kanta na yin qasa.....
Hannun Ayanah dake rawa sosai ta dago ta tare fuskar Bahar din tana hanata yin qasa da kanta ta zuba mata nata idanuwan itama tareda kafe gurbin idanuwanta dasu wanda shi kadai ne kammannin Abaas dake tattare da Bahar din wadda da alama komai na kamminta na mahifiyarta ne,
Dayan hannunta dayake rawa ta daga ta kamo hannun Bahar din wanda yake dauke da lambar Abaas ta maida idanuwanta akan numbar tareda kafeta da idanuwanta dake jajir tana jin zuciyarta na wata irin karaya da rawa me karfi ta kankame hannunta tareda dago nata hannun me lamba ta hada dana bahar din ta rintse idanuwanta tareda gangaro da wasu irin hawaye masu tsananin zafin da suka sauka akan hannun Bahar ta rintse idanuwa itama nata hawayen na gangarowa sbd a jikin mahaifinta bai rasu ba sainda yayiwa jikinsa lambar ayanah a jikinsa bayan yayiwa Bahar din tasa lokuta da dama saiya hada hannuwansu ya zubawa hannuwan nasu ido yana ji a jikinsa bazai sake rayuwa da Ayanah da zuhrah ma kaman yanda iyayensu suka tafi suka barsu har abada kila shima a shi kadai zai qare ganawa da haduwansa da 'yan uwansa ta qare,
Rawa jikin Ayanaah yakeyi sosai wanda yake tsananta gudun hawayenta zuciyarta na radadin da kaman zata tarwatse ta janyo Bahar jikinta da wani irin yanayi na karfi da sarewa daga dukkanin buri ta rungumeta da karfin gaske a cikin jikinta tana fasa wani irin kuka mara sauti tana jin kowane gaba da tsigar jikinta tana karba da Jin bahar a cikinta tana jin tamkar Abaas dinta ne a jikinta sbd jin jininsa a jikinta ya sakata tinawa da asalin yanda dumi da qamshinsa yake a duk lokacinda ta rungumesa a jikinta tin yana qarami sosai.
Qanqame Bahar tayi tareda cigaba da wani irin kuka mai ratsa kowane lungu na zuciyar Bahar din da Maa sakinah da itama hawayen takeyi na yanda a yanzu Ayanah dole zata san Abaas dinta baya duniya bazai taba dawowa ba bazata taba ganinsa ba harta bar duniya kaman yanda take fada sedai ta kalli jininsa daya bar mata Bahar wadda batada kowa a yanzu bayan Ayanah din da 'danta.
Tenya ma data kasa zama so takeyi taxo ta ga yar Abaas da basu saniba suka tashi aikata babban kuskuren da zai damesu har abada shigowa tayi dakin kai tsaye sai ta tarar da yanayin wanda ya saka jikinta mutuwa gabaki daya ta qaraso daqyar ta tsaya gefen Sakinah tareda kallan Sakinah din wadda ta kasa dagowa ta kalli kowa a cikinsu sbd kada ma a tambayeta Abaas batareda tanada amsar badawa ba sbd NUAB shine me alkawarin sanar da mahaifiyarsa rasuwan qaninta da kansa sbd shi kadai ne zai iya bata sassaucin halinda zata iya shiga.
Bahar hawaye masu tsananin gudu da zafi take fitarwa batareda ta iya cewa komaiba ko motsawa ba sbd yanayin datake jin yana shigarta a karan farko data ji wa mahaifinta dumin rabin rayuwarsa hakama a karan farko da wani asalin jinin daya daga cikin mahaifinta ya rungumeta taji dumin asalin kauna ta jini daga dangin iyaye,
Tsananta hawayen sukai da zuba ta daga hannuwanta biyu a hankali ta qanqame Ayanah din cikin wani irin sanyi wani irin kuka me sauti na zuwar mata sbd burin mahaifinta ya cika na haduwanta da ayanah ghaz dayake cewa ita ya haifawa ita koda basu haduba har abada ita ya haifawa yarsa Bahar,
Ayau ta hadu da ita din amma bayanan.
Kukan Bahar ya saka kukan Ayanaah tsagaitawa tana sake rungumeta dakyau tana jin asalin kauna da kowace uwa ke abinda ta haifa da cikinta me karfin gaske tana ratsata akan Bahar dan haka rintse ido tayi kaman daga sama ta bude baki tace
'Ayanah Bahar ina mahaifinki hasken rayuwata shi nake jira tsawon shekarun nan,
Shine hasken daya rage babu a rayuwata,
Abaas nayi tsananin kewa da rashinka ina yake?
