Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   64 / 100

189K to 192K   out of 299.8K words

sakata saukowa daga gadon datake idanuwanta a rufe ta koma gurin mahaifinta tin kafin ta iso gabansa ta zube qasa jikinta na tsananta rawa tafara rokonsa cikin mummunan tashin hankalin daya sakasa cewa mum dinta ta jata su tafi kawai bayason jin komai.

Tana jin hakan kanta ya qarasa zarewa gabaki daya ta fara wani irin kuka tana jin son barin duniya kawai,

Janta Zuhrah tayi akan dole suka koma daki wanda har lokacin wani irin kuka takeyi tana jijjiga sbd batajin zata iya zaman aure da kowane namiji har abada idan ba NUAB ba,
Idan NUAB dinne yace bazai auretaba tafison abarta ta tsufa harta mutu tana jiransa har yayi raayin auren nata amma bazata taba iya auren dan uwansa ba wanda tana aurensa batada sauran hope ma sbd aurenta da NUAB ya gama haramta kenan matiqar Asim din yana raye...

Rungumeta zuhrah tayi da sauri a jikinta tana qanqameta sbd ganin yanda jikinta ke wani irin bari yana fizga sbd tsananin tashin hankali da baqin cikin dake neman buga zuciyarta a banza.

Kukan datakeyi ya wuce na hankali dan haka jikin zuhrah yafara sanyi tana jin fargaba na shigarta dan kuwa da gaske kila mutuwar zatai sbd take ta sauya idanuwanta sunyi jajir ba kyan gani,

Rungumeta zuhrah ta sake yi tana kokarin rarrashinta sedai ko jinta leylah batayi.

****Asim shima a ranar Yayarsa Neesa ta iso boyem sbd auren tareda yayanta duka dan haka dole ya fito sbd babban 'danta daya samesa har bangarensa ya gaidasa sukai fira sosai wanda a bakinsa yake jin maganar auren wadda bai fahimtaba sam duk da yayi mamakin zuwan nasa katsam amma sam bayajin a daidai yaji maganar dan haka ya dan sake kallan Farhan din yace

'Kace hidimar aure kukazo??

Gyada kai yayi yana ajiye wayarsa gefensa ya sake kallan uncle din nasa yace

'Eh,naso ma zuwa tin shekaran jiya kafin su Maamah su iso flight ne na baro germany ban samuba zuwa gida dole sai daga baya na samu shiyasa dole na jirasu muka taho tare'

Asim still bai gane ba dan se bai sake magana ba sbd baya ma son farhan ya gane halinda yake kokarin shiga dan haka yabar maganar har saida farhan din ya wuce tukuna ya shirya ya baro bangarensa kai tsaye bangaren sultan ya fara zuwa ya gaidasa cikeda girmamawa wanda sultan ya kallesa da mamakin yanda ya koma tamkar wani sakarai sbd kome mahaifiyarsa ta dora akai hawa yakeyi batareda tinanin komaiba duk da hakan ba illa bane amma kasancewansa namiji ya kamata yasan wani tinanin da aikin na mata ne kadai koda kuwa uwa ce.

Babu wata sauran kwana kwana ko boye boyen dayasan haile nayiwa Asim din ya sanar dashi halinda ake ciki akan daurin aurensa da zaayi banda goben kuma ya tabbatar masa da baya buqatar kowace irin hayaniya ko wani sabon zance ya tashi ya tafi kawai yaje yayi shiri.

Yanda sultan yayi maganar a daure da kaifin umarni ya saka Asim kasa cewa komai yai mutuwar zaune yanajin duniyarsa na juyawa,

Ta jima zaune bai iya motsawa ba kaman gunki kafin ya motsa daqyar ya miqe ya fice zuciyarsa na wata irin tafasa da radadin dayake jin kaman gangar jikinsa zata kama da wuta sbd mameensa ta rifesa tayi masa abinda ya mugun ruguza zuciyarsa akan ayyukanta daga yau hakama ta kashe masa sauran hope na rayuwar dayake dashi dan kuwa har abada bazai taba so ko rayuwar aure da kowace macen da ba Bahar ba,

