Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   5 / 100

12K to 15K   out of 299.8K words

duniya babu tausayi ko Imani ko kadan,
Ganinsu ko mafarki mummunan tashin hankali da tsoro ne sbd Al’adarsu ma da kadai yanayin shigarsu da wasu irin hudan kunnuwa dana hanci dake tattare dasu ga gashinsu da basa Daurewa a sake yake ga wainda basada gashina kuwa wani irin kitso ne me tsoro ga zane a jikinsu da shima alama ce ta kusrawa ga kowace kusra.

Asamah ce ta bude hannuwanta tana karesu dan basu kariya itama jikinta koina rawa yakeyi tana jin wani iri kaman haukacewa zatai sbd yanda zuciyarta da kirjinta ke tsananin nutso a cikin qunci da tabarbarewan rayuwa data samu kanta na halin data saka rayukan da basu adadi tareda maida yara sama da daruruwa marayu,
Tareda saka mata sama da daruruwa rasa mazajensu zasu zamo bayi,
Yaya da iyaye sama da daruruwa sun rabu babu ranar haduwa har abada sbd kowa da inda ya gudu da kuma inda zaa siyar dashi.

Juyawa kanta yaci gaba da yi zuciyarta da kwakwalwanta na sake kasa dauka idanuwanta na rage gani sbd haqqin ran daruruwan mutanen dake kanta,

Rintse idanuwanta tayi tana sake ganin duhu kanta na Juyawa sosai amma har lokacin karesu takeyi da hannuwanta,

Jin kaman zuciyarta na Neman bugawa ta juyo tsoronta da tsananin tausayinta akansu na qaruwa sbd sun riga sun rasa yanci da gata harma da asalinsu tareda rayuwansu batareda sun San yaya duniyar take ba a wajen gidansu,a kuma wajen garinsu,a Bayan ran iyayensu,
Basusan yaya zasu gudanar da rayuwarda babu iyayensu a cikinta ba koda iyayensu na raye bare yanxu da basa duniyar,

Ko a darasin ilimin rayuwa da iyayensu ke musu tareda tarihi da labarun rayuwar dake gudana a duniya wadda baa cikin ANJOM ba baa taba fada musu menene asalin zamowa bawa ba da ukubar dake cikin bauta wadda bakasan karshentaba ko Ka samu yanci wata rana kokuma Ka mutu a cikinta.

Wani irin Jan rikitarwa idanuwanta suka tana saka hannunta daya a kirjinta tana dafewa Ahankali ta kalli Ayanah tareda bude bakinta ahankali ta Ambaci sunanta kafin ta maida idanuwanta Akan Abaas datafi shaquwa dashi tareda tsananin kauna a tsakaninsu me karfin gaske ta qura masa ido wasu irin hawaye masu tsananin ciwo na gangaro mata ta sunkuyar da kanta qasa tana jin rayuwarta kwata kwata bata da sauran amfani.

Dagowa tayi ta kalli kusrawan da sukayo kansu kowannesu na zaro mummunar wuqar da zata yanka Mutum a qanqanin daqiqu fit ta rabaka da ranka.

Lumshe idanuwa Ayanah tayi suna sake rungume junansu dukkaninsu suna samun nutsuwa da saukin a rabasu da ransu su bi iyayensu yafi musu saukin rayuwan da basusan yaya ake gudanar da itaba,
Rayuwar da babu tabbacin ko zasu take ko wahala da gagari zasu yi karshe su mutu a cikin garari dan haka gwara tin a qasar garinsu batareda sun bar garin da gawar iyayensu take ba subar duniyar.

Abaas dayansu ya fizgo da karfin gaske yana Dora wuqa mai tsananin kaifi da wani mummunan fadi a wuyansa zai fizge jijiyar wuyansa da wuqar
Asamah ce da idanuwanta ke cikowa da hawaye masu radadin gaske ta bude baki jikinta na saki tace

‘Inada damar alfarma guda daya tak da khams ya bani a matsayin abinda zaa biyani dashi kuma dukkaninku kun San da hakan’

Cikin rashin Imani Wanda yake riqe da wuqar a wuyan Abaas yace

‘Damarki guda daya ce tak kina fadarta shikenan kin rasa kowace irin dama……

Katsesa tayi muryanta na sake raunana da cewa

‘Kar a kashe ko dayansu shine abu daya tak danake so……

Dukkanin kusra dariya me karfi suna kece da ita kafin babban cikinsu ya kalleta cikin tinatar da ita babban gangancin da zatai wa rayuwarta sbd Ana cika mata wannan buqatar ita rasa nata ran zatai yace

‘Kina sane a dama daya tak da aka baki zaki iya zabar abarki da rayuwarki kitafi duk inda zaki ki Gina sabuwar rayuwa?
Kina sane da hakan?
Sannan Kina sane da idan kika zabi rayuwarsu ke bazaki rayu ba???

