Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   72 / 100

213K to 216K   out of 299.8K words

lura dashi ta tsaya cak cikin wata irin shock da firgicin da bata tsammata ma ba,

Baya tayi kokarin ja tana dauke idonta akansa wainda take suka sauya suna,

Hannunta daya ya kama batareda ya motsa ba kuma batareda ya dauke idanuwansa daga tafiyarta ba wanda ke tabbatarwa da bayyanar masa da abinda yayi,

Batada kuzari sosai dan haka hannunta ta zare tana sake dan ja da baya da karfi wanda ya saka wata radadi ratsata tayi saurin dauke numfashi tana rintse ido da karfi,

Hannuwansa biyu ya saka a qugunta ba tsammani ya dagota cak ya dorata a kafafunsa batareda ya tashi ba sbd kadama ta taka ta sake jin abinda taji wanda yaji yana ratsa har tsakiyar kansa dan shima saida ya dan rufe idanuwan dan kuwa a jikinsa yaji abinda taji,

Jinta akan kafafunsa ta bude ido tana qin kallansa ta kalli hannuwansa biyu da suka zagaye qugunta akan kafafun nasa ya zuba mata ido shikuma yana kallan fuskarta tareda bin ruwan dayake kan fuskarta da kallo yana jin dumin fatarta tana shigarsa,

Gangarowa ruwan yayi a wata slow zai diga akan cinyarta dake bayyane gabaki daya sbd kusan rigarta da batada tsayi ta dan sake daukewa ya saka hannunsa akan cinyar tata yana bude tafin hannunsa ruwan suka diga akai ya kallesu kafin ya dawo da kallansa kan fuskarta da itama sai a lokacin ta dago ta kallesa idanuwanta na cikowa da hawayen laifin abinda yayi mata.

Bude baki yayi muryansa me sanyi da kauri ta ratsa kunnuwanta da suke kusa da bakinsa yace

'Yaya?yaya jikinki?you feeling better right??

Janye fuskarta zatai ahankali ya riqeta da hannunsa yana hade fuskarsu da kyau zafin numfashinsa na daukar mata direct a fuska ta sake rufe ido tana jin komai na dawo mata cikin kwakwalwan dan haka zuciyarta ta fara bugawan dayake jin kirjinta yana sama yana gogarsa yana komawa.

Rufe ido yayi ya budesu da wata slow a fuskarta kafin ya saka hannunsa daya ya zare towel qarama dake hannunta ya dagosa yafara goge mata sanyin ruwan dake fuskarta wanda hakan ya saka jikinta dan fara rawa sbd yanda yake bin fatar fuskar tata da slow yana bata waiwayi.

Jin yanayin yayi mata yawa ya sakata dora hannunta ta riqe nasa cak ta tsayar dashi tareda bude idanuwanta a kansa wanda daman hakan yake jira ya kalli cikin idanuwanta da take suka bugar dashi ya sake feso mata numfashinsa me zafin daya sakata jan numfashi mara sauti da karfi kafin ta fitar ya mannata da jikinsa ya bude baki ya sake tambayarta lafiyanta sbd yaji idan saiya nema manyan likitoci mata.

Rufe idonta tayi tana girgiza masa kai alaman ya zaketa tukuna amma baima fahimci hakan ba dan haka ya sake maimaita tambayarsa sbd tafiyarta ta saka shakka da wani irin yanayin me karfi a cikin kansa zai kaita kowace qasar dake duniyar dan tabbatarda dawowan tafiyanta daidai indai su maa sun kasa.

Ganin ya kasa sakinta ya sakata bude baki ta tattaro kalmar da gabaki daya yinin yau su maa batai musu magana ba can qasa tace

'Naji sauki'

Shigar kalmanta kunnuwansa ya sakasa dan dagota kadan yana kallanta yace

'Then meyasa kike tafiya ba daidai ba'

Wani iri taji ta rasa amsar basa kawai ta dago ta kallesa tana tsiyayo masa hawaye daya kalla dakyau yana basu matsayin bata warke ba kenan.

Kamo fuskanta yayi ya zuba mata ido yana rasa me zai fada mata dan baisaniba kwata kwata dan haka ya kalli bakinta data bude zata fara kuka me sauti yakai bakinsa akai ya rufe yana zira harshensa cikin sanyi yana mata tsotsan da sanyinta ya hanata shiga tashin hankali da tsoro sedai ta janye tana son cigaba da kuka a tsananin ciwon dake cinta da damuwa tace

'Me zan fadawa Ammi idan tadawo taga ina tafiya haka,
Wlh kunya kasheni zatai bazan iyaba ka.....