Bahar yake so kuma akanta yake shirye da mutuwa dan kuwa tinda ba aminta NUAB yayi ya amsa aurenta ba ya tabbatarda zata fito idanma bata fito dinba kenan dan haka bai taba cire rai daga mallakarta ba,
Me zaiyi da wata 'yar yunar wadda NUAB ya gama cewa baya so shine zaa liqa masa to shima baya so sam baya kauna,

Tsananin bacin rai da baqin cikine me girma suka cike zuciyarsa da idanuwansa dayaje jin inama ya bude ido ya gansa a inda shi kadai zaiyi rayuwa batareda kowaba sbd baqin cikin da sukai masa,

Fasa zuwa bangaren mahaifiyar tasa yayi sbd babu amfanin zuwansa ga abinda yasan ba fasawa zaayi ba hakama a yanzu da sultan yayi magana ko mameen tasa bata isa ta saka a fasa wannan auren ba wanda baida suna a zuciyarsa,

Bangarensa ya wuce kai tsaye tareda manyan bayinsa biyu dake biye dashi,

Yana zuwa rife kansa yayi bai sake fitowa ba hakama bai sake barin kowa ya shigoba dan umarni ya bada haka ya kebe kansa wani mummunan baqin ciki na neman kashe sa,

Haile hidimarsu kadai sukeyi sbd zuwa lokacin tasan ya sani amma tinda bai taho ba itama tafison hakan dan ko yayane koma wane halin zai shiga ya shiga ita dai ta samu a daura auren ko zata samu nutsuwan zuciya.


***bangaren leylah gabaki daya ta fice hayyacinta ta wuni ta kwana kuka har karfinta ya qare tas ko tashi zaune bata iya yi sbd jiri da ganin da batama iyayi sbd kumburan ido da fuskarta,

Zuhrah tayi iya yinta akan rarrashinta amma sam babu cigaba ko sassauci dan haka ta barwa Allah ta ringa yi mata addua gashi ta kasa fadawa Ayanah sbd kada ma Ayanah tayi tinanin tirsasa NUAB dan auren kwata kwata hakura dashi sune best ga dukkansu,

Tadai sanar mata zaa daura auren a kurarren lokacinda bazasu samu tahowa ba dan haka ayanah tace ana daura auren su taho uk din honeymoon a matsayin nata tukuicin.

Leylah na jin hakan sake shiga mummunan hali tayi,
Asim kuwa sakon na isar masa take zuciyarsa tayi naam da hakan cikin wata irin sanyi daya manta yaya take a zuciya dan kuwa damar dayake jira ta tsawon lokaci ta samu zai bar boyem kuma kai tsaye uk zashi,uk dinma kai tsaye gurin wadda Bahar dinsa take hannunta..

Wannan sakon shine ya sauya halinda Asim din yake ciki take ya dan warware yana fara shirin daya kamata yayi na auren wato gyaran jiki dana fuska irin na maza da dai sauransu.

Duk yanda akaso yiwa Leylah gyaran daya kamata baa samu cikakkiyar damar ba sbd mugun yanayin datake ciki wanda gabaki daya ma a qanqanin lokaci ta rikice ta yamutse tamkar ba itaba ta koma kaman me zaman takabar miji da 'yaya.

Duk da hakan zuhrah bata kyaletaba dole tayi mata aka dan fara yimata gyaran da zai samu sbd ko anyi baya wani bayyana dan halinda take ciki na baqin ciki da qunci.

A haka dai ba dadi bangaren Amaryar suka samu akai duk abubuwan daya kamata har zuwa daren daurin auren wanda har safiyar garin ta waye leylah bata rintsa ba taba zaune tana kukan da baida magani,

Ba kyan gani ko kadan ta tashi a safiyar daurin auren hakama ta rufe dakinta babu wanda ya ganta duk yanda akai akai tafito abin ya gagara sai kawai zuhrah tace a kyaleta,

Kafin daurin auren da safe Maa sakinah ta iso ita kadai sbd dole dayansu na buqatar kasancewa a gurin bikin yar zuhrah duk tsanani kuwa ko ita ko Ayanaah sbd sune iyayen amarya kuma iya su kadaine dangin Zuhrah dan haka zuwansu dole ne.

Ayanah bata taho ba sbd akwai abinda NUAB yayi mata ashe batareda saninsu ba na bazata iya barin qasar ba sai shekaru biyu dan haka dole ta hakura zata shirya tarban su Leylah din da mijinta acan.

