Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   36 / 100

105K to 108K   out of 299.8K words

duqufa fadawa Allah sbd dawowan hankalinta da tinanin wata sabuwar masifar ce a rayuwarta da kowane irin baqin cikin data dandana zai dawo mata sabo fil.

Sultan tsananin tsaro ya qarawa bangaren Ayanah din hakama shima NUAB Zafafan securities dinsa mata sun iso daga Moscow sune ciki da wajen bangaren Wanda a yanzu Bayan tenya da sakinah sai likitanta Dr Amed babu me shiga dakin datake idan ba NUAB din.

Sultan bai taba zuwa dubata ba al’adar dake kansa matsayin shugaba dan haka zuciyar NUAB take sake tsananta akansa.

A bangare daya kuwa Wani tsananin bincike aleey yakeyi me gigitarwa Akan Neman Abaas Wanda NUAB yayi alkawarin Nemowa kafin watan nan daya da ake saka ran tashin Amminsa ya cika dan kuwa a yadda likitocin sa suka basa tabbacin indai aka samu abinda zuciyarta tafi tsananin so ko maitarsa fiyeda komai a memory dinta na baya aka gabatar mata dashi tana farfadowa to hakan zai iya tabbatarda tsayuwar hankalinta da memories dinta.

Hakan ya saka Kai tsaye ya bada umarnin duk inda Abaas yake a duniya yanason aleey ya qure lissafin kwakwalwansa Akan inda zaa fara nemansa.

Wannan ya saka qwaqwalwan Aleey budewa da kyau ya nutsu ya buqaci ganawa da Wanda yasan Abaas a duniya Bayan Ammin.

Kai tsaye Sakinah ce wadda zata basa bayanan dayake so dan haka a lokacinda ya zauna a palon da zai tattauna da Maa sakina dagowa yayi a natse ya kalleta da idanuwansa masu sirkin blue blue na asalin baturen Russia ya bude baki Bayan ya dauki iPad din dake hannunsa dan dauka da tattara duka bayanan da zatai masa ya dago yana nutsar da duka hankalinsa akanta yace

‘Maa’

Kallansa tayi a natse itama batareda ta bude bakiba sbd nauyin da bakin yayi mata na rayuwarsu dake dawo mata,

‘Maa,waye Abaas??
Ina Abaas yake?
Bata yayi ko guduwa yayi kokuma korarsa akai?
Idan bata yayi daga ina ya bata?
Idan guduwa yayi daga ina ne ya gudun?
Idan korarsa akai waye ya koresa,me yayi aka koresa?
Meye cikakkiyar alaqar Abaas da Ammi?
Shekara nawa yanzu da rabuwan Ammi da Abaas?’

Numfashi me nutsuwa ya sauke yana kallan Maa din Wadda idanuwanta sukai jajir ya sake tausasa muryansa yace

‘Maa,Maa duka wannan bayanan shine zai bani daman dawo da Abaas rayuwarku,
Da wannan bayanin da zaki mun Maa nayi miki alkawarin Nemo Abaas matiqar yana raye insha Allah dan haka kowane bayaninki Maa ki sani yanada mahimmanci da rawar dazai taka a wannan aikin.’

Numfashi me Zafi da wasu hawaye masu Zafin gaske suka gangarowa Maa sakinah wadda Bayan shekaru masu tarin Yawa Ayau NUAB kila zaiji tarihin mahaifiyarsa da bai taba saniba mai daci da rashin dadin ji.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

61
A hankali cikin tsananin sanyi da mutuwar jikin radadin dayake dawo mata da quncin da harsu mutu bazasu manya dashi ba Maa sakinah tace

‘ABAAS GHAZ shine ‘da na karshe a jinin sarautar GHAZ data shafe a duniya gabaki daya yanzu,
Shekaru masu yawan gaske ne da bazan tinaba suka Baro mu da asalin ANJOM GHAZ wato garin da mahaifin Abaas yake mulki,
Abaas da Ayanah uwa daya uba daye suke tareda yan uwansu biyu da duka iyaye daya ne suka haifesu,

AYANAH GHAZ itace babba sai ZUHRAH GHAZ sai NURAT GHAZ kafin ABAAS GHAZ……..

Ahankali tafara basa mummunan labarin rayuwarsu dayake cikeda baqin cikin da bai taba gogewa ba daga zuciyoyinsu,baqin cikin da dashi zasu mutu,baqin cikin da shine ya kawar da lafiyar kwakwalwa da gangar jikin Ayanaah,baqin cikin da shine zai zama abinda zasu mutu dashi,baqin cikin da har zuriar Bayan baya tasu Ayanah zasuyi baqin cikin jinsa har cikin jininsu,baqin cikin da a yanzu shine yake Neman raba Ayanah da rayuwarta….

