tsaye takowa yayi cikin sanyi da nutsuwa ya inda NUAB yake zaune ya sai kawai yakai gwiwowinsa qasa ya zube da karfi gabaki daya yana yin qasa da kansa cikin bayyanarda mafi qasqancin yanayi a gaban dan uwansa akan mahaifiyarsa ya dago ya kalli NUAB din wanda yake kallansa da mamaki me tsanani da shock.
Sultan ma dayake kwance cikin wani irin mamakin da karfin hali ya miqawa kadir hannunsa yana son ya tadasa zaune yana son magana daqyar.
Shi kansa kadir shock din ya shiga sbd babu wani jinin boyem da duk duniya yake durqusawa wani idan ba ubangijinsa daya haliccesa ba gurin ibada.
Hannuwansa biyu yakai yana kokarin dafa kafafun NUAB zai bayyanarda tsantsan rokonsa akan sassauci wa mahaifiyarsa NUAB ya riqd hannunsa cak da karfin gaske yana kallansa shima nasa idanuwan suna ja sosai har hannuwansa suna rawa ya bude baki da yanayi me bayyanarda zafin abinda Asim din yayi yace
'Kada ka yadda ka sake durqusawa kowa duk duniya haka,
Kai namiji ne da babu abinda zaka bayyanarda rauninka irin haka harka durqusawa waninka koshi waye'
Sakinsa yayi yana cikin zafi me tsanani a bayyane yana jin baqin cikin shedar da hakan ga wanda yake kalla a matsayin wanda zai mulki boyem.
Shiru dukkaninsu sukai sultan na kallan Asim din a karo na farko da wata irin tsantsar tausayawa me karfin gaske da kauna yana jin inama zai iya sauya kaddararsa zuwa me kyau da aminci ba irin wannan da mahaifiyarsu ta saka su a ciki ba gashi zata tafi tabarsu da kuncin da zai lalata rayuwarsu shikenan ba har abada.
Kadir NUAB ya kalla yace ya karbo masa sako a hannun Aleey.
Asim kasa dagowa yayi ya kalli mahaifinsa da NUAB din sbd jikinsa dake wata irin rawa kowace daqiqa dake wucewa ayau da bushewan jinin jikinsa take tafiya,da hankali da tinani da kwakwalwansa suke tafiya duka yana jin yana rasa kansa wanda bazai taba dawowa daidaiba.....
Zaunawa NUAB yayi tareda nunawa Asim din guri ya zauna ya dago ya kalli sultan wanda shi yake kalla ya bude baki cikin nutsuwa da sanyi da bayyanarda soft yanayinsa na tsananin kaunar jininsa da bai taba bayyanarwa kowa duniya ba hatta mahaifiyarsa batasan yanada wannan bangaren na tsananin son jininsa zuciyarsa sai ayau gaban mahaifinsa da dan uwansa dake kallansa suna neman alfarma da dukkanin sassauci da rahamarsa.
'Ka tin a ranar farko daka bani kurjeranka dan nayi mulkin qasarka ka roke ni alfarma daya daya akan 'danka Asim na inganta rayuwarsa na basa girma da matsayi da mutuncin daya kamace a karkashin mulki na,
Ban baka amsaba sbd ban taba karban kujeran mulkin boyem da riqewa har abada ba,
Shine yake da buri da shauqi da nacin mulkinta tin kuruciyar,
A baya yana son mulkin ne sbd raayin mahaifiyarsa wanda matiqar yana bin kowace irin rayuwan da zata sakasa har abada bazan bari ya mulki boyem ba nima kaman yanda kaima har abada bazaka basa ba,
Ayau sabon mutum ne a gabanmu,
Ayau baya tareda kowane raayi na mahaifiyarsa saina kansa,
Ya kasance me kishi da sanin darajar kai da fatan kawo sauyin cigaba a rayuwansa wanda hakan na nufin zai kawo cigaba da sauyin da ake nema ga alumma,
Mulki da sarauta ba nawa bane,
Ba burina bane,
Yanci da walwalata nake nema bayan kawo sauyi da cigaban da masarautar ke nema kuma wanda mahaifina yake fatan a kawo boyem na kawosu na sauya su dan haka kaddarata zata tsaya ne daga nan sbd zaman boyem da mulkinta ba nawa bane.,
Dawo da idanuwansa da sukai jajir yayi akan Asim wanda yake wata jijjiga me sanyi har lokacin sbd duniyarsa kowane second collapsing takeyi da wani sauti daya ratsa kunnuwansu su duka tsigar jikinsu suka miqe ya ajiye takardun daya amsa daga hannun kadir ya ajiye gabansa yace
'Bazan iya janye hukuncin mahaifiyarka ba sbd hukunci ne daya fito daga bangaren sharia da hukunci na saka hannu ne kawai,
A yanxu babu wanda zai iya janye hukunta kaf duniya amma idan ka saka hannu anan a yanxu zaka zama sultan Asim Almazz zaka iya daga ranar hukuncin zuwa lokacinda zuciyarka zata iya dauka......
