Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   78 / 100

231K to 234K   out of 299.8K words

da sabon kuka tana tashi zaune ta sauko qasa ta zube gaban Ammin tana kama kafafunta tace

'Wallahi Ammi shine yamun dole bada son rainaba,
Ammi ko su Maa zasuyi shedan dole yamun,
Hakama ko tafiyar Birmingham daga zuwa ganin likita ya tafi dani bada son raina ba dan Allah Ammi kiyi hkr kada kiyi fushi akan hakan ki tafi Boyem ki barni Ammi bazan sake ba dan Allah kiyi haku.....

Somewa kusan Ammin tayi daga zaune idanuwanta na tsayuwa cak akan Bahar din cikeda mamaki me girma na jin sabon zance kuma bayan wanda takeji a kwanakin kullum,
Me bahar din ke nufi?

Miqewa tayi hannuwanta na dan rawa ta kasa cewa komai sbd ita lura da yanayin sanyin Bahar din daya saura rayuwanta a kwanakin ya sakata jin tausayinta takejin ko zata tafi da ita ta yawato ta dawo ko zata koma daidai duk da batasan meyake damunta ba ya sakata zuwa dakin amma tana jin sabon zancen tashin hankali.

Kafe bahar din da ido tayi tana rasa abin cewa har lokacin tana qare mata kallo zuciyarta na bugawa da abinda ke shirin faruw tace

'NUAB dinne ya miki dole?
NUAB dinne ya tafi dake Birmingham daman?
Me kukaje yi acan?
Meye hadinki da tafiyarsa?
Duka su sakinah suna me harya kwasheki kuka tafi?
Tafiyan wuni guda ce ko kwana?

Rikicewa bahar tayi da tambayoyin tayi shiru tana tsiyayo hawaye wanda ya saka Ammin jin tafara fusata dan haka juyawa tayi tabar dakin ta nufi dakinsu sakinah kai tsaye.

Tana zuwa tambayar data jefa musu shine meya faru tsakanin NUAB da Bahar?

Da mamaki suka kalleta kafin sukai shiru take tinaninta yake inda bata son yaje wani baqin ciki da bacin rai take ya rufeta ta rasa abin fada ta juya tabar dakin tana zuwa wayarta ta dauka ta kira tace ticket din tafiyarsu takeso na tafiya dukansu a goben.

Tana kashe wayarta numbern NUAB data kasa dauka kwana biyun ta kira ido rufe.

A natse ya dauka cikin kwanciyan hankali sbd tinda ya dawo boyem baya cikin nutsuwansa sbd ayyuka da 'yarta data tsayar da rayuwarsa guri daya cak.

Babu abinda ya fara sauka a wayar tasu bayan tambayarta data saka wayoyin nasu shiru.

'NUAB meya hadaka da Bahar daka zo??

Shiru yayi na mintina maganar na amsa kuwwa mara karfi a cikin kunnuwansa ya sauke numfashi mara sauti yana bude kyawawan idanuwansa masu kwarjini ya ajiye file din dayake hannunsa yana dubawa ya bude baki da muryansa me sanyi yace

'Ammi zaki iya jin amsar tambayanki???

Kashe wayar tayi da sauri tana jifa da wayar sbd zai iya bata amsar da zata kasheta kafin safe dan haka gwara ta jira garin ya waye su isa boyem din ya fuskanci fushinta sbd ga dukkan alama yafara lalata karatun yarinyar nan san taga alama amma bata dauka aikinsa bane.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

142
Dukkaninsu ba wanda yayi baccin arziki musamman da a daren ta sanar dasu tafiyan gabaki dayansu zasuyi yanzu zuwa boyem din.

Bahar sake shiga fargaba da tsoro da damuwa tayi sbd fargaban abinda zaa tafi yi,
Idan ta hadasu da NUAB ta tambayesa zai iya fada mata amsar duk abinda zata tambayesa wanda kila bazata taba iya sake kallan fuskar Ammi ba har abada dan haka taji tana fatar masa magana kafin Ammi ta hadasu guri daya ta tambayesa.

Sanyi jikinta yayi tanajin bata taba tafiyan dataji hankalinta yana tsananin tashi ba faduwan gaba na kamata ba idan ta tina irin wannan.