Sake dora bakinsa akan nata yayi yana mata wata tsotsa me zurfi da tsananin shauqin data sakar masa na magana tana kukan ya dago ya zuba mata idanuwansa da suka sauya ya bude baki da wata sautin daban data fara shaqewa yace

'Ni zan fada mata ba laifinki bane idan ta dawo.....'

Wani irin kuka me karfi ta fasa sbd jin abinda ya fada tana miqewa da sauri daga jikinsa sbd balain ma iya fadar dayayi cewan zai fadawa Ammi a kunnenta.

Baya tayi shikuma yana bin tafiyanta da kallan mamakin meyake faruwa ya miqe idanuwansa na sake sauyawa daidai nan Maa sakinah da Leylah suka shigo jin fasa kukanta me karfi,

Ganinsa a dakin ya sakasu tsayawa cak daga bakin kofar maa na rasa me zata ce sai kawai tayi karfin halin cewa

'Lafiya kike wannan ihun haka bahar?

Nan gurin tenya itama ta iso ta tsaya jiran jin amsa.

Kasa magana bahar tayi sbd bazata iya fada ba dan haka akansa suka maida kallansa ya taso a natse ya nufi kofar batareda ya kallesu ba kaman yanda suma suka dauke idanuwansu cikin jin nauyi ya bude baki kai tsaye yace

'Maa a tafiyanta ya zama wani iri a shiryata a zamuje likitoci su dubata may ba akwai matsalan da take buqatan doctors'

Maa tenya na jin hakan tayi saurin juyawa tabar gurin itada leylah har suna bigewa gurin rige rige sbd tinda suke basu taba shiga muguwar kunyar data zama kaman azaba kai tsaye sai ayau.

Maa sakinah kasa motsawa tayi ta sauke kai kaman ruwa ya cinyeta dan haka batada zabin cewa to.

Yana fita kaman mahaukaciya hannuwanta har rawa sukeyi ta sakawa bahar din doguwan riga ta janyota tana kuka sosai ta fito da ita daidai nan Su Asim da Shuraim suka sako kai palon sbd Aleey dayace abarsu dan tini ya juya musu kan mota ficewa daga gidan zasuyi.

Maa na fitowa da bahar din da ko wayarta bata daukoba shima NUAB din yana fitowa dan haka hannunta kawai ya kama suka fice a palon bama tareda ya gane su waye zaune a palonba suna binsu da kallo kaman yan wasan kallo.

Suna fitowa aleey ya budewa NUAB din mota ya fara saka bahar kafin ya shiga suka bar gidan take wanda aleey ya fidda wayarsa yana duba ticket din daya siya yanzu yanzu sai karfe 6 na asuba zai tashi dan haka kai tsaye masaukinsu suka nufa.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

131
Tamkar marasa wayo da hankali su Asim din sukabi NUAB din da ido wanda baima san dasu ba kwata kwata,

Zuciyoyinsu harbawa sukeyi da karfin gaske kaman yanda nasu maa ke harbawan kowa da nasa tashin hankalin daban,

Shi shuraim dayake likita kai tsaye tafiyar bahar din datakeyi tana rintse ido batareda azabar datake ji ba ta boyu idanuwansa suka sauka ya kasa motsawa yana karantar yanayin bugun zuciyarsa na sauyawa daga tsoron ko laifi bahar din tayi farko zata fuskanci hukunci zuwa tashin hankalin abinda ayanzu idanuwansa ke bayyanar masa wanda yake nuni da akwai tabbacin abinda ya faru,

Asim da shima yasan da zancen kallo daya yayiwa bahar din ya dauke idanuwansa dake cika da wasu irin hawaye yana maidawa akan NUAB yana binsa da kallo idanuwansa jajir harya fice ya bacewa ganinsa,

Dukkanin wanda yake palon zuciyarsa a cikin mummunan hali ta samu kanta da tsananin sanyin jikin dayake cigaba da mutuwa sbd tashin hankali musamman Asim dayake jin numfashinsa na dannewa yana toshewa,

A jininsa Allah ya hallita masa kaunar bahar me tsananin gaske dayake jinta kamar bazai iya rayuwa batareda samuntaba a cikinta,

