ikon Allah kukane da zallan kunci da baqin ciki yake qin zuciyarta batareda ta some ba ko fita hayyaci sbd karfin hali da taurin data sakawa kanta na son ta dandani kowane irin radadin da kuncin da rasuwar Abaass zata bata ya ratsata da ha hankalinta da tinanin batateda ta some ko shiga halinda radadin zai rage.
Shiru shiru har kukan nata ya dena fita tsawon lokaci kafin tayi shiru ajiyan zuciya kadai take iya saukewa mara karfi a jikin Sultan din wanda har lokacin yake rungume da ita batareda tace komaiba ya bata damar tayi kukan da duk ta buqata yi.
Wuni guda cur babu sakon komai daga bangaren Ammin zuwa na sultan LEUL hakama Sultan yasar sai daya tabbatarda ta samu wani irin dangana sbd adduoi da Bahar daya ringa tinatar mata da ita wanda ya saka zuciyarta jin danganar da bata taba tinanin samuba a irin wannan ranar.
Cikin nutsuwa sultan ya sanar da ita ta shirya a goben zai kaita har gaban kabarin Abaass.
Bayan fitar sultan babu wanda ta buqaci gani bayan Bahar wadda maa sakinah ta kawo mata ita har dakin ta fice ta basu guri.
Daga su maa sakinga har NUAB da har lokaci yake jiran kowane irin sako cikin rashin dadin zuciya shiru sukaji,
Leylah data kasa sanin meyake faruwa dakinta ta koma ta zauna bakin gado ta fasa wani kukan baqin cikin dayake cinta yana nukurkusan rayuwar ganin Bahar ta shige har dakin Ayanah shiru,
Wayarta ta dauka ta saka kiran mahaifiyarta wadda tana dauka kai tsaye batareda taji komai daga baki leylah din ba ta sanar da ita jirgin safe zata biyo zuwa boyem din a gobe.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
101
Shiru bangaren yayi wanda babu motsin kowa bare na komai har safiya ta waye Bahar na dakin Ayanah wanda hakan ya bawa Sakinah nutsuwa sosai da samun kwanciyan hankali,
Kwantar da kan Bahar tayi a kafafunta suka kwana a hakan shiru batareda kowannensu yace komai ba ajiyan zuciya kawai take iya saukewa ahankali cikin tsananin sanyin jiki da jin dumin kan bahar na ratsata tamkar Abaas dinta ne a kan kafafunta kaman yanda yakeyi a baya da suna gaban iyayensu cikin mutuncinsu da gatansu tareda asalinsu ba yanzu da dukkaninsu suka rasa asali da rayuwarsu ba duniya ta rarrabasu ga kaddara daban daban.
Ita kanta Bahar shiru tayi kawai a lafe tinani kala kala a ranta a haka suka ratsa daren har zuwa asuba.
Sallar asubar ce ta fiddo Bahar din wadda har lokaci itama leylah ta kasa rintsawa taji motsin fitowanta ta dago idanuwanta da suka qanqance ta kalli kofar tareda sauke wata wahalallan ajiyan zuciya tana rintse ido har Bahar din ta qarasa ficewa daga palon.
Dakin maa ta nufa ta shiga tareda nufar bathroom kai tsaye wanda motsinta ne ya tada Maa din wadda ta farka tana miqewa zaune tana saukowa gadon kanta yayi nauyi sbd rashin samun baccin da wuri sbd halinda suka kasance a ranar da daren.
Bata wani jima sosai ba ta fito tana kallan Maa din wadda itama ita ta kalla tareda kama hannunta kadai ta sumbata ta shafa kanta tukuna ta wuce bathroom din itama dan sallar da aka tayar a masallacin masaurautar.
Bahar dinma Kayan jikinta ta sauya zuwa doguwar riga Abayar sallah ta tada sallar.
Kusan a tare da maa suka sallame sallar sukai addua sosai dasu azkar kafin suka gama Maa ta kalleta tareda sake rarrashinta da nasihu masu kyau akan hakuri da tawakkali na maraicin da Allah ya kaddaro mata kafin ta fara sake bayyanar mata da labarin asalin waye ayanah a gurin Abaas hakama waye Abaass a gurin Ayanaah dan haka kaman ayanzu da ayanah tasan waye ita tana tabbatar mata da kaf duniya babu wanda zaiso ta kaman yanda ayanah zata sota ta kaunaceta kaman ayanar.
