Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   45 / 100

132K to 135K   out of 299.8K words

tsaya ba itama sanin bazai taba fadar komai ba batareda izini ko umarnin NUAB ba dan haka cikin wani sanyin jiki da kafafu ta nufi bangaren nasa dan dubo meya samu Bahar dinta.

Ko daya isa securities da suka San matsayinta a gurin maigidansu dama Bahar din basu hanata ba kai tsaye bude mata kofa sukai da girmamawa me girma ta shige.

Tana shiga babban lafiyayyan palon nasa dayake tsit komai na palon tsarin rayuwarsa ce ta Russia da taste dinsa,
Qamshinsa ne koina yake cike da niimar iskar da kake shaqa dan babu abinda bai gama kamuwa da tsadadden qamshinsa ba da baa jinsa a gurin kowa,

Kallan koina tayi tana rasa ina ma zata ga Bahar din dan haka kai tsaye bude muryanta tayi ta Ambaci sunan Bahar din wadda sautin muryan Maa din na shiga kunnenta ta fasa wani kuka Mara sauti a hankali sbd bazata iya fitowa ba babu Riga a jikinta.

Sake kiran sunanta Maa tayi tana tinkarar dakin datasan ba shine na NUAB ba dan nasa dakin sam idan bame gyaransa ba babu me shiga shima Wanda yake gyaran a cikin Yaransa ne babu bawa ko daya dasuka yadda dashi Akan komai na maigidansu dan haka sune securities sune kuma bayinsa ba wata dama ko yar qanqanin da kowa yakeda ita ta iya cutatar dashi sbd sun tare tako Ina rayuwarsa da tasu rayuwar.

Maa sakinah na isa dakin kai tsaye murdawa tayi ta bude idanuwanta suka sauka kan Bahar din wadda take durqushe a qasa ta rufe jikinta da tafin hannuwanta.

Faduwa gaban Maa yayi da karfin gaske har kafafunta na rawa ta ta iso gurinta da sauri tana isowa ta janyota jikinta ta rungume da karfi tana Jin faduwan gabanta na tsananta tace

‘Bahar meya sameki?
Meya faru na ganki hakan?
Ya akai?

Lafewa jikin Maa din tayi tana fasa sabon kuka tareda qanqameta tana bude baki tace

‘Inason barin nan Maa,Inason komawa ANJOM maa.’

Saurin sake rungumeta Maa tayi tana Jin zuciyarta na sosuwa da abinda ya faru koma menene,

Bata taba Jin zata tirsasa Bahar a zuciya da rayuwar NUAB ba sbd dukkaninsu babu Wanda zata iya yiwa dole Akan dan uwansa,
Bahar amanarta ce da Abaas ya damqa a hannuwanta data karba zata riqe da rayuwarta da karfinta harsai rayuwarta tabar jikinta,

Dukkanin soyayya da kaunar datake wa Ayanah zata bawa Bahar irin wannan kaunar ne sbd daga ranar da Ayanah tasan waye Bahar zatai baqin ciki da kukan tsanar kanta da ‘yar Abaas dinta ta kasance a qarqashinta da sunan baiwa.

Idanuwanta da sukai ja ta rintse tana budewa ahankali ta saukesu Akan Bahar da fuskarta tayi ja sbd kukan datake yi sosai a jikinta.

Mayafin dake rufe da ita ta zare tana share mata hawaye a hankali tareda Jin itama a Karan farko zaman BOYEM ya isheta ANJOM takejin son komawa indai zata rayu da Bahar acan ta bata farin ciki da kulawa tareda kauna har zuwa lokacinda shi NUAB din yaji yayi niyar fadawa mahaifiyarsa waye Bahar.

Miqewa tayi tsaye tareda miqar da Bahar din tsaye tareda ficewa kai tsaye cikin bacin rai ta isa dakin NUAB da babu me shiga.

Shigarta kai tsaye babu inda ta dosa a dakin sai closet dinsa da kayansa sama da Kala dari suke a Jere babu Wanda ba original designer ba,

Babu zabi ko kallansu data tsaya kai tsaye shirt ta dauko fara qal ta juyo har lokacin nauyi ne danne da kirjinta,

Dakin ta koma ta isa har gurin Bahar din wadda take cikin yanayi da nauyi da radadi a kirji,

Da kanta ta saka mata rigar wadda tayi mata mugun yawa sosai amma hakanan ta kamo hannunta suka fito,

Suna fitowa kofar palon cikin tsananin girmamawa me girman gaske yaran NUAB din suka dan sauke kai suna kasa barinta ta wuce da Bahar sbd babu umarnin hakan daga shugabansu daya ajiyeta a gurin.

