Hayateem 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Adventure

Chapter   59 / 100

174K to 177K   out of 299.8K words

qasan zuciyarta ta kalle shuraim bayan sun zauna a cikin lafiyayyan jirgin ruwan dazai bar dajin garin gabaki daya dasu ta sauke ajiyan zuciya tana kallan shuraim tace

'A hakan kake tinanin zan iya hada miji da illiterate macen data taso anan?
Tayaya ma zata iya rayuwa a tsakanin ni na SULTAN din da mukeda tarin ilimin da batada shi?
Bama zan iya zama da jahila ba sbd ilimin nawa 'yayan dazan haifa.....

Shuraim ne yayi saurin dora hannunsa akan nata cikin wani irin salon da Ammi data tsare leylah din da ido bazata gane ba ya dan dakatar da ita yana fuskewa.

Ayanah shiru tayi tana kallan Leylah cikin sanyi da nutsuwa hakama wani nauyi yana danne kirjinta da batajin komai a cikinsa yanzu bayan zallan kauna da soyayyar bahar wadda itace zata kasance uwa kuma ubanta.

Zuhrah ma da zancen ya ratsa zuciyarta da kaifi tareda rakaici da baqin cikin jin hakan daga bakin 'yarta akan 'yar dan uwanta kallan ayanah tayi a sanyaye sedai ganin ayanah ta dauke idanuwanta ahankali akan leylah din batateda tace komaiba ya saka itama tayi shiru kowama yayi tsit har suka isa ba wanda yace kala.

Suna isa kai tsaye masaukin sultan aka nufa da ayanah su zuhrah kuwa a ranar suka bi jirgin dare suka koma.

Ayanah tinda ta dawo sultan ya fuskanci damuwa sabuwa dake tattare da ita dan haka a daren bai samu nutsuwa ba saida yaji damuwarta wadda kai tsaye ta sanar masa tanason bahar tabar boyem ta tafi wata qasar karatun datake son ta sauya rayuwarta ya bata yancin zabar raayin auren NUAB ko sabaninsa.

Sultan daya fahimci daci da radadin dayake zuciyarta akan bazata taba iya barin bahar ta samu tangardar rayuwa ba NUAB yace ta fara sanarwa,

Girgiza kai tayi cikin nutsuwa tareda bude baki tace

'Nice zan dauki nauyin karatunta da kaina banason NUAB yayi mata komai akan duk abinda ya shafi neman iliminta'

Sultan hakan shine yayi daidai da nasa raayin akan Bahar wadda Ayanaah zata tsayawa tai mata gatan komai kaman yanda Kowa iyayensa ke tsaya masa su basa ilimin daya kamata dan haka kai tsaye ya kira kadir ya bada umarnin komai na bahar da karatunta ya kammalu a cikin qanqanin lokaci.

******Ayanah batai raayin baro kasarta ba a kwanaki kadan dan haka kusan sati uku suka share a qasar batareda kowa ya taba samunsu a waya ba sbd hatta tenya su Zuhrah tabi ta koma.

A bangaren kadir ma cikin wata irin rashin bata lokaci da tsayuwa cak akan umarnin sultan din ya nemarwa Bahar kusan komai da ake buqata na karatu a qasar UK sbd sunada manyan connections.


Sai da sukai wata guda cif a qasar suka diro boyem wanda yayi daidai da lokacin tafiyar bahar da NUAB baisan da itaba hakama daidai dawowan haile da yayanta hakama tsawon wannan lokacin BAHAR da NUAB din basu taba haduwa ba.

A ranar da suka dawo a ranar saura kwanaki kadan a tafiyar bahar din wadda zata tafi tareda maa sakinah a gidan da aka tanadar musu acan domin rayuwa a cikinsa.

A daren Ammi tana isowa ta kira NUAB ta sanar dashi wanda yayi shiru ya rasa abin cewa zuciyarsa na wani irin daukan zafin dayake ciki tsawon wata gudan nan da sukai basa nan sbd sultan daya gama shan gabansa akan mahaifiyarsa.

Baicewa Ammin komaiba akan tafiyar haka ya miqe ya tafi zuciyarsa kaman zatai bindiga sbd yasan koma menene da ina wannan tsarin ya fito ya fito ne daga mahaifinsa dan haka shima zai san ya tabasa,

Yana dawowa bangarensa kai tsaye aleey ya kalla da jajayen idanuwansa ya basa umarnin a nemawa Ammi komai na tafiyar bahar da ita zaa koma UK din tabar boyem har sai bahar ta kammala su dawo tare.

