Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   16 / 100

45K to 48K   out of 299.8K words

ke ciko idanuwanta da sukai jajir tana hana nata hawayen sauka sbd kada a gano halinda suke ciki sedai tata zuciyar harma tafi ta Zuhrah karaya da samun wata irin nutsuwar ruhi da bata taba samu ba tinda rayuwarsu ta wargaje,

Qanqame hannun juna sukai batareda sun juyo sun kalli juna ba ko motsin da zaa gane kowa da abinda yakeji a zuciya da gangar jiki,
Zuhrah kuka takeyi sosai tana sake sunkuyar da kanta qasa sosai tana rokon Allah kada ya raba hannunta dana Ayanah har sai ranta yabar jikinta.

Ayanah ma da kukanta ke komawa zuciyarta kukan zucin takeyi sosai jikinta na wata irin rawa tana sake qanqame hannun da shine hasken rayuwarta.

A wannan yanayin suka share duka awannin da aka dibar musu a cikin ruwan har saida ruwan ya wuce salap suna cikinsa tukuna aka bude kofar tareda shigowa da wasu irin tsaftaccin towels masu dan girma farare qal a basket me kyau kowannensu da baiwar da zata basa nasa.

A cikin wata irin saa me girman gaske saiga sakinah a cikin masu kawowan wadda kai tsaye gurin Ayanah ta nufa a natse kanta a qasa tana isa ta durqusa gaban a hankali tareda dago mata kyakkyawan kwandon da towel din yake ciki yana fidda qamshi me dadi.

Cikin karfin Hali zuciyarsu na yanka suka raba hannuwansu kowacensu na Juyawa ta fice batareda kowa yaji muryan kowa ba sbd basuda daman magana baa basu damar ba.

Towel din Ayanah ta dauka ahankali ta daura a jikinta Bayan sakinah ta miqe a natse ta tayata zare halfvst din jikinta,

Juyawa sakinah tayi zata bar gurin kanta a qasa idanuwanta suka sauka akan Zuhrah wadda ke fitowa daga ruwan itama take jiri me karfin gaske ya dibeta saura kiris ta kife Allah ya bata ikon tsayawa dakyau tana hana firgicinta bayyana sbd zata iya rasa rayuwarta.

Tsurawa Zuhrah idanuwanta tayi tana tafiya kanta na tsananin sarawa da abinda take gani,

‘Zuhrah da Ayanah a matsayin imebēti na Mutum daya?’
Wace irin mummunan qazamiya kuma haramtacciyar kaddara ce wannan?
Tayaya Mutum daya zai kusance su kuma su samu cikinsa su haihu?
Tayaya ma wannan tashin hankalin kaddarar zata fara?
Shin Ayanah da Zuhrahn sunga junansu kuwa?
Idan sun gani sun kuwa San menene yake shirin faruwa dasu?
Idan har sun sani tasani zasu gwammaci su mutu su dukan dasu yadda da wannan mugun tashin hankalin’

Koda sakinah ta fito daga gurin bata ganin gabanta sosai sbd tama kasa yadda da Zuhrah ce idanuwanta suka gano mata dan bama zai taba yiyuwaba wannan kaddarar a yanzu kam tayi nauyin da kila dole zaa iya rasa dayansu biyun.

Su kuwa suna gama daura towels din daya bayan aka nuna musu wata kofa suka shiga toilet ne masu kyau da tsari a jere dan suyi wanka da ruwan dumi sosai kafin su fito kowacensu akaita sabon gurin da zata zauna,

Suna shiga gurin a kebe yake dan haka rufe su akai sbd su ayanzu ba kowa akeso yaga jikinsu ba dan kuwa sun zama tamkar Al’aurar da haramun ne ganin jikinsu,

Ana rufe su kowacensu ta nufi toilet daya ta shige aka bar Ayanah a tsaye tareda Zuhrah wadda itama take tsaye cak babu Wanda ya motsa a cikinsu tsawon mintina uku,

Tsit gurin yayi sai motsin ruwan daya fara tashi ahankali na fara wankan da Sauran sukai,

Sai a lokacin Ayanah ta dago ahankali cikin wani irin slow na tsananin mutuwan jiki ta Dora fararen idanuwanta masu kyau da kashe jiki akan fuskan Zuhrah wadda itama dagowan tayi ahankali.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

27
*_UMMU ASLAM COLLECTION_*
08035014107
-Ina mata yan kwalisa masu son burgewa?
-Shin Kayan kitchen na zamani masu sauki da rahusa na kitchen din yan gayu dama na gargajiya kike so?
-shin abayas na yayi da daukan ido da burgewa kike nema?
-kokuwa original misk dahara kuke buqata dan asali?
-kokuwa Kayan GHT na Neman lafiya da gyara kike so?
-ke harma laces da atampopi na alfarma masu sauki kikeso?
To duka kinzo gidansu indai sune abinda kike buqata ba bata lokaci kinzo kin gama samu kawai tintibi UMMU ASLAM COLLECTION 08035014107 duk inda kike zata aika miki batareda bata lokaci ba.

