Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   81 / 100

240K to 243K   out of 299.8K words

ido duk da ba wani gyara sosai yasha ba sama sama ta gyarasa.

Fuskanta tayi wani irin fresh tana glowing tamkar ba wadda suka taho da ita a cikin matsananciyar damuwa ba,
Qamshinta me sanyi da shiga zuciya ne ya shiga hancinsu suka juyo suna kallanta tana tahowa a natse hannunta riqe da wayarta tana duba sakon Neesah dake tambayarta yaya ta hadu da sultan kuwa.

Qarasowa tayi ta zauna gefen Mum zuhrah tana kallan Amminta cikeda kunya da tsananin kewanta datake jin tanayi ta gaidata.

Dagowa Ammin tayi ta zuba mata ido tana kallanta cikeda kauna da kewa itama ta sauke ajiyan zuciya ta amsa tana miqa mata hannu da sauri ta tashi ta kama tana komawa gefenta ta rungumeta tana ciko idanuwanta da hawaye da sautin sanyi tace

'Ammi kiyi hakuri'

Shafa kanta Ammin tayi tana cewa

'Ya wuce amma duk da hakan zanyi magana dashi zaiga bacin raina'

Shiru bahar tayi tana kasa cewa komai gabanta na dan faduwa.

Salmah ce ta kawo mata breakfast a jere cikin wata lafiyayyar tr3y ta ajiye akan table dake gabanta tana juyawa takawo mata madara din da maa sakinah ta dafa mata tinda safe bayan ta sake zafafa shi yana tiriri ta ajiye mata tabar gurin.

Chips ne da kebab na qoda dayaji carrots da peas sai ketchup da fresh fruits masu sanyi harma da kusan kankara a cikin glass bowl da small fork na ci a ciki soke.

Madaranta ta fara dauka tana sha ahankali tana jin zuciyarta fes Amminta ta dena fushi da ita hakama hakanan ganinta zagaye da iyayenta ya saka zuciyarta jin nutsuwa da farin ciki.

Tana shanye madarar ta ajiye cup din ta dauki fork tafara cin chips din a natse tana sauraron firar su Ammin tana dan chat da Neesah data kasa barinta ta zauna kalau.

Shigowan qamshinsa ne daya ratso palon a natse cikin sanyi yana ratsa hancinsu da gauraya numfashin niimar gurin ya saka dukkaninsu yin shiru suna sanin shine ya shigo bangaren,

Bayi fara ficewa sukai tas dan haka koda ya qarasa isowa palon iyayen nasa ne kadai a zaune dukansu kallo daya sukai masa suka dauke idanuwansu sbd kwarjininsa da haibarsa data cika idanuwansu.

Qarasowa yayi a natse idanuwansa suna kan Amminsa wadda itama shi take kalla.

Gefenta daya Leylah ce a zaune daga ciki kenan sai dayan gefen nata na kusa Bahar ce a zaune kusa da ita sosai dan haka yana qarasawo gefenta da Bahar din ke zaune ya iso a natse ya zauna cikeda kamewa sa ikon dayake yawo a jininsa.

Dago idanuwansa masu haske da kyau yayi ya gaida iyayen nasa daya bayan yana amsa tasu gaisuwan kafin ya tsayar da idanuwansa akan Amminsa wadda kewanta ce tafi komai ya yawa a tattare dashi yanxu sbd ya dade sosai bai sakata a idanuwansa ba tinda tabar boyem a baya sai yau din dan haka numfashi me sanyi da nutsuwa ya sauke yana gaidata cikeda kulawa da kauna.

Amsawa tayi a daidai lokacin su maa suka miqe suka bar gurin hakama leylah aka bar Zuhrah da Ammin sai Bahar wadda ta kasa motsawa sbd tsakiyar da suka sakata qamshinsa na shigarta da kyau yana kashe duk wani kuzarin jikinta.

Jin tayi maqoshinta da cikinta sun cushe da abincin datake cusawa dan haka ta ajiye plate din a hankali tana kasa juyawa ta kallesa ta dauki bowl din fruit dayake gabanta koda su idan taci zasu iya wucewa tunda basuda karfi.

Magana yafara yi da Ammi a natse idanuwansa na kan yatsun hannunta farare tas masu tsayi dasuke daukan idanuwansa tana sakawa a cikin bowl din ta dauko water melon jajir da ira datai sanyi yankan cubes ta nufo bakinta da ita ta bude baki ta saka tana taunawa ahankali.