Shock ne me firgicin gaske ya shiga dukkaninsu a lokaci daya da sultan baisan lokacinda ya tashi zaune da kyau ba yana kallan NUAB din hannuwansa na rawa,
Kadir ma firgita ya shiga ya juyo gabaki daya yana kallan NUAB din,
Asim kuwa rinte idanuwansa yayi ya bude jikinsa bai dena rawa ba saima wata irin tsananta da yayi abin yana yawa kafin kowanensu yayi kowace yunkuri aka buga kofar bedroom din.
Aleey ne a tsaye idanuwansa jajir ya kalli kadir daya bude ya sanar dashi mummunan labarin daya zo dashi dan isarwa na rasuwan Haile wadda koda aka isa daukanta Allah ya mata rasuwa sanadin bugawan zuciya suke saka rai.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
173
Kaman saukan aradu haka kadir yaji zancen ya dakesa ya juyo da sauri ya kalli sultan wanda duka kofar suke kalla kuma sultan yaji abinda aka fada sbd hankalinsa da idanuwansa dake kofar dan haka rife idanuwansa da sukai jajir yayi a hankali yana jingina bayansa da gado hannuwansa na fara rawa kadan kadan.
Asim kadir ya juya da dukkanin idanuwansa ya kalli wanda ya zubawa takardar gabansa idanuwa yana jin babu komai na kaunar sarauta dayayi saura a zuciyarsa yanxu dan hakanne shima yake da raayin barin boyem yayi rayuwan da babu dauri a cikinta,
Takowa kadir yayi ya tsaya gaban sultan NUAB yana qasa da kansa cikin tsananin girmamawa ya bude baki da alhini yace
'Allah ya karbi rayuwar Queen haile koda akaje.......
Bai qarasa ba Asim ya dago cikin mugun slow na rashewan da duniyarsa ke yi a take ya kallesa yana miqewa da wani irin sauri ganinsa na daukewa ya juya baya ko ganin gabansa ya fice daga dakin koina nasa na jijjigar rawa me karfi.
Yana tinkarar bangaren nata da securities din da aka zuba suka janye sun bar bangaren ana cewa ta rasu sbd babu sauran abinda ya rage musu suyi
Wani sautin ihun kukan Meryam ne da nysah ke amsa kuwwa da amo tin daga nesa ya fara jiyowa kafafunsa suka fara neman sarewa daqyar ya iso bangaren yana shigowa a palonta na farko ya tadda gawarta a rufe gaban yan uwansa dake wani irin kuka me ratsa rai da kunnuwa da tashin hankali.
Zubewa yayi kan kafafunsa yana rintse idanuwansa hawaye na qafewa daga idanuwanta jikinsa na rawa cira ya rarrafo ya iso gaban gawar ya saka hannu ya bude fuskanta yana budewa ya saki rufar yana sunkuyar da kansa tareda dunqule hannuwansa dake fizga yana kasa dagowa.
Gabaki daya yan uwansa su ukun kuka sukeyi mai tsananin gaske kaman rayukansu zasu fita sbd iya su yayanta ne kadai suka sani tukuna dan an hana kowa zuwa bangaren.
Jikinsa Nysah ta fada ta qanqamesa tana kukan da sam bayajin komai shi sbd jinsa da ganinsa sun dauke dip na wucin gadi.
Babu wanda yayi yunkurin shigowa saida aka basu lokaci suna kukansu da tashin hankalinsu na farko tukuna aka janyesu ana ficewa dasu.
Acan ma dakin sultan bayan ficewan Asim kadir ya bude ido ya kalla yana buqatan a kawo wheelchair dinsa a ajiye a kusa sbd dole zaije gurin gawar haile yayi mata addua a matsayinsa na mijinta da harta bar duniya akwai aure a tsakaninsu.
