rashin karfi ya zayyanewa NUAB labarinsu tas Wanda baida dadin ji me tarin qunci da baqin ciki.
Nasa labarin yake kokarin Dora masa Maa Sakinah ta shiga kafafunta na Takawa ahankali cikin sanyi da rawar zuciyar dake gap da bugawa.
Suna kallan juna Abaas ya fashe da Wani irin kukan daya saka dakin yin tsit gashin jikinsu na tashi.
Itama Maa sakinah zubewa tayi qasa tana fasa kuka a gabansa koina jikinta na rawa tana kiran sunansa da sauti me ratsa jiki.
Bude baki yakeson yi ya Ambaci sunata da tambayar yan uwansa amma karfinsa yayi qasa sosai dan haka ta rarrafo da sauri tana bude bakinta dayake rawa cikin sautin daya sake saka gurin daukan tsit ta fara fada masa dukkanin halinda suka shiga har zuwa halinda ake ciki yanzu da Ayanah dake tsananin so da buqatarsa a rayuwarta.
Magana zeyi harshensa ya fara kokarin karyewa dan haka take aleey yace securities su daukesa Ayi gaggawar tafiya dashi.
Riqe hannun sakinah Abaas din yayi da karfin dayake na barin duniya yana kallanta daqyar ya iya furta ‘yata jinina AYANAH BAHAR….
Kasa qarasawa yayi jikinsa na sakewa gabaki daya.
Gaggawar fita dashi suke kokarin yi sbd har lokacin akwai Sauran rai a jikinsa
Sarkin gida na ganin hakan buga tsalle ya tare kofa tareda kiran fadawa yana cewa kada a Bari su fita koina da Shiguba da yarsa har sai ancika burinsa na auren yarsa Wanda hakan zai basu tabbacin kariyarta Bayan tabar nan sbd igiyoyin auren sa zasu tabbatar musu da zaa iya riqe amanarta matsayinta na ‘yar shugabansu hakama basuda tabbacin Ayanah din da gaske tana raye amma tinda ga ‘danta a gabansu bazaa tafi dasu ba saiya aureta koda Abaas ya rasu kafin akai to ta samu gatan zama Inuwar aure.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
63
Da Wani irin yanayi me ‘dacin gaske da jajayen ido NUAB da aleey suka dago dukkaninsu suka kalli Sarkin fadar Wanda ya sake tsayawa Akan maganarsa ba tsoro sbd wannan shine gatan da adalcin da zasu wa ‘yar shigabansu jinin GHAZ data rage a duniya a idanuwansu,
Su dai bazasu bi su ba hakama bazasu Hana a tafi da Sugabansu ba dan nema masa lafiya sbd yana tsananin buqatarta amma kuma basuda tabbacin zai rayu ko bazai rayu ba a yanda sukaga jikin nasa yayi nisa dan haka gwara ‘dan Ayanah kaman yanda ya fada ya auri Bahar ‘Dinsu a gaban idonsu ta yanda koda Allah bai tashi kafafun Abaas ba sunsan zaman aure zatayi a cikinsu ba zaman garari ba dan haka tsoro ya cire a zuciyarsa matiqar ba auren BAHAR zasuyiba gwara abar musu shigabansu ya cika a gabansu su dauki amanar yarsa wannan shine tsayuwarsu matiqar ba hakan ba kuma sedai a kashe su a tafi da Abaas da BAHAR Bayan ransu.
Kuka Sosai Maa sakinah takeyi tana Jin zuciyarta kaman zata fashe sbd idan Abaas yabar duniya Zuhrah ce kadai ta ragewa Ayanah wadda tafi tsananin kauna da son Abaas a rayuwarta fiyeda komai,
Tayaya Ayanah zata iya jure wannan rashin?
Sake qanqame hannun Abaas din sakinah tayi dake cikin hannunta tana rintse ido da sabon kuka me tsananin rasa zuciya.
Aleey da ransa ya gama baci gashi ba lokaci da gaggawar gaske suke son tafiya da Wanda shine rayuwar Ammmi,
Kallan Securities yayi da idanuwansa jajir yace su kawar da kowa har sai sun fice dashi.
Sarkin fada na Jin hakan ya sake tare hanyar tareda fidda wata irin mahaukaciyar wuqa a jikinsa me munin da zata zata aikaka lahira ba bata lokaci.
Wuqar sa ba komai bace a gurinsu sbd sunada wainda sukaci uwarta da ubanta a jikinsu Wanda zata katse jijiya take kafin kyaftawar ido kawai banbanci tasa dafin gaske ne a cikinta da shine zai kasheka bama kaifinta ba kila.