Suna dakin basu fito ba har karfe goma na safe sbd Bahar sai a lokacin baccin ya dauketa me karfin gaske.
Maa sakinah ce ta fito karfe goman ta isa har bedroom din ayanah wadda ta tadda a shirye tsaf idanuwanta sunyi mugun kumbara da ja hakama fuskarta tayi jajir,
Hakuri ta fara bata akan boyewan da sukai mata kafin itama ta dora da tata nasihar ta girman daukan tawakkali akan kowace kaddarar ubangiji tareda tayata murnar kasancewan NUAB mijin Bahar wanda Abaas ya sheda hakan kafin barinsa duniya.
Numfashi me dumi da mutuwan jiki ayanah kawai ta iya saukewa tareda lumshe idanuwanta tana gyada kai kawai bata iya cewa komaiba.
Tenya ce ta shigo dakin ta hada luggages masu shegiyar tsada na tafiyar da Ayanah din zatai a safiyar tareda sultan yasar bama tareda Sultan NUAB ya sani ba har lokacin sbd tsawon daren bai rintsa ba jiran kowane irin kira daga bangaren yake.
Karfe goma da rabi Sultan yasar ya aika kiran Aslam batareda sanin kowaba ya sanar da ita su shirya yau suma jirginsu zai daga zuwa india ya gama hada musu komai batareda sanin kowa ba dan yasan komai da suke ciki hakama bayason kowama ya sani dan haka kai tsaye su ya fara tabbatarda barinsu boyem kafin shima karfe sha daya jirginsa ya daga da Ayanah batareda sanin NUAB ba wanda Ayanah din tayita kiran wayarsa bata shiga kuma bata cikin nutsuwan da zata iya aikawa kiransa dan ko magana kwata kwata batason yi idanuwanta da ruhinta babu abinda yake tsananin kewa da so kamar isa qasarta garinta cikin gidansu a gaban kabarin iyayenta da dan uwanta.
Daga ita sai sultan din sai tenya da wasu bayinta biyu sai kuma securities din Sultan din masu karfin gaske.
Suna ficewa daga masarautar motocin da suka dauko yunar da matarsa Zuhrah ghaz suna isowa gate din shigowa masarautar suka shigo cikin nasu securities din tareda babban danta 'dan uwan haihuwan Leylah Shuraim boyem.
Shigowansu masarautar wadda take da dibbin tarihi me girman gaske a rayuwar zuhrah da yan uwanta ya saka jikinta daukan wata irin rawa bugun zuciyarta na qaruwa da nauyin kirji idanuwanta sukai jajir,
'Danta shuraim dake gefenta juyowa yayi a natse ya kalleta cikin sanyi da nutsuwa sbd shine kadai yasan asalin tarihin mahaifiyarsa data fada masa a lokacin daya fahimci tana cikin quncin dayake ganinta a ciki tin tasowansa bai huta ba saida yasan tarihinta kuma yayi alkawarin sadata da yar uwarta wadda dokar mulkin boyem ta rabasu sunaji suna gani.
Hannunsa ya daga ahankali ya dora akan hannunta yana kamawa tareda kallanta dan bata nutsuwar abinda yasan tana ji a zuciyarta.
Bude motocin sukai suka fito securities suka fidda kayansu zuwa bangaren masaukin mai girma yunar din.
Suna isa bangaren nasu leylah ta iso bangaren cikin tsananin kewan iyayenta da damuwan datake ciki ta rungume mahaifiyarta tana jero ajiyan zuciya.
Sakin Mum din tata tayi ts juya gurin mahaifinta shima ta dan rungumesa tayi masa varka da zuwa kafin ta koma gurin dan uwanta twin dinta shuraim suka rungume juna yana jin tausayin ganin yanayinta dan kuwa yanada labarin qin karban auren ta da Sultan LEUL NUAB yayi.
Hutawa zasuyi na gajiyan da suka debo kafin neman Sultan NUAB zuwa gobe su tayasa murnar Hawansa mulki dan kuwa suna isowa aka sanar dasu tafiyar sultan yasar dan haka dole zasu jira saiya dawo yanda ma zasu huta dakyau sosai musamman a yanzu da yunar yake shawaran dawowa boyem da zama sbd yarsa da zata zama sarauniyar boyem tinda NUAB ya karbi sarautar mulkin boyem din.