**Ana gama sallar jumaa a babban masallacin qasar boyem dake cikin masarautar boyem aka daura auren na LI'ULI ASIM ALMAZZ BOYEM da LEYLAH YUNAR BOYEM wanda dubban manyan qasa da sarakunan qasashe suka sheda tareda yan jaridu akan sadakin silallan zinari masu yawa sa Sultan LEUL NUAB ya biya masa wanda ko sultan yasar bai tsammanin hakan daga garesa ba amma yaji dadin hakan sosai.

Ana gama daurin auren Asim ya koma bangarensa ya rufe yana jin kaman zai kone sbd baqin ciki da tiririn dayake,

Ita kanta leylah din ana gama daurin auren wanda kunnanta akai komai suna ji koina a cikin masarautar silalewa qasa tayi tana rintse idanuwanta da suke a jan su tana dafe kirjinta dayake wata irin zafi da quna tana jin a ranta matiqar zata samu NUAB wlh Asim saiya bar duniya.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

116
Su kuwa masarauta da mutanen dake cikinta dama wainda suka zo bikin hidima akeyi sosai hakama tini masu shirin amarya suka taho wanda ga mamakin zuhrah da maa sakinah da babu rarrashin da basuyi mata ba amma sam taqi sassautawa kanta sai gashi kaman a mafarki ta bari ayi shirin nata dan haka ruwan wankan madara da kayan qamshi da lalle aka hada mata masu karfi kafin maa sakinah ta kamata da kanta ta kaita da kanta zata mata komai.

Sosai Maa sakinah ta jiqata a cikin ruwan lallen da madara tsawon lokaci kafin ta fito tabarta ta qarasa tubewa tayi wanka.

Kodata fito dukansu suna dakin nata suna jiranta,Maa sakinah da mummy dinta dan haka cikin kulawa maa ta isa inda take ta zaunar da ita gaban mirror tana goge mata gashinta dayake daukan ido sbd baqinsa da gyaran dayasha gurin jiqon da maa din tai mata a toilet.

Tana gama goge mata gyarasa tayi ta busar mata dashi da hand dryer ta gyarasa tsaf da abubuwan da duka suka kamata kafin tabarta tashafa mai da kanta ta sake binta da wasu mayun tirarika masu qamshin dayake kashe zuciyar duk wanda ya shaqesa tukuna aka bawa masu kwalliya da shirinta daman shigowa su kuma suka fice daga dakin.

Gyarata akai tsaf kafin aka fito da ita cikik shigar asalin yar gatar sarauta datake daukan ido aka fice zuwa taron gagarumin bikin da zaayi a cikin masarautar wanda aka barar da dukiya gurin hadashi.

Haile bata damu da alaqar dake tsakanin Zuhrah da Ayanah ba wadda aka bayyana sbd tasan dai basa kaunar junansu yanda ya kamata shiyasa suka rabu tsawon shekaru masu yawa hakama wata sabuwar damace gareta ta samun makusancin Ayanaah a jikinta dan zatafi jin zafi da cutatuwa idan aka damu damarta ta hanyar qanwarta uwa daya uba daya hakama duk kaunar da zasuwa juna dole sai zuhrah tafi son yar data haifa akan ayanah hakama mijinda leylah ke aure sai yafi mata 'dan yar uwarta NUAB daya qi yarta.

Bikin alfarma aka gudanar a wuni guda wanda ya zaga koina an baza arziki an zubar dashi anyi duk wata gagarumar al'adah a ranar har dare tukuna aka gama aka watse.

Sabon bangare na musamman washe gari aka warewa Li'ul Asim da amaryarsa wanda aka zubawa sabuwar dukiyar jin dadi luxuries ne tako ina suke kuka sai da akai kwana biyu ana gyaran kafin aka kammala tukuna akai shirin kai Amarya leylah wadda tasha nasiha sosai a gurin iyayenta kafin aka kaita gurin Haile da danginta suma sukai mata tasu nasihar suna jin karfinsu da farin cikinsu ya dawo dan kuwa Asim dole yanzu zai fara dawowa a hanyar da suke buqata dan kuwa dole yana sanin wata 'ya mace zai manta da bahar sbd jin kansa a duniyar da bai taba saniba hakama a duniyar da kila itace yake kokarin son sani a gurin Bahar din tinda daman a imebēti zai karbeta.