*********
Idanuwansu na haduwa sarewa Ayanah taji kafafunta na Neman yi ta dafa bango ahankali wannan Karan hawayenta gangarowa sukeyi suna sauka fuskanta har zuwa kirjinta ta rintse ido wani yanayi na cikata ta sake bude idanuwanta akan Zuhrah dake kuka sosai itama tana jin kafafun nata sun gaza,

Ahankali suka tako zuwa juna babu kowa dake ganinsu dan haka suna qarasowa wata irin runguma sukaiwa juna Ayanah na zubewa qasa Zuhrah ta bita qasan suna rungume da juna qamqam kaman zasu shige jikin juna,

Kuka sukeyi sosai kaman ransu zai fita mara sauti sbd kada a jiyo su,

Hannuwan Ayanah suna wata irin rawa ta kamo fuskan Zuhrah ta tsira mata ido hawaye na gudu sosai akan fuskanta tsawon mintina kafin takai bakinta ta sumbaci goshinta ta sumbaci gefen fuskanta ta sumbaci tsakiyar kanta ta kamo hannuwanta suka ta sumbata koina jikinta rawa yakeyi sbd jin kaman zata Hadiye Zuhrah,

Zuhrah kuwa batada Sauran kowane irin kuzari qanqame Ayanah din kawai takeyi tana kuka kaman ranta zai bar jikinta jikinta na rawa itama sosai,

Magana sukeyi wa juna amma ba daman hakan sbd zaa iya jinsu dan haka babu Wanda ya iya bude baki a cikinsu sedai ido da hannuwansu ke aiki,

Zuhrah duk yanda taso kasa riqe kanta tayi ta gama ficewa hayyacinta kamo fuskan Ayanah tayi da tafin hannuwanta biyu takai bakinta kan kunnenta ta bude baki da wani irin sauti daya saka gabaki daya dan Sauran karfin halin Ayanah rushewa tace

‘Yēne Ayanah(my Ayanah),hiyiwēteni(my life),Yene widi(my precious)’

Rintse idanuwa Ayanaah tayi tana sake qanqame Zuhrah kafin ta bude bakinta cikin tsananin sanyi da mutuwan jiki tace

‘Ina rokon Allah ya zama gatanki Zuhrahna ya baki kariya da juriya tareda ingancin rayuwa,
Bazan taba barin a gurbata rayuwanmu da alaqar mu ba,
Duk halinda zamu shiga bazamu taba zama a cikin qazantacciyar alaqar da akeson mu zauna ba,zan baki kariya da rayuwata koda bama tare,
Zan zabi mutuwa akan a hada mu a qazamiyar shimfidar mu yada mummunan zuriar datake ta Allah wadai a garemu matiqar muka hada shimfida da Mutum daya…..’

Kuka sosai Zuhrah ke qarawa sbd maganganun Ayanaah din dake sake kashe rayuwarta sbd sunzo gabar da kaddarar tayi musu muni me girma bama girma ba,

Duk shauqin ganin junansu Ayau Bayan shekara guda bai taho musu da alkhairi ba dan kuwa wannan shine mafi girman quluwar kaddararsu da basusan tayaya zasu fuskancetaba kuma tinda aka zabesu din to tabbas Ana nufin sai sun sauke buqatar sultan din BOYEM Wanda mutuwar dayansu ce kadai zata Hana hakan idan kuma sun fito sun bayyana alaqarsu sbd Kaucewa hakan to dukansu ne zasu rasa ransu sbd sun aika laifi me girma ita kuma a yanzu tanason ko yayane dayansu ya rayu sbd Abaas dayake raye a duk inda yake.

Sun jima a hakan kafin daqyar suka iya rabuwa da jikin juna sbd motsin fitowan wasu wanka dan haka kai tsaye a sanyaye suka fada toilet daddaya suma take suka sakar wa kansu ruwa sbd kukan ruwan ya hana aji sautin kukan dasuke fasa a tare.