Kallansa aleey yayi da dan sauri cikin fargaba da mamaki amma baida ikon fadar komai haka dan haka cewa yayi angama kawai ya juya fice yana daga wayarsa dan samar ma da bayanin komai akan tafiyar ta bahar da inda zata zauna da inda zatai karatun wanda ba iya Ammi kadai ba hatta su zai samar da komai na tafiyarsu ya ajiye sbd daga yanzu qasar zata zama gurin zuwansu kowane lokaci.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

106
Bahar har zuciyarta tafiyarta karatun yayi mata daidai tareda bata dukkanin nutsuwan datake jin tana buqata na rayuwa a wajen Boyem sbd a cikin wani irin tsananin tsaro suke rayuwar babu yancin shan iskar rayuwar da duk kake buqata,

Damuwarta daya ce rabuwan da zatai da Ayanah wadda a yanzu kauna ce me karfin gaske a tsakaninsu sbd ita kallan Abaa dinta takeyi mata kaman yanda itama ayanah din kallan Abaas dinta takeyi mata hakama a yanzu da suka san juna suke tare da juna suke kuma kaunar juna a bayyane a zahirance babu shamaki ko daya,

Kauna ce ta asalin bayyane dake cikin jininta ayanah kewa bahar din wadda kusan a hankali duk wanda yake tareda dasu a masarautar suke sani,

Itama bahar a yanzu tana kokarin sakewa da Ayanah din kaman yanda ta sabu da maa sakinah dinta dan bawa ayanah din dukkanin sanyin zuciyar datake buqata daga gareta,

A bangaren daya tenya da Maa sakinah gabaki daya soyayyarsu suma da kaunarsu akan bahar din take duk da suna nunawa Leylah tata kaunar sosai itama amma sbd kaunar da sukewa Bahar ta bangare uku ce zuwama hudu sai tata din tafi bayyana,

Ta farko asalin kaunar mahaifinta ce,
Ta biyu ta zamtowanta mata a gurin 'dansu da suke tsananin so wato sultan LEUL,
Ta uku kasancewanta Rabin zuciyar ayanah da bata hada da komai,
Saina karshe shine zamtowanta marainiyar da batada uwa batada uba saisu,

Ita kanta Zuhrah kauna me karfi mara sirki takeyiwa bahar din wanda taso saka hannu sosai akan bawa bahar din ilimi da inganta rayuwarta amma Ayanah ta dakatar da kowa daga hakan bata son kwandalan kowa a gurin bawa Bahar din ilimi sbd har abada tako wane bangaren bata son ayiwa Bahar gorin komai na rayuwa matiqar dukiya zata nema ta samar mata dashi koma menene.

Hakan ya saka ta sake ta fidda dukiya me yawan gaske dan sauya rayuwar 'yarta zuwa duk inda 'ya mace me gata zata kai,

Bedroom daya aka warewa Bahar din acikin bangaren itama aka gyara matashi da komai sabo me tsadar gaske da duk wani jin dadi da tsarin da zai tabbatar maka daka shigo dakin mace yar gata me aji,

Closet din gaske aka kira masu shiryawa suka shirya mata da wasu irin designers na kasashe daban daban fiyeda a tsaya kirgawa,

Undies da kayan bacci ma haka aka taho dasu masu kyau da tsada ba adadi aka jere kafin suma designer shoes and hand bags harma suitcases na tafiya da tirarika da wasu duk abubuwan da akasan mace na buqata an kawo an jere su a dakin an kammala mata komai tamkar ba wadda zatai tafiya ba tabarsu kuma taje can a siya wasu kayan,

Ba iya kayan designers aka tsaya ba hatta sitirun sarauta dana Al'ardarsu an kawo su masu tsada an jere mata su tareda Tirarikan da Maa tenya ta hado mata da kanta wainda suna kama jikinka to shikenan ka gama zama mai ratsa zuciyar duk wanda zai shaqa qamshin wanda komai na irinsa akwaisa zaka samu a gurin (SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387)

Maa Sakinah ganin rayuwar Bahar ta sauya sawu zuwa kyakkyawar rayuwar da kowane dan gata me uwa da uba zai samu ya saka zuciyarta da hankalinta kwanciyan da a yanzu babu abinda take so da buqata arayuwa bayan gamawa lafiya.