Ina zan samesa?
Meyasa baizo ba ya aiko ki gareni bayan hadda shi din ina tsananin kewa da son gani.......
Kalamanta suka saka Sakinah kasa riqe kanta ta fita da sauri tana rufe fuskarta sbd wani irin kuka daya taho mata mutuwar Abaas dinma ta dawo masa sabuwar datake jin radadinta a cikin tsakiyar zuciyarta da kirjinta.
Tana ficewa ma bahar kuka me tsima zuciyar ta sake tana kuka da bata samu tayiba na rashin mahaifinta wanda ya saka kafafuwan Ayanah sanyi suna fara wata irin rawa wanda ya sakar da jikinta da sauri tenya ta iso tana tareta idanuwanta itama jajir sbd tana hango abinda ayanah din bata hango ba a tattareda da bahar din da sakinah na Abaas baya duniya kila dan haka hankalinta yayu mummunan tashi jikinta yayi sanyi ta rintse idanuwa ta zaunar da su duka biyun a kujera har lokacin hannuwan bahar biyu suna riqe cikin na Ayanaah ta kasa sakinta jikinta na wata irin rawa sosai wadda ta saka Bahar yin shiru tana tsiyayar hawaye amma ta kasa dagowa ta kalli Ayanaah sbd bazata iya fada mata Baa dinta ya rasu baya duniya ba.
Gabaki daya Ayanaah jin tayi tana rasa nutsuwa da kanta da tinaninta tareda kasa iya hakura da komai buqatan sanin inda Abaas yake kawai takeyi dan haka haka ta sake dagowa ta kalli Bahar data kasa kallanta da jajayen idanuwanta koina jikinta yana tsananta rawa da sautin daya saka hankalin tenya fara tsananta tashi ta juya ta fice dan tambayar sakinah me yake faruwa dan suyi saurin kiran SULTAN NUAB ko Sultan yasar idan ayanah tasan abinda bai kamata ta sani ba batareda shiri ba.
Tana fitowa a palon ta tadda Sakinah ta rufe fuska tana kuka sosai wanda ya saka tenya kai tsaye bude baki kirjinta na harbawa tace
'Ya rasu ne??
Fadar hakan datai ya saka sakinah sake rufe fuskarta tana jin wani irin radadin kalmar sbd haka take a tabbace,
Tenya zubewa tayi a kujera da karfi zufa na keto mata hannuwanta na dan daukan rawa sbd shiga tashin hankali me girman gaske dan kuwa koda bata taba ganin abaas ba tasan waye shi da tarihinsa da matsayinsa me girma a gurin Ayanah wanda kusan ta wani bangaren yafi 'danta ma data haifa matsayi a xuciyarta.
Cikin tashin hankalin tenya ta kalli sakinah tace ki sanar da Sultan NUAB abinda yake shirin faruwa sbd Wishmah ta tsananta tana neman rikicewa gabaki daya tanason sanin komai a gurin bahar wadda bazata iya daukan pressure dinba ta kasa fada dama ta rashin fada din.
Sakinah datasan ma hakan zai iya taba bahar sbd itama fama takeyi da maraici da ciwon rashin iyayen da rayquwar quncin data taso da ita dan haka idan Ayanah ta tsananta son sani Bahar zata iya fada mata wanda duka su biyun abin zai iya tabawa dan haka wayar tenya din dake ajiye gefenta ta dauka sbd tata tana daki ta saka kiran Aleey sbd Sultan LEUL din yanada wuya samunsa kai tsaye.
Aleey ma bako wane lokaci ba kuma kowace kira yake dagawa ba amma bai taba wasa da kira ko text din duk wanda yakeda matsayi a gurin LEUL dinsu ba dan haka kai tsaye ya daga kiran wanda babu wani tsaiko ta sanar dashi komai ta kashe wayar ta ajiye.
Dagowa aleey din yayi ya kalli NUAB wanda yake zaune a dining da aka cike da breakfasts kala kala da fruits da teas kusan kala uku zuwa hudu shima wanda sai a lokacin zaiyi breakfast din.
Farin kyakkyawan teacup din daya dauka zai kai bakinsa ya ajiye a natse batateda yayi magana ba jin aleey baice komai ba bayan kammala wayarsa wadda ya tabbatarda daga bangaren Amminsa ne tinda yaji an ambaci Maa.