Kasa hadiyewa tayi sbd jin idanuwansa akanta tsaye tsaf.

Motsawa tayi a hankali tana son miqewa tabar gurin taji saukan tafin  hannunsa akan nata daya data dafa zata tashi.

Sarqewa tayi da wani irin karfi sbd rikicewa me karfi ta kasa juyowa ta kallesa bare hannuwan nasu da suka hadu sbd su Ammi dake zaune sunata magana batareda sun san meyake faruwa ba.

Ammi ce ta dan juyo ta kalleta cikin kulawa tana mata sannu
Daqyar ta hadiye abinda ke bakinta tana gyadawa Ammi kai ahankali cikin fargaba.

Zare hannunta zatai Amma jin ya juyo da hannunta ahankali ya hade tafin hannuwansu ya sakata faduwan gaba me karfi tana kokarin sake sarkewa Ammi ta juyo gabaki daya tana kallanta tace

'Yayi miki sanyi da yawa ki ajiye tinda kinsan kina fama da zazzabi kwanakin nan'

Ajiye bowl din tayi da hannu daya tana dagowa a natse cikin sanyi ta kallesa shima idanuwansa ita suka kalla a natse da kamewansa batareda shakkar komaiba.

Wani irin taji na mutuwan jiki da irin kallan da yayi mata ta sauke idanuwanta tana zame hannunta da dan sauri tana kallan Ammi wadda idanuwanta suka kan Zuhrah kafin ta dawo dasu akan NUAB wanda ya dago idanuwansa a natse daga kan Bahar din yana dawo dasu akan Amminsa wadda ta dan kame fuska sosai sbd kaman taga Bahar yake kalla.

Bahar na ganin hakan itama ta miqe a natse cikin sanyi tabar gurin tana qin juyowa sbd jin kaman idanuwansa akanta.

Tana barin gurin shima bai wani tsaya magana dasu Ammin ba musamman tinda ba ita kadai bace mum zuhrah na gurin magana bazata yiyuba a tsakaninsu dan haka ya bar bangaren.

Yana fita wayarta date hannunsa ya sake riqewa a natse sbd a tsakiyarsu wayan take dan haka ya dauko.

Office dinsa ya nufa na cikin masarautar tinda ya wuni ya kwana be leqa ba.

Itama bahar tana barin palon dakin maa ta nufa acan ta shige mata maa din na biye mata cikeda kauna da kulawa.

Bata ankara da wayarta bata nan ba saida tai kusan rabin wuni a dakin maa ta fito ta duba wayarta koina bata ganta ba ta nufi har dakinta ta duba bata ganta ba dan haka taje ta karbi wayar maa ta kira tata wayar.

Kira kusan uku bata ji ringin nata koina ba dan haka ta bari sai kowa ya watse idan koina yayi tsit zuwa koda yamma ne ko irin bayan magrib haka kowa ya shige zata iya jin ringing nata idan ta kira.

Dakinta ta koma ta janyo laptop dinta tana duba abubuwa na classes nata da sauransu.

Leylah ma data zo ta zauna kusa da ita tana waya daqyar ta gama wayar tana jin zazzabi da kaman amai yana taso mata tana gamawa toilet ta fada ta dade sosai a ciki tana amai kafin taji sauki sauki tayi wanka ta fito jikinta da zazzabi sosai.

Shiryawa tayi lokacin magrib ma ta riga tayi tana yin sallah ta zube a gurin tana dunqulewa.

Ita ma bahar din ajiyewa tayi tayo alwala tayi sallah tana idarwa ta miqe tabar dakin ta tafi dakin Ammi.

Acan takai har ishai sukai tareda Ammin ta dawo daki tayi wanka tai shirin bacci har zata fita cin abinci zuwa dining ta tina wayarta bata hannunta har lokacin dan haka ta sake komawa dakin Ammi ta dauko wayar Ammin ta fito da ita tana sake kiran wayarta.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

148
Ko data fito da wayar Ammin dakinta tafara nufa dan kiran wayar tata tana shiga ta tadda Leylah na toilet ta zauna bakin sofa tana saka kiran wayarta,

Ringing tayi harta yanke bataji komaiba ta sake saka kiran ga mamakinta sai taga an dauka dan daka takai wayar kunnenta ta dora tareda bude baki da muryanta ne dadi tace

"Maa kece??

