Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   68 / 100

201K to 204K   out of 299.8K words

jin tayi kishin bahar din me tsananin gaske yana rufeta ta juyo ta kalli maza biyun da suka gama mutuwa akan bahar din wadda batama jin bahar din ta basu hankalinta dama zata san me suke ciki,

Tsoki taja mara sauti sosai cikin takaici da baqin ciki tana kallan Asim da farin ciki yake bayyane sosai a fuskarsa duk da ya dena kallan hanyar da bahar din tabi amma kana kallansa zakasan yana cikin farin ciki da walwala.

Akan Shuraim ta maida kallanta shima wani tsokin baqin cikin ta sauke tana jin kwata kwata ma ta gaji da gidan fitarsa take son yi.

Tinda bahar ta shige bata fitoba ba wanda ya sake ganinta tana bedroom dinta tayi wanka ta saka skinny jeans da farar loose top tayi kwanciyanta a daki tana wayoyinta da duba abubuwa a laptop abinci ma sedai tayi waya me aiki ta kawo bata har dakinta taci tana harkan gabanta hankali kwance.

Har yamma ba labari NUAB dan haka yanzu kam sun sakewarsu gabaki daya duk da a cikin zuciyoyinsu suna jin tsananin rashin jin dadi kuma har lokacin har wayarsa harya ayanah bame zuwa.

Da daddare suna kokarin fara dinner a table yauma sukaji shigowan mota wadda kai tsaye ta saka kowa shan jinin jikinsa sbd dai ba bahar bace tinda tana gida motarta ma tana pake.

Maa sakinah ce ta baro dining din hakama tenya suka dawo palo tareda baro su Leylah can wainda suka fara cin abinci daga Shuraim har Asim hankali kwance da farin cikinsu.

Bude kofar akai kai tsaye aleey ya sake bayyana kaman jiran sedai babu NUAB din a tareda shi ga mamakinsu luggages din da suka tabbatarda na NUAB ne sbd tsarinsu da sanin tsadar da suke screaming aleey ya fara shigowa dasu bayan ya tsaya a gabansu cikin girmamawa me karfi ya gaidasu yana sake tambayar Ammi ta dawo??

Ganin ba tare ake da NUAB dinba ya saka tenya bude baki tace

'Aleey na tabbatarda zuwa yanzu kai kasan bata nan kuma mun kasa samunta a waya kwata kwata dan Allah kada ka bari NUAB ya dawo nan wlh yana dawowa zai iya sanin abinda kansa bazai dauka ba.'

Kasa kallanta aleey yayi sbd girmamawa kafin yace

'Maa banda abinda zan iyayi sbd tin acan nayi kokarin hana zuwan tinda yaxo da kansa koma menene zai sani sbd ya kamata ya sani din'

Maa sakinah kuwa mutuwa jikinta yayi da sanyi ta tabbatarda akwai matsala babba dan kuwa dawowan NUAB gidan batareda cewa komaiba kasawa zaiyi ya tsare ya ganewa kansa lokacinda Ammin zata dauka ta dawo daga koma ina ta tafi kuma ta tabbatarda hakan da yayi yana nufin bazai sake tambayar kowa komaiba kawai da kansa zai tabbatar kuma hakan alamar ya gama kai qarshen bacin rai da fushi me zafi akansu.

Masu aiki biyi Maa sakinah din ta kira ta je ta dauko card din bude palon da basu taba shiga ba wanda master bedroom na gidan yake ciki sedai a bude duk bayan kwana biyu a gyara a sake rufewa,
Bawa masu aikin tayi tace suje su gyara komai da kyau da tsaftar datafi duk wadda suka sani a duniya.

Karba sukai suka tafi daman sun saba gyaran dakin dan haka wata irin gyara sukai masa a cikin kiyayewa sbd komai na bangaren kana gani kasan yafi koina a gidan.

Ba bata lokaci suka gama aleey ya isa dakin da kansa ya jere kayan NUAB din a tsarin dayasan zai san inda komai ya buqata yake dan duk inda suka tafi ko duk inda zasu sauya guri aleey bai taba sauya yanayin tsarin yanda yake aje komai na NUAB dinba dan haka duk inda yaje yana shiga dakin da duk zai zauna yasan inda zai samu komai sbd tsarinsa da aleey bai taba sauyawan ba.