Kallansu tayi zuciyarta na Wani irin cika da mummunan bacin rai da fushin dabai taba bayyanar mata ba sbd hakuri da rashin yanci ta bude zatai magana dayansu ya saka kiran Aleey ya sanar dashi.

Kashe wayar aleey yayi da sauri yana tahowa,

Koda ya iso Maa sakinah na fada sosai Wanda babu Wanda ya dago a cikinsu kansu na qasa suna sauraronta cikin girmamawa amma bazasu iya bude kofar ba.

Aleey na isowa da sauri yayi qasa da idanuwansa daga kan Bahar sbd kai tsaye rigar dake jikinta da hadda itace ta saka yaran gabaki daya qasa da kai suna kasa dagowa.

Da Kansa aleey ya budewa Maa din kofa yana bata hakuri a natse.

Ficewa tayi har lokacin hannun Bahar din yana hannunta a zuciyarta ta yanke shawarar komawa ANJOM sbd samarwa Bahar nutsuwa da kwanciyan hankalin datake buqata,
A yanzu tanada dukiyar zinarin da zata maida garin ANJOM garin dayake a baya dan haka zata tafi da Bahar ta bata rayuwar Jin dadin data cancanta samu.

Koda suka iso bangaren kai tsaye daki suka shige babu kowa a palon,

Suna shiga Zaunawa tayi tareda zaunar da bahar gefenta sukai shiru babu me cewa komai kowannensu idanuwansa a quntace kaman zuciyoyinsu suke a quntace.


******Acan palon Ammi kuwa NUAB dinne ta kalla da dukkanin nutsuwa da zuciyarta ta bude Baki tareda Dora hannunta daya Akan nasa tace

‘Hayateem ka samu sakon auren da aka Baka na sani Wanda ina tsananin son auren nan har cikin Raina kuma nayi Naam dashi amma Ka sani bazan taba tirsasa Ka matiqar Baka raayi sbd bazan taba son Ka auri Leylah yunar Ka quntatar da rayuwarta da rashin soyayyarka sbd tamkar ‘yar daba Haifa haka nake jinta a zuciyata……..

Dago jajayen idanuwansa da suka sake tsananta da ja yayi ya kalleta bakinsa cikin wani irin nauyi da rashin kasa danne abinda yakeji yace

‘Saboda tana jinin ZUHRAH GHAZ????
Kin karya alkawarin hadin auren dayake tsakaninki da Abaas ne?
Idan Baki karya ba tayaya zan auri ‘yaya biyu daga duka yan uwanki Ammi??
Ammi ban taba shaawar aure ko rayuwa da mace ba anan kusa?
Wannan auren sarauta ne Wanda babu shi a cikin tsarin rayuwata har abada,
Bazan taba mulkin BOYEM ba sbd BOYEM bata cikin rayuwata har abada,
sultan ya aiko mun sakon auren Wanda a yau zan mayar masa da amsar ban karbi kyautar aurenba’

Wani irin zufa ne ya fara gangarowa goshin Ammin sbd Jin zuciyarta na bugawa da karfin gaske Jin sunan Zuhrah a bakin NUAB Wanda bata taba fadawa labarinta ba amma yasan Zuhrah da bazata iya fuskantar iya hana Leylah yar Zuhrahn ba abinda take so ba sbd haka take Jin Leylah har jininta sbd ita kaddararta Akan soyayyar datake wa yan uwanta ne da duk abinda zasu haifa.

Kallansa tayi tareda sake Kama hannunsa ta hada da nata ta bude baki tace

‘Kafin komai Hayateem Kamun alkawarin bazaka taba hayaniya da tashin hankali da mahaifinka ba sbd bazai taba janye wannan auren ba matiqar ba zaka cika sharadinsa ba na abinda yake so kila,
Kamun Alkawari Hayateem bazakai tashin hankali ko fitina ba kowace iri da sultan’

Kafesa da ido tayi tana maimaita maganar wadda ta sakasa zame hannunsa ahankali daga nata tareda rungumeta jikinsa batareda ya iya cewa komaiba sbd yasan tsoronta Akan kada sultan ya sake rabasu ya koresa daga masarautar Wanda a yanzu sultan baida wannan karfin dazai rabasa da mahaifiyarsa.