Ayanah ma kasancewan Bahar din a rayuwartata ya saka dangana me karfi da tawakkali da cire dukkanin wani qunci a ranta suke shigeta tasan bazata taba manta rayuwar data fito da kaddara me girma da muni ba amma kuma samun Bahar ya lullube mata kaso me girma a cikin baqin ciki da quncinta ga kuma ganin Zuhrah a tareda ita da 'yayan Zuhrah dan haka ta rungume sabuwan rayuwan data zo mata da hannu biyu dan hana 'yayansu shiga damuwa da quncin da zasu ringa fuskanta da gani a tattare dasu.

Zuhrah da itama ta samu hadin kai sosai daga mai girma yunar akan kasancewa da yar uwarta ba shamaki sakewa tayi suna bayyanar da kaunarsu da aka raba ta shekarun da sun riga sun rasa dan ba lallai su maimaita irinsu ba..

Duk wannan shirin da akeyi da kokarin inganta rayuwar Bahar LEUL baya ciki sbd sosai zuciyarsa ta tabu da hakan dan babu inda ko shawara Amminsa tayi dashi dan haka yaqi cewa komai ya kuma dena shiga komai din dan kuwa ita kanta Bahar bayajin zai sake bi ta kan rayuwarta kwata kwata zebarwa Amminta ita koma me sukeso suyi,

Ya rage shigowa sosai bangaren na Amminsa sbd ayyukan gabansa da sukai masa yawa da kuma tattara komai nasu da yayi ya ajiye musamman koyaushe bangaren kusan a cike yake da Zuhrah da 'yayanta dake wuni bangaren basa taba tafiya sai dare duk da leylah har lokacin a bangaren take bata koma bangaren iyayenta ba,

Sultan ma dayake bangarensa hutun gaske yake samu babu kowane irin damuwa da tinanin mulki dayake kansa dan haka shirye shiryen barin qasar yakeyi zuwa dogon hutun da kansa sai sake bayan shekaru masu yawa akan mulki,

Leylah duk inda hankalinta yake baya cikin jin dadi ko kadan kowane dare da baqin ciki take wuni hakama kowane wuni da baqin cikin take wuni sbd yanda aka jingine maganar aurenta tsaf a gefe da sultan me mulkin boyem an maida hankali akan yanda zaa inganta rayuwar wadda take ganin aikin banza ne kawai sbd har abada bazata samu ilimin da zai saka LEUL me boyem sonta ba harma ya iya zaman aure da ita sbd alamu suna nunawa mulkin yanzu da zai wakana a boyem na sauyin zamani da ilimin boko ne da baa buqatar duk wani mara ilimin a cikinsa.

Bahar bata taba damuwa da kiyayyar datake gani a idanuwan leylah ba sbd tana daukan hakan ne a matsayin rashin sabo da sakewan da basa dashi kwata kwata a tsakaninsu dan sam ko guri daya basa zama sbd ita kanta hakanan bata jin shaawan zama idan leylah din ta fito a guri sbd irin kallan datake mata da magana a cikin rashin mutuntawa ko nuna darajar dan adam gareta ita kuwa sam bata iya zama da duk wanda yake hakan dan batajin tanada rashin darajar da har zaa ringa mata kallan qanqantacciya dan haka saima tafi leylah din rashin son zama a duk inda take sam bata buqatan zamowa inuwa daya da ita.

Shuraim kuwa tinda ya dora idanuwansa akan bahar a ranar farko yaji zuciyarsa ta nutsu da ita nutsuwan dayake jin zai iya rayuwa a duk inda take dan haka sai bayada gurin zama fira a boyem din idan baa bangaren Ammi ba a tareda iyayen nasa da Bahar wadda take wata irin sauyawa tamkar ba ita dinba dan kuwa sosai ayanzu tenya take mata gyara itace ke kulawa da komai na bahar din musamman kasancewanta mace akwai abubuwan buqatarta da amfani da dole sai masu kyau da tsari da banbance ta da sauran matan daba jinin sarauta ba data tanadar mata suna jere birjik toilet dinta da gaban mirror dinta a tsare.