Bayan gama komai seta sanyin aircon daidai da yanda LEUL din yakeso yayi ya sauya qamshin dakin zuwa blooming wolf wanda take dakin yayi daidai yanda NUAB zai nutsu dashi tukuna ya fice dan hatta toiletries nasa da duka abin amfaninsa an jeresu tsaf.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

123
Aleey na fitowa daga bangaren koda ya iso main palon su Maa din na zaune shiru babu me abin cewa hakama su Asim suna zaune suna qara har fira kafin wucewansansu batareda sun san meyake faruwa ba bama susan Aleey yazo yana cikin gidan ba saida suka gansa kwatsam a palon suka dago suna kallansa cikeda mamaki shima kallan Shuraim din yayi da mamakinsa daya kasa barin ya fito fuskarsa ba kyau duk da bazaka fada a bace da rai yake kai tsaye ba dan shi Asim ko kallansa baiyiba dan yana kokarin danne zuciyarsa ne daga musu abinda zaifi wulaqanci ya dan haka time din agogon hannunsa na blackmambaC36 ya kalla ya bude baki yace

'Sultan zai kasance anan nanda mintina kadan if you guys c......

Bai qarasa ba leylah ta bude baki zatai magana Asim ya katseta yana cewa ta tashi su tafi tukuna gobe sa dawo.

Girgiza kai leylah tayi tana kokarin mayarwa Asim din magana Aleey da baida time ya juya yabar gurin yana ficewa gabaki daya.

Securities ne yazo dasu masu karfi ya fito yafara musu bayani suna zagaye harabar gidan shirinsu na bawa gidan tsaro sbd mai qasa daya dawo gidan.

Aleey ma daya gama tabbatarda komai yayi daidai da ina NUAB din zai iya rayuwa dakin dayake daga wajen harabar ya isa daman shima an gyara masa ana gamo gyaran na NUAB ajiye ipad dasu laptop da sauran abubuwan da baya nesa ko kadan dasu yayi ya fito yaja mota ya fice gidan tareda tabbatarwa da securities kafin ya dawo da NUAB duk wanda yake cikin gidan ya fita bayan su maa da masu aiki ko waye a tabbatarda an fidda shi idan bai fita ba a mintinan da suka wuce talatin.

Aleey na ficewa gardama da fada ya barke tsakanin leylah da Asim sbd batajin zata bisa ayau din dan ganin aleey ya tabbatar mata da NUAB yana nan har yanxu kenan dan haka ba inda zata.

Asim kuwa dagewansa akan tafiya da ita sbd ya ringa fakewa da ita yazo kawowa kullum ya shigo yagaisa da bahar sabanin idan ya barta dole zai daga kafa kwana biyu kafin yazo gidan dan haka yace saita tashi.

Maa sakinah da aleey yana ficewa tabar gurin ta isa kitchen tana bawa masu aiki umarnin su sake gyara koina kuma yanzu da Sultan me boyem zai kasance a gidan sai sun kiyaye sosai sun sani,

Shai ta fara kokarin hada masa ita kuma wanda yakeda karfi a lafiyar kwakwalwa da lafiyan jiki batareda tana da wani karfin jikiba sosai sbd dawowansa gidan kadai hukunci ne me karfi ga dukkansu sbd zai tabbatarda kasawarsu a abubuwa da dama dazasu ji kunyarsa akan kasawan.

Tenya dake zaune cikinsu ma itama barin gurin tayi bama tareda ta ankare da wai fada ne sukeyi ba sbd maganarsu bata wani tashi sosai
Tana barin gurin suka fara daga muryansu wa juna suna kokarin bankada sirrinsu a gaban Shuraim wanda yake mamakinsu da fada akan abu qanqani dan haka ya bude baki yana kokarin dakatar da leylah ita datake mace yana rokon Asim din akan ya barta ko kwana daya ne iya yau tayi shikenan.

