Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   9 / 55

24K to 27K   out of 163.1K words

ganni da Jidda sai su yi tunanin ƙanwata ce. Saboda na haifi Jidda da ƙananun shekaru shi ya sa muka ta so kamar ƴa da ƙanwa sannan na mori ƙaramin jiki.

Ji kawai na yi Jidda ta manna min waya a kunne ta ce ga Abba na mgana. Sai da na cire facemark na tofar da miyau a ledan da ke hannuna sannan na karɓi wayar

" Yallaɓai."

"Congratulations My Sady. "

"Congratulations Yallaɓai na."

Na faɗa a hankali ina murmushi.

"Alhamdulillah Allah abin godiya. Kin gani ko? Daman ni a jiki na na ke jin ba ki gama haifa min ƴaƴa ba Sadiya. Yanzu kin aminta da magana ta?

"Na aminta Yallaɓai."

Na faɗa a hankali saboda jikina gabaɗaya ba ƙarfi, faɗi yake yi yana cikin farinciki mai tsanani sai na katse shi da cewa.

"Yallaɓai ban da lafiya. Jikina ba ƙarfi ba na iya cin abinci ba na shan ruwa."

Na ce kamar zan yi masa kuka shi kuma sai ya ruɗe.
"Sannu. Me likitan ya ce! Me ya sa ba su riƙe ki a can ba?
Sai na kasa mgana domin maganar ma wahala take yi mini sai kawai na ce ya bari mu koma gida sai mu yi magana. Dalilin da ya sa ya katse wayar kenan muna ko komawa gida ya sake kira ya na tambayana yadda nake ji.

"Yallaɓai miyau ya yi ta taruwa a bakina. Ni komai ma baya mini daɗi ban iya zama fa sai kwanciya ban taɓa laulayi mai zafi irin wannan ba."

Yallaɓai duk ya damu sai lallashina ya ke yi, daga ƙarshe ya ce zuwa gobe zai dawo na kula da kaina. Sai da ya kashe wayar na ji taruwan kwalla ina tausayin kaina ina tausayin shi ban ɗauka bayan tsawon shekaru goma zan sake samun ciki ba. Amma na yi yaƙini da ubangiji mai bayarwa a lokacin da ya so da kuma wanda ya so. Na saka a raina in ina da rabo Allah zai sake ba ni sai ga shi kuma ashe ina cikin waɗanda Ubangiji ke yi ma Ni'ima in sun yi haƙuri ya ƙara musu a lokacin da ba su yi tssammani ba. Ban taɓa tunanin Yallaɓai zai yi mini rawan jiki in na samu ciki ba sai ga shi yana yi min bawan Allah ya na son haihuwa. Na ɗauka tun da Gimbiya ta haifa masa biyu duka maza yanzu ba ya zumuɗinta amma sai ya kore mini shakku. Lokacin da na faɗa masaa na yi ɓari da ya nuna da yakinin wata rana zan sake samun ciki na haihu bai ɗadani da ƙasa ba kamar yadda bayan samun cikin ya nuna farincikin sa.
Kwana ya yi ya na kirana yana jin jiki. Jidda kam ya yi mata kashedin ta kula da ni ban san adadi ba. Baby da Jidda ta faɗa mata Umma za ta haifa musu wata Baby yini ta yi tsalle da ihu ni dai ina kwance zama ma ba na so ina yi.

Washegari da rana Yallaɓai ya dawo duk da ba gidana zai sauka ba, yana gidan Gimbiya ne tun da ni ranar da zai bar gidana ya yi tafiyar. Amma duk da haka gidana ya fara sauka ya duba ni ya iske ni kwance da gwangwani miyau da a ka cika min da ƙasa. Ya rumgumeni nima na lafe a jikimsa shi ina sauke numfashi. Yallaɓai ya yi ta shafa marata kamar ya buɗe ya ga abin da ke ciki. Shi kan shi ya ce na rame bakina ya bushe ya yi ɓawo to ko ruwa fa ba na sha sannan ban iya cin komai sai kunin tsamiya.

Duk bakina da surutu na bakina ya mutu. Allah ya sa Jidda na gida ita ke kula da gidan da yin abinci. Yallaɓai ya faɗa ma Gimbiya ina da ciki ya kuma kawo ta ta duba ni ita da su Khalipa, ina kwance ne ina fama da kaina a saman kujeran falon su Jidda. Ina kallon Gimbiyar tun da muka gaisa ta koma gefe ta tsume. Duk da ban da lafiya amma na fahimci kamar ranar ranta na bace ne, sai na danganta haka da ƙila ita da Mijinta ne. Ko jiran shi da ya ce ta yi ma ba ta yi ba, la'asar na yi ta ce min za ta ta fi wai za ta biya ta shago. Su Khalipa ma da Jidda ta ce ta bar su sai ta ce wai daga Shago Gwammaja za ta biya shi ya sa ba za ta bar su ba. Ni dai ina kwance amma sai da na tofa na ce ta bar su mana in Yallaɓai ya dawo sai ya mai da su amma sai ta ce kar wai su dame ni ba ni da lafiya. Ina jin haka ban takura ma kaina ba na ce su gaida Nene in sun je.

