sai sunyi kusan sati kafin su fita dajin.
A wannan kwana da wunin babu wanda ya farfado a cikinsu Ayanah saida aka kuka wuni tukuna suka fara farfadowa shima sbd ruwan da aketa zuba musu ne masu tsananin sanyi.
Suna bude idanuwansu cikin Ayanah ce ta fara bude ido taga inda take cikin wani irin rikitaccen karfin da baifi ma jaririn rago ba ta yunkura tana tashi amma bata iyawa sosai,
Sunan Abaas tafara ambata cikin dan karfin datake dashi tana dudduba gefenta dataga mutane barkatai sama da Dari duk wasu a kwance.
‘Zuhrahhh,Abaas,Nurat,Sakinah……..
Haka ta ringa jerosu tana kiransu jikinta na Wani irin mummunan rawar tashin hankali.
Zuhrah ce ta fara jiyo Ayanah din da sauri itama t bude idanuwanta tana kwala sunan Ayanah din da dan karfi hankalinta a tashe ko gani batayi ta miqe tana kokarin takawa ta kife sbd kacar dake kafarta.
Bude ido tayi a inda ta fadi sai idanuwanta suka sauka Akan Abaas cikin sauri ta cakumosa tana kwala kiran Ayanah.
Ayanah gurin ta rarrafo ta iso suka rungume juna da karfin gaske suna jin sassauci.
Nurat suka fara kira itama tareda sakina sai kuwa gasu sun gani a guri daya take suka rungume juma kaman Ana partyn ‘yayan aljanu sbd yanda suke hada qasusuwan jikinsu suna rungumewa.
Can Kurya suka rakube inda baida haske sbd basason Abaas na bayyana sosai kada tsautsayi yasa a gane duk da bazaka taba kallansa kai tsaye kace ga ba macen bane suka maqale juna a zazzaune kowannesu da kaca a kafansa.
Tsoro ne zuciya da gangar jikinsu sbd sun gama tabbatarda sun Riga sun zama bayi,
Sun zama bayinda har abada basu yancin rayuwarsu sai yanda akai dasu,
Sun rasa sunansu,sun rasa asalinsu rayuwa kuma yanzu sedai wadda aka zaba ko hukuntar musu.
Bude kofar qaton dakin da suke akai daga sama kofar take.
Kallo wanda ya bude kofar yayi musu tsaf kafin ya fara Jeho musu daurin gayar tuwon alkama da akai da nono.
Masu dan karfin cikinsu take suka fara ruguwan Abinci suna tura Bakinsu cikin tsananin yunwa da ficewa hayyaci.
Sakinah ma cikin karfin Hali ta yunqura tana wawaso abincin tana jefo musu take jikinsu na rawa suka fara sararsa suna Turawa Bakinsu hannuwansu na rawa.
Zuhrah dataji kaman bazata iya tsayawaba yake itama ta rarrafa ta fada cikin wawason tana Turawa bakinta a haukace.
Abaas ma fadawa yayi hakama Ayanah da Nurat
Take suka zama kaman mahaukata kowa wawa yakeyi yana Turawa bakinsa a haukace.
#MAMUH
#BEST STORY
#BEST LOVE
#ROMANCE
#ROYALTY
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali_*HAYATEEM*_
Mamuhgee
12
A cikin Hali na wawason suka ringa Turawa Bakinsu ko taunawa basa yi hadewa kawai sukeyi yana wucewa maqoshinsu da wani irin karfin gaske,
Wani irin kuka hanjinsu keyi na samun abinda suka dade basu samuba wato abinci,
Danne juna ake yi sosai Ana yiwa juna rauni da hakan suka samu suka cika cikinsu sedai kusan dukkaninsu sun samu rauni dan haka suka rarrafa gefe suka rabe suna dunqulewa sbd tsananin ciwon ciki daya taso musu.
A kwance suka wuni ba lafiya sosai sbd ciwon ciki da lafiyarsu da daman babuta yanzu,
Tsakiyar dare haka aka sake zuwa aka kawo abincin Ana jeho musu suna wawaso sedai wannan karan ba kowane ya iya tasowa ga abincin ba sbd kusan duka dakin basa da lafiya dan kuwa duka kusan ciwon su daya ne ciwon ciki sbd dade wa me tsayi ba abinci,
Zubewa suke son yi kwance su jujjuya ko azabar ciwon cikin zai rage amma dakin babu gurin da kowa zai samu ya kwanta sedai suyi rayuwar zama a cikinsa ko bacci sedai kayi daga Zaune.