Gangarowa hawayen cikin idanuwanta da sukai jajir sukai ta juya sake kallansu babu Wanda jikinsa baya kakkarwa cikin wani irin mummunan halin daya saka zuciyarta sake nauyi,

Abaas ta zubawa idanuwanta idanuwansa na rufe yana jiran barin duniyar kafin ta dawo da idanuwanta Akan Ayanah dake kallanta cikin yanayin da suka fi buqatan mutuwan Akan rayuwar

Zuhrah ce ta iya bude baki da tsananin kuka me ratsa zuciya tace

‘Asamah mun zabi bin iyayenmu dan Allah karki zabi barin mu kema sbd kece wadda a yanzu muke kallan zaki zame mana ido a wannan rayuwar da muke makafi bamusan komaiba dan haka munfi tsananin buqatan komawa ga mahaliccinmu kaman iyayenmu……

Ayanah data kasa magana sbd tsananin shidewan datake sbd tsananin tashin hankali da kukan da hawaye basa fita a cikin dare daya da wuni hawayenta sun kafe kallan Asaman takeyi tana girgiza kai dukkanin jikinta na rawar da bata hayyaci bace.

Rintse idanuwa Asamah tayi ahankali tana bude su Akan su duka tace

‘Allah zai zama gatanku,
Allah zai Baku kariya,
Allah zai kawo ido da haske a rayuwarku kudai ku jajirce karku rabu duk tsanani ku kasance bangon juna’

Maida kallanta tayi kan kusran ta basa amsarsa da cewa

‘Na zabi rayuwansu Akan tawa a cika mun damar da aka ban ta hanyar barinsu da rayuwansu harsai lokacin da ubangijin daya halitta musu ita zai karba da kansa…

Ayanah ce tayi saurin yunqurowa da rarrafe mai sauri ga Asaman tana miqa hannu zata riqeta sbd suna tsananin buqatanta a yanzu……..

Jinin daya fesu a fuskanta da hannunta data miqa ne yawa na Asamah ya sakata sanqamewa a gurin tana dauke wuta hannunata na kakkarwa me tsanani.

Wuqar da kawai aka fizge fatar wuyan tareda jijiyan Asamah kaman wucewan iska Wanda ya saka jinin bartsi sosai ta kalla a hannun Wanda yayi aikin batareda bata lokacin su ba sbd zabinta ne.

Wurgar da Abaas sukai a gaban yan uwansa da gawar Asamah dake gangaro da jini,

Mutuwan Zaune dukkaninsu sukai tareda dauke wuta sbd babu Wanda a jikinsu jinin bai bartsanwa ba,

Abaas daya kasa matsawa yana kwance a inda suka jehosa kaman mataciyar dabba rufe idanuwansa yayi hawaye na zubowa idanuwansa yana kasa motsawa.

Babu Wanda yace musu komai haka suka juya suka bar gurin shugaban cikinsu ma dago murya yace

‘Kusra bata tada Alkawari idan tayi dan haka ku tafi an cika mata burinta ko bata raye amma wannan damar itace ta cika Alkawari idan mun sake haduwa daku kun zamo namu’

Har suka bace wa gurin babu Wanda ya motsa a cikinsu Ayanah sbd babu wanda ya dawo hayyacinsa,

Sakinah dake Bayan Ayanah motsawa tayi ahankali tareda qarasowa gaban gawar Asamah ta saka hannunta yana rawa sosai ta shafe idanuwanta suka rufe tana fasa kuka mai tsima zuciya itama.

A lokacinne Zuhrah ta fasa kukan itama me karfin gaske tana fadawa jikin Ayanah.

Nurat da bata hayyacinta miqewa tayi da sauri a zare tana bin hanyar daji kafafunta na hardewa tana qwala kiran sunan Abaansu.

Ganin tana Neman nisa ne ya saka Abaas miqewa da gudu yana kamota ya rungume yana kiran sunanta da karfi da fashewa da sabon kuka.