Tun kuma daga ranar sama da sati ba ta dawo ba na tuna lokacin cikin Khalipa da kwanciyar da ta yi ta yi a asiniti ina jigila da ita. A raina na ce da ban haihu ba da na ji haushin duniya. Munnira ce ta kira ni a waya tana faɗa mini haihuwar Salma Yayar Jawahir C.S a ka yi mata, a ranar da ta kira ni ta ce jiya da daddare ne ta haihun shi ne ta kira ni ta ji yaushe za mu je! Tun da anan Kano ne a Dala. Shi ne na ce mata ba ni da lafiya ma ina gida. A ranar ta zo duba ni kafin in faɗa mata ina da ciki ita ta fara cewa matar injinya ciki ne da ke na ce mata e sai ta buga shewa ta riƙe hanci ta rangaɗa guda ta kuma kira Hauwa tana faɗa mata sai Hauwa ta fara faɗa min an ware ta ba a faɗa mata ba. Ni ko na ce ba wanda na sanar ma wa, nan Munnira ta yini har da lissafin sai ta ɗauko DJ ranar sunan na yi dariya kawai a raina na ce Allah ya sa na rabu dai lafiya.

Washegari sai ga Hauwa ta zo duba ni. To su ne da aka haɗu ca gidan Salma ranar suna duk wanda ya ga bai ganni ba sai su ce ina gida ina fama da laulayi. Anan ne wasu suka ji, su Anty Bahijja kuma ina da tabbacin Gimbiya ta faɗa mata gwara ma Anty Maimuna in ta ce ba ta sani ba amma zai yi wahala Anty Bahijja ta ji abu ita ba ta ji ba musamman za ta kira ta a waya ta faɗa mata. Anty Zuwaira har gida ta zo ta duba ni ta ba ni dubu ashirin ta ce na siya gero tun da na ce kunu kawai nake sha ina son ta saboda wallahi tana da matukar kirki shi ya sa nake girmamata. Ita ta ce mini Nene ce ta faɗa mata ba ni da lafiya ta zo ta duba ni, Nenen kuma na san Yallaɓai ne ya sanar da ita. Mubeena na zuwa duba ni akai akai har Marwa ma ta zo ita kuma Kawu ne ya faɗa mata ita kuma ta yaɗa ma Ya Aina ta nan maganar cikina ya faso a dangin mu kowa ya ji sai ya ce ikon Allah lalle bayan wuya sai dai daɗi sannan ba a cire ma Ubangiji yaƙini in ka yi hakuri za ka ci riba. Sun zo dukkansu sun duba ni har da Ma'u Gwaggo ma ta zo har gida kuma na ji daɗi su Ya Hamza a waya suka gaishe ni da matan su. Zainatun Ya Abubakar ta zo yi min yini, ta yi mini wanki da girki ranar.

Ranar da Nene ta zo ita da Hajiya iya da Maman farko a raina na ce duk abin dake cikina ɗan gata ne. Tun da har su Nene suka zo duniya. Nene ko faɗi ta ke yi Allah ya raba lafiya. Amma ko su kan su sun yi ta ƙorafin rama ta da rashin cin abinci na ce komai na ci sai na yi amai kuni kawai ke zama a cikina shima mai zafi. Ruwa ko rabon da in sha har na manta. Yallaɓai tsausayina ya ke yi sai ya ce ya za a yi ɗan adam ya rayu ba ruwa na ce to ga shi dai ka gani. Gimbiya sau ɗaya ta dawo shima ba ta daɗe ba ta tafi sai na ga kamar ba ta murna da samun cikina. Amma sai na yi saurin cire tunanin haka a raina sai na yi mata uzuri na kuma saka mata kyakyawan yaƙini. Inna Mariya ni da kaina na kira ta na faɗa mata ta yi ta murna ta kuma zo har gida ta duba ni.