Dago fararen idanuwansa yayi masu kyau da tada tsigar jiki yayi ya kalli aleey din yana dakatawa daga komai ya bude baki cikin nutsuwa da wani irin iko da kamewa yace
'Uhumm???
Dagowa aleey din yayi ya kallesa a natse tareda bayyanarda girman kulawa da girmamawansa ya fada masa komai akan Ammi ta riqe ghaz Bahar da sai ta fada mata inda Mahaifinta yake wanda zai iya zama trauma ga ghaz princess din hakama itama Ammin.
Lumshe idanuwansa yayi wani irin yanayi yana sauka zuciyarsa me nauyi da dumi wanda baiso zuwansa a yanzu ba sbd yaso ne ya sanar da amminsa rashin dan uwanta a lokacinda zai bata cikakkiyar lokacinta dan rage mata radadin daya san saiya kusan zautar da ita wanda hakan ya saka yasa tayi masa alkawarin bazata tambayesa ba kuma tayi amma a yanzu bahar datake tambaya bazata iya sanar da mutuwar mahaifinta ba wadda itama har yanzu bata gama fitowa daga tashin hankalin rashinsa ba dan ma tayita shiga tashin hankali a zuwanta boyem wanda ya dan shiga gaban halinda take ciki wand ayanzu zata iya komawa ciki.
Numfashi ya sauke me dumi mara sauti kafin ya miqe a natse yabar dining din yana cewa aleey ya dauko masa sakon Abaas din daya barwa Amminsa.
Numfashi shima Aleey ya sauke me dumin gaske kirjinsa na nauyi kaman na maigidan nasa ya fice yaje ya dauko ya fita ya sanarwa securities da fadawan dake na bangaren masu karfin gaske na sarauta cewan Sultan NUAB din yana fitowa.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
100
Gabaki daya shiryawa securities da fadawan sukai cikin tsantsar girmawa aka bude masa kofa ya fito a kame da nutsuwa da tsantsar iko da mulkin da dashi aka haifesa kwarjininsa da asalin kyansa na jinin ghaz da boyem yana hana idanuwan duk wanda yake gurin dagowa ya wuce aleey da keelah suna bayansa da wasu daga cikin fadawan mulki masu karfi su uku suka nufi bangaren Ammin tasa.
Suna shiga gabaki daya duk bayin dake bangaren fitowa sukai waje suka jeru a kofar shiga,
Maa sakinah da Maa tenya dake palon farko suna ganin shigowansa miqewa sukai tsaye dukansu a natse jikin kowannesu a sanyaye batareda kowa yayi magana ba.
Idanuwansa sauya suka fara yi sbd abinda yake zuciyarsa na halin quncin da mahaifiyarsa zata shiga ayau da zata fuskanci wata gaskiyar da bata sauyuwa a cikinta wadda daman dole wannan ranar zata zo.
Kofar dakin maa sakinah ta bude masa da kanta wanda ya saka Bahar dake kuka sosai batareda ta iya bude baki tayi magana ba duk da jijjigar da Ayanah take mata tana tambayar abaas cikin wani mummunan yanayin dagowa ta kalli kofar idanuwanta jajir sbd bazata iya bude baki itama tace Baa dinta ya rasu ba bazata iyaba batama taba fada ba sbd kaf duniya idan baa yau ba babu wanda ya taba ce mata idan mahaifinta ba,
Zubawa Amminsa idanuwa yayi yana jin zuciyarsa na sosuwa da yanayin daya ganta tin a yanzu din,
Akan Bahar ya maida kallansa wadda yanayinta yayi muni itama sbd kukane takeyi wanda bata samu damar yiba na rasuwar mahaifinta,
Dauke idanuwansa yayi sosuwan zuciyarsa na qaruwa dan haka ya tako a hankali batareda ma Amminsa tasan da bude dakin ba bare jin motsinsa saukar hannunsa kawai taji a nata ahankali cikin nutsuwa da sanyi ya kama hannunta yana kallanta da duka idanuwansa da sauyawansu yake bayyana.
Juyowa tayi da sauri tareda kasa sakin Bahar tana kallansa tanason furta masa maganar dake neman zarar da ita amma bakinta ya kasa sbd ganin yanayinsa a shirye yake da fada mata koma menene dan haka ta fara Girgiza masa kai wasu zafafan hawayen dake fitiwa daga qasan zuciyarta suna gangarowa daga idanuwanta.