Ya taso ya rayu a cikin buri na kaunar sarauta da hawa mulki,
Ya rayu a cikin wannan burin,
Ya gino past dinsa da present da future dinsa duka akan burin da mahaifiyarsa ta gina a ransa tin yana rarrafe da baisan kansa ba harya fara sanin kansa ya taso a cikin burin da ba nasa ba,

Soyayyar Bahar da tsananin burin samunta a rayuwarsa shine burinsa na farko a rayuwa wanda yake na asalin qashin kansa ba wanda aka rayar dashi acikinsa ba,

Samunta da soyayyarta ta ganar dashi burinsa shine gaban komai akan rayuwarsa bana mameensa ba bare yayunsa

Samun cikar da burinsa ya gane shine zai basa rayuwar yancinsa da farin cikin dayake buqata bata hawa mulkin dazai zama ana juyasa ba juyawan da har abada baida nasa raayin ko burin ko yanci zai mutu ne yana cika burin wasu ba nasa ba maana na mahaifiyarsa da yayyansa.

Burin Bahar daya qwallafa rayuwansa yayi niyar ya mutu a gurin nema da samunta,
Ya shirya mutuwa da rayuwa duka akan soyayyarta wadda ayau rayuwa da kowane burinsa ya tsaya cak akan faduwa da haduwan dukkanin rashin nasara,

Ya rasa cikar burin samun sarautar mulkin qasar jininsa ga NUAB wanda yake dan wishmah ba matar auren sultan ba akan idonsu da kunnuwansu wanda zamtowansa 'dan matar auren kuma queen bai samar masa ba bayan yana ganin shine 'da mafi daraja a kaf qasar boyem sbd shine 'dan sultan din na farko namiji kuma na mata bana wishmah ba,

Ayau ma ya rasa burinsa na karshe dayake dashi akan macen data shafe karfin wancan ikon ga NUAB again wanda ko yanzu ya dake tabbatarda kaddarar kowane dan adam daban take da matsayin dayake dashi ko kuma matsayin ko shi waye,

Rufe idanuwansa da sukai jajir yayi yana sauke kansa qasa ahankali wasu hawaye masu dumi da tsananin zafi suna gangaro masa ya saka hannu ahankali ya taresu tareda gogewa a gefen rigarsa abinda ko yana yaro bai taba ya miqe duka jikinsa a tsananin sanyaye ya kasa dagowa ya kalli kowa ya juya ya bude bakinsa daqyar yayi musu sallama yana nufar kofa,

Leylah da tin dazu idanuwanta suke kafe akansa tana kallansa idanuwanta jajir itama tana jin dukkanin radadi da mutuwan jikin dayake ji sbd itama zuciyarta ta gaji da dakon baqin cikin da babu wanda yasan sunayi miqewa tayi tareda kasa kallan kowa tai musu sallama tana bin bayansa kafafunta a sanyaye tana jin karfin jikinta ba ko daya hakama bazata iya zama a gidan ba zata koma masaukinsu wanda take jin bama amfani zamansu aqasar yanxu gwara su koma gida ko su tafi wata qasar zaifi bata sassaucin abinda takeji.

Asim baisan data biyosa ba dan haka tafiya yakeyi ahankali kansa a qasa sanyin daren na ratsashi yan isa har bargon jikinsa amma baya jin ko mota zatabi ta kansa ayanzu zaiji radadin kaman yanda yake jinsa a zuciyarsa da kwakwalwansa.

Tafiya me tsayi sukayi batareda sun san sunayi ba sbd babu wanda baiyi nisa a tinani ba musamman Asim da har lokacin baisan tana bayansa ba sbd hawaye ne suka ciko idanuwansa suna komawa suna sake cikowa suna komawa.

Shuraim da shima jiki sanyaye yayi sallama dasu maa ya fito gidan bayan ya samu tabbacin cewan Bahar ta zama cikakkiyar macen NUAB a gurinsu sbd maganin dasuka buqaci ya rubutawa bahar din idan ta dawo tasha.

Hannuwansa na rawa ya rubuta musu maganin zuciyarsa na rasa duk wani buri da hope dayake dashi a hankali daya bayan daya harya kamma rubuta ya ajiye musu ya miqe yayi musu sallamar gabaki daya ya juya ya fice idanuwansa jajir.