Numfashi me Zafin gaske ya sauke ahankali ba sauti tareda sumbatar tsakiyar kanta kafin ya saketa a natse ya miqe ya fice yabarta Zaune cikeda zullumi da tsoron gaske kashi uku,

Yaya NUAB ya San Zuhrah?
Da gaske yasan zuhran jininta ce?
Ya akai yasan alkawarin dake tsakanin sa da Abaas?
Yaga Abaas ne?
Meya yasa yake mata maganar Alkwarin auren da basuda tabbacin Abaas din ya samu yancin haihuwa??????
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laoualiHAYATEEM
Mamuhgee

78
Yana barin kanta ya tsananta Juyawa tana kasa yadda da maganar NUAB din wadda yayi mata wadda magana ce da akai a ANJOM basu taba tada ita ba anan tinda suka samu sauyin rayuwar da babu farin ciki a cikinta,
NUAB bai taba sanin komai Akan Abaas dinta ba Bayan sunansa da matsayinsa na rabin rayuwarta datake wa so fiyeda tata rayuwar,

Ayau yana maganar alkawarin auren dayake tsakaninsu na shekarun da tin Abaas din yana yaro,

Miqewa tayi kanta da kirjinta na nauyin rashin iya samun kwarin gwiwan bawa NUAB daman kasa auren Leylah wadda batajin a yanzu batada zabin daya wuce ta tirsasa hakan dan kuwa Leylah zata dawo gareta shikenan jinin Zuhrah yana hannunta.

******
Yana Baro bangaren Ammin kai tsaye bangarensa ya nufa yana isa bai damu da dubawa ko tana nan ba ko bata nan dan haka sallah sukai tareda Yaransa kafin ya shige bangaren nasa ya sake daukan tsit,
Sai ishai ya fito cikin fararen armanis sukai sallar ishai din yana gamawa kai tsaye bangaren sultan ya nufa har lokacin idanuwansa basu dawo daidai ba kaman yanda tiririn zuciyarsa bai sauka ba,

A daidai wannan lokacin shima ASIM kai tsaye kasa hakura yayi ya kwana a ranar batareda ya isar da buqatarsa dayake son a tashi Washe gari da ita na buqatan imebētinsa ta farko dan haka shiryawa yayi a Daren ya nufi bangaren sultan da tsananin taurin zuciya da karfin burin dayake a shirye dashi.

Koda sakon isowan NUAB daya fara isowa fa sultan yana Zaune palonsa ma hutawa Lumshe idanuwansa yayi cikin nutsuwa tareda sauke ajiyan zuciya sbd yasan daman Ayau din sai Yazo sbd babu yanda zai karbi aure irin wannan kai tsaye shi kuwa damar sake tsananta masa abubuwa Akan cikar burinsa ne ya samu sbd yakai lokacinda yake buqatan sauka mulkin dan bawa macen dayake tsananin so har a cikin jininsa Sauran lokacinsa daya rage a duniya sbd bata dukkanin farin ciki da walwalan da bata sani ba a lokacin kuruciya dan haka a yanzu tako wane halin saiya tabbatarda NUAB ALMAZZ ya karbi mulkin qasar BOYEM da hannunsa dan kuwa shine kadai Wanda Zai iya riqe mulkin a tsaye da dukkanin adalci da tsayuwar da qasar BOYEM taje buqata ta kuma daba dashi daga kowane sultan datai a tarihi hakama yana buqatar yayi wannan auren na YUNAR daya basa na kyautar yarsa sbd yunar zai tsaya masa da karfin nasa ikon a gurin mulkar BOYEM tareda basa dukkanin kariya ta Sharrin mulkin sarautar da baisan ta ina zai fara zuwa ba dan haka yana Bayan auren shima.

Har palon Sultan kadir ya rako LEUL din tareda komawa waje ya basu guri.

Zama cikin nutsuwa NUAB yayi tareda dagowa da idanuwansa da suke sak na mahaifin nasa suna cikeda Sauran fushin dayake cikinsu ya kalli sultan tareda danne zuciyarsa dan Hana kasa furta abinda bai daceba ga alkawarin Amminsa daya hau Kansa a yau din na kada yayi fitina kowace iri da sultan din.

Bude bakinsa yayi da muryansa me cikakken iko da nutsuwa yace

‘Barka da dare me BOYEM,
Barka da hutawa daga gajiyan tafiya’

Cikin iko da milki sultan ya saukar da idanuwansa Akan NUAB din tareda sauke ajiyan zuciya me sanyi tukuna ya bude baki ya amsa da cewa

‘Barka NUAB ALMAZZ,
Wannan ziyarar kai tsaye akwai dalilin yinta Wanda zaka iya fada kai tsaye.’