Bindiga suka daga cikeda rashin tausayi suka seta Sarkin fadar tareda Yaransa da suka taho suka zagaye kofar dakin da makamai masu hadari a hannunsa.
NUAB da jikinsa ke wata irin fizga sbd tsananin tsoron rasa Abaas Wanda shi kansa bayajin zai iya Hadiye radadin rashin sa sbd tsananin kaunar da son dayake masa tin kafin ya gansa sbd shine mutum daya da Amminsa tafi so a duniyarta da rayuwarta fiyeda kowa,
Ko shi kansa data Haifa baya iya gane tsakanin shi da Abaas wane tafi tsananin so dan haka da kaunar Abaas shima ya tashi a ransa hakama da ita zai mutu dan haka bazai taba iya barin ya mutu sakamakon rashin likita ba indai ba Allah ya Riga yayi anan zai cika din ba lokacinsa yayi kenan ba dan haka dagowa yayi da jajayen idanuwansa da sukai mummunan ja kamar ma hadda hawaye a cikinsu ya kalli Sarkin fada Wanda yaja baya kadan sbd tsananin kwarjini da shakkar NUAB din data dakesa zuciya da kafafu amma duk da hakan bayajin zai iya ja da baya Akan abinda ya fada sedai Ayau ya rasa ransa gurin tabbatarda gyara goben BAHAR.
Bude baki NUAB yayi da wata muryan data saka tsigar jikin Sarkin fada tashi gabaki daya yana sake Jin shakkar NUAB na shigarsa yace
‘Ku Bari na ceta rayuwarsa nayi muku alkawarin bawa rayuwarsa data ‘yarsa kariyar da matiqar ina raye sun wuce kowane matsayin da zasu fuskanci kunci ko rashin gata tako ina……..
Girgiza Kai Sarkin gida yayi yana kasa kallan NUAB din Wanda hatta fuskarsa tayi jajir jikinsa rawa yakeyi.
Aleey da zufa ke gangarowa umarni me Zafi ya bada Wanda ya saka aka taqa bindigogin zaa fasa kan Sarkin gida NUAB ya daga hannu daidai nan Maa Sakinta ta zube qasa itama tana fasa sabon kukan daya saka kowa juyowa ya kalleta ahankali da jajayen idanuwa Banda NUAB daya rintse ido hannuwansa dake dauke da Abaas suna wata irin rawar dake bayyanarda halinda zuciyarsa take ciki.
Cikin tsananin kukan data jima batai irinsa ba sakinah ta bude baki tareda dagowa ta kalli NUAB tace
‘NUAB Ka aureta kodan cika alkawarin daka daukanwa mahaifiyarka zaka kawo mata Abaas,
Ka aureta sbd cetan rayuwar Abaas da zuciyoyi da dama bazasu iya jurewaba idan aka rasashi,
Alkwari ne da aka dauka anan cikin masarautar GHAZ tin kafin sanin yaya kaddarar zata taho ba a tsakanin mahaifiyarka da Abaas Wanda idan Ka cikasa Ayau anan inda aka dauki alkawarin zaka cike musu burinsu ne da shi kadai ya rage a tsakaninsu sbd ko baka kaiwa Ayanaah Abaas ba Ka Kai mata auren ‘yarsa dake hannunka Ka cike mata gurbin da Abaas zai bar mata sbd ‘yar Abaas tamkar Abaas dinne a gurinta…..
Tsit gurin yayi kowa na shiga sabon mummunan yanayi Banda NUAB da already yake cikinsa idanuwansa a rufe danan.
Kallansa su aleey sukai dukkaninsu cikin shock da tashin hankali da firgici sbd babu kowane irin tarihin shigowan nace rayuwar LEUL daya tsara,
Bai taba son kowace mace ba sbd baima taba sakasu a tsarin rayuwarsa ba,Amminsa ita kadaice wadda yayi Alkwarin ta ishesa rayuwarsa,
Mata uku ne a rayuwarsa kuma su kadai ne wainda zaiyi rayuwa dasu baya buqatan kowace irin mace Bayan ukun nan iyayensa dan haka aleey yasan babu ta yanda zaayi mace ta shigo rayuwar LEUL dan haka dagowa yayi ya dawo da kallansa kan Sarkin fada Wanda jikinsa ya mace da maganganun sakinah da shima sune yake tsaye akansa.
