kai tsaye dakin daya barta ya nufa idanuwansa jajir bai ganta ba dan haka baya ko gani ya fito ta fice zuwa bangaren Amminsa.
Ko daya isa a daidai lokacin itama Ammin da bata samu isa dakin Maa ba sbd Leylah data tareta suka zauna hira har sukai ishai tana samun kanta ta nufi dakin sakinah daidai nan ya shigo palon idanuwansa a rufe hakama a daidai lokacin tenya ta fito tareda Leylah itama cikeda mamakin gaske suke kallansa bai kalli kowaba ya nufi dakin Maa sakinah.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laoualiHAYATEEM
Mamuhgee
79
Bugun da yayiwa dakin ya saka Maa sakinah dake Zaune Bayan Bahar tana gyara mata gashinta data lallabata ta wanke mata a Daren tana gyara mata sbd duk dai ta samu Bahar din ta sake daga damuwan datake ciki duk da itama tana ciki sosai
Ta juyo a hankali ta kalli kofar cikin mamakin waye yake knocking din Wanda ya saka hatta Bahar jinsa har cikin zuciyarta.
Sake Wani bugun yayi daidai isowan Amminsa wadda ke kallansa cikin tsananin mamaki da fargaban halinda take ganinsa fuskarsa tayi jajir dake bayyanarda tsananin fushinsa da bacin rai na matakin karshe,
Tenya ma cikin zullumi da mamakin take qarasowa tana kallansa hakama Leylah wadda taji shakkar ganin bacin ran nasa sosai haka zuciyarta na tsinkewa.
Hannu ya daga zai sake buga kofar Maa sakinah ta bude cikin mamaki da nata bacin ran dan kuwa qamshinsa daya ratso cikin dakin ya tabbatar mata da shi dinne dan haka sake Jin tayi zuciyarta na daci dan haka ta miqe ta bude kofar tana kallansa cikeda nata fushin,
Ga mamakin dukkaninsu baice komaiba ratse Maa din yayi ya shige dakinta Wanda hakan ya saka Bahar miqewa tsaye tana ja da baya sbd ta gama sanin baida cikakken hankali gashi rigar vest ce fara Kal kadai a jikinta sai dogon wandon bacci.
Kai tsaye ita ya doso batareda ma yana ganin komaiba sbd fushinsa daya kai kololuwa hannunta ya damqo ta fizge da karfi tana Dora kyawawan idanuwanta akansa ta bude baki tace
‘Ka dena wuce iyakarka’
Da Wani irin sauri tenya da Leylah harma da Amminsa suka kalleta sbd kaf ko Amminsa bata masa magana irin haka amma ita sbd kauna ne to bare Wani duniya ya masa irin wannan maganar gatsal a cikin daga murya tareda bayyanarda nata fushin sbd itama zuciyarta ta gama quluwa da duk abinda ma yake Jin yanada shi a jini na sarauta itama jinin sarautar ce dan kuwa a yanzu data zauna a ANJOM itace me ikonta gabaki daya.
Wani kallo ya sauke mata idanuwansa masu rikitarwa yayi mata itama shi din ta kalla idanuwanta na sauyawa kafin ta kasa riqe nasa idanuwan ta dauke kai tana Juyawa a zuciye da gama kaiwa maqura zata nufi toilet ta shige ya sake damqar hannunta wannan Karan tareda fizgota ta dawo baya da karfi bayanta da kirjinsa suka hadu da karfi gashinta dayake da Sauran sanyi sbd basu busar ba ya sauka sauka a gefen fuskarsa ya juyo da ita idanuwansa na sake rifewa ya Kama hannunta na dama yana Juyawa zai fice.
