cup din dayake kaiwa a bakinsa matiqar yana zaune idan ba Aleey ko keelah ba sai kuma iyayensa uku dinnan mata sai kuma matarsa da zata karbi ragamar hakan a gaba.
Fara breakfast din sukai a tare cikin nutsuwa,
Bai wani ci sosai ba sbd har yanxu cikinsa bai gama dawowa nasa ba dan haka tea yasha sosai kafin ya dauki tissue yana goge bakinsa ya dago kyawawan idanuwansa masu haske ya kalli Aleey yace
'Ka bincika su waye likitocin da Sultan ya mayar doctors na ghaz kwata kwata,
Iya na cikin masarautar ghaz din nake nufi bana asibitin da aka gina a garinba,
Idan ka ganeso ka nema contact nasu kayi magana dasu inason sanin meya samu ghaz princess'
Dagowa aleey yayi yana tabbatarda angama.
Fitowa Yayi dukkanin tsaro da fadawansa suna bayansa ya nufi bangaren sultan ya dubasa cikin kauna da kulawa.
Sultan din yana zaune akan wheelchair cikin dan shirin da Kadir yayi masa.
NUAB da kansa ya basa magani bayan yasha tea kadan.
Basu guri kadir yayi sukai magana wadda akan bayar da mulkin da NUAB yaso yi ne ga Asim Sultan ya yanke maganar kwata kwata tareda bayyanarda qin amincewansa a bisa hujja me karfin cewan Asim bazai iyaba yanada rauni ke yawa musamman yanxu daya rasa mahaifiyarsa bazai taba zama mai zarrar da zai iya mulkan karagar mulkin boyem datake da karfin gaske a duniya.
NUAB a rayuwansa baida raayin dawwama a cikin mulkin amma idan har iyayensa zasu zauna dashi a boyem suyi rayuwa zai rungumi kaddarar da Allah ya haifosa a cikinta a karo na biyu,
Zai rungumi kaddarar data saka Allah ya tarwatsa zuriar mahaifiyarsa da jarabawa me karfin data kawo ta boyem ta haifesa sbd kawai Allah yayi zai zamo a cikin tarin jerin sunayen da suka mulki boyem a tarihin duniya.
Numfashi ya sauke tareda kallan mahaifinsa yana gyada masa kai cikeda kauna da kulawa.
Shima sultan din wani farin ciki da nutsuwa yaji ta shigesa a wannan karan 'dansa LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM ya yadda da mulkar boyem akan raayinsa ba akan kowane irin sharadi ko tirsasawaba.
Fitowa sukai NUAB din ke tura kujeran Sultan din da tarin securities masu yawa da fadawa masu yawa dake biye dasu zuwa bangaren Asim a karo na farko da dukansu suka taba zuwa.
Ko da suka isa an riga an iso an sanar dashi zuwan mahaifinsa da dan uwansa Sultan me boyem dan haka yana xaune babban palonsa na farko shikadai sai matarsa dake tsaye akansa tin jiyan tana hana zuciyarsa shiga mummunan duhu.
Gabaki daya tsaron dake biye dasu a wajen bangaren suka tsaya daga NUAB sai sultan da kadir da aleey da keelah ne suka shiga ciki.
A palon suka zauna cikin nutsuwa mulki da izza na dukan juna da zallan nutsuwa da kamewa tareda bayyananniya kulawa da bayyanarda alhini.
Kallansa sukai a lokaci daya kaman yanda ya dago cikin nutsuwa da kamewa shima ya kallesu sbd tin jiyan Allah ya taimakesa yau ya tashi da karfin zuciya da tawakkali da nutsuwa tareda barwa Allah yana mata fatan saduwa da rahamar ubangiji.
Cikin kulawa sukai masa gaisuwan rasuwan gabaki dayansu hadda su aleey cikin girmamawa da mata fatan saduwa da rahamar Allah ya kuma yafe kurakurenta.
Amsawa yayi a natse yana miqa godiyansa ga Sultan NUAB da mahaifin nasu bayan shima yai masa gaisuwanta sbd shima matarsa ce ai.
Suna gama gaisuwan suka bar bangaren suka isa babban fadar masarautar da tarin dubban jamaa ke cike suna jiran fitowan Sultan NUAB ayi masa gaisuwan rasuwa sbd baa dauka sultan yasar zai iya fitowaba.