Sai karfe biyun rana baya sallan azahar mai girma sultan LEUL NUAB ya tinkaro bangaren mahaifiyarsa wanda yake tsit ba motsi ko hayaniya ko kadan sbd babu kowa,
Maa sakinah bata bangaren ta nufi bangaren babban store na masarautar gabaki daya dan dauko abubuwan abincinsu da sukai qasa tareda bayin da zasu dauko mata da abinda ake turawa dan daukowa,
Bahar ce kadai a bangaren itama bata wani jima da tashi ba sallah ta fara yi tana idarwa ta fada toilet tayo wanka ta wanke kanta kaman yanda ta saba ta fito ruwa na tsiyayowa daga gashinta ahankali fatarta na daukan ido sbd lafiya da haske.
Towel qarami ta dauka ta goge kanta ra rage ruwan kanta sosai ta ajiye ta nufi gaban mirror ta dauki turare ta shafa bayan ta dan shafa mai kadan tana jona hand dryer zata fara busar da gashinta aka taba kofar dakin a natsen daya sakata juyowa ahankali ta kalli kofar da idanuwanta masu haske da saukai wani laushin baccin data jima tayi sunyi wani ciki cikin daukan hankali.
Bude kofar yayi kai tsaye kaman yanda ya saba tareda sako kai fuskarsa fresh komai nasa kaman bai taba shiga rana ba dan kuwa sosai kwanciyan hankali da hutunsa ya bayyana a tattare dashi,
Dakatawa tayi cak daga inda take tsaye tana kallansa zuciyarta na dan sauya bugawa
Shima idanuwansa akanta suka sauka dan haka ya fara kallan dakin a kame da izza baiga kowa a dakin ba sai ita din sbd yaje baiga Ammin ba hakama maa tenya dan haka yayo dakin,
Akanta ya dawo da idanuwansa ya tsayar yana kallan fuskarta data dauke idanuwanta akansa tareda kokarin juyawa tabar dakin ta koma bathroom amma takunsa data ji me cikeda zallan izza da iko ya sakata dakatawa tareda juyowa tana qin kallansa taga ita din yake tinkarowa dan haka ta fara ja baya a natse tana qin dagowa ta kallesa duk da tana jin idanuwansa masu kaifi da azabtarwa akanta,
Bata tsayaba sbd shima din bai tsayaba sai dataji ta isa jikin mirror batada gurin sake motsawa shi kuwa a gabanta gap da ita ya tsaya cak har lokacin idanuwansa masu gasa ruwan jikinta suna kanta,
Qamshinsa ne yayi mata yawan dap hancinta da gangar jikinta bazasu daukaba ta dago ahankali zata kalli fuskarsa sai kuma idanuwanta suka kasa qarasawa ta dauke kai tana kokarin juyawa ya qara taku daya zuwa gareta wanda ya sakata yin baya tana dafa hannuwanta da gaban babban mirror din take hannunta ya taba dryer data dauki dan zafi take tayi saurin sake yar qara mara karfi tana dago hannun da sauri wanda ya kama da hannunsa daya a cikin wata irin nutsuwa da wani irin kallan daya sakata kallansa batareda tasan tayi hakan ba.
Cikin idanuwanta yakewa natsatsen kallo yana shigar da dogayen lafiyayyun yartsun hannunsa cikin nata yana kama yatsar daya dan kone din tareda qarasa matseta jikin mirror din sanyin gashinta yana fidda qamshin man datake wanke kan dashi me sanyin kamshi yana shiga hancinta ya juyar da idonsa akan gashin nata yana binsa da kallo sanyin cikinsa na sake saukar masa a fuska,
Motsawa tayi cikin tsananin sanyi tana kokarin zare yatsun hannunta daga nasa sbd yanda qamshinsa yake shigarta sosai ta dago idanuwanta masu sakasa kallanta ta kallesa zatai magana ya matse inda take jin yar zafin ta kallesa da sauri tana bude baki da sauti me tata kamewan tace
'Kada ka manta nan ba bangarenka bane na Ammi ne kuma a dakin Maa.....