Taxi ya tara ya fada yana rintse idanuwansa yana jingina da bayansa zuciyarsa na tsayawa daga kowane tinani bayan na son barin qasar ya koma boyem wanda boyem dinma bayajin zai iya cigaba da zama matiqar ba sassaucin abinda yakeji ba ya samu ba.

Yana gap da isa masaukinsu ya hango su Asim din suna tafiya da kafafunsu sanyi me karfi yana ratsasu ya tsayar da driver ya fita ya kamo hannun Leylah wadda ta miqa hannunta ta kamo Asim
Ya tsaya cak yana kasa juyowa har saida shuraim ya saka hannunsa daya shima ya kamosa ya sakasu a mota suka bar gurin.

A motar babu wanda yayi magana bare iya doguwan motsima kawai shiru sukai dukansu kowa da abinda yake yanka zuciyarsa a cikin sanyi da nutsuwa hakama suna hadiye ciwon da radadin shiru ba cewa komai.

Suna isa haka suka fito suka wuce ciki shuraim ya biyasa ya biyo bayansu har lokacin bame cewa komaiba.

Lift sika shiga ta fara tsayawa ta sauke shuraim kafin su suka wuce saman suna isa suka nufi dakinsu koda Asim ya fidda katin dakin zai bude rawa hannuwansu sukeyi sosai suna wata irin jijjigar data saka katin faduwa qasa ya durkusa xai dauka har lokacin komai nasa rawa yakeyi.

Leylah da idanuwanta sukai jajir wasu hawayen ne suka zubo mata ta durkusa ra saka hannu ta dauki card din ta bude dakin ta kamasa ta miqar dashi suka shiga ta rufe dakin tabiyo bayansa tana kallan yanda kafafunsa ke rawar data sakata rintse idanuwanta,

Taku biyu yayi ya zube a qasa a gurin tareda fasa wani irin kuka me karfin gaske yana dafe kirjinsa da hannuwansa biyu sbd wata irin radadin azabar dayake masa na shikenan ya rasa bahar ta haramta garesa har abada ya sake rasa dadadden burinsa,

Wata irin azaba da qunci yakeji wanda bai taba jinsuba sbd koda ya rasa mulkin msarautar boyem baiji abinda yakeji ba ayanzu na rasa bahar wadda itace nutsuwan karshe da rayuwa da zuciyarsa zasu samu.

Kuka yakeyi sosai jikinsa na rawa sosai yana jin kaman kirjinsa zai yage ya mutu,

Irin yanda kukansa yake ratsa dakin nasu yana saka komai daukan tsit tareda tayar da tsigar jiki ya saka Leylah rabewa taba jingina da bango tareda silalewa tana zamewa qasa ahankali hawaye suna gudu a fuskarta sbd shedar da ayau kaunar da Asim kewa Bahar bata qasa bace ta gasken gaske ce,

Ita kuma tata kaddarar kenan akan bahar,
Namijin datake tsananin so fiyeda rayuwarta ya zabi bahar ya mutu akanta,
Ayau ma mijinta datake aure shima bahar dince rayuwarsa,
Yayi mutuwar da zai iya barin duniya akan bahar........

Hannu ta dora akan kirjinta tana jin wani irin radadin azaba yana keta kirjinta yana saka hannuwanta rawa ta soka kanta a cikin kafafunta tana fasa wani irin kuka me karfi da tada tsigar jikin itama tana jinta ayau tamkar mara gatan da batada ko asali bare zamowa yar jinin sarauta,
Tana jinta yau tamkar ba 'yar mai girma yunar dayake da babban matsayiba dazai iya komai akantaba....

Lokaci me tsayi suka dauka a wannan mummunan yanayin kafin sukai shiru dukansu a inda suke suka raba tsakiyar daren babu wanda ya dago,

Ciwo ne me karfin gaske ya taso ya rufe Asim wanda ya ringa fizga sbd rawar sanyi dan haka dole itace ta miqe ta taimaka ta kamasa suka isa gado ta kwantar dashi ta rufesa ta dauki waya ta kira Shuraim wanda a cikin daren sosai ya shigo dakin idanuwansa jajir bai samu baccin ba shima.

Duba Asim din yayi yace suna buqatar kaisa asibiti sbd kaman attack ne yake kokarin samu.

Manager suka kira take a tanadi motar da zaa kai Asim da ita wadda aka fitar aka taho da gaggawa aka daukesa aka fita dashi zuwa asibiti Shuraim na tareda shi dan hanasa rasa hayyacinsa gabaki dazai taimaka sosia.