‘A daura mun auren da ita ni zan aureta indai hakan ne kadai zai saka ku Bari mu tafi dashi da ita din……..
Kallansa Sarkin fada yayi da sauri cikin tsananin mamaki da fargaba kafin ya maida kallansa kan sakinah wadda ta fasa sabon kuka tukuna ya maida kallansa kan NUAB Wanda ya bude idanuwansa a hankali ya Dora Akan Sarkin fada din batareda ya kalli kowa ba ya saka hannunsa cikin aljihun wandon kakin dake jikinsa na shigowa daji ya ciro Wani kakkauran awarwaron zinari daya me kaurin gaske dayake dauke da sunan mahaifiyarsa da Abaas din Wanda yake nata ne shine ya bata kyautarsa da hannunsa ya qera sa ya saka sunanta dana Abaas din a yanzu dazai taho yaje har dakinta ya dauko sa sbd nunawa Abaas shedan shi dan Ayanah ne ya miqawa aleey dayake mutuwar tsaye cikeda rudewa da mamaki Abaas shima ya miqawa securities yana dawowa gurin NUAB Wanda ya saka hannunsa daya ya kamo hannun Sarkin gida ya saka masa zinarin ya bude baki da sauti me Kai tsaye da tarin tsananin son cikar Buri daya wato tafiya da Abaas dan ganin likitocin gaggawa.
‘Sadakina,a daura auren a yanzu anan a wannan daqiqar bana buqatar qarin mintina ko kadan batareda an daura ba.’
Jikin Sarkin fada rawa ya dauka sbd shakka da firgici amma hakanan ya tattaro karfin Hali da jarumta ya juya da sauri yace a kira masa Sauran masu dan matsayi a fadar da gaggawa.
Aleey matsowa yayi zeyi magana sbd sanin NUAB zaiyi auren ne batareda kaunar ko taba shaawar hakan ba dan haka shi a shirye yake da auren koma yaya take yarinyar sbd LEUL kuma zai rayu da ita komai tsananin yanda lamarin zai kasance dan haka bude baki yayi zaiyi magana,
Daga masa hannu NUAB yayi a natse cikin yanayinsa da baya son magana ko daya sbd koina fuskarsa yayi jajir hadda hannuwansa ma duka sunyi jajir.
Sauran securities ficewa sukai da Abaas cikin gaggawa zuwa jirginsu na bakin ruwa da akwai Dr a cikinsa dan fara basa taimakon gaggawa kafin a gama daura auren.
Sakinah barin gurin tayi ta fito kafafunta da tsananin nauyi ta nufi dakin Ayanaah na baya wainda a yanxu yake na BAHAR din kaman yanda aka fada tana kallan koina a hankali zuciyarta na yanka kuka mara sauti na taho mata hawaye na gudu suna tsiyaya a fuskarta kowane memory na rayuwar da sukai a kowane lungu da sako na gidan suna dawo mata.
Inda daidai Baa ya shimfide gawar Ammah a lokacinda sukai ido biyu da gawar tata idanuwanta suka sauka ta rintse idanuwanta tana dafe kirjinta dake Wani irin ciwo hawayenta na tsananta gudu.
Fara zagayawa dakunan kowa da aka Bari tana fashewa da sabon kukan baqin ciki me tsanani da kewan rayuwar da suka bari anan wadda koda basuyi arzikin da suke dashi a BOYEM ba ko kadan nan din yafi musu farin ciki da nutsuwa tareda kwanciyar hankali.
Koina ya mutu ta zama tamkar kango babu komai da aka sauya,babu komai da aka gyara tin asalin yanda gini d tsarin gidan haka yake haryanzu babu cigaba ako ina dan haka koina a mace yake iya inda suke rayuwa a cikin masarautar yake gyare.
A kofar bakin dakin Ayanah ta tsaya cak Wanda yake fes a gyare koina asalin qamshin jinin sarautar GHAZ na tashi yana fitowa daga dakin na flowern Ahlighazania Wanda gabaki daya ahalin shine qamshin da suke amfani dashi tin farko dan haka suka kasance kamshinsu daya me shiga rai da sanyi tareda wata irin nutsuwan kwanciyan hankali da kashe jiki.
Lumshe idanuwa sakinah tayi tana Jin bugun zuciyarta na tsananta da Wani irin mutuwan jiki da baqin tareda quncin rashin kasancewan su a rayuwa daya koda duka suka Haifa iyalansu,
Idan har mahaifiyar BAHAR bata raye yaya Abaas yayi dawainiyar kulawa da tarbiyantar da ita shi kadai babu dan uwansa ko daya a tattare da ita?