A lokacin ne Ayanah da Zuhrah suka taso suma suna riqeta tana kwacewa cikin wani irin ihu na gushewan hankali Wanda ya saka yan uwanta suna fasa sabon kuka me taba zuciya dukkaninsu suna qara riqeta sbd zaucewa takeyi.
Sakinah ma kukan take fasawa itama tana rungume dukansu.

Ihun Nurat ke fasawa tana fizge fizge tana yakushin kanta da karfi tana kwala kiran Abaa dajin na amsawa sosai.

Qin Sakinta sukai suna sake saka karfinsu su duka suna riqeta sosai kukansu na qaruwa.

Sun jima a cikin wannan sabon tashin hankalin kafin Nurat din ta zube qasa suma suka zube gabaki dayansu har lokacin basu iya Sakinta ba sbd kada ta gudu.

Shiru sukai sai ajiyan zuciyar kukansu dake sauka akai akai na tsawon lokaci shima kafin suka miqe hannun Zuhrah na riqe dana Nurat din suka bar gurin.

Gabas suka kalla suka sake miqa suna kutsawa hanya batareda sunsan inda suka dosa ba.

Yunwa da azaba ce kawai a cike da rayuwarsu a lokacin tareda mafi girman baqin ciki da qunci,

Wuni suka sake shudewa suna zagayen dajin sun rasa hanyar fita bare komawa ANJOM duk da sunsan garin ya zama na kusra yanzu.

Cikin dare sosai suka sake samun wani guri suka zauna tareda maqale da junansu suka dunqule guri daya dukkaninsu suna cikin jikin Ayanah wadda ita kuma sakinah ce ta bata kariya ta bayanta ta hanyar zauna wa ta jingina da bayanta.

Shiru sukai ko dogon numfashin basa yi sbd tsoro da fargaba tareda damuwa.

Darensu na jiya ta tina Wanda suke tareda Asamah ta basu kariya da kulawa a lokacinda suka yanke rahama daga duk wata samun kulawa koman kankantarta,

Maganar Asamah datai musu Daren jiyan ta tina a lokacinda ta Shafa fuskan Abaas.

‘Ayanah akwai rayuwa me tsauri da qalubale a gabanmu dan haka idan matiqar muna son kada a rabamu da Abaas daga cikinmu to tabbas muna buqatan maidasa mace sbd qalubalen da zamu fuskanta zaa iya kaiwa matakin da zaa rabamu sbd shi namiji ne mu kuma mata dan haka sbd Kaucewa hakan muna buqatan boye jinsinsa sbd tseratar da rayuwarsa tareda tabbacin zamansa a tareda ku kada komai ya rabaku’
#MAMUH
#SLAVERY
#HISTORICAL
#ROYALTY
#BEST LOVE
#BEST SISTERS
#BOYEM
#NUAB ALMAZ BOYEM

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali

*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

9

*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********

Rintse idanuwanta Ayanah tayi ahankali tana sake rungumesa jikinta tareda Sauran kannan nata sbd boye jinsinsa da tabbas zatai a yanzu har zuwa lokacinda bata sani ba nakasta rayuwansa ne nakasa me munin da babu ranar gyara,

Jin takeyi kaman bazata iya hakan ba amma kuma bazata iya barin a rabasu ba har abada sbd suna rabuwa babu Wanda zai iya rayuwa a cikinsu batareda juna ba,

Sake qanqamesu tayi a matiqar sanyaye tana jin da gaske yanzu kam ta zama uwa,
Ta zama uwar da batasan komaiba sai yayanta,su kadai ne rayuwarta da duniyarta.

Suna gurin a maqale guri daya kaman ba mutane ba har suka ga duhu ya fara dan ragewa alaman asuba tayi harta gota,

Basu saki juna ba saida gari ya qara haske sosai suna iya ganin koina da komai tukuna suka warware juna,

Ayanah ce ta umarce suyi sallah a yanda suke sbd basuda gurin tsafta ce jikinsu dan babu ruwa babu komai qasar ba babu sosai hakukuwane suka fi yawa sun cike koina.

Shiru sukai tsawon lokaci babu magana Bare motsawa Bayan sunyi sallolin dake kansu.

Shiru tsit babu ko kukan kowace irin dabba a dajin Wanda hakan alama ce ta dajin baida kyau sbd kukan dabbobi ko tsuntsaye yana rage tsoron daji.