Matsowa Maa sakinah tayi cikin rashin Jin dadi ta bude baki zatai magana ya bude baki yana controlling halinda yake ciki a natse yace
‘Maa pls No’
Janta yayi yana yin gaba ya tinkaro kofar dasu Ammin ke tsaye sun mutu a cikin mamaki mai tsananin gaske na abinda yake faruwa batareda sunsan komai Akan abinda yake faruwa Akan Idon nasu,
Hannun NUAB din dayake riqe dana wata mace macen da ba muharramarsa ba hakama a gaban idonta ita mahaifiyarsa da idanuwan Sauran iyayen nasa mata sakinah da tenya harma Akan Idon matar da zai aure ya Kama hannun mace ya riqe idanuwansa a rufe tamkar ba shi ba
Tsayar da idanuwanta Ammin tayi Akan hannun na NUAB tana Jin zuciyarta na sosuwa da abinda Ayau take sheda wa tana kasa ko kyafta idanuwanta daga hannun Wanda kamar a mafarki number dake rubuce a hannun Bahar din ta bayyana seti da daidai numbern NUAB din Wanda suka jeru Akan idanuwanta da suka tsaya cak tareda bugun zuciyarta tana kasa motsawa bare fidda kowane irin Numfashi harya kawo gurinta ya ratsa gabanta ya wuce da Bahar bata motsaba Wani irin nauyin kirji da Juyawa taji kanta nayi Wanda ya sakata dafa bango ganinta na Neman daukewa ta daddafa batareda kowa ma dayake cikin shock ya lura da itaba ta koma dakinta ta zube a bakin gado tana dafe kirjinta tana kasa yadda ko kadan da abinda ta gani sbd ganin numbern ta bauta a jikin yarinyar ya dawo mata da sak irin numbern Abaas dinta ce,
Girgiza kai tayi da sauri tana sake dafe kirjinta sbd tinaninta dayake Neman rikicewa,
Mantawa tayi da abinda NUAB yayi sbd ganin numbern a idanuwanta ya mantar da ita komai a daidai yanzu Bayan dawowan radadi da tinanin rabin rayuwarta dan uwanta Abaas datake rokon duk inda yake Allah kada ya dauki ranta bata gansa ba Allah ya bayyanar mata dashi.
Leylah kuwa acan palon Wani irin daci da nauyin kirji ne me Zafin gaske ya rufeta idanuwanta na sauyawa zuwa ja da wasu irin hawayen baqin cikin da bata taba dandanaba suna zuwar mata ta kafe kofar daya wuce da baiwar wadda sai Ayau take ganinta dakyau dan kuwa har tenya batai noticing baiwar ba wadda harta samu matsayin shiga dakin sakinah ta zauna da irin Kayan da suka gani a jikinta.
Shi kuwa yana fitowa da ita harya nufi kofar ficewa ya dakata cikin zafi yaje har lokacin,
Sakin hannunta yayi tareda saka hannu daya ya bude gaban rigarsa kai tsaye batareda tsayawa bude botiran gabanta ba haka botiran suka zube qasa gabaki daya sbd yanda ya bude gaban rigar ya zarewa lafiyayyar farar fatarsa dake Wani irin daukan ido da kakkarfan jikinsa suka bayyana.
Sake janyota yayi da karfi gabansa Wanda ya sakata fadowa Kansa sedai bata iya barin jikinta da nasa ya qarasa haduwaba ta saka hannunta kai tsaye ta tare kirjinsa hakan ya hanata fadawa kirjinta ya hadu da nasa,
Saukan tafin hannunta Akan kirjinsa ya saka ya kalli hannun nata da jajayen idanuwansa kafin ya kalleta itama shi din ta kalla tana dauke hannunta fuskarta a cike da baqin shaqar numfashin dayake cakude qamshinsa ta ja baya tana dauke idonta gaba daya daga bangaren dayake shima kallanta ya dauke nasa Idon tareda sake Kama hannunta ya jata ya fice da ita tana kokarin kwacewa da karfi amma ba daman kubuta ko kadan sbd irin riqon da yayi mata.
Yana fitowa aleey kallo daya yayi masa yaga ba Riga a jikinsa yake yabi bayansa kawai batareda furta ko kalma ko daya ba suka nufi bangarensu.
Maa sakinah kasa zama tayi ta koma tsakiyar dakin ta dawo bakinsa ta sake komawa ta dawo a sanyaye ba karfi a jikinta zuciyarta da kirjinta na nauyi,
Maa tenya qarasowa gurinta tayi tana kallanta cikeda mamakin abinda yake faruwa tana sake shiga mamakin sukunin data rasa gabaki daya take kaiwa da komowa,
Cikin mamaki da zullumi tace
‘Sakinah menene yake faruwa?
Waye wannan baiwar?
Yaushe ma aka kawota bangaren nan?
Daga ina aka kawo nan bangaren?