Wani irin kuka takeyi mara sautin daya saka aleey daukan tissue ya miqa mata idanuwansa jajir hannuwansa na rawa zuciyarsa kaman zata fado hakama hawaye ne masu Zafin gaske suke Neman cikowa idanuwansa yanajin komai cikin zuciya da kirjinsa,
Babban abinda yake sake saka jikinsa rawa shine yanda wannan mummunan tarihin zai isa kunnuwan LEUL,
Yaya tarihin nan zai isa ga zuciyar datake shirye da mutuwa Akan wadda wannan mummunan tarihin yayi kaca kaca da rayuwarta?
Tayaya zuciyarsa zata riski wannan tarihin kaddarar dayake dabaibaiye da rayuwar Amminsa.

Numfashi Aleey ya sake saukewa yana kallan Maa yayi mata alkawarin zai Nemo Abaas a cikin qanqanin lokaci insha Allah hakama wannan tarihin LEUL ba a bakin kowa zaiji Saba insha Allah Sai a bakin Abaas da kansa.

Ficewa Aleey yayi daga palon yana danna iPad dinsa sbd fara tattara kan bayanan daya riqe tsaf a cikin kansa na tarihin da abubuwan da zasu taimakawa bincikensa.

Bedroom dinsa ya isa ya rufe yana Zaunawa kan sofa da table a gabansa ya bude laptop yana fara bi takan qasashen dake zagaye da BOYEM ta kowane bangare gabas yamma kudi da arewa.

******A Daren ko kadan aleey bai rintsa idanuwansa da kwakwalwansa ba saida ya hada wasu irin fitinannun bincike da bayanai har asuba,

Sallar asuba yayi ya cigaba da hada kan bayanan sa da zai gabatarwa LEUL kuma yana saka ran ta hakan insha Allah Abaas kaman yana hannunsu ne.


Karfe goma na safe NUAB ya fito a shirye cikin brown gucci wears da takarmin berluti brown suma fuskarsa fresh duk da yana cikin tsananin damuwa a kwanakin amma komai nasa yana nan daukan ido da girgiza zuciya yakeyi,

Koda ya fito aleey yana tsaye shirye a palon hannunsa dauke da iPad fuskarsa sanye da farin glass da girmamawa ya yi masa Barka da fitowa yana bin bayansa zuwa dining inda aka cikeda tsaf da breakfast dinsa sbd yanzu da Amminsa take kwance ya Dena cin abinci acan.

Zaunawa yayi a daidai lokacin shima aleey din ya zauna Bayan yayi serving nasa.

Cikin nutsuwa sukai breakfast din suka kammala suka Baro dining din NUAB ya zauna Akan lafiyayyar 2seater Turkish royal cushion dake palon ya dago fararen idanuwansa masu daukan ido ya sauke Akan Aleey Wanda ya sauke ajiyan zuciya a natse ya matso ya bude iPad dinsa ya kamo bayanin dazai masa ya miqa masa a natse da girmamawa kafin ya dan ja baya kadan yana bude laptop din hannunsa daidai lokacinda NUAB ya bude abinda ya gama hada masa yafara bayani da cewa,

‘ANJOM GHAZ shine asalin garin da su Ammi suka fito,
Safarar bayi ce ta fiddosu daga can zuwa nan Wanda a yanda Maa tayi bayani babu sunan qasar da suka sani Bayan anfito dasu zuwa nan din BOYEM,

Abinda na tattara a bayaninta shine tace qasa goma sha shida aka wuto dasu ta ruwa kafin suka iso BOYEM,
A bayanin nata su qasashe shidan nan bawai ta tabbatar bane amma a iya lissafinta tsayuwa goma
Sha shida akai dasu Wanda hakan ya tabbatar mun da qasashe ne suke tsayawa kenan dan babu jirgin ruwa me girman da zai ringa tsayawa koina idan ba bodar wata qasar ya isoba,

Zoomin map din daya hada yayi yana cigaba da cewa

‘Batasan sunan qasar da suka rabu da Abaas ba amma qasa biyu suka qara tsayawa Bayan rabuwarsu dashi a ta ukun ce suke isa inda aka saida su maana nan BOYEM kenan,
A binciken dana tabbatar bisa ga wannan bayanin nata dama hada shima to qasar LARASIA aka siyar da Abaas Wanda idan muka duba qasa biyu ce tsakaninta da BOYEM dan hakan nake da tabbacin larasia dince inda aka siyar dashi.’