Kasa komai tayi dan haka maa sakinah ce ta hada mata kayanta a suitcase guda daya tinda acan tanada kaya sosai kuma sunyi waya kafin su isa su Naimah da salmah zasu fidda komai akai a wanke a sake gogewa da tirarawa na sitirarsu.

Washe gari ansiya duka tickets dinsu na tafiyar dan haka da dare jirginsu zai tashi amma kusan tinda safen suka gama shirin komai.

Breakfast ma sama sama sukai a dining din duk da Tenya da sakinah hidimar gabansu kawai sukeyi tinda dai ba yanda zasu iya yi,
Ammin ce taketa bacin rai da zafinsa sbd taji ciwo da tsananin zafin abinda NUAB din yayi matiqar gaske duk da ta kasa zaunawa ta tambaya taji cikakken bayanin komai a bakinsu sakinah sbd zuciyarta bazata iya daukan jin ba hakama shima datake son yiwa maganar dakyau sbd alkawarin da yayi mata akan zai jira har dai bahar ta gama ko nisa da kama karatun sosai tukuna zaaji raayinta akan shi da aurensa matiqar bata so sunyi alkawarin ba dole zaa sauwake auren a barta ta jira lokacinda duk ta tashi sbd tayi alkwarin bazata bari alkwarinsu itada Abaas ba ya tauye Bahar tinda ko babu komai sun cika nasu alkawarin tinda dai anyi auren.

Yanzu ta tadda wannan labarin da aka boye mata me daga hankali gashi karatun yana neman rikicewa tin baa kusa kammalawa ba,
Qarin tashin hankalinta na biyu da shikenan sedai ta tsinci ciki a jikin Bahar.
Dalilinsa na karya mata alkawarin daya daukan mata tana matsayin uwar data haifesa takeson ji dan kuwa ya saka mata radadi me zafi da hakan da yayi na watsi na alkawarin.

Bahar ma bata iya fitowa cin abinci ba seda Ammin ta saka aka kirata akan umarni ne ta bada.

A silale take tahowa jikinta a sanyaye kaman mara lafiya tana sauke kanta qasa.

Kafeta da ido Ammin tayi tana qarewa tafiyanta kallo data sauya kwata kwata ba kaman da tana budurwanta ba a baya,
Dauke idanuwanta tayi daga kallanta tana jin wani iri duk da tasan su tenya zasu gyara mata ita su bata kulawa fiyeda yanda ya kamata amma dai jin takeyi tayi babban baqin cikin da bata nan ta kula da ita da kanta sannan shi kansa yaga bacin ranta yanda ya kamata dan kuwa duk namijin dazai sauya tafiyar mace bayan maidata cikakkiyar macensa to ba qaramar karfi da wuya tasha ba a hannunsa da nacewa.

Bahar din na isowa zaunawa tayi gefen Ammin tareda bude baki a sanyaye ta gaidata kafin ta gaida maa tenya sbd maa sakinah ita tana dakinta ma tin dazu.

Ammin ce da kanta ta zuba mata abinci da wani kakkarfan hadin madara me zafi datace daga yanzu kullum shi zaa ringa bawa bahar din kullum,

Daman tenya shi take bata tinda abin ya faru tafiyar da sukai ne ta dena sha sai kuma da Ammin ta dawo shima suka dena bata sbd kada ta gani tasan Bahar ta san Namiji kenan sbd hadi ne da kadai ake bawa wadda ta zama macen cikakkiya a cikin masarautar boyem.

Madaran kadai tasha sama sama sai abinci kadan tace ta koshi zata miqe Ammi tace ta sake ci ta koshi.

Sake cin abincin tayi ta tura ta gama ta miqe saita kasa komawa daki taxo gurin Maa sakinah ta lafe gefenta sbd har lokacin ba fuska sosai a gurin Ammi gashi taqi mata fada jira takeyi su isa ta hadasu su biyun kila wanda hakan ke daga hankalin Bahar sosai taji tana shiga damuwa.

Haka suka wuni har dare sukai sallolinsu magrib da ishai suka fiddo komai aka saka a mota suka bar gidan.

Suna ficewa kai tsaye ba doguwan bata lokaci da tafiyan slow suka isa airport daga nan ma ba bata lokacin suka bar qasar zuwa qasar Boyem.

Baccin da basu samu yiba a daren kusan dukansu suka samu a jirgin dan haka hankali kwance sukai baccinsu sbd suna first class,.