Bude baki yayi da wani irin sanyayyan yanayi na karfin hali da jarumtarsa yace
'Ammi ga dukkanin Abinda kike son sani anan,
Abaas ne da bakinsa zai fada miki komai da kansa......
Kallan laptop din hannunsa tayi tayi da sauri wasu hawaye masu dumi suna gangarowa ta saki hannuwan Bahar a hankali duka jikinta na qarasa sakewa da mutuwa.
Kama hannunta yayi sika bar dakin tana tafiya kaman babu lafiya ko daya a jikinta.
Suna ficewa silalewa qasa bahar tayi tana cusa kanta a cikin kafafunta tareda qanqame jikinta tana jin inama Baa dinta da ayanah ghaz basu taba rabuwaba bare yanzu da zataji sun rabu kenan har abada bazasu qara rayuwa a tare ba.
Maa sakinah da tenya duka dakatawa sukai a palon suna kasa binsu sbd lokacine da Ayanah ghaz zaa barta ta amayar da quncinta gabaki daya.
Bedroom dinta ya kaita ya zaunar da ita dakyau cikin kulawa kafin ya ajiye laptop din a gabanta ya kunna kafin ya saka play ya dago ya zuba mata idanuwansa yana kafeta dasu hannunta daya cikin nasa ya riqe gam cikeda kauna da kulawa,
Ajiyan zuciya ya sauke ya bude baki yace
'Ammi kada ki taba manta ke musulma ce wadda Allah yake gwada karfin imaninta,
Kada ki taba yiwa Allah gaddamar imanin daya baki a matsayin musulma,
Hakama Ammi ki kalli Bahar,ki kalli Bahar,ki duba Baha.
Qanqame hannunsa tayi da karfin gaske har qumbar hannunta tana yankar fatar bayan hannnun nasa data qanqame da karfi ta fasa lallausar fatarsa har jini yana fita ahankali,
Baiji komaiba sbd radadin dayake ji a xuciyarsa na ganin halin da suke ciki ya wuce wanda take masa,
Ahankali ya kai hannunsa daya ya saka mata play ya zare hannunsa data ke kasa sakewa ya fice daga dakin sbd zuciyarsa bazata taba iya ganin halinda zata shiga ba dan kuwa ya sani mahaifiyarsa itace rauninsa na karshe.
Yana fitowa ficewa yayi daga bangaren gabaki daya sbd kunnuwansa ma bazasu iya daukan sautin kukan da zatai ba.
Yana fitowa kai tsaye yaransa suka bi bayansa suna barin gurin kwata kwata,
A daidai wannan lokacin sakon Keelah ya shiga wayar sultan wadda take gefensa ya dan waiwayo ya duba ganin sakon keelah ne yaron daya bar qasar boyem dashi tareda NUAB a lokaci daya a rana daya a jirgi daya zuwa qasa daya 'dan cikin kadir wanda ya sadaukar dashi ga sultan ya tafi yayi rayuwa a inda baida kowa sbd kawai ya taya NUAB rayuwar kadaicin dayake ciki da kuma shiga jikinsa dan sanar da kowane irin motsinsa ga sultan da baida kowace irin nutsuwa a duniya bayan ta son sanin kowane hali da rayuwa da motsin da 'dansa zaiyi,
'Dan dabai taba hadawa da kowa ba sbd soyayyar dayake wa mahaifiyarsa wadda duk duniya ba wanda ya sani ba kuma wanda zai iya shedawa hakama zai iya komai zai iya zama komai akan basu kariya da rayuwar dayasan itace zata basu cikakkiyar kariyar dasu basa tinani ciki kuwa ya hadda shirya karban kiyayyar 'dan nasa matiqar hakan zai basu kariya da rayuwar dayake musu shaawa da tabbatacen yanci ga mahaifiyarsa da batasan komai ba bayan qunci da baqin ciki.
Karanta sakon yayi kafin ya saka kiran kadir ya sanar dashi a siya tickets na tafiyarsu datake tintini a shirye renewal dinta kawai ake kashe kudi anayi sbd duk kowane lokacin zata kama tickets kawai zasu siya suyita,
Tafiya ce daya jima da hadawa lokacin yinta kawai yake jira zuwa ANJOM GHAZ wanda shine yayi alkwarin kai Ayanah ghaz qasarta garinta gidansu da kanta har gaban kabarin iyayenta da akai dana dan uwanta.