Dan haka su Ayanah babu Wanda ya iya zuwa cin abincin tsakar Daren se Nurat data fada cikin masu wawan tayita ci da hauka itama sbd rashin cikakken hankali ne kuma duk anji mata ciwo sosai hada bakinta aka fasa yana jini suna kallo babu me iya motsawa saida ta koshi dan kanta ta dawo cikinsu.
Kwantar da kansu sukai a kafadun juna suna sake lafewa jikin juna da babu wani sauran taushi na tsoka sai qashi amma su a gurinsu hakan shine mafi nutsuwa da kwanciyan hankali Jinsu a jikin juna,
Amai wasunsu suka fara wanda ya hargitsa numfashin dasuke shaqa a gurin,
Amai sosai kowa yakeyi haddasu Ayanah din saida dukansu suka galabaita amma a hakan baa bude su ba saida safe gari ya waye sosai aka bude su haka aka ringa zubo musu ruwa masu yawan gaske daga sama Ana wankesu kaman dabbobi,
Bakinsu suke budewa ruwan na shiga har sukasha sosai kafin ruka zauna ruwan na dukansu da ake zubowa har jikinsu ya wanke tas.
Kowa saida jikinsa ya wanke kafin aka fara Fiddosu daya bayan daya daga dakin ana Jere su a fili.
Babu me iya miqewa tsaye sosai sbd yunwa da wahalar data gama cinyesu,
Hasken sararin samaniya suke kalla yana kashe musu idanuwa sbd duhun da suka fito cikinsa,
Kirgasu aka fara yi Ana daya bayan daya Ana raba maza daban mata daban Wanda anan hankalinsu ya tashi tsoro da fargaba suka shigesu Ayanah ta miqa hannu cikin na Abaas da dukkanin jikinsa yake rawa sbd fargaban kada a ganesa,
Su duka rawa jikinsu keyi dan Ana gane Abaas mutuwa ce tahau kansa,
Qanqame hannunsa Ayanah tayi shima qanqame nata tayi Zuhrah kuwa mannewa tayi a jikinsa itama tana riqe sa suna kokarin hana bayyanar tsoronsu da fargabansu.
Shi Kansa Abaas zuciyarsa cikin wani mummunan Hali take na halin da zasu shiga idan asirin hakan ya tonu.
Duk Wanda aka Kirga sai an masa sheda a gefen hannunsa da wani karfen wuta.
Ana zuwa kansu Nurat aka fara fizgo wa aka kirqa baa tsaya komaiba aka manna mata karfen wuta a gefen hannu Wanda ya sakata qwalla wata gigitacciyar qara tana zubewa a gurin.
Cikin firgita Ayanah tayi kanta zata tarota tayi mummunan kife wa kanta na buguwa da katon drum din ruwan dake gurin Wanda ake watsawa duk Wanda ya sume gurin ruwa sbd azaba.
Wani Juyawa kanta ya ringa yi sbd bugawan da yayi bata dawo hayyacinta ba taji saukar azababbiyar azaba Akan gefen hannunta Wanda ya sakata somewa a gurin itama.
Motsawa Abaas yayi da sauri yana yin kanta itama shima ya kife sbd sarkan dake kafarsa hakama Zuhrah.
Anan aka mannawa kowa tasa Shedan cikin azaba suka dunqule suna fidda Wani irin zufa Zuhrah saida ta yanka Wani irin Ihun azabar da bata taba jiba,
Abaas duk tsananin azabar dayaji rana ratsa jini,tsokar jiki,qashi da kwakwalwansa kasa ihu yayi sbd Alkwarin da sukaiwa juna na har abada idan basu fita wannan ukubarba bazai taba magana aji sautinsa ba na namiji dan haka daga lokacinda ya aka saiya jinsa zuwa na mace ya koma kurman da baya magana sedai nuni.
Wasu irin hawaye masu Zafin radadi a ido da zuci ne suka gangaro masa na tsananin azabar dake ratsashi gashi shi ya kasa somewan.
