ta zubawa ido Akan lambar 99 dake zane a hannunta Baro Baro tayi baqi sosai Akan farin hannunta daya keda fari sosai sbd zamanta bata Baro komai na mahaifiyarta ba,
Wasu hawaye masu tsananin zafi ne suka gangaro daga idanuwan sakinah dake Haba kukanta zuwa sbd da wuta aka rubuta lambar 99 din wadda take lambar Abaas ta Shedan zama cikakken bawa da kusrawa sukai musu,
Lambar mahaifinta Abaas ce a jikinta zeti da inda akai masa tasa shima a gefen hannu daga sama gurin gwiwan hannun,
Rufe baki da hannunta daya sakinah tayi tana kukanta bayyana sbd Bahar dake shiru a jikinta,
Nata hannun ta kalla inda tata lambar take Baro Baro a jiki 96,
Zuhrah ce 97 sai Nurat 98 tukuna Abaas dinne 99 Ayanaah 100 Wanda haka akai musu su a Jere babu Wanda a cikinsu haryanzu wannan lambar bata jikinsa Wanda da ita zasu mutu,
NUAAB tin da ya tashi yaga mahaifiyarsa da wannan lambar a jikinta da hannunsa ya zanawa Kansa lambar a jikinsa da wuta sbd itace lambar dazai tabbatarwa Abaas shi din ‘dan Ayanah ne dan haka da lambar mahaifiyarsa ya tashi a jikinsa bata taba dauka Abaas shima yayiwa tasa yar lambar sa ba sbd koda baya raye da lambar sa zasu yadda da Bahar ‘yarsa ce.
Kuka sosai Maa sakinah din tafasa tana kasa riqe kanta sbd har abada sunyi rashin da bazasu taba manta radadin sa ba,
Sunyi rashin da shine mafi ciwon rashin da sukai a baya Bayan nan.
BAHAR dake kwance shiru zuciyarta bata iya komai Bayan bugawa ahankali sbd komai ya tsaya mata cak tana jin sautin kukan Maa sakinah yana shiga kunnuwanta a hankali yana ratsata sbd tasan kukan rashin Abaa dinta ne akeyi.
Bude idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga cikinsu a sanyaye tana sake Numfashi me sanyi Mara sauti batareda ta motsa daga kwancen datake a jikin matar da bata taba saniba a zahiri Sai a tarihi amma ayanzu da ita kadai zatai rayuwa.
Tafiyar kusan wuni guda sukai kafin jirginsu ya sauka a qasar BOYEM suka fito tareda securities din NUAB din duka da aka hado su dasu shikuma daga shi sai aleey suka koma.
Motocin alfarmar GHAZ ne suka daukesu daga airport zuwa Masarautar BOYEM me tarin abubuwa da tarihi dama Wani tarihin da zaa kafa.
Ko a cikin mota hannun BAHAR din yana cikin na Maa ta riqe cikin nata tana bata dumin dazai Haba gangar jikinta qarasa rasa kanta.
Duk duniya da Aljannar duniyar dake tin daga babbar gate din farko ta masarautar bai shiga idanuwan Bahar ba bare zuciyarta sbd komai na rayuwarta a yanzu rufe yake gap babu kowane irin Sauran shaawa ko burgewa a rayuwa da zai shigeta dan haka idanuwanta a kafe suke kawai a waje tana kallan wajen amma kwata kwata tinaninta baya jikinta ko daya tayi nisa a tinanin rayuwar datai a baya da mahaifinta Wanda a yanzu yana kwance cikin qasa,
Tafiya sukai suka sake wuce gate na biyu har zuwa gate na uku suka shige akai parking motocin bakin hanyar da zata kaisu bangaren cikin gida kai tsaye aka bude musu motocin dukansu su biyun a lokaci daya.
Maa ce ta fara fitowa a natse cikin sanyin jiki ta sauke ajiyan zuciya da Numfashi kafin ta zagayo ta miqa hannu cikin motar ta Kama hannun BAHAR wadda bata motsaba tinda aka bude mata motar ta janyota a hankali cikin kulawa ta fito motar,
batareda ta saki hannunta ba ta jata a natse zuwa ciki suna tafiya babu me karfin jiki.