Asim da baiso hakan ba amma sbd kada a gane maitarsa a fili sai ya amince yana daure mata fuska sosai ita kuma farin cikin hakan ya sakata kallansa tana kokarin taimaka masa tace

'Bara na kira Bahar kuyi sallama da ita'

Dagowa Asim yayi ya kalleta da idanuwansa da suka dan sauya ta saki murmushi tana daga masa gira alaman ko bai gode bane?.

Dan sakin fuskarsa yayi yana daga mata tasa girar shima wanda hakan ya saka shuraim dake tsakaninsu jin wani iri sbd kaman ba yanxu suka gama fada ba harsun shirya da dagawa juna gira cikin sexy way bama tareda kila sunsaniba da manta yana guri.

Barin palon Leylah tayi ta nufi dakin da akace mata shine na Bahar shima kofarsa tana dan daga lungu kadan tana isa kai tsaye ta bude kofar dakin wanda qamshin Bahar din me wata irin ratsa kai da zuciya na hadin Oud na gyara tenya daya gama kama jikinta sbd kusan duk bayan kwana biyu tenya ke gyaranta shiyasa hatta fatar jikinta koyaushe qamshi takeyi bare sitirarta da kuma dakinta ko undies nata hatta jerin handbags nata kamshinta sukeyi sbd sun riga sun kama.

Sanyin aircon ne da qamshin suka daki fuskar Leylah tareda shiga hancinta kai tsaye ta dago a yanayi na tsananin mamaki da mutuwan da jikinta yayi na kamshin kadai data shaqa ta kalli cikin dakin wanda komai yake a tsare da tsarin wayewa da turawa da kuma gata da luxuries da koina ke nunawa.

Akan Bahar din dake tsaye gaban mirror ta daure gashinta da band sako sako sbd tayi shirin bacci already kayan bacci ne a jikinta na riga da wando masu santsi maroon mai kyau dataiwa fatarta kyau sbd duhun kalar.

Ita kanta Bahar juyowa tayi a hankali da wata irin nutsuwa tana kallan kofar da aka bude kai tsaye,
Ganin leylah ya sakata mamaki sosai amma bata nuna ba ta baro jikin mirror din tana tahowa a cikin takun nutsuwanta data zama tamkar jan ajinta.

Kasa dauke idanuwa daga kanta leylah tayi tanajin hankalinta kaman yana tashi da halittar datake gani gaban nata tana tinkarota.

Bahar bata qarasa har gabanta ba ta tsaya tana dauke kallanta daga kan leylah ta bude baki a natse tace

'Zaku tafi ne??

Sai a lokacin leylah ta iya hadiye wani 'dacin daya mamaye bakinta tana dan dauke kallanta daga kanta tace

'Yes zasu tafi ni ina nan sai bayan kwana biyu zan tafi so gasu can zasu tafi'

Dan shiru bahar tayi na jin leylah na nan har kwana biyu bayan sam basa jituwan da zasu iya kwana biyun a guri daya amma bata nuna komaiba ta basar tace

'Ok' a taqaice tana juyawa zuwa ina wayarta da sauran su ipad dinta suke ita kuma leylah juyawa tayi kafin zuciyarta ta buga da baqin ciki ta sanar musu ta fada mata tana zuwa.

Bahar kuwa tinda ba cewa leylah tayi ana nemanta ba batai yunkurin tafiya ba sbd ta dauka kawai ta fada mata ne zasu wuce,

Wayarta ta dauka tana kallan time taga 8 ta wuce kuma take taji gidan yana fita ranta sbd batason hayaniya ko damuwan da suke shiga a baya na zama guri daya da leylah dan haka taji inama baa samu matsalar bayyanar NUAB ba a jiya data tattara ta tafiyarta hostel har sai ankwana biyu leylah ta tafi,

Wayarta ta dauka ta saka kiran Neesah ta rarrasheta tazo ta tayata rokarsu Maa akan su tafi hostel gobe sunada wani class tinda sassafe karfe 7.

Tana saka kiran Neesah din itama tana kokarin komawa hostel kenan daga fashion house nasu da bahar din bata samu zuwa ba yau dan haka tana fada mata tace me motar ya juya da ita zuwa gidan akan koda baa barsu tafiyarba ita Neesah zata tsaya ta taya bahar din kwana biyun.