Sun jima a toilet din kafin suka fito kusan a tare suka fito kan kowannensu a qasa batareda sun sake kallan ko inda inuwan juna take ba.

Haka aka fice dasu zuwa inda zasu zauna kowannensu da Wanda zai taimaka masa zama a dakinsa dan sai wadda sultan ya kwana da ita zaa warewa bangarenta me girma da bayi idan ta samu ciki zata cigaba da zama idan bata samu ba sultan ya gama yayinta tafiya ake da ita.

Kwata kwata ba guri daya aka aje su ba kowa da dakinta daban dan haka suna dawowa ba jimaw aka kawo wa kowacensu lafiyayyun Kayan itatuwa da zallan madarar nonon raqumi me dumi da zuma tareda duk wani abu dazai Kama jikin mace na qarin Ni’iman nace me karfin gaske.

Sakinah aka kawowa Ayanah wadda taje taji jikinta ya sake mutuwa Ana rufe musu daki ta zube gaban sakinah tana kuka me karfi da Neman yaya zatai da rayuwarta da wannan sabuwar kaddarar.

Sakinah ma kukan takeyi cikin tashin hankali da rashin sanin tinanin yi dan kuwa wannan Karan ko ita batada shawarar bayarwa sbd abu dayane a bayyane tabbatacce kuma shine Allah ne kadai zai Hana dayansu barin duniya kokuma su dukan ma.

Kuka sukeyi tare tsawon lokaci kafin aka taba kofar dakin wadda ta sakasu shire hawayensu suna Miqewa tsaye kansu a qasa sakinah ta bude dakin.

Tenya ce da kanta tareda masu Binta a baya kaman zasu mata sujjada,

Shigowa tayi tana kallan fuskan Ayanaah din wadda fuskanta ta kumbura sosai tayi jajir alaman kuka me karfin gaske tayi,

Ajiyan zuciya ta sauke a natse tana sake kallan Ayanah din cikeda mamaki da tinani Kala Kala sbd tinda aka kafa tarihin masarautar babu macen data taba kuka akan zaa kaita shimfidar sarki duk kuwa tsoro da fargaban da matan suke shiga babu wadda ta taba kuka na bayyane sedai na boye na zuci amma Ayau idanuwa da komai na jikin Ayanah bayyanarda tsananin qiyayyrt da hakan yakeyi.

Numfashi ta sake saukewa tanajin haka kawai Ayanah din takeson ma idan sultan YASAR ya sauko a Daren ya fara tarawa da ita tsawon sati guda kafin ma a sake kai wata.

Murmushi me kyau ta sauke ahankali tana sake qarewa zallan kyau da wani irin sanyi da nitsuwan Ayanah din ido ta bude Baki tace

‘Yaya sunanki??

Sai a lokacin Ayanah ta motsa tareda dago manyan idanuwanta ta sukai jajir ta bude bakinta da sauti me tsananin sanyi da mutuwan jiki tace

‘AYANAH GHAZ’

maimaita sunan tenya tayi cikin kulawa da jin Ayanaah din na shiga tinani da zuciyarta tareda jin tabbas da tanada ‘da namiji yanta Ayanaah din zatai ta aura masa sbd tanada abubuwan da duk takeson mace ta mallaka dan haka koma yayane Ayanah sultan YASAR sai ya maidata cikakkiyar mace.

Take ta bada umarnin duk abinda aka kawo na Shan a bawa Ayanah a gabanta ta shanye,
Hakan kuwa akai haka aka fara dauko su daya bayan daya Ana bawa Ayanaah din tana shanyewa hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwanta Wanda ya saka tenya sake jin Ayanah na zama dole imebēti.

Su tenya na ficewa Ayanaah ta darare ta zauna bakin gado tana kallan koina na dakin babu kowane irin abu dazai Baka ikon daukan rayuwanka dan haka zame wa tayi qasa tana jin kaman zata Amayar da zuciyarta.

Sakinah na gefe ta rasa abin yi itama se zuru tayi idanuwanta jajir sukai shiru,

Zuhrah ma koda aka tafi nata dakin idanuwanta sosai suka nuna abinda idanuwan Ayanah suka nuna amma ita tayi kokari ta hana a gane sbd tasan a duk inda Ayanah take zaa gane yanayinta.