Duk Taku daya da Bahar ke yi Wani siririn sautin sarkar kafarta ta mahaifiyarta data gada ne yake tashi tareda Wani irin sakar da nutsuwa da saka son juyowa ga duk Wanda sautin ya shiga kunnensa dan hakane duk tayi Taku daya bayin dake jere a hanyar sai sun sauke kansu qasa cikeda girmamawa ga Maa sakinah wadda kowa yasan matsayinta na shaqiqiyar Wishmah kuma jakadiyar bangaren wishmah ta biyu.
Kai tsaye hanyar bangarensu Maa ta nufa da BAHAR wadda har lokacin duk inda Maa ta jata saka kafa kawai takeyi ba Wani kuzari a jikinta.
Isowarsu gap da hanyar data raba bangaren Queen HAILE da bangaren Wishmah Ayanah a daidai wannan lokacin Li’uli ASIM ALMAZZ ya fito bangaren mahaifiyarsa cikin shigar sky blue cashmere mai fitinanniyar tsada qamshinsa yana sauya niimar gurin take dukkanin bayin dake hanyar suka sauke kansu qasa suna tsayawa cak inda suke har saiya wuce.
Maa sakinah dake gap da shigewa da Bahar bata juyowa tayi a natse dan basa girmamawa itama a natse Banda Bahar da batasan me takeyiba daga kafarta tayi tana cigaba da Takawa ba karfi a gangar jikinta ko kadan.
Sautin takunta ne da sarkar kafarta ke fiddawa a natse a gurin daya dauki tsit tamkar babu rai ko daya a gurin sbd bada girmamawa garesa ya sakasa tsayawa da takunsa cak yana dakatawa.
Sake ratsa kunnuwansa sautin yayi Wanda ya sakasa juyowa da Wani irin nutsuwa da mamaki yabi inda sautin ke fitowa da kallo a daidai lokacin Maa Sakinta ta riqota cikin nutsuwa da juyo da ita a hankali sbd inda yake dosa ba can zasu nufa ba.
Kafafunta dake rufe cikin doguwar rigar dake jikinta ash Kala wadda batada adon komai sedai daidai jikinta take ta sauka qasa sosai harma tana dan ja da kasa kadan mayafin rigar ne kadai yakeda adon dayake qawata rigar da fuskar da zata saka kayan ya tsayar da idanuwansa yana kalla amma babu ta inda kafarta ta fito se sautin.
Dagowa yayi a natse ya maida kallansa kan fuskarta zuciyarsa na dauka Wani irin Zafin mamaki da jin abinda bai taba ji ba a bayi sedai yayan sarautar ne kadai sukeda iko da wannan damar dan haka mamakinsa ya dan qaru yana bude idanuwansa da kyau a kanta.
Fuskarta dake bayyane ya zubawa idanuwansa yana kasa daukesu daga kanta mamakinsa na sauka ahankali tamkar wutar da aka zubawa ruwa,
Bin fuskarta yake sakeyi da kallan dayake sake saka zuciyarsa mamaki da jin Wani irin yanayin daya sakasa kasa dauke kallansa akanta.
Shiru gurin ya sake dauka musamman da Bahar din bata sake ko motsawa ba har tsawon mintina kafin ya dauke idanuwansa daga kan kyakkyawar fuskarta ta jinin GHAZ ya juya a natse batareda yace komaiba ya wuce zuciyarsa na riqe kamanninta da kai tsaye suka isa gareta.
Yana barin gurin Maa sakinah ta Kama hannunta suka nufi kofar da take aka bude musu ita gabaki sbd girmamawa suka shige aka rufe.
Babban palon dayake na farkon isa suka shiga Maa sakinah ta sake ajiyan zuciyar samun isowa gida cikin Amintci.
Dakinta kai tsaye ta wuce da Bahar,
Komai na dakin a gyare yake sbd babu ranar da baa Shara so biyu a kunna qamshi,
Ac ne kadai baa kunne ba sai wuta dan haka kai tsaye remote ta dauka ta kunna komai Wanda take haske ya haske dakin gabaki daya tamkar fitowan rana,
Makeken bedroom ne dayake dauke da royalbed me kyau da girma sosai sai Sauran set din royalbed din su wardrobe da dresser tareda bedside da wata lallausan Turkish carpet da table sai couch masu Laushi da tsari,
Duk wani jin dadi da tsarin dayake bayyanarda Hutu da kwanciyan hankali shine a dakin komai a tsaf ga sanyin ac din ya fara ratso wa yana kokarin Kama dakin.