Su Asim jira suketa faman yi na fitowan bahar amma babuta shuraim sai sake son jiran ta fito yakeyi duk da yana kallan time sosai sabanin Asim da duka hankalinsa ya tashi yaji tafiya yakeson yi tin kafin NUAB din da akace ya iso gidan ya sake samunsu shi yanzu bayason matsala a rayuwarsa da kaddara me muni dan haka gwara ya lallaba ya samu bahar din da salama.

Mintina ashirin da biyar ne suka cika take akai Knocking kofar data saka Asim miqewa bai jira komaiba ya nufi kofa yana kasa yiwa su maa saida safe ma,

Shuraim ma miqewa yayi yana bin bayan Asim din yana jin da kaman ya sake aikawa kiran Bahar din ita kuma leylah dazai aika ma tana kitchen da rawar jiki ta saka hannu aikin hadawa NUAB din duk abinda ake kokarin hada masa sbd itace take son takai masa idan yaxo sbd su gaisa.

Bude musu kofa security guard din yayi batareda ma ya iya ce musu komaiba ya basu hanyar datake seti da gate na ficewa gidan alaman su saka kai kawai.

Asim dayake gaba saukowa stairs na kofar yafara yi wanda yayi daidai da bude gate din dakai hasken mota ya haskesu tas suna fitowa da saukowa zuciyarsu na dan shiga shakka.

Qarasa shigowa da motocin guda biyu masu daukan ido duk da dare ne amma akwai haske daya saka ake iya ganin ba kudin banza ya siyesu ba akai harabar gurin ana parking nasu a natse.

Asim bai tsaya ba ya fice gate din gabaki daya,
Shuraim ne yaso tsayawa ya gaida Sultan din Aleey daya fara fitowa ya sanar dashi yaje yanzu ba lokacinda ya kamata bane ya bari sai wani lokacin.

Shuraim na jin hakan ya saka kai shima sbd a yanayin aleey kadai ya gane akwai bacin rai,

Suna ficewa aleey ya sanar da security a rufe gidan a kuma rufe shigowan kowa a gidan saida bincike da izini.

Budewa NUAB din kofa yayi wanda kallo daya idanuwansa sukaiwa Su Asim din dake fitowa a lokacinda motarsu ta sako kai gidan ya dauke idanuwansa daga kansu sbd zuwa yanzu ya gama fahimtar mutanen dake cikin gidan makashi sukeson ya zama.

Fitowa yayi a kame yana nufar ciki kai tsaye idanuwansa a take sukai mugun sauyawa amma baice komaiba bai kuma nuna komaiba wanda duk wanda yake karkashinsa yasan ya harzuqane take da fushi da bacin rai duka wanda wannan gidan dai da ba iyayensa ne a ciki ba dukansu mata da ko waye yake maida gidan tamkar gidan gala da tin jiyan bazaiga safiyar yau ba sbd zai zama makashinda dai suke son ya zama.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

124
Ko daya shigo palon tsit yake sai masu aiki dake sake gyarasa daman fitar su Asim din suke jira kuma kaman sunsan sultan din yana hanya suna ficewa qamshin palon suka fara sauyawa daga qamshin su Asim din suma me tsada daya kama palon.

Kuma dayake ba wata gyara da palon yake buqata sbd dukansu ba yara bane maza ne masu nasu ajin da wayewa da ilimi kawai dai dan abinda baa rasaba sukeyi.

Suna jin bude kofar aleey kadai suka iya gani sukai saurin zubewa qasa batareda ma sun bari idanuwansu sun kalli wanda kallansa tafi karfin idanuwansu suna sauke kansu qasa da tsananin girmamawa suna yin tsit sbd basuma da damar bude muryoyinsu a gaban sultan matiqar ba an buqaci hakan daga garesu bane.

Qamshinsa ne ya ratsi palon yana doke nasu Asim din dama wanda aka kawar danasu dashi ya sauya niiamar palon bai tsaya ba bai kuma ko kalli inda bayin suka zubeba sbd baima lura dasu ba jininsa tafasa yakeyi me tsananin datake bayyana a fuskarsa sbd jan datai musamman kunnuwansa ya wuce kai tsaye dakinsa.