Idan yanzu Allah ya kaddara ciwonsa bana tashi bane yaya zasu fuskanci BAHAR dik a matsayin dangin mahaifinta daya rasa shekaru?
Yaya zata iya rayuwa a cikinsu batareda tasansu ba ko sabo dasu?
Tayaya ma zata iya rayuwan nan babu uwa babu ubanta da shine gatanta,
Zata dandana ‘daci da quncin da iyayenta suka dandana na rashin iyaye da tafiya Wani guri rayuwan da batama san yaya zatayi ba,
Shi kansa auren da ake daura mata a yanzu basusan a mizanin wace kaddara zai hau ba sbd abu ne da babusa a tarihin GHAZ kuma bazai taba zamaba ga asalin jinin Wanda yake kan mulki kuma Wanda yake magaji bazai taba auren wadda ba jinin BOYEM ba haramun ne ma ga jinin da mahaifinsa ya mulki BOYEM kuma shima Ana sakaran ya mulki BOYEM auren wadda ba jinin BOYEM ba.
Tayaya zasu fuskanci wannan auren da zaa kulla yanzu a masarautar da Kai tsaye mutuwarsu ce hukuncin wannan auren da akai indai ya isa gaban sultan da Masarautar BOYEM.
Bude idanuwanta tayi ahankali jajir dasu sun kumbura ta miqa hannunta a hankali kofar dakin ta tura a natse bakinta na budewa da disashiyar murya tai sallama tana saka Kai daidai nan kunnuwanta suka jiyo mata sautin FATIHAR da aka shafa ta DAURA AUREN NUAB ALMAZZ BOYEM DA AYANAH BAHAR ABAAS GHAZ Wanda ya ratsa kunnuwan duk Wanda yake cikin masarautar GHAZ din Banda BAHAR wadda bacci takeyi a kishingide idanuwanta a rufe sbd kanta dayake tsananin ciwon damuwan dake zagaye da rayuwarta Akan ciwon BAA dinta Wanda shine gatanta,rayuwarta,hasken idaniya da rayuwarta.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali*_HAYATEEM_*
Mamuhgee
64
Rufe baki da hannuwa Maa sakinah tayi a lokacinda ta tabbatarda auren ya dauru Wanda hadarine zalla a cikinsa da zai iya raba mutane da yawa da rayuwarsu sbd sun aikatawa masarautar BOYEM gagarumin haram din da zai tono sirri Ka da dama amma koma menene ita saina shirye take da bawa Auren kariya da lafiyarta da rayuwarta har karshen rayuwarta da ba lallai tanada yawa a nan gaba ba.
BAHAR da motsi ya sakata bude manyan fararen idanuwanta da suke sak na mahaifiyarta asalin balarabiyar SHEMALI masu daukan hankali da saka baki da jikinka mutuwa sbd Wani irin sirrin kwarjini da nitsatsen kyau dayake cikinsu,
Akan sakinah dake kofar dakin tana shigowa ta sauke idanuwan a natse tana qarasa budesu gabaki daya akanta tareda tashi Zaune cikin nutsuwa da jinin mulkin GHAZ dake yawo yawo a jikinta batareda ta bude baki ba tayi magana sbd koma wanene shine yakeda damar bude baki ya sanar da ita shi waye meya kawosa dakinta dan haka kafafunta ta ziro a hankali cikin nutsuwa ta saka a cikin Takarmin dayake bakin gadonta tana kafe idanuwanta Akan sakinah dake qarasa shigowa tana bayyana fa hasken dakin na wutar gargajiya dake dakin take ta bayyana a idanuwan BAHAR din wadda Kai tsaye kukane idanuwanta suka fara cin karo dashi matar na yi Wanda ya saka bugun zuciyarta tsayawa cak sbd babu abinda Yazo ranta sai mahaifinta dan haka ahankali cikin wani irin slow ta maida kallanta kan kofar shigowa dakinta tana miqewa tsaye ta nufi kofa mayafin dake rufe da lafiyayyan dogon gashinta na zamewa bata tsaya ba ta rabe Maa sakina jikinta na wata irin rawa ta fice da gudu tana nufar dakinsa idanuwanta na tara ruwan mummunan tashin hankali da tsoron dayake jijjiga rayuwarta dan kuwa bazata iya rayuwar da babu Baa dinta a ciki ba,mutuwa zatayi idan ta rasashi a rayuwarta sbd shine ginshikin rayuwarta da duka rayuwarta take tangale da soyayyarsa.