NUAB kuwa shiru yayi yana kasa motsawa bare tashi daga zaunen dayake yana kallo Sultan ya saka kadir ya dauke takardar gabansa ya fice da ita dan qonawa sbd maganar saukansa mulki sam bama zata fita daga dakin ba bare wani yaji dan kuwa a yanxu babu sultan din da boyem take tsananin buqata da so kamarsa dan haka ko baya boyem matiqar yana raye NUAB bazai taba sauka mulki ba sai lokacin saukansa yayi hakama dole a yanxu bazaiyi zaman dindindin a anjom ba zai dawo boyem da Ayanah sbd su tsaya a karkashin mulkin 'dansu dan basa cikakkiyar albarkarsu a ko yaushe.
******kaman yanda masarautar take cikin shiru da jimamin halinda Sultan ya shiga haka ta sake daukan wani shirun na rasuwan haile wadda tini akace ayi shirinta dan janaizarta batareda bata lokaci ba dan babu amfanin sake kwananta a duniya ba rufeba akan tsarin musulunci.
Fadar irin mummunan halin da Yayanta suke ciki da iyayenta da Asim bame yiyuwa bane dan kuwa a abinda bai wuce awanni ba take suka sauya mummunar kama,
Suna ji suna gani akaiwa mahaifiyarsu sutura sai a lokacin aka turo sultan akan kujera baida kuzari ko kadan da lafiya har zuwa bangarenta cikin palonta gaban gawarta da aka gama shiryawa aka fito da ita,
Yayanta ne a zagaye da ita koda ya iso dan haka kowa ficewa yayi aka barsa daga shi sai yayan nata sukai mata addua.
Sun dan dauki lokaci a ciki kafin sultan ya fito aka turasa zuwa komawa bangarensa sbd bazai iya fita janaizar ba daqyar yake jan numfashinsa daidai ma.
Karfe biyar da mintina akai janaizar haile wadda ta tara dubban jamaa dik da anyi janaizar a lokacinda mutane ma basu gama ankarewa da labarin rasuwan tata ba.
Ankaita gidanta na gaskia an dawo kowa ya shige bangarensa sbd bazaayi zaman gaisuwan ba a bisa ga umarnin daya fito daga sultan yasar.
Shi kansa Asim ba iya matan kadai ba shima bangarensa ya shige ba shiga ba fita baya buqatan fitowa ko ganin kowa.
Leylah ce a tareda shi cikin tsananin damuwa da kulawa tana masa addua tana kokarin basa juriya da karfin zuciya da basa addua sbd kada damuwa ta sakasa mantawa da riqe fadan Allah a bakinsa.
Haka aka wuni a masarautar tsit kaman ba rasuwa akaiba tin karfe 8 da mintina kowane sahu ya dauke a cikin masarautar gabaki daya babu motsi ko sautin komai.
NUAB yana bangaren mahaifinsa tareda shi saida ya tabbatar angama basa dukkanin kulawan daya kamata dasu maganinsa tukuna ya fito ya fice zuwa bangarensa ya nufi bathroom kai tsaye ya cire komai na jikinsa ya sakarwa kansa ruwa yana rufe idanuwansa ahankali yana sauke numfashi me dumi sbd daga karshe Allah me iko yayi yanda yakeso ga duka wanda yaso.
Yana fitowa wanka shirin bacci yayi ya haye lafiyayyan gadonsa ya dauki wayarsa dake kan gefen gadonsa ya nemo numbern ghaz princess ya saka kira.
Bata shiga ba dan haka bai damuba ya sake saka kiran har so kusan biyar amma sam kiran baya tafiya,
Time ya juya ya kalla yaga dare yayi dan haka bazai kira maa sakinah ba yaji ko lafiya baya samunta zai bari sai gobe tukuna duk da a yanzu sun saba babu daren da suke iya bacci batareda sunyi magana ba ko a wannan kwanakin dayake cikin damuwa da tension babu daren da basa waya.
Ajiye wayar yayi yana kwantawa ahankali tareda rufe idanuwansa cikin nutsuwa yana sake fidda numfashi da ajiyan zuciyar da tin rana yake saukewa baisan dalili ba.
A daidai wannan lokacin kuwa acan anjom likitoci sunyi nasarar tsayar da ciki bahar din dayake kokarin zubewa cikin ikon Allah,
Su Ammi dake cikin tashin hankali kashi kashi suna jin an samu tsaida cikin ajiyan zuciya suka ringa jerowa a tare suna godewa Allah musamman Ammin datake jin kaman wani barin jikin nata ne zata sake rasawa idan ta rasa jinin dayake asalin jininta dana Abaas kaman yanda suke fada dan kuwa hada yayansu aure ba shine asalin hada zuriarba abinda zaa haifa dinne.