Zaunar da ita Maa sakinah tayi tareda zare mata rufar kanta a hankali gashinta dayake rufe ya zubo a hankali yana bayyana Maa ta sake sauke ajiyan zuciya tana kallan baiwar data shigo dakin dauke da babban tray da kayan sanyi da fruits masu sanyi ta bude baki tace
‘Ki hada ruwan wanka masu dumi’
Gyada kai baiwar da ake da Salmah tayi tana ajiye tray din ta juya kanta a qasa ta nufi toilet din dayake dakin na Maa ta shige dan hada ruwan wankan.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
71
Ruwan wanka me tsafta,qamshi da dumi aka hada mata Maa sakinah ta taimaka mata har bakin toilet din ta shigar da ita ta Baro bathroom din ta kalli Salmah tace ta taimaka mata gurin tubewa da nuna mata komai.
Salmah ce ta shiga har ciki ta taimaka mata sosai a gurin nuna mata komai da sabulun da zatai wanka dashi me qamshi da kyau da tsada tukuna taje ta kawo mata towels har guda biyu masu dan girma kafin ta fice dan zuwa hado mata abincin da Maa tace a hado mata.
Duk da baa irin wannan daular da duniyar ta tashi ba batada duhun kai dan haka a sanyaye tayi wankan ta fito tareda alwala tana daure da towel daya ta rifo jikinta da Wani Dayan gashinta dayake a sake har lokacin duk ya dan jiqe.
Tana qarasowa Maa sakinah ta miqe ta kamota ta zaunar a gaban mirror tana goge mata fatar jikinta da towel din cikin kulawa tareda bude baki a sanyaye da nutsuwa tace
‘BAHAR,Bahar kiyi hakuri ki zama me tawakkali da karban kaddarar ubangiji a dik yanda tazo miki,
Mahaifinki bake kadaice kikai rashinsa ba Muma mun rasa Wani bangare ne na jikin mu rashinsa a wannan duniyar,
Muna tsananin kaunarsa fiyeda kanmu amma Allah baiyi zamu sake cigaba da rayuwa ba ya rabamu dashi a daidai lokacinda muke saka ran mun sake haduwa,
Addua da dangana itace kadai abinda zaki sakawa iyayenki dashi,
Karki manta dangana da hakurin da zakiyi shine zai baki kwarin gwiwa da nutsuwar yi musu addua da fatar rahamar ubangiji ako da Yaushe dan haka a yanzu sassautawa zuciyarki kada ki saka quncin dazai hanaki ringa aika musu adduar ki ako yaushe,
Anan cikinmu kinsani rayuwar gata da kauna zakiyi sbd muna tsananin so da kaunarki,
Ki saka a ranki cewa ke din hasken rayuwa da idaniyar mu ce koda baki ga hakan daga kowa ba a yanzu zaki gani daga gareni kafin yan uwan mahaifinki susanki susan ke wacece,
Ke Amanata ce da zan bawa kowace irin kauna da kariya da karfina da rayuwata,
Ke hasken idaniyata ce da zuciyata Bahar ki Bari na kaunaceki kaman nice na haifeki da cikina idan har kika sassautawa zuciyarki banason ganinki a wannan yanayin.’
Qarasa maganar tayi tana goge mata kyakkyawar fuskarta me daukan ido sbd bata shiga rana Sam a cikin duhun masarautar GHAZ ta tashi ta rayu ta kuma girma da towel tana daukan body oil na Neutrogena tana shafa mata a jikinta cikin kulawa da gata.
Tana gama shafa mata ta Kama gashinta dan busar mata dashi inda yake a jiqe kafin ta Kama mata shi ba sosai ba da band.
Babu Kayan da zata bata tasaka sbd kayansu bazasu mata ba su manya ne ita kuma budurwa ce me qaramin jiki hakama batada ikon bata wasu kayan ta saka idan ba Wanda duk Wanda baida matsayi yake sakawa ba a masarautar dan haka rigarta me tsayi ta bata hakanan ta saka tukuna ta tashi tafara sallah ita kuma ta fada toilet dan wanka da sallah.