Sosai shuraim yake shigewa Bahar wadda sam bata saba muamala da mutane sosai ba dan haka bata wani sake masa duk da a cikin salo da nutsuwa da kauna tareda saka alaqar zumunci me karfin da suke dashi ya ringa janta a jikinsa duk da yasan akwai auren NUAB a kanta amma a yanda a yanzu Ammi ta tabbatarda aurenta da NUAB idan tanada raayi ne zaaci gaba idan batada shi sam babu zaa raba sbd bata damar rayuwa da zaban duk wanda takeso dan haka kafin ta fara karatu koma karatun yayi nisa ayi wannan zaman tambayar yana buqatar shaquwa da kauna a tsakaninsu dan kuwa a shirye yake da aurenta daga lokacin da auren NUAB ya sauka akanta daman kuma yanada tabbacin ba iddarsa akanta dan kuwa zai kafe ya tsare ya tabbatarda iddar NUAB bazata taba hawa kanta ba,

Leylah ma data samu wannan bayanin batai wani farin ciki ba duk da tafara karantar halinda shuraim yake ciki amma batajin zata iya barin shuraim ya mallaki bahar din dan kuwa shima zai cutu idan ya aureta ya wuce wannan ajin dan haka bazata bari yana rabin jikinta ba ya kwashi sauran wani duk da tana shakkar idan ma NUAB din ya amsa auren bare cikesa da kusantar Bahar da batada dogon banbanci da bayin masarautar a gurinta.

******A daren da washe gari Bahar zasu tafi a daren NUAB ya isa bangaren Ammin da kansa dan isar mata da sakon tafiyar da zaayi din hadda ita,

Tinda fadawansa suka fara isowa kofar bangaren tareda securities suka jeru a natse suna bawa bangaren kariya take bayin bangaren suka fito gabaki dayansu suna rabewa gefe sosai inda bama zai gansu ba dan sai bayi ma masu mahimmanci suke iya ganin Sultan me mulki a masaurautar duk da bayin bangaren Ammin kaf suna yawan ganinsa su kam sbd girman darajar Amminsa da kusan tafi ta kowace macen cikin boyem a yanzu kafin sultan din yayi auren da duniya zatasan matarsa a matsayin matar Sultan LEUL NUAB duniya da yan media su shedar da hakan.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee

107
Tin kafin shigowansa palon Maa tenya ta isar da sakon isowansa wanda itama kafin isar da nata sakon qamshinsa ne yafara ratso palon ya shigesu musamman Bahar da leylah wainda suke kusan saiti da kofar dan haka Leylah ce ta fara dago kanta ta juya a hankali ta zubawa kofar idanuwanta cikeda wani irin shauqi da tsananin natuwa da mutuwa a sonsa tana jiran shigowansa ta kallesa dan jin maitarta tana fadawa da samun sassauci,

Bahar kuwa qin nuna tama ji qamshinsa tayi bare nuna ta fahimci waye ne akace ya iso bangaren bare juyawa ta kalli kofar cigaba da duba laptop din datake gabanta tayi wadda Shuraim yake nuna mata da koya mata abuwa da kuma yanda zatai amfani da ita dakyau.

Shi kansa Shuraim ita ya zubawa idanuwansa batareda ko kyaftawa ba cikeda wani irin sanyi da kauna tareda soyayya me tsafta ba hayaniya da kamewa tareda aji yana jira da kokarin karantar yanayinta akan shigowa da zuwan NUAB din wadda dukansu sun manta yaushe suka samu ganinsa last.

Amminsa dake gurin zaune tsakiyar masoyanta Bahar na gefenta itada shuraim ita muma leylah tana gefen zuhra wadda take dayan bangaren ayanah din.

Maa sakinah tana dakin Bahar tana qarasa hada mata duk abinda zata buqata marasa yawa sbd acan ma zaa siya mata komai dan haka ba buqatar ta kwashi kaya da yawa su tafi dasu.

Sako kansa ya saka niimar gurin qarasa sauyawa a natse da qamshinsa daya kashe jikin leylah gabaki daya hakama iyayensa kamshinsa yana ratsatsu duk da ita zuhrah sai a yanzu ne take saninsa da abubuwan da suka shafesa.

