana cikinsa na rayuwa a garin dama inda suke din dan kuwa a maqale da mahaifiyarta take sam ta fice hayyacinta.
Babu wanda ya maida hankalinsa akanta a cikin su biyun sbd abinda yake kansu shine ya damesu,
Fuskokinsu da idanuwansu kadai zaka kalla kasan suna cikin mugun hali sbd sun kumbura sunyi jajir ba kyan gani hakama ko muryoyinsu basa fita.
Daqyar leylah taga gari ya waye karfe tara tayi anzo daukansu da securities din sultan da wasu mahaukatan motocin da suke iya shiga kowane daji da bindigogi.
Ta riga su Ayanaah fitowa ta fada mota da sauri tana sauke ajiyan zuciya ta kalli Shuraim dayake gaba dan shima bai kwana anan ba komawa yayi yau aka dawo dashi,
Cikin wani irin yanayin dayake fitowa daga