Kasa amsawa sakinah tayi Bayan juyowan datai ta kalli Leylah dake tsaye kaman zuciyarta zata Kama da wuta me tsanani ta dawo da kallanta kan tenya din ta bude baki zuciyarta na tsananta damuwa tace
‘Ba baiwar kowa bace’
Tana fadar hakan kasa dorawa da komai tayi ta juya ta nufi kofa kai tsaye tana kasa jira tabi Bayan NUAB din Wanda take tsananin tsoron kada tsananin fushinsa yakai sa ga yiwa Bahar din Wani abin.
Ficewa tayi tabi bayansu kai tsaye tabar tenya da bin bayanta da Wani irin kallo hakama Leylah Wani kallan baqin ciki da tsanar sakinah din tabi ta dashi sbd ganinta da baiwar da batasan meyasa NUAB dinta zai Kama hannunta ba,
Tsanar baiwar taji me karfi da tsananin gaske tana shigarta sbd irin fushin data gani yana cin idanuwa da jikin NUAB a zuwan nasa tabbas bana tsana bane bare ace laifi tayi koda kuwa laifi tayi dole tanata zarrar da har yasan da itace tayi laifin Yazo hukuntata sbd NUAB kaf masarautar Bayan mahaifiyarsa da mahaifinsa kila babu Wanda ya riqe kamanninsa bare tinawa dashi ko wayene amma wannan ace yasan da itace tayi laifi harma yasan a inda take kuma ya gane itace a tsaye ya Kama hannunta…..Jin tayi batama buqatar tsanarta hukuntata kawai zata saka ayi na iya kallan mijin dayake matsayin nata harma ta iya barin jikinta da baida daraja haduwa da nasa.
Maa sakinah tana fitowa kai tsaye bangaren NUAB Din ta nufa Wanda tin daga nesa jikinta da idanuwanta suka tabbatar mata ba lafiya ba dole akwai abinda ya faru sbd Yaransa gabaki daya a tsaye suke da wasu mahaukatan bindigogin da zasu fasa kan mutum kai tsaye babu bata seconds hakama da alama kwanan tsaye zasuyi yau motsi kadan Zai iya zama ajalinka.
Duk hasken dayake zagaye da bangaren a kunne yake koina ya haske ta yanda ko sauro ya wuce zaka iya ganinsa.
Tin tana doso wa suka gane itace dan haka suka dan sassauta makamansu tana isowa babu Wanda ta kalla a cikinsu suma sadda kai sukai qasa amma babu me alaman motsawa bata hanyar wucewa.
Aleey ne ya iso ya bata hanya da Kansa ta wuce ya bita a baya kai tsaye palon ta shiga.
NUAB din baya palon yana dakinsa yana kokarin calmin Kansa ta hanyar tsayawa bakin window iska me sanyi tana kadasa yana fidda Numfashi me Zafi yana saukewa wutar dake cinsa tana sauka ahankali ahankali amma saima ta jima sosai kafin ta gama fita dan hakane ma kowa yasan bame sake ganinsa sai kuma gobe.
Maa sakinah kai tsaye dakin datasan Bahar din na ciki ta nufa ta bude a natse tareda shigowa tana kallan Bahar din dake bakin gado ta dunqule tana sauke numfashin itama kuka ya kasa zuwar mata sbd tsananin baqin cikin NUAB din.
Maa sakinah na tinkarota ta dago kanta ta kalleta da jajayen idanuwanta kafin ta maida kanta tana Jin kaman zata fasa kirjinta sbd Zafin dayake mata.
Maa Zaunawa tayi kusa da ita tana dafa bayanta cikin rikicewa tace
‘Bahar me yake faruwa ne Wai?
Sake dawowa Bahar tayi ta kalli Maa din tana rasa abin fada sai datai mintina kafin ta iya bude Baki zatai magana Wani qamshinsa me karfi da nutsuwa da sanyi ya shiga hancinta da karfin gaske.
Kasa maganar tayi ta kalli rigar dake jikinta ta miqe tsaye tareda zare rigar ta jefar tana Rintse ido da karfi ta bude tana komawa bakin kujera ta zauna tana dafe kanta dayake sarawa sbd haukar dayake Neman cinna mata irin tasa tinda shi baida hankali saiya maidata mahaukaciyar itama.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
80
Maa sakinah dawowa gefenta tayi tana shafa bayanta a natse tana Dena tambayar sbd ganin kaman Bahar din zuciyarta a kufule take abinda bata taba gani ba a tareda ita tinda ta dawo hannunta.