Ko da nake kwance in ana son Hijabai ko kaya Jidda ke mgana da mai ɗinka min daga Zaria a kawo kuma ta zauna duk ta saka musu sticker ta kuma saka su a ledojinsu shi ya sa ba ni da damuwa. Na shafe wata ɗaya da wani abu ina wannan zazzafan laulayi sannan na ɗan fara samuwa. Na fara cin abinci tuwo haka sai ɗanwake sai awara sai dambu, amma ban da su shinkafa da taliya. Duk sona da fura da kayan marmari na daina son su yanzu, ruwa kuma na fara sha amma sai mai sanyi ko na ce mai ƙanƙara ya na narkewa ina sha. Yallabai ya yi ta faɗa wai sanyi zai kamani amma shi kan shi da ya ga shi ne ruwan da na ke sha sai ya ƙyale ni. Na ɗan fara samuwa tun da na daina kwanciya kasalar sai dare ya yi yanzu ta ke nika min jiki, sannan tun da na fara laulayin nan ban yadda mun yi ɓarnan ruwa da Yallaɓai ba to ina ta kaina. Shima kuma bai matsa mini ba, kuma bai sani ba kwata kwata abin ne na ji ba na ma son shi. Na ɗan fara dan kiɓan kumatu amma fa kaya na duk sun yi mini yawa. Na faɗa a raina na faɗa asarari da cewa wannan cikin ɗan gata ne shi ya sa ya ke wahalar da ni. Amma dai na ji sauƙi sosai ba kamar kwanakin baya ba.

Cikina na wata uku cikin na huɗu aka fara hidiman bikin Sulaihat ɗin Anty Bahijja. Matar nan ba ta zo ta duba ni ba duk da ta san ba ni da lafiya. Amma dai Anty Maimuna ranar ta biyo Nasara sun taho tare. Da Anty Bahijja da Halima ba su zo ba daman ita Halima tuni ta koma bangaren Gimbiya. Yarinyar nan mun sha haɗuwa a Gwammaja ko sha'anin su ta yi kamar ba ta ganni ba. Wai ni ce Halima ta ke gani ta wulaƙanta, lalle na yarda rayuwa ta na cike da mutane masu abin mamaki. Yadda ba a saka ni a shirye shirye ba, ban tusa kaina ba an dai fidda ankon mother eve da na yinin biki. Yallaɓai ya siya mini tun da matarsa ce ta ɗauko Gimbiya. Jidda kuma Anty Zuwaira ta yi mata tare da sauran sa'aninta su Farhan Anty Maimuna Baby ma su suka yi mata, ni ina fama da kaina ba ma ta kan bikin na ke yi ba, bikin zai kama babbar salla saura kwana tara ne.

Na dai san Kaduna za a kai ta. Bikin kuma zai yi jama'a tun da har Anty Zabba da muka yi waya ta ce za su zo gabaɗaya har da yara tun da ba makaranta. Sannan kaf su mazan gidan da ke zaune ne sa za su taho da matan su. Matar Jafar ce kawai ba za ta zo ba ita za ta tarbi bakin nan in ji Anty Bahijja, nima duk a bakin Munnira na ke jin wasu labaran a bakin ta na ji su Gimbiya su ne ƙirjin biki sannan har list an yi na mutanen da za a tafi da su a kaduna. A dalilin ina fama da kaina ban ji a raina zan je kai Amarya kaduna ba, ko da ma ina lafiya ba zan tusa kaina ba.

Ban je gidan bikin ba ma sai ranar laraba da a ka yi mothers eve ɗin. Yallaɓai ma cewa ya yi in ba zan iya ba na yi zama na su Jidda su tafi sai na ce zan iya. Tare da su Hauwa muka tafi can muka iske matar Muhammad Kabir Nafisa har Faridan Tariq ta zo Marwa ma ta zo muna tare da ita tun da gidana ta sauka. Anty Bahijja ta sha gayu ka ce ita ma Amarya ce da ƙawayenta suma yan gayu su Gimbiya ana ta shiga da fita har makeup ta yi su Khalipa ma an sha gayu. Anwar ne ma na gan shi a hannun Baby ta na fama dashi,
Ni dai na je na gaishe da uwar biki na yi mata fatan alheri shi ne ta ke ce mini an ce ba ni da lafiya na warke kenan na ce mata Alhamdulillah.

Kowa ya ganni sai ya ce na rame amma fa na yi shar da ni. Suwaiba kam har sai da ta ishe ni wai ban ga kyan da na yi ba ne ko Tafida ya ganni kafin na fito na ce ban sani ba. Mun haɗu da Gimbiya amma ba ta minI mgana ba da cewa ita ta na fama da jama'a ba ta ganni ba ni ko na ce ba zan bi ta domin mu gaisa ba. Ita da Najan Anty Zuwaira ne akan komai kuma suma sun ui gayyar ƙawayen su irin su yan gayu kirari kawai suke yi mata tun da kusa damu suka zauna a haraban gidan in da aka saka kanofi da kujeru. Su Ma'u ana gefe ba karsashi to ta ga iyayenta a kinibibi dole ta koma baya.