Ammi ce batai wani bacci ba sbd abubuwan dake kanta kala kala dana NUAB dana sultan dana Bahar ma ga damuwan da Zuhrah take ciki itama dan haka kanta ya dan dauki zafi da damuwa.

Bayan asuba har gari ya fara wayewa suka sauka dan haka already motocin sultan yasar guda biyu data securities daya suna airport suna jiransu,

Shiga motocin sukai aka bar Airport dasu zuwa masarauta kowannensu na sauke ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwan sauka lafiya.

Ita kanta Bahar datake cikin sanyin jiki ajiyan zuciya ta sauke a daidai lokacin da aka wangale musu makeken gate din masarautar na farko wanda yaji sauyi da wasu zafafan securities hakama babu inda bai sauyaba a masarautar tin daga gate din komai ya sauya ya zama na asalin zamani dake ihun ilimi da wayewa dan kuwa wata nutsuwa ma ba shakka ko tsoro irin na baya ba masarautar take ba a yanzu dan a baya kana shigowa zakaji kanajin tsoro da shakka sbd koina karfin ikon mulki kawai yake bayyanawa sabanin yanxu da shaawa da burgewa da wani irin ikon mulki me burgewa zakaji kana gani da ji.

Parking motocin akai suka fito bayin bangaren nasu suna jere a tsaye suna jiran isowansu dan haka cikeda girmamwa suka fara musu barka da zuwa suna karban hadbags din kowacensu kansu a qasa kafin suka tafi suka fara jan suitcases dinsu a natse zuwa ciki.

Kamar daga sama suna daga kafa ko taku hudu basuyiba wata lafiyayyan sautin qarar dawowan Uwar sultan me mulki a yanzu me boyem ta fara karade masaurautar tana ratsa koina.

Sultan NUAB dinne da kansa dayake zaune a daya daga cikin lafiyayyun sofas dake office dinsa a hawa na karshe dake building na offices nasu yaji saukar sautin yana ratsa kunnuwansa ya tabbatarda Ammin tasa ce ta iso sbd ya samu labarin barowansu daga daga drivern Bahar dan haka lumshe idanuwansa yayi ahankali yanajin wata niimar sanyi na ratsa gangar jiki da zuciyarsa sbd daga karshe dai matarsa ta iso garesa a maimakon tafiyan da zaiyi zuwa gareta a satin wanda ya shirya tsaf dan fuskantar Amminsa shima.

Sake sauke numfashi yayi me sanyi da nutsuwa yana dago kyawawan idanuwansa da harsun sauya sbd sabuwan nutsuwa da niimar data shigesu ya kalli Aleey da keelah dake gabansa sukai qasa da kai a natse sbd bazasu iya daukan idanuwansa a cikin nasu ba musamman da wani sabon yanayin yake bayyana a cikinsu.

Files din hannunsa ya ajiye a gabansu a natse yana maida bayansa ya jinginar a kujeran dayake ya bude baki yace

'Na duba duka abarsu a yanda tin farko aka tsaro,
And bazasu samu ganina ba sam a yanzu ko a kusa ba sai munga yanda business dasu din zai kasance,
Keelah kaine zaka hadu dasu a Moscow din ka gudanar da komai daidai yanda kasan muna komai na sealing deal din.'

'Yes LEUL' keelah ya fada yana daukan files din a hannunsa yana karanta wasu a ipad din hannunsa sbd daman sun saba dik businesses dinsu sune masu zuwa shi keelah ko Aleey sai manyan ne kokuma wainda suke na mahaukatan daloli yake zuwa da kansa hakama idan har tattaunawansu akan businesses nasu ne na GHAZs basa ambatarsa da sultan da LEUL kaman yanda suka saba suke kiransa wato Zaki sai idan harkar sarauta ce suke tsayawa kansu a qasa su ambacesa da Sultan LEUL boyem.

Su kansu tinda sukaji sautin isowan Uwar me boyem din suka shiga sabuwar nutsuwansu musamman aleey daya san lokacin haduwan NUAB din da sultan yasar yayi sbd Ammin dake tsakani ta iso.

Gama tattaunawa sukai kusan a office din suka kwana suna aiki sosai dan haka yanzune suke kokarin tafiya kowa ya kwanta ya huta dan yau sultan NUAB din bazai fito office ba kwata kwata sai gobe.