Suna isa asibitin aka shige dashi dan taimaka masa shikuma shuraim da aka dakatar dasu Leylah ya riqe a jikinsa tareda cire rigar sanyin jikinsa ya saka mata akan kayanta data wuni yau dasu sbd ko shirin bacci basuda daman yi.

Zaunawa sukai suna jiran tsammani batareda ko iya magana a tsakaninsu ba dan babu me energy.

Har asuba suna zaune tukuna suka samu shiga zuwa dakin da aka kai Asim din ya samu bacci me karfi ya daukesa ya koma kaman bashiba a ciwon da bata taba tsammanin zai iya kamasa akan so ba.

Sallah sukai a dakin kafin ta zauna akan sofa tana lumshe ido bacci ya dan fizgeta shuraim ya jinginar da ita yace ta dan rintsa kafin Asim din ya tashi.

Hakan kuwa tayi take bacci me karfi ya dauketa shi kuma ya fice daga dakin.

Karfe goma sha daya na rana Asim ya farka lokacin harma taje tayo wanka ta sauyo kaya ta dawo tana zaune ta tsaresa da ido tana kallo.

Bude idanuwansa ya hada idanuwansu kai tsaye ta sauke ajiyan zuciya batareda ta motsa ba shima ita yake kalla yana lumshewa ahankali cikin rashin kuzari da mutuwan zuciya.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

132
Shiru sukai a hakan tsawon lokaci kafin ta iya motsawa a hankali ta isa garesa tai masa sannu kafin ta taimaka masa ya tashi zaune idanuwansa jajir sbd bacci da damuwa.

'Thank you' ya furta mata a hankali da sautin da baya fita sosai,

Doctors ta kira suka zo suka sake dubasa suka ga ba buqatan ajiyesa daman dan haka suka sallamesa kawai.

Itama bata wani bata lokaci ba sbd bata son asibiti ta kira drivern da hotel suka basu yazo ya daukesu suka koma.

Suna shiga dakin ruwan wanka ta taimaka ta hada masa ta kamasa har cikin toilet din tukuna ta fito.

Breakfast tayi order ba bata lokaci kafin ya futo har ankawo dan haka ta kawo masa har kurya ta jere a table ta nemi guri ta zauna tana kasa kunna wayarta har lokacin sbd bata buqatan jin kowa kadaici take so a rayuwarta yanxu.

Yana fitowa daga shi sai towel iya qugunsa ahankali ya tako ya iso ya zauna yana goge jikinsa ahakali kafin yayi dan gajeran shiri ya saka kayan shan iska yaxo ya zauna gefenta tare sukai breakfast sbd itama bata samu sakawa cikinta komaiba har lokacin.

Ba wani abincin kirki suka ci ba yasha magani ya miqe yaje ya kwanta tareda rufe idanuwansa
Itama a inda take din ta kwanta tareda runtse idanuwanta.

Shuraim ta wayar Asim ya kira yayi musu bankwana yabar Oxford ranar ya wuce sbd bazai iya zamaba damuwa ruguza rayuwarsa zatai ya lalace a banza akan wainda sun zaba tasu rayuwar sun zubar da kowa da rayuwar kowa dan haka bazai bari tasa rayuwar baqin ciki yayi sanadintaba duk da yana jin radadi da qunci me yawan gaske.

Tafiyan shuraim ya sake saka rayuwan Leylah damuwa da kadaici da qunci dan haka take son Asim ya warware suma su tafi.

******acan gidan Kuwa koda su leylah sukai musu saida safe suka tafi babu wanda yake cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyan hankali sbd tinanin wane irin likita ne kuma zai iya yiwa Bahar abinda zaifi wanda sukai mata dan kuwa a yanda tenya tayi mata wannan gyaran na al'ardasu me karfi batajin akwai wata sauran ma matsalar data rage bayan ta qin sake jiki da bahar din tayi dan kuwa ko a lokacin zaa iya sake shigarta batareda kowace irin tangarda ba amma NUAB ya kalli tsabar idonsu ya tambayi tafiyarta bata koma daidaiba bayan shine mai aikin daya kawo hakan kuma ba yanda zaayi tafiyarta ta koma daidai kai tsaye sbd ba qaramin gurza tasha ba,

Kunyar daya sakasu itace mafi

72 / 100