Gimbiya suke ta raba takeaway da snack a ciki da naman kaza sai ruwa da lemu. Da ta zo wajen ƙawayen na su sai shewa ya hau ta shi ana yi mata kirari.
"Ka ga Saudatu sa'ar mata. Gimbiya kike sunan ki ne. Kuma kin cika Gimbiya a zuciyar Injiniya Yusuf Tafida. Takawarki lafiya giwar Tafida. Takawarki lafiya Amaryan Tafida. Takawarki lafiya uwar maza a gida ko da kika je an haihu amma ke da kika tashi sai kika yi irin haihuwan da ba a taɓa yi ba. Ka ga uwar maza a gidan Alhaji Yusuf Tafida. Ko gobe aka sake masa haihuwa ba za a kwantata irin ta ki ba"

Sai suka buga shewa ta miƙa hannu suka tafa ta jiya musu kugu kafin ta ce" Wallahi ko gobe aka sake masa haihuwa ba za ta kama kafar irin tawa haihuwar ba faɗi ki ƙara."
Ta faɗa ta na wani fari da ƙara juyawa.
"Takawar ki lafiya ki juyi dai Gimbiya a girman ki ne. Kin ci lokacin kuma za ki ci na wasu in sha Allahu kuma daga kanki ba ƙari kin cika duka gurbaben mata huɗun nan"
Sai kawai ta ɓalle jaka ta fara zazzaga ma mai yi mata wannan kirarin kudi suna ta ihu da shewa sai hankula duk ya koma kan su.

Duk da Maganar suke yi amma ko waye ya ji ya san magana ce mai harshe damo ko na ce habaici.
Hauwa ta kalleni ganin na yi shuru kawai ina zaune.
"Kamar fa da ke suke. Wai ko da ta zo an haihu amma ba a yi kamar irin ta ta ba"
"Kuma wai ko da an sake haihuwan ba za a sake irin ta ta ba"
Munnira ta amshe itama.

"Da Sadiya fa suke yi. Shi ya sa na tsani Gimbiyar nan munafuka ce baƙn ciki take yi kin samu ciki ta so ne ita ta yi ta haihuwa ke kuma ki zama yar kallo."

Hauwa ta saki tsski kafin ta ce" Wallahi haka ne ma. Sai kin ji mganganun da take zuwa gida ta na yi. Ta yi ma Tafidan da Dangin sa haihuwan da ba a taɓa yi masa ba. Tun da ta haifi maza har ji fa na yi wai ta ce yadda ya ke son su Khalipa ko su Jidda albarka."

"Ka ji sakarya. Ya fara samun su Jidda? Ai wallahi ƙarya ta ke yi.'

Baƙin ciki suka hana ni mgana amma na daure jin Munnira ta ce wallahi za ta tashi ta je ta yi musu mgana sai na riƙe ta ina faɗin" Rabu da su so suke a tanka a yi wani abu kuma ace ba mu da gaskiya ku ƙyaleta. In za ta je ta faɗa ma duniya cewa Yallabai ma ya fi son ta a kaina ni bai dame ni ba. Fatana na sauka lafiya."

"Allah ya sa ki haifi namiji na ga ta tsiya."

Sai na yi mirmishi ina tuna wayar da na yi da Dr. Aisha AKTH. da na faɗa mata ina da ciki ta yi murna karshe ta ce Allah ya kawo boy ni kuma na ce mata ko boy ko girl duk wanda ya Allah ya bani ina iso.
Yanzu ɗin ma cewa na yi.

"Ko namiji ko mace duk wanda Allah ya ba ni iso."

Suna kallona sai na kaɗa kai kafin na ce" Ni ba ruwana da jinsi Ni ko duka mata zan tara ina so. Ita haihuwan maza ke gabanta."

Daga nan na kashe maganar. Amma har Suwaiba sai da ta zo wajen mu ta na zagin Gimbiya a cewarta ni ban yi kishi da ita ba ita da ta aure mini miji sai ita. Ant Zabba ba ta wajen da ya ke so sun iso har da Amaryan Usman ɗin itama da tsohon ciki za ta yi haihuwa na uku kenan itama kamar Gimbiyar gwarne take yi. Da ta zo wajen mu ta ji ana mai da zence ta yi ta mini masifa ta na faɗin ina da sanyi na daina sanyi da kishiya za ta rika cin kasuwarta a kaina na yi dariya kawai ban ce komai ba.

Sun yi fa abubuwa Gimbiya da gayya ta ke komai amma ni ban biye mata, sai mangariba a ka tashi sai a lokacin Ant Zuwaira ta zo tana zuwa kuma ta nemo ni ni da Munnira da Anty Zabba ta ce mu shirya da mu za a je Kaduna kai Amarya.

"Anty Zuwaira ina fama da kaina'"

"Ai kin ji sauƙi ko ba za ki iya zuwa ba ne?

Sai na kasa musa mata sai ta buga kafaɗata da cewa" Ku ne matan kawunne manya saboda haka da ku

9 / 55