Fitowa sukai tareda hawa lift suka sauko securities da fadawan sultan din na masarauta suka miqe tsaye dukansu sbd suma anan suka kwana din suna gadi.

Gaba yayi a natse cikin kamewa da wata irin kwarjini da kyansa na sanyin safiyar dake hana kowa sauke idanuwansa akansa sbd tamkar wani sabon tauraro me haske haka yake haskawa yana daukan ido sbd lafiya da hasken fatarsa da kyau da jan hankali da cika ido.

Kai tsaye bangarensa su nufa sabo wanda girmansa yafi kowane bangare girma sbd girman ginin da akai da tsarinsa tareda zagayesa da qaramar katangar datai kyau da tsari ta kuma ji security.

Suna isowa aka bude masa kofa wangale duka securities na bangaren suna miqewa tsaye cikin girmamawa ya shige batareda ya bude baki ya amsa gaisuwansu ba da hannu kadai ya iya amsawa sbd yana buqatan hutawan gaske da samun nutsuwa a cikin kwakwalwansa.

Yana shigewa main kofar palonsa na farko tareda keelah da aleey iyakacinsu palon ba farko suma suka dakata tareda kai abubuwansa da suka shigo dasu a hannu inda ya kamata su ajiye suka juyo suka fice.

Zuwa nasu dakunan dake waje amma a cikin bangaren kowannensu lafiyayyan babban room and palo ne da toilet da sukaji luxuries suma suka tsaru suka hadu.

Kai tsaye hanyar bedroom dinsa dake kuryan wani palon na biyu ya nufa yana isa ya shige ya nufi closet dinsa ya zare kayan jikinsa tas a natse ya dauki towel a cikin jerin towels din dake jere kaman shago ya daura a qugunsa ya fada bathroom dinsa me girman gaske da tsari.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

143
Wanka yayi wanda ya dauki lokaci me dan tsayi a ciki yanayi sbd su brush da sauran abubuwan daya saba yi duk safiya kafin wanka tukuna ya fito yana fidda qamshin showerset dinsa dake tashi a fatar jikinsa.

Gashinsa dayake tsiyayan ruwa kadan kadan ya saka towel qarami yana gogewa yana nufar inda zai busar dashi da hand dryer dinsa.

Bai wani jima yana bata lokaci ba ya gama komai ya saka wata black bvlgari tight underwear data kama jikinsa ta zauna a qugunsa ya saka doguwar wando me santsi da fadi ta bacci ya isa lafiyayyan gadonsa ya haye ya shige bargo ya kwanta cikin jerin tarin pillows din gadon masu tsananin laushi ya lumshe idanuwansa yana rufewa take ba bata lokaci bacci ya daukesa hankali kwance.

Bangaren kaman yanda aka saba matiqar yana ciki yana hutawa kowane motsi ya dauke kenan dan haka kowama hutun ya kwanta yanayi sbd hana motsi.

***Haile ma dake kwance tana bacci cikin dan kwanciyan hankalin daya rage mata mara yawa sbd abubuwa sun taru sun tsaya gabanta ba sauki ko kadan sbd gasu Aslam a gabanta zuwa yanzu sun rikice sun fice hayyacinsu sun aje komai aure suke tsananin so ko wane iri ne dan haka ko lokacin komai basuda a yanzu idan bana neman hanyar samun miji ba sbd daga karshe dai sun gaji da zama akan kowace kalar tirban data dorasu tin kuruciyarsu har yanzu da manyancin yazo musu batareda samun komaiba,
Sun taso a wahalar neman mulkin da babu abinda zasuyi dashi suna mata,
Sun lalata future dinsu tin a baya da yaqin neman mulki ga wanda shi kansa yanzu ya tattara mulkin ya aje baya so sbd rayuwarsa data rasa madafar dafawa a yanzu,

Ta bangaren daya Asim tinda ya dawo daga tafiyar da yayi da matarsa ya kebe kansa baya son hayaniya ko doguwan muamala da kowa yana bangarensa gaisuwa kawai yake zuwa suyi ya koma bangarensa ba kamar baya ba hakama ya sauya sosai ko a gurin muamalantar mahaifinsa ya zama sabon mutum na daban ya samu karfi da taurin zuciyar daya rasa a baya ya zama cikakken namiji me dauriya da karfin zuciyar da bazai iya abubuwa da dama ba na mata ko hawa tirban da Mamensa zata sakasa kowace iri ce kuwa.