Shiru akai mata wanda ya saka dago wayar ta kalla taga tata dince dai ta kira dan haka ta sake kai wayar kunnenta zatai magana sautin numfashinsa daya fitar ya sauka a kunnenta ta dakata cak tana kasa cewa komai tareda kasa yadda wayarta a hannunsa tayaya?

Yunqurin Aman Leylah me karfi ne ya sakata kallan kofar toilet din tana kashe wayar hannunta datake neman rikitata sbd jinsa,

Kuka leylah keyi a toilet din tana sake feso amai me karfin daya saka bahar miqewa ta nufi toilet din da sauri tayi knocking kafin ta bude ta shiga kai tsaye tana nufar leylan wadda take kuka sosai sbd azabar aman datake ji.

Taimaka mata bahar tayi ta riqeta tana share mata fuska da towel tana mata sannu harta kammala.

Wanke fuskanta tayi bahar ba riqeda ita har lokacin sbd karfinta daya qare da jiri me karfi.

Fitowa sukai toilet bata iya tsayuwa kafafunta da jikinta na wata irin kakkarwan daya saka Bahar jin tsoro tace

'A fadawa Ammi sbd a kira dr kina buqatan ganin likita da gaggawa'

Riqeta Leylah tayi da hannunta dake dan rawa ta girgiza mata kai tana cewa

'No taimakamun kawai na kira Asim zanga likita acan banason tashin hankalinsu Ammi.'

Batai mamaki ba sbd mijinta tace a kira mata ba wani ba dan haka wayarta taje ta dauko mata a gefen gado kafin ta kawo mata ta miqa mata.

Daqyar ta iya saka numbern kiran Asim din wanda bata jima tana ringing ba ya daga a natse.

'Banajin dadi sosai pls ina buqatan dr'

Abinda tafada masa kenan ta ajiye wayar tana dafe numfashinta da kaman zai dauke.

Ita kanta Bahar wayar hannunta ce ta Ammi ta sake kalla tana son sake kiran tata amma zata bari sai Leylah ta samu kanta tukuna.

Zaunawa tayi gefen Leylah din tana bude mata ruwan roba tana miqa mata ta girgiza kai ahankali sbd tana sha zata sake Amai.

Mintina ko bakwai basu bata ba saiga kiran Asim a wayar Leylah din wanda sai daya kusa tsinkewa ta ita dauka takai kunnenta.

'Ki fito ina kofa' ya fada kai tsaye yana kashe wayar.

Itama tana jin hakan numfashi ta sauke me zafi tana dan tattaro karfin hali ta miqe Bahar ta kamata suka fito.

Koda suka fito Ammi na fitowa daga dakin Tenya zata nufi nata suna ganinta Leylah ta dan kama jikinta cikin karfin hali.

Kallansu Ammin tayi itama tace

'lafiya dai na ganku a haka,
Ina zaku?

Bahar bata iya cewa komaiba sbd batasan me zata ce ba sedai Leylah ce ta bude baki da karfin hali tace

'Zamuje bangaren Mum ne amma zamu dawo yanxu insha Allah.'

Batace musu komaiba suka fice tana wucewa ciki itama sbd shirin kwanciya.

Suna fitowa a natse tana riqe da Leylah a kanta idanuwan Asim dake kallan kofar suka sauka kirjinsa ya tsaya cak da bugawa yana jin kansa na sarawa dan haka ya dauke idanuwansa ahankali daga kanta yana mayarwa akan leylah wadda take kallansa da idanuwanta da suka galabaita tana fahimtar halin daya shiga sbd hannuwansa take suka fara rawa dan haka ta dauke kallanta daga kansa itama tana kallan gabanta suna tinkaro sa.

Kokarin isa inda yake sukeyi hankalin Bahar a kwance batareda tinanin komaiba sbd sam bata tinanin ma akwai komai a tsakaninsu musamman yanzu dayake auren leylah bayan haka ko acan baya ita batasan cewa son soyayya yake mata ba daukanta kawai tsautsayi ne da kaddara ya tashi sakata zamowa imebētinsa amma bawai dan soyayyar ba.