Sallolin dake kanta tafara jerowa a hankali harta kammala ta daga hannu zata fara addua kawai Wani irin kuka me tsananin karfin daya ratsa zuciyarta data qame jin Wani irin azababben radadi na ratsata ya kubce mata ta cusa fuskarta a tafin hannuwan tana wata irin jijjiga kukan na tsananta sbd ta tabbata dai ta rasa mahaifinta dashi kadai ne ya rage mata,ta rasa Abaa dinta sai lahira,
Ta rasa rayuwarta,ta rasa haskenta,ta rasa hope da kuzarin da shi kadai gareta a dare daya,
Abaa ya tafi yabarta a duniyar da batasan komai da kowaba idan bashi ba gashi ta tsinci kanta a inda batajin zata iya rayuwa.
Kuka takeyi sosai mai tsima zuciya da tada tsigar jiki tana jin kirjinta na mata Wani tsananin ciwon da kaman gangar jikinta bazata daukaba.
Maa dake toilet tana jinta tayi shiru jikinta na mutuwa da tsananin tausayinta da jin kaman ta zare kuncin Bahar din ta dawo dashi kanta sbd yarinyar ta samu sassauci da nutsuwan zuciyar da bata taba samuba.
Kasa fitowa Maa tayi ko bayan data gama komai sbd bawa Bahar din damar fidda kukan quncin dayake zuciyarta tin jiyan da mahaifinta ya bar duniya.
Sai Bayan mintina masu tsayi ta fito itama idanuwanta jajir ta zauna ta shirya tana gamawa gefen Bahar din tazo ta tada tata sallar a natse.
Shiru Bahar din take Zaune idanuwanta sunyi jajir sun kumbura hancinta ma yayi jajir sbd kuka ta samu dan sassaucin nauyin daya danne kirjinta ta Lumshe idanuwa tareda kwantar da kanta a hannun couch din dayake gefenta.
Maa ma tana gama sallar aka fara shigowa da abinci aka a gabansu nan qasa kan carpet din dasuke,
Kallan Bahar Maa tayi tana zuba mata abincin Wanda yake lafiyayye da vegetables tareda fruits da madara me Zafi da zuma tace
‘Bahar kici abinci kinji’
Bude idanuwanta tayi ahankali cikin sanyi tareda tasowa daga kwancen da kanta yake sbd Sam rayuwarta bata iya gaddama da hayaniya ba dan haka bazata iya tsayawa cewa aa ba Maa din taci gaba da rokonta ya zamansa anyi hayaniyar hakan dan haka kai tsaye juyowa tayi jiki a mace tareda dago manyan idonta da sukai ja ta kalli Maa sakina a sanyaye.
Jin dadi Maa tayi har cikin zuciyarta na yanda Bahar din batai mata gardama ba dan haka apple tafara yanke mata fatar ta bata kafin ta zuba mata abincin jikinta har rawa yakeyi sbd sauri Wanda ya saka Bahar ta zuba mata ido tana kallanta tausayinta na shigarta dan haka takai apple din bakinta ta fara ci ahankali.
Abincin ma a bakinta Maa sakina a ringa bata har taci bada yawa ba
Maa ta dauki madarar me Zafi ta bata Tasha itama kafin itama taci abincin a natse tana gamawa aka fice da kayan.
Sallar ishai da akai ne ya sakasu miqewa suka gabatar da sallar a tare,
Suna gamawa sukai shiru a Zaune babu me cewa komai har tsawon sama da awa daya zuwa lokacin Wani gajiyayyen baccin dole ya dauke Bahar a gurin sbd maganin dayake cikin madarar na saka bacci sbd zuciya da kwakwalwanta su samu hutawa daga qunci idan ta farka zata ji sassaucin komai insh Allah.
Salmah ta kira ta Kama mata ita suka kwantar da ita a lafiyayyan gadon dakin Maa ta rufeta da bargo me tsananin Laushi ta zauna gefen gadon ta tofa mata addua tukuna ta miqe ta fice daga dakin dan waya da tenya data kirata tana sallah.
Palo ta dawo ta zauna a natse ta saka kiran tenya din wadda tariga ta Baro asibiti itama ta dawo masaukinsu.
Waya sukai sosai tsawon lokaci Akan yanayin jikin Ayanaah har suka gama ko kadan Maa sakinah bata fada komai daya danganci Abaas bama bare rasuwarsa bare ma azo kan Bahar wadda zata rayu a hannunsu tamkar matsayin baiwar masarautar sbd kawar da kowace irin zargi da bincike akanta dan haka kafin ma su dawo zata kula da ita da bata kauna tareda tattali.