Wannan sauyin da haile take gani a tattare da yayanta da suka ajeta suna rayuwan da suka zabawa kansu ba wadda ta zabar musu ba suka koma wasu mutanen daban ya sakata rasa tudun dafawa sbd sune kadai abinda take dasu ta dogara dasu da aikatawa ko samar da kowace irin rayuwar datake so sbd sune tamkar makamanta datake son yaqar kowane yaqin datake so dasu batareda tinanin illar da hakan take musu ba ko zatai musu ba,

Damuwa take cikinta sosai ga Sultan daya tafiyarsa yabar qasar ya tafi ga mistress dinsa yabarsu ya zabeta wanda duniya take shadar da hakan a sannu a sannu,

Ga NUAB ba mulkin da duniya take magana a kai gabaki daya sbd ya kawo sabuwar duniya me burgewa da zamani da ilimi ga masarautar fiyeda wadda sultan yasar ya kawo sbd shima ya ingata masarautar fiyeda sarakunan baya gashi dansa a yanzu yana wanda ya fi nasa juma alfahari da farin ciki yake da hakan,

Su kansu manyan fada dasuke bayanta sun sauya sun zubar da makaman yakinsu sunbi NUAB fiyeda yanda sukai tsammani sbd daya saukesu 'yayansu ya dauka ya dora a matsayinsu dan haka a cikin farin ciki suke hutun sauka kan mulkin suna kallan yayansu a cikin gina sabuwar boyem da shekaru da zamani da qarni masu zuwa zasuyi alfahari da ita.

Jin sautin dawowan uwar me boyem ya saka baccinta yankewa tana bude idanuwanta ahankali tanajin kanta na mummunan sarawar daya saka taji kaman rabin jikinta yana neman dena aiki sbd wata riqewa da jijiyoyin jikinta sukai sbd tafi farin cikin a sakar mata qarar mutuwan sultan da dawowan ayanah rayuwarsu.

Tashi tayi ahankali tana rintse idanuwanta ahankali wani nauyi yana sauka kirjinta daga kanta ahankali ta sauke numfashi me zafi da damuwa me tsananin gaske.

A daidai wannan lokacin itama Maraki data zama tamkar babu ta a cikin masarautar tana zaune a bakin gadonta ta gama sallar asuba ta koma kenan zata kwanta taji sautin wanda ya sakata qasa da kanta tana rufe idanuwanta a hankali taji wani irin nauyi me radadi ya danne kirjinta sbd alkawarin data daukanwa kanta ayau ya tabbata zai cika kenan sbd tayiwa kanta alkawarin daga ranar da Ayanah ghaz ta dawo rayuwar sultan zata barsa har abada bazata iya rayuwa dashi ba kuma sbd zata iya mutuwa da baqin da babu wanda ya sani kaman yanda shi kansa zai iya shiga wuta batareda ya saniba sbd abinda ta tabbatar dashi shine Allah ya kaddari Ayanah ce zuciyar sultan da zai iya bata akanta batareda ya saniba hakama ita daman babu komai a tsakaninta dashi bayan macen biyan buqata sbd bai taba sonta ba a tsawon shekarun nan,bai taba mata kallan macen da zai iya wani girman abu akanta ba,
Bata haihuwa ba dan haka ko matsayin imebētis dinsa bata kaiba su da sun haifa jinin boyem a masarautar,
Mantawa akeyi da ita ko a tarihi da zaman masarautar,
Batada kowane irin amfani,
Batada kowane irin matsayi,
Ta zamar masa dole kaman yanda a yanzu itama ya dade da zamar mata dole,
Dan haka lokaci yayi da zata tafi ko zuciyarta zata samu sauki daga baqin ciki da damuwan datai shekaru tin na kuruciya tana yi,
Shi kansa a yanzu mafita da hanyar tsira yake nema yayi rayuwar aminci da kwanciyar hankali dan haka kaman yanda yayi freeing imebētis dinsa duka tana neman yayi freeing nata ta qarasa rayuwar data rage mata da kwanciyan hankali da dan farin cikin data rasa dan bata taba samunsa ba tinda tayi aurensa.

A zuciyarta ta dauka tanada sauran

78 / 100