Tareda Asim suke wanda NUAB ya fara bayyanarda gaisuwansa garesa cikin girmamawa da mutuntawa tareda tausawa dan nunawa duniya matsayinsa da girmansa da dole a basa,
Hakan kuwa ya saka aka bayyanarda girmamawa da mutuntawa aka ringa masa gaisuwan mahaifiyarsa tareda adduoi masu kyau.
Anan zuka wuni ana gaisuwan ga sultan yasar da Asim harma da NUAB.
Sai yamma lis gap da magrib aka watse aka maida sultan bangarensa shima NUAB bangarensa ya nufa.
Ana magrib motocin da suka dauko su Ammi daga Airport suka iso masarautar suka fito batareda NUAB ma yasan da isowansuba sbd yana masallaci tareda mutane.
Bangarensu suka nufa wanda tin kafin su iso bayi sun isa sun gyarasa tsaf leylah ta sakasu.
Zuhrah ma anan bangaren tayi xamanta dan haka kowannesu daki ya shige
Wanka da alwala sukai suka fito sukai salloli suna idarwa tini aka cike dining da abinci masu lafiya da yawa.
Tenya ce ta sakasu cin abincin dole cikin nutsuwa kafin suna gamawa anyi sallar ishai sukai sallah.
Sai a lokacin ne NUAB yasan da isowansu a wayar Ammin data kirasa dan haka ya kira kadir ya sanar dashi isowan Ammin.
Kadir take ya saka akaiwa bangaren sultan sabon gyaran da duk yake buqata koina ya dauki tsit kowa yabar bangaren fadawan dake tsaron kofar gurin kadai aka bari shima ficewa yayi daga bangaren ya tafiyarsa dan bawa Ayanaah ghaz daman zuwa duba maigidanta wanda daga shi har itan a cikin tsantsan matsuwa da ganin junansu suke sbd zuciyarta kaman zata dena bugawa haka takejinta shikuma ganinta kadai ne abinda yake ganin yana buqata a yanxu sbd zuciyarsa ta samu karfin halin data rasa.
Bangaren Haile dukkaninsu suka dunguma suka tafi dan miqa gaisuwansu akan rasuwanta da babu wanda bata girgiza ba a tsakaninsu.
Cikin tausayawa da nuna kulawa sukai gaisuwa a gaban mahaifiyarta dake zaune ta tsufa sosai Su Aslam dukansu suna zaune tareda ita.
Dukkaninsu zubawa Ayanah ghaz idanuwansu sukai suna kalla cikeda sanyin jiki sbd daga karshe ubangiji ya nuna musu bazasu iya cutatar da wanda shine da kansa yake bata kariya ba sbd batada haqqin kowannensu kaman yanda kakarsu ta fada musu.
Amsawa gaisuwan sukai babu wanda jikinsa baa mace ba dan haka sukai shiru dukkaninsu.
A lokacin ne Asim ya shigo tareda leylah sbd kiransu da akai akan ayanah zasu musu gaisuwan.
Zaunawa yayi a natse yana dan sauke kansa agaban sirikan nasa duk da iyaye suke a gurinsa tinda basu fara da yar jin nauyiba akwai sakewa a tsakani.
Gaisuwa cikin tsananin kulawa su Ammin sikai masa dukansu ya amsa yana miqa godia.
Sun dauki lokaci a bangaren dan nuna kulawansu kafin suka fito.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
175
Karfe goma da mintina kadan Ammin ta isa bangaren sultan cikin nutsuwa da sanyin jiki,
A lokacin data shiga koina tsit ba haske sanyin ac da qamshin NUAB ne daya dan kama bangaren sbd yanda yake wuni da zama acikinsa na kwanakin ke tashi.
Kai tsaye kofar bedroom dinsa ta nufa kowane takunta bugun zuciyarta qaruwa yakeyi yana saka mata tinani kala kala da halinda zata gansa.
Hannu ta saka ta kama handle din kofar dakin ta bude tareda saka kafarta ta dama tana takawa sautin sarkan kafarta da bata taba cirewa ba yana bada sautin daya sakasa dagowa ya sauke mata idanuwansa yana zubawa takunta su kowane taku na dawo masa da ranar farko data fara sako kafarta a cikin wannan dakin nasa tirakarsa dan zamowa cikakkiyar mallakinsa wanda sautin sarqar kafarta ne ya fara sakasa dagowa ya kalleta ko a ranar farkon.
Ita kanta kallan dayake mata ne ya sakata dakatawa kadan tana tsayuwa a inda take tsayen kaman yanda ranar farkon hakan ta faru bama tareda tasan tayi hakan ba.