Bacci mai karfi ne ya sauke Bahar din bayan azababbiyar wuyar data sha wanda ta dauka itama mutuwan zatai,
Bayan wucewan doctors din da gama fada musu hutu sosai na kwana biyu take buqata cikin ya sake tsayawa daidai ba abinda take buqata sai cire damuwa kwata kwata daga ranta.
Suna tafiya shiga dakin Ammi tayi tana isa bakin gadon da bahar din ke kwance tana bacci ta zauna tana dafa goshinta tareda shafawa tana jin tsananin kaunarta da tausayinta na wahalar datasha.
Tenya ce ta kwashi kayan jinin da aka lalata sosai ta fita dasu ta bawa su Naima su wanke.
Basu iya fadawa NUAB abinda ake ciki ba dan haka suma boyo suka hau sbd hana sabon tashin hankalin da zasu iya gani idan ya sani.
Kulawa da wani irin tattali na musamman aka fara nunawa bahar din wadda bata farka ba sai asuba,
Maa sakinah ce ta kwana tareda ita dan haka ruwan wanka masu zafi ta hada mata ta shiga ta dan gasa jininta ta jima kafin ta fito ruwan tayi wanka da alwala ta fito tayi sallah tana idarwa tea me zafi da baa saka shuga ba sedai zuma aka kawo mata da naman da aka dafa mata tin dare akai warming taci kadan tasha magani ta koma ta kwanta take wani baccin ya kuma dauketa.
Koda garin ya waye har rana Bahar na bacci dan haka suka sake tsayuwa akan kulawa da ita da cikin da yanzu shine hankalinsu ya taallaka akai,
Ammi ma hankalinta a rabe biyu yake matiqar gaske sbd bugun zuciyarta ya kasa dawowa daidai idan ba sultan taje ta duba yanda yake ba.
Su kansu su maa sakinah da suka fahimci hakan kuma ko babu komai tana tsananin buqatan kasancewa dashi a wannan lokacin da baida kowa a cikin matansa sai ita ga rashin lafiya dan haka maa sakinah ta nuna mata ta wuce boyem din kawai ita zata tsaya da bahar har saita warke sosai dan babu yanda zaayi doguwan tafiya da ita a wannan halin datake ciki.
Su zuhrah ma hakan sukaga ya kamata dan haka suka karfafa tafiyan tata,
Ita kanta Bahar tana tsananin son Ammin ta tafi sbd sultan da NUAB suna buqatarta.
Ganin Bahar din ta samu sauki ba laifi a cikin kwana daya da wuni kuma jinin ya tsaya cak alaman cikin ya tsaya sai kawai ta shirya tafiyar batareda NUAB ya saniba dan kwata kwata ta dena daukan wayansa dan batasan yasan abinda yake faruwa anan din.
Washe gari aka gama komai suka bar anjom zuwa Bahanian babban garin qasar da Airport yake dan bin jirgi zuwa boyem.
Ammi da tenya da zuhrah ne suka tafi sai bayi biyu aka barsu da tarin sauran duka bayin,
Suna wucewa Bahar ta sauke ajiyan zuciya tana jin samun nutsuwa tafiyan Ammin,
Wayarta ta saka Naimah ta dauko mata ta kunna take massages dinsa suka fara shigowa a hankali tana kallansu cikin nutsuwa da jiran su gama shigowa.
Suna gama shigowa babu wanda ta iya dubawa sbd zuciyarta datai rauni dan haka ta saka kiran numbernsa a natse tana sakawa a speaker ta ajiye gefen gadonta tareda zamewa ta kwanta kan gadon datake zaune ta kwantar da kanta a pillow tana jin wayar na ringing har saida kiran ya kusa yankewa tukuna ya daga a natse sbd yana bacci ne wanda bai samu yi ba tsawon kwanakin.
Cikin muryansa da sauran bacci yake cikinta me kauri da wani irin nauyi da bayyanarda zamtowansa cikakke kuma namiji ba kadan ba ya ambaci sunanta da wani irin slow daya sakata bude idanuwanta dake rufe ta zubawa wayar ido.