Shiru sukai kowa zuciyarsa da abinda take tinani amma ba damar fada,
Lokaci suka dauka shiru kafin Maa sakinah ta sauke Numfashi zata koma tinda dai ta tabbatarda kila NUAB ya sauka daga koma menene ya bata masa rai dan haka tasan bama lallai ya fito ba sai kuma gobe,
Miqewa taje kokarin yi Bahar ta riqe hannunta da sauri tana shigewa jikinta ta rungume tana girgiza mata kai alaman dan Allah kada ta tafi tabarta ta jirata su koma a tare.
Shiru tayi kafin ta koma ta zauna ahankali tana sake shafa Bayan Bahar din wadda har lokacin gashinta yakeda Sauran sanyi gana ac yana shigarta dan haka saita dan dunqule a cikin jikinta tanayin shiru a sanyaye.
Anan dole sakinah ta kwana tareda Bahar din wadda suka kwana kusan kowannesu bai samu ya rintsa da kyau ba tinani da damuwa sun Haba hakan,
Kwanan Maa sakinah a bangaren NUAB ya tabbatarwa dasu tenya da Leylah da suka kwana kusan a Zaune suma sbd tsananin mamaki da tashin hankalin kenan tabbas itama baiwar acan ta kwana bangaren nasa,
Babban abinda ya Haba idanuwan Leylah ko kwatanta rintsa wa shine shin a ina baiwar zata kwana a bangarensa hakama yanada ikon kwanciya da ita ba laifi bane ba illa bace tinda baiwar ce zata iya zama imebetinsa,
Wani sabon nauyi me tsananin radadi ne yake sake danne zuciyarta duk ta Tina da hakan sbd zata iya zama fiyeda abinda ake iya tinani idan wata macen ta fara kwanar mata da miji ba ita ba,
Ayanah ma da suke son ganin halinda zata shiga Akan hakan idan taji sun kasa samun ganinta sbd a shige ta rufe dakinta Wani irin hali tinani da zuciyarta suke ciki na ganin abinda ya saka zuciyarta gabaki daya tashi Akan Abaas Wanda zuwa yanzu ta tabbatarda matiqar yana raye bazai taba kawowa yanzu bai nemeta ba indai ya samu yancinsa sai idan yana cikin bauta haryanzu Wanda tina hakan zuciyarta bazata dauka ba sbd shekarunsu sun tafi sosai ta yanda haduwansu da sake rayuwa da juna da junansu damar na sake qaranta,
Washe gari tinda safe Maa sakinah ta Baro bangaren tareda Baro Bahar acan wadda take bacci sbd Bayan asuba zazzabi ne na sanyin gashinta daya shigeta ya rufeta dan haka magani ta fito ta samar mata a lafiyayyan kitchen din palon na ruwan zafi sosai da ginger ta kawo mata tasha tana gamawa bacci mai dan karfi ya dauketa Wanda Maa tasan zata jima tanayi dan haka ta tafi ta dawo daga baya.
Tana komawa lokacin tenya na dakinta itama baccin Sai a lokacin ya dauketa dan haka dakinta ta nufa Bayan ta dubo itama Ayanah baccin takeyi me karfin da bata samu yi ba a Daren takeyi.
Leylah duk motsin Maa din tana jinsa amma bata fitoba sbd ita har lokacin bata rintsa ba Wani irin tafasa zuciyarta ke yi taba Jin inama zata iya yankewa Maa din hukuncin Kisa kai tsaye da ita zata fara kawar wa dan da alama itace take kaunar baiwar.
Maa sakinah dakinta taje ta dan kwanta itama take bacci ya dauketa sbd bata rintsa ba,
Karfe tara na safen Maa sakinah ta fito har lokacin ba kowa a palon dan haka kai tsaye kitchen ta nufa ta tadda su salma sun gama aikin breakfast sbd suna isa bangaren Li’ul aiki aka koro su sbd Bahar bata cikinsu dan haka suka dawo nan din.
Abinci tace su hada na breakfast din Bahar a tray su biyota dashi.
Cikin nutsuwa kuwa suka hada komai a lafiye a tsare suka fito dashi tayi gaba suna biye da ita dashi zuwa bangaren NUAB din Wanda babu Wanda ya taba zuwa ko hanyar a cikinsu.