Bata qarasa ba ya sake latsa hannun wanda ya sakata yunqurowa da dan karfin daya hade kirjinta da nasa take ya dago idanuwansa ya sauke mata wani kallan daya sakata kokarin yin baya da sauri tana kokarin faduwa ya tarota da cikin sanyi da kamewa tareda dawo da ita jikinsa ta fado kirjinsu ya hade da kyau suna mannuwa da juna ya a jikin madubin.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
102
Dago kanta tayi idanuwanta na dan matsewa ta qi yadda ta sake kallansa ta motsa ahankali tana sbd yanda take hade dashi sosai gashi a jikin mirror din suke sosai,
Turesa takeson yi amma yanda suke din hannuwanta ma bazasu iya shiga tsakaninsu ba bare ta iya turesa din dan haka ta daure ta sake dagowa batada xabin daya wuce daga idanuwanta ta saukesu akansa wanda hakan yake jira sbd idanuwansa suna kafe da ita hannunsa daya yana xagaye da ita dayan kuma yana sarqe da yatsun hannunta daya har lokacin.
Kallo daya tayiwa cikin idanuwansa ta cire idonta a cikinsu sbd bazata iyaba bakuma dan komai ba sai dan yanda tsigan jikinta ke tashi daga kallan cikinsu amma bawai dan tsoro ko shakkarsa ba,
Bude baki tayi zatai magana cikin karfin hali da kame fuska maganar Maa ta bayyana daga wajen palon,
Kallan kofar shigowa dakin tayi da sauri kirjinta na bugawa da karfi,
Zamewa tayi kokarin yi amma riqon bame zarewa bane hakama karfinsu ba daya ba duk da ko kwatan rabin karfinsa bai saka ba,
Kallansa tayi cikin ido ta bude baki tace
'Kasan me kakeyi kuwa?
Shigarsa kalman tayi da kyau da kaifi sbd itace kadai take wuce iyakarta gurin fada masa maganar da zata iya zama ajalin wani idan ya fada akansa,
Bai saketa ba ya bude baki yace
'Kinsan waye a gabanki??
Bakinki da kalamanki zasu iya sanadin wainda kike tareda su idan baiyi naki ba akan abinda yake furtawa.....
Turesa take kokarin yi tana dauke kallanta daga kansa da sautin hankali a kwance daga kalamansa da kuma fargaban dawowan maa tace
'A yanzu dai inaga kana buqatar barin dakin nan kafin me shi ta shigo ta sameka a cikinsa sbd......
Bata qarasa ba ya saketa ya juya a natse ya kalli kofar dakin kafin ya kama hannunta ya juya ya nufi kofar da ita zai kira Maa sakinah din ta shigo dakin ta samesa a hakan yanda bahar din take.
Da sauri taso kwacewa amma ya riqeta da kyau yana nufar kofar batareda kunya ko daya ba dan baima santa ba,
Ganin da gaske yakeyi kiran maa din zeyi ta samesu a hakan tinda tasan zai iya a yanda tasan hankalinsa dan haka da sauri suna kaiwa kofar tasha gabansa tareda dafe kofar da bayanta tana hanasa budewa idanuwanta duka biyu akansa tana kallansa da wani irin yanayin jin zafi,
Daga kafafunta ya fara kallanta zuwa samanta yana qarewa lafiyayyan farar fatarta kallo kafin ya tsayar da idanuwansa akan sarkar kafarta asalin farar azurfar data gada ta mahaifiyarta me tsananin sanyin kyau da rashin ado sosai data zauna da kyau a farar kafarta wadda itace abin farko daya fara gani akanta a ranar farko ta haduwansu a duniya a kuma ranar data zama ta farkon ta zama ta aurensa daya doru akanta,
Hannunsa daya ya miqa zai matsar da ita ya bude kofar ta miqa hannunta ta riqe nasa din batareda tinanin komaiba,
Hannunta daya kama nasa ya saukarwa idanuwansa ya kalla dakyau cikin nutsuwa da yanayin da bata iya gane komai akansa kafin ya dago ya zubawa fuskarta idanuwansa da suka jikinta da babu kaya jin wani irin sanyi na feso mata kaman ana watso mata ruwan sanyi.
Sakinsa tayi a hankali tana dauke idanuwanta akansa sbd ganin irin kallan dayake binta dashi ta sake tare kofar tana jinginar da bayanta jikinta tana dannewa idonta na qin kallansa zuciyarta har lokacin bugawa takeyi sbd idan ya kira maa dakin a cikin wannan yanayin datake kuma tareda dashi a dakin bazata iya kallan Maa din ba dan haka gwara tinda tasan sake komawa maa din zatai dauko wasu kayan idan sun sake juyawa sun koma saiya fice ta shirya batareda maa tasan ya shigo dakin ya sameta a hakan ba harma ya shigo an rufe kofa.