Rana ce ta fara ketowa me tsananin zafi suna Zaune a gurin har lokacin dan haka Ayanah ta juyo ahankali ta fara kallan Nurat dake kwance jikin Zuhrah tana maganganu kadan kadan har lokacin na zautuwa tana ambatar sunan Amma da Abaa.

Lumshe jajayen idanuwanta da suka bushe qayau tayi suna mata wani irin radadi tana dan Hadiye wani Numfashi me cikeda radadi shima kafin ta sunkuyar da kanta tana kasa kallan Abaas Wanda shi da Zuhrah harma da sakinah ita suke kalla sbd fahimtar akwai abinda takeson fada amma ta kasa.

Hanyar da zasu bi ta dago ta kalla idanuwanta na cikowa da hawaye sbd batasan rayuwar da zasu Tatar ba a hanyar idan suka qarasa Binta Wanda tasan duk inda suke basa nesa da ruwa ko lambum wani gari sbd sanyin da suka kwana yana fesowa na alaman hakan Shiyasa koda garin ya waye kaman zasu sanqare sbd sanyi.

Dawo da fuskanta tayi amma ta kasa kallan Abaas Wanda ya tsareta da ido jikinsa na tsananin sanyi hannunsa na rawa ya riqe gwiwowinsa da hannuwansa dake rawar sbd take ya gane abinda yake ranta amma zuciyarta na tareda sbd shima da abin ya kwana a ransa tsoro da fargaba me tsananin yanda zaa iya rabasa da yan uwansa amma kuma duk da baida shekaru amma kasancewansa namijin GHAZ daya bayan mahaifinsa sauyasa zuwa mace shine mafi girman qasqanci da zuriar GHAZ suka samu ko Bayan ransu duka tin daga kakanni,

Shi rayuwarsa ta mutu ne daga lokacinda zai koma mace,
Ya rasa darajarsa,ya rasa sunansa,ya rasa yancinsa da damarsa ta zama GHAZ na har abada sbd yana cikin tsatsauran al’adarsu matiqar namiji ya zama tamkar mace kokuma zamowa mace ko shigar danganci mace to har abada bazai taba karban gadon matsayin shugabancin Ahalin GHAZ ba bare ANJOM.

Rawa jikinsa yafara cikeda wani irin radadi da ciwon daya saka idanuwansa cikowa da hawaye masu Zafin gaske yana qanqame kafafunsa,

Zuhrah data fahimci hakan kallan Ayanah dake sauke kai itama hawaye na gangaro mata da tsananin tsoro da faraba tace

‘Ayanah saimunyi hakan zamu rayu tareda shi,
Bazan iya rayuwa ba idan aka rabamu dashi,
Ayanah koma menene zamuyi masa shi dan rayuwa tareda shi koda hakan na nufin komawansa mace har ranar da Allah zai dauki rayuwarsa ko tamu…

Kuka ta fasa mai sanyi tana cewa

‘AMMA kada kice bazaki iya ba’

Wani irin kuka me karfi Ayanah da Abaas din suka fashe dashi a lokaci daya kowannesu na saka kansa cikin kafafunsa sbd AMMAN data Ambaci Ayanah dashi Wanda daga lokacin ta tabbatarda ita ta gama karban Ayanah a matsayin Uwa duk da ba shekaru masu tsayi tsakaninsu amma dai ta Riga ta maye musu gurbin Ammah kaman yanda su Abaa ke cewa ita uwarsu sbd tsanani son da uwa kewa ‘da take musu suma suna mata tsananin son fa ‘da kewa uwa.

Sakinah ma kuka takeyi sosai sbd rayuwarsa me suna da Abaas zai rasa daga yau shikenan.

Kuka sukeyi sosai a tsakaninsu harda Nurat da bata cikakken hayyacinta kukan takeyi sosai cikeda tausayi me karya zuciya.

Tsananin Zafin rana ke dukansu ga kuka da suka kasa Denawa sai hakan ya fara raunana lafiyansu dan haka daqyar sukai shiru Ayanah sai a lokacin ta dago ta kalli Abaas Wanda kansa ke qasa har qasa lokacin burinsa na zamowa namiji,dan uwa kuma uba dayake fatan wata rana zuriarsa data Ayanah ko daya daga cikin yan uwansa yana narkewa tareda bin iska a yau,zai mutu batareda samun wannan cikar burinba.