Bulala aka daga me kaurin gaske ta fatar dabba aka zabga masa yayi daurin rintse ido numfashinsa na sarkewa akace ya tashi.
Da rarrafe ya koma gefen wainda akaiwa Shedan numfashinsa har lokacin na kokarin yankewa hakama yanason fasa kukan azabar dake ratsashi amma fitan sautin kukansa zai bayyana sautin muryansa datake da dan kauri ta maza dan haka haka yaci gaba da danne azabar yana hadiyewa jikinsa na wata irin muguwan rawa.
Zuhrah ma dake Ihun gigitacciyar azaba har lokacin bulala me Zafin datakai azabar wutar aka sakar mata wadda ta sakata sakin qara me rikitarwa Tana rarrafawa gurin Abaas nenam dauki.
Ruwa aka watasawa su Ayanah da Sauran bayin da suka some Ana dukansu da Bulala a haukace suke rarrafawa gefe suka fadawa kan yan uwansu.
Sakinah ma bata some ba amma tashiga kidima da fitar hayyaci azaba,
Nurat duk rashin hankalinta kuka takeyi sosai na azaba Tana nunawa Ayanah hannunta dake tsananin radadi.
Hawaye Ayanah ke fitarwa Tana rungumesu cikin azaba da wahala me tsanani suna dauriya da karban wannan sabuwar masifar da suka samu kansu kuma a ciki.
Ana gama kirgasu aka fara raba musu Abinci suna karba Ana wucewa dasu dayan dakin da Sauran bayin duka suka ciki sama da daruruwa masu shegen yawa.
A yunwace suna jin azaba suka hau cin abincinsu Bayan sun Nemi guri sun rakube a cikin dakin,
Ana gama shigo da kowa aka rufe kofofin dakin dake sama take dakin yayi duhu nan take kuma aka fara ihu da kuruwa tareda hayaniyar kokuwan masu karfi da marasa karfi gurin qwacen abinci.
Cikin tsananin sabon tsoro su Ayanah suka qanqame juna suna hadewa guri daya take sakinah ta tura Abincinta duka a baki tana hadiyewa tace suka
Suyi hakan.
Tura abincin sukai gabaki daya a baki suna hadewa cikin azaba da wahala yana yankar maqoshi amma haka suka Hadiye.
Kafin kace me gurin anji wa sama da Mutum Hamsin rauni wasu ma a qonuwarsu aka raunatasu.
Su kansu Ayanah sunsha duka da shuri na mutane kafin dakin yayi tsit Angama kokawar.
Wani Daren ne ya tsala sosai koina yayi tsit duk da basa gane dare bare rana sbd duhun inda suke dan amma shirun ya tabbatar da Daren yayi.
Babu Wanda ya samu bacci a cikinsu shiru sukai zuru a jikin juna har lokacin suna maqale,
Zafin zazzabi me karfi ne ya fara saukarwa Nurat har tana dan fizga
Hakan yasa Ayanah rungumeta a jikinta Tana Shafa bayanta Ahankali,
Itama zazzabin take fama dashi sosai amma bata kwantaba sedai jikinta da yayi Wani irin zafi sosai.
Zuhrah ma zazzabin ne ya sakata zame wa ahankali ta kwanta da jingina,
Abaas ma karfinsa lamarin yaci ya bangare a gurin idanuwansa na rufewa jikinsa na rawar zazzabin.
Sakinah duk abinda suke Ji tana jinsa amma haka ta daure ta taya Ayanah kulawa dasu duk da babu abinda zasu iya ko suke musu Bayan Shafa bayansu dan basu sassauci koma yayane.
Gari na wayewa tinda Sauran duhu aka bude kofa aka diba Mutum hamsin aka fice dasu zuwa aiki.
Dayan dakin suka wanke me tsananin girma tareda aikin tsafta ce duka Sauran koina dake jirgin,
Suna aikin suna Shan Wani irin dukan azaba a haka suka gama aka dawo dasu kafin aka fara jeho musu abincin safe Bayan rana ta dade da yi kenan.
Haka suka wuni cikin duhu da azaba har wani Daren kafin aka sake basu abinci Wanda kullum so biyu ko daya ake basu abinci.