Daga kan takunta daya tsaya ya dauke idanuwansa yana dawowa dasu akan fuskanta cikeda nutsuwa da kewa da wata irin kauna me tsafta da karfi ya kalli fuskanta dukkanin jikinsa na mutuwa.
Takowa taci gaba dayi ta iso har inda yake zaune tsakiyar gadonsa yana kallanta ta zauna a cikin nutsuwa tareda kallansa tana bayyanarda dukkanin kulawa da tausayi da alhininta ta fara yi masa gaisuwan rashin haile kafin ta tambayi jikinsa tana dora hannunta daya akan nasa daya bude mata alaman ta saka nata akai.
Hade tafin hannunsu yayi a cikin nutsuwa yana sarqe yatsun hannunsu ya sauke ajiyan zuciya me zafi da radadin abubuwa da dama ciki hadda na rashin uwar yayansa matarsa ta farko.
Amsata yayi batareda doguwan hayaniya ko motsiba daganan sukai shiru kafin ya sake tambayansa yanayin yanda yake ji a yanzu yana bata amsa tana dubasa a natse damuwanta na bayyanuwa.
Ganin halin datake neman shiga na damuwa me yawa na gani wheelchair a dakin ya sakasa janta jikinsa ahakali ya rumgume batareda yace komaiba sbd shirun yake buqata a yanzu.
Lafewa tayi itama tana dauke numfashi dan basa nutsuwa da shirun dayake buqatan.
Haka sukai shiru babu motsi ko kalman komai a hakan suka kwana.
Washe gari bata bar bangarenba saida tai masa komai da kanta ta basa breakfast ta basa magani tana nan dr yazo ya dubasa ya sake mata bayanan komai wanda hankalinta ya kwanta dan haka ta sake basa kulawa sosai dakyau tukuna saida NUAB yaxo anan bangaren suka gaisa a palon Sultan din itace ta turosa a kujeransa har palon suka gaisa da NUAB daga nan ta fice ta basu guri suna magana akan likitocin da aka gayyato daga wata qasar dan dubasa amma an riga an musu komai na anjom zasu samesa gashi kuma Ammin ta baro anjom tazo dan haka dole dai komawan zaayi acan anjom ayi jinyar inda babu ko yan dubiya ko kadan ya samu yayi jinyar nutsuwa.
Sai anyi sati daya da rasuwan haile kowa ya watse tumuna sultan din zai tafi dan haka kulawa dashi kwata kwata ya dawo hannun Ammin wadda a yanxu saita kwana ta wuni batama baro bangarensa ba sedai kullum tana zuwa ta gaida mahaifiyar haile ta sake musu gaisuwa musamman Asim da suke nuna masa wata irin kauna da kulawa sosai dan kuwa ko abincin da zaici daga bangaren Ammin tenya takeyi da kanta tana aika masa acan bangaren wani lokacin ma anan bangaren yake cin abinci da Leylah sun taru sun tsayu akansa sbd kada ya shiga damuwa yana samun kulawan dama bai samu ba a baya rayuwansa dan kuwa kai tsaye kaman NUAB suke jinsa yanzu.
Da daddare Aleey ya gama hada bayanan umarnin LEUL din kuma yayi magana da likitocin amma bai buqaci jin komaiba da kansa sbd yana kiyaye huruminda iya na ubangidansa ne kadai dan haka jin menene yake damun queen din boyem iya gurin me boyem dinne.
Saida suka gama komai Sun iso palon bangaren NUAB din aleey ya kallesa yana daga gefensa cikin girmamaw ya sanar dashi yayi magana da likitocin kuma dukansu suna jiran kiransa kowane lokaci.
Sofa ya nufa yana zaunawa tareda fasa shigewa yana dagowa ya kalli aleey din yace ya kirasu yanzu yaji.
Biyosa aleey yayi yana saka kiran dr Ibrahim wanda shine babba yana dauka ya miqawa NUAB din wayar cikin nutsuwa da girmamawa.
Amsar wayar yayi yana dorawa akan kunnensa take dr Ibrahim ya bude baki ya fara miqo gaisuwansa cikin zallan girmamawa da nutsuwa.
A taqaice NUAB ya amsa yana buqatan bayanin komai a yanda yake na abinda yake damun princess din ghaz.
Shiru dr Ibrahim ya danyi sbd Ammin data ce bata son kowa yasan da cikin da zubewan daya tashi yi amma kuma babu ta yanda zaayi ya kasa amsa tambayar sultan din gabaki daya da kansa dan haka numfashi ya sauke yana farawa da neman afuwan Sultan din akan rashin fadarsu da kuma jajanta masa akan abinda ya kusan faruwan tukuna ya fada masa miscarriage Bahar ta kusan samu amma dai cikin ya tsaya yanxu....