Sake dago manyan idanuwansa NUAB yayi Wanda suka sauka Akan sultan sbd baya buqatar kasancewansa a gabansa kenan ya fada abinda ya kawosa kawai,

Baya buqatan shima qara mintina Akan abinda ya kawosa dan haka takardar hannunsa daya shigo da ita ya Dora a kan table din gaban sultan din tareda dauke hannunsa ya mayar da bayansa ya jingina ya dago ya bude baki a natse yace

‘Ban karbi kyautar da aka bani ba ta aure sbd bana buqatar hakan,
Zanyi aure a duk lokacinda naji inada buqatan hakan’

Wani kyakkyawan murmushi sultan ya sake yana Dora idanuwansa Akan takardar kafin ya dago ya kalli NUAB din yace

‘Ba raayinka aka tambaya ba kokuma abinda kake buqata wannan Umarni ne na sarauta da dole zaka karba,
Kyauta ce da bazaka iya maidawa ba dan haka abinda ya kawo Ka baida amfanin zuwan naka.’

Tasowa da bayansa yayi daga jikin kujeran dayake Zaune yana kallan sultan da Wani irin yanayi na tsayuwa Akan maganarsa sbd aurenta ma a yau daga yanzu ya haramta a garesa har abada tinda har auren da kyautar da ita kanta din duka na sarautar daya tsana da jininsa ne dan haka bude baki yayi zeyi magana kadir ya shigo a natse tareda isowa gefen sultan ya dan rankwafo ya bude baki ya sanar dashi zuwan Li’ul ASIM shima a Daren.

Sultan din bai dagoba kaman yanda baice komaiba bai kuma nuna komaiba,

Murmushi me sanyi ya kuma saukewa yana cewa a basa damar shigowa.

Yau Daren na magadan mulkin BOYEM ne kenan
Yaji na NUAB Sauran ASIM din yaji menene ya kawosa shi kuma.

Kafin shigowan ASIM maida kallansa yayi Akan NUAB Wanda zuciyarsa da jininsa suke tafasa a bayyane,tsananin fushi da dacin zuciyarsa duk a bayyane sultan din yake ganinsu dan haka ya bude baki a natse hankali kwance yace

‘A karo na biyu kanada zabi biyu LEUL BOYEM,
Karban mulkin da koda kazo duniya yana jiranka kokuwa auren macen da itace zata zama macen da har abada zata ringa nuna maka auren sarautar BOYEM ne kayi koda kuwa baka karba mulkin ba aurenta zai ringa tinatar da kai sarautar daka tsana da jininka,
Karban mulkin BOYEM shine zai baka cikakkiyar daman karban auren ko Qin karbansa da kuma damar zabar duk macen da kake buqata a lokacinda zaka tashin a cikin jinin BOYE,

Karka manta harma da yancin mahaifiyarka dana mahaifinka da kake buqata,
Karban mulkin BOYEM zai saukar dani a matsayin shugaban BOYEM Wanda hakan zai Baka daman fuskantata a matsayin duk da kaga dama a tsakanin UBA,ABOKIN FADA,SULTAN ME BOYEM kokuma MASOYIN UWA wadda zan iya komai akanta kana buqatan sanin hakan yanzu….’

Qanqame hannuwansa duka biyu NUAB yayi Wani irin tiririn dacin kalaman sultan din na karshe suna suka da yankar zuciyarsa yanka me zurfi ambatar kalmar masoyin uwa da rufe kalamansa dashi,

Yana tinatar dashi ne ba auren uwarsa yakeyiba ita din wishmah dinsa,
Gatse ne yake yi masa sbd sanin kalmar zata Zafafa zuciyarsa har zuwa matakin karshe,

Yana tinanin karban mulkin nasa zai masa sauki ne ya samu biyan buqatarsa shikenan?
Yana manya tinanin idan ya hau mulki yanada ikon aurar da duk Wanda ya so ga kuma Wanda ya so din ciki kuwa hadda shi dayake mahaifin nasa yanda ikon hakan akansa.

Sultan daya yi masa kallan minti daya dauke Kansa yayi yana sauke Wani sabon lafiyayyan murmushi sbd ya doka a daidai inda yake so sbd akwai abubuwa da zamantowansan sultan Wanda yayi zama Akan karagar mulkin sarautar jinin BOYEM sun haramta ya aikatasu da Kansa amma zasu iya zuwar masa ya samesu a matsayin hukunci a ciki kuwa hadda kudiri dayake dashi na shekaru.

Shigowan ASIM a tsanake shima ya saka sultan dagowa yana maida kallansa Akan ASIM din Wanda idanuwansa suka sauka Akan NUAB da komai nasa yayi jajir alaman yana cikin tsananin fushi da baqin cikin gaske.