Wani bangaren Aleey ya sake zooming yana cigaba da cewa

‘Idan kuma na aka hada lissafin qasa goma sha shida dake akwai daga nan BOYEM ta gabas to Nahiyar qasar BASSHAH kenan
idan kuma daga yamma ne qasa sha shida daga nan qasar ALSIYASH kenan,
Idan kuma ta kudu ne qasar BUHARAQS kenan
Hakama idan ta arewa ne to qasar ANTARIA kenan.

Duka duka wannan bayanin dana hada qasashen nan sune inda zaa fara binciken nemansa amma dole duk qasar da zamu tafi Bayan sauka qasar sai an tafi bakin bodar ruwansu tanan ne dole zaa iya gane garuruwa masu kusa da manyan oceans da zaa iya samun tabbacin samun sa.

Dagowa yayi ya kalli LEUL BOYEM da idanuwansa da suke cike da Basira da wata irin kwakwalwa me hasko komai Akan lissafi da nazari,

Shima NUAB din gama kallan bayanin da duka suke a rubuce da map din Bayan duk bayanan dayayi masa da baki kuma,
Dagowa yayi ya kalli Aleey ya bude baki a natse yace

‘Meye karshen tinani da bayaninka ya hada?

Ajiye laptop din hannunsa yayi tareda kallan NUAB din cikeda girmamawa yace

‘Tinda ta ruwa suka iso qasar to dole bangare biyu ne Hagu da dama Wanda yake kudu da arewa kenan dan haka a cikin biyun zaa fara da daya maana a faro binciken daga inda suka fito tin farko ANJOM GHAZ kenan dan kuwa akwai yiyuwar tinda Abaas namijine to tabbas a tsawon shekarun nan indai ya samu yancinsa to tabbas ya koma gida dan sake ginawa da farfado da sunan GHAZ da bazai taba barin ya shafe ba Bayan ya nema yan uwansa be samu ba kenan,
Dan haka inaga a fara daga can din Kai tsaye sbd tabbatarwa idan bai komaba Sai a Nemi Sauran qasashen.

Kallansa NUAB ya dago a natse yayi cikin yadda da kowane bayanin aleey a koda Yaushe Akan komai sbd baya taba hada lissafin da bai qure kwakwalwansa akansa ba dan haka Numfashi me sanyi ya sake tareda dagowa yace

‘A gobe Inason a shirya tafiya zuwa qasar buharaqs din Wanda a cikinta ANJOM GHAZ take insha Allah.

Gyada Kai aleey yayi sbd yanada tabbacin insha Allah haka bayanin yake ba tantanma indai Abaas na raye yana saka ran ya koma dan farfado da GHAZ matiqar shi namijin jinin GHAZ ne dan ‘dan halak ko baida zarra bazai yadda sarautar gidansu ta fadi ta shafe a tarihi ba.

Juyawa yayi ya bar gurin yana daga wayar sa dan fara shirin tafiyar tasu da bazata wuce kwana biyu su wuce ba.

Bayan barin aleey shiru NUAAB yayi yana Jin Wani irin yanayi na rashin sanin tinanin Kamawa Akan me haduwan mahaifiyarsa da Abaas zata kasance hakama a yanzu da mahaifiyarsa take cikin halin da bazata iya basa labarin cikakken tarihinta ba a bakin Abaas dayake jininta yakeson jin asalin tarihin komai na Amminsa.

*******
Cikin kwana biyu aleey bai hutawa ba sbd bai taba wasa da duk abinda yake na LEUL ba dan haka shirin tafiyar ya tsaya tsayin daka saida ya tabbatarda ya hadata a cikin sati guda Bayan ya gama tanadar da komai na tafiyar wadda ya hadata hadda Maa sakinah da zata kaisu har cikin ANJOM GHAZ Bayan sun isa qasar kenan.

Tenya batasan da tafiyar ba sai ranar da zaa wuce kai tsaye NUAB ya sanar dasu dan haka jiki a mace da tsananin zullumin daya saka jinin Maa sakinah mummunan hawa sbd komawa inda komai ya faro.

Karfe Dayan rana motocinsu a Jere suka fice daga Masarautun zuwa airport Wanda motocinsu na zuwa gate din qarshe daidai nan motocin da suka dauko mai girma YUNAR BOYEM daga airport tareda ‘yarsa LEYLAH YUNAR BOYEM ‘yar amaryarsa ZUHRAH GHAZ BOYEM wadda ya kawo a matsayin tukuicin dawowan MAGAJI LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM ya basa aurenta a matsayinta na jinin BOYEM itama.