#MAMUH
09033181070HAYATEEM
Mamuhgee
174
Jin shiru ya sakasa bude baki a cikin nutsuwa ya sake ambatar sunan dayake kiranta dashi ghaz princess,
Ajiyan zuciya ta sake mai sanyi da nutsuwa wadda sautinta ya ratsa wayar ya shiga kunnuwansa ya bude idanuwansa dake da nauyi har lokacin dakyau tareda fidda numfashi me sanyi shima sbd daga karshe ya samu jin abinda ruhinsa yake tsananin buqatan ji wato koda sautin fitar numfashinta ne.
Kasa magana tayi tana ji ya fara mata magana a natse da wani irin kamewa da tsantsar soyayyarta data gama dashi yasan tana jinsa duk abinda yake fada.
Saida ya gama maganar ta fara fidda hawaye sautin kukanta na fita kadan ta ambaci sunansa sai kawai ta kasa cewa komai ta ringa kukan tana jin gabaki daya ma duk batada lafiya.
Shiru yayi sautin kukanta na ratsashi yana tayar da duk wata tsigar jikinsa a hankali zuciyarsa na sosuwa da jin duniyarsa ta tsaya cak ita kadai yake tsananin son gani a gabansa.
Sai datai shiru batareda kowannensu yace komaiba kafin ta bude baki da muryanta data sake tsimar da gangar jiki da zuciyarsa tace
'Yaya jikin Sultan??
Yaji sauki sosai yanzu?
Kana lafiya?
Jinginar da bayansa yayi gabaki daya jikin gadon dayake kai yaji inama baiji muryanta a daidai wannan lokacinba da bazai iya tsallake komaiba ya tafi gareta dan zuciyarsa kawai ta rasa duk wata nutsuwanta yanxu babu wanda zai iya gane kansa matiqar ba saka Sultana dinsa yayi a idanuwansa ba.
Bude baki yayi ya amsa bata da cewa
'Sultan Alhmdlh yana samun sauki'
'And you?? Tafada tana daukan wayar a hannunta tana riqewa da tafin hannuwanta duka biyun cikeda sanyi.
'Ni bana tareda nutsuwa da kwanciyan hankalina,ina tsaye ne kawai but I'm not myself,i miss you to the core My queen and I'm still missing you Ayanah Bahar ghaz'
Wasu hawayen ne suka gangaro mata masu sanyi da tsantsar kaunarsa da soyayyarsa dake cinta itama ta bude baki tace
'Naso biyo Ammi dubiyan amma bazaa barniba saina sake samun sauki inji Ammi'
'Bakida lafiya?
Meya sameki?
Menene yake damunki?
Meyasa bansaniba?
Meyasa ba wanda ya fadamun?
Meyasa aka boyemun?sosai ne?
Girgiza masa kai tayi kaman yana ganinta sbd batasan wace tambayan zata amsaba tace
'Naji sauki ba wani ciwo bane kawai yanayi ne'
Shiru yayi baice komaiba yace mata ta koma ta kwanta ta huta anjima zai sake kiranta.
Gyada kai tayi cikin sanyi tana cewa
'Allah ya qarowa sultan lafiya'
'Amin' yace yana kashe wayar.
Itama ajiyewa tayi gefenta tana sake kwantawa daidai tareda rufe idanuwanta tana samun kwanciyan hankali da nutsuwa.
**NUAB kuwa yana gama wayar ajiyewa yayi ya ziro kafafunsa qasa yana saukowa gadonsa ya nufi bathroom kai tsaye ya shige.
Dukkanin abubuwan daya saba yi yayi yai wanka ya fito daure da towel gashinsa na tsiyayar ruwa ya zari towel qarami yafara gogewa yana nufar gaban dresser.
Shirin kusan mintina talatin yayi harma da qari kafin ya fito cikin wasu Navy blue native kaya da hularsu da suka nutsu iya nutsuwa a jikinsa.
Aleey yana palon farko inda dining room yake yana jiransa table a cike da breakfast da aka jere a natse.
Kallo daya aleey yayi masa ya sauke ajiyan zuciya sbd nutsuwan ubangidan nasa data fara dawowa,
Gaidasa yayi a lokacinda ya iso gurin
Amsawa yayi yana zaunawa kafin masu serving abincin suka shigo a jere suka fara zuba komai a tsare a natse kansu a qasa dan basuda iko ko daman dagowa daga abinda suke sbd baa buqatan kuskure ko daya a gaban sultan me boyem.
Suna gamawa suka fice a natse sukabar gurin sai angama su sake shigowa gyara gurin,
Suna ficewa Aleey ya dauki ruwa ya bude ya zuba a glass cup dake gurin ya ajiye a gaban NUAB sbd babu me taba