Idanuwansa ya saukar Akan doguwar takardar dake dauke da stamp na Masarautar BOYEM din Wanda take ta isar da umarnin auren NUAB din da Leylah yunar,

Yanayin NUAB din ya sake kalla a sace take ya tabbatarda auren ne bai karba ba Wanda hakan bama abu me yiyuwa bane a garesa kota yaya dan haka Wani sanyi da farin cikine yaji ya mamaye zuciyarsa sbd fitinar Qin karban auren zata qarasa lalata alaqar da NUAB din yake da ita da sultan tareda rasa damarsa a abubuwa da dama dan haka shi a gurinsa wannan kyakkyawan sabuwar dama ce me girman da zai tabbatarda sai anyi wannan auren na NUAB da Leylah sbd ya quntata masa Bayan kuma YUNAR ya tsanesa akan jayayya da auren yarsa dayake ji da ita.

Cikin farin cikin sa daya dan bayyana ya qaraso gaban sultan ya zube qasa a hankali yana cewa

‘Barka da hutawa Me BOYEM da mulkinta,
Ina gaidaka a wannan Daren mai tarin albarka
Allah ya qara maka lafiya da tsawon rayuwa tareda tsarkin zuciya.’

Wani murmushin me kyau sultan ya sake yana Jin zuciyarsa fes ya amsa a natse da cewa

‘Amin amin ina amsa wannan gaisuwan daga Li’ul ASIM ALMAZZ me jiran gado’

Wani sabon murmushin farin ciki ASIM ya sake tareda miqewa ya isa Akan Dayar kujeran dake facing sultan din.

Kai tsaye shima sultan ya kallesa yana sake nutsuwa da zaman duka su biyun a gabansa ya bude baki a natse yace

‘Akwai dalilin wannan ziyarar ta Li’ul ASIM a wannan Daren batareda sanarwar zuwa ganina ba Ayau din?

Numfashi ASIM ya sauke tareda kallan NUAB Wanda har lokacin jininsa ke quna ya dawo da kallansa kan sultan tareda bayyanar da dukkanin biyayyarsa ta Neman biyan buqatan abinda yake so yace

‘Na taho ga sultan ne da Neman izini tareda Neman buqatan a bani damar mallakar imebeti a yanzu,
Ina roko da fatar sultan zai bani wannan damar.’

Numfashi sultan ya sauke a dan natse yana kallan ASIM din kafin ya dan juyo ya kalli NUAB da Sai a lokacin ya dago jajayen idanuwansa ya kalli sultan din batareda ya kalli inda ASIM yake ba.

Bude baki sultan yayi yace

‘Na Baka dama Li’ul ASIM a gobe zaa zabar maka imebētin ko nawa kakeso na Baka cikakkiyar daman hakan’

Cikin tsananin farin cikin da baisan adadinsa ba ASIM ya zube qasa yana cewa

‘Guda daya ce tak nakeso Allah ya qara maka lafiya ina godia’

Takarda kadir ya dauko take wadda take dauke da stamp din hakan sultan zai saka mata hannu kadir na Dora takardar NUAB ya dago idanuwansa ya kalli takardar tareda sake Wani mayen murmushin da baisan fitowansa ba me tsantsar bayyanarda rashin hankalinsa gabaki dayansa Wanda ya saka ASIM saurin kallan sultan zaiyi magana kirjinsa na bugawa sultan idanuwansa a kafe kan NUAB ya katse ASIM da cewa

‘Kaje na Baka damar hakan’

Da sauri ASIM ya miqe yana kokarin ficewa NUAB a kalli sultan yana miqewa shima baice komaiba a fice yabar sultan na bin bayansa da kallan shakka da mamaki.

Yana fitowa cikin wani irin taku dayake bayyanarda Zafin ikonsa ya mummunan tashi yayi gaba Aleey ya biyosa da sauri
Batareda ya juyo ba muryansa mai dauke da tsantsar iko da zafi yace

‘Duk mace ko namijin da dazai taho bangaren Ammin kai kowane irin sako a cire Kansa daga wuyansa a zare jijiyoyinsa Ayi wa karnika noodles dasu.’

Aleey na Jin hakan kai tsaye yace Angama,

Salman dake jiran fitowan ASIM shima yanajin abinda NUAB din ya fada Kansa yayi mummunan sarawa yabi su da kallan mamaki ke girman gaske yana Jin Kansa na Neman Juyawa dan kuwa kila yana cikin yan kai sakon.

Suna barin gurin yana isa bangarensa

45 / 100