Ficewa motocinsa sukai tareda securities dinsa Bayan motocin mai girma YUNAR din sun shigo sukuma batareda kowannensu yaga junaba musamman LEYLAH YUNAR data gama mutuwa akansa tin kafin ganinsa a zahiri sbd kallo daya datai masa a hoton labarai ta shirya zama ko mistress dinsa ce ba matarsa ba dan haka wannan tukuicin da mahaifinta ya badata na aure shine abu mafi farin ciki da girma na rayuwarta dan haka batada baqin cikin dawowan su Masarauta da zama.

Su kuwa suna isa airport Kai tsaye jirginsu ya daga yabar qasar.

Tafiyar awanni masu yawa sukai kafin suka isa qasar bhariqs din wadda saida suka kwana a wata qasar kafin suka sake hawan jirgi suka isa.

Tinda suka iso daga shi kansa NUAAB din Wanda baisan kaddarar mahaifiyarsa da zai tarar acan ko tasa sbd zuciyarsa dake Jin rashin nutsuwa da sukuni,
Maa sakinah ma sosai ta shiga mummunan halin daya sakata fara ciwo me dan karfin da har saida taga likita kafin suka dauki wasu mahaukatan motoci zuwa tafiya me tsananin tsayin da zata kaisu ruwan dake qasar Wanda tacan zasu bi sakinah ta gane dajin garin ANJOM.

Kwana daya da wuni sukai suna tafiya kuma saida suka dauko likita ma musamman sbd ciwon Maa dazai iya tashi koyaushe,

Sun iso garin dayake bakin ruwa basu tsaya komaiba Aleey ya siya musu jirgin ruwa gabaki daya suka shiga dan barin gurin.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

62
Tafiyar wuni guda da kwana daya sukai suna zagaye ruwan da tafiya ke tsayi kafin Kaman a mafarki sakinah ta daga hannu tana nuna gurin daya saka idanuwanta jajir hannuwanta na rawa.

Bakin dajin suka tsaya su aleey da Sauran Yaransa suka fidda drones dan duba duk abinda yake cikin dajin da gari ma idan akwai.

Aleey ne yake riqe da iPad din dayake kallan dajin da drones dinsu suka shiga suna yawo a sama,

Sauran yaran kuwa a tsaye suke da mahaukatan bindigoginsu a shirye da harbe ko dabba ce tayi motsi a gurin,

NUAB yana ciki Zaune yana jiran bayani daga aleey Wanda yake sake kallan iPad din hannunsa da kyau sbd tabbas yaga gari.

Wasu mahaukatan bikes dake shiga daji suka fidda daga jirgin ruwan suka hau tareda kutsawa cikin dajin a shirye da bindigoginsu da wasu manyan wuqaqe masu shegen hadari.

Tafiya sukeyi suna kutsawa kafin sukai tafi me Nisan gaske basu isa garin ba sai yamma lis wanda ya saka sakinah yanke jiki ta fadi tama Dora kafarta a qasar garin ANJOM GHAZ kenan.

Cikin kulawa da bada umarni yace a koma da ita jirgi taga doctor ya dubata abarshi daga shi se aleey su fara ganin lafiyar garin ma tukuna.

Sauran yaran da bikes din tareda Maa sakina Juyawa sukai suka koma.

Kafarsa ta dama ya fara dorawa a cikin garin ANJOM GHAZ daya saka tsigar jikinsa tashi sbd ganin yanda garin ya zama tamkar ba garin da mutane suke rayuwa a cikinsaba sbd duk tsawon shekarun garin bai dawo daidai ba sun rasa niima da tarin albarkar garin nasu.

Akwai mutane sosai da gidaje sosai da kasuwanni a garin amma ba kamar baya ba sbd kusan kowa na garin yasan kowa tinda ba yawa sosai.

Ganin baqi a garin ya saka gabaki daya mutane shiga tsoro da tashin hankali dan haka Kowa ya fara silalewa yana komawa gidansa ya shige ya rufe tinda dai shugaban garin nasu baida lafiyar dazai basu kariya,
Fiyeda shekaru tara yana kwance yana jinyar da ba lallai ya tashi ba sbd yayi mummunan nisa.

Gidan shugaban garin Aleey ya nema a taimaka a nuna musu babu musu kuwa Wani ya kaisu har kofar gidan asalin sarautar GHAZ.

Fadawane suke gadin masarautar amma tsirarru Wanda yake nuni da Masarautar batada karfi ko Kwata kwata tinda garinma duka ba Wani karfi bare Ayi mulki me karfi.