A wannan Daren tin daga Ayanaah har Zuhrah babu Wanda ya rintsa a suka kwana cikin tashin hankali da mugun yanayi,
Sakinah ma bata rintsa ba a Zaunen ta kwana sbd babu mafita tako Ina a masarautar BOYEM din da gaske komai naka a tafin hannunsu da ikonsu yake,

Washe gari yanayin Ayanah sake munana yayi sbd idanuwanta da sukai wani irin mummunan kumburin daya sauya kamannin fuskarta gabaki daya dan haka kai tsaye tenya da kanta yau ta tsaya akan jiqon lallen da akai musu har aka gama tana tsaye ta saka ido babu ta inda ko kallan juna suka samu sukai dan haka suka sake shiga tashin hankali sbd suna tsananin son magana da juna sbd Neman mafitar wannan masifar,

Washe gari ma haka tenya ta tsayu sosai da kanta tayi musu komai aka qara tsananta kulawa akansu,

Tashin hankali da tsananin tsoronsu koyaushe qaruwa yakeyi sbd kwanakin dake kusanto su,

Ayanah gabaki daya rayuwanta ne take jin ta gaji da ita sbd ba iya hadasu da zaayi gurin biyawa Sarkin qasar buqataba da yar uwarta uwa daya uba daya ita kanta batajin har abada zata iya rayuwa a matsayin baiwar biyan buqata a duk lokacinda aka biqaci hakan,
Ta zabi mutuwarta a daidai wannan gabar sbd rayuwar da zata yi a yanzu batada banbanci da abinda akaiwa Nurat dinta kafin rasuwarta,
Bazata iya zama abinda aka zabeta ta zaman ba dan haka rayuwa gabaki daya ta fita kanta Hutu kawai take buqata daga duniyar.

Wannan tinanin ne yake fitar da ita hayyacinta da rashin magana da Zuhrah wadda itama take ficewa nata hayyacin,
Wani irin sauyin kamanni ta fara samu Wanda ya saka attention din tenya dawowa kanta sosai ta dauketa ta sauya mata guri kwata kwata aka fara hada mata da maganin saka bacci a cikin abincin da ake bata Wanda bata ma iya ci Sai an tsareta.

Fara bata maganin bacci ya saka tinaninta tsayawa cak batada lokacin tinanin komai koyaushe cikin bacci take sbd anason ta samu baccin da zai bawa jikinta lafiya.

Zuhrah da baa Ankara da nata tinanin na ganin da gaske babu sauyi a wannan mummunan kaddarar dake tinkaro su hakama kwata kwata ta Dena ganin Ayanah wadda aka kebe daban dan haka zuciyarta ta rasa tinanin kanta batada Wanda zatai magana dashi taji sanyi,batada Sauran hope na rayuwa ko kadan dan haka ta yanke shawarar itama hakura da rayuwan gabaki dayanta dan mutuwarta ce kadai zata hanasu hada wannan kaddarar.

A cikin Daren ta cire Kayan jikinta ta saka farcen hannuwanta biyu duka tafara yagar fatar fuskarta da karfin gaske cikin wata irin azaba me tsananin wuyan hadewa tana kukan azaba mara sauyi jini sosai yana fita daga duk inda ta yaga da karfi,

Fuskanta da fatar wuyanta zuwa kirjinta da hannuwanta tareda bayanta take yaga tana buga kanta jikin bango sbd azaba,

Take jini me yawa yafara lalata inda take karfinta na ragewa ahankali.

A daidai wannan lokacin itama Ayanah ta farfado cikin Daren ta tashi Zaune tareda zare Kayan jikinta ahankali tareda daurewa zata rataye kanta dan kuwa bata fatar ganin washe garin gobe da zaa fara musu shirin matakin karshe na isa tirakar sultan YASAR BOYEM.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee

28

*_UMMU ASLAM COLLECTION_*
08035014107
-Ina mata yan kwalisa masu son burgewa?
-Shin Kayan kitchen na zamani masu sauki da rahusa na kitchen din yan gayu dama na gargajiya kike so?
-shin abayas na yayi da daukan ido da burgewa kike nema?
-kokuwa original misk dahara kuke buqata dan asali?
-kokuwa Kayan GHT na Neman lafiya da gyara kike so?
-ke harma laces da atampopi na alfarma masu sauki kikeso?
To duka kinzo gidansu indai sune abinda kike buqata ba bata lokaci kinzo kin gama samu kawai tintibi UMMU ASLAM COLLECTION 08035014107 duk inda kike zata aika miki batareda bata lokaci ba.