Idanuwansa akan Amminsa kadai suka sauka ya qaraso har inda suke din wanda ya saka shuraim daya mace a gurin yiwa Bahar wata natsatsiyar kallo miqewa cikeda basa girmamawa hakama leylah miqewan tayi suka gaidasa cikeda girmamawa,

Amsawa yayi a taqaice batareda yayiwa kowannensu cikakken kallo ba sbd kallo baya cikin dabiarsa,

Gaida Zuhrah yayi ta amsa cikeda kauna da kulawa me yawa tana sake fuskarta dukda itama tana girmamasa sosai sbd matsayinsa na me mulkin qasa gaba daya.

Amminsa ya tsayar da idanuwansa akanta cikeda kaunar da babu sirki ya gaidata ta amsa tana miqewa zuwa palon da suka saba zaunawa suyi magana suyi fira,

Suna barin palon Bahar dake zaune duka abinda takeyi ta kasa cigaba sbd jin tayi ta dena ganewa miqewa tayi a natse ta silale tabar palon tana nufar bedroom dinta ta shige tareda rufo kofar tana kokarin basarwa da ci gaba da harkar gabanta.

Maa sakinah dake dakin ta kammala komai tana kokarin hada mata undies a wata yar qaramar suitcase dake cikin set na akwatin da zata tafi dasu din ajiyewa tayi tana kallanta tace

'Har kun gama karatun ne??

Gyada kai kawai tayi tana zaunawa bakin kujeran da Maa take hada kayan tace

'Maa ki ajiye hakan ki bari zan qarasa hadawa'

'Kinsan dame dame zaki hada ne to??

Murmushi tayi me kyau tana dasuke kafafunta daga qasa zuwa kan kujera ta lankwasasu tana gyara zamanta dakyau tace

'Eh mana ba iya wainndan ne kadai suka rage ba?

Murmushi Maa tayi tana dan zaunawa itama gefen Bahar din tana biyewa zancenta datake son yi batareda saniba kawai so take tayi ta fira sbd mantar da kanta komawa palon koma fita dakin gabaki daya dan daman koba komai idan ba tareda Ammi ba bata jin dadin sakewa da zama a cikinsu Shuraim da leylah duk da Mum zuhrah ma bata sake da ita ba da kauna me karfi kaman Ammin sbd tana ganin su leylah yayanta ne bazata iya zaqewa ta nuna musu fin kauna akan mahaifiyarsu ba musamman leylah da akan komai kishi da tsanarta takeyi dan hakanne take dan riqewa da taqaita kaunarta akan Mahaifiyarsu.

Acan palon Ammi kuwa lokacinda LEUL ya zauna facin Ammin yayi cikeda kaunar dayake jin tamkar tayi masa nisa a tsakaninsu yanxu sbd a yanzu tana tareda 'yar uwarta da yayan yar uwarta da uwa uba 'yar abaas data ke jinginar da nasa matsayin akan Bahar din kwata kwata tareda manta shi waye a gurin Bahar din batareda tambayar raayinsa ko jiran umarninsa akan komaiba sedai ta sanar dashi kawai ga abinda ta yanke wanda ya tabbata ya sani dorata Sultan yakeyi akan wasu tinanin da abubuwan dan haka shima sam hankalinsa yafi kwanciya ya nesanta Amminsa tasa da Sultan tin kafin ya gurbata masa tinaninta itama zata tafin bazata rasa ilimin koya ba acan ta samu nutsuwan da bata samu ba a shekarun baya,
Taje ta shaqi iska da numfashin 'yanci da tsara kowace rayuwar zata zaba acan.

Ajiyan zuciya me sauti Ammin ta sauke tareda motsawa ta dawo kusa dashi ta zauna gap dashi tareda miqa hannunta duka biyu ta kama fararen hannuwansa masu karfi da lafiyar fata a cikin nata ta sake sauke ajiyan zuciya tana kallan fuskarsa daya dago idanuwansa da ita kanta wani kwarjini me karfin gaske suke mata kawai dai bata sauke masa nata idanuwan ne sbd tana mahaifiyarsa kuma har yanzu babynta dake bacci a jikinta yana yaro take kallansa dan haka zuba masa ido tayi zata bude baki tayi magana ya kalleta da kyau ya dakatar da ita ta hanyar fada mata

59 / 100