Suna gama wayar Zaunawa tayi na dan lokaci tana duba abubuwa a wayarta kafin ta tashi ta koma dakin tayi abinda zatai ta kwanta Dayan gefen gadon cikin nutsuwa tana kallan fuskar Bahar dake bacci sosai a cikin sanyi da nutsuwa.
****Washe gari da safe da dan sassaucin data tsammata Bahar ta tashi dan haka taji itama ta sake samun nutsuwa,
Breakfast sukai a tare kaman jiyan a bakinta ta bata kafin ta hada mata ruwan wanka da kanta wannan karanma itace ta taya Bahar din ta wanke matan kanta tas Wanda yayi qura kafin ta fito tabarta tayi wanka ta fito.
Busar mata da gashinta tayi ta sake bata rigarta ta saka wadda tayi mugun yi mata yawan gaske amma tinda babu inda zata fita hakan ba damuwa bane.
Shiru suka wuni tsit babu dogon motsin komai sbd Sam Bahar bata iya maganar komai idanuwanta koyaushe a guri daya suke tsayawa da tinani Wanda hakanne yake saka Maa sakinah damuwa dan haka tafara kokarin ajiye tata damuwan tana Janta a jikinta sosai tareda ringa mata hirar mahaifinta tin yana yaronsa.
Da wannan tafara saka Bahar din ringa bata dukkanin hankalinta sbd koyaushe hirar mahaifinta idan zaa wuni a kwana Ana mata baa gajiya dan haka tafara sabawa ahankali ahankali da hirar Maa sakinah wadda ta dage sosai da nunawa Bahar menene kauna da walwala.
Kullum tana waya da tenya taji yaya jikin Ayanah wadda ayanzu ake maganar sati uku da rasuwar Abaas din amma bata farfado ba.
******lokaci da kwanaki sosai sun tafi Wanda ya saka kauna me sanyi da sabo tareda yar shaquwa shiga tsakanin Bahar da Maa sakinah wadda ta fara kawo wata rayuwar cikin matacciyar rayuwarta datake ganin bazata taba gyaruwa ba.
Maa sakinah ta sakata bude mata zuciyarta datake a kulle ta shige sbd itace mutum ta farko dataji tana yiwa kauna da shaquwa Bayan mahaifinta kaf duniyarta sai kuma Salmah wadda itama take kulawa sosai da ita tana hayata hira da labarai bisa umarnin Maa sbd Bahar din na buqatan sabawa da mutane.
Farin ciki ne ya cike rayuwar Maa ganin Bahar din tafara kokarin fuskantar rayuwa harma tana zuwa kitchen tareda Salmah sbd tayata ayyukan dasuke yi tareda Sauran bayin bangaren na wishmah hakama tana mata magana yanzu sosai.
Ana cikin wannan halin na farin cikin da Maa sakinah ke yi kwatsam kiran tenya ya shigo mata tareda albishir me dadin cewa Ayanah ta farfado hakama tareda cikakkiyar lafiyayyar memory dinta kawai Sauran rashin karfin jiki ne data rasa ya rage mata Wanda shima insha Allah tana qarasa warware wa zasu dawo gabaki dayansu kowane lokaci.
#MAMUH
KUYI HAKURI MASOYAN ABAAS DA MASU GANIN KASHE KASHEN YAYI YAWA WANDA BANAJIN KUN FAHIMCENI KO KUN FAHIMCI LABARIN,
Amma dai koma yayane ina Bau hakuri tareda miqo taaziyata gareku Allah yaji qansa ya huci zuciyarku kunji Rabin ran Mamuh🙏💋
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali_*HAYATEEM*_
Mamuhgee
72
Yau tinda Bahar ta tashi kaman yanda take komai a natse rashin hayaniya sbd rayuwar data Saba da ita ba hayaniya dan hakanne komai nata kamar a sanyaye yake ba hayaniyar,
Aikin gyaran dakin Maa sakinah tafara sbd yanzu aiki takeyi kaman su Salmah bata iya Zaunawa shiru bata komai sbd zama a cikinsu Salmah din yana dan debe mata kewa hakama itama Maa sakinah ganin tana sakewa da fita tinani sosai idan tana zama cikinsu ya saka bata hanata ba tinda daman a cikin nasu zata fake da bata kariya batareda ansan ko ita din wacece ba dan haka sai ta barta tana komai tareda su suma suna kokarin Janta sosai tana sabawa da komai,
Kayan