Aleey ne ya iso gurin daidai lokacin dasuke isowa gaban Asim din wanda yake jin kaman ya juya yabar gurin amma sbd leylah bazai iya ba dan haka yake a tsaye dake.

Aleey na isowa gurin Bahar din ya kalla cikeda girmamawa da kulawa ya sanar da ita aikosa akai ya rakata karban wayarta.

Da mamaki ta kallesa ta kalli hannuwansa duka biyu bataga komaiba sbd kawai taje da kanta amsa yaqi bawa Aleey din wayar.

Kallan Asim Aleey yayi cikin girmamawa ya gaidasa kafin ya kalli leylah itama ya gaidata duka sbd sunada jinin sarautar boyem ne.

Amsawa Asim yayi a natse da taqaitawa tareda miqa hannunsa a hankali ya kama na Leylah yajisa da zafi sosai ya kalleta yana janta a natse suna barin gurin yace

'Tin yaushe wannan zazzabin me karfi haka?
Da yamman nan??

Gyada masa kai kawai ta iya yi tana godewa Allah daya saka Bahar bazata bisu ba duk da damab bahar din batada niyar binta koina iyakarta rakota kofa sbd ganin halinda take ciki.

Suna barin gurin juyawa tayi ta kalli Aleey zatai magana sai kuma ta fasa ta kalli time na wayar Ammi dake hannunta ta wuce gaba yabi bayanta.

Hanyar office dinsa suke kokarin nufa sakon keelah ya shigo wayar Aleey cewan Sultan din ya baro office yana bangarensa sun iso tareda shi.

Bangarensa suka nufa din yana bayanta tana gaba a natse an dakatar da kowace sahu a bangaren ba kowa sai iska me nutsuwa da dadi dake kadawa ba bayaniyar ko kukan komai.

Suna isowa tin kafin ta iso kofar aka wangale mata ita securities din dake kwana kofar suna miqewa tsaye dukansu kansu a qasa cikeda girmamawa suna mata gaisuwan da batama iya amsawa ba da sauti sedai ta amsa a ciki ta wuce.

Tana shiga aka rufe kofar ruf sai kuma idan ta fito.

Aleey ne ya bude mata kofar palon ta shige ya rufe mata ya juya yabar gurin zuwa dakinsa sai kuma gobe ya shige idan ba wani aikin ya taso ba.

Ko data shiga tasan bazata taddasa a palo ba musamman palon farko dan haka kai tsaye hanyar palonsa na ciki ta nufa ta shiga a natse nan ba baya nan.

Bedroom dinsa ta nufa tana jin yar faduwan gaba sbd batason tsayawa komawa zatai,

Bude dakin tayi ta saka kai a natse qamshinsa ya shiga hancinta yana dukan fuskanta tareda sanyi me dadi.

Ba wani haske sosai a dakin amma kana iya ganin komai da komai dakyau,

Bata gansa a dakin ba ta isa har bakin gadonsa ta duba baya kai dan haka ta dan saurara sai taji alaman yana bathroom dan haka babbar glass door dake baya dakin me matsayin window ta nufa ta saka kafarta a natse ta fita ta tsaya a bakin lafiyayyan pool dinsa dake bakin kofar me kyau da tsantsar tsafta da tsari wanda kana sako kafarka wajen yake gurin babu ma wanda yake taba shiga gurin idan ba masu gyarasa ba ruwan sai daukan ido sukeyi kaman glass.

Sanyi gurin yakeda shi sosai sbd ruwan pool din dan haka wata sanyi taji tana ratsata duk da kayan jikinta riga da wando ne sunada kauri hakama da babbar abaya har qasa a jikinta data sako dan zata fito kawo leylah waje.

Shiru tayi tana kallan ruwan a tsaye taja jiran fitowansa dan kada ta koma palo jiransa baisan da itama ta dade tayi dare sosai hakama bazata iya tsayawa dakinba ya fito wanke ta gansa a yanayin da zai fito ba dan hakane ta zabi tsayawa a gurin tana bawa cikin dakin baya.

****Leylah kai tsaye bangaren Asim din suka nufa wanda suna isa ba bata lokaci likitan daya kira yaxo dan tin kafin ya tafi kiranta ya kirawo likitan bai aikasa can ba sbd bazai iya sakewa ba acan din dan haka yace yaxo nan ya samesu shi kuma ya daukota idan angama dubata din ta koma.