Saka Kai tayi a dakin tana jefa idonta Akan gadonsa dayake kwance taga babu kowa akai,
Wani irin sarawa kanta yayi ta juyo da gudu dukkanin jikinta na wata irin rawar data saka kafafunta suka yanke zata fadi sakinah data biyota da sauri tana hawaye tayi saurin tareta jikinta tana kokarin rungumeta amma ta kasa tsayawa ta nufi fada da gudu idanuwanta basa gani sbd tsananin fita hayyacin data fara ta bude baki da Wani irin sautin daya ratsa kunnuwan duk Wanda yake masarautar cikin wani irin tada tsigar jiki tace
‘Baaa’
Tana saka Kai cikin fadar Kai tsaye da wannan sautin daidai nasu sautin ya shiga kunnuwanta na Sarkin fada dayake cewa
‘Auren NUAB ALMAZZ ya dauru da AYANAH BAHAR GHAZ Wanda muna fatar mutuwa ce kadai zata rabaaaa’
Kamar saukar gudu ma a tsakiyar kanta taji saukar zancen Wanda ya saka idanuwanta qarasa rasa ganinsu ta kafesu Akan Sarkin fada tana bude baki kanta na mantawa da komai Bayan son ganin mahaifinta da sautin daya saka Aleey dagowa a cikin wani irin yanayi me sanyin jikin auren da aka daura amma ya kasa kallanta sbd a yanzu da igiyoyin auren ubangidansa suka riga suka hau kanta idanuwansu bazasu iya mata kallan Kai tsaye batareda girmamawa ba koda kuwa aure ne da a yanzu baida suna bare matsayi kwata kwata a rayuwar me BOYEM din dan kuwa bai dauka auren ne shima yayi ba abu daya ya sani koma menene yayi sa ne dan tabbatarda karban Abaas Wanda yake rayuwar Amminsa.
‘Yet niw Abaa,yet niw Esu?’ Ta fada idanuwanta na kafe Akan Sarkin fada Wanda ya sauke Numfashi me tsananin sanyi da mutuwar jikin rabuwar da zeyi dasu a lokaci daya babu shiru babu sani ba tareda tinanin hakan ba dan ya dauka shine zai shafe Abaas da kansa ya kuma zama uban BAHAR din wadda zai aurar da ita ga nasa dan amma ko a hakan baiyi baqin ciki ba sbd shi kansa zaifi farin ciki idan Abaas yaje amma idan har hakan shine zai hada Abaas da Ayanaah to wannan shine gatan karshe da zai masa shi da Bahar wadda batasan kowaba a dangin uwa da ubanta ba.
Tasowa yayi ya iso gaban Bahar din zai furta sunanta ta ja da baya cikin wani irin mutuwar jiki da mafi girman tashin hankalin rayuwarta tana girgiza Kai ta sake furta sunan Abaa dinta idanuwanta na yin wani irin ja hawaye masu tsananin zafi na taruwa a cikinsu sbd kadaici ze kasheta idan Abaa yabarta shine kadai ran dayake cikin empty rayuwarta da babu kowa a ciki sai zallan sunayen da babusu maana yan uwan mahaifin nata da iya sunansu ne basu ba a rayuwarta.
NUAB da idanuwansa suke rintse tin lokacinda aka shafa fatihar auren dago kansa yayi ahankali yana bude idanuwansa da sukai jajir ya saukesu Akan fararen kafafun dasuke gabansa masu haske sosai na daukan hankali sarkar Farin azurfan dayake kafar duk motsinta daya na ja da Bayan datake Wani sauti me yar qarar dake shiga kunnuwansa yake fitarwa Wanda ya sakasa dauke jajayen idanuwansa zuciyarsa na Wani irin Zafin lokacin daya bata na cetan Abaas a gurin daurin auren da bai dauru ba a zuciya da rayuwarsa dan kuwa aure ne kadai na biyan buqatar wannan lokacin da suke so na tafiya da Abaas dan haka miqewa yayi batareda ya juyo ya kallo kowaba ya nufi kofa a takunsa na natsuwa da jinin mulkin daya dame sarautar GHAZ ya fice batareda ya cewa kowa komaiba.
Yana ficewa Aleey ya miqe shima yabi bayansa Bayan ya dan kalli Maa sakinah dake Bayan BAHAR da Sarkin fada yace suna jiransu a waje.
NUAB na