Fitowa Sultan yasar yayi a lokacin dan isa ga Ayanah wadda a shine kadai wanda yakesa taurin zuciyar sauraron kowane irin kuka da quncin rashin dan uwanta rabin jikinta da zata ji ayau din dan tsayawa ya saurari kowane irin kuka da qunci zuciyarta zata amayar dan kuwa tabbas yasan 'dan cikinta zuciyarsa bazata taba iya sauraron kukan quncin dazai tarwatsa rayuwarta ba.
Yana isowa bangaren koina na bangaren ya sake daukan tsit sbd shirun da akai tin dazu da Sultan NUAB ya fice hakama shirun da suka ji daga dakin Ayanah din,
Tsakiyar palon Sultan yasar ya keta batareda amsa gaisuwan su tenya da sauti me karfi ba cikin nutsuwa da mulkinsa ya amsa gaisuwan tasu wanda daidai lokaci wani sautin kukan Ayanah daya saka bangaren gabaki daya daukan wani dumi ya keto palon tsigar jikinsu gabaki daya ta miqe musamman sakinah data silale qasa ahankali tana lumshe idanuwanta kukanta na daukewa tsaf tanajin wani nauyi yana sauka daga kirjinta na ayau ayanah dai ta san abaas ya tafi sun samu sauke nauyin kirjinsu.
Tenya data rasa abin yi itana silalewan tayi ta zauna a qasa suna jin wani iri har a fatar jikinsu sbd sautin kukane da basu taba jin fitarsa daga ayanah din ba tsawon wannan shekarun sbd kukane dayake bayyanarda ayau duniyarta ta tsaya cak ta rasa mutumin dayafi kowa mahimmanci a rayuwarta.
Kukane dayake tabbatarda ayau burinta na jira yakai karshe har abada,
Kukane da ayau take mummunar ranar karshe ta rayuwarta.
Sultan ma wani irin miqewa gashin jikinsa sukai sbd yanda sautin kukan me tsima dukkanin gangar jiki yake ratsa kowane lungu da sako na bangaren wanda hatta bayin dake kofar bangaren yana sauka kunnuwansu zubewa qasa sukai cikin sauri suna saukar da kawunansu qasa suna sake shiga wata irin nutsuwa me sanyi da kama kai.
Bahar ma dake daki ratsa kunnuwanta sautin kukan yayi wanda baya dauke da ihu sedai zallar quncin dayake cikinsa mai tsananin gaske.
Leylah dake daki tin jiya ta kasa fitowa sautin kukan ne ya ratsata wanda itama take jin quncinsa yana saukar mata tana fitowa sultan na shigewa bedroom din Ayanaah din wanda hakan ya sakata yowa palon farko tana kallan yanda kowa ya dauke wuta idanuwa jajir .
Zaune take a qasa ta zame daga bakin gadon ta qanqame jikinta dayake jijjiga da rawar datai muni kukan na fita batareda tasan tana yinsa ba sbd abinda kunnuwanta da idanuwanta suka gane mata gameda abaas da rayuwar da yayi da haduwansu lafin barinsa duniya batareda ta sani ba,
Qanqame hannunta daya hadu dana abaas din tayi kafin rasuwarsa tanajin inama itama itace ta samu damar hada hannunta da Abaas tajisa a cikin hannuwanta kafin barinta duniya.
Sultan ganin yanda jikinta ke wata irin fizga da rawa tareda jijjigar ya sakasa qarasowa a hankali yana jin radadin nata har cikin tasa zuciyar ya zauna qasa a karan farko na rayuwarsa matiqar ba sallah zaiyiba bai taba zama a qasa ba sai ayau din a gaban Ayanaah ghaz dan sassauta mata radadi da quncinta zuwa ga tasa gangar jiki da zuciyar.
Hannuwansa ya saka suna dan rawa ya kama hannuwanta duka biyu a cikin nasa tareda bata damar jingina da jikinsa ya rungumeta da wata irin nutsuwa tana cigaba da fidda kukan mara dadin ji ko kadan a jikin nasa.
Daga sultan yasar din harsu tenya da Sultan LEUL jiran yanayin da zata iya shiga kawai sukeyi wanda aleey tini ya kira likitoci kusan uku duk sun iso suna cikin masaurautar jiran kira kawai sukeyi na shigarta wani halin doctors din su iso,
Cikin wani irin mamaki da