Koda suka taho bata farka ba amma motsinsu din ya tadata ta bude idanuwanta ahankali tareda tashi Zaune tana sauke Numfashi da addua a zuciyarta.
Kallanta Maa sakinah tayi tana cewa ta tashi tayi wanka taci abinci.
Saukowa gadon tayi Wanda ya saka sa Salma da zuciyoyinsu ke kasa daukan mamakin da suke ciki da tsananin tsiro da tashin hankalin saukar da kansu suna Juyawa suka fice a natse sbd sun gama jere abincin.
Ficewa sukai daga bangaren gabaki daya jikinsu na dan daukan dumi da rawa sbd gabaki daya niimar bangaren cike take tako ina da qamshin LEUL BOYEM Wanda hakan kadai tada tsikar jikinsu yakeyi sbd fargaba da tsoro me girma.
Suna ficewa Kamata ta miqe Maa tayi tareda zuwa closet din dakin dake jere da towels kawai ba Kayan kowa a ciki ta dauko mata sabon towel a cikin sabbin dake Jere a gurin sama da dozen ta kawo mata.
A duk inda Maa sakina take tareda ita tana samun nutsuwa da gurin koda kuwa daji ne hakan take Jinta dan haka a natse ta karbi towel din ta nufi toilet din Wanda komai na bangaren tin daga farkon har toilets toilets da kitchen ya banbanta dana kowa masarautar sbd nasa tsarin daban yake da tsarin kowa.
Sabon brush tayi brush dashi ta yo wanka ta fito tana fitowa Maa tayi dauko Wani towel din tazo ta tsaya bayanta Bayan ta zaunar da ita gaban madubi tafara goge mata gashinta baki bakinsa daya jiqe.
Karfe 9 shima ya fito a shirye cikin wasu three quarter black na Balmain kai tsaye dakin datake ya nufa idanuwansa masu kyau da daukan hankali tareda Wani irin kwarjini sun koma farare su tas qamshinsa me isar da isowansa a dik inda ya dosa yana tashi a jikinsa.
Babu kowa a palon tsit koina babu Wanda ya sako kafarsa palon cikin Yaransa kaf harma da aleey sbd Bahar na bangaren kuma sai ranar data barsa idanma zata Bari din kenan su kawai a yanzu shirye suke a tsaye qyam bakin aikin jiran kowane irin motsi daga koina.
Hannu ya saka kai tsaye ya bude kofar dakin a cikin iko da izza tareda kamewa ya sako kai dakin Wanda ya saka Maa sakina juyowa gabaki daya tana kallansa shi kuwa da baima San da ita ba a bangaren kallanta shima yayi kafin ya maida kallansa a natse Akan Bahar wadda bata tashi ba daga Zaunen datake ta basa baya tana dacin mirror ta cikin mirror din ta dago idanuwanta masu daukan hankali ta kallesa shima ta cikin mirror din ya kalleta kallan da idanuwansa ke budewa da Wani irin iko da isa kanta kafin ya dawo da kallansa Akan Maa duk batareda ya motsa ba tukuna ya bude baki cikin girmamawa da matsayinta a gurinsa yace
‘Barka da isowa Maa’
Kallansa Maa din tayi tana Jin gabaki daya zuciyarta da gangan jikinta sun kasa sakewa da kasancewa a gurin dan haka amsawa tayi tasan kallan kyakkyawar fuskarsa da bata dauke da alaman tsoron komai.
Ficewa ta nufi kofa zatai Bahar batasan lokacinda a miqe da Wani irin sauti ba ta biyota zata hanata tafiya tana kawowa Maa din na saka kafarta palo itama tata zata saka hannunsa daya ya riqe sirirn dantsen hannunta Wanda hannunsa ya gogi daurin towel dinta dayake ta bangaren take ya fara kokarin warwarewan datai saurin juyowa tana dafewa da hannunsa a gurin da hannunta daya.
Fararen idanuwanta da suka kere nasa a kyau ta dago ta kallesa cikin ido hannunta na dafe da nasa Aa gurin kirjinta na harbawa da karfi hakama zuciyarta na wani irin zafi da dukkanin fushinta take kallansa.
Nasa idanuwan ya da dago ya kafa mata su ta yanda zatai qasa da nata dole sbd hukuncin