Koda suka dawo kirjinsa wani irin nauyi yayi masa sbd ganin da yayiwa Bahar wadda se yau ya ganta bayan lokaci me tsayin da yayi dana sanin ganin nata sbd zuciya da batada qashi akan abinda take so.

Yanda jikinsa yayi tsananin sanyi sosai ya saka zazzabin leylah jin ya dauke mata itama jikin nata yayi mugun sanyi haka likita ya dubata dayake mace ce likitar sai ya fice ya basu guri ta gama dubata.

Kallan Leylah tayi bayan ta mata harda pt test da bin pulse nata da kyau ta tabbatarda ciki ne a jikinta ajiyan zuciya tayi cikin tayata murna a natse ta sanar da ita ciki ne a jikinta amma bata san tsawon kwanaki ko satika ko watanninsa ba sai sunyi scanning zasu tabbatar da hakan.

Kafeta da idanuwa leylah tayi tana kallanta cikeda ficewa hayyaci sbd kalman ba qaramin dukanta tayiba.

Saida likitar ta sake maimaita zancen tana dan dafata tukuna ta sauke idanuwanta ahankali tana sauke numfashi me zafi jikinta na matiqar mutuwa da wani irin sanyi sbd jin abinda batasan murna zatai ba ko shiga tashin hankali sbd tashin farko batasan ma tayaya abinda yake cikinta zai samu karbuwa ko isa ga kunnuwan wanda yake ubansa ba amma zuciyarsa bazata taba sonsu ba sbd tana maqale da son wata so mai karfin da batason zamo masa kaman dole a rayuwansa bare abinda yake cikinta.

Numfashi ta sake saukewa tana sake jin shakka da tashin hankali na rufeta sbd a sanin datai Asim kokarin barin boyem yakeyi kwata kwata gabaki daya ya tafi inda zai fara sabuwar rayuwa
Baice zaije da ita ba bai tashi daga kan maganar rabuwan da suka yanke zasuyi da juna ba wandaba ta kasa gane me suka tsaya jira haryanxu duk da tafi saka ran sai zai tafi ne zai sauwake mata yanxu kuma ga ciki a jikinta,

Idan ta sanar masa zai tausaya mata ya duba cikin ya zauna da ita sbd haihuwa wanda har abada batajin zata iya zama dashi akan cikin jikinta,
Batajin zata iya cigaba da auren indai har akan cikinta zai mata hakan
Zata zabi rabuwan matiqar cikin dake tsakaninsu ne zai zama abinda zasuyi zaman auren sbd dashi.

Cikowa idanuwanta sukai da hawaye masu yawa da zafin gaske ta dago ta kalli likitan ta bude baki cikin sanyi tace duk tsanani kada ta fadawa kowa ciki ne a jikinta.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

149
Da mamaki me tsananin gaske dr ta dago ta kalli leyalan zatai magana leylan ta tareta tareda sake roqonta tana kallanta da idanuwanta da sukai jajir tana ji a ranta zata bari kafin tafiyarsa idan har ya rabu da ita din zata sanar masa da cikin bayan ya yanke hukuncinsa na karshe akan aurensu kenan sbd batason cikin ya shiga kowace maganar tasu.

Fitowa dr tayi Allah yasa bata hadu da Asim din ba yana dakinsa yana jin kansa yayi nauyi sake tsanar zaman boyem yayi yana jin kaman yabarta a yau din kwata kwata har abada iyakacinsa da iyayensa a waya sedai kuma idan sun kai masa ziyara a duk inda zaije ya gina rayuwarsa.

Aiki yake nema batareda saka matsayinsa ko asalinsa ko matsayin mahaifinsa a gaba ba dan bayason yayi rayuwar dazai akan kowace irin alfarma a yanxu dan haka a duk qasar daya fara samun aikin a cikin qasashen daya saka akai masa komai ta hanyar mutanensa na arziki acan zai tattara ya koma yayi rayuwansa.

Text dr tayi masa akan ta wuce ta gama duba leylan ta bata magani.

Duba sakon yayi ya ajiye wayarsa ya kasa fitowa sbd bazai iya kallan leylah a halinda yake ciki ba dan bazataji dadin ganinsa ba a hakan hakama tamkar cin fuska ne a gareta dan kuwa tasan akan bahar ne ya shiga wani

81 / 100