Sakina ce cikin tsananin kukan da tasan illa da nakasun da rayuwarsa zata samu daga yau ta saka hannu tana zare ‘yan kunnan azurfan dasuke kunnenta duka guda biyu ta kamo hannun Ayanah dake kuka sosai ta saka mata su ahankali tana Juyawa baya jikinta a sanyaye sbd ita har yanzu baiwar su ce bazata kalla yanda zaa yaga qimar uwayen gidanta ba.

Qanqame abin kunnayen Ayanah tayi a hannunta tana dauke kanta daga kallansu su duka kukanta na Neman tsananta amma dole zata aikatawa dan uwanta hakan.

Zuhrah ce da itama kukan takeyi ta miqe tsaye tareda Kama hannun Ayanah ta kasa maganar da zatai sbd kukan dake zuwar mata sabo mai ciwo dan haka juyawa tayi itama tana Dora hannunta a kirjinta dake ciwo da nauyi.

Rarrafowa Ayanah tayi cikin mummunan gaban Abaas din tareda daga hannuwanta dake rawa sosai takai tafukan hannayenta fuskansa ta tallafo ta kallesa ya Lumshe idanuwansa yana kasa barin taga tsananin rauni da baqin ciki tareda quncin dayake cikinsu sbd kada ya qarasa karya zuciyarta da gangar jikinta.

Bakinta takai kan gefen fuskansa ta sumbacesa hawaye na gangaro mata kafin ta sake dorawa kan goshinsa ta sumbacesa hawayenta na diga kan goshin nasa.

Zuhrah ma cikin karfin Hali tana danne zuciyarta ta juyo ta durqusa gabansa ta Kama hannuwansa biyu ta sumbacesu duka kafin ta sumbaci tsakiyar kansa da gashinsa me tsayi kaman mace yake daure har lokacin.

Tafin hannu Ayanah ta bude ta kalli yan kunnayen kafin ta daga ahankali tareda Kama kunnansa,

Bude idanuwansa yayi ya sauke Akan fuskan Ayanah din wadda cikin idanuwansa take kallo tana masa kallan tsananin kaunar dake nuni da har abada idan kowa zai gujesa su suna tareda dashi har mutuwa sbd su a gurinsu rasa kowace darajarsa ba ta ‘da namiji.

Baice komaiba Bayan rufe idanuwansa da yayi ahankali sbd su kadai yake buqata a rayuwarsa daman kuma idan yana tareda su shikenan zai iya jure komai.

Hannunta ta Dora a kunnansa cikin radadin zuciya ta huda kunnan nasa da karfin da na karfin hali ne,

Zuhrah kaman a zuciyarta haka taji hujin kunnan shi kuwa ko motsawa beyiba sai wasu hawayen da bana radadi bane suka gangaro masa.

Haka Ayanah ta huda Dayan kunnan tana bar masa yan kunnayen a kunnuwansa.

Tallafe fuskansa ta sake yi da hannuwanta tana kallan idanuwansa dake rufe yana riqe kukansa me tsanani dake zuwar masa.

Itama kokarin riqe nata takeyi har saida Zuhrah ta saka hannunta cikin riqe nata kukan itama ta zare daurin gashinsa take gashin ya sauka har kafadarsa,

Wani irin kuka me karfi da gunji suka sake a tareda dukkaninsu suna rungumesa.

Har lokacin Sakinah bata juyoba itama kuka takeyi sosai a yanda take,

Nurat ma kukan ta fasa tana fadawa cikinsu tareda ambatar Ayanah da AMMA itama.

Rigar Zuhrah me dan adon Kayan mata suka zare aka saka masa tasa kuma Zuhrah din ta saka.

Sakinah ce ta matsa kadan gaba ta Debo wani ganye shar ta kawo Ayanah ce ta murza ganyen da hannuwanta biyu ta goga a fuskan Abaas din Wanda bazai bazai taba barin gashi ya fito a fuskansa ba.

Sake rungumesa Ayanah tayi suka sake samun Yar nutsuwa da dangana kafin suka miqe suna kama hannuwan juna suka bi hanya ahankali cikin galabaita Wanda babu ta yanda zaka zan akwai namiji a cikinsu..

Koda rana ta fadi babu me iya tsayuwa sosai a cikinsu sbd tafiya da azaba,
Kafafunsu dukansu babu Wanda bai fashe ba,

Kaman a mafarki suka fara hango ruwa me yawan gaske yake dukkaninsu suka Ji sun samu dan kuzarin daya qare musu.

Ruwan suka nufa suna jin maqoshi da jininsu na sake qafewa.

Ana magrib suka isa ruwan Wanda

5 / 100