Yanda ta tare kofar ya tana dauke kanta daga kallansa ya sakasa rankwafowa sosai yana dafe jikin kofar da ita gabaki daya,
Ba tsammani taji saukan dumin numfashinsa a fatar saman kirjinta da wuyanta har gefen kunnenta wanda ya sakata juyowa da dan sauri sedai fuskarsa na gap da tata ashe take fuskar tasu ta hade hancinsu na haduwa tayiwa qamshinsa da numfashinsa wani shaqa me karfi batareda saninta ba take ta rufe ido tana fidda wani numfashi daya saka kirjinta yin sama tana qanqame hannun kofar ta bayanta da hannunta daya daya tsananin fara rawa.
Nata Numfashin data fitar shima ya shigesa sosai har cikin kansa da kwakwalwansa yaji saida idanuwansa suka nuna hakan dan haka ya dauke idanuwansa daga kanta yana buqatan ficewa sbd abinda yake yawo a cikin kansa da kirjinsa harma da zuciyarsa.
Hannunsa daya ya saka a bayanta ya kama hannun kofar ta sake dora hannunta akai itama tana dagowa ta kallesa idanuwanta suna tausasa da yanayin damuwan halinda zata shiga idan yayi mata hakan sbd maa din na nan har lokacin dan suna jin maganarta kaman waya takeyi.
Kafesa da idanuwanta tayi wanda yanajinsu akansa amma yaqi kallanta dan hakan nada hadari a lokacin dan haka kokarin janyeta yayi dan ficewa yakeson yi kai tsaye a dakin kwata kwata,
Wasu hawaye ne suka ciko idanuwanta ta dan sake dafewa tana kasa dauke idanuwanta akansa ta bude baki cikin wata irin sanyayyar murya me tsananin taushi da magiyar da batada zabi bayan yi tace
'Dan Allah kada ka......
Bata qarasa ba ya riqota gabaki dayanta da hannuwansa biyu ya ciro daga jikin kofar ya maida jikin bango ya jinginar da ita yana dafeta da kirjinsa cikin wata irin yanayin daya sakata rintse ido zuciyarta na harbawa da karfi ta qanqame hannuwansa batareda ta sani ba sbd tinanin jefar da ita zaiyi.
Numfashinsa ne me tsananin dumi yake sauka a fatar fuskarta da wuyanta sbd fuskarsa dake hade da tata fatarsu na gogan juna da jin dumin fatan tana rata dayan fatar.
Kirjinsa dayake hade da nata ya saka numfashinta sauyawa yana fita daqyar dan haka itama kai tsaye nata Numfashin saukar masa yayi a gefen kunnensa wanda take ya saka fuskarsa gabaki daya fara yin jan daya sakasa sakinta kai tsaye batareda ya juyoba ya bude dakin ya fice.
Yana fita kai tsaye barin bangaren yayi sbd babu wanda zai gani a yanayin da fuskarsa din take.
Yana fitowa Maa sakinah data san yana bangaren sbd taga aleey shiyasa ma taqi shiga ta qirqiri wani aikin tinda sai angama juye wancan din kafin su sake komawa.
Ganinsa babu rahama a fuskarsa hakama baida Alama ko fuskar magana da kowa ko tsayawa ya sakata bata ma fito daga kitchen din datake hangosa ba ta kyalesa.
Aleey ma na ganinsa kai tsaye ya sauke kai suna bin bayansa ba kalma ko daya data fita.
Aleey daya samu labarin Sultan me murabus Yasar yabar qasar tareda Ammi a ranar hakama ya fitar da Haile da yayanta duka daga boyem sun daga zuwa wata qasar da bai gama tabbatarwa ba tukuna, yana son sanarwa Sultan LEUL din amma ganin yanayinsa ya sakasa shiru tukuna sbd labarin zai tada fushinsa me tsananin gaske dan kuwa a yanzu dayake sultan me mulkin boyem shine yakeda cikakken ikon mahaifiyarsa fiyeda sultan yasar sbd babu igiyoyin aure a tsakaninsu dan haka baida cikakken ikonta duk da tana matsayin wishmah dinsa a yanzu shi danta dayake sultan ma zai iya