Yana wucewa suka miqe a take suka bar palon kuma suda sake barin ya gansu shikenan,

Aleey ma rufe kofar yayi ya juya ya fice ya nufi dakinsa bayan ya qara tabbatarda karfin umarnin daya bata akan kowane irin baqo bazai shigowaba batareda izininsa ba.

Bayin na shigowa kitchen suka sanar da maa sakinah sultan me boyem ya iso yana gidan,

Shiru tayi kafin tace musu su tafi kawai sai kuma gobe su fito aikinsu daga dakinsu.

Suna barin gurin ta qarasa hada komai da zata hada ta fiddo shi dining ta ajiye tana nufar daki ta sanar da Tenya da batada aiki sai faman kiran ayanah ta fada mata NUAB yana gidan.

Leylah kasa zuwa dakin Bahar tayi hakama bazata iya zama a cikin su maa ba dan haka dakin Ammi ta tafiyarta ta zare kayanta ta fada wanka sbd shirin bacci bayan ta tabbatarda ta gaisa da NUAB.

Tinda ya shige babu wani motsi me karfi daya sake tashi a gidan ko hayaniya sbd kiyayewa dan haka koina ya dauki tsit wanda har bahar datake dakinta hakanan taji kaman koina din yayi tsit batai wani mamaki ba sbd tasan kila su Asim dinne sun wuce dan haka time ta kalla har 9 ta wuce kuma har lokacin bataga neesah ta iso ba dan har kusan kayanta ta hada a qaramar suitcase me kyau,

Fitowa tayi daga bedroom dinta daga ita sai kayan baccin nata tana duba wayarta dan kokarin sake kiran neesah hankalinta kwance,

Jin tsit din yayi yawa kuma tin karfe 9 batareda dare yayi sosaiba yasakata fasa saka kiran tana kallan koina kafin ta nufi kitchen zata saka masu aiki su dafa mata madara da zuma ta tadda babu kowa anma kashe hasken kitchen din dan haka fitowa tayi zata nufi dakinsu Maa idanuwanta suka sauka akan hanyar dining room ta hango kayan teaset a jere dan haka juyawa tayi ta nufi can tana fatar tea dinne tasha.

Tana isa ta miqa hannu ta taba taji da zafi sosai take ta san akwaisa kuma da alama baa dade da gama hadasa ba dan haka zaunawa tayi ahankali ta dauki cup ta zuba sosai a ciki ta dauka tafara sha a natse.

Kurban farko datai jin tayi taste din kaman yayi mata karfi amma sbd hankalinta yana kan wayarta saita cigaba da sha bata ma ankaraba harta shanye tas ta qara ta shanye tana kokarin qarasa shanye na karshen kiraj neesah ya shigo mata ta miqe tana hada wani irin zufa ta nufi palo dan tinanin ta iso amma ga mamakinta bata ganta ba dan haka ta daga wayar kafin tace komai neesah tace 'ki fito kigani'


Kofa ta juya ta nufa tana mamaki kawai ta bude kofar tana kokarin fita batareda tasan tarin securities dake harabar gidan ba da suka hana Neesah shigowa taga hannu unexpected ta bayanta ya zuro ya dafe kofar da harta bude ya maida kofar ya rufe batareda cewa komaiba idanuwansa da tin jiya suke kokarin riqe fushinsa me tsananin gaske jajir dasu kayan jikinta yayiwa kallo daya ya rintse idanuwan ya sake budesu batareda kallanta ba tafasar jininsa na qaruwa.

Ita kuwa kasa motsawa tayi numfashinta na tsayuwa cak sbd qamshinsa da dumin numfashinsa ta bayanta daya sauka akan fatar bayan wuyanta datake bayyane sbd qaramar hula ce kawai a kanta.

Muryan Neesah ce da bata kashe wayar ba ta bayyana zuwa kai tsaye cikin kunnuwansa tana cewa

'Bb ki fito coz bansan meyake faruwa ba securities koina a gidan naku kawai ki fito muje din da safe saimu kira Liverpool mu fadawa Ammi...

Kasa motsawa tayi tana sake samun daukewan numfashi sbd yanda taga hannunsa dayake gaban fuskarta akan kofa yana sauyawa zuwa ja jijiyiyin cikinsu na dan bayyana

68 / 100