Dagowa da idanuwansa da girmansu da haskensu da wani irin kwarjininsu tareda abinda aleey ya gani cikinsu ya kalli aleey din wanda zuciyarsa ta girgiza da karfi sbd kallan yana bayyanarda dukkanin tashin hankalin da ido zai iya bayyanawa.
Bude baki yayi cikin sauti me dauke da tsantsar nutsuwa data shigesa ta kai tsaye akan abinda kunnuwansa suke ji masa da yama kasa ganewa yacewa Aleey
'Wat does miscarriage mean??
Kallansa aleey yayi shima yana rikicewa da amsar dazai bada sbd bace masa kalman tayi take a cikin kai dan haka ya fara kokarin daga wayarsa yana kokarin budewa yana son tabbatarda abinda ya tina da maanar kalman.
A cikin wayar dr Ibrahim ya sake tattaro nutsuwansa yace
'Ranka ya dade miscarriage na nufin zubewan sabon ciki a jikin mace ko fitarsa'
Dawo da hankalinsa yai duka kaf akan dr Ibrahim din yace
'Cikin ne a jikin Ayanaah BAHAR??
And maganar nan da kake fadamun yanzu cikin ya fita kenan daga jikinta??
Are you like for real ko me?
Qarasa rikicewa Aleey yake neman yi yana fasa bude wayarsa jin abinda LEUL ke fada,
Dr Ibrahim cikin sauri da kokarin qarasa bayaninsa cikin nutsuwa ya sanar dashi cikin bai fita ba allah ya basu ikon tsaidasa dan haka.......
Ko gama sauraron kalamansa NUAB baiyiba ya datse wayar yana jefarwa gefensa tareda rufe idanuwansa da suka sauya a take,
Su Ammi kuwa sun san me sukai na boye masa Bahar na dauke da cikinsa?
Sun san me sukai na hana ya sani?
Da cikin ya fita shikenan ya shiga ya fita bai saniba a matsayinsa na ubansa ko me?
Gashin jikinsa ne suka miqe gabaki daya cikin wani irin yanayin dayake jin jikinsa duka yana zafi kaman wutar zazzabi ta dokesa a take.
A hakan ma suna nufin bazaa sanar dashi ba har sai Bahar din tayi ciwon ta warke,
A hakan ana nufin dai yaushe zaa sanar masa?
Rintse idanuwansa yayi da har sun dan fara masa radadi ya dauki mintina a hakan zuciyarsa na shiga fargaban da bai taba samun kansa a cikinta ba sai a lokacinda yaga sultan a kwance cikin halin mutuwa ko rai a gabansa sai yanzu dayake jin fargaban me yawa tana shigarsa na abinda yaji.
Bude idanuwansa yayi ya kalli Aleey da
Yake tsaye cikin shirin jiran kowane irin umarninsa,
Kallonsa yayi ya dauke kai yana bude baki yace
'Ina buqatan ganinta da kaina tareda likitocin dana yadda dasu akan wannan'
'Aiit Sir' Aleey ya fada kai tsaye yana juyawa yabar palon shima yanajin wani irin karfi da zimmar dole ya hada kan manyan likitocinsu dan zuwa duba cikakkiyar lafiyan Magajin boyem,Moscow da ghaz.
Yana ficewa shima miqewa yayi kai tsaye yana wucewa ciki tareda saka kiran wayarta tana dauka saukan sautin muryanta kadai yaji a kunnuwansa yaji ya qarasa rasa nutsuwansa idan ba isa yayi gareta ba ya duba lafiyanta data jininsa dabai san dashiba dayake cikinta yana rasa yama yakeji a zuciyarsa.
Aleey kuwa kai tsaye tin a cikin daren ya fara shirin tafiyan likitan dazasu dashi sbd ba buqatan jiran komai bayan tafiyar.
Washe gari babu wanda ma ya samu ganinsa kaf har iyayensa kuwa dan sedai ta waya yayi magana dasu yaji ya jikin Sultan din,
Baicewa Ammi komaiba hatta ita Bahar din baice mata komai ba akan cikin kawai ganinta yake mutuwan son yi.
Cikin nutsuwa da kulawa sukai wayarsu suka gama bai nuna mata komaiba sbd kadama ta shiga damuwan dazata sake taba lafiyansu.