*******
Shigowan sakinah yayi daidai da ture stool din da Ayanah ke Kai da qafa datai idanuwanta a rufe ta fara Wani irin shura qafa da fizge fizge jikinta na rawa sosai sbd mutuwar da gaske ta taho gadan gadan,

Sakin Kayan hannunta sakinah tayi cikin mummunan tashin hankali da tsananin tsoro da firgici ta isa gurinta da gudu har tana kifewa ta tashi da rawar jiki tsoronta tsananta ta isa gareta ta riqe kafafunta da sauri koina na jikinta na rawa,

Da hannu daya ta dauki stool din duk nauyinsa ta Dora a setin kafafunta ta tsayar da ita kafin a rikice ta taka gadon dake dakin ta taka wardrobe ta zare daurin suka fado qasa tareda Ayanah din tana rungumeta da tsananin karfi tareda fasa kuka Mara sauti sbd tashin hankalin tinanin rasa ayanar da zatayi da bata shigoba a lokacin,

Ayanah da gabaki daya jikinta ya sake idanuwanta a rufe suna gangaro da hawaye masu dumi bata iya motsawa ba sedai kukan sakina kawai dake Ratsa kunnuwanta yana sake kashe zuciyarta da batada Sauran tinanin komai sbd ta yanke rai da rayuwa.

Kuka sosai sakinah takeyi sbd batasan yaya zatai qarashen rayuwarta babu Ayanah ko daya daga cikin jinin GHAZ ba sbd sune rayuwarta itama sune tamkar nata jinin da batada kowa duniya Bayan su hakama har abada matiqar tana tareda Ayanah ita baiwar tace sbd haryanzu bawai ta yanta bane suna tare ne kawai harma suka manta matsayin junansu sbd sun samu kansu a wata ukubar rayuwar data mantar dasu cewan su din baiwa da uwar daki ne amma har abada koda BOYEM ta yantata matiqar Ayanah bata yantata ba ita din baiwarta ce har qarshen rayuwanta Wanda ita kanta indai tana tareda Ayanaah zata rayu da ita har qarshen rayuwanta to batama buqatar yancin zatai mata bauta ta bita har abada.

Kuka sosai sakinah tayi na tsoron halinda Ayanah din ta shiga kafin ta iya sake Ayanah wadda har lokacin yake kaman batada lakar komai a jiki sai idanuwanta dake bude jajir suna fidda hawaye masu dumi dake gangara a hankali.

Gadon sakinah ta gyara har lokacin itama idanuwanta hawayen sukeyi ahankali tana gamawa ta kamata ta kwantar kafin ta maida komai inda yake ta gyara dakin kaman babu abinda ya faru sbd duk motsinta ma bata Bari anji komaiba sbd kada asan abinda Ayanah din tayi kokarin yi hukuncin dazai hau kanta bazai taba zamowa me sauki ba,

Tana gana gyara dakin ta juyo da idanuwanta da suka sauya sosai ta kalli Ayanaah zatai magana aka taba kofar dakin Wanda ya sakata saurin daidaita kanta tana goge fuskanta ta dauki towels din data shigo dasu dan kaiwa inda zata jere su.

Ayanaah ma idanuwanta ta rufe a hankali sbd bata kaunar ganin komai da kowa idan ba yar uwarta jininta ba Zuhrah.

Tenya ce aka budewa dakin ta shigo wainda ke biye da ita suna dauke da wasu magungunan gargaji masu tsafta da kyau aka shigo dasu Ana jerewa a table,

Idanuwa tenya ta zubawa Ayanaah tana kallanta haka kawai taji bata iya Kyale Ayanah akan zamowanta imebēti wadda koda zata sauya kowa bazata taba sauya Ayanah GHAZ ba komai wuya tanason ganinta a imebēti sbd itace kyanta yakeda tsananin nutsuwan da zai iya girgiza Kyan HAILE da qasar take taqama dashi ita kuwa a nata bangaren batada burin daya wuce takai HAILE qasa ta hanyar samun macen da zata kere ta a gurin sultan musamman idan Allah yasa aka samo LEUL ba a gurin HAILE ba sbd Qin HAILE a jikinta yake tin daga lokacinda ta dauke ran qanwarta uwa daya uba daya da ita kadai gareta sbd kawai ta samu cikin sultan a matsayin imebēti a lokacin da tana yayin dauke rayukan duk macen daya kwanta da ita,

Wannan ne dalilin daya saka tenya batada burin daya wuce samar da

16 / 100