Koda aka kai leylah bangaren mijinta babu wani tsayawa dogon bayani aka barota suna ficewa ta miqe daga babban lafiyayyan palon ta wuce bedroom din da aka sanar da ita shine nata bayan guda biyu da suke extra dayan nasa ne wanda yake hade da wani lafiyayyan palon sai dayan dayake nesa kadan da nata din wanda yake extra ko dan baqi tukuna guda daya daga can kitchen wanda yake na bayinta.

Bedroom din ta shige ta rufo kofarta tareda saka key ta fara zare kayan jikinta dake zuba qamshin da duk ya dameta zuciyarta na suya da tafasar baqin ciki ta wurgar dasu ta fada bathroom ta wanke duk qamshin jikinta da adon duka ta fito ta saka kayan bacci tayi kwanciyanta tana jin tafi Asim din matsuwa dasu bar masarautar su tafi inda zatai rayuwarta yayi tasa kafin tasan matakin dauka akansa dan kuwa bazata taba yadda daci gaba da zaman aure dashi ba.

Shi kansa Asim din baida niyar fitowa bare ganinta ko abinda ma zai tina masa da wata macen yake aure a yanzu ba Bahar ba dan haka har safe basuji ko motsin juna ba.

Washe gari bayin da aka aiko daga bangaren Mameensa suka iso dan fara aikinsu dan haka ko da sukai breakfast da sauran ayyukan har suka gama bata fitoba tana daki sai karfe goma sha daya ta fito sanye da riga da wando masu fadi sosai ta nufi dining da wayarta a hannunta tana duba sakon Shuraim dayake ta kiranta bata dauka ba tana bacci.

Zaunawa tayi batareda ko amsa gaisuwan bayin nata ba aka zuba mata abinci taci sama sama ta koshi ta miqe tabar gurin ta koma palon ta zauna har lokacin idanuwanta da fuskarta basu koma daidai ba a kumbure suke jajir sbd ko a daren jiyan tayi kukan baqin cikin ranar daren aurenta na farko ta kasance da wani ba NUAB ba dan kuwa sa NUAB ne da kanta zata kai kanta garesa dan raya masa daren amma a yanzu batajin ko hannu zata iya hadawa da Asim bare shimfida ya jira bahar kaman yanda zata jira NUAB.

Tana nan zaune shima ya fito yana fidda qamshinsa da shigar kayan shan iska shima ya nufo palon yana waya kallo daya yayiwa inda take ya wuce yana ci gaba da wayarsa sbd ganin itama ko kallansa bata dago tayiba batasan yama fita qin aurenba dan shi zai iya keta kowane irin hadari akan Bahar wanda ita ba lallai ta keta akan NUAB ba.

Breakfast dinsa yayi ya gama ya miqe ya baro ya sake shigewansa basu sake ganin juna ba sai dare wanda ko data fito ta iso dining din yana kai dan haka juyawa tayi zata bar gurin ya bude baki yace

'Ba buqatan wannan takura kan ki kwantar da hankalinki sbd ba kinsan waye a gabana da zuciyata,
Ita nake da raayin aure haryanzu kuma bazan huta ba saina tabbatarda na mallaketa a rayuwata so just calm down Miss'

Dakatawa tayi daga inda take din tsaye maganar na shigarta da qani sabon takaici da baqin ta rasa me suka gani a bahar din suke nace mata,
Koma dai menene tinda abinda take so kusan shi yake so na raba NUAB da bahar zata kwantar da hankalinta ta ingisa yayi mata aikin da zata samu abinda takeso hankali kwance.

Ajiyan zuciya ta sauke tareda juyowa ta dawo ta zauna dining din ta kallesa a karan farko wanda shima ita din ya dago ya kalla suka hada idanuwansu a cikin na juna ta fara dauke nata taba bude baki tace

'Tinda kasan nima ba kai nakeso ba to da sauki zan zauna dakai nima kafin na samu tawa mafitar a cikin taka da zaka samu'

Murmushin takaici ya sake kawai batareda ya ce komaiba yaci gaba da cin abincinsa itama tafara ci hankali kwance.