A cikin kwanaki biyu Aleey ya gama hada tafiyarsu wadda ba wanda ya sani bayan likita da aka sanar,
Ammi sosai take kulawa da sultan itama duk da hankalinta yana rabuwa sosai rabi akan Bahar da cikinta datake jin kaman ta daukota ta dawo da ita nan gabanta amma kuma bazata iya daukan risk na doguwar tafiya ga Bahar din ba ya sakata ta daure kawai tinda Sakinah kaman itace tana can tana kulawa da bahar kaman zata tayata renan cikin a jikinta.
Ana adduar kwana biyar iyayen haile zuka wucewansa tareda duka sauran yayan Nysah aka bar Nysah din kawai sai daga baya sbd baa zaman gaisuwan komai iya sune kadai a zaune koyaushe cikin kunci da damuwa bama kaman Aslam da meryam da zaa bari su kadai gwanin tausayi ba kowa a tareda su sai bayinsu da zasuyi rayu dasu,
Ga dukiya da daula da dukkanin jin dadin duniya da tarin arziki me yawa gaba da baya amma ba farin ciki ko kadan ba uwa ba miji ba uba sbd har lokacin babu kauna ko kulawa sosai a tsakanin sultan dasu duk da kullum suna bin Nysah da Asim gurin dubasa da gaidasa amma kulawansa da tsantsar kaunarsa tana bayyane ne akan Asim da nysah dan haka duk suka sake shiga damuwa da zama kalan tausayi.
Ranar da akai sati da rasuwan a ranar bayan addua da yamma da daddare Jirgin NUAB zai tashi dan haka a daren yayi bankwana da iyayensa yayi tafiya me mahimmanci abinda kawai ya fada musu.
Bayan tafiyarsa masarautar ta sake sanyi sbd me ita baya nan yayi tafiya sai kuma ya dawo.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
176
Bayan tafiyar NUAB washe gari itama Nysah ta tattara ta koma bayan da ita da Asim harma da Ayanah sun taru sun rokarwa su Aslam yafiya da afuwan Sultan ya kuma sauko ya yafe musu.
Nysah na wucewa shirin tafiya umrah suma suka fara su biyun dan suna buqatan dan tafiya kansu ya sake warwarewa ko zasu dawo ma sai angama bikin kadir da sakinah da aka daga dole sai nan da wani watan sati hudu dai masu zuwa kenan.
Asim ya san da cikinsa da leylah shima take dauke dashi bayan datai rashin lafiyan wuni daya na rashin hutu da kwanciyan hankalin da sukaita fama dashi a kwanakin.
Farin cikin farko kenan daya iya shigarsa bayan rasuwan mahaifiyarsa dan kuwa ya tabbatarda data raye zatafi kowa farin cikin ganin 'dansa.
Su kansu su Aslam yana fada musu murnan jin hakan sukai tareda sakawa cikin wata irin kauna da soyayya me karfi da tsafta sbd sanin hakan na daya daga cikin burin mahaifiyarsu ganin zuriar Asim dinta a duniya sbd soyayyarsa daban take a duka cikin yayanta.
Irin yanda suke nunawa Leylah kulawa ya saka su ayanah sake jin nutsuwa dasu dan haka sai suka basu daman kulawa da leylah din yanda ya kamata hakanne ma ya saka koyaushe idan bata bangarem mijinta tana bangarensu tareda su ana hidima da ita rayuwansu na dan sauyawa daga kadaici da jinsu kaman mujiyoyin da aka ware daga cikin mutane.
***Tinda tayi sallan asuba maa sakinah ta shigo dakinta ta kawo mata tea me kauri sosai da dan cake taci ta koshi ta koma ta kwanta bata farka ba ayau din bacci takeyi sosai sbd ta samu sauki sosai tama warware sbd daman zuba ne cikin yayi kuma tinda ya zuba din bai sake komaiba itama tinda ta gama jinyar kwana biyun ta warware amma sam duk da hakan babu abinda ake barinta yi ko doguwan motsiba bare tafiyan datake son suyi zuwa boyem suma su duba sultan.
Karfe kusan goma na safe ta motsa kadan ahankali tana jan numfashi me sanyi da mutuwan jikin bacci sbd qamshin dataji ya shiga hancinta wanda ya saka jikint sake macewa daga kwancen.
Cigaba tayi da baccin dayake neman yankewa sbd qamshin dayake shigarta har lokacin,
Kai tsaye kamshin ya sake shigarta yana