Fitsari da kashinsu kuwa anan suke yinsa a cikinsu cikin wata qatuwar durum wadda aka ajiye a karshen dakin cikinsu sai da safe ake sakasu kwasarshi suna zubarwa a iska dan haka a cikin mugun wari da qarni da Zarni suke kwana suna wuni.
*******ahankali ahankali su Ayanah suka fara fuskanta da yadda da wannan rayuwar fa itace yanzu zasu yi har karshen rayuwarsu dan haka duk muninta haka zasu karbi kaddarar rungumarta su koyi yinta,
Hakan ne ya saka suka fara sabawa Bayan sunyi ciwon,sunyi ciwon amma gangar jiki tafara sabawa da duka da wahala,
Hakama hanci da hanjin cikinsu sun fara sabawa da wari tareda manta akwai kamshi a rayuwa,
Idanuwansu da zuciyoyinsu sun saba da duhu da qunci sbd a cikinsa suke rayuwa dip Baka ganin ko dan uwanka dayake kusa dakai Shiyasa su Ayanah basu taba yadda sun matsa ko inci dayaba daga junansu,
Ko lalurar zagayawa Fitsari ko abinda ya fisa ya kamasu tare suke zuwa da sarka a qafafunsu su jira Wanda zeyi su gama su dawo tare,
Sunayin hakan ne na zuwa gabaki daya dan bawa Abaas kariya daga tsautsayin wani ya gansa.
Rayuwar bauta sun Riga sun samu kansu a cikinta dan haka yanzu basuda Sauran Buri Bayan Allah yabar su tare suyita bautar a tare da junansu.
Ahankali yunwa ta fara barin jikinsu duk da ci daya ko biyu suke samu a rana amma sbd suna samu din dai dakuma Zaune da suke guri daya ba rana sai suka fara rage mummunar kamar aljanu da suke cikinta amma ita datti da wahala a jikinsu har lokacin qaruwa ma takeyi ba raguwaba.
Duk wannan rayuwar da suke Abaas ya zama Kurman da gaske bai taba magana ba koda tsautsayi komai wuya kuma baya fidda sauti haka yake hadiyewa musamman idan Ana dukansu bai taba fidda sauti ba ko su yan uwan nasa yanzu da hannu yake musu magana duk da magana ba basu cika yiba sbd baqin ciki da qunci rayuwa daya gama cike zukata da bakinsu babu abin fada sedai ido.
Tafiyar Sati hudu sukai a cikin ruwan kafin jirginsu ya sauka a wata babbar qasar da zasu tsaya su siyar da wasu qalilan daga bayinsu dan siyan Kayan abinci su zuba a jirginsu tukuna su wuce dan haka zasu yada zango anan na kwanaki kafin su wuce.
#MAMUH
#SLAVERY
#ROYALTY
#BOYEM
#AYANAH
#YANAH
#BEST LOVE
#BEST STORY
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
_*HAYATEEM*_
Mamuhgee
09033181070
13
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
**************
Koda suka iso qasar Boshan tsakiyar dare ne amma bakin bodar ruwan tamkar rana tsaka,tamkar Ana gagarumar cin kasuwa sbd mutane sosai da hasken wuta fitilun itace da kyandir koina fes anata cin kasuwar komai da komai a lokacin harma da kasuwar bayi ake ci wadda itace ma tafi komai karfi a gurin wato cin kasuwar mutane a matsayin bayi,
Kaman yanda ake kasa kifi a Jere Ana cinikinsa haka aka baza bayi gasunan kashi kashi daban daban Ana siyar wa,
Kason masu karfi lafiyayyu daban hakama kudin su daban,
Kason masu Yar dama dama daban suma kudin su daban,
Kason gajiyayyi daban da kudinsu suma daban
Hakama akwai Kason yan yara yara daban.
A daure suke da sarka hannuwansu da kafafunsu kowa ya Kebe nasa sai cinikayya ake yi ta siya da siyarwar,
Garuruwan dake qasar boshan din kusan dukansu kaf anan suke zuwa cin kasuwan bayi Ana kaiwa masarautun cikin qasar dan haka wakilan Masarautu ne da dama suke zuwa cin kasuwar hakama Ba Masarautu kadai ba duk wani me arziki ko dan rufin asiri idan yanada kudin sa yana siyan bawa dan hidimarsa da raayinsa Shiyasa ake siyan bayin a duniyar wannan qarnin sosai sbd duk me rufin asiri baya rasa bawa daya ko bayi fiyeda daya a gidansa dan hakan ne sosai kasuwancin bayi yake tafiya a duniyar.