Wuni sukai suka kwana biyu babu wanda yaxo bangaren nasu aka barsu suka huta sosai dakyau kuma suka fahimci juna akan tsayawa manufa daya ba takurawa dan haka suka sake nutsuwa suka dan kwantar da hankalinsu da kwallafa rai a sabon buri me karfi.

Maa sakinah ana sati daya da gama bikin ta tattara ta komawarta sbd Bahar da koyaushe data dameta ta dawo ta dawo.

Maa sakinah na tafiya Asim da leylah suka fara gajiya da matsuwan kiran Ammi wadda tace zata kirasu su taho idan ta gama hada musu komai amma shiru ba kowane kiran,

Leylah gajiya tayi ta cire kunya ta kira Mummynta tayi mata maganar tafiyarsu honeymoon din amma zuhrah ta shareta sbd bazata iya yiwa ayanah maganar ba kuma koyaushe suna waya.

Asim daya kasa hakura kuma bazai iya cigaba da jira ba fara shirya musu tafiyar yayi da kansa kai tsaye,

Koda haile taji tafiyar da suke kokarin yi din bata damu ba bari tayi suje su yawota duniyar su dawo tukuna ta dorasa daga inda ta tsaya dan haka da kanta ta tayasu shirin tafiyar ta hanyar fara yiwa leylah sabbin shirye shiryen gyara da tsimawa da gyaran fata.

Biye mata kawai sukai akan gyaran muradi dai su samu su tafi subar boyem,

A lokacinda Maa sakinah ta koma Uk cikin mamaki ta tadda Ayanah na fama da mura me karfin gaske data kaita har kwanciya asibiti kuma basu fadawa kowaba suka boye shiyasa ma bahar da hankalinta ya tashi sosai ta takurawa Maa din ta dawo sbd ganin ayanah a asibiti ya tada hankalinta sosai ta shiga tsoro sosai.

Ciwon nata ne ya hana sam ta tada maganar zuwansu leylah honeymoon din datai alkawari saita warke,

Zuhrah ma bata saniba sbd tana kokarin waya da ita dan kada ta gane.

Sultan da NUAB kuwa kwata kwata a kwana biyun dena waya tayi dasu wanda take hakan ya sakawa sultan tinanin ba lafiya ba.

Tenya ya kira personally ya tambayeta abinda yake faruwa ta sanar dashi suna asibiti da Ayanah har lokacin sbd kaman sanyi ne ya shigeta sosai amma tafara jin sauki.

Shiru yayi kafin ya kashe wayar kawai ya ajiyeta gefensa tsawon mintina masu dan tsayi kafin ya miqa hannunsa a natse ya dauki wayar ya saka kiran kadir.

Kadir na dauka cikin nutsuwa ya sanar masa ayi masa shirin tafiya uk a kwanakin da bazasu wuce sati daya ba.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

117
Kadir amsawa yayi da tabbacin cika umarnin dan haka yana kashe wayar ya saka kiran hada tafiyar shima,

A daidai wannan lokacin Shima Sultan LEUL me boyem shirin barin qasar yakeyi zuwa Moscow sbd wani babban business meeting da zaiyi da manyan business tycoons dinsa da suka jima suna son ganinsa ba dama sbd sarautar daya tsaya daidaitawa dan haka a yanxu ya basu damar ganinsa zasu hadu a Moscow suyi meeting din dan bazai hade GHAZ business dinsa ba da sarauta dan haka a karan farko bayan hawansa mulki zai bar qasar boyem yayi tafiya zuwa wata qasar dan haka keela ne wakilinsa da zaa bari da sauran manyan masarautar da zasu kula da komai kafin dawowansa.

Koda labarin tafiyar Sultan LEUL zuwa Moscow ya riski Sultan yasar jin yayi ya samu wata nutsuwa da kwanciyan hankalin tafiyarsa a natse duk daman NUAB kome zai zama a rayuwa bazai iya hanasa duk abinda yayi niya ba kawai dai ya zauna ne a bisa umarnin nasa sbd bayyanarda zaman lafiya a idon duniya a tsakaninsa da 'dansa tare kuma da hanasu samun hayaniya a wannan lokacinda NUAB din yake buqatar

64 / 100