A fada suka zauna nan Sarkin fada ya shigo yana kallansu tareda zubawa NUAB idanunwata kaman zasu gado sbd ganin kammanninsa da jinin GHAZ dayake Neman shafewa daga Yauma kila sbd jikin Shugaba yau yayi tsananin da sai Allah.

Kwarjinin NUAB ya saka shine ya gaidasu yana musu Barka da zuwa maimakon su su gaidasa sbd shine kila me mulkin GHAZ anan gaba.

Aleey cikin nutsuwa shima ya dan gaidasa da yarensu Wanda NUAB yakeji sosai sbd mahaifiyarsa dake masa tin yana yaro hakama Maa sakinah shikuwa ya kullafa saida ya iya yaran shikuwa aleey baya wasa saida ya iya shima sbd uban gidan nasa da idan ta Kama.

Kaman daga Sam Kai tsaye NUAB yace

‘Menene sunan shugaban jinin GHAZ daya rage a yanzu???

Da mamaki Sarkin fada yace

‘ABAAS GHAZ sai ‘yarsa qwalli daya tak AYANAH BAHAR GHAZ sune suka rage jinin GHAZ a duniya…

Wani bawa ne ya fado fadar da sauri yana zubewa qasa yace

‘Sarkin fada jikin Maigirma yana sake tsananta kana buqatan zuwa.

Miqewa Sarkin fada yayi yana barin gurin a rikice Wanda ya saka Kai tsaye NUAB miqewa yabi bayansa sbd kowane Hali Abaas din Amminsa yake yanason ganinsa.

Sarkin fada na saka Kai dakin NUAB ma yana sakawa idanuwansa suka sauka Akan fuskar datake sak da sak data mahaifiyarsa.

Abaas dake aman jini ahankali dagowa yayi idanuwansa na sauka Akan NUAB take ya dauke wuya komai nasa na kokarin tsayawa cak yayi baya zai zube

Taku biyu NUAB yayi ta tarosa jikinsa yana Jin dukkanin nauyin dake zuciyarsa yana qaruwa da ganin sanyin idaniyar mahaifiyarsa a wannan halin.

Feso Wani jini Abaas yai da karfi cikin azabar dayake kasa riqewa NUAB ya katse azabar ciwonsa da cewa

‘NUAB ALMAZZ ‘da ga AYANAH GHAZ……

Rintse idanuwana Abaas yayi cikin wani azababben yanka daya ratsa zuciyansa data gama yanke kauna da yan uwansa har abada musamman yanzu dayake kan gadon mutuwarsa,

Riqosa NUAB yayi cikin rashin bata lokaci sbd kafin komai yana Abaas din na buqatar likita da gaggawa,

Girgiza Kai Abaas yayi cikin wani mummunan rashin kuzari da ciwon da baida sassauci ke kadan ya damqi hannun NUAAB din da karfin gaske yana jan Numfashi da qyar yace

‘Ayanah tana raye???

Cikin sauri NUAB din ya Gyada masa Kai tareda bude baki yace

‘Kana buqatan likitan dazai duba lafiyar Ka da gaggawa daga baya duk zamuyi magana amma Ka sani Amminah tana raye,
Tana son ganinka itama kafin tabar duniya dan haka kada Ka tafi Kabarta zuciyarta bazata iya daukaba sbd kaine hasken zuciyarta da idaniyar Abaas ghaz.

Girgiza Kai Abaas ya sake yi yanajin kaman bazai iya ko minti dayaba a duniya dan haka koma yayane Allah yayi masa rahama ne tinda Sauran ransa daya kawo masa dan Ayanaah zai cika a hannunsa Bayan burinsa na hada jini da Ayanarsa ya cika Akan gadon mutuwarsa.

Sake qanqame hannun NUAB yayi yana bude baki daqyar yace

‘Ka cikawa mahaifiyarka Dani burin da muka tashi dashi na hada zuria da juna Ayau cikin Daren yau na mutu da nutsuwar na bada ‘yata daya tak ga jinin Ayanah……

Wani kallan rashin fahimta NUAB yayi masa yaja kallan aleey yace Ayi gaggawar daukansa dan tafiya dashi ga likita.

Abaas zamewa yayi yana sake dan girgiza Kai daqyar yace

‘Lokaci na yayi Allah ya yanke ganawata da Ayanah bazan Kai koinaba zan bar duniya,
Kokarin daukansa aleey yakeyi amma jikin sake rikicewa yakeyi dan haka ba bata lokaci Aleey ya fita ya fidda wayar sa ya saka kiran Sauran yaran yace a kawo Maa sakinah yanzu.

A lokacinda aka iso da Maa sakinah Abaas cikin tsananin ciwo da

36 / 100