Bude kofar inda tarin bayin suke akai na babban jirgin kusrah dayafi kowanne jirgin girma a nahiyar take dukkanin yawancin bayin dake cikin gurin suna Numfashi ahankali cikin wani yanayi dagowa suna saukewa tareda fidda Numfashi me dan nauyi sbd a yanda suke din numfashinsu ya cike dakin koina duk girma sbd tsananin yawansu sai numfashin gurin yayi dum babu inda iskan gaske yake shigo musu dan haka wasunsu da yawa sun Laushi sun galabaita sosai da numfashin wasuma sun fita hayyacinsu wasu kuwa harsun some.
Hakan suke rayuwar ta bayi wadda numfashinda zaka shaqa ma kusan kaman Ana qayyade musu me kyau da mara kyau ne sbd su da samun Numfashi me nutsuwa da iska sai an bude su kuka Ana gamawa ake sake rufe su.
Isowarsu ya saka kasuwar dake daukan shelar isowan kusrawa da tarin bayi masu kyau da lafiya da karfi dan haka kowa ya dakata yana rage siye siye dan Adana kudinsa na siyan bayin kusrah din.
Saida suka dauki lokaci mai tsayi suna fidda bayinsu da kowa ke fatar a nan zaa siyar dashi wahalarsa ta ragu,
Su Ayanah ma da suka fahimci rage bayi zaayi anan din a siyar taje dukkaninsu suka fara fatan suna cikin wainda zaa siyar anan su kubuta daga hannun kusrawan ko zasu samu Numfashi kadai ma ya ishesu.
Cikin rashin saa Ana zuwa kansu adadin wainda ake son diba ya kare dan haka aka turasu da karfi Ana dukansu da bulalar data sakasu rarrafawa zuwa baya aka rufe kofar.
Koina jikinsu radadi yakeyi amma a hakan kallan jikin juna sukeyi kafin duka tsayar da hannuwansu jikin Nurat dayafi na kowa fashewa suna Shafawa cikin duhu suna hura mata tana kasa kuka sai qanqame Abaas datai sbd ita rashin hankali ya saka bata ma iya kowane kuka sedai ihu idan taji azaba.
Bayi arbain suka diba aka fito dasu kowanne da tambarinsa na bayin kusrah a hannu Wanda akai musu da wuta,
Ruwa suka zuba musu sosai Wanda ya wanke daudar da suke cikinta kafin suka fito dasu daga jirgin Wanda aka bude kusrawan na saukowa sama da su tamanin suka fito dan shaqatawa da cin kasuwar dan ko shigabansu baya fitowa duk qasar da zasu idan ba babbar qasa ba dan haka duk kwanakin da zasu yi shi bai cika fitowa ba sedai manyan yaransa su ciye musu kasuwar su siyo Kayan abincin da zaa zuba jirgin dazai dauke su satittika kafin a isa wata qasar idan har ya fito to sun isa inda zasu zube bayinsu gabaki daya su siyar dan hakanne wannan Karan idan ba sun isa manyan qasashe ba ya fito ya dan sha iska ya koma to tabbas sai sun isa BOYEM zai sauko gabaki daya sai kuma sun gama sun bar qasar.
Kaman dabbobi haka aka janyo bayin Bayan an hade sarkar dake daure dasu guri daya gabaki dayansu dan haka a Jere suke kansu a qasa sanyi me tsanani yana ratsasu.
Tambarinsu na kusrah da asalinta yake ma kasuwacin bayi suka nuna tareda rubutun dake cikin busashiyar fatar raqumi suka nuna tukuna aka bude musu bodar shigowa garin qasar dan haka suka shigo Kai tsaye dan daman duk qasar da zakaci kasuwar siyar da bayin Ka sai kanada Shedan kasuwancin wanda shi zai Baka izinin shiga qasar.
Kai tsaye cikin kasuwar suka ratsa da bayinsu inda tini aka fara ganin